Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 3
Camerou da England kuwa" "Shakka babu , na kauracewa halartar kowanne kallon wasa,don matukar tsoron haduwa da farida" Ya dan kalli fuskata ,kallon dana so nasan abin da yake nufi. "Ba mamaki kaima kuhadu da ita acan" Nafada ina kallon fuskarsa,bai yi magana ba amma yanayin fuskarsa na nufin shakka babu da mamaki. Shuraih Usman A daidai wannan lokaci sai zuciyata takara kadawa sabida ganin meenat sanye da atamfa,riga da zani ruwan madara,ta nufo in da muke . A wannnan lokaci dana ganta sai dana tsorata ,a tunanina farida ce ta rikida takoma karama ,domin idan ka san farida,kana ganin meenat ka ga kanwar farida. Ta na zuwa ta rakabu da jikin nasir,tana kallon fuskata. "Habib ! Ko zan sami kasa-kasan fim din hausa a wajenka?" Nasir ya bukata. "Shakka babu,amma sai dai a gida ,idan kanaso zamu iya zuwa" Dani dashi da meenat muka nufi Gandun Albasa. "Habib mama ta gayamin wai a kamfanin jaridar dankari kake aiki" "Shakka babu" "A jaridar ne ake buga labarin BABBAR MAGANA ko ? Agaskiya akwai matukar rikitarwa ,da jefa mutane cikin rudani,kuma kagaya yi daidai da abin dake faruwa akanka " "Shakka babu ,maganarka ba musu" Nafada lokacin dana shigar da motar haraban gidan ahmad. "To mene ne dalilin dayasa kai baza ka buga wanda yanzu yake faruwa akanka ba ?" Nasir yafada lokacin da muka fito daga motar. Shuraih Usman "Saboda babu wanda zai yarda da ni" "BABBAR MAGANA ma da farko mene ne jama'a basu fada akansa ba " Har sai lokacin da aka karanta karshen labarin" Bayan munci abinci saina bashi MUNKAR da TSUNTSU MAI WAYO da kuma SAI DAI MUTUWA. "Baka da NAIRA DA KWABO?' Yabukata "Wallahi bani da shi nasir ,sai dai nahada ma da littafin SAI DAI MUTUWA da kuma WUYA BA TA KISA" Fatima na ganin meenat tace kanwar faridace,haka ma faruk(BBJJ) da bala Barde,muna fitowa zamu tafi suka ce meenat kanwar faridace . Abokaina ne kuma sunga hotonta a wajena . SIRRINSU Littafina daya Chapter 14 By♥ Shuraih Usman Abin mamaki da rikitarwa ya farune adaidai KANO LINE a kan hanyarmu ta komawa tarauni don kaisu nasir gida. Kwata-kwata nasha'afa babu wadataccen mai amotar ,kawai sai ga ni nayi malejin mai nayin nuni cewar mai yakare ,yayin da motar ta tsaya . A lokacin karfe biyu da rabi,ina sauri na kai su nasir gida don ganin wasn England da yake da niyyar zuwa. Sanin cewar akwai 'yan cuwa-cuwa a diga ,sai muka nufi can don sayowa ,nasir rike da hannun meenat. "NASIR ! NASIR !! KAGA ! KAGA !! Arazane meenat ta rinka fada ,tana nuna wata mota kirar volvo da mata biyu keciki. ""FARIDA ! FARIDAAAAAA......" Shima Nasir arazane ya rinka fada ,idanuwansa sun zazzaro ,farida ce ke tuka motar,kodaddiyar matar agefenta kuma titin sabo bakin zuwo suka nufa ,inda muma zamu. Lokacin danayi kokarin duba lambar motar,zundumemiyar harafin "L" ne a makale. Shakka babu meenat da nasir sunyi matukar razanar da tunda suka shaki iskar duniya basu taba razana fiye da haka ba. Shuraih Usman Cikin gaggawa jikina na rawa ,na tsayar da wata taksi babu kowa aciki . Don kada ya bata mana lokaci nazaro damin kudi na bashi, na nuna masa motar ta fara nisa ,nace duk inda tayi yabita . Na saka meenat wadda duk ta fice daga hayyacinta a motar ,sannan shima nasir afirgice na kama hannunsa muka shiga motar. Cikin zumudin da na ba shi ,direban ya zaburi motar cikin matsanancin gudu. A daidai lokacin da muka isa garesu ,sai motar ta shiga matan fada road,kuma adaidai lokacin danja ta tsayar da mu. Cikin matsananciyar gaggawa direban ya kutsa kan motarsa, GARAM!!! Yakade wani dan acaba da zai gifta ,dana duba motarsu farida sun bace. "Shit!" Na fada lokacin dana daki kan motar. A ranar kallon wasan da nasir bayyiba kenan sai da aka masu allurar bacci sannan suka sami nutsuwa. (Lol sun karyata sun ga zahiri) Duk da ina kara razane,sai son farida yadada karuwa a zuciyata .shakka babu ina matukar sonta. Shuraih Usman H JUMA'A 9 ~ 3~ '99 Juma'a babbar rana , wannan juma'ar shakka babu ,koda wani bata zama babbar rana agareshi ba ,a wajen Al'ummar kasar Nigar babbace . Domin da sanyin safiyar juma'arne ,shugaban kasarsu BA'ARE MAINASARA, ya koma ga mahaliccinsa . Sakamakon ruwan harsashi daya fuskanta daga jami'an tsaronsa. Fantsamuwar labarin a duniya keda wuya ,Ahmad yaga muma yadace musamawa jaridar DANKARI kanun labaran tun da dumiminsa. An katse gidajen rediyo,an hana jirage tashi a kasar Nijar, wanda hakan na nufin dole muyi amfani da mota idan muna bukatar shiga kasar. Kada ka dauka mun samu shiga kasar cikin sauki,bayan nune-nunen shaidar cewar mu ma'aikatan jarida ne ,saida wasu kudade daga aljihunmu sukayi balaguro zuwa ga aljihun masu tsaron boda. Shuraih Usman Bayan munyi yanzirga zirga nan da can ,mun kalato abin da muka dawo kasar Nigeria . Duk da cewar Ahmad yayi tukin motar , jikina ya samu wadatacciyar gajiya . Karfe hudu da mintuna takwas,muna cikin birnin dabo a wannan lokaci rana tafara sanyi sai dai babu wani alamar sanyi a zuciyata da kwalkwalwata . Har muka je Nijar muka dawo,zuciyata taf take da tunanin farida ,da kuma tunanin halin da meenat da nasir suka shiga . A wani bangaren zuciyata na so faruwar hakan saboda shakka babu Nasir,da meenat da kuma mahifiyansu za su fi gaskata al'amarin,domin gani ya kori ji. Bayan nayi sallah naci abinci wanka yabiyo baya bansan lokacin dana zurfafa a zuzzurfan kogin bacci ba . Ba don fatima ta tasheni ba, daban san lokacin farkawata ba . Saboda wadataccen baccin danasamu darana ,da daddare sai barci yayi hijira daga idanuwana. Karfe tara daidai naji ina matukar sha'awar fita yawan shakatawa,SULJAM PALACE shine wajen da kai tsaye yayi ungulu a zuciyata. Shuraih Usman Sai dai da nasan akwai mummunan al'amarin da zai sake faruwa akaina dana hakura . Sai bayan dana samu wasu lokuta zaune wajen su nasir ,don ganin halin da suke ciki. Ina fitowa da niyyar tafiya tarauni ,sai ma'aikacin wajen ya zaburo a guje yagaya min wai wasu mata na kirana a ciki. "Wasu mata?" Na rinka maimaitawa har lokacin dayanuna min inda suke zaune . Sannu a hankali zuciyata na mamakin kiran na karasa inda suke. "Wa nake gani kamar habib ?"Daya daga cikin mata uku dake wajen ta tambaya. "Idan dai ba wanine yayi kamama dani ba ina ganin shakka babu nine "na fada lokacin dana fahimci raqeebah da saratu da kuma jameelah ne ,dukkaninsu 'yan unguwarmu ne . "Dama kana zuwa irin wadannan wuraren?" Saratu ta bukata ,lokacin data kurbi tataccen lemu. "Ku yakamata nayi wa wannan tambayar " nafada. Lokacin dana zauna kusa da su raqeebah. Shuraih Usman "Saboda me kafadi haka ?" "Saboda da namiji yana da yancin irin wadannan wuraren musamman ga irinmu marasa aure ,amma ga mace ziyartar gidajen kawayenta zaifi mata martaba akan irin wadannan wuraren" "Kiji son kai" jamila tafada . "Wato ku maza ku zo ku nemi mata koh? Mukuma mata mutafi gidajen kawayenmu?kana nufin kenan mu muje muyi soyayya atsakaninmu ko? To waye baya son hutu ! Koda dutse aka halicci mata ?"(Kujifa yan'uwa) Dukkaninsu sai suka kyalkyale da dariya . " Baki fahimci abin danake nufi ba ,ina nufin kamar yadda yake al'ada ,idan har akaga namiji a irin wadannan wuraren,kawai ana daukarsa mai neman matan banza. Koda kuwa ba hakan ne ya kawoshi ba .to ina ga mace ?da zarar an ganta cewa za'ayi 'yar harkace ma'ana mazinaciya ce" Shuraih Usman Wannan hirarce ta jawo mana musun da ya sha'afar dani harsai dana fahimci daya da rabi na dare ,sannan hankalina ya tashi ,banzo da abin hawaba . Nafito cikin hanzari ina tunananin komawa gida ,sai motar da muka gansu jiya aciki VOLVO,haryanzu zundumemyar harafin "L" din na makale ,suka gifta ta daya bangaren titin. "Farida !"A kidime na kwala mata kira ,sai dana kirata na fahimci gaba dayan gilasan motar arufe suke ,ina rufe bakina sai dan-acaba ya bayyana . Kamar yadda nayi wadan taksi,shima sai naba shi kudi ban san nawa bane , na sanar dashi yabi dukinda motar tayi. SIRRINSU Littafina daya Chapter 15 By♥ Shuraih Usman Hikimar yin hakan zaka ga kasamu biyan bukata da wuri ,don kada a bata lokaci wajen tsadancewa ,sannan idan da zargi a zukatansu,kudin zaiyi saurin fatattakarsa. Ratar dake tsakaninmu bata da yawa sosai ,kasancewar babur dinsa Yana da ingancin inji ,sannan Kuma farida ba gudu take sosai ba. Babu abinda yayi saurin bani mamaki ,irin yadda na gane su farida nan da nan. Suna zuwa wajen wasu yansanda dake tsattsaye kan titi ,mummunar matar ta mika musu kudi ,suka Kuma kyale su suka wuce. Don gudun kada muma su batamana lokaci ,tun kafin mu karasa na zaro kudi ,muna zuwa wajensu na mika musu muma suka kyale mu muka wuce. Haka muka yitayi,duk yansandan da msuka taremu sai mun basu kudi , Har sai da motar su farida ta shiga harabar VILLA GUEST INN . Kai tsaye na umarci dan-acaban, shima ya shiga ciki. Cikin sauri Dan acaban yafice daga wajen bayan na sauka ,don gudun kada nabukaci ,wasu daga kudin Dana bashi. Sai da mummunar matar ta fito daga motar ,sannan na fahimci a matukar buge take . Ganin yadda take tangadi, har sai da farida ta rika taimakamata. Suna shiga reception din, ma'aikacin wajen ya mika wa farida makulli ,wanda na nufin makullin dakin da suke ne. Nayi sauri na zaro kudi daga aljihuna ,nanufi inda yake. Shuraih Usman "wannan kyakyawar yarinyar nakeso ,Kuma na tsara ta yarda ,Amma wannan matar da suke tare ta kawo mana cikas .lambar dakinsu zaka gaya min" Nafada lokacin Dana mika masa kudin . Kafin na san me yayi tuni ya rarume kudin daga hannuna ,kamar yadda kadangare ke yiwa kuda cafkar bazata . "No. 11, dakin dake fuskantar yamma ,daga hannun damanka " Ga mamakisa sai yaga na fice daga wajen ,har na fito Yana lekena .nasamu dogon lokaci ina tsaye ina tunani. "shin menene hadin farida da wannnan mummunar mata ? Nasir yabani tabbacin basu da wata yar'uwa datayi kama da wannan matar ,kai kanta kallo daya zaka yi wa matar kasan babu abin da ya hada ta da farida . Ganin farida danakeyi kullum Akano ya tabbatarmin suna Kano . Abin tambayar shine ,shin akwai wajen dasuke zaune musamman ? Kokuwa tun farko anan Villa guest inn din suke ? Wannnan tamabayar ma'aikacin yadace nayiwa. Banyi mamaki Dana tambayeshi yace yaune zuwansu na farko ba . Kuma sannan kudin kwana daya kawai suka biya ba. Motocin dasuke shiga ina suke samunsu ?farida ta mutu, Kuma kullun suna tare da wannan matar. shakka babu akwai wani kullallen al'amari tattare da matar nan .domin kana ganin matar ,kasan ba mutuniyar kirki bace ,yanzuma ba acikin Maye nagantaba? Shuraih Usman Kuma kana ganin farida kasan bata yi kama da mutuniyar banzaba . Wani bangare na zuciyata ya shawarceni da kai tsaye na wuce wajen yansanda na sanar dasu cewar ,ina zargin wannan matar da sace farida . Tun da iyayenta da kannenta na Kano . Kuma zasu gane yarsu ,tunda dama sunganta sun ganeta ,shiken sai azo acafke matar . Daga nan Sai a sani shin faridar data mutuce kokuwa ? Wani bangare na zuciyata ya bijirewa wannan shawara da cewa na fara sanar da mahaifiyarta . Mu zo mu kama . Sai mu tuntubi hukuma . Kuma da wannan shawarar na yarda , nayi ta jiran Dan-acaba . Har sai Dana fitar da rai da samu Shuraih Usman A daidai lokacin da tsinken agogona ya tsaya akan biyu da minti dudun dare ,saina hangi hasken fitila na nufo ni, sai daya kusa zuwa na fahimci babur ne . Babu Irin daga masa hannun da banyiba ,don ya tsaya ammma ko alamar tsayawa bai yi ba . Inda Allah ya taimakeni sai a she sabi'u ne da muke kira [lastman]. A wajensa ne muke sayen katin duk wani wasan kwallon kafar da ake gudanarwa indai anan Kano ne. "lastman!lastman!! Na rinka zunduma masa kira har sai da jiyo sannan ya Dan tsaya . Abin daya sana tsayar da shi ,na sani sani sokoto road yake , tun dani tarauni zanje sai na yi farincikin hakan . Komai dare komai dare nayi niyyar sanar da mahaifiyar farida inda farida take . Don gudun kada na tafi gida kaddara tasa na makara ,kafin naje tarauni su Kuma su kama gabansu "Dan Allah wasu muhimman takardu ne na manta su a tarauni ,Kuma a Daren nan ake bukatarsu ,ka taimaka ka ajiye ni a nan sokoto road din sai na karasa" Na yi masa karyane don gudun kada ya cikani ta tambayoyin me zan je yi atarauni?bayan ya san unguwarmu . Shuraih Usman 'bawani abu hau mu je " Yafada kafin yarufe bakinsa na dare Vespa din, Saboda ,matukar kaguwa Dana yi ,na ganni a tarauni. Har muka zo sokoto road bamu sokoto road bamau hadu da yansanda ko daya ba . "tarauni wajen ina zaka ?"ya tambayeni. "kasaukeni anan na karasa" Ba wani abu na karasa dakai " "masallacin juma'a na tarauni zani" nafada. ya ajiyeni adaidai masallacin sannnan ya juya . "nagode " nafada . "bawani abu ,Allah ya bamu alkhairi." Banda haushin karnuka da ke tasowa nan da can , babu wani sauran motsi da kunnena ke iya ji . Dayake na gane hanyar da muka bi jiya da sulaiman ,sai na bi har kofar gidan . Koda irin 'yan tauran dake yawon dare , ban gani a layinba ,kowa ya garkame kofar gidansa,kamar har abada bazasu kara budewa ba . Nayi ta faman kwankwasa kofar gidan har na gaji ,in da kasan kofar makabarta nake kwankwasawa, babu wani motsi da ya biyo baya .ganin haka sai na hakura ,da niyyae zuwa bakin titi na samu babur na koma gida, nayi matukar kokari na dawo da asubah. Ina zuwa daidai masallacin juma'a .sai wata bakar Peugeout ta tsaya a gabana ,tun kafin su fito na fahimci......................................... SIRRINSU Littafina daya Chapter 16 By♥ Shuraih Usman Ina zuwa daidai masallacin juma'a .sai wata bakar Peugeout ta tsaya a gabana ,tun kafin su fito na fahimci ,yansanda ne ,Kuma nayi matukar bakin cikin manta I.D. CARD dina a gida . Subiyu ne a motar , mai kakin 'yansanda ajikinsa shine ke tuka motar ,fari kakkaura mai gashin baki . Nakusa da shi Kuma baki kakkaura Mara gashin baki,sanye da fararen kaya. "hey !daga ina ! Zaka ina a wannan tsohon Daren?" Kafin na amsa masa tambayoyin da yayi min, bakin ya fito ya cafi kuguna . "shegiya ! Barawo ,sata zata " yafada lokacin da yake kokarin turani motar . "officer" nafada ,ina son yimusu bayani. "close your goddam mouth" bakin yakara zunduma min tsawa a sukwane ,lokacin Dana shiga motar . "in banda barawo , me mutum yake a waje har yanzu bai kwanta ba ? " Dansandan mai kaki ya fada , wanda sai daga baya na fahimci ashe D.P.O ne . Shuraih Usman Ni dai bance musu komai BA ,kawai ni dai abin daya dameni, kada su farida su kubuce min . Yanzu idan aka kulle ni kafin mana fiti kawai su farida sun min adabo. Kai tsaye D.P.O ya nufi kasuwar tarauni kamar akwai abinda yake nema ,ya zazzagaya kasuwar , sannan ya tuka muka hau titin maiduguri, kana ahankali ya gangara da motar muka shiga layin farko na kusa da lambun tarauni. Ya tsayar da Motar a daidai shagon wani gida ,da wani saurayi sanye da gajeren wando ke shan sigari. D.P.O na fitowa saurayin na fahimta dan sandane .YIP " yafada shagon a tsorace tamkar wanda yaga mutuwarsa . D.P.On bai tsaya bata lokaci BA yabi bayansa, yayin da dayan ya fito daga motar ya tsaya Yana gadina . Babu yadda D.P.On bai yiba don Yafito da saurayin Amma abin ya faskara . Sai ya fito bakin kofa ya umarci dayan ya shiga ya fito da shi. Shuraih Usman Bayan ya shiga , sainaga kwata-kwata hankalin D.P.On ya tattara akan shagon, sakamakon bololon da saurayin keyi. "baba! jamilu ! Wayyo niba barawo bane " Kai idan kaji burarin dayake cikin tsakar dare ,sai ka zata ana kai shi harbe shi za'ayi. Sannan a hankali jikina na rawa , Na bude motar na rufa aguje kamar zantashi Sama . Na sami dogon lokaci ina gudu , sannan na hango hasken fitilar motar na haske min gaba . Nayi matukar gajiya , zuciyata kamar ta faso kirjina ta fado ,sannan tsabar haki yariga ya gama da ni ,Kuma nasan idan har suka kama ni hukuncina sai yafi da tsananta . Saboda babu abin da 'yansanda suka tsana irin su kamaka ka Kuma gudu. Da kyar na sha wata kwana kamar zan kife , ina shiga kwanar dabara tazo min nashiga cikin wani katon tanki dake ajiye kofar wani gida . Sai Dana shiga na fahimci shara ake zubawa a cikin . Sun dade suna zazzagaya unguwar don nemana ,ni kuwa ina cikin tankin gabana na dakan sittin sittin , hankalinsu bai zo gareni Ba. Sai dana tabbatar babu wani sauran motsi dA kunnena ke iya ji, sannan jikina manne da shara na fito, gabana na faduwa . Na fara 'yar tafiya kenan ban yi tunanin ,shin yanzu takamaiman ina. Zani ba , sai na kara hango hasken mota na nufo inda nake banyi tunanin kara komawa cikin tankin dana fito ba ,na kara rufawa aguje . Ina dada gudu gunjin motar na kara kusantoni,har sai lokacin dana zo. titin makarantar sekamdiren tarauni. Sai da motar ta gifta ni, sannan na fahimci honda,ce kuma wani mutum ne shi kadai a ciki. Duk da haka ban tsaya ba sai lokacin dana kai daidai gindin gawo ,ina kokarin tsayawa sai nayi tintiben daya wuntsilar dani har kasa. Shakka babu, naji matukar zafin buguwar da kaina yayi. Kamar ajiyeta aka yi a gabana ,sai ganin motar,sai ganin motar nayi ta tsaya , har 'yansanda hudu sun fito daga motar kowannen su rike da bindigarsa ahannunsa. Ka-ka-ka-Kaf! Karaf !" Shuraih Usman Naji bindigogin sunyi shirin yin ta'addanci,sannan suka cuccuna minsu akaina da bayana . Da kyar na dago kaina motar ,zuciyata takasa tuna komai saboda tsoro. Inter-state-Anti-crime-patrol. Abin dake rubuce kenan ajikin motar, can. Sai naji wata murya kaman na taba jinta tace. "Don't move ,you are under arrest" Babu yadda zanyi kawai sai narufe idanuwana ,jikina kamar ba laka na koma na kwanta ,shakka babu na kamu. 'Ka daka aiwatar da wani yunkuri da zai iya kai ka ga halaka ,ko kuma ya cutar da rayuwarka " Na tuno da gargadin da mahaifiyata tayi min. Anan muka kawo karshen Book 1 sai kun jini a book 2 mai taken MUN-JI-MUN-GANI Authour: Maje~el~hajeej Hotoro ( ya hajeej) Written: Shuraih 99% Shekarar bugu : 1999 Post by: Shuraih 99% An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 3 of 3