Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 3
al'umma sun ganshi sai su rude , su razana suna fadin fatalwar wane ta fito. Shuraih Usman Ko kuma idan mutum yana hulda. Dasu,kuma jama'a sun san hakan kuma ya mutu,sai shi masu rikida da siffarsa,su rinka razana wadanda suka sanshi. Ubangiji yayiwa aljanu baiwar rikida daga wata siffar kuma su wadan su irin halittu na da burinsu kawai su cutar da mutane ,su kuma jefa su cikin rudani. Sai dai abin dubawa shine ,babu yadda za'ayi aljani idan ya rikida a siffar mutum,ya bayyana da cikakkiyar kama ba tare da ansami tawayaba .dole ne idan suka rikida kasamu wani bangare jikinsu,baiyi dai dai da na mutane ba ,komai kyan siffar da suka bayyana. Wasu idan suka fito a siffar mutane zaka samu idanunsu na mage ne,ko kura ko kuma sauran namun daji ,ko kuma ka ga kafafuwansu irin na doki,ko daya tafi daya girma da dai sauransu. Amma mafi yawancin sunfi rikida amunanan siffofi. Kamar mummunan tsohon dake cikin matsanancin talauci,ko kuma siffar halittun tsoro. Shuraih Usman Nayi shiru ina fargaba da mamakin,rikirkitaccen al'amarin daya faru akaina,wanda da wani ne yafadamin ba mamaki zuciyata takasa gaskatawa. To amma ni ai banga wasu kamanni jikin farida,wadanda ba su dace dana mutane ba sai dai matar dake tare da ita,wacce kwata-kwata na tsani na tuna kamanninta a zuciyata. "Fatima! Wani abune ya girgiza rayuwata" Kamar wani abu kenan"cikin doki ta bukata . 'Jiya ne bayan antashi daga wasan Nejeria da costrica a Lagos ,sai muka hadu da yarinyar dake jikin hoton dake hannunki. Mun yi hira da ita ta fadamin sunanta, da kwatancen gidansu a kaduna ,nakuma bata zoben nan dakika bani yau bayan antashi daga wasa naje gidansu kamar yadda ta kwatan tamin. Ina ganin kamwarta da babarta ,naga kamarsu daya,ba wani bambanci, dana nemi akirawo min ita sai suka tabbatar min shekarunta uku da mutuwa. Da farko ban yarda ba sai da suka gamsar dani da hujjoji. Lokacin da aka kaini kabarinta ,sai na ga zoben dana bata akan kabarin. Wannan hoton da kike gani cikin kundin hotunanta na dauko. To waishin wannan da me ya yi kama? Kuma na duba jikinta tsaf,babu abin da bai yi kama dana mutane ba. A takaice ma har taba jikinta nayi" Ta kurawa hoton ido wasu lokuta,ta dawo da hankalinta kan zoben dake hannuna,sannan ta zurfafa atunani. Shuraih Usman "Shakka babu ,wannan al'amari ne babba ,kuma da aljana ce ina ganin ba zata fito cikin taron jama'a ba . Koda yake to idan ba aljana ba ce ,yaya mutum zai mutu shekaru uku kuma aganshi a wani waje daban? Gaskiya al'amarin da rikitarwa" A dai dai wannan lokci sai Ahmad doga dan baki kakkaura fari kyakkaywa sanye da farin boyel doguwar riga da wandonta . Bayan fatima ta cire masa takalmin kafarsa ,ta kwance masa agogonsa,ta sumbaci fuskarsa,sai ta harhada tawagar abincinsu akan tebur. Ko da yaushe tare suke cin abinci. Shi kansa daya samu labarin al'amarin ya girgiza shi. "Wannan sai yayi dai da labarin *_SHAKKA-BABU_*" A gaskiya al'amarin kunshe yake da riktarwa. Ahmad yafada. Kwarai kuwa abinday faru akaina yaso yayi dai de da labarin BABBAR MAGANA. Har fatima da ahmad suka gama cin abinci suka shiga harkokinsu,ina zaune zuciyata makil da tunani ,al'amarin sai faman kai kawo yake cikin kwalkwalwata .idan na kalli hoton Farida sai naga kamar moysi take yi, don gudun kada na zautu ,sai najuya bayan hoton.rubutu ne dara-dara ajikin hoton REST IN PEACE. SIRRINSU Littafina daya Chapter 8 By Shuraih Usman D 5~3~'99 *_ LITTININ_* Shakka babu , al'ummar kano na matukar kishin yan kwallon kafar england. Zuciyarka zata iya gamsuwa da hakan idan ka halarci wasan da aka buga tsakanin AMERIC da ENGLAND,a dakin wasa na *_GENERAL SANI ABACHA_*,daka kofar mata . Wajen yadinke da dimbin al'umma bakamar lokacin da aka buga wasa tsakanin camerou da japan ba . Shakka babu dakin wasan ya yi haduwar ,da ba za a kushewa wadanda suka yi aikin ba . Har aka gudanar da wasan farko babu cikakkiyar nutsuwa,a zuciyata da ruhina da kuma kwalkwalwata . Idan har farida aljana ce mene ne dalilin yin kuka ,har da zubar da hawaye ? Mene ne baiyi kama da halittan mutum ajikin taba?..... Bana mu'amala da da namiji" Me wannan kenufi ? Nasan baza yarda da abin dana fada ba ...... Ni kaina ba'ason raina hakan ya kasance ba " "Sai dai babu yadda zanyi" Shin wadannan zantuttuka ke nufi ? Shin farida mutumce ? Idan mutum ce yaya ta mutu ta dawo? Nayi iya bakin kokarina don samawa wadannan tambayoyi amsoahinsu,yayin da kwalkwata da kuma tunanina . suka gaza don samar da amsa tambayoyin. Da har yanzu dada rikitar da rayuwata sukeyi. Shakka babu na hadu da farida ,nayi hira da ita ,wannan ba mafarki bane $ To kuma na samu gamsassun hujjoji kuma kwarara cewar farida dana gamu da ita shakka babu ta mutu. To mene ne wannan? Wanne suna ta dace aradawa al'amarin? Wannan suma tambayoyine ma bukata amsar dazat gamsar da tunani. Shuraih Usman Da ga ranar dana hadu da'ita izuwa yanzu ,idan kasanni kallo daya zakayiwa fuskata ka tabbatar shakka babu rama ta ziyarceni. Saboda tsagwaron kaduwa da rudewa ,da tunani da hankalina suka yi,wanda hakan ya haifarwa da kwalkwalwata nutson bazata cikin rudu da matsananciyar birkita. Duk don faruwar birkidadden al'amarina. Shakka babu dolene tunanina ya zurfafa ,rayuwata ta girgiza,hankalina ya galaibaita . Ka gamu da mace jiya kuyihira ido da ido,kabata abu ta karba ,ka tambayeta ,ta baka amsa ,karewa ka tabata ,sannan kana daya kacal da haduewar ka daita ka samu tabbacin mutuwarta ,shekaru uku da suka gabata. "Shin wace mummunar matar dake tare da farida" Mene ne hadinta farida? Mene ne dalilin da yasa take takurawarayuwarata ." Shuraih Usman Babu abin dana fiso a rayuwata irin hora da namiji,sai dai bani da wannan damar arayuwata "banda maganganun da mukayi da farida ,kwata kwatakwalkwawata ba ta tuna wasu muhimman al'amura . Shuraih Usman Kwatsam! Sai naji farida ta a zuciyata. Babu abindayafi ban mamaki irin tun dana ganta ,sonta ke dada ruruwa a rayuwata . Maimakon idan tunanin matacciya nakeso,sai ya ziyarci zuciyata na kori son,sai son yakara bunkasa. Kiri kiri,ina ganin ana shiga dakin wasan,yadda za'a fafata tsakanin England da USA,kuma ni kaina ina matukar ra'ayin wasan ,na hakura natsaya a waje ,kuma nakasa tafiua ko ina ,idan ka ganni tsaye ko tunanin gajiya banayi,na kurawa dakin wasan ido ,sai ka dauka so nake nashiga bani da kudin shiga . Shine na kasa daurewa na tafi , nake kallon masu damar shiga.na shiga ,nikuma ina kallon takaicin babu yadda zan yi. Sai dai da ace wani zaizo inda nake ,zai san na zurfafa a tangamemen tekun zunzururutun zuzzurfan tunani. Da ace nasan awajen wani al'amari zai kara faruwa,har ya girgiza rayuwata,fiye da yadda na tunzura jiya da yau ,da ban tsaya tsimayin faruwar tsorataccen al'amarin ba. Amma ina gama ya gama ,uba yayiwa yarsa ciki. Al'amarin yariga. Ya faru. Tun lokacin da na zari hoton farida ,har zuwa wannan lokaci,duk lokacin dana kura mata ido, ina mai maita tambayoyin da amsarsu bazata samu awajena ba,ina dago kaina sai naji zuciyata ta yi tsayawan wucin gadi. Shuraih Usman Kamar lokacin nafara ganinta ,ranta amatukar bace ,kodaddiyar fuskarta ta kara muni,har yanzu idanuwanta jawur suke kamar tira su take yi. Sanye d katuwar rigar shan iska da matan turawa ke sawa,hannun ta rike da makullin mota tana dan karkadawa. Ina ganinta tsoro da matukar fargaba suka lillbe zuciyata ,dukkan jikina ya dau rawa tamkar mutuwa ta na ke gani; Babu abin da ke bani mamki irin yadda nake matukar tsorata da zarar naga matar. Shakka babu na tsani mummunar matar,bana bukatar ganinta a rayuwata. Cikin tsoro ina tunanin guduwa daga wajen ,sai farida sanye da shudayen kwat riga da siket,ita ta fito daga dakin wasan .hankalina yayi matukar girgiza,tunanina ya dagule ,zuciyata bugun ta ya tsananta sannan jinin jikina ya zafafa. Farida ! Shin ba wannace akace tamutu ba ?shinyanzu ma mafarki nake yi?idan dai har aljanu basa rikida batare da na sami wani bangaren jikinsu , Shuraih Usman da baiyi kama dana mutane ba ,farida ba aljana bace .ko ina ajikinta irin na mutane ne ,wannan ko shakka babu. Domin kura mata ido nayi,babu inda ban kalla a jikinta ba . SIRRINSU Littafina daya Chapter 9 By Shuraih Usman Kyan fuskarta ya dada karuwa akan nada ,sannan amintaccen murmushina bayyana adan karamin kyakkyawan bakinta "MINAL JINNATI WAN NAS" Abin da kawai narinka fada kenan. Sannu ahankali ta rinka nufo wa inda nake ,har nayi niyyar cika wandona da iska ,ga mamakina sai kafafuwana suka nauyaya ,ba zan iya gudu ba . A dai dai lokacin da ta zo daf da ni sai ita da hasken suka bace,A ranar kwana nayi ina wuridi don na razana bacci yayi hijira daga idanuna Shakka babu ina cikin rudu babba. Shuraih Usman F LARABA 7~3~'99 Mahaifiyata Nana safiyya ta kasance ma'abociciyar turare ce , Aduk lokacin da zatayi maka gagarumar kyauta turarene Duk lokacin daka hadu da ita ,hancinka zai wadatu da kamshin hadadden turare. Fatima ce babbar yarta. Sannan ni,sai kuma karamin kanen mu sadiku. Kuma shine yafi farin jini a gidanmu sakamakon baiwar hikimar zance da zuzzurfan tunani daya mallaka. Wata rana mahaifinmu da abokansa na hira,kowannen na fadin wanda yafi tsana arayuwarsa,da dalilin daya saya ya tsane shi,kamar wasa sai daya daga cikin abokan mahaifinmu yatambayi sadiku dake zaune kusa da mahaifinmu "Sadiku wanene babban makiyinka aduniya ?" "Sulman rushdie"ya amsa masa "Musamman ya wallafa littafi yasa masa suna ayoyin shaidain(SATANIC VERSES), Acikin littafin yakirawo fiyayyen ANNABIN RAHAMA, Mayaudari mazinaci,ya kuma ambaci tsarkakkan matansa da Allah yakirawo IYAYEN MUMINAI,da cewar karuwai ne. Sannan yanuna cewar yayan gidan ANNABI(SAW) yayan zina ne, Musulmi da suka rasa rayukansu a yak-yaken daukaka kalmar ALLAH,ya kirawo su batattu.(Kai amma Allah ya tsine ma sulman rushdie- kowa ya tsine mai) Shuraih Usman Shaidan salman rushdie bai tsaya nanba ,sai daya kirawo littafin ALLAH mai tsarki al'kur'ani da cewar ayoyine na shaidan. Ayanzu shine littafin dayafi kowanne littafi tsada , Wannan abu da shaidan salman rushdie yayi,ko fir'auna baiyi wannan bakar aniya ba . Azaba mai matsananciyar radadi,da la'anta mai matukar yawa ,su tabbata ga shaidan salman rushdie da yan barandansa" Abokan mahaifinmu sai dai suka shawarce shi ,da ya wadata sadiku da wataccen ilmi,saboda nan gaba zai zama malami mai wadataccen tunani. Aduk lokacin dana saya mata turare,takan dade tana nuna farincikinta ,ganin haka sai na mai dasaya mata turare dabi'ata . Aduk lokacin da nake bukatar daddadan turare ,kai tsaye NAFISATU FASHION nake tafiya . NAFISATU FASHION kayataccen tangamemen waje ne da mata ke matukar alfahari da ziyartarsa. Sakamakon zunzurutun kayan kyale-kyalen,mata masu matukar kyau sai dai tsada . Koda yake nafisatu ta tabbatar musu cewar arha bata ado,kuma sayen nagari mai da kudade gida. Kuma dimbin matan dake narkar da kudinsu a nafisatu fashion sun dade da yin amanna da wannan maganar Shuraih Usman Idan kana bukatan kayan mata masu kayatarwa,ko kuma mace na bukatar hadadden gyaran gashi ,ko tsararren tsari da salo salon kitso,ko kuma amintattun zanannun furanni(Flowers) a hannu da kafa ,idan ta ziyarci nafisatu fashion zuciyarta zata samu gamsuwa daga masana akan sirrin harkokin. Karfe sha dayan rana na tsaida motar honda civic a kofar nafisatu fashion sanye nake da kubta riga da wando ruwan kasa,kaina da hula. Kamar yadda nasir yafada cewar ya gasgata al'amarin daya faru gare nine ,ganin yadda kamannina suka yi mutukar birkita cikin kankanin lokaci tundaga ranar dana hadu da farida. Hakama Ahmad da Fatima suka kara maimaitamin, Kuma ni kaina shakka babu na shaida akan hakan. Dayake unguwar gadonkaya da gidan Ahmad babu yawan mutane , Kuma ni da shi mun kasance masu yawan zirga zirgar daukar rahotanni ,bani da abokai kamar unguwar Albasa da gidan mahaifiya ta yake. SIRRINSU Littafi na daya Chapter 10 By Shuraih Usman Na san da zarar naje Gandun albasa abokaina na ganina sai sun tambayeni game da ramar da keyi. Na samu dogon lokaci ina zaune cikin motar, Amma na kasa fitowa saboda zurfaffan tunani da na yi. "Nan ne gi dan su dela din? Yanzu ku dama shegantaka. Kuka kulla min? Ina zaune lafiya kuka yimin karya kun san ba gidan delar zaku kaini ba ! To mene ne nufin ku da yin hakan?" Wata yamutsastsiyar murya da kaji kasan wacce ta mallaketa , Shekaru sun wada ceta aduniya ta kaste min tunanina . Ina waigawa sai na ga wata tsohuwa ce sanye da riga da zani na atamfar English, Tayi wani irin baudadden daurin fatala. Sannan zanen ma maimakon yatafi daidai sai ya kauce kamar arazane yake ,sakamakon wani irin dauri da tsohuwar tayi masa. A tsaye daf ta wata marsandi ruwan toka , Fuskarta da idanuwanta amsoshi ne na cewar ta dade aduniya. Kusa da ita wasu kyawawan 'yanmata ne guda biyu, Babba da karama kana ganinsu kaga ya da kanwa, Farare sal dasu. Babbar sanye take da burgujejiyar riga da wandon wani zani mai kyalkyali a jikinsa , Kanta babu fatala. Karamar kuma bakin wandon jeans ne ajikinta , Da kuma farar rigar yadi mai hudahuda,da yake baiyanar da bakar shimin dake jikinta ,tayafa katon bakin fatala a kanta.(Tambaya dan Allah mata mene fatala don ni bansan shi ba Shuraih Usman ) Tsohuwar da ke tare dasu duk ta rude kamar tana nuna alamun sato ta sukayi. "Wannan shegantaka har ina ? Kawai ku tashi ku zunbuda min karya ,wai gidan su dela zaku kaini, Shikenan sai ku kawo ni wata uwa duniya ku ajiyeni! Kunsan ba son shiga mota nake yi ba, Wannan dinma dan kunce gidan su dela zaku kaini ne" Tsohuwar take fada lokacin datake kokarin tafiya daga inda yaran suke . "Tsaya kiji Goggo" Babbar tafada . "Gidansu delar zamuje , Mun tsaya anan ne muyi saye-sayen biki, Mukuma gyara gashinmu a kuma zana mana flowers. Sannan kema tunda gobe biki sai a gyara miki gashin ki, Gobe ba sai ki fito fes ba" "Ban gane a gyaramin gashiba ! Da me za'a gyara min gashin nawa ? Kai kunga bana son iya shege da wasu tsarabe- tsaraben banza dana wofi. To ina ma hausar a gyaramin gashi ? To ama gyara min gashi kamar ya ? Shuraih Usman "Kinga Goggo cigaba aka samu , Wani irn inji nasara ya yiwo musamman don gyaran gashi. Za'ayi matukar wanke miki gashinki ,afitar da kowanne irin datti,sannan sai ki zura kanki a cikin injin ya gyara miki gashinki ya rinka sheki , Ya kuma canja miki duk irin fasalin da kike bukata " Ita kanta budurwar sai da ta fada ta gane kuranta. "Allah ya sitiri bukwui! Yanzu don Allah ,Don annabi ina zaman zamana kuka yaudareni babu sidi babu sadada, Wai na zura kaina cikin inji! Wato ya markade min kaina kenan? To idan kun gaji dani alhaji bai gaji da ni ba". "Na zura kaina cikin inji akan wane dalili? Tsohuwar ke fadi lokacin data bar inda matan suke , Ni kuma a daidai lokacin na fito daga motar na fara nufar nafisatu fashion. "Kubarni Allah yakawo wanda zai mayar dani gida, Babu ruwana daku,kuje tsiyarku ta kare akanku ,nazura kaina cikin inji turkashi!" Karamar yarinyar tayi saurin tasha gabanta, Ta fara lallaminta ni kuma adaidai lokacin nazo zan gifta. Bawan Allah kaji zancen nanfa" Tafada lokacin dakai tsaye take fuskantar fuskata( Shuraih Usman ) "Cewa sukayi na shirya su kaini gidan kanwata ,shikenan sai kuka woni nan waina zura a inji, Wai acanja min fasali"ina jin yadda injin makotanmu ke burari, Sannan yanzu don sunana saratu na garkama kaina cikin injin nasara , Ina ruwana da wata gayyar tsiyar nasara". Kafin nayi magana karamar yarinyar tarigani. "Goggo ba markade miki kai zaiyiba , Mutane nawa akayiwahakan? Yanzu zamani ya canja , Abin da babu shi da yanzu an samu bawani abu tattare da hakan?" "Zamanin banza dana wofi,haka kawai garin neman gira a rasa ido. To wai mene ne yayi zafi gira ke hayaki,idoke cin wuta" "Shakka babu tafiku gaskiya ,yaya ga abin da mutun ya saba dashi ,haka kawai rana tsaka ,yarinka nemowa kansa abin da bana saba. Tun da dai ku kuna bukata kuje kuyi, Ita dabataso tayi zamanta a mota, idan kuka fito ku kaita gida. ( Shuraih Usman ) Nafadi hakanne don na kwantarwa. Da tsohuwar hankali. "Sannu dan gari•haka kawai babu gaira babu dalili,kilu ta jawo bau" Tafada lokacin da tafara komawa wajen motar. "Kaduba rannan ina zaune lafiya suka kawomin wata tsinanniyar aba wai ita talabijin, Dalbijin ko masifa? To inbanda masifa kawai sai gani nayi wannan ya cakawa wancan wuka. Wancan ya sari wannan da takobi,a duko bindiga a zunduma wa wannan ,kaga tsiya ! Mutum yafadi ya mutu. Can kuma sai wuta ta kama zaal! Zaal! Zaal!!!" "Kwanana uku ina mafarkin wannan masifar,kuma tun daga ranar nace in Allah yayi duniya don dan Abdullahi ni da talbijin munyi sallama . ( Shuraih Usman ) Tafada lokacin data shiga motar,'yanmartan sai faman dariaya sukeyi suna kallon fuskata. "Ni dadina da Goggo ,haryanzu kanki yaki wayewa " Babbar tafada cikin zolaya . "Fatalar uwarki!kan nawa bai wayeba kullum kike zuwa ki ce na koya miki yadda zaki mallake mijinki ki hana shi fita ?" "Ahayye ! Ayyururi ! Kyale su haka Goggo" Suka fada suna shewa, lokacin da suka shiga Nafisatu fasion ,ina biye da su a baya . Mata ne dinke cikin nafisatu fashion,kowacce na kai- kawo, Don zabin abin da suke bukata . Dayake na san abin daya kawon,kuma nasan inda zan sami turaren kaina tsaye ban tsaya bata lokaci ba na nufi matattarar turarikan. Ina zuwa wajen tirarikan 'yan matan suma suka zo inda nake . "Zainab ! Ni ma fa ina bukatar turare" Babbar ta fada wa karamar,lokacin dasuka fara duddubawa. "Kaima turaren zaka siya ?' Zainab din ta tambayeni. "Shakka babu " Nafada ina murmushi. "Na zaba maka" "Zaki iya yin hakan" SIRRINSU Littafina daya Chapter 11 By♥ Shuraih Usman Queen da heart da kuma daimond , Sune turarikan da zainab ta zaba min. Shakka babu ,nayi matu kar yaba zabin da zainab ta tayi min ,domin tsarin kwalaben kadai sun gamsar idanuwa . A dai dai lokacin dana rike ina dada dudduba , sai naji wata irin daddadan dariya ta diki dodon kunnena . Kwalaben turaren suka kubuce daga hannuna suka tarwatse a kasa, Tsarwatsewar da ta jawo hankalin matan cikin kantin kaina . Hankalina a birkice , Tunanina arazane ,bugun zuciyata yayi matukar tsananta lokacin danaga wacce nake gani , Shakka babu farida ce , Kasancewar nafisatu fashion tangamemen wajene akwai tazara tsakanina da su. Babu abin daya fi tunzurani fiye da komai, Irin duk inda naje sai na ganta . Shakka babu , Dole hakan ya tunzura rayuwata, Dole rayuwata ta rude, Dole rayuwata ta gigita, Tun ranar da Nigeria da costrica,suka yi wasansu a lagos , Kullum sai mun hadu da farida ? Kuma bayan na samu tabbacin mutuwarta . ( Shuraih Usman ) Sanye take da kayan babe bari dogwaye har kasa, Ta nannade jikinta da dogon kayataccen mayafi, Kamar dama zuwanta kenan daga maiduguri. Abin daya dada jan hankalina gareta ,wannan lokacin cikin farin ciki da nishadi farida take, Bakamar ganina da nayi mata a sani abacha stadium da kuma hawan dabar gidan sarki ba . Saboda kada na kara gamuwa da ita, Ahmad yatafi Lagos don dauko rahoton wasan Nigeria da Germany.sannan kuma zai wuce ibadan don halartar wasan gwana da argentina . Babu yadda bai yi dani don mutafi ba , Na dage akan gaskiya na hakura , Kawai do tsoron haduwata da Farida . Wannan lokacin ma tare suke da ko daddiyar matar ,ita ma sanye da zurma zurman bakaken kwat riga da siket. A lokacin nake kollosu,kudin sayayyar da sukayi mayar ke biya . A lokacin dana yi yun kurin zuwa inda suke , Saboda na ga suna kokarin fita sai naji hannuwa sun rikeni. Ina wai gawa saina ga wasu rusa-rusan karti guda hudu, Kowanne fuskarsa a tirbine suna yi min kallon rashin yarda. Sai daga baya na fahimci masu tsaron nafisatu fashion ne . Ai a anan na dawo hankalina na fuskanci ta'adin danayi . Har yanzu zainab da yayarta na tsaye suna mamakin,yadda cikin kankanin lokaci na birkita . Kwata-kwata sai kunya ta lillibeni,dana waiga inda su farida suke tuni sun fice daga wajen. Shuraih Usman Bayan nanemi afuwan ta'adin danayi , Na biya kudin tirarikan sai na kara sayen wasu,sannan cikin sanyin jiki da kunya na nufi inda motata take . Na sami dogon lokaci cikin motar , Na kasa tukawa na tafi. Shin menene dalilin da duk inda nayi sai na hadu da farida? Tambayar da zuciyata tayi ta maimaitawa kenan, Na rasa amsarta har sai da wata murya a sanyaye tace; "Hala wani abu ya tunzuraka?" Zainab ce an matukar kayata gashinta , Sannan hannunta data dora akan murfin motar, Shima ya kayatu da kyawawan furanni lokacin dana waiga. Bayan nayi ajiyar zciya sai nayimata murmushin gaskiya kin-hadu-zainab. Ganin haka ita ma sai ta yi murmushin. Mahaifiyata tayi farincikin turarikan dana kai mata , Kuma ta tambayeni dalilin rama da nakeyi . Ban boye mata ba , Na sanar da ita komai, Kuma shakka babu tayi matukar mamki kamar yadda duk wanda na gayawa sai yayi mamaki. Shuraih Usman Sannan tabani addu'o'in da zan rika yi don neman tsari, Sannan kuma ta shawarceni da kada na aiwatar da wani yunkuri da zai iya kaini ga halaka ,ko kuma ya cutar da rayuwata. Abokaina ma sai da suka tambayeni halin dana ke ciki. Shi kansa mahaifina sai da yayi min tofin wasu ayoyin AL'QUR'ANI a dukkan jikina ,sannan ya tofa min wasu aruwa na sha. Ya kuma umarceni da karanta QUL'HUWALLAHU uku, FALAQI uku, NASI uku,idan nayi sallar asuba. Sannan idan nayi sallar magriba , Da kuma idan nazo bacci . Ya kuma kara umarta ta da karanta AYATUL KURSYU da kuma suratul YASIN. Bayan na dawo daga gandun albasa wajen mahaifiyata ,a ranar idan na runtse ido saina ga kaman farida tana kuka , Idan na bude sai na ganta tana murmushi. Sai dana samu dogon lokaci ina zubar da hawaye sannan na fahimci kuka nake yi. "NA SHIGA UKU" Kalmar dana yawaita fada kenan awann rana. SIRRINSU Littafina daya Chapter 12 By♥ Shuraih Usman G ALHAMIS 8~3~'99 Mata ne dake tinkaho da ilmi, Masu takama cewar mazansu masu fada ajine , Suka dinke dakin taron na makarantar Rumfa College, Don gudanar da taro na musamman akan tallafawa iyali. Maimuna isa kwantagora matan ,kantomar jihar kano,ita ce tayi jawabi na karshe a taron. Kamar yadda Ahmad ya umarceni don na dauko muhimman abubuwa a taron , Na cika wannan umarnin, domin na halarta. A burin Ahmad duk wasannin da za ayi a dakunan da Nigeria ta tanada don gudanar da wasan cin kofin matasa na duniya sai mun halarce su. Da farko nayi matukar farincikin hakan, Amma daga baya na fatattaki farin cikin daga zuciyata,don matukar tsoron kara haduwa da farida. Sanye na ke da farin jeans riga da wando,kafata daure da kito baki Wasan da za ayi tsakanin cameron da England a kano, Bashine a gabansa ba . Wasan japan da USA da za ayi a bauchi, Da wasan zambiya da spain daza a gudanar a calabar,da kuma wasan honduras da brasil da za ayi a por shine abin daya dame shi. Kuma babu yadda za,ayi ya halarce su rana daya ,shine babban abin bakin cikinsa da kuma kekasa kasa danayi nacewa bazan kara halartar kowane dakin wasa ba . Shakka babu baiso hakanba ,don matukar shakuwa da mukayi da shi. Bayan na gama gudanar da abin daya kawoni ina kokarin tafiya hausawa sabon titi,in da kamfanin jaridar Ahmad take ,sai na'urar daukan hoton ta subuce daga hannuna ta fadi. Da farko na bayar faridace,sai daga baya na karbo ashe mahaifiyarta ce , Ita ma tana daya daga cikin matan da suka halarci taron. Nayi matukar girgiza da mamakin ganinta ,wanda ita kanta ta fahimci hakan rubuce a fuskarta. Kuma ita kanta tayi mamakin ganina a wajen Har muka gaisa da ita gabana na faduwa ,shakka babu idan kaga mahaifiyar farida kaga farida . "Da ma anan kake" Tafada cikin mamaki. Shuraih Usman "Wallahi anan nake " "Daukar rahotanni kake yi?" "Da man kai ma'aikacin jaridane?" "Shakka babu" Nafada . "A wanne kamfani kake aiki" "Dankari" "Dankari?" Tasake maimai tawa. "Shakka babu" "Kana nufin jaridar dankari wanda dimbin al'ummma ke alfahari da karantata?" "Shakka babu" Na maimaita. "A gaskiya shakka babu ,ta shiga bakinka "(nima haka daenagani) Tafada tana murmushi. "Shakka babu" Nima nafada cikin murmushi. Murmushin datayi sai ya koma dariya , Nikuma a wannan lokacin zuciyata a farida take daukanta . Duk da cewar tafi farida kaurin jiki da shekaru,gani nake yi zata rikide ta koma farida. "Ina nasir?" Na tambayeta don katse dariyar da takeyi . Shuraih Usman "Tare muka taho,har ma da meenat ,duk suna tarauni" "Tarauni wajen ina " Na bukata . "Don inason gaisawa da nasir" "Kana zuwa daidai masallacin juma'ar tarauni,ka tambayi shagon askin sulaiman ,agidansu sulaiman din muka sauka .sai gobe zamu koma yace yana son ganin wasan England." Abin dayabani mamki har muka rabu bata yi mani zancen ganin farida danace ina yiba . Wanda hakan na nufin TASAN FARIDA TA MUTU ,KUMA TASAN SHAKKA BABU WANDA YAMUTU KAWAI YAMUTU. WACCE NAKE GANI A TUNANINA ,ALJANACE TAKE FITO MIN A SIFFAR FARIDA. TO AMMA ABIN TAMBAYA ANAN WACECE WANNAN KODADDIYAR MATAR SIRRINSU Littafina daya Chapter 13 By♥ Shuraih Usman Bayan naje hausawa sabon titi na bawa ma'aikata rahotannin dana dauko , sai na wuce gida nayi wanka na sauya kayan jikina , da shadda riga da wando launin sararin samaniya ,sai na shiga wata motar Ahmad din TOYOTA CAMRY sai tarauni. Kamar ta kwatanta min,ina tambaya aka nuna min shagon askin sulaiman. Sulaiman farine amma ba dogo ne sosai ba,yana da yawan fara'a da 'yar saurin magana. Kaset din wa'azin AHMAD DEEDAT ne ke tashi a katuwar rediyon dake shagon yana yi wani yaro aski. "Don Allah nasir dayazo daga kaduna nake nema" Na fada bayan ya rage karar sautin rediyon. "Ok,kwarai yana gidanmu. "Nasir ko?" Hakika yana nan. "Don Allah barina gama askin sai mutafi,dama ina zon zuwa gida" Cikin saurin magana yafada,yana sauri don ya gama wa yaron askin. "Bismillah,zauna mana ,nakusa gamawa ,saura kadan" Yafada lokacin da yayi min nuni zuwa ga kujera . Bayan ya gama askin,ya kulle shagon,sai muka nufi gidansu. "Tun dana ganka nake tunanin,kamar na so na sanka " Sulaiman yafada lokacin dana tsayar da motar a kofar gidansu" "A ina fa ?"Na bukata "Shin ko kataba yin karatu a 'yargaya ?" "Shakka b babu" "Haba ni fa tun dana ganka ,nake ma kallon sani,nima a 'yargaya nayi karatu" Shuraih Usman A daidai wannan lokaci sai nasir,sanye da farar riga ya dora mata bakar falmaran ,da wando launin kwai ya fito daga gidan. "Aah! Habib! Yaya aka yi kasan ina nan ?"Cikin mamaki yafada ,lokacin daya nufo in da muke. "Nasir!" Na kirawo sunansa bayan mungaisa. "Ya yi habib ,wallahi ina da saurin mantuwa,mama fa ta fadamin kun hadu dazu a rumfa college " "Shakka babu" "Ok sai anjima ,nizan shiga daga ciki"sulaiman ya fada. "Nagode sai anjima "na amsa masa. "Nasir! Kasan kuwa farida tana kano? Domin jiya sai da nakara haduwa da ita ,a nafisatau fashion dake nan kofar nasarawa. Kuma shakka babu. Bani kadai nake ganintaba ,jama'a da yawa suna ganinta ,kawai dai don basu san tabane " Nafada Shuraih Usman "Habib wannan al'amari yana da matukar mamaki da rikitarwa. Ni kaina idan na tsaya nayi tunani,sai zuciyata ta cika da al'ajabi. Ni dai nasan farida ta mutu,kuma inhar mutum ya mutu ,shakka babu tasa takare . Kuma gashi kai kana haduwa da farida ,abinda yafi mamaki ma ai dole kwalkwalwa da zuciya suyi" Cikin matukar mamki yafada . "Kasan abin dayafi dagula min lissafi nasir? Farida ba aljana bace ,kamar yadda masana SIRRINSU suka sanar dani. Dole idan aljani ya rikida asiffar mutum ,sai ansami alamun daza su tona masa asiri cewar ba mutum bane . Na ga farida har sau hudu,kuma shakka babu ,babu wata alama a jikinta da bata dace da mutane ba". Kuma babu yadda za'ayi aljani yarinka bayyana a bainar jama'a yana hulda dasu . Duk ganin da nake yiwa farida acikin jama'a nake ganinta ". Nasir yayi shiru na wasu lokuta ,nikaina na san tunani ne ke birkita kwalkwarsa. "To shin habib idan wacce kake gani ba aljana bace ,kana nufin farida kake gani, wacce muka binne kuma wacece?" Shuraih Usman "Nikaina wadannan tambayoyin ina matukar kwadayin amsoshinsu"cikin sanyin jikinafada. "To ai sani zaka sake nema daga masana akan SIRRINSU" "Shakka babu,ina ganin abinyi kenan" Bayan mun tattauna akan wannan da waccan,sai naga yadace nakoma . "Habib ,zaka halarci wasan

Chapter 2 of 3