Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 3
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels SIRRINSU Littafin Maje el hajeej hotoro Shekarar bugawa:- 1999 Ebook creator and design by:- Shuraih Usman Publish by:- Shuraih 99% . SIRRINSU Littafina daya Chapter 1 By♥ Shuraih Usman A A 3~4~'99 . *_ASABAR_* Maryam!A'isha! Sai yaushe ?" Kawata banga jakata ba "Faruk ! Banda kwacen budurwa" Boss ! Muhade a tropicana Ka-ce-na-ce, rudu da kuma hayaniyar dasuka ringa tasowa daga bakunan dimbin mata da mazan dasuka halarci filin wasan kwallon kafar, datafi kowace girma da kayatuwa a Nigeria (sulere). Bayan antashi daga wasan costarica da nigeria agasar cin kofin duniya na matasa Cikin halin hargowa da matsananciyar bugun zuciya kamar ta faso kirjina don tsananin bugu da takeyi tun da nake Arayuwata. Ban taba tsintar. Kaina ahalin danake ciki awannan lokciba Domin aranar na hadu da wacce na kirawo mutumce , Aljana ce ko kuma fatalwa , bayan an tashi daga wasan. Anan ne. Na wadata idanuwana da abubuwa da dama. Shuraih Usman Shugaban askarawan nigeria janar Abubakar Abdulsalami da tawagarsa. Sune suka fara ficewa daga filin wasan 'yan jaridu da ma'aikatan gida jen sadarwa nata daukar hotunansu. "Shuraih usman"Alokacin da wasu ke shirye-shiryen tafiya , wasu ke shirin zantawa da sababbin 'yan matan. Da sukayi Turawa kuma na ta daukar hotuna. Sai idanuwanta suka hasku ga kyakkyawar fuskarta Farace doguwa mai matukar yalwar bakin gashi, ta mallaki dara-daran fararen idanuwa kamar madara ,sannan tana da dirarriyar cikar halitta da kan dau hankalin dukkan da na miji Dogon hancinta harbaka da dan karamin bakinta na daya daga cikin abubuwan da suka tona asirin kyawunta kallo daya zaka yi mata ka gamsu cewar duk daga inda tafito tahada dangi da shuwa Ina ganinta sai da wani abu ya taso daga kafufuwana ,har zuwa cikin kwalkwalwata,wanda hakan yasa jikina yayi yarrr! Na wasu lokuta sannan ganinta ya jefa zuciyata a cikin wani irin da tun dana. Shaki iskar duniya ban taba tsintar kaina. A wannan yana yiba. Shuraih Usmanbawai ina nace ban taba ganin macen data fi ta tsarin kyan halitta ba,ko tsarin iya sa kaya ba. Haka kawai ina ganinta na ji kamar akwai wani abu gare dayake fizgeta zuwa wajenta . Babu abin da yafi bani mamaki game da ita, irin duk cikar dakin wasan da yayi , da zunzurutun kabilu daban-daban , maza da mata daga kowane bangare na nigeria , da kuma kasashen ketare kowa na farin ciki da nishadi .Amma ita tana can gefe guda jin gine. Jikin bakar marsandi,ta sunkuyar. Da kanta kas , kamar.duk al'ummar dake wajen bata san da su ba , bata kuma damu da Suba. Hayaniyar kuma da sukeyi bata dameta ba. Wanda wannan na nuni da cewar shakka babu tana cikin matsananciyar. Da muwa arayuwarta . Na dada yin matukar mamaki lokacin dana fahimci duk taron samarin dake wajen babu wanda yakula da kowa. Shuraih Usman bakar kwat da siket dinta da ke sanye a jikinta ,sun mata matukar kyau,da tayi kama da gimbiya LAILA. Kyakkyawan takalmi ne mai launi uku PRINCE sanye a kafarta. Kai tsaye na nufi inda take gabana na faduwa , jikina na rawa kamar mazari,kuma bansan dalilin hakanba . Sai dai abinda bansaniba. Shine ,zuwa wajenta danayi,shine ya jefa rayuwata cikin gagrumin tashin hankali,kamar mutumin daya bude dakin dake cike da mayunwatan kuraye bai sani ba. "Hello".na fada ina murmushin karfin hali a tunanina bata yi kama da wanda ke jin hausa ba. Har nayi magana dago kanata ba. "Yau wa sannu".Ga mamakina naji ta fada ,lokacin data daga kanta ta kalleni ,sannan ta mayar da hankalinta. Ga hannunta. Sannnan ne na fahimci ba hannun take kallo ba ,wani kyakkyawan zare ne mai launin ja, baki da kuma fari, dake hannunta .ni kaina nayi mayukar sha'awar zaren. "Zanyi matukar farinciki idan har zuwana wata matsala arayuwarkiba " "Kwarai kuwa , domin ni kaina na ji dadin zuwanka ,wanda zai debe min kewa dama nake nima "shuraih usman"wannan maganar tafi bani mamaki, fiye da zunzurutun kyanda ta mallaka , wanda ita kanta ta fahimci hakan. "Maganar tabaka mamaki ko?" "Shakka babau, tun ba ma da ta fito dagga bakin mace irinki ba " nafada ina kallon fuskarata. "Kamar yaya mace irina ?" Tunda ta kalleni sau daya har yanzu hankalinta. Nakan kyakkyawan zaren dake hannunta. "Kinsan mu maza mun gama yarda. Cewar duk inda mace take bata kasancewa ita kadai " " To yaya aka yi ka sameni ni kadai" "Ni kaina nayi mamakin hakan ,yanzun ma na dauka wani kike jira" zaka iya sauke abun daka dauka don ni bana mu'amala da da namiji " Na kalleta kallon da ita kanta ta fahimci ban yarada da abin data fadaba ." Shuraih Usman "na san bazaka yarda da. Abin dana fada ma ba ,nikaina. Ba'a son raina hakan ya kasance arayuwata ba saidai don babu yadda zanyi" "Yanzun nan fa kikace kin yi farinciki da zuwana ,daman wanda zai debemaki kewa kike nema ,kuma kince ba kya mu'amala da namiji"• Nafada ina mai kwadayin fahimtar abinda take nufi ,yayin da ita kuma tayi daya mayar da fuskarta ,fuskar data dace data wacce ,wani abu ke kuntata rayuwarta. "Babu abin dana fiso arayuwata irin hira da da namiji,sai dai bani dawannan daman arayuwata .kasancewar. Takunkumin alakakai , data gindayawa rayuwata . Yanzu haka daza ta ganni da kai sai na dandana kudata ,bata son ganina da namiji kwata-kwata arayuwata . Abin yana damu na saidai don babu yadda zan yi ne " Tana rufe bakinata hawaye suka fara zuba daga idanuwanta . Wanda ba karamin bani mamaki yayi ba . "Wace ce ke takura maki ?" Na tambaya cikin mamaki. Kawai saita cigaba. Da kuka tana kallon zaren dake hannunta . "Wai shin yaya sunanki? Ni sunana HABIB?" "FARIDA" Cikin shisshikar kuka ta fada Sirrinsu Littafi na daya Chapter 2 By Shuraih Usman . Babu irin magiyar da banyi mata ba don tafada min amsar wacce ke takura mata .Amma taki bani amsa . Kawai takurawa zaren dake hannunta ido,kamar tana mamakin ganinsa ahannunta "Shin dama Farida ke mutuniyar legos ce?" Na tambaya don canja hirar. Gyada kanta tayi alamar a'a ce amsar tambayata . "Daga ina kikazo" "Kaduna" "Wacce unguwa a kaduna " "Tudun wada " "So nake ki kwatan tamin gidanku" *Shuraih Usman*"kana zuwa tu dun wada ,kusa da makarantar marigayi sheikh Abubakar gumi,duk inda katambaya gidan Alhaji adam za'akaika, shine gidana uku" Tun data fadi wadannan maganganu,bata kara cewa komai ba,sai kawai tacigaba da kukanta ,ga kyakkyawan zaren, kamar aranta yake sainaji. Ina son mallakarsa. Sai naciro zoben azurfa dake hannuna,wanda fatima yayata tabani "Farida" Nakira sunanta lokacin dana mika mata zoben tadaga kanta ta karba ta saka adan yatsanta na hagu.sannan taci gaba da kallon zaren. "Farida"ina son kema kibani zaren dake hannunki,don tunawa dake kafin mukara haduwa" Nasamu dogon lokaci ina tambayarta Amma in da kasan dutse nakeyiwa magana.ko kallon inda nake bata yiba, bata dakuma niyyar kara yin magana . kwata-kwta hankalinta na kan zaren,ganinyadda ta tatattara hankalinta ga zaren saina mika hannuna na rike zaren. Inda kasan aranta yake ,domin ina tabawa ta daga kanta ,sannan tayi wani irin ajiyar zuciyar da sai da na tsorata ,Amma dauk da haka ban saki ba.* Shuraih Usman*. "Mene ne haka ?" Naji wata irin murya mara dadin ji tafada daga bayana , cikin sauri na waiwaya a tsorace ganinta ya dada jefa tsoro da fargaba azuciyata. Kodaddiya ce mummuna gajeriya kuma kakkaura ,mai wasu irin jajayen idanuwa kamar garwashin wuta . Sannan ta mallaki faskeken kai, da burgujejen hanci.tun dana dora idanuna afuskarta ,naji kwata- kwata na tsane ta ,na kuma tsani ganinta da nakeyi . Sai na ji bana bukatar hada ido da ita ,domin da zarar na kalleta sai wani irin kunci yakai farmaki zuciyata . Lokacin dana. Mayar da hankalina ga farida ,sai na fuskanci har yanzu ta daga kanta sama ,idanunta arufe jikinta na matukar tsima kamar tsohon dan taurin da tsiminsa ya motsa . Kuma na fahimci zuwan kodaddiyra matar ce ,kuma nafahimci ita ne ke takura wa farida'kuma na fahimci shakka babu tana matu kar tsoron matar . Saidai abin daya bani mamaki mene ne hadin farida da wannan mummunar matar dako ta ina basu dace agansu tare ba ba?* Shuraih Usman* A fusace kodaddiyar matar takama hannun farida,cikin sauri tabude motar da farida ke jingine ta tura ta ciki da karfi sannantayi min wani irin kallo da ya dada tsoratani sannan taci taya da karfin daya tayar da kura awajen . Kamar fitan harsashi daga bindiga motar ta bace daga harabar dakin wasan . Abin kamar aikin sihiri , awannan ranar babu abinda ke zuciyata . Sai yawan tunaninta ,duk abinda nake yi kwatsam,saita fado min a zuciyata . Sai dai ba zan taba mantawa da haduwata da ita ba ,domin rikirtaccen abin daya faru arayuwata .nakasa gane shin farida ,MUTUMCE KO ALJANA KO KUMA FATALWA Sirrinsu Littafi na daya Chapter 3 By Shuraih Usman B *_SIR.AHMADU BELLO STADIUM_* ,na cikinjerin kayattattun dakunan wasa dake najeria. Shakka babu wannan haka yake. Na yarda da hakan ne don halartar wasan ghana fa crotia. Amma kwata-kwata hankalina baya na kan wasan da ake bugawa yake ba, burina kawai ata shi natafi tudun wada neman gidan su farida .* Shuraih Usman*Tunda jirginmu yata so daga legos ya dira a kaduna ,na so na bincika amma kasancewar Ahmad mijin yayata wanda shine ke daukar dawainiyarmu ni dashi, halartar wasanin da ake gudanarwa. Yabukaceni dana rakashi ziyartar kayatattun hotels,da wuraren hutu,da kuma barikin sojoji. Ana tashi daga wasan ko komawa masaukinmu banyiba ,kai tsaye na wuce unguwar tudun wada . Sai dai kash ban san cewar zan gamu da gawurtaccen al'amarin da zai birkita kwalkwalwata ba . Shadda ce launin ruwan kwai,sanye a jikina. Kamar yadda ta kwatanta min ban sha wahala wajen gane gidansu ba. Babban gidane dayake da bakar kofa,ankuma yi masa shudin fenti. Banyi minti daya da zuwa ba kofa tabude ,wata kyakkyawar yarinya wacce suka yi matukar kama da farida ,sanye da shudiyar doguwar riga tafito daga gidan. Rike da Naira hamsin guda uku ahannunta . A yadda na fahimceta zata kai shekara goma shadaya.* Shuraih Usman* "Sannu"nafada bayan nakirawota . "Yauwa sannu" "Yaya gida?" "Lafiya ta Amsa tana yimin kallon rashin sani. "Ko don Allah nan ne gidansu Farida?" Tayi shiru kamar tana mamkin tambayar ,kafin ta amsa min da cewa nan ne" 'Ke kanwarta ce ?" "Eh" "Yaya sunanki?" "Meenat"Ta fada har yanzu bakon kallon na fuskarta. Ko don Allah ta dawo?" "Wa?"Ita ma ta tambayeni cikin mamaki. "Ina nufin farida" "Daga ina ?" Wannan karon mamakin yafi bayyana afuskarta. "Jiya muka hadu da ita a lagos ,shine ta kwatan ta min gidansu ,idan kika ce habib wanda suka hadu ........ Ni kaina na fahimci matukar razana ,data bayyana karara a fuskar meenat, atunanina kodon farida ta ec bata mu'amala da maza shine take mamakin zuwana .Amma bata tsaya saurarar ragowar abin dazan fadaba , sai * Shuraih Usman*ta ruga gida a guje ,kamar wacce kare ke niyyar cizo. A lokacin da nake tunanin kokirawomin farida ta tafi yi,sai kofa tabude wata mace sanye da fararen kaya ta leko,da farko na dauka farida ce don kamaninta dana gani. Sai daga baya na sauke ashe mahaifiyarta ce. Ta yi min wani irn kallon matukar mamakn kamar yadda meenat tayi min,shin ko tana mamkin nine saurayi na farko da na taba zuwa wajen 'yarta ? A dai de lokacin dana nufi inda take don mu gaisa ,saitayi sauri arazane ta mayar da kofar ta rufe . Haka kawai sai zuciyata ta fara matsananciyar bugu ,jikina yayi wani irin sanyi.har na yi niyyar tafiya ,sai kofar ta kara budewa . Wannan lokcin nayi tsammanin ganin kodaddiyar matar nan,ga mamakina sai wani dogon saurayi fari kimanin dan shekaru goma sha takwas . Sanye dafarar singileti da shudin wando jeans yafito. Tun kafin ya karaso inda nake nafahimci irin kallon mamakin da meenat da mahaifiyarta kemin,shine shima. Akan fuskarsa.* Shuraih Usman*"ko kaine ke neman farida ?"Yatamabye ni bayan ya miko min hannu mun gaisa. "Shakka babu"nafada bagun zuciyata na karuwa. "Kuma kace itace t kwatan ta maka nan gidan" "Shakka babu" "Jiya kuma kuka hadu?" "Shakka babu" Na kara mai maitawa ina mamakin tambayoyin. "A Lagos kuma kuka hadu?"Ya tambayeni cikin shakkar abin dana ke fada "Shakka babu" Yayi shiru yanayimin wani irn kallon mamki,kamar ni ne mutum daya taba gani arawursa. Nikaina kallon mamakin da yake min sai yasa na rika yi masa kallon mamaki. "Ba wani abune yasa nake maka wadannan tambayoyiba , Shuraih Usman saboda agaskiya wani irin. Rikitaccen al'amarine ka zo da shi. Hakika nan ne gidan su farida,saidai ina mai tabbatar ma faridan dake nan gidan ta dade da MUTUWA" SIRRINSU Littafina daya Chapter 4 By Shuraih Usman Cikin matukar mamaki idona yazzaro,bakina a bude na kalleshi kallon da ya karyata Abin daya fada. "Shakka babu,zuciyata bata amince da abin daka fada ba. Na rantse da wanda raina ke hannunsa jiya mun hadu da farida a Lagos ,kuma ita ce ta kwatan ta min nan gidan har na bata zobena .shin ba farida ce doguwa fara mai yalwar gashi ba? Ina ganin meenat nasan kanwarta ce ,don kamar da sukayi" Kallon mamakin dake fuskarsa yai hijira sannan kallon akwai matsala a kwalkwata ya ziyarci fuskarsa. "Dankari! Agaskiya kazo da babban magana ,domin ita meenat daka tambaya har tanzu a tsorace take,a tunaninta kai mahaukacine, tabbas tasan farida ta mutu" Wani dattijo yazo zai wuce yana jan tasbaha , biye dashi wasu almajiraine su uku "Alaramma! Wai kaga wannan ne bai yarda cewa farida ta mutu ba "saurayin yafada lokacin da wannan dattijo yazo gabda mu zai gifta. "Kamar yaya bai yarda. Ta mutu ba ?" Ya tambaya "Malam anshakka babu jiya na hadu da farida a Lagos ,kuma itace ta kwatantamin nan gidan" Shi da almajiran Shuraih Usman suka kura min ido,suna yi min kallon anya ban tabu ba. A gaskiya sai dai kowata faridar,amma wace kenan gidan ta dade da mutuwa kuma mata tace ta wanke gawarta. ******* Na yi shiru ina birkitaccen tunani lokacin da saurayin yashiga gida. Wasu yara suna gara taya,suka zo wucewa na tsayar dasu. "Kai don Allah anan unguwar kuke ?" "Eh"suka amsa "Ko kunsan Farida tanan gidan?" "Mun santa amma ta dade da mutuwa" Adaide wannan lokaci sai saurayin yafito ,rike da kundin adana hotuna (album). "Duba sosai kaga ko wata kagani mai kamar Farida"ya fada lokacin dana fara buda kundin hotunan.*Shuraih Usman* "Shakka babu faridan dake jikin wadannan hotunan ita ce Faridar data kwatanta min wannangidan,kuma ita ce ta karbi zobena a Lagos,wannan ko shakka babu" Narika fada lokacin dana ke nuna hotunanta. Kamar na fita daga hayyacina . "Shinyaya sunanka malam"ya tambayeni. "Habib" "Nikuma Nasir"~ Anya habib ba mafarki kayi kunhadu da ita ba?" "Jiya an yi ball tsakanin Nigeria da Costrica a Lagos?" "Tabbas" yafada. To shakka babu jiya na hadu da farida a Lagos,kuma ita ta kwatantamin nan gidan" "To ai ni abin dake bani mamki shine babu abin da yada farida da Lagos ko da tana da rai domin bamu da kowa aLagos" Ya. Zura hannunsa a aljihun wandonsa ya fito da kundin rubuta muhimman al'amura ,don tunawa gaba(Dairy)ya miko min bayan ya budo inda yake so naduba* Shuraih Usman* RANAR ALHAMIS 1-2-96,RANAR BAKIN CIKICE GAREMU.RANAR DA FARIDA TA KOMA GA MAHALLICCINTA,ALLAH YAJI KANTA,YAYI MATA GAFARA DA RAHAMA. Cikin matukar fargaba da mutuwar jiki kwalkwalwata ta kasa tabuka komai,namika masa littafin. "Don na kara gamsar da zuciyaka,Farida kwananta biyu a hafsat private Hospital ta mutu,zamu iya zuwa can don su kara yimaka bayani ko ka sami cikakkiyar gamsuwa" Ban yi masa musu ba muka nufi hafsat private Hospital. Mun samu likitan dogo siriri wankan tarwada,mai gashin baki sanye da kayan aiki na likitoci a jikinsa.mutum ne mai fara'a wanda yafi dacewa da malami akan likita . "Ka shai dani?"Nasir ya tambaye shi. Bayan mungaisa "Kwarai kuwa. Bakaine kanen farida. Wacce ta mutu anan asibitin shekaru uku da suka wuce ba. SIRRINSU Littafina daya Chapter 5 By Shuraih Usman "Tabbas nine,dama don Allah muna bukatar shaidar cewar anan ta mutu,fatan dai kuna ajiye irin wadannan takardun?" "Hakika muna ajiyewa ,domin dokar asibitin ce ,ku danyi min hakri mintuna biyar,ina zuwa" "Yafada lokacin yanufi wani daki Shakka babu wannan al'amari haka yake,na duba wadannan takardu kuma na gamsu,sai dai har yanzu mamakin al'amarin ya sa kwalkwalwata ta birkice . Na hadu da mace jiya ace ,yau shekarunta uku da mutuwa?" Har zan tafi sai yace na tsaya ya kirawo babarsu,don ita ma ta tabbatar min cewar farida ta mutu. Babu abin da ya kara ba ni mamaki ,irin matukar kama da farida ta yi da mahaifiyarta , Kamar ka tsaga kara gida biyu. Kundin adana hotunan da nasir ya kawo min,har yanzu shine a hannunta. Bayan mun gaisa ta miko min kundin adana hotunan ,tace na kara dubawa,ko dai wata faridar ce . Bayan na duba na kara gamsuwa, sai na zari daya daga cikin hotunan batare da sunsani ba. Sanye take da doguwar bakar riga ,data yi matukar dacewa da jar fatanta. Tasaki yalwataccen gashinta ya zubo har gadon bayanta,sannan tayi amintaccen murmushi dakan dau hakalin kowane namiji. Sannan na mika mata kundin adana hotunan* _ Shuraih Usman _ * "Shakka babu, wacce ke jikin hotunan nan ,itace faridar dana hadu da ita a Lagos. Kuma iace ta kwatantamin nan gidan,kuma har zobena nabata . Wannan ko shakka babu na rantse da wanda ya aiko Annabi dagaskiya ,duk abin dana fada gaskiyane" Tayi shiru tana kallon fuskarta,kallon dake nufin matukar mamkin abin dana fada. "Shakka babu aljana ce ta fito maka a siffar Farida. Wacce kuka hadu da ita ,tabbas ba farida bace . Farida yatace,ni na haifeta kuma yau shekarunta uku akarkashin kasa. Sauda yawa sukan fito ma mutane a siffar mutane ,kamar yanzu yafaru yanzu akanka . Ba mamki so take ku hada gwiwa don gudanar da wani al'amari,domin da cutar dakai zata yi shiga jikinka zata yi. Wanda wannan bakon abu ba ne* _ Shuraih Usman _ *sau nawa aljanu ke shiga jikin mutane? Abu daya kawai za kayi,shine samun cikakken bayani daga masana akan _SIRRINSU_ " Bayan nayi mata godiya ,mun yi sallama ta koma, sai nasir yace muje makabartar da akabinne farida,don naga kabarinta ko na kara gamsuwa . Katuwar makabarta ce da aka katangeta , muna shiga makabartar sainaga kamar film din ban tsoro (Horrow) nake gani kokuma mummunan mafarki nakeyi. Wani tsamurarren mutum gashin kansa amurmurde ya nufo mu ,ashe shine mai gadin makabartar. "Don Allah zan raka wannan kabarin yayata"nasir yafada. "Farida?"Maigadin yafada cikin muryar tausayi. Simin taccen kabari Nasir yanuna min ajerin kabarurruka na takwas. * Shuraih Usman *"kaga kabarinta" maigadin yanuna min. Daga kusa da kabarin kafaffen katako ne anyi rubutu ,balo-balo ajikinsa kamar haka:- *_FARIDA TA MUTU RANAR ALHAMIS 1-2-1996._* Nakurawa kabarin ido ina mamkin,yanzu faridar dana hadu da ita jiya itace a kwance anan!shinfitowa tayi ta tafi Lagos muka hadu?ko kuwa fatalwarta ce_(hmm nima amsar danake ni ma kenan)_ Wani abu dake sheki akan kabrin,shine ya katsemin tunanina ,cikin mutuwar jiki sannu ahankali nanufi kabarin. Na tsinci kaina cikin tangamemen tafkin abin mamakin daya girgiza rayuwata,tunanina da kuma hankalina .Shakka babu abin dake kyalli akan kabarin *_ZOBEN_* dana bawa farida ne jiya a Lagos SIRRINSU Littafi na daya Chapter 6 By Shuraih Usman C 4~3~'99. *_KARFE TARA NA DARE_* Ahmad mutum mai matukar farinjini, da mutunci a idon al'umma .kuma shi yake da hakkin mallakar kamfanin jarida DANKARI,kamfanin jarida mai zaman kansa a hausawa sabontiti dake birnin kano. Kamar yadda yake da farinjini haka ma jaridarsa , tayi matukar karbuwa a wajen al'umma . Jaridar DANKARI,ta kan taba kowanne bangare na rayuwar dan adam,sannan kuma tana kunshe da labarirrikan abubuwan abin mamaki. Da suke faruwa aduniya,wadanda idan badon sun faru ba,idan wani yafada baza'a yarda da shi ba. Ahmad shine yake auran yayata fatima ,saboda shakuwar da mukayi da shi agidansa nake kwana ,kuma a kamfaninsa na ke aiki. Wasu lokutan tare muke shawagin dauko rahotanni,kamar yadda ya tafi dani Lagos da Kaduna . Mexico da Ireland na gama wasansu na karshe muka dawo kano. Gidansa kayattacce ne kuma yalwatacce,bene hawa daya dake fuskantar bakin titi a unguwar. Tara daidai na dare ina zaune a falon gidansa,kwanukan abinci a girke. Akan tebirin dake gabana . Babu abin ke matukar jefa nishadi a zuciyata game da aurensa da fatima ,irin zunzurutun *_SO*_ da kaunar juna da suke yi. Tun data ajiye min abincin ko kara tunawa da shi banyiba ,sakamakon zuzzurfan tekun tunani dana zurfafa. Na tuna lokacin dana mika hannu hankalina a tashe,jikina na rawa na daunko zobena ,dake kan kabarin Farida.*_ Shuraih Usman *_ Shi kansa Nasir da maigadin makabartar sunyi matukar fahimtar razana da kidimewan dana yi. Shakka babu na hadu da farida jiya a legos,kuma shakka babu na bata zobena ,sannan shakka babu na tabbatar ta mutu ,sannan shakka babu zoben dana tsinta akan kabarin shine wanda na bata ta kuma saka ahannunta .(Shakka babu nima shuraih wannan al'amri ya kidimani) Shin yanzu wa zan gayawa wannan birkitaccen al'amari ya gaskatani? Wane ne zai yarda dani idan na ce jiya na hadu da mace a Lagos ,kuma shekarunta uku da mutuwa ?"*_ (shakka babukoni bazan yadda dakaiba )_* "Shine zoben daka bata" nasir yatambayeni cikin kaduwa. "Shakka babu"cikin kidemewa na fadamasa. "Nasir bana son kowa ya yarda da wannan rikirkitaccen al'amari daya faru gareni,domin nasan shakka-babu babu wanda zai gaskatani" "Habib ! Ba na shakka,bana kokwanto wannan al'amari daya faru zuciyata ta gaskatashi." "Shin yanzu aljana ce ta fito min jiya a siffar farida?"*_ Shuraih Usman _* "Shakka babu amsar kenan domin farida ta riga ta mutu" *********** Sai da muka dawo kano na tuna ban tambayi nasir game da kodaddiyar matar dana gansu da farida ba. Shakka babu aljanu na hadu da su,domin kallo daya zaka yi wa mummunar matar nan,ka san cewar aljana ce . Natuna yadda na tsorata lokacin dana ganta ,da kuma yadda naji na tsaneta . Har muka dawo kano hoton farida da zobena da na bata , na kuma gan shi akan kabarinta , Sune abin da hankalina da tunanina suka tattara akai. "Tunanin me kake yi habib?" Fatima fara mai matsa kaicin tsayi da kauri,sanye da a tamfar Holland dinkin sirfani,ta tambayeni tana murmushi. "Tun dana kawo maka abnicin,har yanzu ko taba shiba kayiba " Nayi ga wurtacciyar ajiyar zuciya ,lokacin dana fito da hoton farida daga aljihuna ,na kuma dora zoben akai,sannan na mika mata . *_ Shuraih Usman _* Shakka babu kaki cin abinci kuma kamanninka sun birkita ,wannan irin zukekiyar yarinya ,gaskiya kyakkyawa ce " Ta fada lokacin data dawo min da zoben, hoton har yanzu na hannunta . "So nake kikare ma zobennan kallo" "Kamar ya nakare masa kallo,ba shine zoben dana baka ba ?"Cikin mamki ta fada . "Kin tabbatar shine " "Shakka babu shine" Ta fada bayan ta kare masa kallo sannan na kara zura shi a dan yatsana ,tun lokacin dana daukeshi ban mayar dashi hannu na ba . "Fatima ! So nake na yi maki wasu tambayoyi" "Allah yasa ina da amsarsu" Fatima ta kasance mace ma'abociyar ilmin Addinin islama, ta bangaren tarihi,littatafan fiqhu,hadisai dakuma Alqur ani. "Shin ko a karance -karancen da kika yi na hadisai,dana tarihi,da kuma na fiqhu zuwa Alqur'ani ,kokintaba karo da cewar mutum idan ya mutu an binne shi,kan iya tasowa yaci gaba da rayuwa?" SIRRINSU Littafi na daya Chapter 7 By Shuraih Usman Tayi dan shiru na wasu lokuta ,wanda hakan yasani tsammanin ko gaskiya ne ana mutuwa a taso. "Mutuwa dai na nufin rabuwar ainihin rai da gangar jiki. Ku ma ahakikanin gaskiya idan har ubangiji ya umarci mala'iku,suzare ran mutum,suka kuma zare,shakka babu wannan mutum bazai kara tasowa duniya don cigaba da wata rayuwa ba. Har sai lokacin da ubangiji yakara dawo masa da ransa,don tsaiwar ranar ALKIYAMA. Yana faruwa mutum yai doguwar suma a zanta ya mutu,har sai an masa wanka ana kokarin binneshi sannan ya farfado. Wasu idan suka yi wannan suman sukan sami har kwana daya kofiye da haka. Amma idan har an zubawa mutum kasa aka binne shi , Shakka-babu wannan tasa takare. A kwai rayuwa da akeyi idan anmutu(HAYATU-B ARZAKIYYA)rayuwace da mamaci ke yi idan aka binne shi ,duk wanda aka binne shi akan dawo masa da ransa ,don sanin cewar wani matsayi yake . Idan aljanna ne akan hada masa wani dausayi na aljanna,kamr yadda akan hadawa dan wuta wani narko daga jahannama .*_(wa iya zu billah)_* Shuraih Usman Idan har mutum ya mutu to bashi da wata dama ,da zai cutar da rayayyu ko kuma ya amfanar dasu. Shi wannan tasa ta kare sai yadda Allah yayi da shi" "Shin dagaske ne idan mutum ya mutu,ya kanyi fatalwa ya dawo duniya?" Wannan karonma. Shiru tayi na dan lokci. "Aduk lokacin da mutane suka ji ance fatalwa,abin da kawai suke dauka shine ,bayan mutum idan ya mutu idan ya kasance yana da matukar buri,ko ba'a yi masa sadaka . Sai yakara dawowa,yana tsorata al'umma. Wanda a zahirin gaskiya wannan al'amari bahaka yake ba. A bin dake faruwa shine ,aljanu ne ke fitowa a siffar wanda ya mutu don surika tsorata al'umma ,suna jefa zukatansu cikin rudani" Tana fadin haka sai gabana yai mummunar faduwa. "Wasu lokutan idan shahararren mutum ya mutu,sai aljanu su rikida da siffarsa,da zarar

Chapter 1 of 3