Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 4
a karo na biyu ya kyalkyale da dariyar mugunta wacce tafi ta farko.Cikin tsananin razana da dimaucewa sarki da yarima suka rikito kasa daga kan kafadar dodo lasuruba cikin yanayin suma suka iso kan cinyarsa suka baje,koda ganin haka sai dodo lasuruba ya hura musu iskar cikin hancinsa suka farfado daga suman da sukayi,iskar bakinsa ya hura musu kuwa saida jikinsu ya zagwanye ya narke saboda zafinta da tururinta tamkar na dafaffiyar darma ne.Lokacin da sarki da yarima suka farfado suka mike tsaye a firgice bisa kan cinyar dodo lasuruba sai suka daga kawunansu sama sukayi arba da fuskar lasuruba.Nan take suka firgita ainun fiye da koyaushe saboda ganin yadda fuskar tasa ta murtuke izuwa tsananin fushi.Dodo Lasuruba ya dubesu duk su biyun sannan yayi musu guntun murmushi yace yaku wadannan hatsabiban bil'adama na baku dama kuma kunyi wasa da damar taku,don haka yanzu karshen rayuwarku tazo.Alfarma daya zan iyayi muku a yanzu,idan kuna ganin cewa zaku iya tsere mini to ku falfala da gudu ku fice daga cikin dajina.amma nayi muku alkawari ko kunfi iska karfin gudu saina kure muku gudun na hallaka ku.Koda jin wannan alfarma ta biyu sai sarki ya dubi dodo Lasuruba ya daka masa tsawa yace yakai wannan tsohon azzalumi takadarin matsafi kayi sani cewa ni a rayuwata ban taba guduea ba don wuya ko tsoro domin namijin kwarari baya shakkar mutuwa a filin daga.Ina tabbatar maka da cewa babu inda zamu dara daga nan saidai ka kashemu a nan idan kana iyawa.Cikin tsananin mamaki dodo lasuruba ya dubi sarki yace hakika wannan bil'adama ka cika hatsabibin kanka domin kai ne mahaluki na farko daya taba yi mini tsawa a rayuwata kuma kaine wanda ya taba gaya mini bakar magana tunda na wanzu a doron kasa tsawon shekaru dari bakwai da sittin da uku.Tun ina rayuwa a can bangon karshen duniya bangaren yamma har na dawo nan.Tabbas yau zanyi masa kisan gillah irin wanda ban taba yiwa wani mahaluki ba walau mutum ko aljan.Gama fadin hakan keda wuya sai dodo Lasuruba ya kawowa sarki cafka da hannunsa guda cikin shammace,nufinsa idan ya cafke shi ya rinka gutsurar sassan jikinsa da kadan kadan yana cinyewa harya gama cinye shi gaba daya.Bisa mamaki sai dodo Lasuruba yaga sarki ya daka tsalle sama daga inda yake tsaye ya koma can kan daya cinyar tasa.Hannun Lasuruba ya kama iska karfin hucin iskar hannun dodo Lasuruba tayi jifa da yarima can gefe daya ya maku a jikin wani dutse take kafarsa ta dama ta karye ya kasa mikewa tsaye.Bisa dole ya zauna a kasa dirshana ya zuba idanu kawai yana kallon mugun artabun da akeyi tsakanin sarki da lasuruba cikin tsananin tsoro domin gaba dayan jikinsa ya kama tsuma.Dodo Lasuruba ya cigaba da kaiwa sarki cafka da mangari da dukkan karfinsa da zafin namansa shima sarki saiya cigaba da gocewa yana tsalle tsalle a sassan jikin Lasuruba.Duk sa'adda hannun Lasuruba ya bugi dutse sai kaga dutsen ya tarwatse komai girmansa da kwarinsa.Idan kuwa bishiya ce dagargajewa take kamar an dakata a turmi kuma saita tumbuke har jijiyoyinta.Saida aka shafe sa'a guda ana wannan artabu dodo Lasuruba ya kasa taba sarki ko sau daya.Al'amarin dayai matukar baiwa shi kansa Lasuruba mamaki kenan domin bai taba haduwa da wani mahaluki daya gagareshi hallakawa ba a cikin dakika biyar.Shi kuwa yarima dake zaune acan gefe daya yana kallon abinda ke faruwa kamewa yayi kamar gunki saboda tsananin mamaki ya kasa kifta idanunsa.A iya rayuwar da yayi zama tare da sarki bai taba sanin cewa sarki yana da irin azababben zafin nama ba gami da juriya da jarumtaka haka ba.Lokacin da sarki yaga ya fara gajiya da tsalle tsalle gami da goce goce akan dodo Lasuruba sai hankalinsa ya dugunzuma ainun domin yasan cewa idan bai dauki matakin gaggawa ba karshe lallai dodo Lasuruba zai hallaka shi sannan ya hallaka yarima.Ko kadan sarki bai damu da tasa mutuwar ba burinsa kawai shine rayuwar yarima ta tsira kuma tafi birnin kisra tare da kan dodo Lasuruba domin ya sami damar auren gimbiya Siyamat.Koda sarki ya ayyana wannan al'amari a cikin zuciyarsa sai yaji wani irin sabon karfi ya shigeshi nan take ya daka wawan tsalle na ban al'ajabi ya dira akan hannun Lasuruba.Shi kuwa dodo lasuruba ya dago hannun nasa da nufin yayi cilli dashi,damar da sarki ya samu kenan ya kara yin sama kamar an harbo shi daga cikin kwari da baka,kai tsaye ya shige cikin hancin dodo Lasuruba.Ai kuwa yana isa karshen hancin sai ya daddage iya karfinsa ya naushi hancin.Take hancin ya burma saiga jini na malalowa waje.Ashe ruhin dodo Lasuruba a cikin hancinsa yake,nan fa dodo lasuruba ya kama matagungun daga tsaye ya fado kasa yana birgima in badon sarki yayi wuf ya daka tsalle ta cikin burmammen hancin nasa ba daya kife dashi.Cikin zafin nama sarki ya suri yarima ya azashi a kafadarsa ya falfala da matsanancin gudu don ya fice daga cikin dajin gaba daya.Birgimar da dodo Lasuruba ya rinka yi a kasa ne ta haddasa girgizar kasa.Ruwan jinin daya rinka malala daga cikin hancinsa kuwa saiya cika dajin gaba daya tamkar teku ce ta balle har saida ya shanye su sarki suka rinka iyo a cikinsa.Har su sarki suka fita wajen dajin basu daina jiyo ihun dodo lasuruba ba kuma dajin gaba dayansa bai daina girgiza ba sai bayan sa'a guda sannan komai ya tsaya cak,a sannan ne sarki ya dawo da baya yana goye da yarima a bayansa suka cigaba da iyo a cikin jinin dodo lasuruba suka iso har inda gawarsa take.A sannen ne sarki ya sauke Yarima a gefe daya sannan ya zaro wani gatari daga cikin jakarsa ya rinka saran wuyan dodo lasurua.Wannan karon sai gashi gatarin na datsa kasusuwan wuyan dodo lasuruba da jijiyoyin amma saboda yawansu da kwarinsu saida sarki ya shafe sa'a uku yana saransu sannan ya sami nasarar gutsure kan.Nan take sarki ya dawo inda yarima yake ya gyara masa karayar dake kafarsa sannan ya ciccibi kan dodo Lasuruba ya dora akansa kuma ya sake goye Yarima suka fice daga cikin dajin Shakkaful Zamral cikin tsananin farin ciki bisa samun wannan gagarumar nasara.Kuji Gwarzon Namiji. A Can Birnin Kisra Sarki Da Dansa Yarima Kuzzaru na zaune a fada jama'a sun cika makil ana tafiyar da harkokin mulki sai kawai aka jiyo shewa da hayaniya daga can cikin gari.Al'amarin daya dugunzuma hankain kowa kenan a fadar.Nan take sarki ya tashi manzo yace dashi ya ruga izuwa cikin garin yaje ya gano abinda ke faruwa,kuma sannan aka umarci dakaru dasu fara shiri ko yaki ne ya barko ba'a sani ba.Nan da nan kuwa wannan manzo ya cika umarni sai gashi ya dawo a guje yana haki.Da shigowar cikin fadar saiya fadi gaban sarki yace ya shugabana ai ba wani abu bane ke faruwa ba face dawowar yarima Farhama da mahaifinsa daga dajin shakkaful Zamral kuma sun sami nasarar kashe dodo lasuruba har sunzo da kansa.Koda jin wannan batu sai gaba dayan jama'ar dake fadar suka mike zumbur suka fice waje da gudu domin suje suga zahiri da idanunsu.Ya rage saura sarki,fadawansa,yarima Kuzzaru da boka Zuraita kadai zaune a fadar.Cikin tsananin tashin hankali sarki ya dubi boka Zuraita yace yakai amintaccena yanzu menene abinyi?Ka sani cewa bazan iya rabuwa da yar uwata gimbiya Siyamat ba na bayar da ita inda bazan sake ganinta ba kuma gashi ban isa na karya alkawarin dana dauka ba cewar zan aurar da ita ga wanda yaje dajin shakkaful zamral ya kashe dodo Lasuruba yazo da kansa.Sa'adda boka Zuraita yaji wannan tambaya sai ya sunkui da kansa cikin alamun kunya sannan yace ya shugabana kayi sani cewa wannan al'amari yafi gaban tunanina domin har a yanzu ina shakka ne ace wai yarima Farhama yazo da kan dodo lasuruba.Mu tsaya muga isowarsu nan fada tukunna don idanunmu suga zahiri.Ai kuwa kafin cikar dakika dari uku da hamsin saiga yarima Farhama tare da mahaifinsa sarkin Kairufa sun iso fada bisa dawakansu.Yarima Farhama na dauke da kan dodo Lasuraba.Shi kansa wannan kai na dodo Lasuruba saiya zamo abin tsoro ga jama'a duk wanda ya kallashe sau daya sai kaga ya kau da kai ga barin kallonsa Don gani yake kamar a koyaushe zai iya motsawa ya hallakar dashi.Lokacin daya rage baifi saura taku goma ba tsakanin su yarima Farhama dasu sarkin kisra sai su Farhama suka ja linzamin dawakansu suka tsaya sannan mahaifin yarima Farhama ya sauko daga kan dokinsa ya dubi sarkin Kisra yace yakai wannan sarki mai daraja kuma mai adalci na sani cewa kai mai cika alkawari ne saboda haka yanzu gashi dana ya lashe wanann gasa ta auren yar uwarka gimbiya Siyamat saboda haka saika cika alkawari ka aura masa ita yanzu ka bamu ita mu tafi da ita izuwa birninmu na Kairufa.Ka sani cewa wannan kai na dodo Lasuruba yafi komai daraja a duniya a yanzu domin duk wanda ya mallakeshi tamkar ya mallaki komai da kowa ne na duniya,to amma mu bama bukatarsa domin yar uwarka Gimbiya Siyamat tafishi daraja a wajenmu.Yanzu gani nan gare ka zan damka maka wannan kai domin ka cika mana alkwarin daka daukar mana.Koda gama fadin haka sai mahaifin yarima Farhama ya karbi kan dodo Lasurba daga hannun Farhama ya nufi karagar sarki da nufin ya damka masa.Saida ya rage saura baifi taku uku ba kacal ya isa gareshi sai kawai akaga wata irin iska mai karfin gaske daga can kololuwar sama ta sauko kasa ta sure wannan kai na dodo Lasuruba daga hannun sarkin kairufa tayi masa dashi.Nan take sarkin kairufa yayi nuni da hannunsa izuwa ga wannan iska domin ya dawo da kan Lasuruba ga hannunsa ya zamana cewa shima yana amfani da tasa iskar sihirin amma sai tasa iskar ta kasa tasiri akan waccan.Yana ji yana gani kan dodo lasuruba ya rinka lulukawa can kololuwar sama har ya kule a cikin gajimare.Koda ganin haka sai sarkin Kairufa da yarima Farhama suka tsandara ihu cikin bakin cikin.Daga can sai sarkin kairufa ya dubi sarkin kisra yace yakai wannan sarki mai daraja dajin kai kaga abinda ya faru yanzu da idanunka,saboda haka inason kaji tausayinmu kayi mana adalci ka bamu auren yar uwarka gimbi Siyamat tunda dai mun cika aiki munzo da kan Dodo Lasuruba kowa yaga shaida.Koda jin wannan batu sai sarkin Kisra yayi murmushin mugunta sannan yace tabbas kunzo da kan dodo Lasuruba amma ai baku damka mini shi ba.Ku sani cewa kan dodo Lasuruba shine fa sadakin yar uwata Gimbiya Siyamat.Ta yaya kuke tsammin zan bayar da auren yar uwata babu sadaki?Ai abin kunya ne kuma abin kaskanci a gareni,saboda haka ina mai shawartarku daku sake bazama neman wannan kai na dodo lasuruba ku karbo shi daga hannun wanda ya raba ku dashi daga nan zuwa kwana arba'in.Idan kuwa kuka kasa shike nan kun rasa auren gimbiya.Koda jin wannan batu sai yarima Farhama ya sauko daga kan dokinsa ya ruga izuwa wajen mahaifinsa ya rungumeshi kuma ya fashe da kuka yana mai cewa shike nan na rasa gimbiya,na rasa gimbiya har abada.Ganin haka ne yasa gaba dayan jama'ar dake fadar suka kamu da tsananin tausayin yarima Farhama domin yaga samu kum yaga rashi.Shi kuwa sarkin kairufa saiya janye jikinsa daga cikin na yarima Farhama ya dubeshi cikin murmushi kuma yasa hannu ya share masa hawaye sannan yace daina kuka yakai dana ka sani cewa muddin ina numfashi a doron kasa saika auri gimbiya Siyamat.Koda gama fadin haka sai sarkin Kairfufa ya dubi sarkin kisra a fusace yace yakai wannan sarki ka saurari ranar da zaka rabu da gimbiya Siyamat,rabuwa ta har abada domin nasan abinda kake gudu kenan.Ina tabbatar maka da cewa shi kansa abin dogaron naka boka Zuraita bai isa ya hanani aurawa dana yar uwaraka gimbiya Siyamat ba.Gama fadin hakan keda wuya sai sarkin kairufa ya kama hannun yarima Farhama yaja shi izuwa inda dawakansu suke suka hau suka fice daga cikin fadar.Ai kuwa bayan sati biyu da faruwar wannan al'amari ne aka nemi gimbiya Siyamat sama da kasa aka rasa.Koda boka Zuraita yayi bincike saiya gano cewa sarkin Kairufa ne ya turo wadansu shararrun barayin aljanu wadanda babu kamarsu a duniya suka sace gimbiya Siyamat suka kaita can birnin kairufa har ma an daura aurenta da yarima Farhama.Kuma a ranar da aka daura auren mahaifin yarima Farhama ya rasu sakamakon wannan rauni dake gadon bayansa.A wannan rana yarima Farhama ya tsinci kansa a cikin tsananin bakin ciki da kuma farin ciki.Bayan an binne mahaifinsa ne yasa wani gwanin masassaki ya sassaka masa gunkin mahaifinsa dana dodo lasuruba aka kafa su a tsakiyar gidan sarautarsa kuma ya bayar da labarin duk irin fafatawar da sukayi da dodo lasuruba aka rubuta shi a jikin gini kusa da wadannan gumaka biyu.Bayan boka Zuraita yaga duk wannan al'amari cikin madubin tsafinsa saiya labartawa sarki.Koda jin haka sai sarki ya fusata ainun nan take yasa aka rubuta wasikar yaki ya aikawa da sarki Farhama shima sarki Farhama saiya aiko da raddi.Saida aka kwafsa yaki sau shida tsakanin kasashen biyu amma duk sa'adda akayi yakin babu bangaren dake samun nasara saidai ayi KARE JINI-BIRI JINI har tsawon shekara shida Sarkin Kisra bai sake ganin yar uwarsa gimbiya Siyamat ba.Tsananin yawan tunaninta da begenta ne ya haddasa sarkin kisra ciwon zuciya ya zama ajalinsa.Tun daga sannan ne gaba mai tsananin ta sake kulluwa tsakanin sarki Kuzzaru da Sarki Farhama.Har kwanan gobe sarki Kuzzaru bashi da wani buri wanda yafi ya yaki sarki Farhama ya kawar dashi domin ya karbo yar uwar mahaifinsa gimbiya Siyamat.Wannan shine abinda ya faru a baya kimanin shekaru talatin da suka gabata. *** *** ***Lokacin Da Sarkin Yaki Huzaika ya isa gidan boka Zuraita ya sanar dashi sakon sarki sai boka Zuraita ya kwala ihu idanunsa suka kada sukayi jawur.Al'amarin daya firgita sarkin yaki Huzaika kenan.Daga can sai boka Zuraita ya dubi Huzaika yace ka koma wajen sarki ka sanar dashi cewa idan har yana tare da wannan yaro Shubairu ban isa nazo kusa dashi ba,idan kuwa nazo saina hallaka domin yaron yana da TSATSUBA mai karfi a jikinsa wacce duk wani mai sihirin tsafi idan ya kusance shi zai hallaka,kuma babu tsafin da zaiyi tasiri idain dai yana wurin.Haka kuma ka gaya masa cewa shawarar da yaro Shubairu ya bashi akan attajiri Ubairu itace mafi alheri a gareshi,kawai yayi shirin yaki ya fita ya kawar da Ubairu da jama'asa.Wannan shine iyakar abinda zan iya gaya maka.Koda jin wannan batu sai sarkin yaki Huzaika ya yiwa boka Zuraita sallama ya tafi izuwa gidan sarki Kuzzaru domin ya sanar dashi bayanin da boka Zuraita yayi... SHIN SARKI KUZZARU ZAI FITA YA YAKI UBAIRU DA JAMA'ARSA? IDAN AKAYI YAKIN SU WAYE ZASU SAMI NASARA? YAUSHE NE SARKI FARHAMA DA SARKI KUZZARU ZASU SAKE HADUWA SU KWAFSA YAKI? SHIN SARKI KUZZARU ZAI CIKA BURINSA NA KARBO GIMBIYA SIYAMAT DAGA HANNUN SARKI FARHAMA? A WANE HALI GIMBIYA SIYAMAT TAKE YANZU BAYAN RABUWARTA DA DAN'UWANTA SARKIN KISRA TSAWON SHEKARU? WADANNE IRIN ABUBUWAN AL'AJABI YARO SHUBAIRU ZAIYI NAN GABA A RAYUWARSA? YAYA KARSHEN GABAR SARKI FARHAMA DA SARKI KUZZARU ZATA KASANCE? Mu Hadu A DAKAKKIYAR ZUCIYA Littafi Na Uku Domin Jin Cigaban Wannan Kasaitaccen Labari. Anan Na kawo Karshen Dakakkiyar Zuciya Littafi Na Biyu.Dama kamar yadda na fada muku Littafi na daya dana biyu ne kawai suka fito kuma kuka ce ayishi.To gashi dai mun kammala shi.Saboda karku yimin korafi. Dont just read and Pass. Wai Kusa A ganinku waye ya haddasa Gaba a tsakanin Wadannan sarakuna guda biyu? Sarkin Kisra ko Sarkin Kairufa? An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 4 of 4