Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 4
sarki yayi.Nan yake sarki ya bude baki ya fara karanta wadansu dalasiman tsafi a fili shi kuma Yarima Farhama saiya bude baki yana maimaita abinda sarki ya karanta.Faruwar hakan keda wuya sai wannan iska dake yi musu kawanya ta rikide ta zama wadansu irin gajerun dodanni yan wadanni wadanda tsawonsu bai wuce kamu uku ba.Suna da manyan kunnuwa fala fala kamar na giwa.Hancinsu wawakeke ne babu kyan gani.Haka ma bakunansu,idanuwansu manya manya ne kwala kwala kuma jajaye tamkar garwashin wuta.Komai dakewar zuciyar mutum idan yayi arba da wadannan dodanni sai ya razana musamman idan ya dubi murtuka murtukan kafafunsu wadanda basu da yatsu sai kofato.Gaba daya jikin dodanni a cike yake da wani irin gashi mai tsini tamkar kayoyi aka sossoka.Koda sarki yayi arba da wadannan dodanni sai yayi sauri ya zare takobinsa daga cikin kasa ya mike tsaye zumbur yana mai rike da takobin da hannu biyu,shima yarima Farhama sai yayi koyi dashi suka jingina da bayan juna.A wannan lokaci tuni dodannin sunyi musu kawanya kuma adadinsu yakai dubu.cikin yanayin damuwa sarki ya dubi yarima Farhama yace yakai dana kayi sani cewa a iya rayuwata ta duniya ban taba ganin irin wadannan dodanni ba,kuma ban taba jin labarin irinsu ba.Saboda haka bani da yakinin cewa zamu iya kawar dasu idan kuwa har zamu iya din to tabbas zamu iya shan bakar wahala kila kuma su hallaka mu.Abinda nake so dakai shine kada zuciyarka ta karaya domin da zarar ka sami karayar zuciya shike nan ka baiwa abokin gaba kofar samu nasara.Lallai mu jajirce iya karfinmu da kokarinmu a kan wadannan dodanni domin kubutar da rayuwarmu.Kafin sarki ya gama rufe bakinsa tuni dodannin gaba dayansu sun afka musu.Nanfa wuri ya yamutse aka ruguntsume da azababben yaki,in badon sarki da Yarima Farhama sun kasance masu zafin nama da sadaukantaka ba da tuni dodannin sun hallaka su cikin dakiku kadan.Bababban abinda yafi dugunzuma hankalin su Farhama shine ko kadan dodanni basa jin SARA DA SUKA domin a koyaushe ma kare hari suke da hannayensu suna dade yanyame su sarki,da karfin damtse sarki ke tarwatsa su suna kutsawa ta cikinsu amma duk dodan da suka bazar a kasa sai suga ya mike tsaye zumbur ya cigaba da kai musu hari.Abinda ya kara daurewa sarki kai shine tsafinsa yaki yayi tasiri bare yayi amfani dashi wajen hallaka dodannin.Sa'adda sarki yaga an shafe rabin sa'a ana wannan gumurzu basu sami nasarar komai ba akan dodanni sai hankalinsu ya dugunzuma ainun domin ya fahimci cewa a duk lokacin da suka gaji shida yarima sannan ne dodanni zasu sami galaba akansu.Koda fahimtar hakan sai hankalin sarki ya dugunzuma amma dayaga bashi da wata mafita sai ya dada jajircewa ya ciga da yakin iya karfinsa.Ana cikin fafatawar ne daya daga cikin dodannin wani mai zafin nama da nacin tsiya ya daka tsalle a sama ta bayan sarki ya karta masa faratan hannayensa biyu a gadon baya.Saboda kaifin faratan dodon saida bayan sarki ya dare jini yai tsartuwa da feshi.Sarki dai bai san sa'adda ya kwala uban ihu ba yayi taga taga zai fadi amma saboda taurin rai da karfin zuciya bai fadi ba a haka ya cigaba da yakin.Koda yarima Farhama yaga wannan rauni da akayiwa mahaifinsa sai zuciyarsa ta harzuka ainu shima ya zabura cikin zafin nana ya daka tsalle sama ya tari wannan dodo wanda ya yiwa sarki mugun rauni cikin mugun nufi dodon ya kawowa Farhama suka da farcen hannunsa a makoshi.Farhama ya sunkuya dodon ya sari iska.Cikin zafin nama Farhama ya doki tsakiyar kan dodon da kotar takobinsa.Nan take sai yaga kan dodon ya lotse har kwakwalwa tayi fantsama ya fado kasa matacce.Koda sarki yaga gawar wannan dodo kuma ya fahimci cewar ruhin dodanni a tsakiyar kansu yake sai ya cika da tsananin murna ya kara zage damtse ya cigaba da ragargazar dodannin suka rinka bajewa kasa mattatu.Shima yarima Farhama yayi koyi dashi cikin kankanin lokaci suka hallakar da kimanin dodanni dari uku.Koda dodannin suka ga anyi musu wannan mummunar barna sai suka ja da baya gaba dayansu a lokaci guda kamar zasu gudu amma sai suka dunkule a waje guda kamar an cura nakiya sannan suka rikide suka zama katon dodo guda daya wanda tsawonsa yakai zira'i dari fadin kirjinsa kuwa yakai kamu arba'in.Koda dodon ya wangame bakinsa ya kwarara uban ihu saida dajin gaba daya yayi amsa kuwwa,bishoyoyi suka kama rangaji suna kakkaryewa,kasa kuwa ta kama girgiza kamar zata rufta komai ya fada cikinta.Koda ganin wannan al'amari sai hankalin sarki da na Yarima Farhama ya dugunzuma ainun domin duk irin tsallen da zasuyi b zasu iya tabo kan dodon ba saboda tsawonsa yayi yawan gaske bare su sari tsakiyar kansa inda ruhinsa yake,haka kuma ba zasu iya kayar da dodon ba ya fadi kasa tunda nauyinsa da girmansa yafi gaban wasa.Bayan dodon ya gama wannan ihu da mugun gurnani sai ya fara taka kafafunsa ya nufi inda sarki da Farhama ke tsaye.Duk taku daya idan yayi sai dajin gaba daya yayi girgiza kamar zai kife saboda karfin takun sawunsa.Sa'adda sarki da Yarima sukaga wannan dodo ya dora kafafunsa kai tsaye sai sukaji kamar su yarda takubbansu su ruga da gudu amma saboda taurin rai da DAKAKKIYAR ZUCIYA irin ta mazajen kwarai sai suka tsaya cak suka cigaba da jiran isowarsa garesu.Yayin da ya rage saura kamar taku goma a tsakaninsu sai sukayi kukan kura suka ruga da gudu suka taro dodon aka ruguntsume da sabon masifaffen yaki.Sarki da Yarima suka wanzu suna masu kaiwa dodon sara da suka cikin zafin nama amma saboda zafin naman dodon yafi nasu dole suka rinka ja da baya baya.Duk sa'adda takubban nasu ya hadu da jikin dodon saidai kaji kamar karfe da karfe ne suke gogayya kuma har tarwatsin wuta ne ke tashi.Koda dodon yaga suna bata musu lokaCi sai ya daka tsalle daya ya dira a gaban yarima.Kafin yarima yayi wani yunkuri tuni dodon yasa hannu ya mangareshi a kafada.Yarima yai tsalle can gefe daya ya fado kasa sumamme,domin tsananin karfin dukan ma yasa ALLON kafadarsa ya goce.Yayin da sarki yaga abinda ya faru ga dansa sai zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone saboda fushi.Kawai saiya takarkare ya kwarara uban ihu irin wanda ke TARWATSA MAZA a filin daga,sannan ya ruga da gudu a karo na biyu ya tari dodon.Wannan karon saiya daka tsalle ya dira akan cinyar dodon sannan ya cigaba da tsalle a sassan jikin dodon tamkar DAN BIRI akan bishiya yana kokarin ya isa kan kafadarsa.Idan mutum yaga yadda sarki ke wannan tsalle tsalle cikin bajinta da jarumta dole ne ya sallama mishi yasan cewa ya cika GWARZON JARUMI.Lokacin da dodon ya fahimci nufin sarki saiya rinka kai masa cafka da mangari da dukkan hannayensa biyu,shi kuwa sai ya cigaba da tsalle tsalle kan dodon yana gocewa harin dodon.Wani lokaci saida kaga sarki ya dira bayan dodon ko gabansa kai kace kadangare ne ke hawa bango.Hakika al'amarin akwai AL'AJABI a cikinsa.Da yake dodon yafi sarki zafin nama sai ya zamana cewa a wasu lokutan dodon na samun damar kartar jikin sarki da kaifin faratansa.Duk sa'adda dodon ya karci jikin sarki sai ya zabga uban ihu sakamakon mugun zafin da yakeji da kuma zogi.Nan da nan ko ina a jikin sarki ya cika da raunika,jini ya rinka zuba,wannan rauni na farko dake bayan sarki kuwa yafi dukkan raunikan girma da rashin kyan gani.Domin shine ma yasa sarki ya fara galabaita har yaji kamar numfashinsa na daukewa da dawowa.A wannan lokaci juwa ta fara daukar sarki.Al'amarin dayai matukar girgiza hankalinsa kenan domin yasan cewa idan har wannan dodo ya sami nasarar hallaka shi shike nan yarima ma bazai rayu ba,shikenan duk burinsa ya rushe.Koda gama aiyana haka sai sarki ya kara fusata ainun ya tabbatar da cewa dole ne yayi yunkuri na karshe don ceton rayuwar yarima,shi kuwa tasa rayuwar tuni ya mika wuya domin yana gani cewa abu ne mayuwaci ya kara sa'a guda nan gaba yana numfashi sakamakon raunikan dake jikinsa masu yawa haka.Koda gama ayyana haka sai sarki ya yunkura iya karfinsa daga kan cinyar dodon ya daka wawan tsalle sama,bisa tsananin mamaki sai yaji ya dira akan kafadar dodon.Yana dira kamar an tabe sifirin an sakeshi haka ya kara daka wani tsallen sai gashi a saman kan dodon.Cikin zafin nama na ban mamaki ya daga takobinsa da hannu biyu ya caka a tsakiyar kansa.Take takobin ta nutsue cikin kan dodon,sai ga jini ya bullutso yai tsiria sama tamkar IDANIYAR RUWA ta bude.Kawai sai dodon ya sulalo kasa a lokacin da sarki ya dafe wuyansa.Dodon ya tumu da kasa tamkar giwaye goma sun fadi ya baje a kasa matacce.Shima sarki saiya bake akan bayan dodon yana KAKARIN MUTUWA.Adaidai wannan lokaci ne yarima Farhama ya farfado daga dogon suman da yayi.Koda yayi arba da gawar dodon kuma yaga mahaifinsa kwance a bayan dodon yana kakarin mutuwa saiya yunkura domin ya mike tsaye yakai masa dauki amma saiya kasa sakamakon mugun zogin da yaji a allon kafadarsa.A sannan ne ya lura cewa kashin kafadarsa ya goce har ya kumbura suntum,Farhama ya kurma ihu cikin tsananin takaici ya fara kukan bakin cikinKoda yaga cewa kuka bazai yi masa maganin komai ba sai ya fara jan jiki da rub da ciki cikin matukar juriya har ya isa inda dodon yake da kyar da sidin goshi ya janye mahaifin nasa daga kan dodon sannan ya bude jakar guzurinsa ya dauko garin magani ya rinka shafawa a gaba daya jikin sarki.Gama hakan keda wuya sai jini ya daina zuba.A sannan ne sarki ya dan dawo daga cikin hayyacinsa ya rinka kiran ruwa ruwa..Koda jin haka sai yarima ya taba salkar ruwansa yaji babu komai a ciki ya taba ta sarki dake rataye a wuyansa yaji itama babu komai a ciki sai hankalinsa ya DUGUNZUMA ainun.Ba shiri ya cigaba da jan ciki yayi ta tafiya a haka har ya riski inda wata korama take ya tsoma bakinsa ya fara sha,sannan ya tsoma salkarsa ya cikata ya juya da rubda cikin yana jan jiki har ya dawo inda sarki yake.Da zuwa sai yaga idanun sarki sun kafe kuma babu inda yake motsi a jikinsa.Koda ganin haka sai yarima ya kurma ihu ya sake fashewa da matsanancin kuka... Gaskiya Sarki Da Yarima Farhama sun bani tausayi wallahi.. DAKAKKIYAR ZUCIYA!!! Littafi Na Biyu (2) Part B KODA GANIN HAKA SAI YARIMA YA KURMA IHU YA SAKE FASHEWA DA MATSANANCIN KUKA.BA zato ba tsammani sai yaga bakin sarki ya motsa alamar yana fadin wani abu.Cikin tsananin murna ya zubawa sarki ruwa a baki ya kwalkwala.Gama shan ruwan keda wuya sai sarki yayi ajiyar numfashi sannan ya dubi Yarima yayi masa dan guntun murmushi.Cikin tsananin farin ciki yarima ya dago sarki ya rungume shi kuma ya sake fashewa da kukan murna bisa ganin cewa sarki bai mutu ba.Bayan yarima ya kwantar da sarki sai ya kama allon kafadarsa da hannayensa biyu ya shiga gyarawa domin ya mayar da kashin daya goce.Kaico komai rashin tausayin mutum idan yaga yadda yaruma ya rinka kwarara ihu a lokacin da yake yiwa kansa wannan gyara na allon kafada dole ne ya tausaya masa.Saboda tsananin zogi da radadin da yakeji saida ya jike sharkaf da gumi tamkar an tsomashi a cikin kogi.Yana gama saita kashin kafadar kuwa ya sulale kasa sumamme.Duk wannan abu dake faruwa sarki na kwance daf dashi yana kallonsa kawai amma ko motsi bazai iya ba sai hawaye ne ke sartu a cikin idanunsa.Yarima Farhama bai farfado ba sai bayan iska mai karfi ta kada.A firgice ya farka ya mike zaune ya dubi sarki yaga yana nan a inda yake kuma a raye.A wannan lokaci ne Farhama yaji raunin jikinsa ya ishe shi da zogi cikin hanzari ya dauko garin magani ya shafawa kansa.Gama hakan keda wuya saiya mike tsaye yaje ya kafa musu tanti yayi shimfida a ciki,sannan yazo ya dauki sarki yakai shi cikin tantin ya kwantar dashi da rubda ciki,saboda wannan lafcecen rauni dake bayansa.Saida Yarima Ya kwana bakwai yana jinyar sarki da kansa a cikin wannan tanti sannan sarki ya sami saukin jikinsa har ya iya budar bakinsa yayi magana Cikin sanyin murya ya dubi Yarima yace yakai dana maza kayi mana shiri mu cigaba da wannan tafiya domin saura kwana biyar mu isa dajin shakkaful zamral.Koda jin haka sai yarima Farhama ya cika da tsananin mamaki ya dubi sarki a cikin alamun karayar zuciya yace haba Abbana aini tuni na hakura da wannan buri nawa na auren gimbiya Siyamat domin yanzu ne na tabbatar da cewa ba zamu iya yakar dodo Lasuruba ba har mu sami damar hallakashi mu yanko kansa.Yanzu fa ka duba ka gani tun kafin mu hadu da dodo Lasuruba mun hadu da wasu dodanni wanda basu da rabin karfin damtsensa da rabin karfin sihirinsa amma kiris ya rage su hallakamu.Tsananin sa'a da nisan kwana yasa muka tsira da rayuwarmu.Abu na biyu ka dubi halin da kake har yanzu fa wannan rauni na bayanka bai gama warkewa ba kuma ko tafiya da kafafuwanka ba zaka iya ba.Dajin haka sai sarki ya turbune fuska yace nifa ba rokonka nake ba umarni na baka.Lallai ka tashi ka shirya mana mu cigaba da tafiyarmu nan da cikar sa'a guda.A iya rayuwar yarima Farhama bai taba jin sarki yayi masa magana da kakkausar murya ba irin haka kuma cikin bacin rai don haka saiya mike sa sauri ya shiga kimtsawa.Kafin cikar sa'a ya gama dukkan shirye shiryen da ya kamata.Nan da nan ya kamo dokin sarki yazo dashi inda sarki yake kwance ta daukeshi ya dora shi akan dokin.Don gudun kada sarki ya fado daga kan dokin yayin da suke tafiya sai daya daddaure shi a jikin dokin da igiya sannan shima ya hau nasa dokin suka bar wannan daji suka nausa gaba.Wani abin mamaki shine duk da cewa sarki baya ruke da linzamin dokinsa amma kamar shine yake sarrafa shi,domin dokin ya jera dana yarima ko tsayawa dokin yarima yayi sai shima ya tsaya kuma baya yarda a sami tazara a tsakaninsu.Haka dai suka cigaba da tafiya ba dare ba rana kuma basa yada zango face sun gaji ko kuma duhu yayi yawa,babu hasken farin wata har tsawon kana uku.Wani abin mamaki shine a tsawon kwana ukun basu sake haduwa da wani mugun abu ba kuma a sannan ne sarki ya samu lafiya sosai har ma yana iyayin komai da kansa,saidai har a sannan raunin gadon bayansa bai daina zogi da radadi ba,ya zame masa tamkar dafin maciji babu alamar zai warke gaba daya.Bisa dalilin haka ne sarki yayi bincike a madubin tsafinsa a sirrance ba tare da yarima ya sani ba ya gano cewa wannan rauni dake gadon bayansa bazai taba warkewa ba har abada kuma shine zai zama SANADIYAR AJALINSA.Da ganin wannan al'amari sai hankalin sarki ya dugunzuma ba don komai ba sai don tsoron kada ajalinsa ya riske shi kafin burin yarima ya cika.Sarki yayi shiru yabar wannan al'amari a cikin zuciyarsa bai sanar da yarima ba.A daren wannan kwana na uku ne suka yada zango a bakin wata korama bayan sun daure dawakansu kuma sun kafa tanti sai suka kunna wuta suka zauna a gaban wutar suna jin dumi sakamakon sanyin dake kadawa.Tsawon yan dakiku suna zaune dayansu baice uffan ba.Daga can sai yarima yaga sarki ya kura masa idanu kawai,nan da nan kwalla ta ciko a cikin idanun nasa.Al'amarin dayai matukar girgiza hankalin Yarima kenan ya dubi sarki cikin matukar damuwa yace yakai abbana ina dalilin kura mini idanu da kayi yanzu kuma har kwalla ta cika maka idanu? Sa'adda sarki yaji wannan tambaya sai ya girgiza kai gami da ajiyar zuciya sannan yace yakai dana kayi sani cewa ba wani abu bane ya sani kallonka da zubar wannan kwalla ba face tsananin tausayinka bisa yadda zaka tsinci rayuwarka a nan gaba koda kuwa bayan ka cika burin rayuwarka ne.Koda jin wannan batu sai yarima ya cika da tsananin mamaki yace haba ya Abbana saboda me zaka ji tausayina alhalin ina cikin daula da farin ciki a wannan lokaci?Ka tuna cewa fa babu abinda zan nema a duniyar nan na rasa tunda muna da tarin dukiya kuma gamu da karfin mulki.Sannan gashi na mallaki abar bege na.To mene ne kuma zai dame ni a rayuwata?Lokacin da sarki yaji haka sai yayi murmushi yace yakai dana kayi sani cewa kai yaro ne abinda na hango maka kai ba zaka iya hango shi ba koda kuwa ka hau kan tsaunin da yafi dukkan tsaunukan duniya tsawo.Ina tausayinka akan abubuwa uku amma yanzu zan iya gaya maka guda daya,ragowar guda biyun kuwa bazan fada maka ba saidai ka gansu da idanunka a lokacin da babu ni.Abu na farko da nake tausayinka akai shine a halin yanzu kana soyayya da macen da baka san matsayinka ba a cikin zuciyarta,kuma sau daya ka taba ganinta a rayuwarka.Koda ka ci wannan gasa ta neman aurenta meye tabbacinka cewar zata kaunace ka kamar yadda kaka kaunarta?Ka sani cewa shi SO GAMON JINI ne kuma abu ne wanda bashi da tabbas.Ba a yiwa so dole kuma ba lallai bane jarumtakar ka ta burge ta ba har taji tana yi maka so na gaskiya.Kai kuwa a yanzu kana sonta da begenta ne saboda tsananin kyawunta kuma tasan don haka kake sonta sabanin yadda ni nayi soyayya da mahaifiyarka,ya zamana cewa mun so juna da gaskiya ba don kyau ba ko matsayi.Lokacin da sarki yazo nan a zancensa sai jikin yarima yayi sanyi,nan take yaji yana nadamar shiga wannan gasa ta neman auren gimbiya Siyamat kuma yaji ya tsani komai a rayuwarsa.Cikin takaici ya dubi sarki a lokacin da hawaye ya subuto masa yace yakai Abbana me yasa tun farko baka shaida min wannan al'amari ba?Na rantse da darajar mahaifiyata idan daka yi mini wannan bayani tun a farko da bazan shiga wannan gasa ba.Koda jin haka sai sarki yayi murmushi yace ai tsananin kaunarka da son ganin farin cikinka ne yasa naki nayi maka wannan bayani tuntuni.Hakika da sannu zaka fahimci mecece rayuwa a cikin wannan duniya.Nima sa'adda nake da kuruciya irin taka na aikata wadannan kura kuran.Yarima ya numfasa yace to yanzu naji abu daya daga cikin abubuwa uku da kake tausayina a kansu na kuma gamsu cewa tabbas ni abin tausayi ne.Ina rokonka da girman iyayenka da suka gabata da ka gaya mini ragowar wadannan abubuwa biyu.Sarki ya bata rai yayi shiru bai kara cewa komai ba daga can kuma saiya saki fuskarsa ya dubi yarima Farhama yace yakai dana kayi sani cewa yanzu muna daf da shiga cikin dajin shakkaful zamral tabbas nan da kwana biyu zamu shiga farkon daji.Ka sani cewa wannan shine karon karshe da zanyi maka kashedi kuma wannan ce damarka ta karshe wacce idan kayi wasa da ita har abada ba zaka daukaka ba a duniya.Ka sani cewa bani da burin da yayi saura a duniya face naga ka lashe wannan gasa ta auren gimbiya Siyamat in yaso ko a sannan na fadi na mutu.Babban bakin cikina shine bazanga abinda zaku haifa ba kaida gimbiya Siyamat.Koda jin haka sai yarima ya dubi sarki cikin firgici yace yakai Abbana waishin wace irin magana kake fada ne haka?Shin kana zaton zaka rasa rayuwarka ne a cikin wannan tafiya da mukeyi ko kuwa kana ganin cewa ba zaka koma gida a raye ba?Sarki ya kada kai yace ba zan mutu ba komai gagarin da zamu shiga kuma zan koma gida a raye.Yarima yace to yaya akayi kasan cewa ba zakaga lokacin da zan haihu ba?Dajin wannan tambaya sai sarki yayi shiru baice komai ba kawai saiya mike tsaye ya nufi cikin tanti yabar yarima zauna yana mai binsa da kallo cikin tsananin mamaki,zuciyarsa cike da wasi wasi da fargaba.Kashe gari da sassafe sarki ya tashi Yarima suka kimtsa suka hau dawakansu suka cigaba da tafiya suka nausa cikin dawa.Tun safe da suka fara tafiyar dayansu baice uffan ba har rana ta fadi a sannan ne suka sake yada zango a gaban wani katon dutse sukayi shimfida suka zauna suka fara cin abinci.Bayan Yarima yayi loma uku saiya yi gyaran murya yace yakai Abbana dazu kace zakayi min kashedi na karshe amma saika manta baka shaida mini ko na menene ba.sarki yace kwarai kuwa na sha'afa dama ba wani abu bane gace naja maka kunne akan KARAYAR ZUCIYA.Na fuskanci cewa tun bayan mun fafata da wadancan dodanni ka sami karayar zuciya a cikin wannan tafiya.Ya zama wajibi a gareka ka cire dukkan tsoro,wasi wasi da fargaba a cikin ranka kafin muyi arba da DODO LASURUBA.Ka sani cewa kwarin gwiwarka shine nawa,idan har zuciyarka ta karaya nima bazan sami kwarin gwiwar taimaka ba.Ina son ka kasance mai DAKAKKIYAR ZUCIYA a koyaushe domin sai zuciyar namiji ta dake sannan zai iyayin abin al'ajabi wanda ya gagari sauran maza.Yakai dana inason ka ajiye abin tarihi ya zamana cewa ka karya alkadarin Dodo Lasuruba domin labarin jarumtakar ka ya basu a ko ina cikin duniya.Koda jin haka sai yarima yaji ya kamu da tsananin tausayin sarki har kwallah ta zubo masa yace yakai Abbana ka sani cewa duk abinda zan zama idan dai babu kai ba zan zama ba.Saboda haka idan ma nayi wannan gagarumi abin al'ajabi bazan yi alfahari da jarumtakata ba saidai da taka,kuma nayi alkawari zansa a sassaka gunkinka dana dodo Lasuruba a tsakiyar gidan sarautarmu nasa a yi bayanin duk abinda ya faru tsakaninmu dashi a rubuce idan har mun sami nasara domin yaya da jikokina masu zuwa su riske wannan babban tarihi.Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube sarki ya rungume Yarima ya kankame shi a kirjinsa yana mai zub da hawaye.Daga can saiya sake shi suka dubi juna yace:- Maybe tomorrow I will not post.Saboda zanje wani waje insha Allah.But not really sure.Sai abinda Allah yayi. DAKAKKIYAR ZUCIYA Littafi Na Biyu (2). Part C DAGA CAN SAIYA SAKE SHI SUKA DUBI JUNA YACE YA KAI DANA YANZU DA ZARAR MUN KAMMALA CIN WANNAN ABINCI INA SON MU CIGABA DA TAFIYARMU SABODA inason mu shiga cikin dajin Shakkaful Zamral da rana tsaka ido na ganin ido.Bana son mu shige shi da daddare.Dajin haka sai yarima yace ni kuwa ina ganin cewa ai zaifi kyau mi shiga cikin daren yadda zamu yi ta sanda har mu isa inda dodo Lasuruba yake ba tare daya sani ba mu shammave shi mi yi masa kwaf daya.(lol kaima dai Yarima Kazo da wasa.Kamar Dodo Lasuruba ayi masa kwaf daya.)Koda jin haka sai sarki ya bushe da dariya sannan yace yakai dana na fuskanci cewa ba kasan waye dodo Lasuruba ba.To ka sani cewa komai sammakon mahaliko Lasuruba a tafe ya kwana.Komai karfin damtsen mahaluki jariri ne shi akan Lasuruba.Komai malamtakar Mahaluki a tsafi almajirin Lasuruba ne.Ina tabbatar maka da cewa dodo Lasuruba ya wuce tunanin mai tunani ko hangen mai hange.Babu wani abu da zaisa mu sami nasarara a kansa face DAKEWAR ZUCIYOYINMU da kuma imaninmu bisa yarda da samun sa'a.Hka dai sarki da Yarima suka cigaba da hira har suka kammala cin abincin sannan suka tashi suka cigaba da tafiya.Sannu sannu su Yarima suka sake kwana suna tafiya.Lokacin da gari yayi haske ne suka fara gyangyadi akan dawakansu saboda bashin baccin da suka dauka.Yarima Farhma na cikin yin wannan gyangyadi sai yaji dokinsa yayi turjiya gami da haniniya.A firgice Farhama ya bude idanunsa suka washe sarai,koda yayi arba da dajin da suke ciki sai yaji zuciyarsa ta buga da karfi sosai.Tunda yazo duniya bai taba jin tsoro ba irin na wannan lokaci ba.Ba komai ne ya tsorata yarima ba face ganin yanayin dajin da suka shigo.Wani irin daji ne wanda ke cike da bishiyoyi,duwatsu,duhuwoyi da ciyayi irin wanda bil'adama bai taba gani ba domin wadannan abubuwa suna da siffofi ne na ban tsoro.Wasu bishiyoyin saika ha suna yiwa mutum gizo suna sauya launi.Su kuwa duwatsun wasu siffofin dodanni gare su wasu manyan macizai da sauran mugayen dabbobin daji.Ashe duk wannan abu ba komai bane face karfin sihirin tsafin dodo Lasuruba.Ba komai ne yasa dokin yarima yayi turjiya da haniniya ba face ganin yadda kasa ke fafakewa da kanta tana yin wawakeken rami wanda zai fada ciki.Duk wannan kadan ne daga sihirin dodo Lasuruba.Da yake sarki ne akan gaba yana jin wannan haniniyar doki na yarima saiya wartsake.Cikin hanzari ya sauko daga kan dokinsa ya zare takobi sannan ya waiga ya dubi Yarima yace kaima sauko kabi inda duk na sauke sawuna kuma ka daure dokinka a nan.Ka sani cewa rabon da wani bil'adama ko aljan ya shigo wannan daji shekara dari kenan.Ko shakka babu dodo Lasuruba ya san da shigowarmu cikin wannan daji.Babu mamaki ma yana kallonmu kawai so yake yaga iya gudun ruwanmu.Koda gama fadin haka sai sarki ya cigaba da tafiya yana waige waige yana kallon gabas da yamma,kudu da arewa cikin matukar nutsuwa,kawai so yake yaga ta inda dodo Lasuruba zai kawo musu hari.Hakika masu iya magana sunyi gaskiya da sukace rashin sani yafi dare duhu,domin kuwa ashe duk wannan abu da sarki da yarima keyi dodo Lasuruba ya ganin tun sa'adda suka shigo dajin don haka saiya kwanta a kasa ya saje da kasar dajin gaba daya tamkar babu shi a wajen.Takan ruwan cikinsa suke tafiya su da dawakansu,wannan kasa data rinka fafewa kuwa har dokin yarima ya tsorata ashe ba kasa bace ruwan cikin dodo Lasuruba ne saboda tattakawar da dawakansu sukayi ne yake motsawa yana lobawa kasa yana tasowa.Haka dai sarki da yarima suka cigaba da tafiya a kasa bisa kafafunsu rike da takubba suna waige waige suka baro dawakansu a can baya.Koda suka iso daidai kan kirjin dodo Lasuruba sai ya gwale manyan idanuwansu guda guda biyu.Cikin razana sarki da yarima suka ja da baya domin gani sukayi kamar TAGWAYEN TAURARI ne suka sauko kasa daga sararin samaniya saboda tsananin hasken idanu.Duk da cewa safiya ce saida dajin gaba ya ya sake haskakewa da azababben haske.Nan take dodo Lasuruba ya wangame katon bakinsa mai kama da kofar gari ya bushe da mahaukaciyar dariya wadda ta haddasa gagarumar guguwa.Yawun bakinsa ya rinka tsiri a sama yana tururi,tururin kuma ya haifar da zubar ruwan sama tamkar lokacin damina ne.Sarki da yarima suka fado daga kan kirjinsa suka jiyo kamar daga kan dogon tsauni suka rikito kasa.Kafin su iso cinyar dodo Lasuruba saida suka shafe dakika dubu da dari biyu.A matukar galabaice suka fado.Da kyar suka yunkura suka mike tsaye a wannan lokaci dodo Lasuruba ya sunkuyo kansa ya dubesu sannan ya bude baki yace yaku wadannan manyan hatsabiban bil'adama kuyi sani cewa nayi matukar mamaki bisa yadda kuka iya shigowa cikin wannan daji alhalin fiye da shekaru dari baya manyan jarumai da matsafa sun kasa shigowa.Bisa wannan dalili ne naki na hallaka ku farat daya.Na sani cewa babu mahalukin da zai saida rayuwarsa ya shigo cikin wannan daji face don ya hallakani ya cire kaina ya tafi dashi.To yanzu na baku sa'a guda kuyi iya kokarinku ku datse kaina kuyi tafiyarku,idan kuwa kuka kasa har sa'a gudan ta cika zan hallaka ku nayi kalaci daku.Koda gama fadin haka sai dodo Lasuruba ya tsuke bakinsa yai shiru kuma ya daina motsi tamkar gunki.Koda ganin haka sai sarki ya kwance wata doguwar igiya daya nannade a kugunsa sannan ya bude jakarsa ya fiddo kugiya ya daura a jikin igiyar sannan ya wulwula igiyar ya cillata sama ta sakalo wuyan dodo Lasuruba.Kawai saiya maida takobinsa cikin kufe sannan ya kama igiyar da hannu biyu ya rinka hawa jikin dodo Lasuruba domin ya isa kan kafadarsa.Koda ganin haka sai shima yarima ya maida tasa takobinsa cikin kufe ya kama igiyar yabi bayan sarki,saida suka jima suna hawa igiyar har suka gaji kuma suka jike sharkaf da zufa sannan suka isa kan kafadar dodo Lasuruba suna ta faman haki.Dirarsu keda wuya akan kafadar dodo Lasuruba sai sarki ta sake zare takobinsa sannan ya karanta wadansu dalasimai na tsafi ya tofa a jikin takobi.Nan take takobin ta kara kauri da kaifi ninkin da sau uku.Cikin hanzari sarki ya karbi takobin yarima itama ya karanta wadannan dalasimai na tsafi ya tofa mata ta koma irin tasa.Gama hakan keda wuya saiya mikawa yarima takobinsa yace muyi ta saran wuyan dodo har sai mun tsinke nasa kai.Nan take kuwa suka kama wannan aiki,cikin zafin nama ba sassauci amma duk sa'adda takubban nasu suka sari wuyan dodo lasuruba sai suji kamar dutsen wuta suke sara.Maimakon wuyan ya rinka darewa sai kaifin takubban nasu ya rinka dakushewa,tarwatsin wuya ya rinka tashi yana haifar da tururin hayaki,shi kuwa hayakin ya cika musu hanci da idanu suka rinka fita daga hayyacinsu.Amma saboda naci basu daina saran wuyan dodo Lasuruba ba har saida takubban nasu suka ratattake kamar an daddaga danyen ice.Bisa dole suka hakura sukayi jifa da ratattakun takubban suka zauna akan kafadar dodo lasuruba suna ta faman haki da tari kamar suyi kumallo.A daidai wannan lokaci ne kan dodo lasuruba ya motsa kuma ya sake wangame katon bakinsa

Chapter 3 of 4