Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 4
ya kwanta. DAKAKKIYAR ZUCIYA Littafi Na Daya (1) Part C. KAGA SAI KA AURAR DA ITA GA DAN SARKIN DA HANKALINKA YA KWANTA.SA'ADDA SARKIN KISRA YAJI WANNAN JAWABI NA BOKANSA SAI YA JINJINA KAI UACE,yakai amintaccen bokana hakika a duniya babu abinda nake so sama da wannan yar uwata tawa Siyamat.Saboda haka kuwa bazan iya aurar da ita ga inda bazan sake ganinta ba.Da dai nayi asarar Siyamat saidai sarkin Kairufa yayi asarar dansa Farhama.To yanzu wace irin gasa ce wacce babu mai iya lashewa kake ganin zan shiryawa manema auren Gimbiya Siyamat? Lokacin da bokan yaji wannan tambaya sai ya bushe da dariya sannan yace ya shugabana abinda nake so dakai shine kasa a yi shela cewar kana neman dukkan masoyan gimbiya Siyamat.Bayan sun taru sai ka shaida musu cewa ba zaka bayar da auren yar uwarka ba face ga jarumin dayaje dajin SHAKKAFUL ZAMRAL ya kashe DODO LASURUBA ya yanko kansa yazo maka dashi.Koda jin wannan batu sai sarkin Kisra ya zazzaro idanu cikin tsananin mamaki yace haba yakai amintaccen bokana ai duk wanda yaji wannan gasa yasan cewa kawai bana son na aurar da yar uwata ne.Kowa ya san cewa fiye da shekaru dari baya babu wani mahaluki daya ratsa ta cikin dajin Shakkaful Zamral ya wuce lafiya ko ya fito a raye.Kai ance ma ko tsuntsu ma ya gifta ta saman dajin saidai akaga ya fado kasa matacce saboda masifar karfin maitar dodo lasuruba.Masu bincike na duniya sun tabbatar da cewa babu wata halitta mai karfin damtse a wannan zamani tamkar dodo Lasuruba.Kuma babu mai karfin Sihirinsa.Kai naji ance ma idan mutum ya mallaki kokon kan dodo Lasuruba zai iya hada wata gagarumar tsatsuba wacce zai iya mallakar komai da kowa na duniyar nan.Ta yaya kake tsammanin cewa akwai wani mahaluki walau mutum ko aljan da zai iya shiga cikin dajin Shakkaful Zamral har yayi arba da dodo Lasuruba?Sa'adda sarkin Kisra yazo nan a zancensa sai bokan nasa ya bushe da dariya yace tabbas abinda ka fada gaskiya ne domin kakana da mahaifina ma duk rayuwarsu ta salwanta ne a cikin dajin Shakkaful Zamral don kawai suyi arba da dodo Lasuruba su kashe shi su mallaki kansa.Matsafa da sadaukai sama da mutum dubu arba'in sun hallaka a cikin dajin saboda duk wanda ya mallaki kokon kan dodo Lasuruba ya gana samun sihirin tsatsuba guda dubu daya wanda babu wanda yake da irinsu a duk fadin duniya.To amma fa samun kan dodo Lasuruba shine babban jidali.Koda jin haka sai farin ciki ya lullube sarkin Misra ya amince da wannan shawara wacce bokansa ya bashi.Ba tare da bata lokaci ba sarkin Kisra tasa akayi shela izuwa sauran kasashen duniya cewar yana gayyatar dukkanin masoyan yar uwarsa gimbiya Siyamat.Nan da nan kuwa birnin Kisra ya karbi bakuncin manya manyan baki na yayan sarakai,attajirai da bokaye masu ji da kansu a duniya ya zamana cewa birnin gaba daya ya cika dasu har an rasa ma inda za'a basu masauki dole aka rinka kai wadansu izuwa sauran biranen kasar da kauyuka.Da ranar taro tazo kuwa saida ya zamana cewa har akan katangu da rufin gidajen mutane suka rinka zama don su saurari bayanin sarkin Kisra.Bayan taro yakai taro sai sarkin Kisra ya hau kan wani mumbari mai tsawon gaske a tsakiyar babban fili na fadarsa sannan yayi gaisuwa ga jama'ar gari da manyan baki kuma ya nuna farin cikinsa bisa amsa gaiyatar da jama'a sukayi.A wannan lokaci garin gaba daya yayi tsit tamkar babu wani mahaluki mai numfashi a cikinsa,ba'a jin sautin komai face muryar sarki saboda kowa ya nutsu kawai so ake aji yanayin gasar neman auren gimbiya Siyamat.Sa'adda sarki ya gama jawabin gaisuwa da yiwa baki barka da zuwa sai kuma yayi gyaran murya yace yaku masoya yar uwata gimbiya Siyamat kuyi sani cewa ban taraku anan ba sai domin na sanar daku gasar dana shirya ta neman auren gimbiya.Daga cikin babu wanda zai baiwa auren yar uwata face wanda ya shiga dajin Shakkaful Zamral ya kashe dodo Lasuruba ya yanko kansa ya kawo mini.Koda jama'a sukaji wannan batu sai wurin gaba daya ya rude da hayaniya.Nan take wasu daga cikin masoya gimbiya Siyamat suka fara kuka domin sun san cewa har abada ba zasu mallaketa ba.Nan fa suka fara sulalewa daya bayan daya suna barin filin fadar har ya zamana cewa babu kowa a gaban sarki face mutum daya jal ba wani bane wannan jarumi face Yarima Farhama dan sarkin Birnin Kairufa.Al'amarin dayai matukar baiwa kowa a wajen mamaki kenan aka rinka yi masa kallon mahaukaci.Lokacin da yarima Farhama ya fuskanci irin kallon da jama'a sukeyi masa saiya daga hannunsa sama akayi shiru sannan yace yaku jama'ar da suka taru a nan kuyi sani cewa a cikin masoyan gimbiya Siyamat nine kadai masoyinta na kwarai tunda na yarda na sallama rayuwata domin na mallake ta.Na rantse da darajar kaunar da nake yiwa iyayena saina shiga dajin Shakkaful Zamral na kashe dodo Lasuruba na kawo kansa a matsayin sadakin gimbiya muddin ina numfashi a doron kasa.Da wannan furuci nakeyi muku bankwana lallai baza'a kara ganina ba sai ranar dana zo da kan dodo Lasuruba.Koda gama wannan jawabi sai yarima Farhama ya juya ya tafi izuwa inda dokinsa yake da zuwa yai tsalle ya dira akan dokin sannan ya zabureshi ya fita da gudu daga cikin birnin Kisra,dakarun da sukayi masa rakiya su arba'in suka rufa masa baya a sukwane.A sannan ne jama'a suka fara watsewa masoyan gimbiya Siyamat suka tafi izuwa kasashensu cikin tsananin bakin ciki suna kuka.Lokacin da Yarima Farhama ya koma birnin Kairufa ya sanar da mahaifinsa abinda ya faru a fadar sarkin kisra sai mahaifin nasa ya kamu da tsananin bakin ciki ya rungume shi yana kuka yace haba yakai dana saboda me zakayi wannan wauta alhalin kasan cewa abu ne wanda bazai taba yiyuwa na?Koda jin wannan batu sai yarima Farhama ya janye jikinsa daga cikin na mahaifinsa suka dubi juna a lokacin da kowannensu ke zubar da hawaye yace yakai abbana kayi sani cewa rayuwata bata da wani amfani muddin ban mallaki gimbiya Siyamat ba.Ina tabbatar maka da cewa idan har ban auri gimbiya Siyamat ba ko shakka babu zan iya kashe kaina.Dajin wannan batu sai hankalin sarki ya sake dugunzuma fiye da da ya sunkui da kansa kasa yayi shiru baice komai ba daga can saiya dago kai ya dubi Farhama yace yakai dana kayi sani cewa koda baka sami nasarar yanko kan dodo Lasuruba ba bazan bari ka kashe kanka ba domin ta kowanne hali sai na tabbatar da cewa ka mallaki gimbiya Siyamat.Na sani cewa kai sadauki ne kuma jarumin gaske amma na ninka ka sau uku a komai.Nima rayuwata bata da wani amfani muddin babu kai a wannan duniya saboda haka lallai tare dani zakayi wannan tafiya izuwa dajin shakkaful zamral domin na taimaka maka.Bani da tabbacin zamu sami nasarar samo abinda zamu tafi nema amma lallai zanyi maka babban tanadi akan yadda zaka mallaki gimbiya Siyamat.Koda ni na rasa rayuwata a cikin dajin shakkaful zamral kuma zan tabbatar da cewa kai ka koma gida a raye.Abinda nake so dakai shine ka saki jikinka ka jirani izuwa kwanaki bakwai domin na gama yi mana shirin wannan gagarumar tafiya.Koda jin wannan jawabi sai sarki ya juya ya shiga cikin dakin halwar tsafinsa.Kwanaki bakwai na cika sarki ya fito daga cikin halwar tsafinsa nan take yasa aka shirya musu guzuri aka tanadi kosassun dawakai guda biyu fari da baki.Cikin gaggawa sarki da yarima Farhma suka gama kimtsawa suka fito daga cikin gidan sarautar suka iso inda dawakansu suke.Da zuwa sai suka iske Shadira mahaifiyar yarima Farhama tsaye a wajen fuskarta sharkaf da haye.Koda ganinta sai duk jikinsu yayi sanyi basu san sa'adda su ma suka fara zubar da hawaye ba suka karasa gareta.Shadira ta ruga da gudu ta rumgume su a tare ta fashe da matsanancin kuka.Jim kadai saita janye jikinta daga cikin nasu ta fuskance su tace yaku masoyana inason ku bani amsar tambayar da zanyi muku yanzu.Yaya kuke tsammanin macen data rasa mijinta da danta zaka kasance?Saboda me zaku tafi ku barni alhalin kunsan cewa inda zaku tafi baku da yakinin dawowa?Ta Yaya zan iya rayuwa a wannan duniya idan babu ku?Sa'adda Shadira tazo nan a zancenta sai tausayinta ya sake turnuke sarki da yarima Farhama suka dada kankameta a jikinsu.Daga can sai sarki ya janye jikinsa daga cikin nata ya dubeta yace yake matata hakika bamu da amsa ga wadannan tambayoyi naki amma ya kamata kiyi mana uzuri musamman idan kika tuno da yadda na aureki bayan nasha bakar wahala a gumurzun gasar neman aurenki har na kusan rasa rayuwata.Tabbas a wannan lokaci in badon ina da DAKAKKIYAR ZUCIYA ba da bazan iya yin wannan gasa ba saboda tsananin wahalarta da masifun dake cikinta.Amma sai gashi tsananin soyayyarki yasa idanuna suna rufe bana ganin wannan masifu kawai mallakarki ce a gabana.Yau gashi abinda ya faru a gareni a wancan lokaci yanzu ya faru ga danki.Shin zaki so danki ya shiga mugun hali ko ya rasa rayuwarsa gaba daya a sakamakon rashin masoyiyarsa?Koda jin wannan tambaya sai Shadira tayi shiru ta kasa cewa komai daga can sai ta dubi sarki tace hakika bazan hana yarima tafiya neman auren masoyiyarsa ba amma ina neman alfarma daya a wajenka yakai mijina.Lallai inason kuyi wannan tafiya tare dani domin idan kuka tafi dajin shakkaful zamral kuka barni a gida fargaba da tunanin halin da kuke ciki kadai ba zasu barni na zauna lafiya ba kuma bazan taba samun sukuni ba face naga kun dawo lafiya cikin koshin hankali.Sarki ya kama kafadun Shadira yace yake matata kiyi sani cewa a matsayinki na matar jarumin sarki mai DAKAKKIYAR ZUCIYA bai kamata ki zamo mai fargaba ba.Yana da kyau kema zuciyarki ta kekashe ga barin tsoron komai kuma ki kasance mai fatan cika buri bisa duk abinda kika sa a gabanki.Nayi imani cewa ina da sa'a domin a rayuwata ban taba kokarin mallakar wani abu ya gagare ni ba saboda haka ina da yakinin cewa zamu sami nasara a cikin wannan tafiya da zamuyi nida yarima.Ki sani cewa duk sa'adda muka tuno dake sai munfi kara samun kwarin gwiwa da ZAGE DAMTSE akan abinda ke gabanmu don tabbatar da samun nasararmu domin mu dawo gida a raye mu sake ganinki amma idan muka tafi tare dake ko yaya wani abu ya taba lafiyarki zamu sami karayar zuciya ne mu kasa tabuka komai.Koda gama fadin haka sai sarki ya sumbaci goshin Shadira sannan ya kama dokinsa yahau ya sakar masa linzami yayi gaba.A wannan lokaci ne Shadira ta sake rungume yarima Farhama ta kankame shi a kirjinta tana kuka kamar ba zata iya sakinsa ba.Al'amarin daya karya zuciyar Farhama kenan shima ya cigaba da kukan yaji kamar ya hakura da wannan tafiya.Da kyar dai ya danne zuciyarsa ya janye jikinsa daga cikin nata shima ya kama dokinsa ya hau ya tafi yana waigenta yana zubda hawaye har ya riski sarki suka jera sukayi ta tafiya har suka kule Shadira na tsaye tana kallonsu tana zubar da hawaye sannan ta durkusa kasa bisa gwiwoyinta ta debi sawun dawakansu ta shinshina a lokacin da hawaye ke sartu bisa kumatunta.Sarki da Yarima Farhama suka nausa cikin daji sukayi ta tafiya ba sassauci su kutsa nan su fita can har rana ta fadi magriba ta doso basu hadu da wani mugun abu ba.Sau daya ne ma sukaga giftawar wata kuta.Koda kurar tayi musu kyakkyawan kallo guda daya sai ta kau dakai tabi wata hanyar daban ta nausa can cikin dawa.Yayin da sarki yaga magriba ta doso kai kuma gashi dawakansu sun fara gajiya suna tafiyar sassarfa saiya shawarci yarima dasu tsaya su yada zango.. Note: wannan littafin ba "Bakin Yamutsi" bane but an danyi extract dinsa a cikin littafin kamar yadda akayi extract din "Kasuwar Rayuka" a cikin Wasikar Jini. DAKAKKIYAR ZUCIYA!!! Littafi Na Daya (1) Part D. SAIYA SHAWARCI YARIMA DASU TSAYA SU YADA ZANGO.BA TARE DA GARDAMAR KOMAI BA KUWA YARIMA YA KARBI WANNAN SHAWARA SUKA KARASA KARKASHIN WATA BABBAR BISHIYA SUKA SAUKA SUKA DAURE DAWAKANSU SANNAN SUKA JE CIKIN WATA Fadama dake kusa da bishiyar suka debo ruwa suka shayar da dawakansu sannan kuma suka kafa tanti suka shiga ciki suka zauna.Nan dai suka bude jaka suka dauko abincin guzuri suka kama ci suna cikin wannan hali tsawon dakiku dayansu baice kala ba daga can sai yarima Farhama ya dubi sarki yace yakai Abbana tun ina yaro nake jin labarin dajin Shakkaful Zamral wai shin a ina wannan daji yake ne?kuma daga nan zuwa can tafiyar kwana nawa ce? Sa'adda sarki yaji wannan tambaya sai yayi murmushi yace yakai yarima ai daga nan ma inda muke zuwa dajin shakkaful zamral tafiya ce ta kwana arba'in da daya.Amma zan yi kokari na gajarce mana nisan tafiyar da karfin sihirina izuwa kwana ashirin da daya.Koda jin haka sai yarima Farhama ya dubi sarki cikin mamaki yace to waishin me zai hana ka kirawo wani aljani daga cikin hadimanka ya dauke mu ya kaimu can a cikin kankanin lokaci tunda ka taba gaya mini cewa kana da wani hadimin aljani wanda yake iya shafe tafiyar kwana arba'in a cikin sa'a hudu.Sarki ya sakeyin murmushi a karo na biyu yace ai a halin yanzu duk duniya babu wani aljani daya isa yama doshi hanyar data nufi dajin shakkaful zamral komai karfinsa da karfin sihirinsa.Ida kuwa yayi gangacin hakan take zai narke ya babbake saboda karfin sihirin tsaron dake dajin.Bisa wannan dalili ne ya zama wajibi a garemu muyi wannan tafiya akan doki.Ka sani cewa dajin shakkaful zamral yayi iyaka da birane biyu wato birnin Askan da birnin Nurhil kuma tsakaninsa da kowane birni akwai tazara ta manyan dazuzzuka guda uku uku.Yanzu wannan hanya da muka biyo zamu bi ta cikin birnin Askan ne sannan mu ratsa wadannan dazuzzuka guda uku mu riski dajin shakkaful zamral.Ina san ran cewa zamu isa birnin Askan nan da kwana goma sha biyar inda nake zaton zamu fuskanci matsala shine a cikin birnin Askan domin na sami labari cewa basa bari bako ya shiga cikin garinsu kuma sarkinsu gawurtaccen jarumi ne sadaukin gaske.A tarihin rayuwarda ma ba'a taba cinsa da yaki ba.Saboda haka ya zama dole a gare mu mu shiga birnin Askan ta kowane hali koda yaki zai barke a tsakaninmu dasu domin babu wata hanya da zamu iya bi mu isa dajin shakkaful zamral face tanan sai kuma ta cikin birni Nurhil.Shi kuwa birnin Nurhil gaba daya ba awannan nahiya tamu yake ba yana can nahiyar birnin Hindu ne idan dai munason mu shiga ta cikinsa sai munyi tafiyar kwana dari da hudu kuma masifun dake cikin dazuzzukan waccan nahiyar sun ninka wadanda ke wannan nahiya tamu sai goma.Sa'adda sarki yazo nan a zancnesa sai hankalin yarima Farhama ya dugunzuma ainun ya tabbatar da cewa aikin dake gabansu ya wuce gaban misali.Kuma abu ne mayuwaci ma su sami nasara bisa abinda ya baro su daga gida.Cikin sanyi jiki yarima Farhama ya dauki battar ruwa ya kwankwada sannan ya kishingida domin ya huce gajiyar tafiya fuskarsa cike da alamun damuwa.Koda ganin haka sai sarki ya matso kuwa dashi ya dafa kafadarsa yace yakai dana inason ka sani cewa FADUWAR GABA ASARAR NAMIJI ce,gwarzon namiji baisan tsoro ba ko fargaba ba kuma shine mai DAKAKKIYAR ZUCIYA ta tunkarar kowane irin bala'i.Abinda nake so dakai shine kada ka kuskura ka cire rai ga tsammanin samin rabo daga cikin zuciyarka.Lallai ko yaushe ka kasance namiji mai DAKAKKIYAR ZUCIYA da kunar bakin wake domin har abada matsoraci bashi zama gwani.Gama fadin hakan keda wuya sai shima sarki ya sami wuri ya kwanata.Kwanciyarsa keda wuya saiya fara gyangyadi don haka sai ya dubi yarima Farhama yace yakai dana zanyi bacci izuwa wani dan lokaci saboda haka saika zauna kayi tsaron lafiyarmu idan na farka sai kai ma ka kwanta ka matse.Nan take sarki ya cigaba da bacci abinsa.Shi kuwa yarima Saiya mike tsaye ya fito wajen tantin domin ya dan wasa kafafunsa.Fitowarsa keda wuya saiya hango wata tsaleliyar budurwa a can nesa kadan daga inda yake.Tana sanye da wata farar riga sol mai shara shara wacce ke bayyana surar jikinta gaba daya.Duk da cewa duhu ya fara a wannan lokaci saida yarima yayi arba da kyakkyawar fuskar buduwar.Ai kuwa yana yin arba da ita saiya cika da tsananin mamaki domin ba wata bace face wacce yake bege DARE DA RANA wato gimbiya Siyamat.Kawai sai yaga tayi masa murmushi kuma ta yafitoshi da hannu tana mai kiransa a lokacin data juya baya ta nausa cikin daji.Ba tare da yarima Farhama ya yanke shawara da zuciyarsa ba kawai saiya falfala da gudu yabi hanyar da gimbiya Siyamat ta bi.Duk da cewa yana falfala gudun tsiya amma sai ya kasa riskarta kuma gashi yana hangota a gabansa tana dada shiga cikin wani bakin surkuki.Hakika SO makaho ne saboda tsananin son da yarima Farhama ke yiwa gimbiya Siyamat ko kadan baiyi mamakin ganinta ba a cikin wannan daji bare yayi tunanin ko ba itace ba.Haka ya cigaba da binta da gudu har ta isa gaban wani katon tsauni wanda aka gina matattakalar bene a kansa.Siyamat ta cigaba da hawa kan tsaunin tana taka matattakar shima gogan naka saiya hau kan matattakalr ya cigaba da binta har ya kure matattakalar ya iso kan saman tsaunin kawai sai yaga wadansu kyawawan kuyangi a gaban wani kerarren gida wanda aka gina shi da zallan dutsen murjani.Gaba dayan kuyangin na rike da kwando kuma kowane kwando a cike yake da wani jan fure mai kamshi.Koda gimbiya Siyamat tazo zata gifta ta tsakiyar kuyangin sai suka rinka watsa mata wannan fure mai kamshi.Ba tare da shakkar komai ba shima Yarima ya ratsa ta tsakiyar kuyangin.Bisa mamaki sai yaga shima kuyangin sun kama watsa masa wannan fure mai kamshi.A wannan lokaci ne gimbiya Siyamat ta tsaya cak a inda take har yarima Farhama ya iso daf da ita tana yi masa wani irin tattausan murmushi mai rikita zuciyar 'da namiji.Da isowarsa daf da ita sai ta kama hannunsa taja shi suka kunna kai izuwa cikin wannan gida.Da shigarsu cikin gidan sai kan Yarima Farhama ya juya ya zama cikakken dan kauye ya kama kalle kalee domin tun da yazo duniya bai taba ganin gida mai kayan kawa ba kamar wannan.Koda ya kwatanta fadar mahaifinsa da wannan gida sai yaga bambancin a bayyane yake kamar birni da kauye ne.Komai na cikin gidan anyi shine da zallan zinare sai sheki da walwali suke.Hadimai kuwa gasu nan ba adadi sai kai kawo suke,Siyamat ta cigaba da jan Yarima Farhama har saida suka ratsa ta cikin kofofi goma sha biyu sannan suka iso cikin wata katuwar fada wadda ta kawatu ainun fiye da ko'ina a gidan.Da shigarsu cikin wannan fada sukayi arba da wani santalelen kyakkyawan saurayi zaune akan karagar mulki.Nan take Siyamat ta kufce hannunta daga cikin na Yarima ta ruga da gudu izuwa ga wannan saurayi.Adaidai wannan lokaci ne wata irin iska mai karfi ta cika fadar ta banko kofar shigowa da tagogin fadar duka suka bame.Ba zato ba tsammani sai yarima Yaga wannan saurayi da gimbiya Siyamat sun rikide izuwa siffar wadansu munanan aljanu masu matukar kwarjini da ban tsoro kuma suka bushe da dariyar mugunta.A sannan ne Yarima Farhama ya dawo cikin hayyacinsa ya gane cewa tarko ne wadannan aljanu suka dana masa ya fada suka ribace shi da siffar masoyiyarsa suka janyo shi izuwa cikin wannan gida.Al'amarin daya matukar dugunzuma hankalinsa kenan,saboda sanin cewa bashi da wani karfin sihiri wanda zai iya tunkarar aljanu yayi fada dasu.Kawai sai yaji zuciyarsa tana maiyi masa tambaya waishin menene dalilin da yasa sarki bai bani sihirin tsafinsa ba domin na kare kaina bisa irin wannan rana?Yanzu gashi ya kusa da ni waye zai kare ni daga sharrin wadannan mugayen aljanu?Gama ayyana hakan keda wuya sai daya daga cikin aljanun ya dakawa yarima tsawa yace yakai wannan dan sarki kayi sani cewa yau shekara shida kenan muna jiran zuwan wannan rana da zamu sami damar kamaka domin mu dauki fansar abinda mahaifinka yayi mana.Lallai yau sai munyi maka mugun kisan gilla irin wanda ba'a taba yiwa wani bil'adama ba domin mu kawar da bakin cikin zuciyarmu.Ka sani cewa a dalilin mahaifinka mun rasa dukiyarmu,iyayenmu da duk danginmu.Sannan mun rasa mulkinmu a kasarmu saboa kawai mun bata masa wani aiki daya umarcemu dayi,wanda muka bata shekaru uku muna wahala akan aikin.Yanzu mu bamuga tsuntsu ba kuma bamu ga tarko ba don haka bamu da sauran buri wanda yafi mu cusawa mahaifinka bakin cikin da har ya mutu bazai daina jin radadinsa ba.Ka sani cewa tun kana jariri muke kai maka hari domin muga bayanka mu hallaka ka saida muka kai maka hari sau saba'in da bakwai babu nasara.Saboda mahaifinka ya tsareka da sihirin tsafi kuma daga baya ne muka gano cewa tsafin ba a cikin jikinka yake ba a cikin harabar gidan sarautar yake.A kullum bamu da burin da yafi muga ranar da za'a fito da kai dagta cikin gidan sarauta ya zamana cewa mahaifinka baya kusa da kai amma hakan bata samu ba sai yau.Yanzu take zamu gididdibaka muyi gutsun gutsun da sassan jikinka,kanka ne kadai ba zamu daddatsa ba domin mahaifinka ya shaidaka ya kamu da irin mugun bakin cikin da muma muka dandana.Gama fadin hakan keda wuya sai Aljanun biyu suka bude fukafukansu sukayi sama suka yiyo kan Yarima Farhama da nufin su yagalgala shi da kaifin faratan hannayensu da kafafunsu.Ba tare da fargabr komai ba Farhama ya yunkura cikin zafin nama ya zare takobinsa ya tare su aka fara azababben yaki.Al'amarin dayai matukar baiwa Aljanun biyu mamaki kenan domin a zatonsu cikin farat daya zasu hallakashi sai gashi sun kasa koda lakutar jikinsa,shi kuma yana ta saran jikinsu amma kamar dutse yake sara.Duk sa'adda takobin Farhama ta hadu da jikin aljanun saidai kaji kara kal.Kamar haduwar karfe da karfe sannan kuma tartsatsin wuta ya rinka fantsama.Saida aka shafe sa'a biyu cif ana wannan gumurzu tsakanin yarima Farhama da wadannan aljanu biyu har ya zamana cewa Yarima Farhama ya fara gajiya.Babu abinda ya batawa aljanun rai face ganin yadda idan suma suka sari jikinsa da faratansu sai suji kamar dutse suka sara saidai karfin dukan nasu yana kaishi kas,amma kafin su turmushe shi sai kaga yayi wuf ya mike tsaye an cigaba da fafatawa.Koda aljanun suka fahimci Farhama ya fara gajiya sai suka cika da murna domin sun san cewa da zarar ya galabaita ainun zasu iya turmushe shi da karfin tsiya su murde masa wuya ya mutu. SHIN WADANNAN ALJANU ZASU SAMI NASARAR HALLAKA YARIMA FARHAMA? IDAN SARKIN YAKI HUZAIKA YAJE YA ISAR DA SAKON SARKI KUZZARU GA BOKA ZURAITA WANE BAYANI ZAIYI MASA? ME ZAI FARU TSAKANIN SARKI KUZZARY DA ATTAJIRI UBAIRU WANDA YAZO DA MUGAYEN BAKAKEN ALJANU DOMIN A BAJE BIRNIN KISRA? SHIN YARIMA FARHAMA DA MAHAIFINSA SUNA SAMUN NASARAR KASHE DODO LASURUBA HAR SU YANKO KANSA SU KAWOWA SARKIN KISRA A MATSAYIN SADAKIN YAR UWARSA GIMBIYA SIYAMAT? Mu Hadu A DAKAKKIYAR ZUCIYA Littafi Na Biyu Don Jin Cigaban Wannan Kasaitaccen Labari. DAKAKKIYAR ZUCIYA!!! Littafi Na Biyu (2) Part A. LOKACIN DA AKA CIGABA DA BAKIN GUMURZU TSAKANIN YARIMA FARHAMA DA WADANNAN MUGAYEN ALJANU GUDA BIYU,har izuwa tsawon dan lokaci sai yarima Farhama ya gaji ainun bai san sa'adda takobin hannunsa ta subuce masa ba ta fadi kasa.Nan take daya daga cikin aljanun ya shammace shi ya buga masa wawan dundu a baya nan take Farhama ya kife a kasa da rub da ciki yana aman jini a lokacin da yaji kamar an kakkarya kasusuwan bayansa saboda karfin dundun da akayi masa don haka ko kyakkyawan motsi baiyi ba tamkar ya zama gawa.Koda ganin wannan gagarumar nasara sai aljanun suka cika da tsananin farin ciki.A lokaci guda duk su biyun suka yunkura izuwa kan yarima Farhama da nufin su tsintsinka shi filla filla.Kwatsam ba zato ba tsammani sai sukaji an sarewa kowannensu hannu dai dai.Take hannayen nasu suka gutsure sukayi tsalle gefe daya a lokacin da jini ya kama feshi daga cikin dungulmin hannayen nasu suka kurma uban ihu a lokaci guda.Koda sukayi arba da wanda yayi musu wannan muguwar barna sai suka rikide izuwa guguwa take gaba dayan tagogin fadar suka bubbude wannan guguwa ta fice fit ta cikin taga guda.Wani irin gagarumin ihu na biye da guguwar suka bace bat gaba daya.Saiga guntulallun hannayen aljanun biyu nata daka tsalle a gefe daya tamkar ruhin aljanun a jikinsu yake.Ba wani bane ya sare hannayen wadannan aljanu ba face mahaifin yarima Farhama.A gigice mahaifin nasa ya ruga izuwa inda yarima Farhama ke kwance yana amon jini ya sureshi ya aza shi a kafadarsa sannan ya ruga da gudu ya nufi kofar fita daga fadar.Yana isa gaban kofar ya sa kafarsa ya banke kofar,duk da cewar kofar fadar katuwar gaske ce kuma mai kaurin tsiya ta bakin karfe saida ta karye ta fadi kasa rikica.Sarki ya fice ta cikin kofar a guke dauke da yarima a kafadarsa.Kafin kiftawar ido tuni sarki ya gama fice daga cikin gidan gaba daya har ya iso can inda suka kafa tantinsu.Cikin hanzari sarki ya shigar da yarima Farhama cikin tantin ya kwantar dashi sannan ya bude jakar guzurinsa ya dauko wani garin magani ya jika da ruwa ya dura masa a baki ya hadiye da kyar.Faruwar hakan keda wuya sai yarima Farhama ya farfado daga dogon suman da yayi.Koda ya bude idanunsa yayi arba da sarki a gabansa sai ya kawo gwauron numfashi ya ajiye.A wannan lokaci ne sarki ya dubeshi a fusace yace yakai yarima saboda me kabar harabar wannan inda muka kafa tantinmu har ka fada cikin tarkon wadannan tsofaffun makiya nawa?Koda jin wannan tambaya sai yarima ya sake yin ajiyar zuciya yayi shiru baice komai ba har saida ya suri battar ruwa ya kwankwada sannan ya dubi sarki yace ka gafarceni yakai Abbana ka sani cewa tabbas wadannan makiya naka yaudarata sukayi,dayansu yazo mini a cikin siffar masoyiyata gimbiya Siyamat yajani har izuwa cikin wannan gida nasu dake kan tsauni.Koda jin haka sai sarki ya gyada kai yace hakika kana da tsawon kwana a duniya domin in badan na farka daga baccina ba naga babu kai nayi binciken inda kake a cikin madubi tsafina da tuni wadannan abokan gaba nawa sun gama hallaka ka.Ko dan gaba kada ka sake barin inda duk muka yada zango ba da umarni na ba.Sa'arka daya na baka sihirin tsafina guda daya a cikin abincin da muka ci dazu ya ratsa dukkan jini jikinka.In badon hakan ba da tuni aljanun sun hallaka ka farat daya tun sa'adda kuka fara wannan gumurzu.Koda jin haka sai yarima Farhama ya kawo gwauron numfashi ya ajiye sannan yayi murmushin murna yace ina godiya a gareka yakai ABBANA bisa ceton rayuwata da kayi.Dajin haka sai sarki ya rungume yarima Farhama cikin farin ciki yace ai aikina ne na tsare lafiyarka da rayuwarka don ganin ka cika burin rayuwarka.A cikin wannan tanti sarki da yarima Farhama suka kwana.washe gari kuwa da sassafe suka mike sukayi shiri suka cigaba da tafiya bayan sunyi lakaci.Tsawon rabin sa'a suna tafe dayansu baice kala ba kuma basu hadu da wani mugun abu ba.Daga can sai Yarima Farhama yayi gyaran murya ya dubi sarki yace yakai Abbana waishin menene ya haddasa gaba tsakaninka da wadannan aljanu guda biyu wadanda sukayi yunkurin hallaka ni domin su dauki fansar abinda kayi musu? Sa'adda sarki yaji wannan tambaya sai yayi ajiyar zuciya yace yakai dana kayi sani cewa wannan labari ne mai tsawon gaske ka tambayeni.Domin daga nan har izuwa karshen wannan tafiya da zamuyi bazan iya gama labarta maka shi ba.Kayi hakuri nan gaba idan muna raye zan baka labarin komai bayan burinka ya gama cika.Gama fadin hakan keda wuya sai sarki ya tsuke bakinsa yayi shiru bai kara cewa komai ba suka cigaba da keta dazuzzuka.Sannu sannu bata hana zuwa saidai a dade ba'a je ba.Haka dai su yarima Farhama suka cigaba da ratsa dazuzzuka iri iri har tsawon kwana tara,duk sa'adda suka gaji ko kuma idan dare ya riske su sai su tsaya su yada zango in yaso da safe sai su cigaba da tafiya.Tsawon wadannan kwanaki tara basu sake haduwa da wani mugun abu ba.Da yammacin kwana na tara ne suka shigo cikin wani irin mugun daji mai sarkakiua da duhuwoyi.Hakika dajin yana da matukat kwarjini da ban tsoro.Da shigowarsu cikin farkon dajin sai sarki ya rage saurin tafiyarsa kuma ya zaro takobinsa daga cikin kufenta yana duban gasab da yamma kudu da arewa.Koda ganin haka sai shima yarima Farhama yayi koyi da abinda sarki yayi.Nan take suka fara jin wani irin gurnani ya cika dajin gaba daya kuma suka rasa ta inda gurnanin yake fitowa,sannan suka rinka jin hucin wata irin iska tana gifgiftasu tana kai kawo kuma tana yi musu KAWANYA.Koda ganin haka sai sarki ya dubi yarima yace dashi yakai dana ka nutsu duk abinda kaga nayi kayi koyi dani.Koda gama Fadin haka sai sarki ya duro kasa daga kan dokinsa ya tsuguna bisa guiwoyinsa kuma ya cake takobinsa a cikin kasa.Cikin hanzari yarima Farhama yayi duk wannan abu da

Chapter 2 of 4