Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 4
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels ★DAKAKKIYAR ZUCIYA★!!! Abdul'aziz sani mad akin giñi Littafi Na Daya (1) Part A. A WANI ZAMANI CAN BAYA MAI TSAWO DAYA SHUDE,A BIRNIN KISRA ANYI WANI SAURAYI MAI SUNA SHUBAIRU IBINI HAURAS.Shubairu ya kasance dan kimanin shekaru talatin da uku kuma Allah yayi masa baiwa da yawa.Abu na farko ya kasance kyakkyawa na gaban kwatance domin a gaba daya birnin Kisra babu wani 'da namiji mai irin kyawunsa.Abu na biyu shine yana da tarin ilmi na addinai kala kala har guda tamanin da uku.Abu na uku yana da wata irin baiwa wacce mutane suka kasa gane asalinta domin tana kama da tsafi wasu kuma su kirata da suna TSATSUBA.Ita dai wannan baiwa yanayinta shine ko da Shubairu baisan mutum ba bai taba ma ganinsa ba da zarar ya kalli fuskarsa zai iya ganin duk abinda ya faru ga mutum a rayuwarsa tun daga kuruciyarsa kawo izuwa girmansa har abinda ya aikata a wannan rana.Idan kuwa ya dafa kan mutum da hannunsa na hagu zai iya ganin irin daukakar da mutum zai samu ko kaskanta nan gaba a rayuwarsa.Wani abin mamaki shine duk da yana da wannan baiwa bazai iya gayawa mutum abinda zaiyi ya kare kansa ba daga abubuwan sharrin da zasu same shi.Shidai Shubairu bai kasance dan kowa ba a cikin birnin Kisra,ma'ana shi ba dan sarakai bane ko attajirai ya kasance maraya don tun yana yaro dan shekara shida iyayensa suka mutu a lokacin da suka fita bayan gari kiwon dabbobinsu yan fashi suka kawo musu samame.Bayan yan fashin sun kashe iyayeyn Shubairu sai suka fara kokarin sace dabbobin nasu su gudu dasu.Bisa sa'a saiga dakarun sarki Kuzzaru sun fito kewaye.Koda sukayi arba da yan fashin sai suka fatattake su suka gudu.Dama a wannan lokaci iyayen Shubairu sun fito kiwo ne tare da Shubairu kuma wani iko na Allah yan fashi basu kashe shi ba.Shidai Shubairu tunda yaga an kashe iyayensa saiya fado kasa daga kan rakumi ya rinka tsala kuka.Bayan dakarun sarki Kuzzaru sun kori wadannan yan fashi sai sukaga kyakkyawan yaro na gaban kwatance zaune a kas bisa ciyawa yana ta kuka.Shugaban dakarun wanda ake kira da Huzaika ya tunkaro Shubairu yana mai kura masa idanu cikin alamun tausayawa.Koda Shubairu yaga su Huzaika sun durfafo shi saiya tsorata ainun ya yunkura zai ruga da gudu.Cikin hanzari Huzaika yace dashi tsaya yakai wannan yaro kada ka guje mu domin mu ba masu cutarwa bane a gareka mun kasance dakarun sarki Kuzzaru mai mulkin wannan birni na kisra.Koda jin wannan batu sai Shubairu ya koma ya zauna ya cigaba da yin kukansa.Da isowarsu Huzaika daf da gawar iyayen Shubairu sai suka cika da mamaki domin dukkansu sun gane Mahaifin Shubairu wanda ke kwance a mace.Domin shine yake kai madarar shanu a gidan sarki kullum da sassafe ana biyansa bayan kowane kwana talatin.Cikin matukar mamaki Huzaika ya sake duban Shubairu yace yakai wannan yaro ma'abocin kyawun fuska mene ne dangantakarka da wadannan mamata? Cikin shesshekar kuka Shubairu yace IYAYE NANE.Koda jin haka sai Huzaika yaji ya kamu da tsananin tausayin Shubairu don haka saiya durkusa a gabansa ya share masa hawaye sannan ya rike kafadunsa yace mene ne sunanka?Shubairu ya fada masa sunansa.Huzaika yace daina kuka yakai Shubairu ka sani cewa yanzu zan dauke ka tare da wannan dukiya ta iyayenka na kai ku wajen sarki.Tabbas sarkina mutum ne mai tausayi dajin kai don haka nasan cewa bazai bari ka wulakanta ba.Koda gama fadin haka sai Huzaika ya mike tsaye ya dauki Shubairu ya dora shi akan dokinsa shima ya hau kan dokin ya zauna sannan ya umarci dakarunsa dasu kada wadannan dabbobi izuwa gidan sarki.Dabbobin dai adadinsu bai wuce guda ashirin ba.Guda goma sha biyu shanu ne kosassu ragowar guda takwas kuwa rakuma ne manya lafiyayyu.Nan take dakarun suka cika aikinsu aka nufi cikin gari.Fadar a cike take makil da jama'a ana tafiyar da harkokin mulki kamar yadda aka saba.Sarki Kuzzaru na zaune bisa karagar mulki fadawa sun kewaye shi a gefen damansa kuwa matarsa ce gimbiya Lamrisa a zauna ta caba ado na gaban kwatance kuma gashi ta kasance mai tsananin kyawu tamkar ita tayi kanta.A wannan lokaci gaba dayan mutanen dake cikin fadar satar kallonta sukeyi kuma kullum haka abin ke faruwa domin kowa ji yake kamar ya sureta ya gudu da ita.A wannan lokaci sarki da fadawansa na cikin raha sai hira suke da dariya cikin nishadi.Ita kuwa gimbiya Lamrisa fuskarta a murtuke take.Fiye da shekaru goma sha daya baya babu wani mahaluki daya taba ganin murmushin gimbiya Lamrisa.Shi kansa sarki Kuzzaru rabo da yaga murmushin Lamrisa da dariyarta tun shekarar farko da sukayi aure saadda take amarya.Bayan cikar shekara guda ne da taga bata sami haihuwa ba ta matsawa sarki Kuzzaru akan shiga neman magani da bincike wajen bokaye.Abinda binciken ya tabbatar shine matsalar rashin haihuwa daga gareta ne kuma har abada ba zata iya haihuwa ba.A kalla an ziyarci bokaye dari ba daya duk bayani iri daya sukeyi.Tun daga wannan lokaci ne gimbiya Lamrisa ta kamu da tsananin bakin ciki ya zamana cewa kullim bata da aiki DARE DA RANA face kuka.Saida ta kwana arba'in a cikin wannan hali sannan sarki ya samo kanta da kyar da taimakon bokansa har ta saki jiki ta cigaba da rayuwa amma fa tun daga wannan lokaci ne aka daina ganin murmushinta da dariyarta.Babu irin kokarin da sarki Kuzzaru baiyi ba akan yaga Lamrisa ta manta da batun matsalar rashin haihuwarta amma abu ya gagara don haka saiya hakura ya zuba mata idanu kawai.Ana cikin wannan zaman fada ne aka ga sarkin yaki Huzaika ya shigo dauke da kyakkyawan yaro dan shekaru shida a hannu.Nanfa kowa da kowa ya kurawa yaron idanu cikin tsananin mamaki,ba wani abu bane ya haddasa hakan ba face ganin yadda kamannin wannan bakon kyakkyawan yaro sukà zama iri daya dana gimbiya Lamrisa tamkar itace ta haifeshi alhalin kowa yasan cewa bata taba haihuwa ba.Sa'adda Gimbiya Lamrisa tayi arba da yaro Shuhairu sai ta cika da tsananin mamaki kuma nan take taji ta kamu da tsananin son sa a cikin zuciyarta.Lamrisa dai bata san sa'adda ta mike tsaye ba ta taryi Huzaika ta mike hannu zata karbi Shubairu tana murmushi.Al'ama rin dayai matukar baiwa kowa mamaki kenan a cikin fadar aka bude baki ana kallonta.Kawai sai akaji sarki ya daka mata tsawa.Cikin razana ta tsaya cak ta kame kamar gunki.Sarki Kuzzaru ya mike tsaye ya tako kafafunsa yazo har gaban sarkin yaki Huzaika fuskarsa a murtuke ba sassauci.Gaba daya mutanen fadar saida suka tsorata domin kowa yasan cewa idan ran sarki ya baci kowa sai yaji ba dadi.Duk da cewa ya kasance mutum ne mai saukin kai,hakuri,tausayi da jin kai.Kai wasu ma daga cikin jama'ar dake fadar tuni jikinsu ya kama karkarwa saboda tsoron kada sarki ya fusata ya doka dirkar gini da hannunsa fadar ta rushe gaba daya kowa ya hallaka tunda ya kasance gagarumin Sadauki mai karfin Allah ya isa.Sarki Kuzzaru ya dubi sarkin yaki Huzaika a fusace yace yakai dirkar birnin Kisra a ina ka samo wannan kyakkyawan yaro kuma mene ne dalilin da yasa ka shigo dashi nan fadata?Koda jin wannan tambaya sai sarkin yaki Huzaika ya risina cikin biyayya yayi gyaran murya sannan yace ya shugabana dazu bayan na fita zagaye da safe tare da dakaru don tabbatar da tsaron gari kamar yadda ka umarcemu dayi kullum sai kawai muka hango wadansu yan fashi suna kokarin kada wadansu dabbobi izuwa cikin daji.Nan take muka sukwani dawakanmu izuwa kansu ai kuwa suna hango mu sai suka tarwatse suka ruga izuwa cikin jeji.Muna isa inda dabbobin suke mukayi arba da gawar mutane biyu,mace da namiji.Namijin dai ba wani bane face Lunzaru mai kawo madarar shanu nan fada kullum da safe,macen kuwa matarsa ce mahaifiyar wannan yaro wanda muka tsinta zauna a kas kusa da gawar tasu yana ta sheka kuka.Ya shugabana na sani cewa kai mai adalci da jin kai ne bisa haka ne na dauko wannan yaro tare da dabbobinsa na kawo su gareka domin yaron yana bukatar taimako tunda yanzu ya zamana maraya.Sa'adda Huzaika yazo nan a labarinsa sai kawai yaga hawaye ya zubo daga idanun sarki cikin sanyin jiki sarki ya sumbaci goshin Shubairu sannan ya karbeshi daga hannun sarki yaki ya mikawa Gimbiya Lamrisa ya dubeta cikin murmushi yace karbi wannan yaro yake matata yau kin sami mai kore miki bakin cikin daya addabi zuciyarki tsawon shekaru goma sha daya.Koda jin wannan batu sai fadar gaba daya ta rude da shewa masu kade kade da bushe bushe suka kama aikinsu.Ita kuwa gimbiya Lamrisa saita rungume yaro Shubairu ta fashe da kukan farin ciki ta ruga izuwa cikin gidan sarautar.Sarki Kuzzaru ya koma kan KARAGAR MULKI ya zauna sannan ya share hawayen dake bisa kumatunsa ya dubi jama'ar dake cikin fadar gaba daya yace yaku jama'ata kuyi sani cewa a yau ina cikin tsananin farin ciki haka kuma ina cikin matukar bakin ciki.Ba komai ne yasa nake wannan farin ciki ba sai domin a yau ne matata gimbiya Lamrisa ta fita daga cikin kuncin bakin ciki na tsawon shekaru goma sha daya.Tabbas wannan yaro da aka kawo zai kawar mata da kewar rashin haihuwa domin nasan cewa zata reneshi kamar yadda zata reni dan cikinta.Dangane da bakin cikin da nakeyi kuwa shine wannan talaka nawa da yan fashi suka kashe wato mahaifin Shubairu ya kasance masoyina na kwarai,a duniya ban taba samun mutum MAI KAUNATA ba kamarsa.Tabbas akwai sirri mai karfi a tsakanina dashi amma kuma ban isa na jawo shi jikina ba shi yasa bakusan alakar dake tsakanina dashi ba.Jin ya mutu ne na zubar da hawayena domin nasan cewa na rasa masoyi wanda bazan taba samun kamarsa ba.A iya sanina da Lumzaru ban taba sani cewa yana da aure ba bare ma nasan cewa yana da 'da.Ko shakka banayi yana boye wannan kyakkyawan da nasa ne domin inda wani ya taba ganinsa da tuni labarinsa ya cika gari.Bisa dalilin faruwar wannan al'amari daya faru a yau na tsintar wannan yaro na bayar da hutun kwana bakwai a kasata kowa ya zauna a gida ya huta,sannan kuma na bayar da umarni a sallami dukkan tsofaffun fursunoni a dukkan kurkukun kasar nan wadanda sukayi shekaru uku da tsarewa.Haka kuma na shirya walima ta kwana bakwai kullum dare da rana anan fadata domin taya farin ciki bisa samun wannan yaro kuma ina gaiyatar kowa da kowa,talaka da mai kudi,bawa da basarake ban bambance ba.Koda jin wannan batu sai fadar ta sake rudewa da shewa mutane suka kama farin ciki.Kamar yadda sarki Kuzzaru yayi alkawari haka al'amura suka kasance wato saida aka shafe kwanaki bakwai ana shagalin walima dare da rana a cikin birnin kisra a gidan sarauta.Talakawa,attajirai,sarakai da sauran jama'a kuwa suka rinka cincirindo a cikin gidan sarki saboda yawan jama'a idan mutum ya dubesu sai yayi zaton cewa mutanen duniyar ne kaf suka taru amma duk da wannan yawa na jama'a saida abinci da abin sha ya wadace su kai almajirai ma saida suka daina barar abinci a tsawon wadannan kwanaki bakwai.Daga wannan rana gimbiya Lamrisa ta cigaba da renon yaro Shubairu ta kaunace shi ainun tamkar itace ta haifeshi,dare da rana tana tare dashi babu abinda ke raba su.Duk wani gata na duniya babu irin wanda Lamrisa bata nunawa Shubairu ba,kullum idan tayi masa wanka sai ta caba masa ado irin na yayan sarakai.Kai saboda tsananin son da Lamrisa ke yiwa Shubairu saida tasa wani gwani masassaki ya sassaka gunkinta dana Shubairu wanda yayi matukar kama dasu aka ajiye gumakan biyu a tsakiyar katon falon dake bangaren turakarta.Babu abinda zai dada baiwa ★littattafañ hausa mutum mamaki face yadda gaba dayan mutanen gari ke girmama Yaro Shubairu ya zamana cewa ana kiransa da suna YARIMA.Shi kansa sarki Kuzzaru nan da nan ya shaku da Shubairu yaji kamar dan cikinsa ne amma duk sa'adda ya tuno da cewar Shubairu bazai taba gadonsa ba sai ya cika da tsananin bakin ciki ya kulle kansa a cikin turakarsa yayi kuka ya more.Kullum idan sarki zai tafi fada tare da Shubairu yake tafiya,kuma wabi abin sha'awa shine shiga iri daya sukeyi kuma ko yaushe Shubairu na zaune daf dashi bisa karagar mulki.Shi kansa Shubairu ya tsinci kansa a cikin sabuwar rayuwa ta daula har ya rinka jin kamar bai taba rasa iyayensa ba saboda sa'adda iyayen nasa ma ke raye bai taba samun irin wannan daula ba. WATA RANA da hantsi fada ta cika makil da jama'a Shubairu na zaune daf da sarki saiga wani mutum mai siffar attajirai ya shigo cikin fadar.Da zuwan mutumin saiya fadi gaban sarki ya kwashi gaisuwa sannan ya dago kai ya dubi sarki yace ya shugabana ni sunana Ubairu ibini Lauras kuma na fito ne daga birnin Mirsa.Na kasance bafatake mai tarin dukiya don haka duk sa'adda zan fito fataucina nakan fito da rakuma dubu dari gami da dakaruna mutum dubu hamsin masu tsaron lafiyata da dukiyata.Yanzu da hanya ta biyo ni ta kofar birninka saina yanke shawarar na shigo cikin birninka na yada zango kuma na baje kolina a ranar da kasuwarku ke ci.A halin yanzu masu gadin kofar birninka sun hanani shigowa da rakuma na da kuma dakaruna,ni kadai suka bari na shigo shine nazo neman alfarma a wajenka domin ka bani izini na shigo da hajata da dakaruna.Yanzu haka daya daga cikin masu gadin kofar garin ne ya rako ni izuwa nan fadarka domin yaji da bakinka idan ka amince.Lokacin da attajiri Ubairu yake ta wannan bayani Shubairu ya kura masa idanu.Nan take idanun Shubairu sukayi jawur kuma fuskarsa ta sauya yanayi daga annuri izuwa fushi.Har sarki Kuzzaru ya budi baki zaiyi bayanin amincewarsa akan Ubairu ya shigo da dakarunsa da dukiyarsa sai Shubairu ya tari numfashinsa yace Ya Abbana inason na gana dakai a sirrance.Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama kowa a cikin fadar domin Shubairu bai taba tsoma bakinsa ba a cikin harkokin mulki sai yau. da fatan xaku gafarcemu na dan rashin postin da bamayi wannan ya damo Asaline saka makon rasa wasu littattafan da mukayi da kuma lalacewar computer mu. ★DAKAKKIYAR ZUCIYA★!!! Littafi Na Daya (1) Part B. BAI TABA TSOMA BAKINSA BA A CIKIN HARKOKIN MULKI SAI A YAU.BA TARE DA GARDAMAR KOMAI BA SARKI YA MIKE TSAYE YA KAMA HANNUN Shubairu suka koma can gefe daya inda babu wanda zaiji abinda zasu tattauna sannan ya dubeshi yace yakai dana me kake son zaka gaya mini ne har da ka katse mini hanzari bisa alfarmar da wannan bakon attajiri yazo mini da ita? Sa'adda Shubairu yaji wannan tambaya sai yayi ajiyar zuciya cikin takaici yace yakai abbana ai wannan attajiri wakili ne na babban makiyinka sarki Farhama na birnin Kairufa.Ina tabbatar maka da cewa hajar da yazo da ita bisa rakuma dari ba komai bace face wadansu mugayen aljanu guda dubu dari biyar wadanda idan har ka bari aka shigo dasu cikin birninka sai sun hallaka gaba dayan jama'armu.Sannan ayi maka juyin mulki ayi maka kisan gilla a kone dukkan wadannan kyawawan gine ginenmu.Ya Abbana duk wannan bayani danayi maka yanzu na ganshi ne akan fuskar attajiri Ubairu a lokacin da yake gabatar da kansa.Ina so ka sani cewa a zahiri idan ka tura aka duba wannan haja wacce attajiri Ubairu yazo da ita babu abinda za'a gani face kayayyakin karafa na dangin zinare da lu'u lu'u amma idan mai karfin sihiri zai dubesu zai ga cewa wasu muggun bakaken aljanu neLallai kasan matakin da zaka dauka akan wannan al'amari idan kuwa kayi sakaci lallai karshen mulkinka yazo.Sa'adda yaro Shubairu yazo nan a zancensa sai hankalin sarki Kuzzaru ya dugunzuma ainun ya kurawa Shubairu idanu cikin tsananin al'ajabi.Abu na farko shine tabbas ya san cewa fiye da shekaru ashirin baya sarki Farhama nata shirya masa mugun tanadi don ganin bayansa amma yana tsallakewa bisa taimakon bokansa mai suna Zuraita Ibini Laufur.Abin mamakin shine tunda aka tsinto yaro Shubairu boka Zuraita bai sake zuwa fada ba.Alhakin a da can duk bayan kwana uku sai yazo ya yiwa sarki bayani bisa abubuwan da yake hangen zasu iya faruwa nan gaba a cikin binciken da yayi.To waishin menene ya hana Boka Zuraita zuwa fadar a tsawon kwanaki arba'in da bayyanar Shubairu?Sarki Kuzzaru ya tambayi kansa a cikin zuciya kuma ya kasa baiwa kansa amsa.Sarki Kuzzaru ya sake tambayar kansa yace to wai shin shi wannan yaro Shubairu yaya akayi yasan al'amarin Ubairu?Ni dai a sanina da mahaifin wannan yaro bai kasance boka ba.A ina Shubairu ya sami ilmin tsafi?Bayan sarki Kuzzaru ya gama yiwa kansa wadannan tsauraran tambayoyi a cikin zuciyarsa saiya kawo gwauron numfashi ya ajiye sannan ya dubi Shubairu cikin murmushi yace yakai dana tabbas na yarda da duk wannan jawabi da kayi mini,dalili kuwa shine nasan mahaifinka mutum ne mai gaskiya da amana kuma nayi imani cewa ka gaji halayensa don haka zanyi amfani da wannan shawara daka bani lallai zan san matakin dazan dauka a kai.Koda gama fadin haka sai sarki ya kama hannun Shubairu yaja shi suka koma izuwa kan karagar mulki suka zauna.A wannan lokaci gaba dayan fadar tayi tsit kowa ya zubaido kuma ya kasa kunne yaji abinda sarki zai fadawa attajiri Ubairu tunda ba'a san shawarar da yayi da yarima Shubairu ba.Bayan sarki Kuzzaru da Shubairu sun zauna akan karagar mulki sai sarki ya dubi attajiri Ubairu yace yakai wannan babban bako ka koma can wajen gari wajen dukiyarka da jama'arka ku kafa tantuna ku kwana acan lallai kafin safiya zan yanke hukunci bisa bukatarka.Koda jin wannan batu sai attajiri Ubairu yayi murmushi gami da godiya sannan ya mike tsaye dan ya juya ya fice daga cikin fadar.Koda ya hada idanu da yaro Shubairu sai akaga ya fadi kasa yana tari da kyar ya mike tsaye ya fice daga fadar ba tare daya yarda ya sake hada ido da shubairu ba.Al'amarin dayai matukar baiwa kowa mamaki kenan har shi kansa sarki Kuzzarun.Bayan tafiyar attajiri Ubairu sai sarki ya sallami fadawansa da sauran mutanen gari amma banda sarkin yaki Huzaika bayan jama'a sun watse sai sarki ya dubi Huzaika yace yakai dirkar birnin kisra kayi sani cewa Shubairu yazo mini da shawara bisa wannan bakon attajiri akan kada na kuskura na bashi izinin shigowa cikin birnina tare da hajarsa da dakarunsa domin wakili ne na babban makiyinmu sarki Farhama.Hakika nayi matukar mamaki bisa wannan al'amari wani abu daya sake daure min kai shine tunda ka kawo Shubairu gareni boka Zuraita bai sake kawo mini ziyara ba.Abinda nake so da kai shine yanzu ka tafi izuwa gidan boka Zuraita kace dashi menene dalilin da yasa ya daina ziyarta ta har tsawon kwanaki arba'in,sannan kuma ka gaya masa cewa ina neman shawararsa bisa wannan bakon attajiri dayazo mini.Koda jin wannan umarni sai shi ma sarkin yaki Huzaika ya cika da mamaki amma sai yayi shiru baice komai ba.kawai saiya risina yace an gama ya shugabana.Nan yake Huzaika ya juya ya fice daga cikin fadar ya tafi izuwa gidan boka Zuraita wanda ke can kusa da karshen gari.Sarki kuwa sai ya kama hannun Shubairu yajashi suka shige izuwa cikin gidan sarautar suka nufi bangaren turakar gimbiya Lamrisa. *Al'amarin Attajiri Ubairu kuwa tunda ya baro fadar sarki Kuzzaru ya kasance a cikin matukar tashin hankali da matukar damuwa ya cigaba da tafiya cikin sauri da waige waige kamar ace kyat ya fita da gudu.Kallo daya mutum zaiyi masa ya fahimci cewa lallai babu alamar gaskiya a tare dashi.Da isar Ubairu bayan gari inda yabar rakumansa da dakarunsa saiya umarci dakarun nasa dasu kafa tantuna.Cikin mamaki dakarun suka mike suka kama bin umarnin domin su a zatonsu yana zuwa zaice su kada rakumansu a shiga cikin birnin kisra.Bayan an kafa tantunan sai Ubairu ya shiga cikin nasa tantin ya zauna yayi tagumi yana tunanin abinda zai fissheshi.Yana cikin wannan hali Wani Jibegegn aljani baki sidik ya bayyana a gabansa.Girman Aljanin yakai na wani katon tsauni saboda tsananin munin aljanin kuwa idan mutum ya dubeshi sai zuciyarsa ta tashi yaji kamar zaiyi kumallo.Babu abinda zaifi firgita mutum a tare da wannan aljani face kwala kwalan jajayen idanunsa.Cikin fushi aljanin ya dakawa Ubairu tsawa yace yakai wakilin sarki Farhama saboda me zaka shanya mu a rana tamkar mun kasance bayinka?Shin ka manta ne cewa sarki Farhama ya turo mu ne domin mu baje wannan birni na Kisra a cikin abinda bai wuce yini daya ba?Sa'adda Ubairu yaji wannan batu sai ya dubi aljanin yace haba Darkusa kaima kasan cewa in babu matsala babu yadda za'ayi a sami wani jinkiri a cikin wannan aiki.Tabbas akwai gagarumar matsala domin ina ganin cewa asirinmu ya tonu,sarki Kuzzaru bazai taba bari mu shiga cikin wannan birni nasa ba har mu sami damar cika aikinmu.Koda jin haka sai aljani Darkusa ya cika da tsananin mamaki yace yaya akayi asirinmu ya tonu alhalin karfin sihirinmu yafi nasa kuma yafi na bokansa?Dajin haka sai Ubairu yayi ajiyar zuciya yace ai lokacin dana isa fadar sarki Kuzzaru sai nayi arba da wani shu'umin yaro a tare dashi wanda bzai fi shekaru shida ba a duniya.Muna hada idanu dashi naji zazzabi ya shigeni kuma naji gaba dayan sirrikan tsafina sun daina aiki.Nikam bana raba daya biyu akwai TSATSUBA a tare da wannan yaro.Tabbas idan har muna son mu cika umarnin sarki Farhama dole ne sai mun fara kawar da wannan yaro saboda sun tattauna kuma babu wanda yaji abinda suka zanta a tsakaninsu.Yayin da aljani Darkusa yaji haka saiya tuntsire da dariyar mugunta lokaci guda kuma ya turbune fuska yace.Haba yakai Ubairu yanzu kai kankanin yaro ne zai firgitaka haka amma dai ka bani kunya..To tsaya kaji ni kam bazan yarda ni da jama'ata mu shiga cikin fushin sarki Farhama ba saboda haka daga nan zuwa wayewar gari lallai kasan hanyar da zakabi ka shigar damu cikin wannan birni ko ta halin kaka koda karfin tsiya kuwa.Idan kuwa kaki ni da kaina zan kashe ka in yaso na koma na gayawa sarki Farhama cewa ka kasa gabatar da aikinsa na kashe ka.Lokacin da Aljani Darkusa yazo nan a zancensa sai hankalin Ubairu ya kara dugunzuma fiye da ko yaushe domin ya fuskanci cewa yana cikin GABA TSINI BAYA SIYAKI domin ya tabbatar da cewa idan har ya kasa shigar da rakumansa cikin birnin kisra lallai koda ya koma birnin Kairufa sunansa GAWA domin akan wannan sharadi sarki Farhama ya bashi jagorancin wannan tafiya.Sarki Farhama ya kasance takadirin matsafi kuma GWARZON MAYAKI mai tsananin KARFIN DAMTSE da jarumtaka amma kuma ya shakkar sarki Kuzzaru a bangaren sadaukantaka domin sau bakwai suna kwamarzuwa a FILIN YAKI sunayin KARE JINI BIRI JINI.Wato duk sa'adda sukayi yakin kowannensu yana matukar shan wahala tamkar zasuyi RAGAS! Ba komai ne ya haddasa hakan ba face karfin damtsensu da iya yakinsu yazo daya inda ka sami bambanci shine Sarki Farhama yafi sarki Kuzzaru karfin sihiri.To amma sai boka Zuraita ya rinka baiwa sarki Kuzzaru kariya bisa dukkan sharrin sarki Farhama na tsafi.Gabar dake tsakanin sarki Farhama da sarki Kuzzaru ta samo asali ne tun daga iyayensu akan wani abu daya faru kimanin shekaru talatin baya.Al'amarin ya faru ne a wata safiya sa'adda wadansu fatake daga birnin Kairufa suka shigo cin kasuwa a cikin birnin Kisra ashe ba fatake bane barayi ne wadanda suka kware a iya sata.Musamman sarki Farhama ya dauko hayar barayin daga can wata nahiya daban ya biya su dukiy mai yawan gaske akan su sato masa wata kanwar sarkin birnin Misra wacce ta kasance TAURARUWAR TAURARI a cikin 'YANMATA na wannan zamani ana kiranta da suna SIYAMAT.Saboda tsananin kyawun Siyamat saida labarinta ya bazu a ko ina a duniya a wannan lokaci ya zamana cewa yayan sarakai,attajirai da bokaye suka rinka zuwa neman aurenta daga kowanne bangare na duniya.Mahaifin sarki Farhama kuwa sau tara yana aiko da dumbin dukiya wacce ta shallake hankali a matsayin toshi domin a bashi auren gimbiya Siyamat ga dansa Yarima Farhama.Duk sa'adda aka kawo dukiyar sai sarkin Kisra ya karba ya adanata yace a koma a gayawa mahaifin sarki Farhama cewa ya cigaba da sauraronsa.Lokacin da Masoyan Gimbiya Siyamat sukayi yawa kimanin mutum dari bakwai kuma dukkaninsu masu arziki ne sai hankalin mahaifin sarki Kuzzaru ya DUGUNZUMA ainun ya rasa abinda ke masa dadi domin ya rasa wanda zai baiwa auren Siyamat a cikinsu.Bisa wannan dalili ne ya kira mahaifin Boka Zuraita suka kebe domin yin shawara.Mahaifin Zuraita yayi shiru yana tunani daga bisani ya dago kai ya dubi sarkin Kisra yace ya shugabana kayi sani cewa a halin yanzu a cikin masoya yar uwarka gimbiya Siyamat babu mai matsayi da daraja kamar Yarima Farhama dan sarkin birnin Kairufa to amma fa ka sani cewa idan Yarima Farhama ya auri gimbiya Siyamat har abada ba zaka sake ganin Siyamat ba har izuwa lokacin da ajalinka zai cika.Abinda na gani kenan a cikin bincikena na tsafi.Ka sani cewa idan ka fito fili karara kace ba zaka aurar da ita ga Yarima Farhama ba to fa sai sarkin Kairufa ya nemi yaki da kai.Domin dansa Farhama ya haukace a cikin son Gimbiya Siyamat idan har bai aureta ba zai iya kashe kansa ko kuma hankalinsa ya tabu.A duniya babu abinda sarkin Kairufa ke so sama da dansa Yarima Farhama don haka zai iya sallama komai nasa domin biyan bukatar dansa.Shawarar da zan baka itace kasa a shirya gasa mai matukar wahalar gaske ta neman auren gimbiya Siyamat wacce babu wanda zai iya samun nasara kaga shike nan dole ne Yarima Farhama ya hakura da auren Siyamat in yaso kai kuma sai ka aurar da ita ga dan sarkin da hankalin

Chapter 1 of 4