Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 4
sai da tafito daga cikin keken dokin .Koda suka daga kawunansu sama sai sukaga wata tartsatsin wuta nata nata fantsama a sararin samaniya .Nan take sai wata jibgegiyar tsuntsuwa mai matukar girma irin wayannan tsuntsaye ana kiransu da rukki ne.Bisa saman wannan rukki din wani sadaukin jarumine yana sanye da sulken yaki da kuma kaftareren takobi a gefen kugunsa wannan sadauki ya rufe fuskarsa da wata hular karfe ..Wannan tsuntsuwa tai kasa cikin kankanin lokaci ta sauko izuwa doron kasa ,tana sauka wannan jarumin mai kirar sadaukai ya diro daga samansa ..Sannan yafara tattaki yana nufan wajen da su sarauniya lasmin suke ita da hilal .Yana karisowa yace dasu" yaku wayannan jarumai shin kuna mamakin ganina ne awannan lokaci .Shin kuna tunanin ku biyu kadai ne zakui wannan tafiya izuwa neman TAKOBIN JINI.Toh kusani nima ina daya daga cikinku.Lasmin ta dubeshi sannan tace dashi yakai wannan jarumi ma'aboci lullube fuska shin wanene kai kuma daga ina kake ..Koda jin haka sai wannan bakon jarumin ya cire hular dake kansa .Aiko yana cirewa sai dakarun dake tare da sarauniya lasmin .Suka zube bisa gwuiwowinsu suna gaisuwa gareshi baccin sun idar sai sarkin yaki kumru ya kariso izuwa gabansa yana mai cewa" ya shugabana ka gafarceni bisa dadewa danayi ban iso gareka ba"..Nan take wannan jarumi yadaga masa hannu sa'annan yadubi su hilal yace dasu " nine sarki gulmanu mai mulkar birnin ashdamir"..Sarauniya lasmin ta dubeshi sannan tace dashi "amma mai yasa baka jiramu mun iso izuwa birnin ka ba"Gulmanu ya sauke ajiyar zuciya sannan yace da ita " tabbas bokana ya nuna min duk abin dayake faruwa daku tun daga lokacin da kika fito daga gida har iyanzu da kike dab da shiga birnina ,koda naga kun hadu da jarumin da zamu fita nema sai nayi shirin fita sa'annan na fito don tarbeku .Sannan kusani yanzu bazamu mu shiga birnina ba zamu tafine izuwa cikin wancan tanti daga nan sai muyi shawarar daga inda zamu fara neman wannan takobiYafada yana mai kallon hilal.Hilal yai murmushi sannan yace dasu daza ku yarda ku karbi Addinin musulunci da nikuma sai na dauko maku takobin jini da hannuna kuma batare da zoben wuta ba..Koda gulmanu yaji haka sai ya bushe da dariya sannan yace mai kasani yakai wannan jarumi ba zamu taba yarda mu amshi wannan Addini naka ba .Kasani ba za mu taba watsi da Addinin iyaye da kakanni ba.Sannan da kake maganar mu amshi Addinikan toh izan mun amsa menene Amfanin takobin jinin.Addininka ya haramta tsafi mukuma baza mu taba watsi da tsafi ba ..Lasmin ta dubeshi tace yanzu mene abun daya kamata muyi.Anan gulmanu yai nuni da hannunsa izuwa wani gefe take sai tanti ta bayyana .Dukkansu suka nufi wannan tanti amma banda sauran dakaru .Juyowar da gulmanu zaiyi sai yai arba da shaddadu yana mai murtuke fuska yana binsu izuwa cikin wannan tanti.Nan yadaka masa tsawa yace"kai daedai matsayinka wajen tantin nan badae cikinsa ba .Shaddadu ko sauraransa baiyiba in banda sakai dayayi da nufin ya kutsa cikin tantin aiko yana kutso kangulmanu yai tsalle ya kaftara masa dundu abaya sannan yai nuni da hannunsa gareshi take ya fara daskare wa tundaga kan yatsun hannunsa koda shaddadu yaga yana daskarewa sai ya kurma wata irin ihu ..A yayin dayake ihunne gaba dayan jikinsa ya daskare yakoma tamkar wani mutum mutumi . ..Zanci gaba.TAKOBIN JIN 3!!! Littafina Uku (3) Littafin Shuraih Usman Part 6 . Nan sarki gulmanu ya bushe da dariya wanda ta haddasa karamar girgizar kasa sai da yayi mai isarsa sannan yai shiru ya dubi sarauniya lasmin yace " haka kike da bawa mara jin magana, toh ga abinda rashin jin maganarsa ta janyo masa" . Yana gama fadin hakan sai yasa kai cikin wannan tantin suma suka bishi abaya , Wani kyamushashshen tsohone sanye da warkin fatan zaki , Zaune yake ya nannade kafa , kai kace wani mashahurin malamine , , Gaba daya idanuwansa a rufe suke bakinsa ne kawai ke motsi, , Koda su sarauniya lasmin sukayi arba da wannan tsohon sai suka kura masa idanu suna kallonsa Sarki gulmanu yace dasu" wannan shine dirkar birnina boka bal balin bala'I,sannan kuma da taimakawarsa ne har zamu iya isa inda aljani sham'una yake" . Boka balbalin bala'I ya dubesu daya bayan daya sannan yafara da cewa" Yaku wayannan zaratan jarumai kuyi sani cewa gaba dayanku kun dauko wakanku babban buri wadda muddin ku ka cika wannan buri toh tabbas duniya zata shiga halin kunci da takaici, ,dayanku ne kawai zai mallaki takobin jini, biyun ku kam sai dai su hallaka, , Koda sarki gulmanu yaji haka sai ya dubi boka balbalin bala'I yace dashi" amma mai yasa. Baka sanar dani hakan ba tun da wuri" . "Nima kaina yaune aka sanar dani " . Sarauniya lasmin ta dubeshi tace " waya sanar dakai" . Wani aljani ne daga cikin Hadimaina mai suna Lumzaru ya sanar dani hakan" . Hilal ya dubesu gaba dayansu yace " innalillahi wa'inna ilai hirra ji'un, da zaku tuba ga Allah ku bar shirka ,da tsafi toh da ni zan dauko muku wannan takobi batare da kunsha wata wahala ba" . Gulmanu ya dubeshi yana mai murnushi yace" kai yarone shi yasa kake fadin wannan maganar da kasan bazai taba yiwuwa ba," . "Kubar wannan takaddamar yanzu ba lokacinsa bane , kamata yayi mu nemi mafita game da wannan tafiya da zamuyi" Sarauniya lasmince tai wannan furuci a yayin datake duban hilal da gulmanu . Nan boka bal balin bala'I ya tashi daga zaune ya dubesu yace" wannan tafiya da zakuyi zan hada ku da Aljani lumzaru amintaccen hadimina ne shine kadai zai iya kaiku dajin da aljani sham'una yake , ku sani kafin ku isa wannan daji sai kun fada cikin masifu da bala'I kala kala , Muddin kuka tsallake wayannan masifun to tabbas zaku isa ga wannan jeji da aljani sham'una yake , sai dai nayi nayi in gano inda ya boye suraila , amma nakasa. . Koda gama fadin hakan sai boka bal'balin bala'I ya bace bat, , Bace warsa keda wuya sai wani katon aljani ya baiyana , shi wannan aljani jikinsa gaba daya irin na mutane ne, sai dai girma da Allah ya bashi gashi da wasu fuka fukai a gadon bayansa ,yana dauke da wata narkeken kai wacce in mutum yai arba da wannan kan nasa to yana iya zaucewa ko ya hallaka, ma . Koda bayyanar wannan aljani sai ya dubi su sarki gulmanu yace " Sunana aljani lumzaru, sannan kuma nine zanyi muku jagora izuwa jejin da sham'una yake . Bayan dukkansu sun hau bisa kan aljani lumzaru nan ya tayar da fuka fukansa sannan ya tashi sama ya luluka cikin gajimare . Wani dokar dajine wanda rairayinsa na hamada ne wasu kananun ciyayi sun yi dajin lema, a gaban wannan dajin wani tafkeken korama ce, Ruwan dake gudana a cikin koramar kyalkyal da shi gwanin sha'awa, , Wani bakin abu na hango a sararin samaniya yana yiwo kasa, sai da wannan abun ya kariso izuwa kasa sannan na lura ashe, aljani lumzaru ne dauke da sarauniya lasmin da sarki gulmanu sannan yarima hilal, , Saukarsu a wannan jeji keda wuya, sai yarima hilal ya nufi bakin wannan kogi yai alwala, koda ya idar sai ya tada kabbarar sallah , nan ya shiga ramakon dukkan sallolin da bai samu damar yinsu ba, A gefe kuwa sarki gulmanu ne da sarauniya lasmin tsaye kusa da juna suna kallonsa, yayin dayake gudanar da ibadarsa, "Ni ban taba ganin irin wannan bautar ba," sarauniya lasmin ta fadi yayin da take duban hilal, "Ta yaya zanriga bautawa abin dana ganinsa, "ta sake fadi akaro na biyu Gulmanu ya dubeta sannan yayi murmushi yace" Na tsani wannan Bakon Addinin , dan hasalima dabara na hada ma hilal, tarko ce kuma ya shigeta, " Sarauniya lasmin ta dubeshi fuskanta dauke da alamun rashin fahimta tace " ban fahimci abin da kake nufi daya fada tarkonka ba" Dariya kawai gulmanu yayi yace"tabbas yake wannan sarauniya zaki fahimta nan bada dadewa ba, " yana gama fadin hakan, sai aljani lumzaru yazo gabansa yace" ya shugabana hakika ina son na fada maku wasu abubuwa masu muhimmanci a game da wannan tafiyar tamu" Toh a dai dai wannan lokacine yarima hikal ya idar da ibadarsa salla, sannan ya kariso wajen da su gulmanu suke, Aljani lumzaru yai gyaran murya yace" Ya shugabana lallai kayisani cewa kafin mukai ga . . Tobe continue Hakkin mallaka (c) Shuraih Usman Marubuci:- Shuraih Usman Company:- Shuraih 99% TAKOBIN JIN 3!!! Littafina Uku (3) Littafin Shuraih Usman Part 7 . "Ya shugabana lallai kayisani cewa kafin mu isa jejin da aljani sham'una ya ke sai mun bi ta cikin wasu dazuzzuka Hudu, kowani daji yana dauke da muggun masifa wacce da zarar mun ketare wannan masifa shine zamu isa jejin da aljani da sham'una yake, Dajin farko da zamu fara isa itace GABATUL HAYYAT, . Babu komai a cikin wannan daji face wata Tafkekiyar macijiya mai kawuna biyar, Ita wacannan maciya tafi fiye da shekaru Dubu arba'in a cikin wannan jeji , Maciyar nan tana da kawuna biyar a jikinta kowani kai da irin masifar da yake fesowa, Abu mai mahimmanci da ya kamata kusani game da wannan maciyar shine, KAIFI DA TSINI basa tasiri a jikinta , ruhin wannan maciya, yana cikin daya daga cikin kawunanta, inda ruhin kuwa yake shine tsakiyar kanta , Nayi bincike ainun domin na gano daga cikin kawunanta biyar din nan wanne ne ruhin yake , amma na kasa, . A tarihin wannan daji na Gabatul hayyat babu wani mahaluki daya taba shiga cikinta koya ketare ta cikinta batare da ya zama gawa ba, face aljani sham'una shima kuwa sabida hatsabiban cinsa ne . Daji na gaba kuwa ana kiransa da JEJIN FATALWI, shi wannan jeji babu komai a cikinsa sai wasu irin fatalwi, masu maka makan kawuna , jikinsu kuwa siriri, yayin da kafafuwansu ke barazanar karyewa a ko wani lokaci, Su wannan fatalwi babu wanda yasan iya zamanin da suka deba a cikin wannan jeji , . Muddin kuka shiga cikin wannan jeji na fatalwi, toh baza ku taba tsira da rayukanku ba, yawan adadin wayannan fatalwi yafi metan, kuma wayannan fatalwi ba a ganinsu sakamakon wani mayanin tsafi da suke lullube jikinsu da shi, Amma idan babu wannan mayani, toh zaku gansu ", , Aljani lumzaru ya sauke numfashi "Toh ta yaya kenan zamu bi cikin wannan jeji batare da dayanmu ya hallaka ba" sarauniya lasmin ce ta jefa wa lumzaru wannan tambayar. Lumzaru ya gyara murya sannan yace" ya shugabata su wayannan fatalwi, tsafi da sihiri baya tasiri akansu, sannan kuma da zarar kun shiga wannan jeji to duk wani sihirinku bazai taba aiki ba har sai kun fice da ga cikin dajin. . Dole duk yadda za'ayi ku sami ku kashe daya daga cikinsu, izan kun kashe shi toh sai ku cire wannan mayani da ke lullube a jikinsa, daya daga cikinku sai ya saka ajikinsa, toh anan take zai bace , Toh ta haka ne kawai zaku iya cin galaba akansu , , Daji na gaba kuwa ana kiransa da BAHRAIN , Dajin bahrain , dajine da aka tsaface shi , fiye da shekaru da suka shude sunan wannan daji zuhru , A lokacin da aljani sham'una ya tare a cikin wannan nahiya sai ya sana'anta wani babbar mutum mutumi ya kafe acikin wannan daji , Koda kafe wannan mutum mutumi, sai wannan daji gabadayanta ta koma izuwa babbar kogi, ruwan wannan kogin kuwa, rabinsa, launin fatsi fatsi ne rabin kuwa launin baki gareshi, . A kwai miyagun sihirtattun namun jeji bila adadin a cikin wannan babbar koramar , Abu mai muhimmanci daya kamata kusani game da wannan daji kuwa shine, , Da zarar kun tunkaro dajin zaku gansa a siffar daji , da kun shigeshi kuwa da taku arba'in zai rikide izuwa babban kogi, nan take zaku lume a cikin wannan ruwa, , Muddin kuka yi nasarar hallaka halittun dakae cikin wannan korama , toh wani siririn hanya zai hudo ta cikin kasa, sai kubi wannan siririn ramin , , Ayayin da kuka isa karken wannan rami zaku ga wata kofa, a hannun damarku, sai ku bude ku shiga, anan ne zaku tarar da wannan mutum mutumi a kafe cikin kasa, sai kuzo gaban wannan mutum mutumi din zaku ga wata akwati a gefen kafufuwansa, , Da zarar kun bude wannan akwatin zaku ga wani Kubba, na bakin karfe sai ku dauki wannan bakin kubban , Ku zurashi a bakin wannan mutum mutumi, toh nan take zaku ji wata kara, Mai amo, da zarar wannan kara ta dauke wannan mutum mutumi zai tarwatse, . To a sannan ne wannan jeji zai koma yadda yake , duk wani sihiri da tsafi zai karye, . Daji na gaba kuwa ba jeji bane, yumbun hamada ne , shi wannan yumbun yana da da zafi mai matukar radadi, don zai iya narkar da bakin karfe, . A kasar wannan yumbun kuwa, ramuka ne wayanda yawansu yafi milyan daya, Kowani rami daya tsayinsa, yafi kamu arba'in, fadinsa kuwa zai iya cin mutane dubu ajere, bisa layi, . Yumbun kuwa ya rurrufe wayannan ramuka ta yadda baza ka taba zata akwai wani abu wai shi rami a wajen ba," . Koda aljani lumzaru ya kawo nan a zancensa sai ya dubi sarki gulmanu, sa'annan yace" ya shugabana a yayin da kuka isa bakin wannan yumbun hamada toh sai ku tsaya, a bakin wannan yumbu har sai rana ta kusa faduwa, to a sannan ne zaku ga wata duhuwa ta mamaye gaba daya ilahirin wannan yumbun na hamada, . Da zarar wannan duhuwa ta baiyana to dukkan wani zafi da ke cikin wannan yumbu zai kau, Sannan wayannan ramukan zasu toshe , A sannan ne ku kuma zaku shiga cikin wannan yumbu, Ya zama wajibi a gareku ku hanzarta ku ketare wannan yumbu, kafin cikar sa'a daya," , "Me zai faru izan har muka debi fiye da sa'a daya acikin wannan yumbu" gulmanu ne ya katse shi da fadin hakan , Aljani lumxaru yace"wannan duhuwa itace ta kare ku daga masifar wannan yumbu, toh da zarar sa'a daya ta cika, wannan duhuwa zata yaye, muddin kuwa kuka bari wannan duhuwa ta yaye kuna cikin wannan yumbun toh take zaku narke ku koma tamkar ruwa a sabida zafin wannan yumbun na hamada, , Muddin kuka fice daga cikin wannan daji da rayukanku, Toh a sannan ne zaku isa sansanin aljani Sham'una, . , Am tired men . Tobe continue Hakkin mallaka (c) Shuraih Usman Marubuci:- Shuraih Usman Company:- Shuraih 99% TAKOBIN JINI . Book 3 . Littafin Shuraih Usman Part 8 . Aljani lumxaru ya cigaba da cewa shikuwa sansanin aljani sham'una ko ince dajin dayake da zama , Maganar gaskiya itace bansan komai game da wannan daji ba , sai kun isa tukun zakuga irin masifar dake cikin wannan jeji, . Koda gama wannan zance nashi sai sarki gulmanu ya duvesu yace , gobe da safe zamu isa wancan daji na farko wato dajin gabatul hayyat, daga nan ne izan muka tsira da rayuwarmu sai mu cimma daji na gaba, , Amma kafin wannan ina so na gayamaka," ya maida kallonsa ga yarima hilal kada ka kara yunkurin, kwadaita mana Addininka kayi Addininka muyi Addininmu, Bukata ce ta hada mu da kowa isar da bukatarsa, shi kenan munyi hannun riga . Yarima hilal yayi murmushi sannan yace" naji na amince bazan kara kiranku izuwa Addinina ba Amma ina da sharadi guda daya da zan gin daya maku" . Sarauniya lasmin tayi sauri ta ce" shin kai kuwa hilal wani sharadi kenan da harkake cewa zaka gin daya mana" "Wannan sharadi kuwa itace duk wani masifan da daya daga cikinku ya tsinci kansa, zan barsa ya dogara da ababen bautarsa, da kuma dabararsa a yayin da ababen bautar tasa da dabarartasa suka ki aiki, toh a sannan ne zannuna maku Girman ubangijina, " . Yarima hilal ya fada yana mai murmushi akaro na biyu . Sarki Gulmanu ya takarkare da wata mahaukaciyar dariya wadda ta hassada karamar girgizan kasa, Saida yayi mai isarsa sannan ya tsuke baki yai shiru ya dubi hilal yace " yo ai wannan ba wani abu bane , dukkanmu sadaukaine , kuma matsafa kasani rintsi ko tsanani wuya ko wahala baza su taba sanyani na nemi taimakonka ba" Yana gama fadin hakan ya tashi ya nufi tantinsa , ***** ********* ******* Washe gari da safe, kowa ya fito ya hallara, toh a sannan ne aljani lumzaru ya fara magana kamar haka" kusani cewa wannan tafiya iya kune zakuyi shi ni zan jira ku anan wajen duk lokacin da kuka samu nasarar karbo gimbiya suraila daga hannun aljani lumzaru toh a sannan ne izan kun tsira da rukanku zaku dawo wannan waje ku iskeni' na rantse da tauraruwa zahlu bazan taba muskutawa daga wannan jeji ba harsai naga dawowarku," . Toh dama tun da suka shigo cikin wannan jeji suka samu itatuwa suka sassaka karamar kwalekwale wanda zasu tsallaka wannan Ruwa da shi, Yanzu kuwa da su ka gama jin wannan zance daga bakin aljani lumzaru sai suka , nufi wajenda kwalekwalemsu take a gabar wannan korama, suna isowa suka shiga cikin wannan kwalekwale sannan suka tuka , basu sha wata wahalaba suka tsallako izuwa dayan barin wannan jeji, toh a sannan ne suka kutsa kai ciki batare da wata shakka ba , Ayya rashin sani yafi dare duhu lallai da su sarki gulmanu sun masifar da zasu tarar a wannan daji na gabatul hayyat toh da sun hakura da wannan bukata tasu sun koma da baya, . Dajine mayalwacin dogayen bishiyu, wayanda ganyayyakinsu . Ya lullube sararin samaniya, sakamakon hakannema dajin yazama tamkar wani stadium din buga wasa, Ga iska mai dadi dake ratsa sassan jikin biladama, Suna cikin tafiyane sai sarauniya lasmin taji kamar kukan wani karamin dabba ta cikin wani sarkakiya, nan da nan batare da fargaba ba ta nufi wannan sarkakiyar ta na isowa bakin sarkakiyar sai tasa kai ciki, toh a sannan ne, taji motsin wucewar wani abu nan da nan tabi wannan abu da kallo koda ta lura da kyau, sai taga ba wani abu bane face irin saiwan bishiyarnan masu lilo tamkar igiya, Nan take hankalinta ya kwanta, . Sarki gulmanu ya dubi hilal yace " nifa na kagu nayi arba da wannan maciya don naimata kisan wulakanci sannan kaima na nuna maka karfin sihirin tsafina," Hilal yace mai "kada kadamu menene na hanzari, komai da kake gani lokacine zai nuna, inma cika baki kake toh duk lokaci zai nuna," Suna kan wannan zance nasu ne sai gabadaya wannan inuwa dake cikin wannan jeji tafara yayewa, take gaba daya bishiyoyin wannan jeji suka fara bushewa, ganyayyakin jikinsu kuwa suka zube kasa, nan take hilal ya bude baki yana ganin ikon Allah, take gaba daya bishiyoyin wannan daji suka bushe tamkar basu taba rayuwa ba, , Wani gurnani ya biyo baya wannan gurnani kuwa yana da amo don harsaida su gulmanu suka toshe kunnuwansu. . Nan take sarauniya lasmin takariso wajenda su gulmanu da hilal suke cikin al'ajabin wannan gurnani da basu san daga inda yake fitowa ba . Wannan gurnani ya sake matsowa toh anan ne sukai arba da abunda ya kusan haukata tunaninsu, . Ba komai bane face wata narkekiyan macijiya mai kawuna biyar , girman wannan macijiyar kuwa zai kai na babban tsauni, tsayinta kuwa yafi kamu dubu, kowane kai dake jikin wannan maciyar yana feso masifane, kai nafarko wani bakin ruwa yake fesowa a duk inda wannan ruwan ya zuba kuwa toh nan take wajen zaiyi rami, mai dan karen zurfi, Kai na biyu kuwa wani mummunan dafi yake fesowa shi wannan dafin iz*n ya zuba ajiki bishiya toh nan take bishiya take , yankwanewa ta kone kurmus . Kai na uku kuwa wuta yake fesowa duk inda wannan wuta ta lasa take abun yake konewa kurmus . Kai na hudu kuwa wani miyau tako dalalar wa a yayin da wannan miyaun ya zuba akasa take zakaga kasa tana soyewa tamkar an saka kullun kosai a cikin tafashashshen mangyada, , Kai na biyar kuwa baya feso koma saidai kuma wannan gurnanin to shine yake yinta, . Koda gulmanu da lasmin sukai arba da wannan maciya sai suka dake su kaki nuna alamun tsorata a tattare dasu shiko hilal Addo'I kawai yake karantowa a cikin zuciyarsa, . Kai na biyar dake jikin wannan maciyar mai gurnani ,yai shiru da gurnanin dayake sannan yafara magana da wata sauti maradadin sauraro kamar haka "Yaku wayannan biladama masu karar kwana, shin baku samu labarin wannan jejin bane da har kukai gangancin shigowa ciki, toh lallai ina sanar daku na rantse da wannan kawuna nawa dayanku bazai fita daga cikin wannan jeji arayeba" . Gulmanu yace" kisani yake wannan bakar macijiya , lallai munji labarinki, asabida hakannema muka shigo wannan jeji don muga bayanki lallai yau bazaki taba tsira ba, " . "Kai gafalalle yi mani shiru kafin na gididdibaka da ranka, lallai kayi sani cewa jarumai masu takama da jarumta, manyan bokaye masu takama da sihirin tsafi,manyan dakarun aljanu masu takama da sadaukantaka sun gagara hallakani daga karshe nine na hallakasu, toh bare kai kuma wani karamin cinnaka wanda nake mai ganin abin kalacina," wannan macijiya ta fadi . Gulmanu yasake dubanta cikin fushi yace" ai dama karamin cinnaka shike sa giwa tika rawa, sannan kuma karaminm sani kukumine" . Duk wannan abin dake wakana hilal da sarauniya lasmin na gefe suna kallo , hannun sarauniya lasmin yana bisa kufen takobinta, . Take wannan macijiyar tayi kara sannan takaiwa gulmanu daya daga cikin kawunanta take wannan kai ya feso wani irin bakin ruwa, cikin zafin nama gulmanu ya goce , sauran kawunan kuwa suka dumfari lasmin ai nan take ta fidda takobinta , ta tunkari wannan kawuna guda hudu yayinda wayannan kawuna sukaita fesomata masifa tana gocewa, abinda yadaure mata kai game da macijiyar shine batajin sara bare suka, wannan maciyar ta shammaci, lasmin ta doketa da jelarta a kirji nan take sarauniya lasmin tai baya yadda kasan anjanyeta ne da kuge, Koda gullmanu yaga haka sai ya kara zage damtse yana saran wannan macijiyar tako ina ajikinta amma yadda kasan yana sarar dutse, toh a sannan ne shima ta sure shi da jelarta ta fyda shi da kasa , gulmanu yaji zafin wannan duka sosai don ji yake ma tamkar, kashin bayansa ne ya karye, cikin zafin nama, ya daka tsalle ya sari wannan mciyar a wuya amma saiyaga nanma baiyi tasiri ba , Kawai sai ya yar da takobinsa sannan ya dunkule hannu ya naushi wannan , macijiya , amma saiyaji tamkar hannunsa zai fita, nan yata gwada karfin sihirinsa da karfin tsafinsa akan wannan macijiya amnma yaki tasiri, itako sarauniya lasmin wacce take akwance a sume yayin data fada bayan wani karyayyen bishiya tsininsa ya soke ta a hannu wanda dalilin zafin data jine har ta some, . Nan da nan wannan macijiya ta hada wa gulmanu ji da majina, sannan ta nanna deshi da kanta, ta zuko dayan kanta da nufin ta gutsire masa kai ta hade ganganjikin, Kwatsam ba zato ba tsammani sai yarima hilal yayi kabbara sannan yadaga takobinsa yasari wannan macijiya take wannan macijiyar tai kara sakamakon wani radadi daya ratsata wanda a dalilin hakannema ta jefar da gulmanu akas, . Nan da nan fa hilal ya cigaba da saran wannan maciya baji ba gani , ita kuma tana kawomai hari da kawunanta cikin ikon Allah yana gwocewa, . Azuciyar wannan macijiyar kuwa cewa take lallai yau na hadu da gamona toh waishinma wane irin biladamane tamkar shaidani, . Hilal kuwa babu abin dake damunsa illa rashin samun lagon wannan maciya nan dananfa wannan maciya tafara gajiyar dashi gajiya tafara kamashi , ya tuna inhar ya debi tsawon lokaci yana wannan gwagwarmayar toh lallai zai iya gajiya , kuma idan ya gaji toh wannan macijiya zata samu nasara akansa kenan . Cikin zafin nama yafara karanto ayoyin alkur'ani a fili, bai dade dafara karan towa ba sai ya tuna da bayanin Aljani lumzaru dayake fadamusu ruhin wannan macjiya a saman kanta yake , . Ai yana tunawa sai wani gagarumin karfi ya zo masa,nan ya daka tsalle ya soke tsakiyar kan wannan macijiyar ta farko nan take yaji tamkar ya soki dutse , ya sake daka tsalle ya soki tsakiyar kan wannan majiyar na biyu nanma tamkar ya soki dutse cikin zafin nama ya dunga soke tsakiyar kawunan macijiyar har yaci sa'a ya soke kanta na biyar, take wannan macijiya tai kara wanda ya haddasa babbar girigizar kasa nan take ta fadi rikica yadda kasan wani babban jirgine ya fado. . . KARSHEN TAKOBIN JINI LITTAFI NA UKU Shekarar:- rubutawa-: 2017 Marubuci:- Shuraih Usman SHIN YARIMA HILAL, SARKI GULMANU SARAUNIYA LASMIN ,ZASU SAMU NASARAR KETARE SAURAN DAZUKAN SU ISA SANSANI ALJANI SHAM'UNA . WANI IRIN GWAGWAR MAYA ZASU SHA . YA LABARIN ALJANI LUMZARU . SHIN WANE NE ZAI MALLAKI TAKOBIN JINI Don jin wannan amsoshi mu hadu a littafi na hudu wanda shine karshe Zai dauki lokaci kafin ya fito. Hakkin mallaka (c) Shuraih Usman Marubuci:- Shuraih Usman Company:- Shuraih 99% An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 4 of 4