Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 4
wasika ta kunsa sai tai umarni da a fille kan wannan manzo da ya kawo wannan wasika , . Koda manzon nan yaga Abin dake shirin faruwa sai yazare takobinsa sannan yadan ja baya kamar taku biyar haka sannan yai wata irin wasa da takobinsa , Nan take wani murgujejen kato daga cikin fadawan mahaifiyata yataso da niyyar yai ma wannan manzo kwaf daya koda bakin bawan ya kaimai sara sai ya tsuguna saran tawuce , . cikin zafin nama manzonnan ya shammaci wannan bakin bawan Aljanin ya fille mai kai. . Haba aikoda sauran fadawa da askarawa sukaga abin daya faru ga dan uwansu sai gabadayansu sukayi kan wannan manzo kowannensu rike da mugun makami . . Karasowarsu kedawuya wannan manzo Ya taresu da sara suka ,woho ho idan da mutum zai ga yadda bil'adama daya kadai ya gagari dubun Aljanu, . Baka ganin komai face jikkunan Aljanu dake yawo a sararin samaniya, Idan bala'I tai bala'I masifa tai masifa toh yan kallo kanshiga tasku mai tsanani, Ai koda sarauniya dubyalu wato mahaifiyata ta fuskanci idan akaje ahaka wannan manzo zai iya karar mata da mayaka, . Cikin kunan rai da zafin murya tace ma dakarunta su tsaya bayan sun tsaya Sai tai dubi izuwa ga wannan manzo ma'abocin rufe fuska,sannan tace yakai wannan manzo kasani kayi mani babbar barna kuma sai ka fanshe wannan barnar dakayi mani , Sannan kuma ka gaya wa sarkinku cewa mu baza mu bar bautar wannan gunkiya ta maciji ba, . ba zamubar tafarkin iyaye da kakanni ba, Kuma kafada masa muma mun shirya mayakin ya tare mu izan yana ganin zai yi nasara . ****** ********** **************** Kasar nurul ansar kasace na musulmai zalla wadda sarki abul abbas yake mulka . Sarki abul abbas Adaline kuma mai jinkan talakawansa . Talakawa na alfahari da shi sannan kuma suna jin dadin mulkinsa don yana kwatar musu yancinsu daga hannun azzaluman attajirai . Babu abinda ya tsana kamar zalunci da azzalumai Burinsa shine kaf duniya su kasance musulmai baki daya . Jarimin gaskene don acikin tarihinsa ba asamu wanda yayi galaba akansa ba Har iwannan zamani . Yana da 'da guda daya wanda ake kira da yarima hilal . Kyakkyawa ne wanda ma a ranar da'aka haifesa sai da mutane suka ringa tururuwan zuwa ganinsa daga kauyuka da sauran kasashen nahiyar baki daya . Mata kuwa binsa suke suna kokarin cusa kansu gareshi amma shi basu bane a gabansa ba . ********* *********** ********* Koda wannan manzo da sarki ya aika kasar sarauniya dubyalu. Yadawo ya zaiyane ma sarki abin daya wakana . Nan take sarki ya harzuka yace ma sarkin yakinsa maisuna lamiru . "Ya kai lamiru ina son gobe inga tawagar da zamuje mu rusa birnin kafirannan . Lamiru yace' angama ranka shi dade . Washe gari runduna ta hadu iya haduwa aka buga kugen yaki Sannan aka tasamma garin iblisha garin da sarauniya dubyalu ke mulki ....... Sarauniya dubyalu ta dade da samun labarin tashin su sarki abul abbas . Nan itama ta hada nata rundunar suka nufi filin daga ••••••••••••••• /TAKobin jini . Book 2 . Part 2 Marubucin Littafin Shuraih Usman . Isowar su sarki abul abbas filin daga keda wuya sai suka tarar da mahaifiyata wato sarauniya dubyalu da dakarunta na aljanu . . Su dai rundunar su sarki abul abbas dakarunsu sun kai milyan biyu . Abul abbas ne agaba sai sarkin yaki agefen hagunsa yayin da yarima hilal yake gefen damansa . Yarima hilal shima zartone kuma jarumi don shi kadai yana iya fada da mutane sama da dari sannan ya karsu . . Mu kuma rundunar mu wato rundunar mahaifiyata sarauniya dubyalu Yawan adadinmu ya ninka na su abul abbas sau uku amma wannan bai tsorata su ba . . A lokacin da'aka kacame da masifaffen yaki duk ina kallon abin dake faruwa ta hanyar wani madubin tsafi . Yayin danaga yarima hilal yana yi mana mummunar barna sai na shiga tura masa da wasu guma gumai na wuta Koda wayannen guma gumai suka zo daf da shi sai naga ya fadi wata kalma nan take wannan guma gumai suka juyo izuwa kan dakarunmu suka ringa kashesu . Koda nai duba izuwa ban garen sarki abul abbs sai naga yana tai mana barna domin duk inda ya dosa sai de kaga gabobin aljanu na yawo a sararin samniya . Yayinda mahaifiyata dubyalu keta barna cikin dakarun su abul abbas sai aka samu wani barde mai zafin nama ya sari dokinta nan take ta fado daga kan dokin hade dayin wata wuntsilawa wanda kafin takai kasane ta rarumi mutane biyar sannan tai kasa da su nan ko shurawa ba suyi ba .$ Yarima hilal ya lura da irin barnar da dubyalu ke musu $ Wannan tasa ya dumfareta koda ya rage baifi saura taku isshirin ya kariso wajen da take ba sai ya falfala da wata azababben gudu sai da ya kusa zuwa inda take ne sai yayi wata tsalle yai sama yayin dayake dawowa izuwa kasane yasa kafa ya doki kirjin dubyalu . Nan take ta furzar da wani gudan jini daga bakinta sannan itama ta falfala da gudu ta nufe shi da takobinta wanda ya rine da jinin bil adama $ . Haduwarsu keda wuya ta kaimai wani sara da nufin ta fille masa kai amma cikin zafin nama ya tsuguna wannan sara ta wuce ta saman kansa . Ko juyowa bai gama yiba dubyalu takara kai mai wani saran ta gefen cikinsa nan ya kare saran da takobinsa nan tartsatsin wuta ya fallatsa . Shima hilal sai ya kaimata wani naushi da nufin ya zubar mata da hakori baki dayansu amma koda ya naushetan sai yaji tamkar ya naushi dutse Yayin da dubyalu taga haka sai ta kyalkyale da wata mahaukaciyar dariya sannan tace$ . Kasani yakai wannan jarumi kayi babbar kuskure wadda sai kayi dana sanin yinta yayin da danasin bazai amfaneka da komai ba . Kasani yau zan dandana maka dacin mutuwa wanda ban taba yiwa wani bil adama ba$ . Koda jin haka sai hilal yace yake wacennan sarauniya wadda take cikin bata , ina yimaki kashedi na karshe da ki bar wannan Addini na shirka da kike ki dawo ga tafarkin gaskiya tafarkin Annabi Ibrahim AS Izan kuma ki ka bijire wato kikaki toh lallai zan hallakaki halaka mai muni . Dubyalu najin haka sai ta fusata ainun sannan ta daka wani tsalle tai sama yayin datake saukowa ne ta kai ma hilal sara cikin zafin nama da gwaninta ya goce na saran sannan shima ya kai mata nashi . Sai da suka shafe kimanin sa'a biyu suna dauki badadi sannan hankalin dubyalu ya tashi ta tuna cewa ita fa basadaukiyace acikin aljanu ta gagari sarakunan aljanu da dama amma wannan karamin bil'adaman naso ya bata mata lokaci Aikoda tagama ayyana hakan aranta sai tayi wani tsalle sannan ta kaima hilal sara acinya da nufin ta fille cinyra gaba daya cikin zafin nama yatare wannan saran amma sabida karfin saran saida ta yankkesa a gefen cinya nan ya kwala ihu Koda dubyalu taga haka sai tayi dariyar mugunta sannan tayi kansa da nufin ta hallakashi wani wawan sara ta kaimai takai cikin zafin nama taga anyi sama da shi sannan wannan saran data kau an tare sa da wani irin takobi nan take wata tartsatsin wiyta ta bayyana . Sarki abul abbas ne ya baiyana yana mai rike da wata takobi da kuma garkuwa . Nan take sarki abul abbas ya fiddo wata yar batta sannan ya karanta wasu addu'oi sannan ya bude battar aiko yana bude battar sai mahaifiyata dubyalu ta ji tamkar ana fizgota da wani irin kuqiya nan take ta ringa rikedewa izuwa hayaki tana shiga cikin wannan battar$$ . Tana gama shiga sarki ya like bakin battar sannan ya bada umarnin akai yarima can tanti amai maganin wannan rauni da sarauniya dubyalu ta mai . Ta wannan hanyarne aka cimu yaki sannan aka kama mahaifiyata aka kulleta acikin wani kurkukun kasan kasa cikin wani akwati . . . Nan take suraila ta rude ta rasa yadda zatayi amma haka dai tai dauriya ta kara tambayasa " To ni kuma mai na maka da har kakeson ka hukun tani. . Yayin da aljani sham'una yaji wannan kalami nata sai ya bata rai yaringa huci wani bakin hayaki na fita daga bakinsa . Yace da'ita" ki sani cewa na kai tsawon watanni goma ina jiran zuwanki . Don tsafina ya tabbatar min kece kawai zaki iya taimakamin na samu abin da nake nima . Ki sani cewa yayin da sarki abul abbas ya kama mahaifiyata na shiga tsananin kunci da bakin ciki. . Nayi ta neman hanyar da zan ci galaba akan sarki abul abbas amma bansamu ba sai da na shiga halwar tsafina nayi bincike na tswon wata biyar sannan na gano wata hanya . . "Bazan taba cin galaba akan sarki abul abbas ba sai na mallaki TAKOBIN JINI Wanda ayanzu haka yana can cikin kogon sha jini. . . Binciken tsafina ya nuna min in harde mna mallaki takobin jini toh duk duniya Babu wanda zai ci galaba akaina ki sani zan mulki duniya gaba dayanta kowani mtum a duniyar nan zai dawo karkashina . " . . Sannan yakara da cewa" banason wani tambya dga bakinki" yana gama fadin haka sai ya sureta suka luluka sama . . . Wannan shine al'amarin daya afku ga suraila matan marigayi sarki ashbir . ¤¤¤¤¤¤¤¤. ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤. ¤¤¤¤¤¤ . . Al'amarin gulmanu kuwa ya wakilta wazirinsa dariku akan yaje kasar dimashka don ya nemo mai auren sarauniya lasmin. . Duk da waziri dariku yasan masifar dake cikin wannan tafiya haka ya daure yabi umarnin sarki don ya zauna lafya. . Washe gari da safiya ya hada dakaru mutum dari sannan ya fice daga birinin ashdamir . . Yayi tafiya mai tsawon gaske tafiya ta kwana ashirin ba yada zango , Sannan suka iso binin dimashka isowarsu keda wuya suka yada zango abayan birnin sakamakon lokacin darene Baccin sun yada zango kenan sun huta sannan suka kafa tanti kowa yafara shirin bacci . . Wayanda aka barsu suyi gadi suna cikin gadi sai suka ga gari yai duhu sosai hasken farin watan dake haskaka wajen ya dushe . Can sai suka ga wasu dakaru manya manya in ka gansu ka rantse samudawa ne. . Koda isowar wayannan dakaru sai shugaban su yai wata irin kara wadda tasa su waziri dake barci suka farka a gigice. . . Waziri ya fito daga cikin tantinsa Koda yayi arba da wayannan dakaru sai wata matsananciyar tsoro ta baiyana a fuskarsa karara . . Shugaban wayannan dakaru masu kama da samudawa yace ma waziri " Ya kai wannan bawa makaskanci mai ya rudi zuciyanka har kazo yankinmu . Toh kasani kayi babban kuskure a rayuwarka wadda sai kayi dana sanin yinta yayin da dana sanin bazai amfanekaba . . Shin meya kawoka wannan yanki Badakaren ya tambayi waziri cikin daka masa tsawa . Waziri baki na rawa yace "Sar-kin-n kas-ar ashda- a.mir ne ya" Kai kayi magana man katsaya sai in ina kake min .badakaren yasake daka matsa tsawa akaro nabiyu . . Sannan yace koma waye ya aiko ka in kaje gaban sarauniya ai kayi bayani , Nan wayannan jibga jibgan dakarun suka kame gabadaya dakarun waziri dashi kansa . Suka tasa keyarsu izuwa cikin birnin TAKOBIN JINI . Book 2 Part 3 Marubucin Littafin Shuraih Usman . . Yayin da suka isa dasu cikin birini dimashka basu wuce ko ina dasu ba sai wani katon gida da alama dAi Duk mai waNnan gidan to dan shan iska ya ginashi$ . . Gidan baya da fasali da ga waje amma in kashigo ciki to anan ne zaka ganema idanuwanka ababen al'ajabi . Bakaramin gida bane Acikin wani daki ne aka sauke waziri sauran dakarun kuwa suma wani dakinne akayi dasu . Wannan shugaban dakarun yace ma waziri gobe zamu gurfanar daku agaban sarauniya duk hukuncin data yanke gareku deade yake . . Hantar waziri taa kada yayin daya yi dana sanin zuwansa . Da gaei ya waye aka fiffito fada Wannan shugaban dakarun yazo daf da kunnen sarauniya lasmin ya fada mata wani magana . . Sarauniya lasmin itace ke mulkar birnin dimashka Ta gaji mulkine a wajen kawunta sarki hutmus . Ta kasance tana lullube fusakarta da wani mayafi duk lokacin da zata fito fada hakan yasa bakowani mutum bane yasan fuskarta . . Koda taji wannan magana sai tace " Yakai hibru maza jeka kazo min dasu wayannan bakin . . Wannan garjejen katon shugaban rundunar wadda sarauniya ta kirashi da hibru ya tashi ya fice daga fadar . Can bayan wasu dakikoki sai hibru tafe da waziri dariku Sai muzurai yake . Koda suka iso fadar sarauniya lasmin anan zuciyarsa ta kusan tsayawa domin kuwa ko ba'afada ba ruwa ba sa'an kwando bane . Tun da waziri dariku yake a duniya bai taba ganin wata fada wadda takai na birinin haduwa ba Domin ita wannan fada dabenta anyi sane da zubarjade . Yayin da akayi wata karaga ta zinari wadda aka mata ado da yakutu ajikin karagar wasu zane ne na takubba wanda adadinsu yakai asihirin . Azaune akan karagar ba kowa bace face sarauniya lasmin . Da wannan lullubi a fuskarta . Sannan tace ma waziri "Yakai wannan bako mene ne dalilin dayasa kashigo nahiyata batere da iznina . Nan waziri yai sauri ya zaro wata wasika Ya mika ma wani bafaje . Koda bafajen ya karba sai ya mikata izuwa hannun magatakarda Magatakarda yasoma karantawa " Sako daga sarkin sarakai sarkin duniya Wato sarki gulmanu mai mulkin kasar ashdamir. Izuwa ga kyakyawa kuma sarauniyar kyawawa kisani tunda na naga wannan fuskar taki dakike rowanta naji duk duniya babu wacce nake muradin ta xama mata in bake ba . Ga waziri na nan shizai. Wakilce ni adaura sannan sai ku taho kasata tare dashi . Sako daga mai duniya . . Koda maga takarda yakawo karshen wasikar sai sarauniya lasmin tai wuf cikin zafin nama ta zare wani takobi sannan ta kaima waziri dariku sara Sai da yarage bai wuce taki daya ba ta guntule kan waziri sai tsayar da takobin dedai wuyansa. . Waziri kuwa ya riga daya sallama jira kawai yake yaji saukar takobin amma sai yaji shiru . . Koda ya bude idonsa sai yaga abin daya firgitashi . Kyakyawar fuskar Sarauniya lasmince yai maraba ma idaunawansa . Dukda tana cikin bacin raine amma ya tabbata kafin asamu kyakyawa kamar ta sai antona . . Farace siririya wadda fuskarta shima yake madaidaici takasance ita ba doguwa ba kuma ba gajeruwba . Fararen idanuwanta masu sheki wayanda on mutun bai lura ba sai yace bata da bakin ido . . "Kayisani yakai wannan dan sako ni nafi karfin sarkin ka Sannan kaje kafada mai cewa nace in yaki yake ji toh TAKOBIN JINi . Book 2 Part 4 ¤¤¤¤¤ Marubuci Littafin Shuraih Usman . Sannan kafada mai kar yaga ya kashe sarki ashbir ya zata cewa nima irinsa ce Ni dabance acikin sarauniya . . Nice mai mulkar dimashka gabaki dayanta shine zaice in auresa . Wannan ma ai zancen banza ne . Nan take sarauniya lasmin tasa aka kame gabadaya dakarun waziri dariku su darin . Ta antaya su cikin kurkuku sannan tacema waziri dariku . Kayisani cewa wannan jan kunnene agareka da kima sarkinka . . . ¤¤¤¤¤¤¤¤¤. ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤ ¤¤¤¤¤¤¤¤ . Gulmanu yana zaune akan karagarsa ta mulki . Ana ta fadanci, ya harde sai annushwa yake , . Sai gani akai waziri ya dumfaro aguje kan doki sai sukuwa yake Yana isowa gaban sarki gulmanu ya tsai da dokin sannan ya sauko yai gaisuwa . Farin cikin dake fuskar gulmanu ta canja izuwa ba cin rai sakamakon ganin wazirinsa yadawo babu dakarun daya deba sannan babu sarauniya lasmin . Yadaka ma waziri tsawa cikin hasala "Yakai wazirina shin meya faru gareka naga duk ka fita daga hayyacinka " Nan waziri ya bayyanawa sarki gulmanu duk abinda yafaru . . Ai ko karisawa baiyiba sarki gulmanu ya karfi takobi ya saremai yan yatsu guda biyu . Sannan yai jifa da takobin yaringa dukan fadawansa naushi yarin ga yi musu harsanda wasu daga cikinsu suka mace . Sannan wani wuta yafara bullowa ta gaban waziri wanda tunda aka yanke mai yantsu yake sume haryanzu bai warke ba . Koda wannan wuta tafara fitowa tanata yaduwa har ta taba waziri dariku Nan take yatsunsa da sarki gulmanu ya guntule suka dawo . Sai gani akayi boka balbalin bala'I ya bayyana hannunsa rike da wata al'amudi na zinari . Koda gulmanu yai arba da boka balbalin bala'I nan take yadawo cikin hankalinsa sannan yazo ya zauna akan karagarsa . . Boka balbalin bala'I na ganin haka sai ya. Dubi sarki gulmanu sannan yace mai ka sani yakai gulmanu baza kataba yin nasara akan sarauniya lasmin ba haka itama baza ta taba yin nasara akanka ba . In har kanason kayi nasara akanta to ya zame ma dole kanemi TAKOBIN JINI Inhar ka mallaki takobin jini to tabbas zaka mulki duniya gabaki dayanta . Kowa a duniya zai dawo karkashin mulkinka , " Aina zan samu takobin jinin" Gulmanu ya tambaya cikin fushi Nan boka balbalin bala'I ya barke da wata dariya wadda shikansa gulmanu sai da razana . "Yanzu haka takobin jini yana can a kogon shajini" Boka balbalin bala'I yafda sannan yakara da cewa gobe zan baka labarin TAKOBIN JINI da yadda za'ai ka mallaketa . ¤¤¤¤¤¤¤. ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤ ¤¤¤¤¤¤¤¤ Al'amarin sarauniya lasmin kuwa da dare ya raba sai ta sudade ta fita daga gidan sarauta sannan ta yanki daji taita gudu akan doki . Sannan takai bakin wani dutse sai ta fadi wasu kalamai wadda ita kadai tasan ma'anarsu . Rufe bakinta keda wuya sai wannan dutsen dake gabanta ya tsage sannan ya rabu bari biyu bari daya yai gefen dama dayan barin kuma yai gefen hagu . Wani tsohone tukuf dashi gashin kansa yai tuntu Sannan kasumbarsa ta rufe mai baki gabadaya fuskarsa ba kyan gani . Yana sanye da riga falmara na fatan bauna . Sai wani wando data tsaya mai dedai kauri Wannan tsoho ya bude idanuwansa Sannan yace maraba da zuwa yake sarauniyar duniya . Nasan abinda ke tafe dake . TAKOBIN JINi . Book 2 . Marubucin Littafin Shuraih Usman Part 5⃣ . Marubucin littafin Shuraih Usman Wannan tsohon yaci gaba dacewa "ina son kisan wani abu yake sarauniyar duniya kada ki tari yaki da sarki gulmanu . Don bazaki yi nasara akansa ba . Haka shima bazai yi nasara akanki ba sannan kisani shima yana da dakaru kimanin yadda kike dasu ga shi babban gwarzone wanda yake dakama maza gumb........ . "Nima ai basadaukiyace kuma jaruma don haka babu abin da zai hanani in yakeshi .ta katse shi dafadin hakan "Kayisani yakai boka kamsusul lajani babu wani mahalukin dayake duniyarnan wanda bai da lago . Shima haka zata kasance agareshi kuma sai kasheshi da wannan hannun nawa . . Boka kamsusul lajani yace tabbas zaki iya kashe sa . Kisani yanzu aduk duniyarnan babu wata makami daza kiyi amfani da ita wajen ganin bayan sarki gulmanu face TAKOBIN JINI . "Menene kuma takobin jini" Sarauniya lasmin ta tambaya cikin matukar mamaki . Tabbas zan sanar dake labarin takobin jini . Da kuma wajen da zakije ki daukoshi Sannan da irin hadarurrukan daza ki shiga kafin kikai ga mallakar wannan takobi . Kisani anyi jarumai,bokaye ,da aljanu mutane ,wayanda suke son mallakar takobin jini amma duk sun rasa rayukansu garin fafutukar mallakarsa . Ayanxu dai takobin jini ya can wani kogo wanda ake kira da kogon shajini . Izan tauraruwa zahlu ta yarje maki gobe sai kizo in sanar dake labarin takobin jini da kuma hanyar daza kibi ki mallakeshi . . ¤¤¤¤¤¤¤¤. ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤. ¤¤¤¤¤¤¤¤ Sarki abul abbas kuwa tunda suka yaki birnin aljanun sarauniya dubyalu suka ci galaba akansu . Suka dawo cikin birnin nurul ansar hade da ganima mai tarin yawa . Bayan wasu yan kwanaki yarima hilal yana cikin barci sai yayi mafarki " Yana cikin tafiya acikin wata daji mai sarkakiya Sai yaringa jin ihun mace tana neman taimako koda ya kariso wajen Nan take yai arba da kyakyawan fuskarta masu matar da dukkan gabban jikin dan adam . . Tana ganinsa sai ta yi wuf ta rungemeshi tana cewa ka taimakeni kataimakeni yatsanta nanuni da wani waje daban . Koda yarima hilal ya lura da kyau sai yaga ashe wata babbar macijiyace wadda tsabar girmanta zata iya hade mutani dari alokaci daya . Wannan macijiyar takasance kanta na wani mummunar aljani ne yayin da gabban jikinta na macijiyace . Nan take yarima hilal ya fiddo takobinsa sannan yafara addu'a yana neman tsari . Aiko nan take wannan macijiyar ta bace kamar bata taba wanzuwa a wajen ba . . Firgigit ya farka daga barcin sannan yai addu'a . Abin ya tsaya mai arai ya ringa tuno fuskar ta wanda bazai taba goguwa a cikin kwakkwalwarsa ba . Ya kishingida akan lallausar katifar dayake kwance akai . Ya runtse idanuwansa. Amma ina daya runtse idanun baya ganin komai sai fuskarta mai alamar tsorata karara . . Shin wacece ita To be con TAKOBIN JINI . Book 2 Part 6⃣ Marubucin littafin:- Shuraih Usman . Nan fa nan fa hankalin yarima hilal tai matukar tashi ya . . Har asubah bai samu ya runtsa ba Haka yaje masallaci yabi jam'i Bayan yadawo daga masallacinne wata nannauyan bacci tai awon gaba dashi . Sarki abul abbas bisa kan karagar mulkinsa ya harde sai annashwa yake halama dai yau yana cikin farin ciki . Koda sauran fadawa da hakimai suka haka suma sai wannan farin cikin ta bayyana a fuskarsu . Ba komai bane yasanya su farin ciki ba illa tunda ga ranar da matan sarki abul abbas ta rasu Duk wata walwala da annashwa suka kaura ga fuskar sarki abul abbas Amma abin al'ajabi sai gashi yau sarkine yake cikin walwala wanda takasa boyuwa , Koda ganin haka sai sarki abul abbas yace ma waziri "Yakai waziri kayi sani yau ina cikin wani yanayi na farin ciki wanda ban taba tsintar kaina aciki ba, " . Waziri yace "Ranka shidadea nima kaina na fahimci wannan yanayi dake fuskarka ayau dinnan da alama wani babban al'amarine ke shirin faruwa . Sarki yace"Tabbas maganarka haka take wani Al'amarine ke shirin faruwa kuma wannan Al'amari ina murna da farin ciki da zuwansa domin shine Abin dana ke fata kafin Allah (SWT) yadauki raina na ganshi da Idona . Koda waziri yaji wannan zance daga bakin sarki abul abbas sai fuskarsa ta fadada da murmushi sannan yace"nima ina farin ciki da faruwan wannan Al'amari" . Yayin da yarima hilal ya farka daga barci sai ya tsinci kansa yana mai begen wannan kyakkyawar fuskar daya ganta cikin mafarki . Lokacin daya iso fadar sai ya zauna akan tasa karagar sannan ya dubi mahaifinsa yace mai "ya Abbana ina son nayi magana dakai" . Koda jin hakan sai sarki ya mike yashiga cikin gidan sarauta yayin da yarima hilal ke biye dashi " Wani hadadden lambu mai furanni tako ina yayin da dabbobi keta yawa tawansu aciki . "Yakai dana shin menene ke tafe da kai" Sarki abul abbas yafada yayin dayake duban yarima hilal . "Abbana kasani jiya nayi wani mafarki acikin mafarkin nawane naga wata kyakkyawar sura tana neman taimako na , Abba kasani na kamu dason wannan sura " Hilal yafada yayin dakansa ke asunkuye . Nan take sarki abul abbas yafashe dawata mahaukaciyar dariya sannan yadafa kafadan hilal yacemai" yakai dana ni na yarje maka akan wannan yarinya kaje ka nemota duk inda take Sannan kuma zan taimaka adaren yau zanyi istihara ingani ko wannan yarinya matarka ce Da kuma inda take . Nan take yarima hilal ya rungume mahaifinsa yana mai murmushin farin ciki *********** *********** ********* Koda safiya tayi aka taru afada sarki gulmanu sai huci yake kamar mayunwacin zakin daya fito farauta . Ayayin da fadawa da sauran hadimai ko wa yashiga taitayinsa domin sun san ayadda gulmanu yakennan zai iya kashe daya daga cikinsu batare da sun aikata wani laifi ba . Gaba dayan fadan ta ringa girgiza wani sauti na fita ,sautin irin karar rugujewar duwatsu nan danan hadimai da fadawa suka hankalinsu ya tashi . Kamar walkiya sai ganin boka balbalin bala'I akayi ya bayyana Kamar kowani lokaci ya na sanye da jememmen rigar fatar damisa sai wani warki tare da kashin kan bil adama a rataye a wuyarsa . Koda ganinsa take sarki gulmanu ya gabato gabansa sannan yace masa "Sannu da karisowa yakai bokan duniya gaba daya kayisani kai nake tsumaye tuntuni ,ka labarta min labarin TAKOBIN JINI . Boka balbalin bala'I yadubi gulmanu sannan ya bushe da dariya mai amon gaske sai da yayi mai isarsa sannan yace mai "Zahlu tabaka nasara kayisani yanzu zan labarta maka labarin TAKOBIN JINI . . . KASANCE TARE DANI Takobin jini . Book 2 . Marubucin Littafin Shuraih usman Part 7⃣ . . Boka balbalin bala'I yaci gaba da cewa Kayisani yakai gulmanu TARIHIN TAKOBIN JINI Anyi wani hatsabibi kuma jarimin gaske shekaru dubu shida da suka wuce shi wannan hatsabibin jarumin ya kasance bokane sunansa MURAISU Muraisu ya gagari duk wasu jarumai da bokayen nahiyarsu Muraisu na iya yaki da dakaru dubu sannan kuma ya kashe su dukkaninsu batare da ya nuna alamun gajiya ba . Muraisu yana da wata kanwa tasa dayake matukar sonta wadda itakuma ko kadan bata son halayensa hakan nema tasa ta tafi ta barshi taje can nisa dashi tayi aure . Duk da cewa muraisu ya binciko inda take acikin madubin tsafinsa hakan baisa yaje gareta ba . Sabida kafin ta tafi ta gargadeshi da kada ya tafi nemanta . To ayayin da muraisu yaga tsufa tazo masa sannan wannan tarin kundin ilimin tsafinsa izan har ya bari wani ya mallakeshi bayansa toh yana iya zama gagara badau a bayan kasa baki daya wannan tasa ya sana'anta wani takobi wanda har takaishi tsawon shekaru biyu sannan ya kammala ta , Wannan takobin takasance marikinta na jauharine yayin da jikinta gabadaya anyisane da lu'u lu'u sannan aka gauraya da Jini wannan shiyasa jikin takobin gaba dayanta launin jaa ce . Yayin da muraisu ya sana'anta wannan takobi sai yasa wasu dakaru Dubu dari na Aljanu su tsareta sannan ya dauki takobin yakaita Kokogon sha jini Ita wacannan takobi na muraisu yayin da mutun ya mallaketa toh baza ka taba cin nasara akansaba sannan kuma wannan ma mallakintan zai mulki duniya gaba dayanta sabida karfin sihirin dake tattare da takobin sannan kuma manyan sarakunan Aljanu har su biyar na ma wannan takobin bauta duk ma mallakin wannan takobin to zasu kasance masu biyayya agareshi . Kasani yakai gulmanu babu wani mahaluki a duniya daya taba shiga kogon shajini sannan ya fito araye Domin ita wannan kogo ta kasance matattara ce ta masifu dubu ' Kai kodama kayi nasarar shiga cikin kogon to baza ka iya daukar wannan takobi ba Koda duk mutanen duniyarnan zasu taru bazasu iya daukar taba domin tana cike da wasu manyan sihiri . Muddin kanason ka mallaki Takobin jini

Chapter 2 of 4