Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 4
ya zamo wajibi agareka sai ka sanya wata zoben wuta a yatsan hannunka na hagu .ita zoben wuta jarumi kuma boka muraisu ne ya sana'an tata kasani batare da zoben wuta ba Bazaka mallaki takobin jini ba har abada Zoben wuta tana can dajin Hajrul ma'ut a saman wata bishiya kasani babu wani mahaluki daya isa ya shiga dajin hajrul maut sannan yafito araye domin wannan dajin masana sunyi ittifaqin cewa gaba daya dajin dunya babu wata dajin da ta kai ta hatsari . Sannan ko kayi nasarar shiga dajin hajrul ma'ut kasani bazaka taba ganin wannan zoben ba ballan tana ma ka daukota . Ita wannan zoben muraisu ya sana'anta tane da jininsa kasani izan ba wani wanda yakasance jininsa bane Toh lallai babu wanda ya isa ya ma iya ganin wannan zoben barema har ya daukota . Sannan ire iren muraisu wato danginsa sun dade da shafewa daga doron kasa A cikinsu mutun dayace tayi saura kuma ba kowa ba ce illa GIMBIYA SURAILA matar sarki ashbir . Kasani nayi bincike a cikin halwar tsafina na gano tana nan araye amma saide tana tare da wani hatsabibin aljani mai suna sham'una wanda shima burinsa knan ya mallaki wannan takobi na muraisu . . Ku sance tare dani TAKObin jini . Book 2 . Marubucin Littafin Shuraih usman Part 8 . Kasani nayi bincike a cikin halwar tsafina na gano tana nan araye amma saide tana tare da wani hatsabibin aljani mai suna sham'una wanda shima burinsa knan ya mallaki wannan takobi na muraisu . Sannan muddin bamu gaggauta karbar suraila a hannunsa ba to tabbas zai iya ratsawa har cikin dajin hajrul ma'ut ya dauko zoben wuta sannan ya nufi kogin shajini ya daoko takobin jini . Izan har Aljani sham'una ya mallaki takobin jini to tabbas duniya zata kasance a karkashinsa sannan burinka na zama sarkin sarakai na duniya bazai tabbata ba. ,nan take gulmanu ya harzuka matuka gaya sannan yadubi boka balbalin bala'I yace mai "Toh yanzu me ne ne mafita Koda jin haka sai boka yai wata guntuwar murmushi sannan yace ma gulmanu . Kasani duk fadin duniyar nan babu wani mahaluki daya isa ya hallaka sham'una har ya karbo gimbiya suraila a hannunsa . Wani sadauki ma'abocin wata bakuwar Addini wanda yanxu haka wannan bakuwar Addinin ta fara bazuwa a sassan duniya baki daya . Shi wannan sadauki ba kowa bane face Yarima hilal da ga sarki Abul abbas mai mulkin birnin nurul ansar . Kasani yarima hilal yafada soyayya da gimbiya suraila ta dalilin hakan ne zai fita nemarta Awannan fitar dayayine zaku hadu dashi sannan ku labar tamasa inda gimbiya suraila take . Yayin daya ceto gimbiya daga hannun Aljani sham'una sai ku san yadda zakuyi ku shammace shi ku kashe shi sannan ku tafi da gimbiya zuwa dajin hajrul mau't inda zata dauko maku zoben wuta . Kasani wannan aiki bazai taba yi wuwa ba face kun hada karfi da karfe kai da saruniya lasmin mai mulkar birnin dimashka . Sannan kafin ku isa dajin hajrul mau't akwai wasu masifu guda uku wa yanda da zarar kun sallakesu araye toh tabbas zaku isa wannan dajin . Rufe bakin boka bal balin bala'I keda wuya Gulmanu yabama sarkin yakinsa umarni daya debi dakaru dubu sannan yasa magatakarda ya rubuta wasika . Gama rubuta wasikar keda wuya sarki gulmanu ya buga hatiminsa sannan ya mika ma sarkin yakinsa mai suna kumar Yace mai "Ku tafi izuwa birnin dimashka sannan ku mikawa sarauniya lasmin wasikar " . . Sarkin yaki kumar ya dukad da kansa kasa sannan yace angama ya mai duniya" . Koda kumar ya mike sai ya haye saman dokinsa ya falfala da gudu sannan wasu dakaru suka bishi abaya " Wannnan shine abin daya faru a fadan sarki gulmanu ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤. ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤. ¤¤¤¤¤¤ Sarauniya lasmin ce kan wata bakar doki yayin da dakru wajen dari ke biye da ita Nan suka ja tunga daidae wajen wani katon dutse sannan sarauniya lasmin ta sauko daga saman dokin ta nufi wannan dutsen tana zuwa bakin dutsen sai ta furta wasu dalasimai na tsafi nan take ta bace bat . Bata bayyan ako'inaba sai acikin kogon da boka kamsusul lajani yake . Nan kuwa tai arba dashi zaune akan wata mashimfidi na fatar giwa. . Ta budi baki zatai magana keanan sai boka kamsusul lajani yai mata ishara da tai shiru . Sannan yace mata barka da zuwa yake sarauniyar duniya baki dayanta . Lallai zan sanar dake labarin Takobin jini . Yafara bata labrin muraisu da yadda akai ya sana'anta takobin da kuma inda ya ajjeta sannan yakra da cewa shi wannan takobi bazai daukuba sai da zoben wuta , Nan ya labarta mata wajen da zoben wuta yake ajiye sannan hade da fada mata sirrin wannan zoben babu wanda ya isa ya dauko shi face wani tsatso na muraisu sannan kuma wannan jini nasa yanxu dayace kacal ta rage a duniya . Nan ya labarta mata labarin gimbiya suraila Koda sarauniya lasmin ta saurari wannan labari sai ta nisa sannan tace toh yanxu me nene mafita . Babu wani mahaluki. Daya zai iya hallaka Aljani sham'una sannan ya ceto suraila face yarima hilal . Sannan baza ki damar ganin yarima hilal ba face kin hada kai da sarki gulmanu , Wannan bukata taki baza ta taba samuwa ba face kun hada karfi da karfe , Sannan boka kamsusul lajani Yakara dacewa yanxu haka gulmanu ya turo da sarkin yakinsa tare da wasika a gareki yana fadin hakan sai ya shafi wata dutse Shafar wannan dutsen keda wuya sai ga sarkin yaki kumru tare da dakarunsa sun bayyana ajikin wannan dutsen sai tsala gudu suke cikin jeji . . ¤¤ END OF BOOK 2 ¤ SHIN SARAUNIYA LASMIN ZATA YARDA TA HADA KAI DA GULMANU . SHIN MEKE KUNSHE CIKIN WASIKAR DA GULMANU YA AIKA . YAYA LABARIN ALJANI SHAM'UNA TARE DA SURAILA . WACECE WANNAN DA YARIMA HILAL YaYI MAFARKINTA . SHIN A CIKINSU WAYE ZAI MALLAKI TAKOBIN JINI . . DOMIN JIN WAYANNAN AMSOSHIN MU hADU A TAKOBIN JINI lITTAFI NA UKU . . MARUBUCI:- Shuraih Usman . . SHEKARAR RUBUTAWA:- 2017 TAKOBIN JINI 3 COMPLET TAKOBIN JIN 3!!! Littafina uku (3) Littafin Shuraih Usman Part 1 . . Sarkin yaki Kumru suka iso birnin dimashka ,masu tsaron kofar garin na hangosu suka bude musu kofa . Abin daya ba ma su sarkin yaki kumru mamaki kenan har sun fara shirin yaki , Koda suka isa cikin birnin dimashka sai wani bafaje yazo garesu Sannan yace musu" Sannunku da zuwa yaku jama'ar birini ashdamir kusani sarauniya lasmin ce ta aikoni izuwa shugabanku " Kumru najin haka Sai ya budi baki yace" yakai wannan dan aike kasani mu ba da yaki muka nufo birnin ku ba sako ne zamu isar zuwa ga sarauniyarku. Nan wannan dan aike yajasu yakaisu masauki . Babban gidane ainun sannan gidan ya kawatu Dagani kasan irin wannan gidajen dama anyisune musamman dan karban baki. Yayin da su kumru suka shiga gidan sai suka bude bako galala suna ta kalle kalle kamar wasu yan kauye, Gidan ya tsaru matuka gaya domin gidan kusurwa kusurwa ne sannan ga wani faffadan kilishi wanda yake barazanar hadiye kafafuwansu . Bayan kowa ya samu waje ya huta sai aka shigo masu da abinci Bakomai bane illa Gurasa da farfesun dawisu sai kuma wasu tambulan kayan shaye shaye wanda wasu ke kunshe da ruwa wasu kam barasa da dai sauransu. . Nan sukaci suka sha sannan sukayi hani'an Wannan bafajen ya iso gaban kumru sannan yace dashi ku kwanta ku huta zuwa gobe sarauniya zata yi magana da kai , Sannan ya fice ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤. ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤. ¤¤¤¤¤ . Sadauki yarima hilal tunda sassafe yazo fada sannan ya haye kan karagar mahaifinsa ya harde sai wani annashwa yake . Yayin da kowa idan yazo fadar sai ya kwashi gaisuwa Sannan ya nemi waje ya zauna . Tunda ga nisa Abul abbas ya hangi dansa akan karagar mulkinsa sai shima wata farin ciki ta cikashi wai yau ga dansa kan karagar mulkinsa , Koda ya Iso wajen sai kowa ya tashi ya kwashi gaisuwa , Yarima hilal ya mike tsaye sannan ya durkusa har kasa ya gayar da abbansa , sarki abul abbas ya dafa kafadar hilal sannan ya tasheshi zaune , Yai mai murmushi yace "hakika yau naji dadi dana ganka kan karagar mulkina ina farin ciki da haka ,sannan zan sanar dakai labarin wannan yarinya dakai arba da ita acikin mafarkinka , Koda jin haka sai fuskar hilal ta fadada da wata murmushi alamun farin ciki suka bayyana akan fuskarsa yace yakai abbana gaggauta sanar dani labarin wannan sarauniya ta kyawawa . "Yaku yan majalisata kuma wannan al'amari ya shafeku bama kuba gaba dayan mutanin duniyar nan wannan al'amari ya shafesu .sarki abul abbas yafada cikin daqa murya , Yayin da yan majalisan suka ji haka Sai waziri yace "ya mai girma shin tayaya wannan al'amari yashafemu " Koda jin haka sai sarki abul abbas Yadubi yarima hilal sannan yace " Jiya nayi istihara kan matar da dana zai aura Allah sWt ya nuna min acikin baccina Ita wannan kyakkyawar yarinya diyace ga sarki MULKEsH sarkin birnin Askandariya yayin da wannan yarinya takai munzalin aure sai mahaifinta wato mulkesh ya aurar da ita ga wani sarki mai suna ashbir yana mulkar garin ashdamir Shi wannan sarki adaline Amma yanzu wani hatsabibin boka hade da wani jarumi sun hallaka shi har suka nemi hallaka wannan yarinya wato matar sarki ashbir sai Allah ya tseratar da ita , Yanxu haka tana hannun wani shu'umin al'jani wanda shikuma wannan aljani dane ga Dubyalu sarauniyar aljanun dana kama na daureta cikin kurkukun karkashin kasa , , Zan cigaba TAKOBIN JIN 3!!! Littafina uku(3) Littafin Shuraih Usman Part 2 . . . Yayin da mahaifinta labari yazo masa cewa wani azzalumi ya hallaka sarki ashbir tare da yarsa Sai wani bakin ciki ya turnukeshi Nan take ya hadiyi zuciya ya mutu . Ita wannan yarinya sunanta SURAILA Yayin da ta tsira daga masifar azzaluminnan sai ta nufi wannan kasa tawa bisa rashin sa'a tayi arba da wannan shu'umin aljani . Wannan aljani sunansa SHAM'UNA burinsa kuwa itace ya mulki duniya baki dayanta , Yayin dazai mallaki wata takobi ta sihiri wanda muddin bayana tare da suraila ba to tabbas bazai mallaki wannan takobi ba shiyasa ya dauketa . Yanxu haka wasu manyan sarakuna na wancan nahiyar sunyi shiri zasu fita neman shi wannan aljani sham'una su karbe suraila a hannunsa daga bisani su tasamma inda wannan takobi yake . Su wayannan sarakuna sunyi bincike sun gano baza su taba iya yakar aljani sham'una ba. Sun gano duk duniya babu mai iya yakar shi wannan aljani face dana yarima hilal , Koda jin haka sai yarima hilal yadago dakansa wanda tun da sarki abul abbas yafara bada labarin kansa na sunkuye . Abul abbas yaci gaba " Yanxu haka suna shirin zuwa ga dana hilal domin su. Yaudareshi ya hallaka aljani sham'una daga bisani shima su hallakashi . Amma abin da basu sani ba shine sune zasu hallaka $ .$ Yaku jama'ar birnin nurul ansar kusani wannan wata damace da zamu yayata Addinin musulunci a duniya baki dayanta $ ,$$ Ayayin da zamu nuna ma kafirai cewa Addinin musulunci shine addinin gaskiya shine tafarkin Annabi ibrahim AS $$ ,$ Sannan yakara da cewa yakai dana ka je ka yi shiri gobe domin wannan aiki ba wani ne zai yiba face kai kadanka $ Kasani cewa na yarda da jarumtarka $ $. Koda gama fadin haka sai hilal wanda kansa ke a sunkuye ya dago kai sannan ya dubi dandazon jama'ar dake fadan yai kabbara da iya karfin muryarsa aiko nan take jama'a suka amsa ALLAHU AKBAR . Washe gari yarima hilal yai gagarumar shiga sannan yafito fada ya sanya wata bakar riga ce falmara sannan yasanya wata sulken karfe wadda take dabai baye da wasu irin kaNa nan duwatsu Masu daukar ido Sannan yasaka wata bakar wando agefen maransa kuwa ya rataraya takobinsa $ . Kai duk wanda yagansa a irin wannan shiga lallai zaice wannan wane mutum . Nan sarki yafito fada hilal ya je ya kwashi gaisuwa sannan yai sallama da mahaifinsa sarki abul abbas Ya haukan dokinsa sannan ya fita daga cikin birnin Nurul ansar yayin da jama'an gari keta binsa abaya $$ .$ Wannan shine abun daya wakana a birnin nurul ansar yayin da yarima hilal ya fita nemar wannan kyakkyawa wato gimbiya suraila ¤¤¤¤¤¤¤¤¤. ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤. ¤¤ . Kumru kuwa bayan sun huta sai yanemi da amai iso zuwa fada aiko wannan dan sakon ya rakashi harfada . Sarauniya lasmin na zaune bisa karagar mulki ana tafiyar da harkokin yadda suka dace . Kawai sai aka hango sarkin yaki kumru tare da wannan dan aike koda sarkin yaki kumru ya gabata a fadan sai ya kwashi gaisuwa ga sarauniya sannan ya ciro wata fata wadda duk tabi ta jeme saboda danshi dayake rabarta . Yamika wannan jemammiyar fatar ga maga takarda shikuma ya mika wa sarauniya Amma sai tai mai umarni daya karanta abin da abin wannan fatar ta kunsa na take ya bude wannan fatar$ Yasoma karantawa kamar haka Sako daga sarki Gulmanu mai mulkin birnin ashdamir zuwa ga sarauniyar kyawawa ta duk duniya Kisani cewa yanxu ba maganar aure ce ta sa na aiko da wannan wasikar ba ,dalilin wannan wasika itace ina son muhada karfi da karfe don ganin mun mallaki wannan takobin duk dana san kina da labarin takobin $ .$ Kisani amintaccen bokana ya tabbatarmin da cewa bazan taba mallakar wannan takobi ba face mun nahada hannu dake $kamar yadda kema amin taccen bokanki ya tabbatar miki bazaki taba mallakar wannan takobi ba face mun hada karfi da karfe . Sannan kuma in kin amince sai ki rubuta wata wasikar sannan kibawa wannan dan aiken nawa ya kawomin ni kuma sai inyi shiri inzo in sameki a birnin ki $ Sannan kuma ki sako min mutanena da kika kulle a gidan kurkuku $ Koda maga takarda ya rufe bakinsa sai waziri mai suna hammadu yace ya Ranki shidade anya zamu iya yadda da sarki gulmanu kuwa kinsan shi dan adam baya da tabbas kada kizo ki amincemai Daga baya kuma bayan bukata ta biya ya nemi ya yaudareki$ . Koda sarauniya kasmin taji haka sai ta kyalkale da dariya sannan tace kada damu yakai hammadu babu abin da zai faru dani awannan tafiya da zamuyi kuma aishi baisan wacece sarauniya lasmin mai mulkin dimaskha bane shiyasa har yake kokarin yaudarata amma bai san kansa yake yaudaraba Takar juyawa izuwa gefen sarkin yakinta sannan tacemai yakai musabbih inason gobe a hadamin dakuru mutum doma wayanda kayarda da jarumtarsu lallai gobe zan isa zuwa birnin asdamir sannan inaso dakarun nan afiddasu daga kurkuku a hadasu da kumru gobe zamu wuce ¤¤¤¤¤$ Zanci gaba TAKOBIN JIN 3!!! Littafina uku (3) Littafin Shuraih Usman Part 3 . . Washe gari sarauniya lasmin ita da sarkin yaki kumru suka dauki hanyar birnin Ashdamir . Sunyi tafiya mai nisa sosai sannan $arauniya tabada umarnin a yada zango bako ina bane suka yada zango illa acikin wani daji mai sarkakiya wanda bakajin motsi ko kukan tsuntsaye . Nan take suka kama aikin kafa tantuna Bayan sun gama kafa tantunan Sai suka fiddo da guzurinsu domin su cika cikinsu dashi . Ayayin hakanne sai sukaga wata kura ta turnike gabadaya ilahirin gabashin dajin ba zato ba tsammani sai wasu jibgagan mutane suka fara bayyana wayanda adadinsu sunkai dubu . Gabadayansu suna rike da makamai kala kala . Su wayannan jibgajibgan mutane. Sun kasance narka narka wanda girmansu ya ninka na dakarun sarauniya lasmin sau uku .$ Wayannan gabza gabzan masu kama da samudawan farko Suka fara darewa suna bada wata siririyar hanya a tsakaninsu Gama darewarsu keda wuya sai ga wani narkeken kato ya bayyana yana mai cusguna fuska Hannunsa na dama yana rike da wata sharbebiyar gatari wadda idan karti goma zasu taru baza su iya rabata da kasa ba a yayin da dayan hannunasa yana mai rike da kugunsa . Wannan kato dai da halama shine shugaban wayannan samudawan$ .$ Nan take dakarun sarauniya lasmin suka firgice da ganin wayannan samudawa kai hatta sarkin yaki kumru shi kansa daya ke takama da cewa shi gwarzon mayakine sannan ya fita yaki kala kala akalla sun kai talatin . Bai taba ganin irin wayannan mutanen ba kuma ko a labari bai taba jin irin nasu ba . Dayai duba izuwa ga sarauniya lasmin sai ya cika da mamaki Domin yaga ita ma ko kula da samudawqan batayiba in banda cin abincinta da take . Shugaban samudawan ya kariso gaban su kumru sannan yace yaku wayannan matafiya shin meya rudeku da har kuka baro kasarku gidajenku yan uwanku matanku ku ka kawo kanku izuwa mahallakarku . Lallai da halama baku taba jin labarina ba ,sai budhe da dariya mai kama da karan aradu koda yai dariyar mai isarsa sai ya tsyuke baki kace bai taba yin dariya ba tunda yake a duniya Sannan yakara da cewa Nine shaddadu rikakken dan fashin daya gagari dukkan sarakunan wannan nahiya . Ban san yafiyaba balle hakuri lallai yai sai na dandana maku azababbiyar mutuwa wadda ban taba dandana ma bil adama ba $ Yana rufe bakinsa sai ya lura da sarauniya lasmin wadda ko tasan ma yana wajen in banda cin abancinta babu abinda take$ . Koda ganinta haka sai ya harzuka sannan ya daka mata tsawa yace ke fingalalliyar sarauniya lallai kisani tunda nake aduniya babu wanda yataba arba dani batare daya tsorata ba . Kece mutun ta farko wacce tai arba dani naga ta shagalta sabida bata san ko waye niba amma da sannu zaki sani . Ko rufe baki baiyiba sarauniya lasmin ta mike tsaye sannan ta kyalkyale da wata irin dariya koda ta idar da wannan dariya sai ta dubi shaddadu ta daka mai tsawa 'kai la'ananne kuma matsoracin dan fashi tuni labarinka ya zomini cewa kana kwace ga marasa karfi lallai yau dubunka ta cika tana rufe baki ta zare takobinta ta afka cikin wayannan samudawan koda samudawan suka ga haka suma sai suka yi shirin tarbarta $. Ayayin data iso dafdasu sai ta daka tsalle sannan ta shafka ma guda daga cikinsu sara akai aiko sai takobin ta tsarge shi gida biyu . Koda sauran samudawan suka ga haka ai sai suka mata ruf dugu ita kuma sai ta cigaba da saransu tana sukansu nan fa suka cigabada da faduwa kaasa matattu , Koda shugaban samudawan shaddadu yaga muddin akaci gaba a haka toh lallai za ta iya karar da yaransa Itako lasmin sai ta zama kamar wata shaidaniya a tsakaninsu sai saransu take. $$ Tana wani kalar tsalle tsalle A duk lokacin da tayi tsalle sama sai dai kaga kan basamude ya fadi kasa Cikin lokaci kan kani ta karar da wayannan samudawan dukkaninsu Yarage saura shaddadu ¤¤¤¤¤¤¤¤¤. ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤. ¤¤¤m Al amarin suraila kuwa a yayin da aljani sham'una ya luluka da ita cikin sararin samaniya sai suka yi ta kutsawa cikin sama har suraila ta suma . . Zanci gaba TAKOBIN JIN 3!!! Littafina Uku (3) Littafin Shuraih Usman Part 4 . Farkawanta keda wuya saita tsinci kanta kwance kan wani katifa mai tsananin laushi , cikin wata daki wadda babu komai cikin wannan dakin face wasu tarkace da kuma kayan tsafi . Sannan kuma dakin gabadayansa an ginashine da zallar dutse wani abin mamakinma shine babu wani alama da har zaisa mutun yagane wannan dakin da dutse aka ginashi . Koda suraila ta gama duba izuwa dakin da kayan dake cikinsa saita fara tuna abubuwan da suka faru tun fitowarta daga birnin ashdamir har haduwarta da aljani sham'una da kuma abubuwan daya faru tsakaninsu . Koda tagama wannan tunani sai ta fashe da kuka tana mai danasanin kasancewarta a wannan duniyar . Tana cikin kukanne sai taji kamar motsi a bayanta Tana waigawa saita ga wani gefe daga cikin dakin yana janyewa izuwa yayin da wata kofa tafara samuwa koda kofarnan tasamu sai ga Aljani sham'una ya baiyana fuskarsa tana mai cike da farin ciki . Ya dubeta sannan ya kyakyace dawata mahaukaciyar dariya kai kace rufin dakinne ke barazanar fadowa Alokaci guda kuma ya tsuke bakinsa. Sannan ya murtuke fuska tamkar wanda aka aikomasa da sakon mutuwa . Yace yake wacannan budurwa kiyi sani cewa na dade ina jiran zuwarki domin na mallaki wata makami wadda muddin na mallaki wannan makami toh gaba dayan duniya zata dawo karkashina Amma kuma wannan makami a zan iya mallkarta ba batare da taimakawarki ba$ Kisani yanzu haka wannan makami yana can wata kogo a ajiye . . Ke kin kasance kinada nasaba da jarumin duniya muraisu kuma ke ce kadai gudan jininsa data rage a duniya . Aikoda suraila taji wannan zance saita kara fashewa da kuka sannan tace yakai wannan azzalumi kuma macucin aljani lallai kasani nagani acikin barcina wani jarumi mai shigar kamala ya shigo har cikin wannan gida taka sannan ya yakeka ya kuma kubutar dani$ . Lallai kasani nan da wani lokaci na tabbata wannan mafarkin nawa sai ya zama gaskiya ' Domin ni na kasance duk abin dana gani cikin mafarki toh sai ya faru dani a zahiri . Tana rufe baki sham'uma ya sake bushewa da wata dariyar wadda amonta ya dauka a gabadaya cikin dakin . Lallai baki san wanene sham'una ba kisani yanzu haka wannan gida da kike ciki yana karkashin wata kasace wadda ita wannan kasar samanta kankara ce kasarta kuma ruwane zalla . Babu ta inda wani aljani ko bil'adama zaiyi har ya gano wannan gida . Ke koma ya gano wannan gida toh bazata shigu mai ba . Shin ta hakanne kike ganin shi wannan jarumin zaiyi iya shigowa cikin wannan gida . Babu wani mahaluki aduniyarnan walau mutum ko aljan wanda har ya isa ya tunkareni face nayi gutsu gutsu da naman jikinsa$ .$ Yana gama fadin haka saiya turbune fuska sannan yai nuni da hannunsa izuwa ga bangon jikin dakin . Yana nuna bangon dakin da hannunsa sai wani siririn haske mai kamae walkiya ya fita daga hannun nasa ya dire akan bangon dakin . Yana sauka akan bangon dakin sai wata duhuwa tafara lullube bangon can sai wannan duhuwar ta yaye wani haske ya bayyana acikin haskenne yarima hilal ya bayyana yana mai tsala gudu akan dokinsa . Suraila ta kura ma hilal ido tana mai wani irin kallo wadda ke tabbatar da ta taba ganinsa . Sham'una yace" gashi shi wannan jarumi tuni na sami labarin fitarsa daga masarautar su wadda itace karshen rayuwarsa , Domin Neman wannan gida nawa tamkar neman jaki mai kahone . Yana gama fadin hakan ya janye hannunsa ga nunin dayayi , aiko yana janyewa wannan hasken daya bayyana surar hilal take ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba. . Yajuya da nufin ya fice daga wannan daki Yana fita wannan kofa ta kulle kanta Yadda kasan babu kofa a wajen domin wajen ashafe yake da bakin dutse .¤¤¤¤¤¤¤. ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤. ¤¤¤¤¤¤ Shaddadu yadubi sarauniya lasmin cikin bacin rai sannan ya zaro takobinsa daga cikin kubenta yai kukan kura ya dumfari sarauniya lasmin da gudu , Babu abin da zaiba mutum mamaki face ganin ita sarauniya lasmin ma ko wani yunkurin kare kanta batayiba face murmushi da take , Aikoda shaddadu ya kariso gabanta sai ya kaimata sara ta fuska cikin zafin nama da bajinta irin na manyan sadaukai lasmin ta tsuguna saran ya wuce ta saman kanta , Ai shaddadu bai bari ta waigo ba yakara kai mata wata saran shima tai nasaran goce masa , Ai shaddadu sai ya haukace mata sara da suka yashiga kaimata da zabgegiyar takobinsa. Sarauniya lasmin kuwa sai zullewa da gocewa saransa take cikin bajinta Koda shaddadu yaga wankin hula nason ta kaisa dare sai yashiga hadawa da karfin sihiri nanma baiyi tasiri ba . Domin kuwa duk wani masifan daya wurgomata saidai yaga ta je kamar zata tabata amma tana zuwa kusa da ita sai ta juwa ta koma kansa , Nan danan shaddadu yafara gajiya amma abin mamaki sai yaga lasminj ko alamun gajiya babu ajikinta . Sai ma murmushi da take mai Nan ya hasala yai wurgi da takobi sannan ya bare rigar da take jikinsa Woho hoho da mutum yana wajen da shaddadu ya yage rigar jikinsa yai wurgi da ita toh lallai da mutum ya gane ma idanuwansa abin tsoro . Wani murdaddiyar jikice garshi sannan ga wannan tozon naman gefen wuya sun yi burda burda . Daga kan kafadarsa izuwa kirjinsa abude suke amma cikinsa zuwa mararsa sirarane Gabadaya ilahirin jikinsa duk kwanduwane duk sun burbudo . Ita kanta sarauniya lasmin da taga wannan sura nashi sai da ta ayyana aranta cewa lallai yau tagamu da gamonta . Koda lasmin tagama ayyana haka aranta sai tayi jifa da takobinta tana sauraran isowar shaddadu . Shaddadu na ganin hakan sai yayi kukan kura ya falfalo da gudu izuwa kan lasmin saida yarage baifi taku biyu ba su hade ba sai ya kaima ta wani wawan naushi Lasmin ta tsuguna ta goce ma naushin Yakara kaimata wani naushin ta gefen ciki ita ko lasmin saita tare wannan naushin da hannunta sabida karfin naushin sai da tayi baya baya tamkar zata fadi amma sai ta tirje . Anan ta murtuke fuska itama ta kaimai wani naushi ta gefen hakar kari dukda shaddadu yayi kokarin ya kauce wa naushin amma ina sai da naushin ta sameshi a hakarkari take ya kurma wani uban ihu wanda tasa dakarun dake tare da sarauniya lasmin wayanda tunda akafara wannan gumurzu tsakanin lasmin da shaddadu suke kallo sannan suna matukar mamakin jarumtakar sarauniya lasmin. suka toshe kunnuwansu don ji sukai tamkar dodon kunnensu ne zai fashe . Lasmin tai wani tsalle asama ta kaimai bugu da kafa . Koda wannan bugu ya sameshi sai yai sama yana katantanwa sannan ya fado ji kake jagab faduwar kato . Yana faduwa lasmin ta dauki takobinta tai kanshi aikoda shaddadu yaga haka sai yayi sauri yazo gaban sarauniya ya zube akasa yana magiya yana ce mata " Yake wannan sarauniya ki mani rai nayi alkawarin daga yau zan zama daya daga cikin fadawanki kar ki kasheni na tuba na biki . Koda lasmin taji haka sai ta kyalkyale da dariya sannan tace mai "ya kai wannan dan fashi kasani kaine mutun na farko aduniya da ya tsere wa kaifin takobina daga yau kazama shugaban dakaruna " Taba gama fadin haka ta nufi dokinta sannan ta hau shima shaddadu nan aka bashi doki ya hau suka nufi birnin ashdamir . Akwana a tashi har suka isa birnin ashdamir batare da sun haduu da wani abin cutarwa ba ¤¤¤ Wannan shine abin daya afku ga su sarauniya lasmin akan hanyarsu ta zuwa birnin ashdamir . . Koya zata kasance . Muje zuwa part 5 TAKOBIN JIN 3!!! Littafina Uku (3) Littafin Shuraih Usman Part 5 ¤¤¤Al amarin yarima hilal kuwa tunda ya fice daga birnin nurul ansar sai ya yanki daji yaita tsala gudu batare da ya tsaya yada zango ba sai daya Sai dayayi kwana da kwana ki yana tsala gudu kan dokinsa Sallah ce kadai ke tsaida shi sannan yadan ci wani abun .Wata rana yana cikin tafiya sai ya hango wasu dandazon mayaka tare da wani keken doki Agefen keken dokin wani shirbeben sadaukine yana zaune kan doki .Koda hilal yai arba da wayannan dakaru sai ya kariso garesu cikin tsananin mamaki sai yaga dukkansu sun tsaya sannan kofar wannan keken doki ta bude .Wata kyakkyawar mace ta fito Duba daya yaimata yagane wannan macen tana da wata matsayi a masarautarsu.Wannan matar tai mai murmushi sannan tace da shi" Marhaban bika yakai wannan jarumi kuma sadauki mai daka ma maza gumba yarima hilal dan Abul Abbas mai mulkar birnin nurul ansar.Nan alamun mamaki suka bayyana a fuskar hilal ya dubi wannan kyakywar matar ya tambayeta "Shin wacece ke sannan kuma ya akayi kika sanni ".Koda taji haka sai ta kyalkyale da dariya sannan tace" hatta abin daya baroka dAga birnin ku nasani sannan kuma ina mai tabbatar maka da cewa baza ka taba samun galaba akan Aljani sham'una ba face ka hada kai damu "Kisani niga ubangijina na dogara kuma shine zai bani nasara akan dukkan abin dana sa agaba "Ya tari numfashinta cikin hasalaYasake cewa da ita "wannan furuci da kikayi ya tabbatar min kece sarauniya lasmin mai mulkar birnin dimashka to kisani zan hada kai dake amma bawai don bazan iya tunkarar shm'una bane A'a saidai don inason na kafa tutar musulunci awannan na hiya taku kuma shi kansa takobin da kuke ta zumudin ku mallaka .Ni zan iya dauko maku shi batare da zoben wuta ba amma ina son naga shin dabarar ku da karfin sihirin ku zasu iya taimakon ku ku mallaki wannan takobi .Koda sarauniya lasmin taji haka sai tayi murmushi sannan ta dube hilal tace mai ka yi tafiya mai nisa don haka kana bukatar hutu ,,Tana gama fadin haka ta juya ta shige cikin wannan keken doki shikuma hilal sai yabita da kallo ...Bazato ba tsammani sai sukaji wata irin kara daga sama tamkar aradun ce zata fado ita kanta lasmin

Chapter 3 of 4