Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 4
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels TAKOBIN JINI 1 Littafina daya 1 complet Marubuci:- Shuraih Usman (c) shuraih 99% 2016 TAKOBIN JINI »» . Littafin shuraih Usman Part 1 Awani zamani can daya shude adaular larabawa acikin wani babban birni maisuna ashdamir Ashdamir babban birnine wanda yake karkashin jagorancin sarki gulmanu gulmanu ya kasance tun yana yaro azzalumine kuma hatsabibi don ko acikin yara sa`oinsa tsoronsa ake Wani abin mamaki shine allah yazuba masa karf,ga jarumta don tun yana dan shekara goma shabiyar yake kwace a hannun mutane ko fatake da kun zaburo mai sai dai wasu bakuba dan bai dauki ran mutun a bakin komai ba mahaifiyarshi ta rasu shiyasa mahaifinshi yake mutukar sonshi suna rayuwane awani kauye sai suka yanke shawaran yin hijira zuwa birnin ashdamir koda suka iso birnin . Bayan kamar sati daya sai gulmanu yafara sana'anshi wato zalunci todama sarkin wannan birni adaline sunan shi asmir bin hubbal sarki asmir bayason zalunci kuma bashida abokin gaba sai azzalumi koda sarki yasamu labarin gulmanu da irin zaluncin daya keyi sai ya umarci dakaru dasuje sukamoshi. Baccin anka month shine sarki yasa ai yekuwa kowa da kowa suzo fadan sarki aiko nan take fadan ta cika da mutane makil sannan wani bafaje yafara magana kamar haka. Yaku jama'ar wannan birni mai Albarka kusani wannan mutumin yaka sance yana aikata zalunci acikin wannan birni dun haka hukuncin shi bulala dubu sannan kuma musa shi agidan yari na wata shida cur,wannan sai yazama darasi ga yan gaba. Nan take aka mai bulala dubu sannan aka wuce da shi gidan yari mahaifin sa yana kuka yana neman gafara akan abashi danshi haka amma ina yana kallo aka wuce dashi Shuraih 99% TAKOBIN JINI 1 Part 2 TAKOBIN JINI»» Part 2 Bayan ankai gulmanu gidan yarine. Sabida haushi da takaici mahaifinsa ya hadiyi zuciya ya mutu. Da safiyar ranan ne labari ya riski gulManu ai mahaifinshi ya mutu nan take ya runga kuka yana birgima akasa. Bayan wannan rana gulmanu yana cikin kurkuku sai yaga wani koren haske yana fitowa kadan kadan kai har yamamaye cikin dakin da yake amma ko alamar tsorata babu afuskan gulmanu har koren hasken nan ya rikide yakoma siffan wani kyamu shashshan tsoho babu riga ko wando a jikin sa sai wani warki ta fatan zaki duk jikinsa gashine. Ga wani kashin kwanyan mutum a rataye a wuyanshi. Mutumin bata rai sannan yace yakai gulmanu kasani cewa yadda kakeson ganin bayan sarki Ashbir nima haka nake son ganin bayanshi kai mahaifinka yakashe amma ni yaya na guda biyu yaka shemin. Tsohon yace gulmanu kayi sani cewa suna boka balbalin bala'I ina rayuwane acan kan wani dutse anakiranshi dutsen bala'I. Arayuwana ban san yafiyaba kuma bani da imani koda miskala zarratin ne Ina dawata kyakyawan mata wadda nake sonta ainun amma garin haihuwa tarasu soyayyan danake mata sai takoma wajen yayanta data haifa yan biyu nasamu suna SAKRADIYYU da SAKRADISA ina masifan son yayana har sukakai shekaru Ashirin aduniya sannan nafara koya masu sihiri kalakala. Wata rana suka ce mun nabarsu su je farauta ni kuma na yarjemusu. Da suka fitane sai sukakamo hanyar wannan birni. Har suka iso suka shiga cikin birnin nan take suka fara amfani sihirinsu suna kwace ,yima mata fyade dade sauransu. Shikuma dokan wannan garin shine duk wanda aka kama yacuci wani koya zalunci wani ta hanyar amfani da sihiri to hukuncinshi kisane. Ai kuwa nan da nan jama'an garin suka gane su nan take suka kai kara wajen sarki. Sarki ashbir yasa wani bokan shi mai suna KUMRU bincike ai ko nan take boka kumru yace tabbas magana wayannan mutanen gaskiyane ya shu gabana. Nan sarki yace aje akamosu aiko nan take a kaje aka kamosu sarki ashbir yatara jama'an gari duka afada sannan. Aka kashesu. Al'amarina kuwa tun danaga sunyi sati basudawo ba hankalina ya tashi na dauko madubin tsafina naduba nan da nan naga duka abin daya faru dasu nan na Kwala wani uban ihu wanda nikaina bansan lokacin danayi shiruba hawaye nazuba a kuncina nan ta ke nayi wani sihiri mai karfi na jefawa boka kumru nan take ya tarwase acikin fadan sarki ashbir don ni duk wani bokan na hiyannan shayina yake nayi nayi in kashe sarki ashbir amma abin yagagara kawai saina shiga halwan tsafina yau ne futowana daga halwan tun bayan shekaru ashirin da biyar kenan. Nan boka balbalin bala'I ya sauke numfashi. Gulmanu yace yanzu nimekake nema awjena nan boka balbalin bala'I yace kasani acikin halwan tsafina naga babu yadda za ai naga bayan abokin gabana har saina zo na sameka mun hada karfi da karfe sannan za mu iya ganin bayan shi TAKOBIN JINI 1 Copyright Part 3 Shuraih Usman 2016 TAKOBIN JINI »» part 3 gulmanu ya takarkare yafashe da dariyar mugunta. Wannan dariyar ita ta tabbatar da boka balbalin bala'I cewa gulmanu ya amince da bukatarsa. Ai ko sai boka balbalin bala'I yai nuni da yatsansa izuwa gulmanu sai gulmanu yaji wani kaman an tsikareshi ya dan lumshe ido budewanshi keda wuya sai yaganshi acikin wani babban gida. Wanda aka mamaye cikin gidan da yakutu da lu'ulu' ga kilisai ta ko ina sai yai duba hannun damanshi nan take yai arba da boka balbalin bala'I akan wata karaga na zinari. Boka balbalin bala'I yace kasani gulmanu gobe zamu kai ma sarki ashbir likafanin mutuwan shi har gida sannan kai na doraka akujeran domin arayuwana i ina matokan son azzalumi da zalunci shiyasa nake son na dauraka akujeran sarki ashbir don kata aika ta zalunci. Amma kafinnan ina so kaje kahuta. Bayan gulmanu yahuta sosai. Sai ya kishingida don yadan runtsa amma ina tunanin mahaifinshi. Ta hanashi runtsawa. Washe gari bayan gulmanu yayi shiri irin namayaka. Sai boka balbalin bala'I yashigo har dakin. Gulmanu yace kasani gulmanu yau shine ranar daukan fansa a kan abokin gabanmu don haka babu tausayi acikin wannan tafiya tamu. Ai kuwa sai boka balabalin bala'I yai wasu surutai sai ga wata katuwar tsuntsu ta sauka akofar gidan sannan boka ya umarci gulmanu daya hau shiyananan zuwa. Bayan hawan gulmanu bayan wannan tsuntsu sai tsuntsun yatashi yanausa sararin samaniya sai gudu ya ke kaman baze dainaba******Al'amarin sarki ashbir kuwa tunda ya samu labarin gulmanu ya tsere agidan kurkuku sai hankalinshi yatashi ainun nan yakirawo bokanshi mai suna hibrussalal. Koda zuwan hibrussalal sai sarki ashbir yace mai yakai boka hibrussalal kayisani cewa yaronnan gulmanu yasamu nasaran tserewa da ga gidan kurkuku don haka inaso kadubo min inda yake sannan ka qara dubomin wanda ya temaka masa don nasan ba zai iya tserewa daga wannan kurkuku shi kadai ba nan take boka hibrussalal yace ya sarkin sarakuna ina son abani daga yau zuwa gobe da safe. Takobin jini 1 Copyright Part 4 Shuraih Usman 2016 Takobin Jini 1 TAKOBIN JINI»» . Marubucin Littafin Shuraih usman . part Washe gari koda boka hibrusallal yazo fada sai ya kwashi gaisuwa. Agun sarki sannan sarki ashbir yace boka hibrusallal menene sakamakon binciken dakayi jiya. Boka hibrusallal yace kayisani ya sarki mai Adalci cewa jiya bayan narabuda kai babu inda nazame sai kokon bincikena. Sannan boka yai shiru sarki ashbir yace to ina jin ka mene sakamakon don na kagu da inji meke faruwa. Boka hibrusallal. Alkaluman tsafina sun nuna min wani babban masifa da ke shirin faruwa acikin wannan birni namu nan da nan hankalin sarki ashbir ya dugunzuma ainun yace ma boka kadena kwanekwane kawai kafads min meyake shirin faruwa acikin kasata sai boka hibrusallal yace wato maimartaba bawani bane ya taimaki gulmanu har ya tsere daga kurkuku ba illa tsohon abokin gabanmu wato boka balbalin bala'I yanzu haka sun hada karfi da karfe wato karfin tsafi da karfin damtse zasuzo suya keka sannan gulmanu yahau karagan mulkinka. Koda jin wannan batu sai kowa da ke cikin fadan hantarsa ta kada akafara kace nace. Sannan sarki ya dakamusu tsawa sannan aka natsu. Sarki yace yanzu suna inane. Sai boka yace yanzu sunanan acan dutsen bala'I. Kuma kasani daga can zuwa nan tafiyar kwana biyar ne kaga muna da lokacin da zamuyi shawara. Da jin wannan maganan sai sarki ashbir yace yanzu meye abun dayakamata muyi. Sai boka hibrusallal yace shawarata itace muma mutaresu dayaki na san tauraruwa zahlu zatabamu nasara Tauraruwa zahlu itace duk yan nahiyar suke bauta mata. Sarki ashbir yace lallai boka hibrusallal. Kakawo shawara dun haka sarkin yaki kadibi dakaru dubu biyar kutsaya abakin kofar gari kuhana kowa fita sannan kuhana kowa shiga.wannan shine abin daya wakana abirnin ashdamir *********** Al'amarin boka balbalin bala'I kuwa yana rabuwa da gulmanu bai zame ko ina ba sai wani daki inda shima ya sake tsuma kanshi acikin tukunyan tsafi har tsahon kwana daya sannan ya fito koda yafito sai ya kama karanto wasu dalasimai na tsafi ai sai. Ya bace bat kaman bai taba wanzuwa awajenba ********** ********* Gulmanu kuwa tunda yahaau kan wannan tsuntsu ta lula da shi sararin samaniya. Yana cikin tafya kenan sai yaga kaman wani abu yana yawo asaman dayalura sosai sai yaga ashe boka balbalin bala'ine nan suka kwashe kwana uku suna tafiya asararin samaniya sai arana ta biyarne suka yada zango abayan birnin ashdamir nan boka balbalin. Bala'I yace ma gulmanu ya shirya yanzu zasu shiga garin. Aikuwa nuni kadai bokabalbalin bala'I yayi da tafin hannunshi sai wani haske ya bai bayesu can sai hasken yayaye nan suka tsinci kansu akofan fadan maimartaba sarki ashbir ga dakaru nan fululu tako ina suna kai da kawowa nan da nan boka balbalin bala'I ya bace batt shikuma gulmanu koda ganin haka sai yashigi wayannan dakaru dasara dasuka duk inda gulmanu yayi saide karinga ganin sassan jikin dan adam suna faduwa can sai dakarun sukaga in akacigaba ahaka to lallai zai iya qarar da su sai su ka mai zobe sannan wani ya wurgomai raga ai kuwa yai sa'a ragan tada baibaye gulmanu nan suka rufumai suka mai daurin huhun goro suka dauko shi basu tsaya dashi ako ina ba sai agban sarki ashbir koda sarki yaga gulmanu acikin sarka sai yai murmushi yace yau kazo hannu kuma gobe za'a yankema hukuncin kisa agban kowa da kowa*** TAkobin jini 1 Copyright Part 5 Shuraih Usman 2016 TAKOBIN JINI�� . Marubucin Shuraih Usman Part . . Bayan sarki yasa ankai gulmanu kurkuku an kulle can sai gulmanu yafara sakesake acikin ranshi. To shi Boka balbalin bala'I dama ya yaudarenine yana kan wannan sakesaken ne sai ya ji motsi ta bayanshi wai ga wan dazaiyi kenan abin mamaki ba sai yayi kicibis da boka balbalin bala'I ba Haba ba sai gulmanu ya fara kokarin balle sarkan da aka daureshi da itaba. Boka balbalin bala'I ya bushe da wata mahaukaciyan dariya wanda tasa gulmanu ya dena kokarin balle sarkannan. Ya dauki lokaci mai tsawo yana wannan mahaukaciyar dariyan na shi sannan yai turbune fuska izan ka ganshi zaka rantse bai taba dariya aduniya ba Yace ya kai gulmanu kayi sani cewa ina sane na aikata ma haka. Gulmanu ua tunzura sannan ya ce lallai kacika maci amana kuma matsoraci. Ashe duk harbin iska ne kake tayi wai kai za ka kashe sarki ashbir amma ga shi anzo ka gudu nanemeka harnagaji sannan baka taimakamin dakomiba Koda jin haka sai boka balbalin bala'I yasake bushewa dawata mahaukaciyar dariya can sai kuma ya juyar da dariyar izuwa murmushi. Sannan yace Gulmanu kai yarone shiyasa bazaka hangi abin dana hanga. Kayisani cewa wani tarkone na dana ma sarki ashbir kuma yafada. Wato kaga kama kannan da akayi suna zaton kai kadaine kazo. Sannan yanzu haka nasan sarki ashbir yananan yana bacci cikin kwanciyan hankali mukuma. Sai muyi amfani da wannan daman wajen halakashi sannan kuma inaso kadauka azuciyanka nayi haka ne don tseratar da rayuwanka Nan take boka ya balle ma gulmanu wannnan sarkan sannan yakama hannun gulmanu ba sai ga su a bakin kofan turakan sarkiba. Gulmanu ya kashe masu tsaron kofan. Sannan ya kutsa kai cikin turakan ba sai ga sarki kwance ba yana ta minshari. Nan gulmanu yadaga takobinshi sama bai sauketa ako'inaba sai a wuyan sarki ashbir aiko Nan kan sarki tai sama to adaide wannan lokacin matan sarki mai suna suraila. Ta make abakin kofan tana jin duk abin da gulmanu kefadi koda ta fahimci gulmanu ya kashe mijinta saita kwarara wani uban ihu sannan taruga aguje koda gulmanu ya ji ihu sai ya fita da gudu yabi bayan suraila yana bintanne kwatsam sai yaji an dagashi sama an buga da kasa waigowan da zai yi kenan sai yaga wata majaujawa tanufo shi gadan gadan da niyyar halakashi bawannan bane ya tsorata gulmanu. Ganin majaujawan sam bai tsoratar da shiba illa Rashin ganin marikinta domin a iska majaujawan ta ke zuwa koda ya rage bai fi tiki biyu majaujawan ta fille maikaiba Sai yaga majaujawan tana komawa dabaya. Nan sai boka balbalin bala'I ya bayyana yana rike dawani babarbara katuwa sannan boka hibrussallal shima ya bayyana ahannun shi na dama yana rike da majaujawa hannun hagu kuwa wata makekiyan garkuwane. Takobin jini 1 Copyright Part 6 Shuraih Usman 2016 TAKOBIN JINI»» . Marubucin Littafin Shuraih usman . Part . . Sai boka bal balin bala'I yai furta wasu dalasimai nan da nan wata bakar wuta mai tafasa ta kawo ma boka hibrusallal wani wawan sura da niyan ta lullubeshi koda boka ya gahaka sai shima yai wasu surutai wanda shi kadai yasan meyafada nan take wannan bakar wutan ta bace kaman bata taba wanzuwa awajen ba wannan ne ya basu daman rabuwa har da yar tazaran zira'I tara sannan boka balbalin bala'I ya bushe da dariya sautin muryarsa duk t dauka acikin gidan sarautan lokaci guda kuma ya tsuke baki kaman bai taba dariya aduniya ba yace kasani hibrusallal kadebo ruwan dafa kanka kuma ina mai rantsuwa da tauraruwa zahlu ko burbushin ka baza a tararrba. Karo na farko kenan da gulmanu wanda tun farkon gumurzun yana wajen yasaka aranshi lallai boka hibrusallal taimakonsa yake. Batun gaskiya dai boka hibrusallal bai da karfin sihirin boka balbalin bala'I amma saboda zuciya irin na boka hibrusallal yadake sannan yace kayisani yakai wannan azzalumin boka yau karshen zaluncinka tazo ina mai tabbatar maka ko kayi nasaran kasheni to kasani watarana kaima sai ka....... Bai gama rufe baki ba yaji wata zafi ta mamaye sassan jikinshi. Nan boka balbalin bala'I yakece da dariya hannunsa na nuni izuwa boka hibrusallal nan boka hibrusallal yafara yankwamewa yana shanyewa har takai yakoma kaman jariri koda gulmanu yaga haka sai yace acikin ranshi cewa boka balbalin bala'I bakaramin hatsabibi bane shikuwa boka hibrusallal nan take kasa ta shanye shi gaba daya in badon a gaban gulmanu wannan abun yafaruba da sai ya rantse babu wani mutum daya taba wanzuwa awajen Sannan boka balbalin bala'I ya sauke hannunshi tare da yin wata irin huci ba sai gulmanu yaga kayan jikinsa sun canja sunkoma kayan sarakai ba wadda ko acikin sarakan sai antona. Gulmanu yatashi daga zaunen dayake ya tsaya akan kafafunsa sannan yace waye zai jadani nine gulmanu ibn hubruz azzalumi kuma uban Azzalumai. Bayan gari ya waye jama'an gari suka tsinci kansu acikin wani yanayi na bakin ciki sabilida kashe Adalin sarkinsu da Akayi aka kafe kanshi acikin wata itaciya. Ga badaya jama'an gari suka yi sahu sahu afada don ganin waye ya kashe sarkinsu ya haye kujeransa bayan yan mintoci sai ga boka balbalin bala'I ya bayyana a tsakiyan fadan sannan aka ga gari yayi duhu can da duhun yayaye. Gulmanu ya bayyana da kayan sarauta nan da nan jama'a suka fara ihu suna suna cewa bazamu yadda ba suna kan fadin haka sai wata iska mai karfi tatashi sama tana tashi sai ga kawunan mutane nan burjik akasa koda jama'an gari suka ga abin dayafru da yan uwansu wayan da suke gaba gaba sai sukai tsit sannan wata dariya ta barke sanda mai dariyan yayi ta ishesshi sannan yai shiru bawani ke dariyan ba illa Gulmanu. Sannan yace kuyisani ya ku mutanen birnin ashdamir daga nine sarkinku kuma duk wanda yaki yin muba yi a agareni abin daya faru ga wa yennan shine zai faru agaresa. Sannan sarki gulmanu ya shige gidan sarauta. Jama'a suka watse. Takobin jini 1 Copyright Part 7 Shuraih Usman 2016 TAKOBIN JINI . Marubucin Littafin Shuraih Usman . Part . . Al'amarin gimbiya suraila kuwa tun da ta samu ta fice daga cikin birnin Ashdamir sai ta yanki daji taita gudu har tsawon sa'oi. Goma sannnan wani mugun gajiya ya lullube matA gabobin jiki taji bazata iya ma tafiyaba,can dai dataga babu yadda zatayi tafiya ya zamar mata wajibi sai ta cigaba da tafiya tana yi tana layi kamar wadda ta kurbe tulunan giya guda biyar !kamar daga sama saI taji karar zubar ruwa , Nan take farinciki ya lullubeta taji ma dukkan gajiyan dake jikinta sun kau ahaka ta karisa bakin wannan korama ,. Wannan korama takasance babban kogi ne ma'abocin zubar da ruwa shi wannan kogin yana saman wani tsauni ne yayin da ruwan cikinsa ke gangarowa zuwa kasa wannan ruwan dake kasan shine ya samar da koramar da suraila ta tunkara cikin farinciki tana ji kaman tabace ne ta bayyana atsakiyar wannan korama sabida kaguwa da tayi da kuma kishirwa ta ke damunta. Koda ta iso bakin wannan koramar sai tafada cikinsa ta sha daga wannan korama, sannan tafito tacigaba da tafiya saida ta kwashe kimanin kwanaki talatin tana tafiya wani lokacin tasamu abin dazataci wani lokacin kuma har sai tafarauto wani lokaci kuma yayan itatuwa takeci gimbiya suraila kenan ta taso cikin jindadi da gata sannan ta auri Mutumin da kowane talaka ke alfahari dashi. Kyakkyawace tagaban kwatance don duk tsananin kamewar mutum muddin zai hada ido ko yai duba izuwa gimbiya suraila to sai yaji yana matukar sonta , Farace tas fuskarta shimfidaddiya ma'abocin murmushi ,kwayan idunuwanta wanda yakasance kamar lu'u lu'u ne gata da bakin gashi wadda ya gangaromata har gadon bayanta, Amma yanzu duk tafita daga hayyacinta tai baka kayan jikinta duk yabi ya kyamushe sannan ta dan rame. Wata rana suraila tana cikin tafiya wadda ita kanta batasan ina ta nufaba, Sai taga wani bishiyar rumma ta kariso gindin wannan bishiya sannan tafara kokarin cire yayan rumman nan taci, Koda tai tsalle da fixgo wani daga cikin yayan rumman din sai taji kasa na girgiza wata sauti wadda batasan ta'ina yake fitowa ba yakarare kunnuwanta , Nan take gari yai duhu wannan bishiyar Kuwa sai tai sama ta rikide izuwa wuta , Wuta mai tsoratarwa nan take suraila tai matukar tsorata batasan lokacin da dan rumman dake hannunta ya fadi akasa ba , Bacin gari yai duhu bakikirin baka ganin komai sai sai wannan wutar da take barazanar kone dajin gabadaya. ¤¤¤¤. ¤¤¤¤. ¤¤¤¤ Gulmanu kam baccin yatara mutanen gari ya shaida masu cewa shine sarkinsu Kuma duk wanda yaiyunkurin kawo masa wata rikita-rikita ko batanci , Zai dandana mai bakar azaba sannan ya kashe shi, Haka gulmanu ya cigaba da mulkin zalunci a kasar Ashdamir laifi kalilan mutum zai aikata amma hukuncin kisa za'a yankemai, Boka balblin bala'I kuwa tunda yaga gulmanu yasami nasara , sai ya koma Izuwa kokon dutsen da yake rayuwa sannan yacigaba da taimakon gulmanu ta hanyar aika da sakonni , Kuma duk wata al'amari data shige ma gulmanu ido toh boka balbalin bala'I ne ke sama mai mafita , Wata rana afada anacikin fadanci ga waziri agefe! Hakimai da de saurasu suna gefe anacikin fadan ci sai ganin gulmanu akai ya kyalkayle da dariya wadda tasa jama'a da sauran fadawa kowa yashiga taitayinsa don muddin sarki gulmanu ya barke da dariya toh fa wata babban al'amarine ke shirin faruwa . Ya kai wazirina kayisani yau na samu matar da zan aura,sarki gulmanu yafada bayan ya sayar da dariyar dayake cikin nishadi yafadi hakan ,ko da waziri da sauran fadawa sukaji haka kauwa sai washe baki yake yana farincki dun ba mutuwa za'ayi ba, Takobin jini 1 Copyright Part 8 Shuraih Usman 2016 TAKOBIN JINI»» . Marubucin Littafin Shuraih usman . Part . . . . Yayin da waziri da hakimai da sauran fadawa sukaji Abin da sarki gulmanu yafada , . sai farinciki ya lullubesu Dalilin wannan farincikin kuwa shine izan har muddin sarki gulmanu ya kyalkyale da dariya haka kawai batare da wani daliliba , toh hakan na nufin yana marmarin yin kisa, Sannan kuma wannan kisan kowaye ya samu kashewa yake don ya kashe babban hakiminshi da kuma galadima duk ta dalilin wannan dariyar. . Shiyasa yanzu dayayi dariyar hankalin waziri ya dugunzuma ainun , amma koda yaji sarki ya ambaci abin dayasa shi wannan dariyar sai shima ya kamu da farinciki. . Sannan Gulmanu yace kayi sani yakai wazirina sannan kuma dirkar birnina Na samu macen da zan aura kuma ba wata bace illa Sarauniya Lasmin mai mulkin birnin Dimashka. . Koda waziri dariku tare da sauran fadawa sukaji abinda mai martaba gulmanu yafadi nan take suka shiga hankalinsu farincikin dake fuskarsu yakau sannan wani alama na tashin hankali ya ziyatarci fuskokinsu, nan take Gulmanu yacigaba da bayani sannan kuma kai waziri dariku kaine zaka wakilceni kaje birnin dimashka ka nemo min auren sarauniya lasmin,nan da kwana biyu zakuyi shiri kutafi izuwa birnin dimashka , . koda sarki gulmanu ya idar da maganarsa bai jira amsar da wziri zai basa ba ya tashi sannan yanufi cikin gidan sarautarsa Wannan shine Abun dayafaru abirnin ashdamir sannan afadar sarki gulmanu . . ¤¤¤¤. ¤¤¤¤¤. ¤¤¤¤¤ . . Al'amarin gimbiya suraila kuwa wato matar marigayi sarki ashbir yayin dataga wannan bishiyar ta rikide izuwa masifaffen wuta , sai ta rufe idanunta da tafukan hannunta. Don tagama sadakarwa cewa mutuwarta tazo, yayin da wannan wuta yai sama can kololuwar sama , . sai wata murya mara dadin sauraro maikama da karan aradu ta Barke da dariya sannan takara ta fashe da kuka ,haka tacigaba da kuka mai hade da dariya bayan tayi mai isanta sai tayi shiru sannan kakkausar muryar tafara magana; . ki yisani yake wannan bil'adama kin gama cutata Aduniya gabaki daya Amma kafin na hukuntaki,zan fadamiki sanadiyar wannan dariyar mai hade da kuka danakeyi, Da farko sunana sham'una da ga dubyalu sarauniyar bakaken Aljanu na duniya gabaki daya , Mun kasance muna bautawa wata gunkiyace wadda muke ta maciji sannan duk bayan sati muna yankamata bil'adama sannan jinin mu bata tasha. . Mahaifiyata ta gaji sarautar sarauniyar aljanuce a hannun kanin mahaifinta mai suna saxraz , Wata rana mahaifiyata tana fada anacikin fadanci sai ga wani manzo, Yana sanye da fararen kaya wadda akayimata ado da zubarjadi,sannan daura wata rawani wadda tarufe fuskarsa , . koda wannan bako yakaraso. Gaban mahaifiyata wato dubayalu , . Sai ya fito dawata takarda sannan ya mika mata , . Dubyalu tai ma magatakarda umarni akan ya amshi takardar ya Karanta afili Domin aji abinda ta kunsa. . Magatakarda ya amshi wannan takarda , Yafara karantawa kamar haka; . sako daga sarkin musulmai na bil'adama zuwa ga sarauniya dubyalu na bakaken Aljanu, kiyi sanicewa nasmi labarin cewa kina bin hanyar bata amma ban damu ba nace ma fadawana, . aiku Aljanu ne wata kila acikin Aljanu yan uwanku asamu wadda zasu nuna muku tafarkin Allah madaukakin sarki, Amma koda nasmi labarin jahilcin naki har yakai ga kina kamo bil'adama a cikin birnina kuna yankawa wannan gunkiya ta maciji,sai hankalina ya dugunzuma ainun , . Ina mai kira agareki yake wannan sarauniya daki bar wannan hanya dun bamai bullewa bane ,kidawo tafarki na gaskiya, Ki shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Annabi muhammadu(saw) manzonsa ne. . Izan kuma kikayi taurin kai Wato kika bujire zan zo da runduna in yakeki. . Sannan inkafa daular musulunci abirnin naki Daga sarkin musulmai Abul Abbas bin hafiz, sarkin birnin nurul Ansar. . . END OF BOOK 1 . SHIN SARAUNIYAR AlJANU ZATA AMINCE DA BUKATAR SARKI ABUL ABBAS . . WACECE SARAUNIYA LASMIN . SHIN ZATA AMINCE TA AURI GULMANU . . IZAN SARAUNIYA DUBYALU TAKI AMINCEWA DA BUKATAR SARKI ABUL ABBAS SHIN WANI IRIN YAKI ZA A KWAFSA . YAYA LABARIN SURAILA DA ALJANI SHAM'UNA . . SHIN WANI HUKUNCI NE ZAI MATA SANNA WANI LAIFI NE TAYI MASA Domin jin wayannan tarin amsoshi sai ku tareni a TAKOBIN JINI littafi na biyi MARUBUCI Shuraih Usman Shekarar rubutawa 2016 Hakkin mallaka (m) Shuraih Usman Copyright Shuraih Usman Company Shuraih 99% Don dauko wannan littafi a dama wasu littatafaina a matsayin pdf,doc,txt . Etc kuna iya shiga wayannan shafukan MY wepsites http://shuraihusman.blogspot.com/ http://shuraih99.nextwapblog.com/ http://shuraih+wapgem+com http://shuraih.waphall.com/ http://shuraih.faceblog.id/ http://Shuraih.nettmi.com/ http://shuraih.blogwaper.com/ http://shuraih.blogyz.com/ http://shuraih.blog48.com/ http://m.vk.com/shuraih99 Zaku iya bibiyana a facebook ko twitter, Facebook ID shuraih usman . Twitter ID shuraih_usman TAKOBIN JINI 2 Littafina biyu 2 complet Marubuci:- Shuraih Usman (c) shuraih 99% 2016 . TAKOBIN JINI»» . Littafi na biyu Marubucin Littafin Shuraih usman . Part 1⃣ . . Izan kuma kikayi taurin kai Wato kika bujire zan zo da runduna in yakeki. . Sannan inkafa daular musulunci abirnin naki Daga sarkin musulmai Abul Abbas bin hafiz, sarkin birnin nurul Ansar. . Koda mahaifiyata taji abinda wannan

Chapter 1 of 4