Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 5
gabanki dakuma yadda kika bani labarinki naji cewar kin rabu da daya 'yar taki wato usainar Dabira wacce kika bayar da ita ga 'yar uwarki Nuzaira. Tun daga sannan na ji na kamu da tsananin tausayinki da kuma kaunar dabira, shiyasa na rokeki akan cewa komai dadewa kada kisanar da dabira cewa bani ne na haifeta ba har sai bayan shekara ashirin alokacin da zatayi aure murabu da ita an nuna mini a mafarki cewa a gobe-gobennen allah zai kawo wani sadaukin jarumin musulmi daga can nashiya daban wanda yafi Dabira jarumtaka kuma suna haduwa zasu kamu da son junansu akan wannan daliline na yi kundun bala na shirya wannan haduwa tamu domin na bayyana miki sirrin zuciyata. Idan harkin amince da tayina ina son a daura aurena da ke gobe". Koda jin wannan batu sai humaira ta fashe da kukan farin ciki taji kamar ta rungume sarki raihan humaira ta budi baki domin tace wani abu sai kawai suka ga dabira ta fito daga cikin turakar humaira idanunta sun yi sharkaf da hawaye. Cikin firgici da matukar mamaki sarki raihan da humaira suka mike tsaye suka kura mata idanu. Dabira tasa hannu ta share hawayen ta sannan ta dubesu daya bayan daya tace, "me yasa kuka buye mini wannan sirri tsawon shekara da shekaru ? Na rantse da girman allah duk inda 'yar uwata take sai na tafi nemanta! Waye ya kashemini mahaifina? Kuma ko waye ya kashe mahaifina sai na bincikoshi duk inda yake na hallakashi! Ina tabbatar muku da cewa bazan taba yarda nayi aure ba face na cika wadannan burika ". Koda gama fadin haka sai taji ta tsani birnin kisra da duk mutanen cikinsa saboda jin cewa asalin mahaifiyarta humaira daga can take. Koda sarki raihan da humaira suka ga dabira ta fashe da kuka sai han kalinsu ya dugunzuma suka yunkura zasu je gareta domin su rarrasheta amma saita ruga waje da gudu ta nufi turakarta. Da zuwa sai ta shiga can cikin dakinta mai kofa ta rufe ta sake fashewa da sabon kuka. Cikin sauri humaira da sarki raihan suka karaso kofar dakin dabira suka yi ta rokonta akan ta bude kofar amma taki, duk suka hakura suka koma turakar Humaira suka zauna. Tsawon lokaci duk su biyun sukayi tagumi basu ce komai ba. Daga can sai sarki ya mike tsaye ya dubi Humaira yace, "yanzu muna cikin tashin hankali da damuwa saboda haka sai gobe naji amsar tayin dana yi miki " Koda gama fadin hakan sai sarki yajuya ya fice daga cikin falon gaba daya. I ta kuwa Humaira ta bishi da kallo kawai cikin damuwa da tunani. Har dare ya raba sosai Humaira bata rintsaba saboda fargaba da tunani bisa jin abinda Dabira tafada cewar duk inda 'yar uwarta take saita tafi nemanta kuma sai ta nemi wanda ya kashe mahaifinta. Shima shi. Abinda ya tayar wa da humaira hankali shine, tasan irin bala'in sarki Daksur da sadauki Zaihar da irin sadaukantakar da karfin tsafinsu,don haka yana tsoron karonta da su don tana ganin cewa zasu iya hallaka farat daya muddin ta kai kanta inda suke. Haka dai humaira ta kasance acikin tsananin tashin hankali ta kasa zaune ko tsaye ta dinga kai komo acikin turakarta. Tana cikin wannanhali ne ta tuno da batun tsoho kasim au yi ` yar hira nan take ta aiyana zuwa dakin tsoho kasim ta tasheshi koda kuwa barci yake yi. Batare da bata lokaciba humaira tafito daga cikin turakarta acikin dare da durfafi bangaren da dakin tsoho kasim yake duk inda ta ratsa sai taga dakaru a tsaitsaye suna kan aikinsu na gadi kuma gaba dayan gidan sarautar a haskake yake da fitilu gwanin ban sha awa duk inda tazo giftawa sai dakaru su ratse su bata hanya babu inda aka dakatar da ita har ta iso kofar dakin tsoho kasim. Da zuwanta sai ta iske kofar dakin a kulle take ruf. Haka ma gaba dayan tagogin dakin. Koda ganin haka sai jikin humaira yayi sanyi ta tuna cewa yau fa tsoho kasim acikin matukar gajiya yake sakamakon artabun da yayi da kurayen nan har maya sami raunika saboda haka bai kamata ta tasheshi daga barci ba nan take humaira ta juya da baya da nufin ta koma turakarta. Amma sai ta jiyo sautin kuka acikin dakin tsoho kasim kuma sautin na muryar mace ne. Al amarin daya matukar bata mamaki ke nan domin ita a saninta ai tsoho kasim ne aciki wannan daki to mene neya shigar da mace cikin dakinsa ? Cikin fargaba da sanda ta koma izuwa kofar dakinta leka ta cikin kafar kubar ai kuwa tana lekawa ta hango zabgegiyar kyakkyawar budurwa ta gaban kwatance zaune akan kujera tana faman sharba kuka a gefe daya daya ga wadannan tufafi na tsoho kasim ajiye a gefe daya wadannda akansu an dora layu da guraye na tsafi humaira ta kurawa fuskar budurwa idanu kawai sai ta lura da idanunta taga iri daya ne sak! Dana dabira. Koda ganin wannan al amari sai zuciyar humaira ta buga da karfi ta dafe kirjinta da hannayenta biyu ta juya baya cikin ajiyar numfashi tace a ranta. ” Duk yadda aka yi wannan yata ce ussainar dabira tazo mana a cikin kamannin tsoho kasim mene ya kawota garin nan ? Shin tazo neta cutardamu ko kuwa ta gano cewa mu jininta ne ta zo domin mu sadu ? ” Nan fa humaira ta kasa baiwa kanta amsar wadannan tambayoyi cikin tsananin fargaba da tashin hankali humaira ta koma dabaya don ta koma turakarta. Lokacin da ya rage saaura kiris ! Ta iske kofar turakarta sai kawai taga dabira tsulum ! A gabanta kamar daga sama ake jefota kafin humaira ta budi baki tace wani abu sai dabira ta dubeta tace. Yake ummata menene ya kaiki dakin bakonmutsoho kasim ? Kai sani sani cewa nida sarki duk bamu yarda da tsoho kasim Ba kuma na funkanci cewar akwai wata alaka tsakanin da shi. Da shi saboda haka gobe kafin na bar garin nan zaki yi mini cikekken bayani akan rayuwarki kafin ki baro birnin kisra ki da dawo nan misra da wannan kalami nake miki sallama allah ya tashe mu lafiya ” koda gama fadin hakan sai dabira tajuya ta koma izuwa cikin dakinta tamai da kofa ta rufe nan fa humaira ta sake rudewa ta kidime ta rasa abin da ke mata dadi a duniya domin bata san bayanin daya kamata ta yiwa dabira da sarki ba a goben. Da kyar humaira ta koma cikin dakinta ta kwanta taci gaba da tunani da zullumi. Har aka yi assalatu bata sami damar yin barciba. Kamar yadda humaira ta kasa barci hak shima sarki raihan ya kasa barci saboda tsananin damuwa har yaje masallaci da asuba. Ya dawo turakarsa bairintsaba. Itama dabira bata rintsa ba wato dai duk su ukun basu yi barciba amma wani ikon allah ita jaruma yazila batasan saadda barci yasace taba daf da lokacin daza ayi sallar asuba. Lokacin da aka idar da sallah a masallaci sarki ya waiga ko ina bai ga tsoho kasim ba sai jikinsa ya sake bashi lallai akwai wani boyayyen al amari a kansa don hak sarki na baro masallaci sai ya tura aka kirawo dabira yace da ita ta tafi izuwa dakin bako tsoho kasim ta fada dakin cikin shammace taga a halin da yake ciki domin baizo masallaci sallar asubaba lallai akwai wani abu na shin gaskiya a tare da shi. Domin tun da ya garin babu wanda ya ga yayi sallah koda jin wannan batu sai dabira tatafi izuwa dakin tsoho kasim a fusace wadansu dakarunta guda biyu na biye da ita. Tana sanye da hularta ta karfe. Da zuwan kofar dakin tsoho kasim sai tasa kafarta guda ta daki kofar. Take kofar ta burma ciki ta fadi kasa. Karar dukan kofar na yasa yazila ta farka firgigit! Kafin tayi wani yunkuri sai kawai taga jaruma dabira tare da dakartunta biyu tsaye akanta rike da makamai koda su dabira sukayi arba da yazila sai suka cika da tsananin mamaki. Gashi dai agefe daya kuma suka ga wannan tsufaffun kayan tsoho kasim ga layu da gurayen tsafi akansu sai al'amarin ya daure musu kai. Nan fa Dabira ta kurawa yazila ido tana tunani a zuciyarta. Abinda ya fadomata a rai shine, ta san fuskar yazila tun da sun gwabza yaki ba sau dayaba, amma bata taba yimata kallon kurilla ba sai yau. Tabbas dai yanzu ta gane cewa abokiyar gabarta ce tayi bad-da-kama ta shigo birninsu domin ta cutar dasu. Amma kuma me yasa a bokiyar gabar tata take kama da ita? Anya kuwa yazila ba ita ce 'yar uwarta ba? Ai waka abakin mai ita tafi dadi,bari naji daga bakinta. Nan take dabira ta dubi yazila tace, "wace ce ke, kuma meyasa kika batar da kamanninki kika shigo birninmu?". Koda jin wannan tambaya sai yazila ta bushe da dariya tace, "Nice jaruma Yazila babbar abokiyar gabarki! Kuma na shigo wannan birnin naku ne domin kawai nayi yakin karshe dake mu bambance tsakanin aya da tsakuwa!!!". Da jinhaka sai itama Dabira ta bushe da dariya sannan ta hade rai tace, "ke tsohuwar abokiyar gaba kiyi sani sani cewa kinka wo kanki GIDAN MUTUWA! Lallai bazamu kashekiba da azaba ko taron dangi ba, lallai nida ke zamu raba raini a yau dinnan. A matsayin ki na mai laifi, dole ne yanzu nasa a kamaki akaiki kurkuku a tsare ki inyaso yau da farkon yamma yammaci afito dake izuwa filin fada inda zamu fafata yakin karshe ni dake inda za arufe mu a cikin keji har sai dayanmu ya wanda duk ya rayu sai ya bude kejin ya fito. " Koda gama fadin hakan sai dabira ta dubi dakarunta dake tare da ita tace dasu su sawa Yazila ankwa sannan su tafi da ita kurkuku, Bisa mamaki sai dabira taga yazila ta tsaya kyam! Ansa mata ankwa a hannayenta da kafafunta batare da tayi wani yunkuriba sai murmushi kawai take har aka tusa keyarta a gaba aka tafi da ita. Al'amarin daya matukar jefata cikin tsananin mamaki kenan da wasi-wasi domin a sanin dabira yazila jarumace ta gaske ko ita kanta bata isa tasa mata ankwa ba cikin sauki, amma sai gashi dakarunta sunsa mata ankwar sun tafi da ita. Abin dabata saniba shine yazila tana sane ta saki jiki aka kamata saboda dalili uku. Dalili na farko shine tana son su fafata yaki domin dabira ta cire mata wannan laya dake wuyanta dalili na biyu shine tanason takai dabira kas har ta cire wannan hular karfe ta kanta domin taga kamanninta dalili na uku shine bata son dabira tace zata bita sutafi izuwa birnin kisra don daukar fansa akan sarki daksur shiyasa taki gayamata cewa ita yar uwartace ta jini Bayan an tafi da yazila izuwa kurkuku sai dabira ta tattara wadansu layu da guru na tsafi ta kunna musu wuta nan take suka kune kurmus ! Suka zama toka. Har tajuya zata fita daga cikin dakin sai taga jakar guzurin yazila a rataye ajikin bango kai tsaye ta nufi inda jakar take zata dauko ta duba abin dake ciki sai kawaitaji an kira sunanta. Tana waigowa sai taga ashe sarki raihan ne a tsaye da kansa. Sarki raihan ya dubeta fuskarsa babu walwala yace " yan zu kin daina fushi damuzaki iya sauraron bayanin dazan yimiki ?” Koda jin haka sai idanun dabira suka ciko da kwalla. Tace. ” Ka gafarceni yakai abbana. Kayi sani cewanima nayi nadamar nuna muku fishina. Ina fatan zaku gafarceni ? ” Koda jin wannan batu sai sarki raihan yayi murmushi yace. ” Babu komai yake. Yata yanzu dai kizo muje fada akwai wani gagrumin abu daya taso wanda zamu zauna mu tattau tare da sauran yan majalista hukuncin da kika yanke yanzu akan wannan abokiyar gaba tamu dataso ta yaudaremu yayi kyau ”. Koda jin haka sai dabira ta taho wajen sarki raihan ta ruke hannunsa suka jera suka fice daga cikin dakin ya zamana cewa gaba daya ta manta da batun wannan jaka ta yazila. Ita dai wannan jaka babu komai a cikinta face wadansu kayayyakin tarihi wadanda da zarar humaira tayi arba zata shaidasu. Domin kaya nena yar uwarta nuzaira wanda ayanzu haka tana da irinsu aajiye kuma kullum sai ta kallesu don tunowa da yar uwarta ta. Banda wadanda kayan tarihi kuma. Akwai rigarda aka sawa yazila aranda aka haifeta kuma dabira ma tana da irin rigar wacce har yanzu humaira nanan da ita aajiye don tarihi. Dabira ta sha ganin humaira tana dauko rigar tana kallenta kawai har tana kwallah amma duk saadda ta tambayeta dalili sai tace da ita kawai ta tuno wahalar data sha ne a lokacin data sami cikinta saadda ta haifeta. Lokacin da sarki raihan da jaruma dabira suka iso fada sai suka iske gaba dayan yan majalistar a zaune. Suna jiran karasowarsu al amarin daya razana dabira kenan domin ta san cewa duk saadda taga yan majilista sunyi irin wannan taro ya zamana cewa kowa ya zo to lallai akwai wani abu gagarumi al amari daya taso. Ko dai annoba ta barko. Ko kuma yaki zaayi. Da shigowar dabira da sarki cikin fadar sai suka je suka zauna inda suka saba zama. Zaman su keda wuya sai wazirin sarki Raihan yayi kyaran murya sannan yace, "yaku 'yan majalissar wannan birni namu mai albarka, da yawa daga cikinku sun san dalilin taruwarmu anan. Ga wadanda basu saniba, yanzu sai su sani. Wannan al'amari ba komai bane face a yau dinnan kimanin sa'a daya data shude mun sami rahoton cewar abokan gabarmu mutanen birnin kisra sun taho da zugasama da dakaru miliyan dari hudu da hamsin domin su yakemu. Wannan zuga ta hada da dakarun gudummawa daga sauran kasashen kafirai na wannan nashiya, kuma sun taho da alwashin cewa wannan karo adan za a shekara ana wannan yaki bazasu janyeba har sai sun tabbatar da cewa sun baje birnin mu sun kashe mazajenmu sun kama matayenmu da yaranmu a matsayin bayi sun kwashe dukkan dukiyoyinmu. Ku sani cewa adadin wadannan dakarun abokan gaba ya ninka namu sau goma, wato gaba dayanmu bamu wuce kaso daya ba a cikin kaso gomansu ba. Yanzu menene abinyi? Tabbas idan muka ce zamu fita mu tari waddannan abokan gaba za su iya murkushemu a cikin dakika kadan. " Sa'adda waziri yazo nan a jawabinsa sai Jaruma Dabira ta mike tsaye zumbur! A fusace, kuma ta zare takobinta a lokacin da jikinta ya kama tsuma. Cikin fushi ta dubi waziri tace, "yakai waziri kayi sani cewa bamu da wani karfi wanda yawuce karfin allah katuna cewa bayau ne karo na farko da muke fita yaki da abokan gaba da kuma ya zamana sun fimu yawa, amma sai kaga mun yi RAGAS dasu kokuma musami nasara akansu. Duk bawan da yayarda da allah kuma ya sallama al'amuransa a gareshi tabbas allah zai iya masa abinda ya gagareshi. Ina tabbatar muku da cewa koda abokan gaba yawansu ya kai cikin duniyar nan gaba daya idan ni kadai ce na rage musulma a wannan birni na rantse da girman Allah sai na fita na yakesu dan kare martabar addinin allah koda kuwa zasuyi gutsin-gutsin da sassan jikina. Na sani nan dagobe wadannan abokan gaba zasu iso kofar birninmu don haka zan jagoranci dakarunmu mufita mu yakesu wanda duk yake ganin zai bi bayana yabi, wanda ba zai bi ba yayi zamansa!". Koda dabira tazonan azancenta sai sarki Raihan ya zare takobinsa yace, "Ina bayanki ya ke 'yata, lallai dani za ayi wannan yaki gobe!". Koda ganin haka sai fiye da rabin 'yan majalissar ma suka yi abinda sarki raihan yayi. Kalilanne daga cikinsu basu yi hakan ba, domin sun gama tsorata da wannan yaki daza ayi, kuma imaninsu ya raunata. Wannan shine a binda ya faru a fadar sarki raihan bayan 'yan majalisar kasar sun yi taro na musamman. Al'amarin yazila kuwa, lokacin da aka kaita kurkuku aka kulleta sai taji ko kadan bata damu ba face kawai tana zumudin yamma tayi a fito da ita a kaita filin fada inda zasu yi yakin keji ita da jaruma Dabira. Har rana ta take Yazila ta kasa tsaye ta kasa zaune a cikin kurkukun. A lokacin ne aka kawo ma ta abincin rana. Ko kallon abincin batayi ba bare ma taci. Ai kuwa bayan an idar da sallar la'asar da kimanin rabin sa'a sai aka bude kofar kurkukun aka tasa keyar yazila izuwa fada. Tana tafe tana jan sarkar da aka daure kafafunta da hannayenta, dakaru na biye da ita. Lokacin da aka iso filin fadar da jaruma YAZILA sai taga filin fadar ta cika makil da jama'a fiye da kullum, harma mutane sun rasa inda zasu tsaitsaya sai akan katangau. A tsakiyar fadar kuwa, an ajiye wannan katon kejin karfe mai tsawo da fadi wanda aka yi masa 'yar karamar kofa ta shiga. A can gefe daya kuwa, sarki RAIHAN ne da 'yan majalisarsa a zaume kuma daf da shi JARUMA DABIRA ce a tsaye cikin gagarumar shigar yaki fuskarta a rufe cikin hular karfe kamar kullum. Koda aka ga anzo da YAZILA sai aka yi sauri aka bude kofar wannan keji. Cikin hanzari aka kwancewa yazila sarkokin dake hannayenta da kafafunta aka bata takobi sannan aka ingizata izuwa cikin kejin. Nan take Jaruma Dabira ma ta baro inda su sarki suke ta nufi inda kejin yake. Koda ganin haka sai fadar ta rude da kabbara aka rinka yiwa Dabira Jinjina har ta shiga cikin kejin aka rufe kofar kejin. A sannan ne aka yi tsit! A fadar gaba daya tamkar mutuwa ta gifta. Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin jaruma Dabira da Jaruma YAZILA. Jaruma Dabira ta dubi yazila cikin murmushi tace, "yau mun hadu a inda babu damar gudu, kuma babu yankewar yaki face dayanmu ya sami nasara akan daya. Ina so ki sani cewa tuni na kona gaba dayan layoyinki da gurayenki na tsafi yanzu dame kuma za kiyi dogaro?". Koda jin wannan tambaya sai Yazila ta bushe da dariya tace, "ke yarinya, aikin kashe micijine baki sare kansa ba. Kin ga wannan laya dake wuyana wani malami ma'abocin addininku ne ya bani ita bayan an bashi dukiya mai tsananin yawa. Kuma ya tabbatar mini da cewa in dai ina tare da ita babu wani mahaluki daya isa ya sami nasara akaina ". Koda jin haka sai Dabira ta fusata ta zare takobinta ta afkawa yazila suka ruguntsume da azababben BAKIN ARTABU wanda ya dugunzuma hankalin kowa a wajen, domin su biyun babu wanda ke da alamun samun nasara akan abokin gwaminsa. WAYE ZAI SAMU NASARAR WANNAN GAGARUMAR HADUWA DA AKAI ? SHIN DABIRA ZATA CIRE LAYAR WUYAN YAZILA ITAKUMA TA CIRE HULAR KANTA? IDAN SUN SAMI NA SARAR HAKAN ME ZAI FARU ? YAUSHE ZA A KWABSA YAKI TSAKANIN RUNDUNAR BIRNIN KISRA DA RUN DUNAR BIRNIN MISRA? A WANNE HALI HUMAIRA MAHAIFIYAR DABIRA TAKE CIKI? SHIN DABIRA DA YAZILA SUNA GANO CEWA SU 'YAN UWAN JUNANE ? IDAN SUN GANO ZASU JE DAUKAR FANSA ABIRNIN KISRA AKAN SARKI DAKSUR? Muhadu a littafi mai suna BAKIN ARTABU don jin cigaban wannan kasaitaccen labari Alham dulillah a yau na kawo karshen littafin jaruma yazila 1-2-3 kamar yadda nagaya muku tun farko shine a hannuna ban sami cigaban saba amma idan na sami cigabansa zan kawo mukushi. Na ku BASHEER ISHAQ TOKARAWA BASH I TKRW 08105808371 JARUMA YAZILA Littafi na Uku Na Abdul'aziz sani madakin gini Created and design by:- Shuraih Usman Publishing shuraih 99% From http://shuraih.wapsite.me To download more Ebooks follow this link http://shuraih.wapsite.me An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 5 of 5