Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 5
hada jini da mutum sai kaga wani abu ya zamo iri daya da nasa bare kuma ni da 'yar uwata mun kasance tagwaye ai dole ne asami kama ni da ita kamar yadda kika bani labari cewa tamkar an tsaga kara muke. " Nuzaira tayi ajiyar zuciya sannan tace, "nidai na umarceki da kada ki kuskura kice zaki ce zakiyi wannan ta fiya izuwa birnin misra kuma ina mai gargadinki da kada ki kuskura kice zaki je kiyiwa sarkin yaki zaihar wani abu, domin kina tabashi mijina da sarki daksur zasu gane cewa na sanar dake sirrin rayuwarki don haka komai zai iyafaruwa a gareni. Yake yazila ki tuna cewa nice na shayar dake harkika girma kika zama mutum, ki tuna nice naci kashinki, na sha fitsarinki, kuma nice na sha wahalar renunki idan kika bari su sarki daksur suka cutar dani lallai kinci amanata kuma kinci amanar zumuncin dake tsakanina da mahaifiyarki." Koda gama wannan jawabi sai nuzaira tayi shiru bata kara cewa komai ba , sannan ta mike tsaye ta fice daga cikin dakin ta bar jaruma yazila a zaune cikin tsananin damuwa, gami da tunani mai zurfi.Haka dai yazila taci gaba da sake-sake acikin zuciyarta ta kulla wancan ta kwance wancen har dare yaraba ya zamana taka sayin barci sai kai kawo kawai takeyi acikin dakin nata tana zarya. Bayan tayi dogon nazari da tunani akan abinda zai fishsheta sai taje ta dakko takadda da alkalami ta rubuta wata wasika ta ajiye a karkashin matashin kanta sannan ta cire kayan jikinta ta sanya wadansu bakaken sulke na yaki ta dauki makamanta na yaki ta soke a jikinta nan take tayi girgiza bace bata bayyana ako ina ba sai a kofar gidan sarkin yaki zaihar da baiyanarta sai taga masu gadi a tsaitsaye suna kan aikinsu kai tsaye jaruma yazila ta durfafosu koda masu gadin suka hangota sai suka cika da tsananin mamaki bisa ganinta a cikin wannan lokaci na tsawon dare cikin ladabi da biyayya masu gadin suka risina suka gaisheta yazila ta dubeshi a fusace tace kubude mini kofa da salama na shiga dfomin naga mai gidanku idan kuma kuka yi gardama yanzun nan takobina zata sha jininku !“. Koda jin wannan batu sai jikin masu gadin ya kama karkarwa cikin firgita sukayi sauri suka bude mata kofar ta kunna kai ciki da shigar yazila cikin gidan sai tazare takobinta taci gaba da kutsa kai tana leka cikin dakunan gidan domin taga inda sarkin yaki zaihar yake. Karar zare takobin yazila daga cikin kubbenta ne yasa sadauki zaihar ya bude idanunsa alokacin da yake kwance tare da matarsa acikin turakarsa dama bai dade da kwanciya ba bisa bata lokaci da yayi wajen bincike a hallarar tsafinsa. A cikin binciken da yayi ya ga wata gagarumar masifa dake shirin afko masa amma sai ya kasa gane irin masifar da kuma lokacin dazata zo masa abin da ya saya kasa barci ke nan ya kwanta kawai yana tunani cikin fargaba. Koda zaihar yaji karar zare wannan takobi sai yayi wuf ya mike daga kan gadonsa yayi sauri yasanya kayan yakinsa sannan ya zare tasa takobin ya fita waje yana neman wanda ya shigo masa gida cikin wannan tsohon dare. Lokacin da jaruma yazila ta shigo cikin wani katon falo na gidan wanda babu komai acikinsa face shimfidar jan kilishi mai taushi da kujeru na alfarma sai tayi kicibus ! Da sarki yaki zaihar tsaye ruke da takobi a wannan lokaci falon a haskake yake dahasken fitilu tazarar dake tsakanin zaihar da yazila bata wuce taku asirin ba. Koda zaihar ya ga ashe yazila ce ta shigo masa gida acikin wannan dare sai ya cika da tsananin mamaki kuma yaji ajikinsa cewa lallai ba lafiya ba akwai wani abin daya faru da dai dai ba saboda haka saiya tsaya a inda yake ya dubeta yace yake halifata mene ne ya kawoki gidana a wannan dare?“ Yazila ta dubi zaihar a fusace tace ,“ nazo na dauki fansar mahaifina dakakashe ne ya kai babban azzalumi !“ Cikin matukar mamaki zaihar ya dakawa yazila tsawa yace ,” wannan kuma wacce irin maganar banza kikeyi ? Shin ke ba yar mai girma barzuk bace ? Yaza ayi kice na kashe mahaifinki alhalin barzuk na nan araye ?”. Dajin haka sai hawaye ya zubowa yazila tace ” Kayi tunani izuwa shekaru goma sha takwas baya lokacin da kabi bayan hukairu dan uwan barzuk sa adda ya gudu tare da iyalinsa izuwa birnin misra daf da kofar birnin misra kuka fafata yaki kai da matarsa humaira tan goye da jaririyarta to ka sani cewa wannan jaririr yar uwata ce mun kasance tagyaye nida ita kuma hukairu ne ya haifemu ita kuwa nuzaira abin data haifa mutuwa yayi sai humaira taba ta daya daga cikin tagyayen data haifa kuma ni ce jaririyar da aka bata kagake nan hukairu shine mahaifina ba barzuk ? Lallai mahaifina ka kashe , babu makawa sai na dauki fansa a kanka kuma a yanzu ”. Sa adda yazila tazo nan a zancenta sai sarkin yaki zaihar ya bushe da mahaukaciyar dariya. Ya ce ” yake yarinya karyarki tasha karya. Ba a zama wane a banza. Kafin na sami wannan matsayi na sarkin yakin birnin kisra sai dana taka mukamai masu daraja da yawa kuma sai dana sha bakar wahala. Duk abin da kike takama da shi a yanzu na mallakeshi tun kafin kizo duniya saboda haka yanzu ga fili ga mai doki idan kina ganin zaki iya daukar fansar mahaifinki ki jarraba ki gani ina tabbatar miki da cewa kamar yadda na kashe mahaifinki haka kema zanka sheki !”. Kafin zaihar ya gama wannan jawabi tuni zuciyar yazila ta fara tafarfasa kawai sai ta dag takobinta sama ta ruga gareshi shima sai ya daga tasa sama ya rugo gareta suna haduwa kowanne su ya kaiwa dan uwansa mugun sara kowannensu ya kare saran da takobinsa da takobinsa tara tsatsin wuta ya fantsama izuwa kas. Nan fa suka rugunzume da azababben yaki ya zamana cewa suna kaiwa juna sara da suka cikin tsananin zafin nama juriya da bajinta. Wohoho ! Idan sabon hannu da tsohon hannu akahadu a gumurzu dolene aga tsagwaran jarumta t ban al'ajabi. Ita yazila tana ta kama da kuruciya gami da sadaukan taka ta zamani shikuwa zaihar yana ta kama da kwarewa da sanin makama ne. Da dabarun yaki irin na tsofaffin sadaukai inda aka sami babban bambanci shine, ita yazila tafi zaihar juriya da dadewa ana gumurzu, shi kuma yafi ta zafin nama. Sai da aka shafe rabin sa'a ana wannan gumurzu dayansu bai sami na sarar komai ba, ya zamana cewa dauki ba dadin da sukeyi yasa gaba daya hadiman gidan sun rugo izuwa falon da suke fafatawa a dimauce. Itama matar zaihar saita farka daga bacci a firgice ta ruga izuwa dakin da danta ke barci, wani karamin yaro dan shekara hudu kawai, saita sungumi yaron a kirjinta taruga izuwa falon da ake gumurzu tsakanin yazila da zaihar. Dazuwa sai ta iskesu cikin masifaffen artabu. Gaba daya hadiman gidan sun ra kabe a tsorace suna kallon abin dake faruwa. Nan fa itama matar zaihar ta kasa yin komai saita tsaya ka wai tana kallon fafatawar cikin tsananin tsoro da fargaba da mamaki bisa ganin wacce ke gumurzu da mijinta. Saboda zafin naman zaihar sai ya shammaci yazila ya yanketa acinya. Kafin tayi wani yunkuri ya sake yankarta a damtsen hannunta na hagu. Bisa dole yazila tayi alkafira da baya ta koma nesa kadan da shi ta durkushe kasa bisa guiwowinta a lokacin da ta dafe raunikan jikinta biyu cikin jin zugi da radadi. Koda taga jini na zuba saita fusata ainun kuma tayi sauri. Ta daure raunikan da wani tsumma dake daure a kugunta. Ka wai sai ta mike tsaye ta sake zare wata takobin a kuibin cinyarta ta hagu ya zamana cewa ta hada takubba biyu ahannunta. Koda ganin haka sai shima zaihar yaciro wani gatari dake rataye a bayansa ya hada da ta kobin hannunsa ya fuskanceta. Kawai sai yazila ta rugo gareshi suka sake kacamewa da sabon azababben yaki amma awannan karon sai yazila ta sauya salon fadan ya zamana cewa tana tsalle tana alkafira a kasa da sama. Nan da nan kuwa ta ruda zaihar, bai ankara ba sai yaji ta dan kara masa sara acinyarsa. Take wajen ya dare jini yayi tsartuwa. Zaihar ya rankwala uban ihu yatafi da baya taga-taga ya fadi Koda matar zaihar taga abinnda aka yiwa mijinta zaihar sai itama tarusa ihu ta fashe da kuka. Yazila ta kara rugowa da gudu izuwa kan zaihar ta ci gaba da kaimai sara da suka cikin iya zafin namanta bata yarda ta bashi damar da zai daure raunin nasaba. Nan fa jini ya cigaba da zuba daga cinyar zaihar har jiri yafara dibarsa amma saboda naci da juriya irinta 'YAN MAZAN JIYA sai yaci gaba da yakin a haka. Ya yin da zai har ya fus kanci cewa idan akaci gaba da wannan gumurzun a haka har izuwa wani lokaci mai tsawo zai iya gala baita yafadi saka makon jinin dake zuba a kafarsa sabo da haka sai ya fara amfani da karfin sihirinsa yana watsawa yazila mugayen abubuwa kamar; masu, wuta, kibiyoyi da sauransu. Bisa mamaki sai yaga tsafin baya tasiri ajikinta, domin karfin sihirin nasu yazo daya duk abin da ya watsa mata sai itama ta watso masa irinsu sulalata juna. Al'amarin daya dugunzuma hankalin zaihar kenan ya tabbatar da cewa bashi da wata mafita face yayi amfani da iyakar karfin dmtsensa da kwarewarsa ta yaki. Bisa dole yakara ZAGE DAMTSE suka cigaba da bakin gumurzun, yazamana cewa ta shi hankalin komai da kowa dake cikin falon. Sai da suka shafe sa'a biyu suna wannan gumurzu ya zamana cewa kowannensu yasake samun nasarar yiwa abokin gwamisa rauni. Zai har ya sami nasarar saranta a kirji, ita kuma ta sami nasarar sokarsa agefen kirjinsa na dama alokaci guda duk subiyun suka kwala ihu suka ja da baya taga taga kamar zasu fadi amma sai suka sake rugowa suka kacame da a zababben yaki. Hakika idan mutun ya ga irin wannan juriya, naci da jarumta irin ta zaihar da yazila dolene ya jinjina musu ya tabbatar da cewa sun cika zaratan sadauki ababan misali. Bayan sun dada kwarmazuwa bisa hadawa da naushi da bugun juna sai suka jigata ainun ya zamana cewa da kyarma suke kaiwa juna hari. Duk wannan abu dake faruwa matar zaihar na rakabe a gefe daya rungume da danta ta na kallongumurzu cikin ta shin hankali kuma tana kuka. A na cikin wannan fafatawar ne duksu biyun sukA yiwa juna wani irin mugun naushi a fuskokinsu har jini yai tsartuwa bakunansu suka zube kasa kafin yazila tamike tsaye sai zaihar yayi sauri ya zaro wata wuka siririya mai kaifi da atsini ya wurgawa yazila wutar da tafi tsananin gudu zata cake ta cafi wukar ta maida ita inda aka jehota nan take tsinin wukar ya lume acikin goshin zaihar nan take zaihar ya sulale kasa matacce koda ganin abin daya faru sai matar zaihar ta kwala ihu ta rugo kan gawar mijinta ta ajiye danta a gefe daya ta rungume gawar tana kuka sauran hadiman gidan kuwa sai suka firgice suka kama guje guje suna ficewa daga cikin gidan gaba daya jaruma yazila ta yaka kafafunta da kyar ta nufi inda matar zaihar take koda ganin haka sai matar zaihar ta dago kai ta dubeta ba tare da tsoron komai ba tace.” Yake dirkar birnin kisra ma za ki kasaro ki kasheni ni da dana domin na huta da wannan abin takaicin da kika bar mini ban ga amfanin rayuwarmu a duniya tun da kin yanke mana farin cikin rabamuda masoyinmu. ”. Yazila tayi shiru bta ce komai ba har ta iso kan gawar zaihar kawai saitasa hannunta ta zare wannan wukar wacce ta lumamai acikin goshin zaihar sannan ta dubi matarsa a lokacin da hawaye ya zubo mata. Tace ina bukatar alokacin wannan wuka domin da sonki san cewa bazan kashe kiba kuma bazawara kamar yadda uwata humaira ta zama bazawara kuma inason wannan da naki ya zama maraya kamar yadda ni da yar uwata muka zama marayu ina son ki isar da sakona ga sarki daksur cewa ni “jaruma yazila ” na kashe sarkin yaki zaihar bisa sanin cewa shi ne ya kashe mahaifina na gaskiya bisa umarninsa don haka ya saurari ranar da zanzo daukar fansa a kansa ki sanar dashi cewa na san sirrin layar da suka rataya mini a wuya tun ina jaririya kuma na tafi inda za ayi cire mini layar koda gama wannan furuci sai jaruma yazila ya goge jinin dake jikin wannan wukar daga jikinsa ta daura a kugunta kawai sai ta juya ta fite daga cikin gidana tana tafe tana tangadi ita kuwa matar zaihar sai ta bita da kallo kawai cikin tsananin mamaki bisa jin abubuwa data zaiyano mata a matsayin sako sarki daksur. * * * Al'amarin hadiman gidan zaihar kuwa, dasu da masu gadin gidan Bayan yazila ta sami nasarar kashe maigidansu Sai suka ruga da gudu izuwa gidan sarki daksur suka isar da labarin abinda ya faru ga man yan hadiman gidan. Ai kuwa acikin wannan dare labari ya riski sarki Daksur. Cikin tsananin firgici da dimauta sarki daksur yamike zumbur yayi shigar yaki ya jagoranci dakaru dubu a shirin da kansa acikin dare suka bazama neman jaruma yazila acikin birnin kisra amma sai da suka duba ko ina basu gantaba. Shikuwa hakimi barzuk yajin labarin abin da yafaru sai ya ruga izuwa dakin yazila a fusace rike da takobi. Da shigarsa cikin dakin sai ya iske matarsa nuzaira atsaye rike da wasika tana karan tawa tana zubar da hawaye cikin fushi barzuk ya fisge ta kardar ya karanta jawabin dake cikinta kamar haka. YAke ummata ki gafarceni bisa abinda zan aikata. Kiyi sani cewa bani da wani zabi face na aikata hakan kuma ki gayawa mijinki da sarki daksur abinda ya faru da sarkin yaki zaihar suma yananan tafe garesu nan da wani lokaci a ko yaushe kuma ina gargadinsu akan idan suka taba lafiyarki nima saina taba lafiyar dukkanin danginsu, sai na tabbatar da cewa na share dukkanin zuri'arsu daga doron kasa. Idan har sun matsu. Da son ganina su nemeni acan birnin misra..........." Koda barzuk yazo nan akara tun wasikar sai zuciyarsa ta kama ta farfasa kamar zata kone. Saboda tsananin fushi da bakin ciki ka wai sai yasa hannu ya fyade nuzaira ta fadi kasa sumammiya. Nan take ya kwalawa wasu hadi mansa kira yace su dauki nuzaira su kaita can babban kurkuku na kasar suce asamata sarka atsareta har sai ranar daya nemeta. Nan take kuwa wadannan hadiman suka cika wannan umarni. Bayan hadiman sun tafi da nuzaira sai yafita da sauri ya hau dokinsa yatafi gidan sarki da zuwansa kuwa ya iske sarki daksur ya dawo daga neman gimbiya yazila bai gantaba. Yana zaune a fada shi kadai cikin tsananin fushi tamkar zai kona gidan sarauta gaba daya barzuk ya zube kasa gaban sarki daksur ya sunkui da kansa kas cikin tsananin ladabi alokacin da gaba daya jikinsa ke karkarwa don tsoro kada fushin sarki ya kare a kansa Bazato ba tsammani sai barzuk ya bushe da ma haukaci yar dariya. Al'amarin daya matukar bashi mamaki ke nan ya dago kai a tsorace yana kallonsa. Sarki daksur ya turbune fuska sannan yace , "hakika matarka taso ta watsa mana dukkan shirimmu ta tona mana asiri bisa sakacinka na kula da sa ido akanta. Hakika in ba don kayi mata hukunci ba da kanka kasa ankaita kurkuku da tuni kai da ita duk nayi muku hukuncin kisa. Bisa bincike da nayi a halin yanzu na gano cewa tuni jaruma yazila tayi nisa da barin wannan birnin wannan kasa tamu saura tafiyar kwana daya da yini daya jal ! Ta isa kofar birnin misra. Jaruma yazila tana da matukar karfin sihirin tsafi don haka bani da wa dansu hadiman aljanu da zan turasu su hallakata kafin ta isa cikin birnin misra. A cikin binciken da na yi na gano cewa idan ta shiga cikin birnin misra bazata sami nasarar samun abinda taje nemaba. Kuma zata sha tsananin wahala wacce zata iya zama sanadin ajalinta. A kwai wani lokaci da zaizo muyi yakin karshe da sarki raihan na birnin misra a wannan yaki ne zamu sami nasara akansa mukama birnin nasa gaba daya a sannanne zamu shiga har cikin birnin mukama yazila da mahaifiyarta humaira sannan mu binciko duk inda 'yar uwarta take dabira itama mu hallakata. " Sa'adda sarki daksur yazo nan azancenta sai farin ciki ya lullube barzuk bai san sa'adda ya bushe da dariyar murnaba. Nan fa duk su biyun suka ci gaba da kyakyata dariyar kamar bazasu dainaba. A dai-dai lokacinne matar zaihar ta shigo cikin fadar ita kadai rungume da danta tana zubar da hawaye. Batare da fargabar komaiba ta iso har gaban sarki Daksur ta risina ta kwashi gaisuwa sannan ta zaiyana musu sakon da jaruma yazila tabata. Koda matar zaihar ta gama jawabi sai jikin sarki daksur ya kama tsuma. Nan da nan zufa ta karyo masa. Zuciyarsa ta kama bugawa da karfi kamar zata fado kasa cikin tsananin zafin nama ya zare ta kobinsa ya fille kan matar zaihar ta saki dan dake hannunta ya cafeshi da hannu daya. Gangar. Jikin matar zaihar ya sulale kasa alokacin da dan nata ya fashe da kuka. Sarki daksur ya yunkura zai sare kan dan sai barzuk yace, "kayi masa rai ya shugabana ai kankanin yarone"Sarki daksur ya sauke takobinsa kasa sannan ya bushe da dariyar mugunta ya killata barzuk wannan yaro ya cafe yace dashi katafida shi izuwa gidanka ka raineshi ya taso a cikina bayinka masu yi maka hidima hakika mahaifiyarsa ta cuceshi data sayi ajlinta a lokacin da yafi bukatarta a rayuwa tayi kuskure babba da tazo gabanmu da mugun lafazi domin itace mace ta farko datata ba zuwa gabana ta fadi mugun sako. “ Koda gama wannan ne abin daya faru sarki barzuk ya nufi hanyar fita daga fadar rike da wannan yaro yana ta tsala kuka bai fasaba. “ Wannan shi ne abin daya faru a birnin kisra tsakanin jaruma yazila dasu sarki daksur bayan ta sami labarin asalinta. Acan birnin misra kuwa tun kimanin shekaru sha takwas da suka gabata wato a lokacin da sarkin yaki zaihar ya kashe hukairu a gaban matarsa humaira saita ruga da gudu izuwa kan gawar mijinta a lokacin da masu gadin kofar birnin suka rugo izuwa wajen suka. Kewayeta suna kallonta kawai cikin alamun tausayawa domin sun fahimchi cewa mijinta aka kashe. Kuma ga jaririya a goye a bayanta. Bayan humaira ta dade tana kuka har ta gaji sai wadannan dakaru suka haka kabari suka binne gawar hukairu a gabanta sannan suka shigar da ita mata jagora har izuwa cikin birnin misra daya daga cikin yayi masa bayanin duk abin daya faru ga humaira a gaban idanunsa bayan wannan badakare ya gama jawabi sai sarki raihan ya dubi humaira cikin alamun tausayawa yace wannan bakuwa ina mai yi miki marhaba izuwa wannan birnin. Namu mai albarka wato birnin misra kiyi sani ma abota addinin musulunci ne kuma bisa tafarkin addininmu bamu yarda da zalunci ba saboda haka muna son kibamu labarinki iyakar gaskiya bisa abin dake tsakanin da wancan mutumin wanda ya biyoku har izuwa kofar wannan birnin namu ya kashe mijinki kuma igudu idan har kina da gaskiya akansa da iznin ubangiji duak inda ya gudu zamu tura a kamoshi domin ayi masa hukunci dai dai da laifin da ya aikata kafin sannan muna son muji sunanki da kuma sunan garin da kika fito. “ Lokacin da sarki raihan yazo nan a zancensa sai humaira ta sunkai da kanta kas kamar bazatace komai ba kuma taji tsoroya shigeta bisa sanin irin tsananin gabar dake tsakanin birnin kisra dabirnin misra amma data tuna cewa sarki raihan yace shi mai adalci ne sai taji dukkanin tsoro ya kau daga zuciyarta nan take ta baiyana masa sunanta da kuma kasardata fito. Koda jin haka sai gaba dayan jikin sarki Raihan yakama tsuma, idanuwansa suka kada, zuciyar sa takama tafarfasa kamar zata kone bisa jin sunan kasar mutanen dasuka zamo sana diyar mutuwar 'yar uwarsa guda daya jal a duniya wadda yake matukar kauna fiye da komai a rayuwarsa. Cikin tsananin fushi sarki raihan ya kai hannunsa izuwa kan kuben takobinsa da nufin ya zare takobin ya sare kan humaira amma sai ya kasa kawai sai hawaye ya zubo masa ya kasa yin komai ya kura mata ido kawai. Daga can sai yayi ajiyar numfashi sannan yace, "yake Humaira hakika kinci albarkacin adalci irinna ma'abota addinin musulunci amma da tuni yanzu nasare kanki da takobina. Kiyi sani cewa na tsani kasarku, natsani mutanen kasarku domin sarkin kasarku ne ya kashemin 'yar uwata wadda na fiso fiye da komai aduniya a ranar da mukafara yaki. Haka kuma sarkinku ya tsani mutanena ya tsani addininmu. A duk sa'adda wani daga cikin jama'armu yaje kasar ku koda da zummar fatauci ne sai yasa a kamashi ayimasa. Kisan gilla. Ki sani cewa mu bazamu kashekiba bisa tarbiyyar addininmu, amma akwai sharadi mai girma a tsakaninmu daku. Ba zamu yarda kuzauna a kasarmuba face kun karbi addininmu idan kina ganin bazaki iya karbar addininmu to kijuya ki tafi izuwa wata kasar daban inda zasu iya karbarki". Ya yin da sarki raihan yazo nan a zancensa sai Humaira ta fa she da kuka sannan tace, "ya kai wannan sarki mai adalci, kayi sani cewa babu wata kasa dazan iya zuwa na tsira daga sharrin sarkinmu da mijin "yar uwata face wannan kasa taka. A iya abin da na fa himta yanzu a zuwana kasarka nagane cewa wannan addinin naku addinine na a dalci gami da tausayi da jin kai, domin da farko dakarun da suke gadin kofar birnin sun kamani da karfin tsiya zasu kawoni gabanka amma dasu fahimci halin dana ke ciki suka an kashe min mijina kuma suka ganni da goyon Jaririyata sai suka tausaya min suka tsaya suka binne gawar mijina sannan suka taho dani izuwa nan fadar ka cikin salama ba tare da cin zarafinaba ko su taba lafiyata ba. Kaima da aka kawoka gabana da kaji cewar na fito ne daga birnin kisra sai zuciyarka tayi baki ka harzuka kamar zaka ka sheni amma saboda tausayi da adalci irin naka sai kakasa kasheni. Tabbas iya wannan karamci dana gani daga gareku ya isa na gamsu cewa wannan addinin naku shi ne addinin da yafi cancanta ga bil'adama a doron kasa. Saboda haka ni yanzu a shirye nake dana karbi wannan addini naku mai daraja. " Koda Humaira tazo nan azancenta sai taji gaba daya jama'ar fadar sun rude da kabbara kuma kowa ya kamu da tsananin farin ciki. Shikuwa sarki rai han baisan sa'adda fuskarsa ta fadada da murmushi ba. Nan take sarki raihan ya biyawa kumaira kalmar shahada ta maimaita sannan ya umarci wani hadimi nasa yace da shi a kai Humaira cikin gidansa na sarauta abude mata dakin matarsa marigayiya kuma a bata sutura da duk abinda take bukata. Nan take kuwa wannan hadimin ya tafi da Humaira izuwa cikin gidan sarki ya cika wannan umarni. Daga wannan rana Humaira ta tsinci kanta a cikin sabuwar rayuwa mai cike da dumbin farinciki da kwanciyar hankali, domin babu abinda tanema tarasa. Haka kuma sarki yasa wata baiwa masanar addinin musulunci ta dinga koya mata yadda ake ibada kuma ta dinga karan tar da ita addinin musulunci. Humaira taci gaba da renun jaririya dabira tataso a cikin son addini kawaici, fasa ha da jarumta. Tsananin kyawun dabira ya dimauta gaba dayan mutanen birnin misra, don haka tun tana da shekara bakwai 'ya'yan sarakai da 'ya'yan attajirai suka rinka zuwa wajen sarki raihan kamun kafa. Shikuwa sai yarika gaya musu dabira 'yace ta amana awurinsa don haka ba shi da ikon bayar da ita face ta girma ta zabawa kanta miji. Lokacin da sarki raihan yaga dabira ta taso da.matukar basirar daukan karatu da kuma jarumtaka taban al'ajabi saiya ji ya kauna ceta ainun tamkar hi ya haifeta. Bisa wannan daliline yasa yazana cewa kullum sai ya tura a daukota ta yini a wajensa yana koya mata karatu da kansa kuma yana koyamata yaki. Hakane yasa dabira ta shaku ainun da sarki sarki raihan ta dauka azuciyarta cewa shine mahaifinta, don haka tana kiransane da "abbanta". Ita kanta Humaira bata gayawa dabira gaskiyar al'amari ba domin kada hankalin dabiran ya dugunzuma ta shiga wani hali. Kai a birnin ma gaba daya in banda wadanda suka san taihi zuwan Humaira garin da yawan matasa sun dauka cewa dabira yar sarki raihan ce ta Cikinsa. Wani abin mamaki shine, a tsawon wadanan shekaru har dabira ta cika shekara goma sha takwas sarki raihan da Humaira basu taba zama tare ba tsawon dakika dari da sittin. A koda yaushe duk su biyun suna gudun faruwar hakan domin gudun kada soyayya ta shiga tsakaninsu. A binda basu saniba shine sun makara, domin tun a ranar da sarki raihan ya musuluntadda ita duk su biyun suka ji suna kaunar juna. Shidai sarki raihan tun da matarsa ta mutu a lokacin da tazo haihuwa ya zamana cewa dan cikin nata ma yarasu sai yaji gaba daya baya sha awar yin aure a rayuwarsa domin a ganinsa ba zai taba samun wacce zata maye gurbinta ba. Tun a sannan ne yayi al'kawari a zuciyarsa cewa bazai sake soyayya ba. Ita kuwa humaira a duk sa'adda ta tuno da tsohon mijinta Hukairu sai taga kamar butulci za tayi idan ta sake yin wani auran. Abu na biyu idan ta tuno cewa itafa ba jinin sarauta bace sai taga babu yadda za ayima sarki raihan ya sota har ya aureta. Bisa wannan daliline ta dunga baya-baya da shi ta na tsoron duk wani abu da zai jawo wata hulda a tsakaninsu duk da cewa sautari ta kanji begensa yana darsuwa azuciyarta domin gaba dayan halayensa suna burgeta. Al'amarin gimbiya dabira kuwa lokacin da ta shekara goma sha takwas, kyawunta ya kara bayyana karara a fili fiye da ko yaushe kuma ta zama gawur tacciyar mayakiya kuma jaruma wacce babu kamarta akasar gaba daya. Sai sarki yasa aka bata sarautar sarkin yaki. Tun daga wannan rana ne dabira ta samu damar rufe fuskarta da hular karfe, bata cire wannan hula face tana cikin turakarta amma ko acikin gidan sarauta idan zata je wajen ma haifiyarta ko wajen sarki sai tasa hular sai ta shiga wajen nasu sannan take cire hular saboda yawan kallon da mutane suka yi mata yayi yawa bama maza ba, hatta 'yar uwata mata da zarar sun ganta sai kaga sun kura mata idanu baza su daina kallonta ba face ta kule. Allah yayi dabira da tsananin kyawu na dirin jiki,sannan gashin kanta baki ne sidik ga kyalli da sheki tamkar madubi ya zubo har kasan kwankwasonta. Saboda tsananin kyallin ga shin idan mutum ya tsaya a bayanta sai ya dinga ganin fuskarsa a cikin gashin. Dabira nada dara-daran idanu farare soll masu dauke da digon baki tamkar yankan wuka. Tana da dogon wuya tamkar na barewa. Kalar fatar jikinta kuwa bata kasance fara ba ko ja ba, wani irin launine na musamman wanda ido bazai iya tantance waba saboda tsananin kyau. Kai a ta kaice dai babu wani da namiji da zaiyi arba da jaruma dabira ba tare da ya kamu da tsananin sonta da begen taba. Lokacin da samari masu isa suka yi caa ! A kan neman auren gimbiya Dabira sai ta taka musu birki tace baza tayi aureba har sai ta

Chapter 3 of 5