Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 5
banu mun lalace sai mulkimmu ya rushe. Kuma sai talakawanmu sun zama shugabanninmu sun dauki fansar zaluncin da muka dade muna yi musu tsawan shekara da shekaru ta han ya daya ce ka dai zamubi kada azo da ita fadata kada abari tayi arba da fuskata kuma kada ka nunawa matarka bacin ranka koka gaya mata abin da muka tattauna anan yanzu A can daji kuwa inda manomi hukairu yayi gidansa suna wayi garine a cikin farin ciki da bakin ciki dalili farinkinsu shine na haihuwa da humaira tayi nayaya tagwaye mata duk da cewa tayi kyautar byar goda ga rayuwarka nuzaira shi kuwa mummuna mafarkin wanda himaira tayi a jiya da daddare da safe sa adda humaira ta farka daga bacci ta fara bawa mijinta hukairu labarin mafarkinda tayi a jiya al amari daya matukar dugunzuma humaira duk hankalinsa kenan dalili kuwa shine a iya saninsa da matarsa humaira duk abin datayi mafarkinsa saiya tabbata a gaske. Bawani abu humaira ta ganiba acikin mafarki ba face saukar wadansu dakaru kamar daga sama wadanda suka bukawa gidan wuta ya kone kurmus babu abin da ya tsira. Lokacin da hukairu yaji labarin mafarkin da humaira tayi sai hankalinsa ya dugunzuma ainun rasa abin dake masa dadiya shiga tunani mai zurfi daga can saiya dubi ita humaira yace yake matata kinsani cewa wajibine a garemu muyi hijra mubar gabadaya yankin wannan kasa tamu idan har muna son mu da abin damuka haifa mutsirada rayuwarmu naji ajikina cewa sarki daksar kasurgumin matsafine don haka na tabbatar da cewa abinda ya faru tsaka nimmu da 'yar uwarki nuzaira ya gani kuma ya nunawa barzuk bisa wannan da lilinne za su turo a hallakamu lokaci yayi da zan gaya miki wani sirri wanda bantaba gaya mikiba. Tun muna yara nida dan uwana barzuk bokan ma haifina wanda muka sami sirrikan tsafi a wajensa yace mana cewa agaba daya kasar nan babu wani mahaluki mai karfin sihirinmu face sarki daksar amma duk 'yar da muka haifa idan tayi arba da idan sarki daksar to zata samu duk irin sihirin da sarki daksar yake da shi a cikin kwana uku harta samu nasarar Hallaka shi ta hau kan kara garsa face ya kasheta kafin cikar kwana uku shi kansa sarki daksar ya san da wannan sirri don haka bazai taba barin abun da muka haifa arayeba dun haka ba zai barmuba yazama wajibi muyi shirin gaggawa yanzu muyi hijira mukara gaba. Sa adda hukairu yazo nan azancensa sai humaira ta ce yanzu ina kake tsammanin zamu shiga mu buya ba tare da sarki daksar yaturo an kashemuba Hukairu yace waje daya ne zamu iya zuwa muyi rayu wa acan kuma mu tsira daga sharrin sarki daksar da dan uwana Barzuk. Bawani waje bane face birnin misra inda sarki Raiyan ke mulki. " Koda jin haka sai idanun Humaira suka zazzaro tace "ya ya za ayi muje birnin misra kuma muyi rayu wa alhalin mutanen can sun kasance musulmai mukuma ma abota tsafine da gunki? Humaira tace "shin ka manta ne sarki daksur bashi da wani makiyi wan da yafi sarki Raiyan na birnin misra? Ai idan sarki raiyan ya fa shinci cewa mu mutanen birnin kisra ne sai yasa anyi mana kisan gilla domin ya dauki fansar ran 'yar uwarsa gimbiya Numaira wacce sarki daksur ya ka she yayin da aka fafata kazamin yaki da su a shekaru uku baya. " Hukairu yayi ajiyar numfashi sannan yace "duk nasan da wannan al'amari amma abinda nake so ki fahimta shi ne abinda ya koro bera yafada cikin wuta ya fi wutar zafi. " Koda gama fadin haka sai hukairu ya mike tsaye yakama hada kayyayyakinsu domin suyi hijira. Bayan ya gama hada hada komai a waje guda ya dora a kan rakumansa wasu kuma akan shanunsa sai yaje tsakiyar filin gidan ya haka rami sai ga shi ya tuno wata laya. Nan take ya rataya layar a wuyansa, sannan yakira Humaira ta fito da ga cikin daki goye da jaririyarta. Ba tare da bata lokaciba suka hau kan ra kumansu biyu sukayi gaba suna janye dabbobinsu. Koda hukairu ya juya ya dubi gonarsa da wannan gida nasa sai idanunsa suka cikoda kwalla saboda takaicin ya tafiya bAr kasa mai albarkar noma wadda abu ne mawuyaci ya sake samun irinta. Bayan kamar sa a hudu da tafiyar hukairu da matarsa humaira sai ga sarkin yaki haizar bin mausus bisa doki tare da dakaru dari biyar suna take masa baya dukkaninsa dauke da muggan makaman yaki tun daga nesa haizar ya dauko wani gilashi na sihiri wanda sArki daksur ya bashi ya ce da shi da wannan gidashi ne kadai zai iya hango gidan hukairu. Haizur yasa gilashin a kan idanunsa amma bai hango komaiba dan haka sai suka kara kaimin gudu bisa da wakansu. Jim kadan da faruwar haka sai suka hango gidan daga can nesa. Daya daga cikin daka runnasane ma ya fara hangowa ya nuna masa al'amarin daya matukar ba shi.mamaki kuma yaba shi tsoro ya fara tunanin duk yadda a kayi su Hukairu basa gidan kuma lallai ya tone wannan laya wacce sarki daksur ya bashi labarin cewa hukairu ya binneta a tsakiyar gidansa. Tun da ga inda suka hango gidan Haizar yabada umarnin a fara harba kibiyar wuta izuwa gidan. Ai kuwa cikin kan kanin lokaci gidan gaba daya ya kama ya kama da wuta yana ci balbal. Su sarkin yaki haizar suka karqso gaban gidan aguje bisa dawakansu suka yiwa gidan kawanya kuma suka dana kwari bisa baka suna jira suga wani abu mairai yayi fitar burgu don ceton ransa su harbeshi amma hargidan yagama konewa kurmus yazama toka ko kyanwa basu ganiba. A sannanne sarkin yaki haizar ya sakko daga dokinsa ya duba tsakiyar gidan nan take kuwa yayi arba da wannan rami wanda hukairu tone ya cire layarsa ta sihiri. Cikin tsananin ta kaici da fushi haizar ya kwarara ihu sannan ya dakko mudubin tsafinsa ya shafeshi sau uku yana mai karanta wadansu dalasiman tsafi guda uku. Faruwar hakan keda wuya sai ga fuskar sarki daksur ta bayyana akan madubin suka dubi juna. Kafin haizar ya budi baki yace wani abu sai sarki daksur ya tari numfa shinsa yace "maza ku ruga gaba domin tuni Hukairu da matarsa sunyi nisa, taza rarku da su ta kai nisan sa'a hudu. Idan kuka yi sakaci suka shiga yankin kasar misra shi ke nan baza ku taba riskar suba. Tun da hukairu na tare da wannan laya baza ku taba ganin koda sawunsuba amma i dan kayi amfani da wannan gilashin sihiri da na baka zaka i yaganin sawayensu. Idan har kana son kariskesu sai kunyi ta fiyar kwana uku bayada zango babu barci. Idan har kasami nasarar cika wannan aiki kana dawo wa birnin kisra zanbaka wazircina kuma zanbaka dukiya ninkin goman abin da ka mallaka a yanzu. Koda gama wannan jawabi sai fuskar sarki daksur ta bace bat, daga cikin madubin sarkin yaki haizar nan take yaji farin ciki ya lullubeshi dan haka sai yaruga kan dokinsa yayi tsalle ya haye kan dokin ya zabure shi cikin matsanancin gudu koda ganin haka sai suma ragowar dakarun suka sakarwa dawakansu linzami suka rufa masa baya. Lokacin da ake wannan mugun artabu tsakanin Hukairu da Zaihar tuni humaira ta isa bakin kofar birnin misra amma sai ta ja linzamin ra kumin ta ta tsaya cak ta kasa shiga birnin ta juyo cikin ta shin hankali tana kallon gumurzun da akeyi tsakanin mijinta da sadauki zaihar. Lokacin da sadauki zaihar yaga wankin hula zai kai shi dare sai ya fusata ya fara amfani da karfin sihiri domin ya hallaka hukairu amma sai ya ga ashe shima hukairu ba kyalle bane abangaren tsafi domin karfi ya zo daya. Haizar yaja da baya yaduru daga kan dokinsa ya tsaya cak a waje daya yana tunanin dabarar da ya kamata yayi. Koda ganin haka sai shima hukairu ya duro daga kan ra kuminsa ya gyara tsayuwa yana mai fuskan tarsa sannan ya kyalkyale da dariya yanuna haizar da dan ya tsa ya ce "ya kai wannan tsohon azzalumi ba wan azzalumai ka sani burin mai gidanka bazai cikaba a kan iyalina domin sun tsira daga sharrinkku a yanzu tunda sun haye iyakar kasarku. Ko a yanzu ka kashe ni bani da na damar komai. Yayin da haizar yaji wannan batu sai shima ya kyalkyale da dariya sannan yace "ai kuwa yanzu zan kasheka sannan nabi iyalinka har bakin kofar birnin misra suma na hallakasu tun dadai sun kasa shiga cikin birnin sun tsaya suna kallo domin suga irin mutuwar dazakayi. " Koda jin wannan batu sai hukairu yajuya da sauri domin ya dubi bakin kofar birnin misra kafin ya juyo da kansa tuni Haizar ya zaro wata wuka siririya mai kaifi da tsini ya wur gamasa take wukar ta cake atsakiyar kirjinsa ya dur kushe bisa guiwowinsa koda humaira ta hango abinda ya faru da sai ta tsandara uban ihu al'amarin da ya janyo hankalin masu gadin kofar birnin misra kenan suka rugo waje da gudu rike da makaman yaki suda yawa. Yayin da sarkin yaki ya hango fito war wadannan mayaka sai ya juyo da sauri ya ruga izuwa kan dokinsa na sihiri ya zabure shi da gudu yanufi baya. Ita kuwa Humaira sai ta diro kasa daga kan ra kuminta ta falfala da gudun tsiya tana kuka izuwa inda mijinta yake durkushe. Koda zuwanta gabansa sai ta tabashi sai taji ya bingire kasa ko motsi baiyiba alamar cewa yamutu ba shi da rai nan fa ta rungume gawarsa tasake fashewa da matsanancin kuka. Tana cikin wannan haline dakarun misra suka zo gareta suka banbareta daga jikin gawar da karfin tsiya suka tafi da ita izuwa cikin birnin misra tana ta iface iface da koke koke tamkar sabuwar mahaukaciya. Wannan shine abin da ya faru ga Humaira matar Hukairu bayan srkin yaki ya riskesu ya kashe hukairu, ita da jaririyar sun tsira A can birnin kisra kuwa lokacin da hakimi barzuk ya koma wannan gida nasa inda ya ajiye matarsa nuzaira sai ya shaida mata duk wadannan dokoki wadanda sarki daksur ya shimfida masa a kan jaririyar data haifa ko da jin wadannan dokoki sai ta cika da tsananin mamaki ta dubeshi tace to wai shin laifin me mukayi harda sarki zai kafawa yarmu irin wadannan dokoki masu tsauri dayawa haka?” Koda jin wannan tambaya sai barzuk ya tumbune fuska yace ” ni kaina bansan daliliba amma babu mamaki akwai babbar hujja data janyo mana hakan saboda haka indai kIna son mu tsira rayuwarmu da mutuncinmu lallai kikiyaye wadannan dokoki ” daga wannan rana kowa nuzaira tacigaba da renon jaririyarta da ranar suna tazo sai aka radawa jaririya suna yazila tunda nuzaira ta acikin wannan gida na mijinta acikin birnin kisra batata bin hanyar gidan sarauta ba bare ma taga sarki da idanunta bare kuma jairiyar datake raino. Tafiya sannu sannu kwana nesa darare na wucewa kwanaki na shudewa sai aka wayi gari yarinya yazila ta cika shekara bakwai a duniya nan da yazila tazama sananniya a birnin kisra saboda kasancewarta tataso da tsananin kyau dakuma jarumantaka domin tun a sannan tana iya daga kato komai girmansa ta rankwalashi da kasa har sai datakai cewa ana shirya mata gasar kokawa da mazaje majiya karfi tana zama zakarar gasar daga nan kuma sai lamari nata kara samun cigaba domin ta fara koyon sarrafa takofi`mashi`kwarida baka. Duk mutumin daya fara koya mata amfanida kayan yaki sai yaga tafi kwarewa acikin kwanaki uku kacal. Tun da yazila ta taso taga wata farar laya a wuyanta bata son abin da zai rabata da layarba dare da rana har kwanciyar barci kuwa. A takaice dai batata cire layarba kuma tana iya tuno lokacin da mahaifiyarta hakimi barzuk ya samata layar sa adda batafi shekara biyarba aduniya. Koda wasa yazila batata bin hanyar gidan sarki ba kuma kojitayi sarki zai shigo cikin gari tobazatataba fita daga cikin gidan domin a rayuwarta babu data tsana tagani ko taji zancensa face sarki. Abinda batasaniba shine. Wannan laya da aka rataya mata awuya itace sanadin dataji batason taga sarki. Ana nan cikin wannan hali har yazila ta cika shekara goma sha takwas. Alokacin ne kyawunta yaruda gaba dayan jama ar birnin kisra ya zaman cewa duk inda mutun yaje saidai yaji ana labarinta. Afagen jaruman taka kuwa al amarin maya wuce tunanin mai tunani domin duk sa adda aka fita yaki da mutanen birnin misra tana ya musu mummunar barna wata jaruma guda daya takeci mata tuwo akwarya wadda itace sarkin yakin mutanen birnin misra a wani lokaci ita dai larziya taji ana yiwa jarumar kirari da basadaukiya dabira babban abin takaita awjen yazila shine batataba ganin fuskar wannan abokiyar gaba tata ba domin duk sa adda zata fito yaki tana rufe fuskarta ne da hular karfe. Akalla yazila da dabira sun fafata kazamin yaki kamar sau hudu amma duk sa adda suka hadu.kare jini biri jini sukeyi. Koda rauni suka yiwa juna sai kaga raunin yazo adadi daya baya gotawa sukansu suna matukar mamakin wannan al amari babu irin kokarin da yazila batayi ba don ganin ta cire hular karfen datake dabira taga fuskarta amma abu ya gagara. Akwai.wata rana da dabira ta tambayi bokanta wanda ake kira mushrid bin affan tace dashi yakai abin dogarona yaza ayina sami nasara akan abokiyar gabata absadaukiyar dabira na kai kasa kuma har na cire hular karfen dake kanta naga fuskarta ?” Koda jin wannan tambaya sai boka mushrid ya kyalkyale da dariya sannan yace ” idan har kina son ki sami wannan nasara sai dai ki cire wannan laya dake wuyanki kije har cikin fadar sarki daksur ku yi arba da juna in dai kikayi haka sai kin nasara akan jaruma yazila har kiyi.mata rauni sama da adadin wanda zatayi miki. Kuma ki kaita kasa ki cire hular karfen dake kanta kiga fuskarta amma ki sani cewa ranar da wannan tashin hankali irin wanda baki tabaga shigarsab” Koda jin wannan babu sai jaruma yazila tasa hannunta ta kama wannan farar laya dake wuyanta da nufin ta cireta amma sai ta ji kamar an soka mata allura guda dubu a sassan jikinta. Ba shiri ta saki layar ta kama ihu kuma ta fadi kasa a matukar galabaice tana haki wadda aka yi yunkuri zare ruhinta. Nan ta jike sharkaf da gumi da kyar ta dago da kanta ta dabi boka mushrid tace ” meya sana kasa cire wannan laya daga wuyana kuma taya ya zan iya rabuwa da ita ?” *WACCE AMSA BOKA MUSHRID ZAI BAIWA JARUMA YAZILA? *YAUSHENE JARUMA YAZILA ZATA YI ARBA DA FUSKAR SARKI DAKSUR? *YAYA AKAYI BASADAUKIYA DABIRA TAZAMO SARKIN YAKIN BIRNIN MISRA? SHIN ITAMA TA ZAMA MUSULMA CE? *I NA LABARIN MAHAIFIYARTA HUMAIRA? *SHIN NUZAIRA DA HUMAIRA ZASU SAKE GANIN JUNA? MUHADU A JARUMA YAZILA NA BIYU DON JINCIGABAN WANNAN LABARI. . JARUMA YAZILA Littafi na daya Na Abdul'aziz sani madakin gini Created and design by:- Shuraih Usman Publishing shuraih Usman From http://shuraih.waphall.com JARUMA YAZILA Littafi na biyu 2 Na Abdul'aziz sani madakin gini Created and design by:- Shuraih Usman Publishing shuraih Usman From http://shuraih.waphall.com . Lokacin da jaruma yazila ta tambayi boka musrid bn Affan dalilin da ya sa takasa cire wannan laya daga wuyanta da kuma yadda zata iya rabuwa da ita sai ya yi ajiyar nunfashi sannan yai shiru ya sunkui da kansa kasa cikin halin tunani tsawon lokaci mai tsawo yana tunani baice komaiba daga can sai ya dago kai ya dubeta cikin tsananin damuwa sannan yace ya ke jarumar jarumai ki yi sani cewa yau kin tambayeni babban al amari wanda yafi karfina domin idan na ce zan matsa bincike bisa wannan al amari zan iya rasa rayuwata. Ita dai wannan laya ta wuyanki tun kina jaririya mahaifinki Barzuk ya sanyata a wuyanki kuma duk ranar da kika sami damar cireta a ranar ne zaki sanwani babban sirri dangane dake kanki da kuma mahaifinki da sarki daksur har kiyi arba dashi in kuwa kika yi arba da shi duk irin sihirin tsafin da yake da shi saikin sameshi. Ina tabbatar miki da cewa duk duniya a halin yanzu babu wanda zai iya cire maki wannan laya face abokiyar gabarki dabira ta birnin misra. Sa'adda boka mushrid yazo nan a zancensa sai jaruma yazila ta cika da tsananin mamaki kuma zuciyarta tayi bakikkirin ta dubi boka mushri ta ce, "yanzu ashe ke Nan akwai wani babban sirri dangane da rayuwata wanda ma haifiyata da mahaifina suka boye mini?" Boka mushrid yace kwarai kuwa akwai wannan sirri kuma kada kiga Laifinsu domin sanar dake bazai haifar da komaiba face tsananin ta shin hankali agareki baki daya. Koda jin haka sai hawaye ya zubowa jaruma yazila tace, "Ai kuwa a yau dinnan sai na tambayi mahaifiyata wannan al'amari ko menene zai faru kuma zan yi shiri na tafi birnin misra wajen abokiyar gabata jaruma dabira domin na san dabarar dazan yi tacire min wannan sarka bare bata saniba. " Cikin firgici boka mushrib ya kama kafadun jaruma yazila yace, "yake jarumar jarumai, kiyi sani cewa abinda kike shirin yi tamkar ki aza gammo ne a kanki kice zaki dauki duniyar nan gabaki daya ina mai shawartar ki da ki hakura dayin wannan abu domin a karshe allura ce zata tono garma." Koda jin haka sai yazila ta mike tsaye zumbur! A fusace tace, "ya kai wannan amintaccen bokana kayi sani cewa babu wani abu da ya isa yahanani yin waddannan abubuwa guda biyu face mutuwa kuma yanzu_Yanzu zan tafi na fara gabatar dasu ." Koda gama fadin haka sai yazila ta juya ta fice daga daga gidan boka mushrib tana isa kofar gidansu tayi kicibis da boka mushribtsaye gabanta fuskarsa a murtuke babu annuri.Mushrid ya dubi yazila yace, "bazan barki kije ki ai'watar da wannan al'amariba domin nifa zaki jefani cikin masifa da bala'i". Yazila tayi murmushi sannan tace, "kayi sani cewa dan zaki yagirma banga ta yadda zaka iya hananiba, idan kuma kana ganin zaka iya toka jarraba". Gama fadin hakan ke da wuya sai ta yun kura da nufin ta wuce ta gabansa. Take mushrid yayi nuni da hannunsa izuwa gareta sai wata irin murtukekiyar sarkar tsafi ta kanannadeta tun daga kan kafafunta har zuwa kanta ta daureta tamau, idanunta da fuskarta ka dai ake gani. Yazila ta girgiza jikinta don ta tsinke sarkar amma ta kasa kwancewa. Koda ganin haka sai boka mushrid ya bushe da dariyar mugunta yace "kika ce dan zaki yagirma kodai dan kyanwane?" Yazila ta kyalkyale da dariya sannan ta ce, tabbas dan zakine wannan ba dan kyanwa bane. " Kafin boka mushrid ya kara cewa wani abu sai yazila ta ambaci wata kalma daya daga cikin da lasiman tsafi. Nan take wannan sarkar tsafi ta narke tazama ruwa. Kafin boka mushrid ya yi wani yun kuri tuni yazila ta fincikoshi da hannu daya tayi hajijiya da shi a sama ta fyada shi da kasa kuma tatake masa wuya da kafadaya ya fara kakarin mutuwa. Yazila ta dauke kafarta guda daga kan boka mushrid tacce, "kaci albarkacin kyautatawar da kayimin abaya da yanzu zan kasheka. Kasani cewa dokata ta farko.akan kowa itace, ba ayimini dole, kuma idan nabada umarni ba a ketare shi daga yau idan ka sake saba wannan doka zan kau da batun mutunci dake tsakaninmu na yi maka hukunci dai-dai da laifinka. " Koda gama fadin haka sai jaruma yazila tayi girgiza ta bace bat ! Tamkar bata taba wanzuwaba a wajen. Al'amarin daya matukar baiwa boka mushrid mamaki kenan ya bita da kallo ka wai zuciyarsa cike da wasa- wasi yana mai cewa, "yaya akai yazila ta sami wannan sihirin tsafin mai karfi haka ? Abinda bai sani ba shine, yazila ta ziyarci manyan bokayen duniya ta sami sirrikan tsafi da yawa. Wadan da suka finasa. " Lokacin da jaruma yazila ta isa gida sai ta iske mahaifiyarta nuzaira zaune a turakarta. Ko masana yazila bata mataba sai ta wuce kai tsaye izuwa cikin turakarta, al'amarin da ya matukar baiwa nuzaira mamaki kenan domin a duk sa'adda yazila ta dawo gida da gudu take shigowa turakarta, ta rungumeta cikin farin ciki ta sumbaci goshinta. A rayuwar jaruma yazila babu take kauna sama da nuzaira ko kadan bata son taga abin da zai sosa mata zuciya, haka kuma duk abin da nuzaira ta umarci yazila tayi sai tayi shi bata taba yimata gar dama. Bayan yazila ta shige cikin dakinta sai nuzaira ta mike tsaye ta kira wata kuyanga mai suna rafina wacce itace ke kula da komai na yazila ta ce da ita taje ta kawo mata abincin yazila. Cikin mamaki rafina ta dubi nuzaira tace , "ya shugabata ai yanzu zan je na kai mata abincin". Nuzaira tace yau ni da kaina nake son na kai mata" Koda jin haka sai rafina ta juya da sauri tatafi dakin girki ta dakko abincin yazila bisa faranti ta kawowa nuzaira ita kuma ta karba ta tafi dakin yazila ". Yazila na zaune bisa gefen gadon ta tayi ta gumi cikin halin tunani mai zurfi. Ka wai sai taji anturo kofa an shigo. Yazila ta dago kai da sauri tayi arba da ma haifiyarta Nuzaira kawai sai ta kau da kai ga barin kallonta ta sun kui da kanta kas. Cikin sanyin jiki nuzaira ta matso daf daf da yazila ta ajiye farantin abincin wani benci karami sannan ta zauna bisa wata kujera dake fuskan tar yazila ta dafa cinyoyin yazila tace, "yake 'yata yau kuma wanene yabata miki rai a waje har da fushinsa zai shafeni?" Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa yazila ta kasa cewa komai. Al'amarin da ya matukar razana Nuzaira kenan ta cika da tsananin mamaki. Kawai sai yazila ta kama hannun nuzaira ta dora akanta tace, yake mahaifiyata ina son ki yi ran tsuwa bisa dara jar kaunar dake tsakaninki dani ki gaya mini gaskiyar al'amarin da zan tambayeki a yanzu. Kisani cewa idan kika gaya mini sabanin gaskiya kuma na gano hakan anan gaba lallai zan kashe kaina domin ban ga amfanin rayuwataba a duniya tunda wadda na aminta da ita fiye da kowa bata aminta daniba". Cikin rudewa Nuzaira tace mene ya kawo duk wannan al'amarin haka yake 'yata ? Shin wani ne yace akwai abu dana buye miki ?" Yazila ta share hawayen i danunta tace, "dafarko ina so n'ki gaya mini asalin wannan layar dake wuyana da kuma dalilin da yasa aka sakamin ita. Ina son ki gaya mini sirrin dake tare da rayuwata da taki. Na ran tse da darajar soyayyar da nake miki idan kika boye mini gaskiyar al'amari bazan taba yafe miki ba " Sa'adda Nuzaira taji wannan tambaya sai tacika da tsananin mamaki bisa abin da ya janyo yazila tayi mata wannan tambaya. Nuzaira ta dubi yazila tace, "mene ne dalilin daya sa kika yi mini wannan tambaya?" Koda jin haka sai yazila ta kwashe labarin duk abin da ya faru tsakanin ta da boka mushrid ta zaiyane mata. Sa'adda nuzaira taji wannan batu sai han kalinta ya dugunzuma ta dubi yazila tace, "yake 'yata hakika yau kin zomini da babban al'amari don haka yana da kyau ki bani lokaci. Isasshe nayi tunani tukunna. Yanzu dai ina son ki kwantar da hankalinki sannan kici abincinki inyaso nan da wani lokaci na dawo gareki muci gaba da wannan magana". Har nuzaira ta mike tsaye zata fita daga dakin sai yazila taruko hannunta ta zaunar da ita alokacin da hawaye yaci gaba da zuba akan kumatunta. Yazila tace, "ya ke Ummina ina tabbatar miki da cewa idan baki bani amsar tambayata a yanzu ba ba zan kara cin abinci ba a rayuwata sai dai yunwa da kishirwa su kasheni".Koda jin haka.sai hankalin nuzaira ya kara dugunzuma fiye da ko yaushe domin ta san halin yazila duk abin da ta ce za ta aikata bata fasawa kawai sai yaZila ta ga hawaye ya zubowa nuzaira sannan kuma ta fashe da kuka al amarin. Da ya matukar dugunzuma hankalin yazila kenan taji ta yi nadamar matsawar datayi mata a kan wannan tambaya batare da nuzaira tace komai basai tamike tsaye taje ta kulle kofar dakin sannan ta kulle tagogin dakin ta dawo daf da nuzaira ta zauna ta fara ba ta labari tun daga lokacin da hukairu da humaira suka yi hijra daga kauyen himsarul aswad suka koma can da birnin kisra suka cigaba da rayuwa kawo izuwa lokacin da nakuda ta kamata ta tafi can inda su humaira ta haifi yan mata tagyaye ta dauki daya ta bata ta dawo wajen mijinta barzuk suka koma cikin birnin kisra da zama da duk irin dokokin da sarki daksur ya kafawa jaririyar har barzuk ya kawo wannan laya aka sanyawa jaririyar a wuyanta. Lokacin da nuzaira ta gama baiwa yazila wannan labari sai yazila ta fashe da matsanancin kuka kamar baza ta daina ba. Kuma tacika da matukar mamaki da bakin ciki da kyar da sidingoshi nuzaira ta rarrashi ta tadaina kukan sannan ta roketa akan tabar wannan magana a zuciyarta domin idan tace zata dauki wani mataki akan barzuk da sarki darkus bazata sami galababa. Yazila ta gyada kai cikin matukar takaici sannan tace yake ummata kiyi sani inda na san cewa niba yarki bace bazan tsaya nayi yaki da muyanen birnin misra ba tsawon shekaru kuma ina tabbatar miki da cewa lallai sai na sami nasarar cire wannan laya daga wuyana kuma komai dadewa sai naga bayan mijinki da sarki daksur. Domin sun kasance azzalumai kuma bara gurbi a doron kasa shin yanzu kina da labari yar uwarki humaira da yar uwata dake tare da ita ?“ Koda jin wannan tambaya sai nuzaira tayi ajiyar zuciya tace ai rabona da su tun sa adda na rabu da su a can gidansu daji amma na taba ji a bakin sarkin yakin garin nada wato sadauki zaihar cewa hukairu da humaira tare da yarsu sun gudu izuwa birnin misra amma ya bisu har ya riskesu kafin su shiga birnin har ya fafata yaki da mahaifin naki hukairu ya sami nasarar kasheshi amma bai sami damar kashe humaira da yar uwarki ba domin dakarun birnin misra ne suka yiyo kansa ya gudu ya yin da yazila taji haka sai zuciyarta ta kama tafarfasa kamar za ta kone tace yanzu sarkin yaki zaihar ne ya kashe mahaifina ?“. Nuzaira tace tabbas haka ne babu shakka “ yazila kuwa indai makaifiyata da yar uwata suna raye tabbas suna cikin birnin misra ni kuwa ta kowanne hali sai na shiga birnin misra ni kuwa ta kowanne hali sai na shiga birnin misra na sadu da su dama ina da burin naje na sadudA jaruma dabira domin ta cire mini wannan laya dag wuyana kuma ina son muyi yakin karshe da ita domin nasami damar kaita kas har na cire hular karfen da take sawa a kanta domin naga fuskarta kin ga kenan ina da manyan bukatu har guda uku acikin birnin misra don haka zama bai kamani ba dole ne nayi shiri na tafi birnin misra". Koda jin wannan batu sai hankalin Nuzaira ya dugun zuma ta dubi yazila cikin firgici tace, "yake 'yata kin sani cewa mutanen birnin misra sun kasance ma'abota addinin muslunci saboda haka zuwanki birninsu abu ne mai hadarin gaske da zarar sun ganki zasu hallakaki tun da kin kasance tsohuwar abokiyar gabarsu. Ki tuna cewa kin kashe musu jama'a ba adadi. A bu na biyu koda 'yar uwarki da mahaifiyarki suna nan araye yanzu kodai suna kurkuku kokumaa suma sun zama musulmai don haka baza suyi mar haban da keba tun da kun banbanta addini da yanayin rayuwa. Ke koma dai babu banbancin komai ai baza sutaba shaidakiba tun da basu sankiba kema baki sansuba. Shekara goma sha takwas ai ba kwana goma sha takwasbane. Na tabbata yanzu 'yar uwata Humaira ta tsufa, kamar yadda nima na tsufa, ta yaya zata shaidaki alhalin rabonta da ke tun kina jaririya?". Lokacin da nuzaira ta zo nan a zancenta sai yazila ta mike tsaye ta kama kai kawo sannan ta tsaya cak ! Ta dubi nuzaira tace, "yake ummina ki sani cewa dan uwa-dan uwane, har abada idan ka

Chapter 2 of 5