Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 5
gimbiya tayi kwana biyu a kwance tana jinyar wannan rauni nata kafin ta fara takawa saboda kyakkyawan motsi ma zai iya sawa dinkin ya farke.Koda jin wannan batu sai ran sarki Darwaz ya baci ainun,zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone saboda kin haushin cewar babu dama a cigaba da wannnan tafiya a yau bare a hanzarta cimma su Shugaba Sharwan.A daidai wannan lokaci ne billen Sarki Darwaz ya dameshi da zogi har ma yana digar da jini.Koda likta ya lura da hakan sai ya shiga tsaida jinin sannan ya dubi Sarki Darwaz a tsorace yace ya shugabana akwai bukatar ayi masa dinki a kan wannan rauni naka.Cikin matukar takaici Sarki Darwaz ya ce idan ka dinke raunin zai fatar da tabonsa har abada?Jikin likitan na rawa yace,ai har abada tabon wannan yanka bazai taba bacewa ba daga kan fuskarka.Kafin likitan ya gama rufe bakinsa tuni sarki Darwaz ya 11 hours ago Abubakar Haleefah Physicist zaro wata sharbebiyar wuka a kugunsa ya kirbawa likitan a cikinsa,kuma ya damki makoshinsa ya daga sama da hannu daya a lokacin da yake kakarin mutuwa yace,kai ne mutum na karshe wanda zai sake ganin wannan bille.Yana gama fadin hakan yayi wurgi da gawar likitan sannan ya bude kofar dakin ya kirawo dakaru suka dauke gawar likitan suka fice da ita kuma aka goge jinin daya fara zuba a kasa.Tun a wannan Sarki ya ruge fuskarsa da rawani,idanunsa kadai ake gani.Nan take yasa aka kawo kuyangi guda hudu wadanda zasu lura da Gimbiya Huraisa,sannan ya fice daga cikin daki.Yana fita ya jagoranci wadansu dakarun nasa sukayi ta yawo a cikin gidan suna bincika cikin dakuna,lunguna da sako-sako ko zasu ga matar Sultan,amma shiru ko alamarta babu.Saida suka bincike ko'ina sannan sarki Darwaz ya hakura ya koma can falon Sultan ya zauna don hutawa.Bayan an kawo masa abinci da abin sha yaci yayi hani'an sai ya kori kowa daga cikin falon hatta kuyangin dake cikin dakin suna jinyar gimbiya Huraisa kuwa saida suka fice,sannan ya kullo kofa da kansa yaje gaban wani katon madubi ya tsaya.A sannan ne ya kwaye rawanin dake fuskarsa yaga billen da Sultan yayi masa.Bille ne mai tsawo da fadi,wanda yasa masa muni,nan take zuciyar Sarki Darwaz ta kama tafarfasa kamar zata kone a karo na biyu har saida kwallar takaici ta cika amsa idanu.Ba komai ne yasa shi zubar da wannan kwalla ba face sani cewa shugaba Sultan ya karya masa tarihin jarumtakarsa,domin tunda yake yaki da gumurzu a rayuwarsa ba'a taba fitar da digin jini ba a jikinsa,amma yau gashi ma anyi masa raunin da indai zai bar fuskarsa a bude kowa sai ya gani.Sarki Darwaz ya tuna cewa duk wannan abu daya faru Siyama ce silarsa tunda inda bata kashe dan'uwansa ba da ba zai fito farautarta ba har yayi yaki da Sultan yayi masa wannan bille.Nan take Sarki Darwaz yaji ya kara tsanar Siyama fiye da koyaushe kuma ya tabbatar da cewar ransa bazai taba yin fari ba face a ranar dayaga ya sare kan Siyama kamar yadda ya sare na abokin mahaifinta wato Sulta.Nan take Sarki Darwaz ya kudurce a ransa cewar bazai sawa wannan rauni masa magani ba,kum bazai yarda a dinke shi ba saidai yayi ta ciwon da zaiyi har ya daina son kansa yayi warkewar dole,sannan kuma ya kudirci niyar cewa babu wanda zai sake ganin fuskarsa saidai idan ya zama gawa hatta matarsa da 'yarsa kuwa.Koda ya gama aiyana hakan,sai Sarki Darwaz ya sake rufe fuskar tasa da rawani sannan yaje kan wata doguwar kujera ya kishingida yana kwanciya barci ya saceshi saboda tsananin gajiya gami da tsamin jiki bisa gumurzun da yayi da shugaba Sultan. ??? ??? ??? Al'amarin su shugaba Sharwan kuwa suna cikin tafiya a daji a cikin ayarin nasu gaba daya sai kawai suka ga Shamirat matar Shugaba Sultan taja linzamin dokinta ta tsaya cak a lokacin da jikinta gaba daya ya kama tsuma kuma kirjinta ya kama daka kamar zuciyarta zata faso kirjin ta fado.Koda ganin haka Sai hankalin Shugaba Sharwan,Ilela dana Siyama ya dugunzuma suka rugo gareta aka sauko da ita daga kan dokinta akayi mata shimfida a kasa saboda tsammanin ko kamuwa tayi da wata rashin lafiya.Nan fa suka shiga tambayarta inda uakeyi mata ciwo a jikinta.Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa Shamirat ta dubi Sharwan tace,sun kashe mijina,naji a jikina baya numfashi a doron kasa.Koda jin wannan batu sai Sharwan ya takarkare ya kurma uban ihu wanda ya tsorata kowa a wajen sannan ya fashe da matsanancin kuka kamar bazai daina ba.Al'amarin daya karya zuciyar Ilele da Siyama Kenan suma suka rungume Shamirat suka taya ta kukan.Saida shugaba Sharwan ya jima a tsugunne bisa gwiwoyinsa yana kuka sannan ya dago kai ya dubi Shamirat,bisa mamaki sai taga yayi mata murmushi yace,mijinki bai mutu rago ba.Na tabbatar da cewar kafin su Sarki Darwaz su kashe shi saida yayi musu mummanar barna saboda nasan irin jarumtakar abokina gami da taurin ransa.Bana raba daya biyu,sai ya bar shaida a jikin Sarki Darwaz.Ina son ku sani cewa zamanmu a waje daya yana da matukar hadari,don haka zaifi kyau mu tashi muci gaba da tafiya.Ba tare da gardamar komai ba kuwa aka kimtsa aka cigaba da tafiya ana keta dazuzzuka masu sarkakiya,kwazazzabai,koramai da fadamomi iri iri suna masu tunkarar hanyar da zata kaisu Birinin Darul Hunam.Saida suka shafe kwanaki arba'in suna tafiya sannan suka iso wani daji mai tsananin fadi mai cike da sahara.Iya hangen mutum a cikin dajin babu bishiyu ko daya,babu duwatsu ko alamar wani danshi na ruwa sai rairayi tsabarsa tsubi-tsubi,wani rairayin ma tudunsa yakai na tsauni.Da isowars wannan wuri sai Shugaba Sharwan ya bada umarni aka tsaya aka yada zango.Bayan an kafa tantuna anci abinci kuma an huta,sai Siyama ta dubi Sharwan tace,yakai Abbana menene dalilin da yasa ka bada izinin mu yada zango a nan wajen?Lokacin da Sharwan yaji wannan tambaya sai yayi ajiyar zuciya sannan ya dubeta cikin alamun takaici yace,yake 'yata idan baki manta ba abokina Sultan ya gaya mama cewa tsakanin birninsa da birnin na gaba wanda ake kira Darul Hunam tafiya ce ta kwana arba'in da daya,yau kuma kwananmu arba'in cif muna tafiya.Kinga kenan saura tafiyar kwana daya jal mu riski birnin Darul Hunam.Dole ne mu tsaya daga nan mu tura dakarun leken asiri domin su gano mana halin da garin ke ciki.Idan an dana mana wani tako ne mu san yadda zamu tsallakeshi.Idan kuma garin bazai shigu ba mu nemi hanyar dazamu kewaye shi.Sa'adda shugaba Sharwan yazo nan a zancensa sai gaba dayan jama'ar banu Hanzar suka aminta da shawarar tasa.Nan yake aka tashi wadansu kwararrun dakarun sumame guda uku wadanda akeji dasu aka turasu izuwa cikin birnin Darul Hunam. &GUDUN TSIRA& Littafi na hudu(4) Part B &A-H Physicist& Nan take aka tashi wadansu kwararrun dakarun sumame wanda ake ji dasu aka tura su izuwa cikin birnin Darul Hunam. ??? ??? ??? A can birnin marigayi Shugaba Sultan kuwa tunda Sarki Darwaz da gimbiya Huraisa suka kama barci basu farka ba har saida gari ya waye rana ta take.Huraisa ce ta fara farkawa tana bude idanunta sai ta yunkura da nufin ta mike tsaye,amma sai wata kuyangarta mai suna Badura tayi sauri ta dannan kafadunta kasa ta dubeta tace,yi hakuri ya shugabata,kiyi sani cewa likita yace kada mu bari kiyi kyakkyawan motsi,domin yin hakan zai iya janyi farkewar dinkin da aka yiwa rauninki.Koda jin wannan batu sai bakin ciki ya turnuke Gimbiya Huraisa ta koma ta kwanta,sannan ta dubi Badura cikin tsananin takaici tace yanzu ina mahaifina yake? Badura tace yana falo yana ta fama shara bacci tun jiya bai farka ba.Huraisa tace maza ki koma wajensa yanzku ki gani,idan har ya tashi daga wannan barcin kice dashi inason na gana dashi yanzu yanzu cikin gaggawa.Badura ta risina tace an gama ya shugabata.Nan take Badura ta mike tsaye ta fice daga cikin dakin ta nufi babban falon na marigayi Sultan.Fitarta ke da wuya sai idanun Huraisa suka kai kan wata babbar akwatin karfe dake jikin bangon arewa na dakin,wacce aka kulleta da wani katon kwadon madubi.Huraisa ta dubi wata kuyanga dabam tace,maza kije ki nemo mini makeri ina son na cire wannan makulli domin naga abinda ke cikin wannan akwati,domin koma meye a ciki yana da matukar muhimmanci ga shugaba Sultan,amma kuma menene dalilin da yasa ya barshi anan bai kaiwa matarsa Shamirat ta tafi dashi ba?Kuyanga ta risina tace an gama ya shugabata.Itama sai ta mike tsaye ta fice daga cikin dakin.Jim kadan da fitar wannan kuyanga saiga Sarki Darwaz yashigo cikin dakin kuyanga Badura na biye dashi kuma fuskarsa na rufe cikin rawani idanunsa kadai ake gani.Koda Huraisa taga Sarki Darwaz a cikin wannan yanayi sai ta yunkura ta mike zaune,sannan ta dubi gaba dayan kuyangin dake dakin tace,ku bamu wuri.Take kuwa kuyangin suka fice suka janyo kofa suka rufe.Sarki Darwaz ya zauna a kan gefen gadon data ke kwance,ya dubeta yace,ki gafarceni yake 'yata,daya yau kema bazaki saki ganin fuskata ba,domin bana son kowa yaga wannan shaida da Sultan yayi min.Koda jin wannan batu sai Hankalin Gimbiya Huraisa ya dugunzuma ainun ta dubeshi cikin alamun tsananin damuwa da takaici a lokacin da idanunta suka ciko da kwalla,tace haba yakai Abbana ai idan har zaka boyewa kowa fuskarka bai kamata ace ni da mahaifiyata ka biye mana ba,saboda zamu iya zama da kai a cikin kowacce siffa ko da kuwa fuskarka tafi komai muni a cikin wannan duniya,tunda ba fuskar taka muke so ba,ruhinka muke bukata ya kasance tare damu dimun da'iman.Lokacin da Gimbiya Huraisa tazo nan a zancenta sai Sarki Darwaz yayi murmushin farin ciki,yace,yake 'yata na sani cewa kuna kaunata kamar yadda kuke son kanku.Ina so ki sani cewa abin kunya ne kuma abin kaskanci a cikin tarihin jarumtakata duniya ta san cewa gwamnan da yake karkashina shine yayi mini rauni a fuskata.Idan kika ga wannan fuskatawa a fili to gawata ce a kwance.Mene ne dalilin da yasa kika aika kina son yin magana da ni yanzu?Koda jin wannan tambaya sai Huraisa tayi ajiyar numfashi sannan tace, ba wani abu bane yasa na aika kazo ba,sai domin na nemi gafararka bisa sakacin danayi har Sultan ya sami nasarar yi min rauni a kafata gashi hakan ya haddasa matsala a cikin tafiyarmu.Kamata yayi ace munci gaba da tafiya yanzu don karfa abokan gaba su kara bamu tazara sosai.Na kirawo kane yanzu domin na baka shawara,shawarar kuwa itace ku kara gaba kada ku tsaya jirana har izuwa gobe don ci gaba da wannan tafiya.Ka tuna cewa idan har wadannan abokan gaba namu suka sami nasarar fita daga cikin nahiyarmu shikkenan sun tsira.Lallai ya kamata mu kure musu wannan GUDUN TSIRA da sukeyi mu kawo karshensu.Yayin da Gimbiya Huraisa tazo nan a zancenta sai hankalin Sarki Darwaz ya rabu gida biyu,ya rasa hukuncin daya kamata ya yanke..Kwatsam sai suka ji ana kwankwasa kofar dakin.Cikin fushi sarki Darwaz ya daka tsawa yace wane ne nan yake kwankwasa mini kofa?Kawai sai sukaji muryar Boka Hurgas yana mai cewa nine ya shugabana.Cikin hanzari Sarki Darwaz ya mike yaje ya bude masa kofar ya shigo.Hurgas ya risuna sannan ya dubi sarki cikin biyayya yace ya shugabana zamanmu a wannan gari har izuwa gobe zai iya janyo mana dalilin dazamu kasa cimma abokan gaba da tazarar kwana daya rak.Abinda za'ayi shine,a dauki Gimbiya a sanyata cikin keken doki a cigaba a tafiyar a haka.Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube gimbiya Huraisa,ba tare da sarki Darwaz yayi wata gardama ba sai ya bada umarni nan take aka fara shirye shiryen tafiya.Kafin abar garin saida Sarki Darwaz ya dora wani babban hadiminsa mai suna Zukairu akan kujerar marigayi Sultan,sannan akayi hawa aka fice daga cikin birnin gaba daya aka durfafi hanyar da zata kaisu birnin darul Hunam. ??? ??? ??? Lokacin da dakarun leken asiri na kabilar Banu Hanzar suka tafi izuwa cikin birnin Darul Hunam domin su gano halib da birnin ke ciki da kuma sirrin komai na birnin,Saida suka kwana suka yini basu dawo ba.Al'amarin daya dugunzuma hankalin su shugaba Sharwan kenan suka fara tunanin ko an kama sune,don haka suma a koyaushe za'a iya kawo musu harin sumame.Nan da nan shugaba Sharwan ya hada taron gaggawa domin suyi shawara bisa abinda ya kamata ayi.Nan fa shawara ta yawaita wasu suce kawai ayi shirin yaki a bi sawun dakarun da aka aika guda uku.Wasu kuma suce a sami wuri a buya a dan kara saurarawa a gani.Saida kowa ya fadi albarkacin bakinsa san nan Siyama ta daga hannu akayi tsit.Siyama ta dubi shugaba Sharwan tace,yakai Abbana inason ka tuna cewa dakarun sumamen da muka tura suyi mana leken asiri a cikin wannan birni na darul Hunam sune suka fi kowa kwarewa a aikin leken asiri a can birnin Kisra gaba daya,kuma sama da shekaru goma suke rike da wannan kambu ba'a taba turasu aikin dasu ka kasa ba.Haka kuma sun kasance dakaru masu tsananin karfin damtse da tsananin karfin gudu da iya jure wahala ta tsawon kwana uku.Bisa wannan dalili nake ganin cewa duk rintsi ko da mutum daya ne daga cikinsu sai ya sami nasarar dawowa nan garemu a raye ya bamu labarin abinda ke faruwa,saboda haka zaifi kyau mu dan kara musu lokaci daga nan zuwa tsakar date ko zuwa gobe da safe,saboda babu mamaki ma yanzu haka suna kan hanyarsu ta dawowa.Lokacin da Siyama tazo nan a zancenta sai jikin kowa yayi sanyi,aka sake yin shiru tsit aka rasa wanda zai soko shawarar data kawo.Kawai Sai shugaba Sharwan yayi murmushi ya dubi Siyama yace,yake 'yata hakika kina da kaifin tunani gami da hangen nesa,don haka na amince da wannan shawara taki.Lallai zamu ci gaba da sauraron dawowar dakarunmu na leken asiri,daga na har zuwa wayewar gari.Amma duk da haka yanzu zamu tura dakarun tsaro mutum bibbiyu izuwa kowane bangare na wannan daji.Wato gabas da yamma,kudu da arewam,nisan tafiyar zngo guda domin su labe su zuba ido.Da zarar sunji wani motsi wanda basu aminta dashi ba,ko sunga wata zuga ta dakaru su rugo su sanar damu.Koda jin wannan batu sai gaba dayan yan majalisar suka mince.Ai kuwa saida dare ya raba sannan akaji dawowar dakarun sumamen da aka aika birnin Darul Hunam,sun taho a guje suna yin alamarsu ta kukan wani tsuntsu.Dama babu wanda yayi bari a cikin ayarin,sai kuwa kowa ya mimmike aka tarye su.Dakarun sumamen suka iso su uku suna ta faman haki kamar ransu zai fita.Suka zube kasa wanwar suna numfashi da karfi kamar ransu zai fita.Saida suka bari suka huce sosai,suka dawo cikin hayyacinsu sannan aka basu ruwa suka sha.Bayan sun nutsu ne Siyama ta dubi babbansu mai suna Hatmara tace ba mu labari yakai tauraruwa mai wutsiya,mu kuka gano a cikin birnin Darul Human? Sa'adda Hatmara yaji wannan tambaya sai yayi ajiyar zuciya sannan yace ya shugabata kiyi sani cewa an sanya tsattsauran tsaro a cikin birnin darul Hunam da kewayensa.Babu ta inda mutum zai ratsa ba tare da ya fada hannun dakaru ba walau ta gabas,yamma,kudu da arewa,amma duk da haka saida mukayi amfani da kwarewarmu muka shiga har cikin tsakiyar birnin ta cikin bututun ruwan kwata dake karkashin kasa,amma da zamu dawo sai wannan hanya ta gagare mubi dole saida muka rafke dakarunsu guda uku a cikin daren yau mukayi shigarsu mukayi kasadar biyo hanyar cikin gari,a kyar da sidin goshi muka iso bakin kofar birnin.Anan ne fa muka gane kuskurenmu saboda saida asirinmu ya tonu aka kama mu aka kai mu wajen shugaban masu gadin kofar.A nan ne akayi kuskure aka shigar da mu cikin wani daki domin gana mana azabar da zatasa mu fadi ko mu su waye.Cikin sa'a muka bubbuge dakarun da suka kamamu a cikin dakin,muka sumar dasu suma mukayi shigarsu muka dawo baki kofa.Inda anan ma mukayi wani yakin na sumame muka bazar da gaba dayan masu gadin kofar kimanin mutum saba'in sannan muka bude kofar garin muka fito muna masu falfala azababben gudu,har sai da muka iso nan yanzu.Ya shugabata a cikin binciken da mukayi a cikin birnin darul Hunam mun gano cewa aljanu sun kai labarin guduwar jama'armu daga can birnin kisra,kuma gwamnan garin ya kafa doka cewa duk dan garin daya boye irin jama'armu a cikin gidansa hukucin kisa ne a kansa.Yanzu shawara ta rage garemu mu san matakin dazamu dauka amma komai zai iya faruwa domin gwamnan birnin darul Hunam zai iya turo dakarunsa su biyo sawunmu su iso har nan su riske mu gaba daya,kuma zau iya tsayawa a bakin birninsa yayi mana mugun tanadi na yakarmu.Babban abinda ya tayar mana da hankali shin yawan dakarun birnin sun ninka namu sau uku,inda mukace zamuyi fito na fito dasu zasu iya karar damu gaba dayanmu.Lokacin da badakare Hatmara yazo nan a jawabinsa sai hankalin kowa ua dugunzuma ainun har da shugaba Sharwan aka rasa wanda zaice kala har izuwa tsawon yan dakiku masu yawa.Kwatsama sai Siyama ta dubi Sharwan tace,zama bai kama mu ba yanzu,dole ne mu tashi yanzu muyi shirin yaki muje mu tari dakarun birnin darul Hunam a kan hanya tun kafin su iso nan.Amma yakin sunkuru zamuyi musu,kuma dole ne mu gaggauta gamawa dasu,sannan muyi shigar su su shiga izuwa cikin birnin muyiwa gwaman garin juyin mulki,domin mu sami damar shiga garin har mu kwana,inyaso da safe mu kara guzuri mu ci gaba da tafiyarmu tunda bamu da wata hanya dazamu bi face ta cikin birnin.Lallai bamu da wani zabi wanda yai muyi kamar yadda na shirya yanzu ni ba haka ba kuwa karshen mu ya yazo.Sa'adda Siyama tazo nan a jawabinta sai wani babban dan majalisa mai suna Dairuf ya dubeta yace,ai juyin mulkin da zamuyi bashi da wani amfani tunda dai bazamu iya sani daga cikin jama'armu ya hau karaga ba,kuma babu wani dan gari dazai yarda ya karbi karagar saboda tsoron Sarki Darwaz.Siyama tace ai bukatarmu bata son karaga bane sai dan kawai mu sami damar kwana a garin da samun garin guzuri da ikon wuce gaba.Shugaba Sharwan yayi ajiyar numfashi sannan ya dubi Siyama yace na yarda dake a kan cewa bamu da wani zabi wanda yafi muje mu yaki wadannan mutane,amma fa hadarin dake cikin yin hakan yana da yawan gaske,kuma ban ga hanyoyin daza'abi a sami nasara.Siyama tace nayi nazarin duk irin hadarin da kake tunani,kuma nayi tunani akan irin dabarun da ya kamata muyi don ganin mun sami nasara.Abinda nake bukata kawai shine ka bani dakaru guda dari biyi kacal daga cikin dakarunka na musamamn masu tsaron lafiyarka,zan jagorance sumu kai ga nasara.Sa'adda Siyama tazo nan a zancenta sai Shugaba Sharwan Sharwan yayi shiru yana mai sunkui da kansa kasa ya fada cikin kogon tunani ba tare daya nemi shawarar yan majalisarsa ba.Daga can sai ya dago kai ya dubeta yace,yake 'yata kiyi sani cewa dalili daya ne zaisa na yarda dake na baki dakaruna na musamman don zuwa aiwatar da wannan aiki mai mugun hadari.Dalili kuwa shine tun kuruciyarki kawo iyanzu ban taba ganin wani abu ya gagareki ba muddin kinyi niyyar aiwatar dashi,haka kuma ban taba ganin kin shiga hadarin da kika kasa fita ba.Zanyi kundubala a yanzu na baki dama,amma ina gargadinki daki sani cewa idan har kika kasa samun nasara kika janyo dalilin da kabilarmu ta tarwatse ko kuma mukayi asarar dumbin rayuka da dukiya mai yawa bazan taba yafe miki ba.Idan kin yarda da wannan sharadi na baki izini ki debi dakarun anwa yanzu ki tafi.Koda jin wannan batu na shugaba Sharwan Sai hankalin Siyama ya dugunzuma ainun saboda tasan abinda yake nufi bazai taba yafe mata ba,yana nufin cewa zai datse duk wata alaka dake tsakaninsa da ita tamkar ma bai taba sanin taba,amma saboda ki fadi da tashin karayar zuci irin ta Siyama sai taki nuna tashin hankalinta a fili kawai ta dubi shugaba Sharwan cikin murmushi tace na yarda da wannan sharadi naka ya shugabana.Tana gama fadin hakan sai ta waro wadannan dakaru na musamman guda dari biyu tayi musu umarnin suje su shirya cikin gaggawa.Nan take kuwa suka sanya bakaken tufafi suka rufe ko'ina na jikinsu idanunsu,bakinsu da hancinsu kadai ake gani.Wani irin talakarma suka sa a kafafunsu masu taushin gaske,gami da duhu yadda komai suka daka baza aji sautin sahunsu ba sannan a jikin kowanne daya daga cikinsu akwai wadansu kananan wukake masu azabar kaifi da tsini sirara guda dari.Haka kuma suna dauke da kwari boye a bayansu mai cin kibiya dubu da kuma karamar baka rataye a bayansu da kuma sharbebiyar takobi.Sudai wadannan dakaru an basu horo na musamman wanda yasa suka kware ainin a wajen iya kisan mummuke.Bayan wadannan dakaru sun gama shirinsu sun jera akan layi sahu biyu,sai ga Siyama ta fito daga cikin tantinta itama tayi shiga iri daya da tasu.Al'amarin daya baiwa kowa mamaki kenan a sansanin domin ba a taba ganinta ba a cikin irin wannan shiga,kuma babu wanda ya san cewa ita ma tana da horo irin na wadannan dakaru.Nan take Siyama ta karaso gaban Shugaba Sharwan ta bukaci yasa nata albarka,kuma ya nema mata sa'a a wajen iyaye da kakanni saboda su dai wannan kabila ta Sharwan basu da wani addini guda da sukyi imani dashi face iyayensu da kakaninsu amma dai suna aiki da tsafi ko sihiri.Nan take Shugaba Sharwan ya dafa bayan Siyama kuma ya sumbaci goshinta yasa mata albarka,kuma yayi mata addua.Nan take Siyama taji wani irin gagarumin karfin gwiwa ya shige ta.Kuma taji dukkan tsoro ya kau daga cikin zuciyarta.Ba tare da bata wani lokaci ba sai Siyama taja wadannan dakaru suka falfalwa da gudu izuwa cikin daji suna yin wani irin gudu na ban al'ajbi tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya,kafin kace wani abu tuni sun kule uma sun bace a cikin duhun daren.Saida su Siyama sukayi 'yar doguwar tafiya ta yan dakiku masu yawa tana kan gaba sannan ta tsaya cak suma dakarun guda dari biyu sai sukayi cirko cirko a bayanta.Siyama ta tsuguna kasa ta kara kunnenta a kasa tayi sauraro dan kadan sannan ta mike tsaye zumbur ta yafito dakarun su duka sukayi mata kawanya,tayi musu radar wata magana.Nan take dakarun sukayi wani sihiri su duka a lokaci guda.Kawai sai kasa ta tsage suka shige cikinta kuma kasar wajen ta koma ta hade kamar wani abu bai taba faruwa ba a wajen.Itama Siyama ta shige cikin kasar ta kule.Faruwar hakan keda wuya da kimanin tsawon rabin sa'a saiga dakarun birnin Darul Hunam su da yawa bisa dawakai dauke da muggan makamai sun iso daidai wannan wuri.Da isowarsu sai shugaban nasu ya daga hannu ya tsaya.Take sauran yaran nasa ma suka ja linzamin dawakansu,dawakan sukayi turjiya da haniniya.Shugaban dakarun ya shaki kamshi har sau uku yace,tabbas zuga ta bil'adama ta tsaya a nan.Kafin ya gama rufe bakinsa sai sukaji kasar wajen ta kama tsagewa,dawakansu na ruftawa ciki.Kafin dayansu yayi wani yunkuri duk an wurgo musu wukake masu tsani sun caccake su a wuya da makogwaro.Nan fa suka rinka sulalewa kasa daga kan dawakansu suna bajewa kasa matattu,kafin kiftawar ido su duka sun zama gawa,sauran shugabansu shi kadai a tsaye jikinsa na karkarwa yana waige waige da dube dube,amma baiga wanda yayi musu wannan barna ba.Bazato ba tsammani kuma sai yaga kasar ta kara tsagewa,sai ga dakaru na fitowa sama daga cikin karkashin kasa su dari biyu suna yi masa kawanya.Saida suka gama fitowa gaba dayansu sannan na cikon dari biyu da daya ya fito,kuma ba wani bane face Siyama.Kafafunta na dira kan kasa saita durfafi shugaban wadannan dakaru kai tsaye tana rike da sharbebiyar takobi,a lokacin dashi kuma ya nutsu ya daina tsoron komai ya kura mata idanu kawai yana mai sadudar jin kaifi ya ratsa shi.Bisa mamaki sai yaji Siyama ta dora fadin takobin akan kafadarsa sannan ta dubeshi cikin murmushin mugunta tace shin kana da iyali? Mutumin yace kwarai kuwa inda da mace daya da 'ya daya.Siyama tayi murmushin murna tace nasan zaka so ka koma garesu a raye,don bazasu so su rasaka ba,kaima bazaka so ka rasa su ba.Idan kabi umarnina da dokokina zaka koma garesu a raye kuma cikin koshin lafiya,amma fa idan ka sabawa umarnina da dokokina ko gawarka ma iyalin naka bazasu shaidata ba.A yanzu inason ka yi mama jagowa mu koma har izuwa cikin birninku kuma har cikin gidan sarautarku gaban sarkinku a matsayin mune jama'arka ba a kashe maka ko yaro daya ba,ka bar sauran yaranka ne a baya.Kada ka kuskura kayi rawar baki ko ka munafuncemu yadda asirinmu zai tonu.Idan kayi haka tabbas a bakacin ranka.Koda gama fadin hakan sai Siyama ta dubi dakarun nata tayi musu alama,nan take suka tube kayan matattun dakarun suka sanya,kuma suka dau makamansu suke haye kan dawakansu.Ita kuma Siyama sai tayi irin shiga irin wannan,sannan tasa wannan shugaban dakarun ya hau nasa dokin itama ta hau dokin suka jera da ita dashi.Sauran dakarun nata na biye dasu a baya.Babu abinda zai baka mamaki a cikin wannan hikima da Siyama tayi face yadda ta shirya dakarun nata girman jikinsu yazo iri daya dana dakarun da suka kashe masu bin wannan shugaba a baya.Ita kanta sai gashi jikinta yazo iri daya dana mataimakinsa kai kace wancan din ne wanda aka kashe.Karkakara Kaka.Laifin dadi karewa.Muje ga littafi na biyar don jin ci gaban wannan kasaitaccen labari.Sai mu hadu a 5 gobe gaba dayansa Insha Allah.Dama kamar yadda na fada 1-5 ne ya fito. Seriously Ina Bukatar Addu'ar ku.Don Allah a taimaka a sakani a ciki akan Allah ya cikan wasu bukatu na. GUDUN TSIRA Littafi na hudu Na Abdulaziz Sani m gini Ebook creator:- Shuraih 99% For more adventure hausa ebooks visits our wepsite www.shuraih.waphall.com Domin samun wasu littatafan yaki a matsayin ebooks sai ku ziYarci shafinmu akan www.shuraih.waphall.com ??GUDUN TSIRA 5 Littafi na biyar Na Abdulaziz sani madakin gini Ebook creator:- Shuraih Usman 99% Domin download na wasu kayatattun littatafan Hausa a matsayin Hausaebooks tayadda zaku iya saukewa ku karanta acikin wayoyinku sai ku ziyarci wannan shafi www.shuraih.waphall.com Sannan ku zabi littafin da kuke so For more download of some non- fictional hausa books as a hausaebooks so that you can download it to your phone and read it at any time (offline reading) then visit our wepsite at www.shuraih.waphall.com Adress and select your books for offline reading Gargadi:- wannan ebook din bana sai ruwa bane kuma ba anyishi bane don batanci ga wani koh ga wata Sannan ni shuraih Usman 99% bana tura littafi ta private kuma bana whattsapp sannan banda group a whattsapp ga wanda yaga wani kuskure da muka making acikin wannan littafi sai kiramu akan wannan nombar 08170707521 Ga duk wanda baisan yadda ake downloading na littatafanmu ba sai ya ziyarce mu akan wannan adireshin yanar gizo gizon http://keffians.xtgem.com/forum Sannan yayi tambaya in sha'Allah muku ma zamu mai bayani dalla dalla akan yadda ake sauke littatafanmu Sannan ina kara maimaitawa bana whattsap kada wani ya ha'ince ku ta hanyar amfani da sunana a whattsap asha karatu lafiya Hakkin mallaka (m) Abdulaziz sani madakin gini HAKA DAI SU SIYAMA suka ci gaba da tafiya a cikin shigar dakarun birnin darul Hunam,har suka iso birnin.Da isowarsu bakin kofa sai daya daga cikin masu gadin kofar ya dauki fitila ya bude wata yar karamar taga a jikin kofar wacce ta kasance ta karfe ya haska.Koda yayi arba da fuskar sadauki Samhur wanda shine ya jagoran dakarun da suka fita dazu sai yayi murmushi ya bude kofar.Nan take su Siyama suka kunna kai izuwa cikin birnin.Kwatsam sai sukaga wasu dakaru masu yawa sun taso musu sunyi musu kawanya suna masu ritsa su da makami.Daya daga cikin dakarun ya dubi sadauki Samhur yace,yaya dazu ka fita tare da dakaru kimanin dubu uku,amma yanzu ka dawo da yan tsiraru,kayi bayani mu ji idan bamu gamsu ba yanzun nan zamu kaddamar daku.Koda jin wannan batu sai sadauki Samhur ya dakawa mai maganar tsawa yace kai Zambaru shin ka sami tabin kwakwalwa ne?Ya za ayi na dawo tare da dakaruna gaba daya alhakin harin sumame muka kai don gamawa da yan kabilar Banu Hanzar?Ai mun isa har can sansaninsu mun tarwatsa su sun gudu,kuma sun bazama izuwa cikin daji.A dalilin hakane na bar dakaruna a can suka lallabe domin idan suka dawo su gama dasu.Yanzu na dawo ne da tsirarun yarana domin na sanar da gwamna halin da ake ciki,saboda asan matakin da ya kamata a dauka a gaba.Lokacin da Zambaru yaji wannan batu

Chapter 4 of 5