Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 5
suyi MUTUWAR KASKO.Koda ya kawo mata sura sai ta sunkya ta shige ta karkashin kafafunsa ta dako gadon bayansa da kafafunta ta baya,kawai sai ya fadi kan katakon karyayyen wannan gado.Take wani icen gadon ya tsireshi a ciki ya hudo ta gadon bayansa.Sarki Ruguzan ya rinka kwarara uban ihu da kururuwa sannan idanunsa suka kafe,jikinsa gaba daya ya sandare ya zama gawa.A sannan ne Siyama ta mike tsaye tana layi sakamakon jinin dake zuba a gefen kanta saboda ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????      !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????      !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~???????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????naushin da Sarki Ruguzan yayi mata dazu ya tsaga mata kanta kuma har sannan hancinta bai daina yoyon jini ba.Hakika ita kanta Siyama bata taba zaton cewar zata tsira ba daga sharrin Sarki Ruguzan ba,kawai ta saida ranta ne akan ko tayi nasara kota rasa rayuwarta.Lokacin da Sarki Ruguzan yayi mata wannan naushi a fuskar ta ta kife kasa ba suma tayi ba,amma ta fita daga cikin haiyacinta saita dauke numfashinta tayi kamar suman tayi.Damar datayi amfani da ita kenan ta shammaceshi ta zaro wannan kashi daga cikin aljihun wandonta cikin bakin zafin nama ta soka masa a makoshinsa.Lokacin da Siyama ta dubi gawar Sarki Ruguzan ta tabbatar cewar ta mutu sai tayi murmushin farin ciki amma data juyo ta dubi kofar gidan ta tabbatar da cewar bazata iya budeta ta fita ba sai hankalinta ya dugunzuma ainun sannan ta dubi ko ina a cikin gidan taga babu ta inda zata iya fita sannan ta tuno cewar idan fa aka sake jimawa akaji shiru za a bude kofar dakaru su shigo,in kuwa aka shigo aka ga ta kashe Sarki itama rubdugu za a yi mata a kasheta kuma tabbasa sarkin yawa yafi sarkin karfi.Kuma bayan an kasheta za a bi sawun dukkanin jama'arsu a hallakasu.Koda tazo nan a tunaninta sai hankalin ya kara dugunzuma fiye da ko yaushe ta rasa abinda ke mata dadi a duniya,nanfa ta kama kai kawo a cikin gidan tana mai ci gaba da kalle kalle da tunani.Tana cikin hakane ta daga kanta ta kallo rufin saman gidan saita ga ashe na katako ne.Nan take farin ciki ya lullubeta kawai saita daka tsalle sama ta kama rufin tayi ta tafiya a kansa da hannayenta da kafafunta tamkar kadangaruwa har saida ta iso wani wuri inda ta dan hango hasken wata yar karamar huda sannan tasa hannunta ta doki wajen take katakon daya rufe wajen ya burme.Tana zura kanta ciki ta shigo sai gashi ta fito a saman gidan.Cikin sauri tayi ruf da ciki akan rufin saman domin dakaru ta hango suna takai kawo a ko ina cikin gidan sarautar don tabbatar da tsaro.Saida ta shafe yan dakiku a kwance a saman ginin sannan taga dakaru sun rarrabu saura mutum daya jak a wani sako.Cikin hanzari ta daka tsalle ta duro a bayan wannan badakare ta murde wuyansa ya sulale kasa matacce,kawai sai ta jashi izuwa cikin wani sako mai duhu ta cire kayan jikinsa tayi canji da nata,kawai sai ta bude wani kwandon shara na karfe ta jefa gawar badakaren a ciki ta rufe kawai sai ta fito daga cikin sakon ta kunna kai izuwa hanyar fita daga gidan sarautar gaba daya kai tsaye ba tare da shakkar komai ba ta saje a cikin dakarun gidan sarautar masu fita.Duk da cewar ta saje da dakarun zuciyarta sai bugawa takeyi da karfi domin gani take yi kamar a koda yaushe asirinta zai iya tonuwa a gane ko wacece ita.Wani iko na Allah kuma ta gaban wannan hadimi daya kaita inda Sarki yake ta wuce harma suka hada idanu amma bai shaidata ba.A Wannan lokaci hadimin ya kagu yaga Sarki ya bude kofar wannan gida ya fito amma sai yaji shiru.A wannan lokacin ji yake kamar ya bugawa sarki kofa amma saboda tsoron kada yayi laifi shi yasa bai buga kofar ba kuma yayi tunaniin ko har a sannan sarko bai gama more rayuwarsa ba da Siyama.Har Siyama ta iso bakin kofar karshe ta gidan Sarautar babu wanda ya tareta,amma tun kafin ta iso bakin kofar taga masu gadin su hudu sun kura mata idanu suna yi mata kallon rashin sani da rashin yadda.Nan take Siyama ta gane cewa lallai idan ta karaso bakin wannan kofa baza'a barta ta fita ba sai an binciketa,in kuwa aka binciketa sai an gano wacece ita.Koda ya rage baifi taku uku bata riski masu gadin sai ta daka tsalle sama ta makesu da kafafunta su duka hudun a fuskokinsu a lokaci guda suka zube kasa sumammu.Ai kuwa dakarun dake bayanta suka hango abinda ya faru suka falfalo da gudu,itama Siyama tana durowa kasa bisa kafafunta sai ta falfala da azababben gudu na ban al'ajabi ta fice gaba daya daga cikin gidan sarautar.A sannan ne fa dakaru suka bita duu!suna ihu suna harba mata kibiyoyi.Idan mutum yaga yawan dakarun da suka bi bayan Siyama suna son su kure mata gudu,kuma mutum yaga irin ruwan kibiyoyin da ake yi mata dole ne yayi rantsuwa cewa babu yadda za'ayi ta tsira da rayuwarta.A can kofar wannan gida na cikin gidan sarautar wanda Siyama ta kashe Sarki Ruguzan a cikinsa.Koda wannan hadimi yaga dakarun gidan sarautar gaba daya sun rude suna ihu kuma sun ruga izuwa can kofar fita daga gidan sai shima ya dimauce yayi zargin ko Siyama ce yabi ta wata hanyar daban ta gudu,don haka hannunsa na karkarwa yasa kuba ya bude kofar yaja wadansu dakaru masu yawa suka ruga izuwa cikin gidan.Suna isa inda gadon nan na sarki yake sai suka iske gawar Sarki Ruguzan soke a jikin katakon gadon.Koda sukayi arba da gawar sai kowa ya firgita ainun kuma suka cika da tsananin mamaki.Nan take wannan hadimi ya kurma uban ihu mai tsananin firgitarwa ya dakawa dakarun dake bayansa tsawa yace maza kuje ku gayawa sarki yaki cewar 'yar shugaba Sharwan ta kashe sarki kuma ta gudu.Nan take wadannan dakaru suka juya da baya da gudu shi kuma sai ya fara kokarin cire gawar daga jikin katakon da take tsire.Saida aka shafe sa'a uku da rabi ana tseren gudu tsakanin Siyama da wadannan dakaru su basu cimmata ba ita kuma ba ta bace musu ba,tun ana cikin birnin kisra har aka shiga cikin daji.Babu abinda ya daurewa dakarun kai yayi matukar basu mamaki face ganin yadda Siyama ta tsallake harin ruwan kibiyoyin da ake yi mata ta sama da kasa kai kace aikin sihiri ne.Koda aka shiga cikin wani daji wanda Siyama ta saba yin farauta a cikinsa tun tana yarinya karama ta lakanceshi ainun sai ta fada cikin wani surkuki mai yawan duhuwoyi,hanyoyi barkatai gami da koramai da kwazazzabai da kuma manyan ramuka da ciyoyin fadamomi da koramu.Tana shiga cikin wannan surkuki sai dakarun suka nemeta sama da kasa suka rasata tamkar anyi ruwa an dauke.Amma saboda naci har gari yayi duhu Dakarun basu bar dajin ba suna ta neman Siyama a cikin kowanne sako da lungu har cikin kogon duwatsu shiga suke suna haska ko ina da fitilun itatuwa.A karshe dai ba basu ganya ba sai sukayi hakurin dole suka koma izuwa can gidan sarautar.Suna zuwa ne suka iske gidan sarautar a cike da mutane ana gabatar da jana'izar sarki Ruguzan.Da yawa daga cikin mutanen garin murna sukeyi bisa mutuwar sarki Ruguzan saboda tsananin mulkin zaluncin da yake yi musu,to amma saboda tsoron dan'uwansa Yarima Darwaz wanda shine zai gaji karagar mulkin babu wanda ya nuna farincikinsa a fili. Babu wanda ya nuna farincikinsa a fili.A wannan lokaci tuni an binne Sarki Ruguzan a cikin kabarinsa,yarima Darwaz ya kwanta akan kabarin yana ta faman rusa kuka da ihu.Da kyar da sidin goshi fadawa suka bashi baki suka lallabeshi ya tashi daga kan kabarin.Yarima Darwaz da Sarki Ruguzan sun kasance uwa daya uba daya,kuma yarima Darwaz ya girmi sarki Ruguzan,asali ma shine ya kamata ya hau kan karagar mulki amma saboda tsananin son da yake yiwa dan uwan nasa Ruguzan ya hakura ya bar masa sarautar.A takaice dai a duniya babu abinda Yarima Darwaz yakeso a duniya sama da Sarki Ruguzan,don haka a wannan rana yana cikin tsananin bakin ciki wanda ba zai iya misaltuwa ba kuma gashi ya kasance mutum mai bakar zuciya gami da rashin imani fiye da Sarki Ruguzan,don haka a wannan rana hatta fadawan kasar ma a tsorace suke dashi suna baya baya don gudun kada ya huce haushinsa a kansu.Lokacin da wadannan dakaru masu wadanda suka tafi neman Siyama suka dawo sai suka zube kasa agaban Yarima Darwaz suka sunkui da kawunansu kas aka rasa wanda zaiyi bayanin cewar ba aga Siyama ba wacce ta kashe Sarki Ruguzan.Koda Darwaz yaga haka sai ya kara fusata ainun ya yunkura da sauri ya zare takobinsa da nufin ya hau Dakarun da sara,kawai sai yaji an daka masa tsawa.A fusace ya waiga,koda yaga wanda yayi masa tsawar sai jikinsa yayi sanyi ya sauke takobin tasa kasa cikin sanyin jiki.Ba wani bane yayi masa tsawar ba face matarsa ZUMAIRA.Zumaira ya karaso gaban Darwaz ta karbe takobin dake hannunsa ta dubeshi tace,idan ka kashe wadannan dakaru bazaka sami sakamakon komai ba face na dadin bacin rai da bakin ciki tunda asarace ga masarautarmu.Tunda dai Sarkin yaki da manyan zakwakuran dakarunsa sun bi bayan wannan Yarinya na tabbatar da cewar sai ka yanke mata hukuncin daya dace da laifin data tafka.Koda Zumaira tazo nan a zancenta sai Yarima Darwaz ya zubar da hawaye sannan ya matsa gaban kabarin dan uwan nasa ya dafashi yace,Na rantse da kaunar da nake yiwa Sarki Ruguzan sai nayiwa Siyama mugun kisan gilla irin wanda ba a taba yiwa wani mahaluki ba a doron kasa,kuma sai na shafe gaba dayan kabilarsu daga kan doron kasa yadda har abada ba za a sake tunowa dasu ba.Koda fadin hakan sai Darwaz ya sake kwantawa akan kabarin Sarki Ruguzan ya fashe da sabon matsanancin kuka har saida Zumaira tazo ta tasheshi tsaye ta shiga rarrashinsa ta jashi izuwa cikin gidan Sarautar sannan kowa ya kama gabansa. ??????? SARKIN YAKIn birnin kisra basu dawo daga bin sawun Siyama da jama'ar kabilarta ba sai bayan kwana uku.A wannan lokaci ma tuni anyi bikin nadin sarautar Sarki Darwaz ya hau karagar mulki amma a tsawon kwanaki ukun Sarki Darwaz bashi da wani sukuni da kwanciyar hankali,burinsa kawai yaga sarkin yaki ya dawo tare da Siyama.Da rana tsaka su Sarkin yaki suka shigo fadar birnin kisra suna shigowa fadar suka iske Sarki Darwaz zaune bisa karagar ya sunkui da kansa kas,gashi ana ta tafiyar da harkokin mulki amma shi Sarki Darwaz yayi shiru kamar bashi ne sarkin ba domin fadawa ne suke zartar da komai.Koda Sarki Darwaz yaji sawun dakaru da yawa sun shigo cikin fadar saiya dago da kansa da sauri amma dayaga sarki yaki akan gaba babu Siyama a tare dashi sai jikinsa ya kama tsuma,zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone saboda tsananin fushi.Sarkin yaki ya zube kasa gaban sarki Darwaz bisa guiwoyinsa yana mai sunkui da kansa kas yace,ya shugabana munbi sawun Siyama har izuwa sansaninsu a daji inda muka isle babu ko kaza a wajen sun kwashe komai nasu sunyi hijira.Mun sake bin sawunsu izuwa cikin dajin har tsawon kwanaki biyu amma ko duriyarsa bamujiba domin sawunsu dana dabbobinsu ma ya dauke.Al'amarin dayayi matukar bamu mamaki kenan tamkar aikin sihiri.Koda sarkin yaki yazo na a zancensa sai sarki Darwaz ya mike tsaye a fusace ya kwarara uban ihi wanda ya firgita kowa a cikin fadar.Faruwar hakan ke da wuya sai ga Bokan Garin wanda ake kira HURGAS IBINI SALBARU ya bayyana tsulum a tsakiyar fadar.Hurgas ya karasa gaban Sarki Darwaz suka kurawa juna idanu sannan Boka Hurgas ya risina yace Ya shugabana,Siyama da sauran jama'arsu suna nan a cikin yankin kasarka sun saje da mutane a cikin daya daga cikin biranenka,bisa wannan dalili ne yasa ba a gano inda suka ba.Idan har ka bari suka fice daga cikin wannan nahiya tofa har abada baza a dauki fansa akansu ba kuma komai daren dadewa sai Siyama ta dawo kasar na ita da jama'arta ta rushe mulkinmu sun karbi karagar kasar bisa taimakon wata hatsabibiyar jaruma wacce zata addabi gaba dayan sarakuna da attajiran duniya.Koda Boka Hurgas yazo nan a zancensa sai hankalin Sarki Darwaz ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe ya dubi Hurgas cikin alamun tsananin damuwa yace,yakai abin dogarona iyaye da kakanni maza ka sanar dani birnin da su Siyama suke domin nayi shiri da kaina na jagoranci dakarun yaki masu yawa muke mu shafesu daga doron kasa.Koda jin wannan batu sai Boka Hargus yayi ajiyar zuciya cikin alamun karayar zuciya yace,ai nayi iya kokarina domin na gano inda suke amma na kasa saidai kawai na sami nasarar ganowa cewa suna bangaren gabashin kasar nan.Don haka ku hanzarta tunkarar dukkanin manyan birane da suke gabas har izuwa karshen iyakarmu.Koda jin wannan batu sai Fuskar Sarki Darwaz ta fadada da murmushi na farinciki nan take ya dubi Sarkin Yaki Amzad yace maza kaje ka shirya mana sabuwar runduna ta mayaka dubu dari uku,ni da kai zamu jagorancesu izuwa gabashin kasar nan kuma tun kafin mu tafi inason a tashi manzanni su tafi izuwa biranen dake karshen iyakokinmu a gayawa shugabanninsu cewar su rufe kofofin garuruwansu yadda ba shiga ba fita har sai na aiko da umarni.A sannan ne fada ta watse kowa ya kama gabansa.Har Sarki Darwaz ya jiya zai shiga cikin gidan sarautar saiya juyo da sauri ya dubi Boka Hurgas a cikin alamun damuwa a karo na biyu yace,yakai abin alfaharin birnin kisra waishin wace shu'umar budurwar jarumar da idan ta hadu da Siyama zata taimaketa har ta rushe mulkinmu?Koda jin wannan tambaya sai boka Hurgas yaja dogon numfashi gami da ajiyar zuciya sannan yace hakika kayi tambaya mai kyau kuma mai muhimmanci saidai a yanzu babu isasshen lokaci wanda zai isa na baka labarin wannan shu'umar jaruma wacce daidai take da GUGUWAR ZAZZAGAR BALA'I ga dukkan sarakunan duniya.Shawarar da zan baka kawai itace kayi hakuri zan baka labarin wannan jaruma ko da akan hanyarmu ne ta dawowa bayan mun sami nasarar gano inda su Siyama suke mun shafesu daga doron kasa. A WANE HALI 'YAN KABILAR SU SIYAMA SUKE CIKI? SHIN SARKI DARWAZ ZAI CIKA BURINSA? INA LABARIN SIYAMA DA TAKE GUDUN TSIRA? SHIN ZATA KOMA CIKIN KABILARTA? A WANE HALI MAHAIFINTA DA MAHAIFIYARTA SUKE CIKI? INA LABARIN ABOKAN TAFIYARTA DATA UMARCESU SUYI GABA,A WANE HALI SUKE CIKI? Mu hadu a GUDUN TSIRA kashi na uku don jin cigaban wannan kasaitaccen labari. Da alamu littafin bai karbu ba ko Dan ba samun comments. Barkan ku da Sallah.Allah ya maimaita mana.Ameen. Gudun tsira Littafi na biyu 2 Na Abdulaziz sani m gini Ebook creator::- Shuraih 99% You can download more hausa novels ebooks At http://shuraih.waphall.com Zaku iya downloading na wasu littatafan mu amatsayin ebook ta hanyar latsa wannan blue din rubutun www.shuraih.waphall.com ??GUDUN TSIRA Littafi na Uku Na Abdulaziz Sani m gini Ebook creator:- Shuraih 99% For more adventure hausa ebooks visits our wepsite www.shuraih.waphall.com Domin samun wasu littatafan yaki a matsayin ebooks sai ku ziYarci shafinmu akan www.shuraih.waphall.com &GUDUN TSIRA& Littafi Na Uku(3) Part A &A-H Physicist& KODA JIN WANNAN BATU NA BOKA hurgas sai Sarki Darwaz ya dubi hurgas cikin matukar mamaki yace,au dama tare da kai zamu tafi neman Siyama da jama'arta?Boka Hurgas yace kwarai kuwa ai na fika tashin hankalin idan har ban tabbatar da mutuwar Siyama ba da jama'arta saboda in dai wannan lokaci yazo to duk wani Boka dayake wannan nahiyar ma sai sun kashe shi sun shafe harkar tsafi gaba daya tamkar ba a taba yinta ba a wannan nahiyar,duk cikin bincikena na ga wannan al'amari.Sa'adda sarki Darwaz yaji wanann batu sai ya gyada kai yace ai kuwa indai muka hada karfi da karfe mu ta kai dole ne muga bayan wadannan makiyan namu.Yanzu zan shiga cikin gida nayi shiri in yaso ka samemu a can kofar fada inda zamuyi zuga mu tafi gaba daya.Lokacin da boka Hurgas yaji wannan batu saiya bushe da dariya sannan yace aini bana bin zugar mutane saidai ku riskeni a can gaba ko hanya ina jiranku.Nine zan zamo mai yi muku jagora har mu riski abokan gaba tunda nine zanfi kowa saurin gano inda abokan gabar suke.Koda gama fadin sai boka Hurgas ya bace bat daga cikin fadar tamkar bai taba wanzuwa ba a wajen.Koda ganin hakan sai sarki Darwaz ya ruga izuwa cikin gidan sarautar ya iso cikin ainihin turakarsa ya shiga kimtsa kansa yana sanya kayan yaki.Yana cikin wannan haline matarsa Larisa tare da 'yarsa gimbiya Husaira suka shigo cikin turakar da sauri cikin tsananin tashin hankali.Husaira ta kasance kyakkyawar budurwa abar kwatance domin da kadan Siyama zata fita kyau.Ga wanda ma bai iya tantance kyawu ba cewa zaiyi sunyi kunnen doki.Lasira da Husaira suka sha gaban Sarki Darwaz idanunua cike da kwalla suna shirin fashewa da kuka.Kawai sai Lasira ta kama kafadun Darwaz ta rike a lokacin da hawaye ya zubo mata ta dubeshi tace,haba yakai mijina saboda me zaka bar karagar mulkinka ka tafi farautar kabilar Banu Hanzar alhalin baka da tabbacin ganinsu tunda sunyi hijira sun gudu.Kayi sani cewa zata iya yiyuwar cewa tuni ma sun fice daga cikin nahiyar nan gaba daya.Ka tuna cewa fa kwananka uku kacal akan karagar mulkin nan,Idan har wani tsautsayi ya sameka a cikin wannan tafiya shike nan fa ka rasa karagarka nida 'yarka kuma rayuwarmu ta shiga cikin hadari kenan tunda ka san cewa kana da makiya da yawa a cikin majalisar garin nan da cikin jama'ar gari.Lokacin da Lasira tazo nan a zancenta sai Sarki Darwaz ya bushe da dariya,al'amarin dayai matukar baiwa Larisa mamaki da haushi kenan,ta kura masa idanu,ita kuwa Husaira sai ta sunkui da kanta kas tana zubar da hawaye kawai.Daga can sai Darwaz ya tsuke bakinsa kuma ya hade fuska ya dubi Lasira yace,yake matata yanzu ke ashe har kina tunanin cewa wani abu zai iya taba lafiyata a wannan fita da zanyi?Ashe kin manta da cewa ni mutum ne mai tsananin sa'a da rabo bisa dukkan abinda na sa agabana?A iya saninki dani tun muna matasa wane abune kika taba ganin ya gagareni?Larisa ta girgiza kai tace duk abinda kasa agabanka sai kaga bayansa amma wannan karon naji a jikina cewa lallai zaka riski matsala kasancewar mai Laya ya kiyayi zamani.Darwaz ya gyada kai cikin murmushi yace,ai ko Giwa ta fadi tafi karfin karnuka su dasa mata wawa sai a sannu.Kada ki manta cewar 'yarki Husaira ta gadoni a jarumtaka gani da taurin zuciya,don haka ko babu ni dole ne ayi shakkarki saboda ita kuma itace zata gaji karagata.Ke Husaira mene dalilin da yasa kike zubar da wannan hawaye daga idanunki?Shin kina tsoron kada na fita ne wani tsautsayi ya sameni?Koda jin wannan tambaya sai Husaira ta dago kai ta dubi sarki Darwaz cikin murmushi tana mai share hawayenta tace,ko kadan ni bana tunanin akwai wani mahaluki ko wani tsautsayi da zai sameka.Ina zubar da wannan hawaye ne saboda kawai takaicin kace bazaka tafi tare dani ba.Ka sani cewa a rayuwata ban taba fita yaki ba na daukar rayukan bil'adama da yawa.Wannan ce kadai damar da nake da ita wacce zan gwada tsantsar iyakar jarumtakata kuma a yanzu ne takobina za ta sami damar shan jini mai yawa ta more,amma gashi ka hana.Ina mai rokonka don darajar iyayenka da kakanninka wadanda suka shude kayi mini izini yanzun nan naje na kimtsa cikin gaggawa ayi wannan tafiya dani.Ka tuna cewa ni kaina jarumtakata ta ninka ta marigayi sarki Ruguzan sau uku,bare kai kanka.Ai abin kunya ne ma ace kaine da kanka zaka tari Siyama ka yaketa,ni ya kamata ka barni da ita a matsayina na 'ya mace kamarta nayi mata kisan gilla na ciro kanta nazo maka dashi.Lokacin da Husaira tazo nan a zancenta sai mahaifiyarta ta shara mata mari ta dubeta a fusace tace,yanzu ke dama manufarki kenan,ashe ban sani ba?Wato zuciyarki ta kekashe ta zama irin ta ubanki kin gadoshi da rashin imani da tausayi alhalin kina matsayin 'ya mace wacce nake son tayi aure ta bar mini zuri'ar dazanyi alfahari da ita mai farin jini a cikin al'umma?Koda Larisa tazo nan a zancenta sai Husaira da Sarki Darwaz suka duni junansu suka bushe da dariya.Husaira ta hade rai ta dubi Larisa tace yake ummina ki sani cewa kyan 'da ya gaji ubansa,idan mai mulki yana son ya sami karfi da biyayyar talakawansa dole ne ya kasance mara tausayinsu.Ni SARAUNIYAR GOBE ce wadda take da burin dama yafi na mahaifinta don ni so nake na mallaki duk kasashen dake nahiyar nan gaba daya su zamo a karkashin mulkina.Koda jin wannan batu sai Sarki Darwaz da Larisa suka kurawa Husaira idanun cikin tsananin kaduwa da mamaki,daga can sai Sarki Darwaz ya bushe da dariyar farinciki yace,tabbas yaune na san cewa banyi haihuwar banza ba tabbas na sami irin 'yar dana dade ina mafarkin samu.Koda gama fadin hakan sai Sarki Darwaz ya rungume Husaira cikin murna yana A*H PHYSICIST maicewa,jeki ki shirya yake 'yata lallai tare dake zamu tafu wannan gagarumin yaki.Kafin Sarki Darwaz ya gama rufe bakinsa tuni gimbiya Husaira ta ruga izuwa cikin turarkata.Ita kuwa Larisa saita durkushe a kasa ta fashe da kukan bakinciki.Ko kallonta Sarki Darwaz baiyi ba ya gama shirinsa ya zuba dukkanin makamansa na yaki a jikinsa sannan ya fice daga cikin turakar ya bar Larisa a zaune a kasa dirshen tana rusa kuka.Wannan shine abinda ya faru a cikin birnin Kisra bayan Siyama ta sami nasarar kashe Sarki Ruguzan da kyar da sidin goshi domin ta kawo karshen mulkin zaluncin da yakeyi a nahiyar harma jama'arsu su sami damar gudanar da rayuwarsu a cikin daji a kwanciyar hankali.Abinda bata sani bashine ALLURA TA TONO GARMA,domin babu wani sauki talakawa zasu samu face karin matsawa,talauci da fatara wacce sai sun gwammace mutuwarsu akan rayuwars a doron kasa.Kuma ta tsokano tsuliyar dodon daya shafe shekara da shekaru a kwance yana faman shara barci kuma ta kulla gabar da ba a san ranar karshenta ba. ?????????? AL'AMARIN JARUMA SIYAMA KUWA,lokacin da ta samu ta fice daga cikin gidan sarautar sarki Ruguzan tayi ta gudu a cikin daji har ta isa inda ta bacewa dakarun birnin Kisra,ashe cikin wata korama ta shige tayi nutso izuwa karshenta ashe akwai wata barauniyar hanya a kasan koramar nan wacce ta bulle har izuwa cikin wani kogon dutse wanda yake a cikin wani daji daban dake nesa sosai.Koda tayi doguwar ninkaya a kasan koramar ta tabbatar da cewar ta iso cikin wannan kogo sai ta taso izuwa saman ruwan ta shaki numfashi kuma ta tsaya ta dan huta sannan ta cigaba da tafiya a cikin ruwan har saida ta iso karshen katon kogon dutsen ta cikin wani dan karamin rami wanda mutum bazai taba tsammanin cewar za'a iya ficewa ta cikinsa ba. Tana fita daga cikin kogon ta tsinci kanta a cikin wannan katon daji wanda tace jama'arta su jirata.Nan take ta kama waige waige da kalle kalle cikin tashin hankali tana zargin ko wani abu ya sami jama'arta ne?Nan take tayi wani irin fito na inkiyar da sukeyi a daji a duk sa'adda suka shiga daji farauta a yayin da suka hango dabbar da suke son kamawa.Bisa mamaki sai taji an amsa mata da irin fion nata sai ga wani babban hadimi na mahaifinta ya fito daga cikin wanu surkuki daya buya ya dubeta cikin murna ya yafito ta da hannu.Cikin farin ciki ta ruga izuwa wannan hadimi shima ya juya ya ruga izuwa wani bangare dabam na dajin.Saida sukayi tafiya mai tsawo tana biye dashi taga an shiga wani sakon daban wanda ma bata taba shigarsa ba sai taga dajin ya zamo sabo a wajenta.Kwatsam sai ta an shigo da ita wani sabon tafkeken kogon dutse wanda ya akai girman gari guda wanda bata taba sanin wanzuwarsa ba a cikin dajin.Shidai wannan kogon dutse a karkashin wadansu dogayen bishiyoyi yake masu manya manyan ganyaye wadanda suka lillubeshi babu yadda za ayi mutum yaga wannan kogon dutse face ya ture ganyayyaki da bishiyoyi.Suna shiga cikin kogon sai Siyama tayi arba da gaba dayan mutanen kabilarsu mazansu da matansu,yaransu da manyansu.Shugaba Sharwan ne kadai a tsaye,amma kowa a zaune yake a kas sun jeru sahu sahu kuma duk sunyi shiru tsit tamkar babu mai rai a cikinsu.Koda aka ga shigowar Siyama cikin kogon dutsen sai kowa ya kamu da tsananin farinciki.Nan take Sharwan ya ruga gareta suka rungume juna yana mai cewa ni san cewar sai kin dawo a raye gareni.Jikina ya bani cewar bazaki mutu ba yake 'yata abar alfaharina.Cikin tsananin farin ciki Siyama ta janye jikinta daga cikin na Sharwan ta dubeshi cikin mamaki tace,yakai Abba yaya akayi ka amince da duk abinda na umarceka da ayi a cikin wasikata.Kuma yaya akayi kuka gano wannan boyayyan kogo inda Dakarun Kisra bazasu taba ganowa ba?.Koda jin wadannan tambayoyi sai Shugaba Sharwan ya bushe da dariya sannan yace yake 'yata kiyi sani cewa ba wani abu bane yasa na bi duk umarnin da kika bani ba acikin wasikar taki ba face na yarda da kwakwalwarki gami da tunaninki da hankalinki baki taba shirya wani abu ba wanda aka kasa samun nasara ba.Dalilina na biyu wanda shine ne mafi muhimmanci shine bamu da wani zabi na samu tsira daga sharrin Sarki Ruguzan face mu yanke hukuncin kashe shi kuma muyi hijira ta zuwa wani dan lokaci kafin a sami sauyin Sarki mai adalci...Saidai Kash!Mun saki reshe mun kama ganye domin sarkin daya hau karagar mulkin Birnin Kisra a yanzu masifarsa da bala'insa sun ninka na Sarki Ruguzan sau goma.Samun azzalumin sarki kamarsa a duniya sai an tona.Nidai a sanina Sarki.Darwaz wanda ya kasance yaya ga Sarki Ruguzan ya tafi wata nahiya dabam ya tare a cikin daji yana farauta kuma yace bazai dawo gida ba sai bayan shekara ashirin,ashe ya dawo birnin Kisra babu shiri sakamakon wata rashin lafiya da dan'uwan sa Sarki Ruguzan yayi bara.Ina mai tabbatar miki da cewar a duniya babu abinda Sarki Darwaz yakeso sama da dan'uwansa Sarki Ruguzan don haka duk yadda zai yi yaga ya dauki fansar ran Ruguzan a kanmu sai yayi don haka nasan cewa da kansa zai jagoranci dakaru ya fito farautarmu.Dole ne yanzu muci gaba da tafiya dare da rana babu sassauci,kuma dole ne mu kiyaye shiga cikin biranen kasar nan face mun tura 'yan leken asirinmu sun gano halin da birnin yake ciki ta hanyar batar da kamanninsu izuwa matsayin 'yan gari.Ba zamu taba samun kwanciyar hankali ba face mun ga mun fita daga cikin wannan nahiya gaba daya.Yake 'yata inason ki sani cewar muna cikin tsananin TSAKA MAI WUYA dole ne muyi niyar yaki da dukkanin karfinmu da ranmu kodai mu tsira ko kuma a shafemu daga doron kasa gaba daya.Lokacin da shugaba Sharwan yazo daidai nan a jawabinsa sai hankalin Siyama ya dugunzuma ainun fite da ko yaushe.Nan take idanunta suka ciko da kwalla tace,yakai Abbana ka yafeni kai da dukkan sauran jama'armu hakika na jefamu a cikin masifa.Koda jin wannan batu sai Shugaba Sharwan yayi murmushi yace yake 'yata kiyi sani cewa baki da wani laifi a wajenmu domin kokin yi abinda kikayi ko bakiyi ba sai mun shiga cikin wannan tashin hankali da masifa tunda tuni Sarki Ruguzan ya jefamu a cikin wannan tafarki.Inason ki kwantar da hankalinki kuma ki tattauna da dukkan dakarunmu domin mu san hanyar da zamubi mu kare kanmu harmu sami nasarar fita daga cikin wannan nahiyar gaba daya.Yanzu ba baku rabin sa'a kacal ku gama dukkanin shirinku domin mu cigaba da tafiya.Koda jin wannan batu sai Siyama ta kirawo gaba dayan dakarun nasu suka taru a gabanta,a sannan ne taga su Muzaru ashe tuni sunzo sun riski su Shugaba Sharwan.Saida Siyama da dukkanin Dakarunta suka shafe rabin sa'a cif sannan suka kammala dukkanin shirye shiryensu,nan take akayi wata dabara aka lullube jikin kowa da koren ganya,hatta dawakai da dabbobi saida aka lullubesu da ganyaye yanda ko kada ba a ganin jikinsu sannan aka fito daga cikin kogon dutsen aka ci gaba da tafiya,mata suka goya yara kanan,su kuma tsofaffi da miskinai matasa suka goyasu a bayansu akayi ta tafiya cikin sauri sauri gudu gudu.A ko yauhse dakarun da suka kware a iya leken asiri suna kan gaba sai sunyi tafiya mai nisa sun tabbatar da cewar babu wani mugun abu a gabansu sannan suke dawowa su bayar da umarnin a cigaba da tafiya.A bayan tawagar kuma a ko yaushe wadansu dakarun leken asiri ne suna bazuwa gaba da yamma,kudu da arewa don tabbatar da cewar ba wanda ya biyo sawunsu.Haka dai aka ci gaba da wannan tafiya ba dare ba rana har tsawon kwana uku ba tare da an gamu da wani mugun Abu b?.&GUD?N TSIRA& Littafi Na uku (3) Part B &A-H Physicist& Ba tare da an gamu da mugun abu ba

Chapter 2 of 5