Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 5
kuma duk sa'adda aka gaji ko lokacin barci yayi sai a nemi wuri mai huduwar gaske mai hadarin gaske inda baza a taba zaton cewa wani abu mai rai ba zai iya shiga wajen ba,sai a shiga a kwakkwanta.A safiyar kwana na ukun ne suka hangi wani babban Birni wanda ake kira MADINATUL SULTAN a can gaban dajin da suke,tazarar dabata wuce ziri'a dari da sittin ba.Koda hango wannan birni na Madinatul Sultan sai kowa ya cika da farin ciki musamman Shugaba Sharwan.Nan take Sharwan ya dubi Siyama cikin murmushi yace,yake 'yata ki sani cewa mun iso birnin Madinatul Sultan inda zamu iya hutawa har tsawon kwana uku a cikin kwanciyar hankali kuma mu kara hada guzuri mai kyau mu ci gaba da tafiyarmu.Koda jin haka sai Siyama tayi ajiyar zuciya sannan tace,yakai Abbana kayi sani cewa nikam bani da kwanciyar hankali a duk inda zamu shiga,ina mai shawartarmu damu hakura da shiga cikin birnin Madinatul Sultan kawai mu kewaye ta bayan birnin mubi ta cikin daji mu ci gaba da tafiyarmu.Yayin da Sharwan yaji wannan batu sai ya girgiza kai yayi murmushi sannan yace,shin kin manta ne cewar shugaban da yake mulkin birnin madinatul Sultan abokina ne kuma aminina?Tun muna yara kanana muka saba a daji wajen farauta saboda shakuwar da mukayi dashi ne ma na bashi 'yar kabilarmu guda daya ya aura a sirrance ba tare da Sarkin Kisra ya sani ba.Akwai amana da alkawari mai girma a tsakaninmu dashi,ai na tabbatar da cewa baza a hada baki dashi ba a cutar damu ba,kuma ko me ake ciki ma ai yanzu mun baro dakarun kisra a can bayanmu,koda an aiko manzon sai mun rigashi isa birnin Madinatul Sultan bare batun dakaru masu yawa wadanda zasu dana tarkon cutar damu.Siyama ta numfasa tace na yarda da duk abinda ka fada ya Abbana.Bazan hanamu shiga cikin wannan birni ba,amma kafin mu shiga din inason ka fara aikawa da manzo a sirrance yaje ya gana da Sultan ya sanar dashi duk halin da muke ciki,idan har yace mu shigo cikin birnin nasa sai mu shiga tunda dai mun bashi amanar kanmu.Koda jin wannan batu sai Shugaba Sharwan yayi murmushi yace,tabbas nima na gamsu da wannan shawara.Nan take aka tashi wani kwararran dan leken asiri wanda ake kira da Jamar yayi shiga irin ta fataken birnin Kisra aka bashi dukiya da dakaru kimanin mutum arba'in bisa keken doki suka durfafi birnin Madinatul Sultan.Suma dakarun nasa gaba daya shigar irin dakarun Birnin Kisra sukayi.Lokacin dasu Jamar suka iso kofar birnin Madinatul Sultan basu fuskanci matsalar komai ba don ana ganinsu aka bude musu kofa ko cajesu ba ayi ba suka kunna kai cikin birnin,sukayi ta tafiya basu tsaya a ko ina ba har saida suka iso kofar fadar birnin.Suna zuwa aka yi musu iso suka shiga cikin fadar suke zube a gaban Sultan suka kwashi gaisuwa.Sultan ya dubesu cikin alamun mamaki yace yaku wadannan bakin fatake ku gabatar da kanku domin ban sanku ba daga cikin fataken dana saba yin mu'amala dasu ba daga Birnin Kisra ba.Koda jin wannan batu sai Jamar ya zura hannunsa a cikin aljihu ya dauko wata wasika ya bayar a mikawa Sarki Sultan.Koda Sarki Sultan ya warware wasikar ya karantata a gaban fadawansa sai ya kamu da tsananin farinciki ya mike tsaye da sauri ya rungume Jamar yana mai yi musu lale marhaban tamkar yaga 'yan uwansa na jini.Al'amarin daya daurewa 'yan majalisarsa kai kenan.Nan take Sarki Sultan yasa aka kai su Jamar masauki mai kyau aka kawo msu abinci da abin sha mai rai da lafiya.Kafin ma su fara cin abincin sai ga Sarki Sultan da kansa yazo har cikin turakar da suke,dakarunsa na take masa baya.Nan take ya sallami dakarun nasa yace duk su kama gabansu su bashi wuri yana son ya gana da bakinsa.Nan take kuwa dakarun suka fice daga cikin gidan suka barshi tare dasu Jamar.Suna gama fita Sultan yasa aka rufe kofar turakar da tagoginta don kada ma iska ta dauki sautin zancen da zasuyi takai izuwa kunnen dakarun nasa.A sannan ne Sarki Sultan ya dubi Jamar yace,Ya kai wakilin babban aminina,kayi sani cewa lallai rayuwar kabilar Banu Hanzar tana cikin tsananin hadarin gaske domin tuni wani aljani yazo da sako daga sabon sarki na Kisra cewar da zarar kun iso Birnina na sa a kamaku gaba dayanku a tsare a kurkuku har Sarkin yazo ya riskeku.Tuni na karbi wannan sako kuma na tabbatar da cewar zanbi umarni a zahiri,amma a badini nayi watsi da umarnin Sarki Darwaz domin irin amanar dake tsananina da Shugaba Sharwan bazata barni na bari a cutar daku ba.Tuni wannan aljani ya juya da nufin ya koma wajen Sarki Darwaz ya sanar dashi cewa ya isar da sakonsa a gareni,amma sai na tura wani babban hadimina wanda yafi aljanin karfin damtse dana sihiri ya bishi a baya ya tsafanceshi ya kulleshi a cikin wata kwalbar sihiri domin kada ya ganku akan hanya yaje ya tona muku asiri a riskeku a kawar daku.Yanzi ina son ku bari sai dare ya raba sannan kuje ku shigo da mutanenku izuwa cikin garin nan.Hatta masu gadin kofar birnin nan zansa a sauyasu a cikin daren nan na yau na zuba yardaddu a kan aikinsu.Idan ku ka shigo zan rana muku dukkan kayayyakin daya kamata domin ku saje da jama'ata domin ku sami damar tanadar da guzurin da kuke bukata ku kammala dukkan shirinku sannan ki ci gaba da tafiyarku harku cimma burinku na fita daga wannan nahiyar gaba daya. Ina mai tabbatar muku da cewar sai kun bar birnina da kamar kwana bakwai sannan su Sarki Darwaz zasu iso kuma duk irin binciken dasuyi bazasu taba gano cewar na baku mafaka a birnina.Lokacin da Sultan yazo nan a zancensa Sai farinciki ya lullube su Jamar suka zube kasa suna yi masa godiya.Kamar yadda Sarki Sultan ya shirya kuwa haka al'amarin suka kasance wato saida dare ya raba san nan aka sauya nasu gadin birnin na Madinatul Sultan sannan akaje aka shigo da kabilar Banu Hanzar gaba dayansu izuwa cikin birnin a sirrance ba tare da kowa ya sani ba bayan an yi musu shiga irinta mutanen birnin.Siyama da mahaifiyarta da shugaba Sharwan kuwa har cikin ainihin turakar Sultan aka kaisu suna yin arba da juna sai Sultan ya ruga ga Sharwan suka rungume juna suna masu fashewa da kukan farin cikin sake saduwa domin rabonsu da ganin juna a kalla yakai shekara goma sha biyar.Sultan ya janye jikinsa daga cikin na Sharwan a lokacin daya Hango Siyama da mahaifarta ya dubi Siyama cikin tsananin mamaki sannan ya dubi Sharwan yace,yanzu wannan Siyama ce ta girma haka?Sharwan ya gyada kai cikin murmushi yace,kwarai kuwa wanna Siyama ce rabonka da ita tun tana da shekara uku kacal a duniya,wata rana sa'adda ka kawo mana ziyara a lokacin da ka fito farautarka ta karshe harka daura mata wata laya a wuyanta kace mu adanata a jikinta har abada.Yanzu haka layar na jikinta tun wancan lokacin tana bata tsananin kulawa yadda ya kamata.Koda gama fadin hakan sai Sharwan ya taka yaje inda Siyama take ya zura hannunsa cikin wuyan Rigarta ya janyo wata siririyar laya dake zagaye a wuyanta wacce akayita da hakorin zaki guda daya.koda Sultan yayi arba da wannan laya sai ya kamu da tsananin farinciki sannan ya dubi Siyama yace yake 'yata kiyi sani cewa asalin wannan laya ta kakana ce wanda ya haifi ubana nima gadonta nayi kuma ubana ya tabbatar mini da cewar duk wanda ya girma tare da layar a jikinsa babu makiyinsa dazai taba samun nasara akansa.Kuma duk irin tsananin rintsin da mutum zai shiga sai dai kawai yasha wuya.Har yau har gobe ban haihu ba kuma bisa binciken danayi a tsafi da wanda matsafa sukayi mini bazan taba haihuwa ba a takaice dai har na mutu bazan sami magaji ba.Mahaifinki yayimini abinda har na mutu bazan iya saka masa da komai koda kuwa zan bada raina a matsayin fansa ga nasa,bisa wannan dalili ne na sallama wannan laya tawa a gareki tunda kina yarinya karama,tunda shima bashi da wani 'da a duniya saike kadai.Rayuwarki taci gabanki har izuwa lokacin da zaki gajeshi shine kadai babban burinsa a doron kasa.Ina son mahaifinki yaga wannan rana da idanunsa kafin ajali ya riskeshi.Koda Sultan yazo nan a zancensa sai na take Siyama taji ta kamu da tsananin kaunarsa don haka bata san sa'adda ta ruga gareshi ba ta runguemshi tana mai fashewa da kukan farin ciki domin ta tabbatar da cewa basu da wani masoyi a doron kasa wanda yafi Sultan.Bayan hake ne Sultan ya kirawo Matarsa wacce ta kasance 'yar uwar Ilela mahaifiyar Siyama uwa daya uba daya wacce ake kira da suna SHAMIRAT.Koda Shamira ta shiga cikin turakar tayi arba da yar uwarta Ilela sai ta cika da tsananin mamaki gami da farinciki.Lokac i guda suka ruga suka rungume juna suna masu fashewa da kukan murna suna kankame jikinsu tamkar kara aka tsaga,kuma a danginsu su kadai ne suka rage.Bisa dole aure ya rabasu suna kuka kuma tin daga ranar da Sultan ya auri Shamirat ya dawo da ita birnin Madinatul Sultan ita da Ilela basu sake ganin juna ba,kuma basu taba zaton zasu sake saduwa ba,domin a ka'idar dokar Birnin Kisra duk mutumin da aka bashi mukamin shugabanci na wani Birni to shida Iyalansa shiga cikin Birnin Kisra da dukkan dazuzzukan da suke kewayenta sun haramta gareshi.Saida Ilela da Shamirat suka dade a kankame da juna suna kukan murna sannan Shamirat ta farga da Siyama ta hangota a tsaye a can gabansu.Da yake Siyama tana kama da mahaifiyarta,Shamirat na ganinta ta gane cewa 'yar suce,don haka sai ta cire jikinta daga cikin na Ilela ta bude hannayenta a lokacin da hawaye ya zubo mata tana kallon Siyama tace,taho gareni yake 'yata naji dumin jikinki kafin mu sake rabuwar karshe.Nice kadai 'yar iwar mahaifiyarki wacce tayi saura a doron kasa.Koda jin wannan batu sai Zuciyar Siyama ta karaya,nan take itama idanunta suka ciko da kwalla ta fara zubar da hawaye bata san sa'adda ta ruga izuwa ga Shamirat ba suka rungume juna suka suna kuka.A'amarin daya baiwa su Sharwan matukar tausayi kenan suma suka ci gaba da kukan.Kamar yadda Sultan ya tsara haka duk al'amarin ya kasance wato saida Kabilar su Siyama suka kwana biyu a cikin Birnin Madinatul Sultan ba tare da wani dan garin ya fahimci hakan ba,sannan Sultan yasa aka shirya musu guzuri mai yawan gaske,kuma aka nuna musu hanya mafi sirri wacce zasu fice daga cikin nahiyar gaba daya.Lokacin da Sharwan yazo suyi bankwana da Sarki Sultan sai duk su biyun suka kasa cewa komai suka fashe da kuka suka rungume juna.Tsawon 'yan dakiku suna kankame sannan Sultan ya janye jikinsa daga cikin na Sharwan ya dubeshi a lokacin da hawaye ya zubo masa yace,yakai abokina kayi sani cewa wannan rabuwa da zamuyi yanzu ina ganin cewa itace rabuwarmu ta karshe wadda har abada baza mu sake saduwa ba tunda zaku bar wannan nahiyar tamu ne gaba daya,bansan ranar da zaku sake dawowa ba.Wata kila kafin ku sake dawowa bana raye,wannan hawaye nawa da kaga ya zubo bisa dalili biyu ne.Dalili na farko shine na SO da KAUNAr dake tsakanina dakai.Dalili na biyu kuma hawaye ne na takaici bisa zamu rabu alhalin har yanzu ban sami damar dazan iya saka maka bisa abinda kayi mini a baya ba.Koda Sharwan yaji wannan batu sai nan take shima hawaye ya zubo masa yace,yakai Abokina kayi sani cewa bana fatan naga ranar dazaka saka mini bisa abinda nayi maka a baya.Kuma ko a yanzu ka gama saka mini tunda harka bamu mafaka a cikin birninka a irin wannan lokaci wanda babu wani shugaban birnin dake karkashin masarautar Kisra yayi kundunbalar dakayi domin ka siyar da rayuwarka ne Domin tamu. G?D?? TS?RA& Littafi N? uku ( 3 ) Part C &A-Haleefah Physicist& Domin ka siyar rayuwar ka ne domin tamu.Koda jin wannan batu sai Sultan yayi murmushi yace ai taku rayuwar itace mafi amfani akan tawa domin kune kadai zaku iya kawo sauyin rayuwa a wannan Nahiya gaba daya,ku kawar da zalunci ku shimfida adalci.Abokina idan har hakan zata tabbata raina fansa ne akan naku.Inason ka saurara da kyau kaji shawarar dazan baku yanzu wacce idan karkuyi amfani da ita sai mafarkinku ya tabbata gaskiya a wannan Nahiya.Abinda nake nufi shine sai sauyi yazi mana an kawar sa zalunci irin nasu Sarki Darwaz.A duk sa'adda kuka hadu da wadansu mutane wadanda suka zo muku da wani sabon addini to ku yarda dasu kuma ku karbi addinin nasu.Sa'adda Sharwan yaji wannan batu shida Siyama da Ilela sai suka cika da tsananin mamaki.Sharwan ya dubi Sarki Sultan yace,yakai abokina yanzu kana nufin kenan akwai wani addini wanda shine na gaskiya wanda yafi duk Allolin da ake bautawa a wannan Nahiya,kuma yafi tsafi da dukkan Aljanun da akayi imani dasu?Sarki Sultan ya gyada kai yace kwarai kuwa kuma saduwa da ma'abota wannan addini shine burina na karshe.Tuni na dade da samun labarin wannan addini a wajen iyayena kuma suma tun suna yara suka sami labarinsa a wajen nasu iyayen.Da zarar na sadu da wadannan mutane zan ajiye tsafi na rungumesu.Lokacin da Sultan yazo nan a zancensa sai Sharwan ya kawo gwauron numfashi ya ajiye sannan ya dubi Sultan yace,yakai abokina yanzu yaza ayi na shaida wadannan mutane a duk sa'adda na sadu dasu?Sultan yayi gyaran murya sannan yace zaka iya shaida wadanan mutane ta hanyoyi guda biyu,hanya ta farko itace yanayin shigarsu.Ko yaushe zaka gansu a cikin sutura ta kamala mazansu da matansu,basu barin tsiraicinsu ya bayyana ba.Abu na biyu kuma shine sun kasance mutane masu gaskiya,amana gami da rikon alkawari.Basu dauki duniya a bakin komai ba.Babu abinda suke gudu sama da dukiya da mulki.Koda jin wannan batu Sai Sharwan ya girgiza kai yace,ni kuwa zan sa ido sosai duk ranar dana sadu da wadannan mutane zan karbi addininsu hanni bibbiyu domin kana fadin halayensu yanzu naji na kamu da tsananin kaunarsu bisa kyakkyawar mu'amalarsu,wanda duk wani mahaluki daya dauki irinta zai gudanar da rayuwarsa cikin kwanciyar hankali dajin dadi na har abada.Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube Sultan ya rungume Sharwan yana mai masa godiya sannan ya sake janye jikinsa daga cikin nasa suka fuskanci juna ya ce,yakai abokina kayi sani cewa tafiyar dake gabanku da kuma hadarin dake cikinta ba kadan bane domin kafin ku sami damar fita daga cikin Nahiyar nan sai kunyi tafiya ta a kalla wata bakwai da rabi,kuma akwai manyan kasashe guda uku a gabanku.Wannan birni nawa na Madinatul Sultan yayi iyaka da wata babbar lasa da ake kira DARUL HUNAN.Kafin ku isa iyakar sai kunyi tafiya ta kwana arba'in da daya.Indai kuka ketare wannan iyaka lafiya ba tare dasu Sarki Darwaz sun riskeku ba kun tsallake dukkan hadari.Ina ji a jikina cewa abune mayuwaci ku isa har can su Sarki Darwaz basu cimmuku ba domin nasan cewa sai sunyi amfani da kowacce hanya don ganin sun riskeku saboda da zaarar sun iso nan Birnina sunga bakwa nan zasu tabbatar da cewa kun wuce gaba.Tunda bani da tabbacin zan tsira da rayuwata,ina son ku tafi da matata Shamirat tunda kune kadai kuka rage mata a doron Kasa.Idan kuka barta anan tare dani Sarki Darwaz zai iya kashemu tare.Koda jin wannan batu sai Shamirat dasu Ilela suka fashe da kuka,shi kansa Sharwan bai san sa'adda ya kama kukan ba.Sultan ya dubi Siyama yace,yake 'yata kiyi sani cewa sai kin gaji da wannnan GUDUN TSIRA da kukeyi kinji kamar ki tsaya a kasheki ki huta,amma inason ki kasance mai juriya bisa duk irin tsananin da zaki fuskanta,kisa a ranki cewar dukkan tsanani yana tare da sauki.Idan gaba dayan Kabilar Banu Hanzar zasu kare ya zamana cewa ke kadai kada ki sare kuma kada ki cire babban burin dake ranki nason dawowa wanna kasa tamu domin kawar da zalunci.Koda gama fadin hakan sai Sultan yayiwa Sharwan bankwana na karshe inda matarsa Shamirat ta rungumeshi suka fashe da matsanancin kuka na bakin cikin rabuwa.Da kyar yar uwarta Ilela ta janyeta daga cikinsa,ai kuwa sai Sharwan ma ya sake rungumeshi ya fashe da kuka yana mai cewa Abokina bazan yarda na tafi na barka basaidai na zauna azo a kashemu gaba daya tare ko kuma mu tafi tare mu mutu a cikin wannan GUDUN TSIRA da mukeyi.Sa'adda Sultan yaji wannan batu na abokinsa Sharwan sai yakamu da tsananin tausayinsa ya dubeshi yace,na sani cewa babu ranar bakin ciki sama da ranar rabuwa da masoyi,to amma babu yadda zamuyi da kaddara,haka tamu kaddarar tazo,babu abinda zamuyi face mu kasance masu tunawa da junanmu tare da yiwa junanmu fatan alkhairi har sa'adda mutuwarmu zata riske mu,zanji dadi mutukar ka rike wannan a ranka.Haka dai Su Sharwan suka yiwa Sultan Sallama suka tafi matarsa Shamirat tana waigensa tana faman rusa kuma ana janye da ita.A lokacin Sharwan da Siyama ma suka yi ta waigen Sultan Suna zubar da hawaye zuciyarsu na kuna kamar zasu fasa yin tafiyar.A cikin daren ne su Sharwan suka sake sulalewa daga cikin Birnin Madinatul Sultan suka fice suka sake nausa cikin daji suna tafiya cikin sauri sauri gudu gudu kamar yadda suka saba ba dare ba rana har tsawon kwana bakwai.Duk sa'adda suka hadu da gungun yanfashi ko wadansu mugayen dabbobin daji sai kaga sun tarwatsasu farat daya sunci gaba da tafiyarsu. ????????? A DAREN KWANA NA BAKWANI NE DA tafiyarsu Sharwan,Sarki Darwaz ya iso cikin Birnin Madinatul Sultan tare da rundunarsa ta yaki,'yarsa Husaira na daf dashi bisa kan doki sun jera.Suna isowa kofar Birnin saiga Boka Hurgas ya baiyana tsulum a gaban Sarki Darwaz yana mai kyakyacewa da dariya.Cikin fishi Sarki Darwaz ya dubeshi yace da kana ina muka shafe wannan doguwar tafiyar baka bayyana ba sai yanzu alhalin kace kaine zaka yi mana jagora a cikin tafiyar?Yayin da Boka Hurgas yaji wannan tambaya sai yayi murmushi yace ya shugabana ai tunda aka fara wannan tafiya ina biye daku kuma ina muku jagora saidai na baku tazara mai yawa,domin na iso nan Birnin tun a kwanaki shida da suka wuce.Tabbas zuwana da wuri yayi amfani domin na samo mana wani labari mai muhimmanci dangane da abinda muke zargi.Ko shakka babu shugaba Sultan yayi wadansu baki daga birnin Kisra a matsayin yan kasuwa,wato fatake,amma a cikin kwanaki biyu aka nemesu aka rasa acikin birnin nan.Bisa bincikena danayi na tura wadansu zakwakuran hadimaina na aljanu sun bi bayan wadannan fatake basu gansu ba kuma basu ji duriyarsu ba.Ya shugaba kasani cewa Sultan gawurtaccen matsafi ne don sihirin tsafinsa yafi nawa karfi,Ni abinda nake zargi shine wadannan fatake da akace sunzo fatauci kabilar banu Hanzar ne,kuma Sultan ne ya basu mafaka suka sauka har tsawon kwana biyu sannna suka sulale suka bar birnin nasa.Idan har Sultan yana son ya kubuta daga wannan laifi toya gaggauta fada mana inda wadannan fatake suke ko kuma ya gaya mana garin da suka nufa tafi muje mu gansu da idanunmu.Abu na biyu shine a bisa binciken danayi kafin mu baro Birnin Kisra na gano cewa akwai wata tsohuwar alaka ta zumunci mai karfi tsakanin Sultan da shugaban Kabilar banu Hanzar tun suna yara kanana,sa'adda suke haduwa a daji wajen farauta Kaga kenan akwai yiyuwar shugaba Sultan zai iya taimakon Kabilar Banu Hanzar ta kowacce Siga.Koda Boka Hurgas yazo nan a zancensa Sai Sarki Darwaz ya fusata ainun har jikinsa ya kama tsuma,zuciyarsa kuma ta kama tafarfasa,kawai sai ya yunkura zai sakarwa dokinsa limzani ya zabureshi da gudu izuwa Birnin Madinatul Sultan,amma sai Boka Hurgas ya daga masa hannu yana mai tsayar dashi.Kawai sai Boka Hurgas ya tsugunna ya debo kasar kofar Birnin ya shinshinata kawai yayi murmushi ya dubi Sarki Darwaz yace,ba shakka babu mutanen kabilar Banu Hanzar sun shiga cikin wannan birnin gaba dayansu don haka duk inda ma suke shugaba Sultan ya sani domin naji kamshin sawayensu a kan wannan kasa.Kafin Hurgas ya gama rufe bakinsa tuni Husaira ta zare takobinta ta sakarwa dokinta limzami ta banke masu gadin kofar birnin da karfin tsiya ta kunna kao cikin birnin a fusace.Ai kuwa sai Sarki Darwaz da sauran Dakaru suka rufa mata baya suka bar Boka Hurgas a tsaye anan yana ta kyalkyala dariyar mugunta da farinciki.Kai tsaye Gimbiya Husaira suka durfafi gidan sarautar Sarki Sultan.Bisa mamaki suna isa gidan sarautar sai suka iskeshi a bude wanwar ko masu gadi babu.A cikin gidan sarautar kuwa gaba dayan dakarun suna zazzaune sun ajiye makamansu a kas,kuma basa shirin tararsu.Koda suka iso tsakiyar gidan sarautar inda wani badakare yake sai suka iske wani mutum guda daya jal a cikin gagarumar shigar yaki.Koda suka matso daf dashi sai sukaga ashe ba wani bane face Shugaba SultanKoda suka zo dab dashi sai suka ja Linzamin dawakansu suka yi tirjiya kuma suka yi masa KAWANYA.Cikin tsananin fushi Sarki Darwaz ya dakawa Sultan tsawa yace,yakai Sultan kayi sani cewa kaci amanarmu ka hada kai da makiyanmu da basu mafaka,idan kana son ka tsira da rayuwarka data iyalanka to ka hanzarta sanar damu inda kabilar Banu Hanzar Suke.Koda jin wannan tambaya sai Sultan ya bushe da dariya,Al'amarin dayayi mutukar baiwa su Sarki Darwaz mamaki kenan.Daga can sai Sultan yayi shiru ga barin dariyar ya murtuke fuskarsa ya dubi Sarki Darwaz yace,ko me zai faru bazan sanar daku inda Kabilar Banu Hanzar suke ba kuma matata tana tare dasu.Yakai wannan azzalumin shugaba nawa kayi sani cewa ni bani da sauran buri a rayuwata face guda daya jal,wanda ko ban cika shi ba wadda ta kashe Dan'uwanka Sarki Ruguzan sai ta cika mini shi,wato Siyama 'yar aminina shugaba Sharwan.Na sani cewa zan mutu a hannunku amma ku sani kafin a kashe Gwaggon Biri sai yayi muguwar barna.Sultan na gama fadin hakan sai ya zare takobinsa ya daka tsalle sama kamar tsuntsu ya hau dakarun Birnin Kisra da SARA DA SUKA a saman yana fille musu kawuna tamkar ya kasance mai fuka fukai,yana shawagi a kansu saboda karfin sihirinsa.Koda Sarki Darwaz da Husaira suka ga irin mummunar barnar da Sultan yake yi musu sai suma suka zare takubbansu suka daka tsalle sama suka tare shi aka ruguntsume da sabon azababben yaki mai tsananin ban tsoro da ban al'ajabi. WAYE ZAI SAMU NASARA A WANNNAN GAGARUMIN GUMURZU TSAKANIN SU SARKI DARWAZ DA SARKI SULTAN? SHIN SARKI SULTAN YANA FADUWA KASA KUWA? A WANE HALI KABILAR BANU HANZAR SUKE CIKI? SHIN ZASU SAMI NASARAR FITA DAGA NAHIYAR NAN HAR SU HADU DA MA'ABOTA ADDININ MUSULUNCI SU MUSULUNTA? SIYAMA NA CIKA BURINTA NA DAWOWA NAHIYAR TA KAWAR DA MULKIN ZALUNCI? YAUSHE ZA'A YI GABA DA GABA TSAKANIN SIYAMA DA GIMBIYA HUSAIRA 'YAR SARKI DARWAZ,INDAN SUN HADU ME ZAI AFKU A HADUWAR TASU? WANE IRIN BURI BOKA HUGAS YAKE DASHI A RAYUWARSA? Mu hadu a GUDUN TSIRA kashi na hudu don jin ci gaban wannan kasaitaccen labari Amsa: Su Sarki Darwaz ne suke samun Nasara. Eh Sarki Sultan yana faduwa kasa. kwarai kuwa suna samun damar fita bayan sun sha wahala har su hadu da ma'abota addinin musulunci. Eh Siyama tana cika burinta,amma ba'azo gunba. Idan Siyama da Husaira sun hadu ana tafka azababben yaki mai tsoratarwa. Burin Boka Hurgas ya mallaki Birnin Kisra da Nahiyar tasu. GUDUN TSIRA Littafi na Uku Na Abdulaziz Sani m gini Ebook creator:- Shuraih 99% For more adventure hausa ebooks visits our wepsite www.shuraih.waphall.com Domin samun wasu littatafan yaki a matsayin ebooks sai ku ziYarci shafinmu akan www.shuraih.waphall.com ??GUDUN TSIRA Littafi na hudu Na Abdulaziz Sani m gini Ebook creator:- Shuraih 99% For more adventure hausa ebooks visits our wepsite www.shuraih.waphall.com Domin samun wasu littatafan yaki a matsayin ebooks sai ku ziYarci shafinmu akan www.shuraih.waphall.com GUDUN TSIRA Littafi na Hudu(4) Part A Lokacin da aka rungumtsume da masiffafen yaki tsakanin shugaba Sultan dasu Sarki Darwas sai ragowar dakarun nasu sarki Darwaz suka zama yan kallo,suka koma kwashe gawarwakin yan'uwansu suna koma gefe daya.Dama wadannan dakaru sun firgita ainun da al'amarin shugaba Sultan saboda a cikin abinda bai wuce dakika dari biyu ba ya kashe sama da dakaru dari takwas da karfin sihirin tsafi gami da karfin damtse da kwarewa a iya yaki.Koda aka fara wannan baki artabu sai Gimbiya Husaira da sarki Darwaz suka gane cewa lallai Sultan ba karamin jan gwarzo bane,tunda gashi sunyi masa rubdugu su biyun,amma tsawon dakika dari dayansu ya kasa koda lakutar jikinsa.Babban abinda ya bata musu rai mashi ne a hakan ma dada zullewa yake yana ci gaba da saran dakarunsu yana mai ci gaba da yin mummunar barna.Koda ganin haka sai Sarki Darwaz da Huraisa suka kara fusata ainun suka kara kuntata shi.Lokaci guda sai Sarki Darwaz da Huraisa suka dubi junansu a sannan suka yi wata alama,kawai sai suka doki kirjin Sultan da kafafunsu lokaci guda.Saboda karfin dukan sai da Sultan ya fado kasa tim yana aman jini,amma saboda tsananin naci da tsananin juriya bai yarda takubban hannunsa ba.Cikin zafin nama ya mike tsaye zumbur a daidai lokacin da Sarki Darwaz da Huraisa suka duro kasa gabansa aka ci gaba da gumurzu.Wohoho,wanda ya iya ya huta.Hakika su Sarki Darwaz sun sha matukar mamaki,domin basu taba zaton cewa Sultan yana da jarumtaka da karfin sihiri a haka ba.Ba wai tsagwaron karfin damtse ne da Sultan ba,amma ya sami tsananin horo na iya yaki gami da tsananin zafin nama,tabbas ya cika tshoho mai dakawa yara gumba.Saida aka shafe sa'a guda da rabi cif ana fafata kazamin yaki tsakanin Sultan dasu Sarki Darwaz amma ya zame musu alakakai,kuma saida ya samin nasarar fitar da jini a jikin kowannansu,duk da cewar suma sun yanke shi,domin a kalla sunyi masa manyan raunika guda tara.Sakamakon jinin dake zuba a jikinsa ne jiri ya fara dibarsa ya fara gigta.Damar dasu Sarki Darwaz suka samu kenan suka ci gaba da kai masa sara da suka gami da naushi da bugu da dukkan karfinsu.Nan da nan suka sami lagonsa ya zamana cewa tun yana tsaye saida ya durkushe kasa bisa gwiwoyinsa.Babban abinda ya fusata Sarki Darwaz shine Sultan yayi masa wani siririn yanka a kumatu,yayi masa billen dole,wanda har abada tabonsa bazai bata ba.Ita kuwa Huraisa a kan cinyarta ta hagu ya yanketa kuma wurin yayi dan zurfi dole ne tayi jinya ta kamar tsawon kwana uku,tsananin juriya ne da jarumtaka tasa taki sarewa.Sultan na tsugune a kasa sai Sarki Darwaz da Huraisa suka ci gaba da saran jikinsa suna sukar cikinsa da takobi yana ihu,jini na tsartuwa da fallatsi a jikinsa har saida sukayi fata- fata da sassan jikinsa.komai rashin imanin mutum idan yaga yadda aka daddatsa sultan sai tausayi ya kamashi,amma duk wannan abu da akayi masa bai mutu ba saboda taurin rai.Ana cikin haka ne Kan Sultan ya lankwabe kasa ya daina motsi,Sarki Darwaz da Gimbiya Huraisa suka dubi Junansu sukayi murmushin murna bisa ganin sun sami nasarar kashe shi.Kwatsam ba zato ba tsammani sai suka ga Sarki Sultan ya dago kansa sama ya dubi Sarki Darwaz yayi masa murmushin mugunta sannan yace,ko ba komai harka mutu billen danayi maka bazai face ba daga kan fuskarka dashi a za'a binne ka a cikin kabarin ka.Kafin Sultan ya gama rufe bakinsa tuni Sarki Darwaz yasa takobinsa ya fille masa kai.Take Kan yayi tsalle can gefe daya ya rinka mirginawa da gudu har saida bango ya tokare shi,sannan gangar jikin nasa ma ta bingire kasa.Cikin tsananin fushi Sarki Darwaz yaje inda kan Sultan yake ya sunkuya ya dauka sannan ya mikawa wani hadimi nasa yace,inason a tsire wannan kai a daidai kofar shiga fadata ya zamana cewa,kullum sai nayi arba dashi idan zan shiga,kuma ya zamo abu na farko wanda baki zasu fara tozali dashi a duk sa'adda suka zo.Hadimin ya risina yace an gama ya shugabana.Kawai sai hadimin ya jefa kan Sultan a cikin wata jakar fata ya kunshe.Adaidai wanann lokaci ne Gimbiya Huraisa ta fara dingisa kafarta ta hagu wacce ke zubar da jini,kawai kuma sai ta kasa daukar nauyin jikinta ta fadi kasa,cikin dimauta Sarki Darwaz ya ruga izuwa kanta ya dauke ta ya ruga izuwa cikin gidan Sarautar Sultan yana mai bada umarnin a je a nemo babban likitan shugaba Sultan.Bayan likitan ya gama sawa Gimbiya Huraisa magani kuma an dinke raunin saboda yayi zurfi;sa'a mata yi kaifin takobin Sultan bai taba kashin cinyarta ba.Nan take Huraisa ta kama barci akan gadon shugaba Sultan dake tsakiyar turakarsa,sakamakon maganin barcin da likitan ya bata ta sha.A wannan lokaci ne likitan ya mike tsaye daga kan gefen gadon ya dubi sarki Darwaz cikin alamun damuwa yace,Akwai bukatar

Chapter 3 of 5