Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 4
sabon fada ya zamana cewa suna kaiwa junansu naushi da bugu da hannu da kafa.... Page 7. Zidane kd.. Kaico idan jarumtaka ta hadu da sadaukantaka dole ne yan kalllo suga abubuwan al ajabi tamkar almara. Sai da wadannan jaruman hudu suka sake shafe kimanin daKiku dubu biyar da yaya suna yin wannan dauki ba dadi batare d dayansu yasami nasarar cutar da abokin gwaminsa ba. Al amarin daya fusata su kenan duk su hudun suka kara kaimi cikin fusata gami da sauya salon fada iri iri. Hakan ya sa suka fara samun damar cutar da juna.. Nan danna suka fara hadawa da junan jini da majina. Babban abin mamaki shi ne da zarar dayansu ya sami nasarar naushin daya kafin yasake kaiwani hannun sai kaga wanda aka nausa din ya rama.. Haka suka cigaba da gabzar juna cikin juriya da zafin nama tamkar jikinsu na karfe ne ba na jini da tsoka bane. Page 8. Zidane kd. A wannan lokacin ne hankalin gaba dayan yan kallo ya dugunzu,a domin babu tabbaccen bangare dazai samu nasara a wannan gasa sbd dukkaninsu sun fara jigata ainun ga jini na yoyo a bakunansu da hancinsu kuma fuskokinsu sun kumbura jikinsu yayi tsami amma sbda naci kowannensu yaki yarda ya fadi kasa.. Har sai data kai cewa basa iya kai wajunan bugu da naushi sai suka kaure da kokawa kowa na kokarin kayar da abkn gwaminsa. A dai dai wannan lokacine hankalin yan kallo yasake dugunzuma fiye da ko yaushe har ta kai cewa mutane na mikewa tsaye daga mazaunansu suna kasa zama sbda kaguwa firgici da damuwa akan ganin gwanayensu ne suka sami nasara. Page 9. BIRNIN AZZALUMAI 6. LIttafe na shida. Na abdul aziz. Part B. Type. Suleiman zidane kd. Whatsapp. 09064179602: Akan ganin gwanayensu ne suka sami nasara. Abin da zai bai wa mutum mamaki shine da yawa daga cikin mutanen garinma suna son suga Husam da Lasmir Son su ga Husam da lasmir son sami nasara ba don komai ba sai sbda jarumtakarsu tayi matukar burge su. A birnin gaba daya babu jaruman da suka kai sarki zarmus da yarsa Gimbiya Zarisha kuma duk shekara idan aka yi wannan gasa sune suke lashewa duk dace wa bakin jarumai suna zuwa daga kasashe makota. Yau sai gashi an sami zakakuran jaruman da suke neman karya musu alkadarin da tarihin da suka kafa tsawon shekaru shida. Ana cikin wannan haline na rashin tabbas ko kwanto da fargaba a cikin gasar sai kawai aka ga dukkaninsu jaruman hudu sun yi wata irin rukunkumar junan ta bazato da shammace tare kuma a lokaci guda suka fadi da baya ya zamana cewa duk su hudun bayansu ya taba kasa. Page 10. Zidane kd. Nan fa yan kallo gaba daya suka dafe kai cikin tsananin mamaki sanan suka rufe da shewa gami da jinjina. Ai kuwa sai alkalin gasa ya rugu da gudu ya shigo tsakiyar filin ya tsaya ya fuskanci jama a ai kuwa sai aka yi tsit tamkar mutuwa ta gifta. A sannan ne zarisha ta taimakawa Husam suka mike da kyar kamar yadda su zarisha sukayi alkalin gasa yayi gyaran murya yace ya ku mutanen wannan birnin mai albarka ku yi sani cewa sakamakon wannan gasa shine ragas. Jama a su rufe da shewa gami tafi da jinjina alkalin wasa zai daga hannunsa sama asake yin tsit sannan yace sakamakon wannan ragas da akayi tafiyar da su sarki zasuyi izuwa birnin azzalumai babu wanda zai shugabanci su face wannan bakon jarumi mai suna zaunal wanda yazo tare da su Husam. Page 11: zidane kd. Dajin haka sai jamaa suka sake rudewa da shewa shi kuwa jarumi zaunal sai abin yayi matukar bashi mamaki domin bai ga dalilin da zai sa a bashi shugabanci tafiyar ba tun da babu shi a cikin gasar da akayi. Bayan filin gasar yawatse kowa ya kama gabansa sai sarki zarmus da Husam suka kadaita a cikin turkarsa inda ya tura aka kirawo lkitoacinsa guda biyu suka shiga duba su gami da yi musu magani bisa raununka da suka ji a wannan gasa. Page 12. Zidane kd. Kowannensu ya cire rigarsa ya zamana babu komai a jikinsa face gajaren wando domin tabbatar da cewa an duna ko ina a jikinsa. Ana cikin duba ne Husam ya lura dacewa sarki ZARMUS na cikin damuwa don haka sai yadubeshin akwai wani abu ne wanda yabata maka rai a yau?. Sarki zarmus ya gyara kai yace babu abin dayataba mini rai amma a cikin firgici da razani bisa gagarumin aikin dake gabanmu sbda shirin da makiyanmu suka yi akan mu yawuce duukkanin zatonka da tunaninka. Ko dajin wanna batu sai Husam ya mike zaune daga kwance ya dakatae da likitan dake shafa masa wani magani akan fuskarsa don bajewar kumburi ya dubi sar zarmus cikin alamun mamaki yace wane irin shari sarki baskae da boka zarmus suka yi akamu? Page13 Sarki marzuk ya numfasYace yau saerki wata uku kenan suna baiwa kansu sababbin horo na yaki kuma sun tanadi sabbin kayan yaki wadanda ba a taba amfani da su a wannan nahiyar ba. Sun dauko sojojin haya kwararru na musamman daga wasu kasashe dake can gaban nahiyarmu . Bayan ga haka sun tanadi dukkanin sirrinkan su na tsafi gami da gudumawar mayan bokayen daga wadansu nahiyoyin . Tabbas wannan shiri nasu akwai ban tsoro a cikinsa wanda idan har kaga mun sami nasara a kansu sai tsananin sa a da robo. Lokacin da sarki marzuk yazo nan a jawabinsa sai Husam yayi doguwar ajiyar zuciya yace yakai wannan sarki msi irin burina kayi sani cewa raina da dukkan dukuyarya ba a bakin komai muddin zan dauki fansa akan makiyana baskar na raba shi da matata jaruma zamirat. Babban burina shine na sake ganinta ko da sau daya ne kafin mutuwata . Page 14. Burina na biyu shine na ciro tadaga cikin kurkukun da baskar ya ajiye ta tsawon ya yanke mana farin cikinmu da soyayyarmu. Koda Husam yazo nan a zancesa sai sarki marzuk ya kamu da tsananin tausayinsa har shi ma kwalla ta cika masa idanu marzuk ya mikezaune kamar yadda husam yayi kuma ya dafa kafadarsa yace yakai abokina kayi sani cewa duk duniya babu mutumin da nakeso wacce muka kasance uwa daya uba daya. Page 15. Ita ce kadai nake kalla ta dauke min kewar iyayyena da na rasa. A duk sa adda na kalle ta na ji tamkar bani da wata bukata ko guda daya a cikin duniyar nan. Ita ce wadda komai mutum yake nema a waje na da zarar tasa baki take zan bashi ita ce kadai mai bani umarni na bi kuma bata taba zuwa gareni da bukata na ki ba. A tsawon shekaru goma sha da boka zarmus ya rabani da ita ban tabayin barci sa a uku ba koami tsawon dare sbda begen ta da tunaninta kuma hakan ne ya haddasa mini ciwo zuciya kuma ba zan taba warkewa ba face naga na rabata da bola zarmus kuma na kashe shi da hannuna. Tun lasmir tana yarinya kara yar shekara bakwai bola zarmu ya kamu da tsananin sonta a sannan bai fi shekara sha biyar ba a duniya amma ya ce bawa ne sai ya bayyana soyayyarsa akanta domin yasan cewa idan ya mabata kashe shi za a yi. Bisa wannan daliline zarmus ya dukufa wajen neman ilmin tsafi domin kawai ya sami damar da zai iya mallakar lasmir. Duk sa adda na aike su izuwa kasashe to shi baya yin komai face ziyarta bokaye a sirrance yana yi musu hidima kamar zai mutu. A hakan ne ya sami sirrrikan tsafi d yawa har ya zuwa a lokacin da ya shekara talatin da uku a duniya. A wannan lokacin ne ya tara mayaka a sirrance dare daya ya kawo harin summane izuwa garin nan domin yayi mini juyin mulki. Bai sami nasara yi mini juyin mulkin ba kuma mun fafata kazamin yaki da shi har mana kusa halaka shi amma sai yayi amfani da karfin tsafi ya sace yaruwata lasrin ya gudu amma mutum daya daga cikin dakarunsa bai tsira da rayuwarsa ba . Babu irin neman da banyi wa boka zarmus da yaruwata Lasrin ba a wannan nahiya ta mu da sauran nahiyoyi amma ko duriyarsu ban sake ji ba tsawon shekaru bisa wannan da Lilin ne na tara bokaye suka shiga yi mini bincike na tsawon kwanaki arba in. . A ranar kwana na arba in dinne suka zomini da magana daya. Maganar kuwa itace bazan taba samun damar karbo yaruwata ba a wajen boka zarmus face idan wani bakon sarrki daya rasa karagarsa yazo gareni irin matsalata a hakan na cigaba bincike na gano cewa kai ne saekin da zaizo gareni.. Page 18. Zidane kd .. Domin haka nayi ta zaman jiran zuwanka sai gashi kuwa kazo a wannnan lokaci. Tabbas ni ma yanzu na sallama raina dukiyata da mulkina don ganin bayan wannan makiyin nawa don haka ba gudu ba ja da baya. Kasani cewa a halin yanzu na tanadin dakarun yaki guda dubu dari.. Uku gami da bokaye dubu arba in wadanda zasu bamu gudummawa a cikin wannan gagarumin yaki da za mu tafi kuma nan da cikar kwanaki uku kacal za mu tafi. Sa adda sarki marzuk yazo nan a lbarinsa sai farin ciki ya turnuke Husam ya rungume shi suka kana zubar da hawaye. Kamar yadda hira ta kare tskanin sarki marzul da Husam haka mata kasance tsakanin gimbiya zarisha da jaruma lasmir a lokacin da wata likata ke duba lafiyarsu sakamakon gumurzun da suka yi a wajen gasa. Zarisha ce ta fara magana tace yake kawata idan har kinaso mu samin nasara a yakin da zamu tafi can birninku to dole ne ki cire kishi a zuciyarki a kai na dangane da jarumi zaunal. Page 19. Zidane kd. Ina mai shawatar ki da ki cire sonsa gaba daya daga cikin zuciyarsa sbda ba akwai matar da xzai aura wadda baki taba zatonta ba. Ki sani cewa nima ina tsananin sonsa kome ya ke bukata a wajena zan iya bashi koda kuwa bazai aure ni ba amma na hkra dashi sbda bai dace dani ba.. Sa adda lasmir taji wanna batu sai hakalinta ya dugunzuma ta dubi gimbiya zarisha cikin alamun tsananin damuwa da rashin fahimta tace to wai shin wacce wannan mace daza ta mallaeke shi anan gaba? Zarisha tayi murmushi tace sanin hakan a gareki ba shii da amfani. Page 20. Zidane kd. Zai fi kyau ki sani a loakcin da ya dace gama fadin hakan ke da wuya sai zarisha ta koma ta kwanta aka cigaba da duba lapiyarta. Kamar yadda sar marzuk ya fada haka abin ya kasance wato sai bayan kwana iki sannan suka yi gagarumin shiri tare da dakarun yaki da bokayen aka debi kayan yaki masu yawan gaske gami da bayi da barri aka kama hanya aka durfafi birnin azzlumai. KUBIYO MU A LITTAFE NA GABA DON JIN YADDA ZA TA KAYA.... Kash Saidai kuma naifito. Amma inyato zamu cigaba.. Muhadu a littafe mai suna sadauki. Naku har kullu Suleiman Zidane kd. Whatsapp 09064179602 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 4 of 4