Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 4
sawun dakin nasa ma ya bace bat. Bisa dole suka hakura suka koma can masaukinsu.. Da isarsu sai Husam ya duni zaunal da lasmir yace Sarauniyar kasuwa ta ci amana ta tabbas wadannan dakarun da suka zo mana aiken makiyanmu ne baskar. Dole ne mu kwashe kayanmu daga nan mu tafi izuwa birnin daban. Domin neman dakaru dubu dazasu taimaka mana wajen shiga birnin azzalumai kamar dole nemuyi taka tsatsan akan komai da kowa. Tabbas yanzu sarki baskar da bokan zarmus sun san cewa mun fito shirin zuwa birnin azzalumai . Batarre dawata gardamaba sai zaunal da lasmir suka shiga hada kayayyakinsu.. Page 9 zidane kd. Nan da nan kuwa suka gama kintsawa suka nufi wani bangare daban a cikin daji.. Suna cikin tafiyar ne zaunal ya waigo bayansu sai yaga wani abu daya bashi mamaki ba wani abu yagani ba face yadda sawayen dakarunsu ke bacewa bat nan take amma da yake ya san cewa akan shirin Husam sai kawai yayi murmushi ya juyar da kansa suka ci gaba da tafiya.. Sai da suka kwana uku cur suna tafiya kuma ba sa yada zango face dare yayi sosai kuma sai da duhu sannan su kwana , kashe gari kuwa sai su tashi da sassafe su cigaba da tafiya a kwana na uku ne da farkon yammaci suka hangi wani dan bban gari a gabansu. Da yake Husam ne akan gaba sai ya ja linzamin dokin ya tsaya cak ya kurawa garin idanuwa da ganin haka sai summa zaunal suka yo koyi dashi.. Tsawon kusan dakika dari shida Husam na kallon garin idanunsu a kafe ko sau daya bai kifta ba alamar cewa nazari yake yi acikin halwar tsafi.. Daga can sai yai doguwar ajiye zuciya gami da motsa idaninsa ya dubi zaunal da lasmir yayi murmushi yace ba mu da wata matsala acikin wannan gari sai guda daya.. Caraf sai zaunal yace wace irin matsalar mutanen wannan garin ita ce tsananin son kudi, mazansu da matansu. Akan kudi babu abinda ba zasu iya yi ba. Koda jin haka sai lasmir tayi murmushi tace aikuwa indai suna da son kudi za muyi saurin samun abinda muke bukata....... ANAN ZANDAKATA SAI KUMA IN ALLAH YAKAIMU GOBE DA SAFE ZAKU JINI DA CIGABAN WANNA LABARIN . NAKU HARKULLUM SULEIMAN ZIDANE KD.. KUYI COMMENT.. DA share :...... IZUWA WANI GROUP.. ANA TARE.... BIRNIN AZZALUMAI 4 Littafe na hudu Part B. Typing.. Suleiman zidane kd.. 09064179602: KODA JIN HAKA SAI LASMIR TAYI MURMUSHI TACE AIKUWA INDAI SUNA DA SON KUDI ZAMUYI SAURIN SAMUN ABIN DA MUKE BUKATA.. Page 11 Tana gama fadar hakan sai ta kada linzamin dokinta tayi gabata na mai tunkarar kofar birnin... Batare da barta lokaci ba kuwa sai Husam ya bi bayanra sannan zaunal... Da isowarsu kofar garin sai suka iske kofar a rufe dakaru biyu na tsaye daga waje a wajen shigar yabi daga ciki kuma akwai kimanin dakaru guda dari a tsaitsaye cikin sharin ta kwana ... Daya daga cikin masu gadin biyu ya dubi su lasmir da kyau ya kare musu kallo yace kusu wannenne? Kuma menene ya kawo ku nan sarlak? Har lasmir ta bude baki zata bashi amsa sai Husam ya tari numfashinta yace mu mutanen birnin hal ne sannan kuma fatauci ya kawo mu nan. Page 12 zidaen kd.. Koda jin haka sai badakaren nan yayi murmushi yace barkanku da zuwa sarlak.. Batare da wani bata lokaci ba sai badakaren ya bude musu kofa ya ceku zo ku shige.. Husam ya bude su cikin mamaki yace ai baku cake kayanmu ba.. Badakaren yayi murmushi yace kar kadamu ai mun sauya tsari.. Gimbiya na ciki ita ce za ta caje ku.. Koda jin haka sai hankalin su Husam ya tashi jikinsu ya basu cewa ruwa ba ya tsami banza lalle akwai wani abin da yafaru wanda ya sa aka sauya tsarinan wannan garin.... Kai tsaye suka kada dawakansu izuwa cikin gari na Sarlak amma wannan karo husa, ne akan gaba zaunal na biye da shi lasmir . Suna shiga akan mai da kofa aka rufe .. Take suka ga wadansu dakaru guda dari cikin gagarumar shigar yaki.. Page 13 zidane kd.. Hamsin na tsaye a dama Hamsin na tsaye a hagu.. A tsakiyarsuu akwai wani karamin gado na katako mai dauke lema samansa. Kwance akan gadon wata jarumar ce cikin shigar kayan yaki na karfe., kanta mana cikin hular karfe tana shara barci abinta .. Koda su hasam suka zo zasu gifta ta gaban wannan mayakiya da ke barci sai kawai suka gata daga hannunta guda nan take dakaru suka sha gabansu husam kana tsayar dasu.. Mayakiyar ta mike zaune daga kwance sannan tasa hannayenta biyu ta cire hular karfen dake kanta... Nan take kyakkyawar fuskarta ta bayyana a lokaci da dogon gashin kanta ya tarwatse a sama cikin iska kuma ya zubo a bayan gadonta.. Koda ta bude kyawawan fararen idanunwata ta dubi su Husam sai nan take zaunal yaki zuciyarsa ta buga d karfin tsiya fiye da lokacin da yayi wa lasmir ganin farko.. Page 14 zidane kd.. Koda mayakiuar tayi arba da zaunal sai ta kura masa idanu ko kifatawa bata yi kuma ta kasa mikewa tsaye har sai da daua daga cikin dakarunta yayi mata magana yace ranki ya dade ba duba su zaki yi bane.. A kasannan ne mayakiyar ta mike tsaye zumbur tamkar wacce ta farka daga mafarki ta karaso wajensu ,.. . A wannan lokacine lasmir ta murtuke fuskarta nayiwa mayakiyar wani irin kallo na rashin yarda... Nan dai mayakiyar ta sa aka caje kayansu Husam koda taga suna dauke da dinare mai yawa sai fuskarta ta fadada da Murmushi ta dubi Husam cikin risinawa da biyayya tace lalle marhaban da sarkin jiya na birnin azzalumai .. Page 15 Koda jin wannna batu sai zukatan su Husam suka buga da karfi sbda tsananin mamaki har firgicinsuu ya bayyana karara akan fuskokinsu... Daga nan haka sai mayakiyar ta tuntsure da dariya sannan ta dubi husam cikin nutsuwa tace kwantar da hankalinka yakai ma abocib adalci wannan dakeson daukar fansa akan mace amanarsa.. Ka yi sani cewa har abada bazan taba zama mai cutar dakai ba saidai na taimake ka akan kokarin cika burinka.. Yau shekara goma kenan nae jiran zuwan wannan rana da zakazo wannan birnin namu domin a dalilin nima zan sami damar cika nawa burin. Sannan gimbiya risha ya ga sarki marzak na wannan birnin namu. A dalilin wanna zuwa nakane muka sauya tsarin tsaro a garinmu ba don komai ba sai don mu hana makiyan ka samun damar shigowa birninmu. Page16 Lallai ku manyan baki ne masu daraja a wannan gari kuma mahaifina zai yi matukar farin cikin zuwanki.. Ku zo mu karasa fada.. Zarisha na gama fadin hakan sai ta nufi inda aka daure dokinta.. Nan fa husam lasmir da zaunal suka kama kallon juna ba tare da daynsu ya iya cewa koamai ba... Husam ne ya fara kada dokinsa ya bi bayan gimbiya zarisha .... Koda ganin haka sai zaunal da lasmir suka bisu .. Zarisha ta ci gaba da yiwa su zaunal jagora izuwa cikin gari amma sai tarinka yawan waiwayowa baya tanba kalon zauunal, hakan ne yasa lasmir taji ranta ya baci, ta cigaba hararrarta... Page 17. Duk da zarisha ta lura da yadda lasmir ke hararrata ko kadan bata dam ba shi kuwa zaunal da yaga kallon da zarisha ke yi masa yayi yawa sai ya sunkuyar da kansa kasa ya daina yarda suna hada idanu.. Shi kuwa Husamm wani abu ne ya sameshi wanda yayi matukar daure masa kai yajefa shi cikin wasi wasi da fargaba.. Ba kamai ne ba wannan al amarinba face jiyayi a karon farko yayi arba da zarish ya kamu da tsananin sonta ku,ma so ron wanda namiji ke yi wa matar da yake son mallaka a matsayin abokiyar rayuwarsa... Akan wane dalili zanso wannan budurwar sa ar yar cikina alhalin tsawon shekaru goma ina begen matata zamirat mace dana so fiye da dukkan matan duniya kuma akan tana fara soyayya kuma ban kara jin ina son wata ba sai yanzu... Page 18 zidane kd.. Amma dai idan haka so yake to tabbas so mahaukaci ne kuma kuruciyarsa tafi ta yaro dan shekara uku tun da gashi yana neman jefa ni cikin ramin karya.. A bangaren jarumar las,mir kuwa itama zuciyarta cika makil da wasi wasi tarinka yiwa kanta tambayar barkatai mnarasa cikakkiyar amsa ... Tambayar farko da ina kishin kallon da zarish ke yiwa zaunal? Shin hakan na nufin na kamu da sonsa kena? Kyau ko jarumtaka? Bai fini kyau ba. Jarumtaka kuwa in yafini ai da kadan ne. Babu wata hukka da zata sa na kamu da sonsa.. Kamar yadda lasmir ta kance a cikkin wanna hali na zance zuci haka shi ma zaunal ya kasance.. Abin da zuciyarsa ta fara raya masa shine ina ma ace allah zai mallaka masa wadannan matan Page 19 Biyu a matsayin matansa na auew ai da shikenan ya rufe kofar karin aure,,. Wata zuciyar kuma sai tace dashi kai wawa ai da baka taba zaton zaka ga wata mace mai kyan lasmir ba sai gashi kuma kaga wacce mata fitta zarisha? Sa adda zaunal yazo daidai nan a zance zucinsa yaga sun iso fadar sarki marzuk mahaifin gimbiya zarisha.. Nan take suka sauka daga kan dawakansu su hudu hadinai suka kama dawakan su tafi su. Page 20 Zarisha ta wucce gaba suna biye da ita suka kunna kai cikin fadarr ba tare da wani shamaki ba... Marubuci yace ABIYO MU A LITTAFE NA GABA DON JIN MAI ZASU TARAS A FADAR... NAKU HARKULLUM SULEIMAN ZIDAN KD..... PAGE... Aslm yan uwa ga page dinnmu sai kayi kokari shiga domin samun Littafe Kala Kala cikin blue dinnan Na kasa.. Duniyar Masoya Litattafan yaki only Home of Littafan Yaki And Hausa Novels Hausa Novels And Yaki by Zidane Matan Arewa Special Group Zauren Muslims BIRNIN AZZALUMAI Littafi na Biyar 5 Na Abdulaziz Sani M Gini Complet Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.com.ng Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.com.ng Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com BIRNIN AZZALUMAI 5 Littafe na Biyar . Complete book 5 Typing.. Suleiman zidane kd... Shekaran bugan littafe 2018: Page 3 Fadace Babban kuma kasaitacciya. A kwalla sai da suka ratsa ta cikin kofofi bakwai sannan suka iso inda sarkin Zaruk yake. Bisa wata katuwar karaga suka hango shi azaune fadawa da dakaru da mutane gari sun yi masa kawanya ana ta tafiyar da harkokin mulki cikin nishadi da farinciki . Koda sarki zarmuk ya hango Gimbiya zarishi tare da su Husam sai ya mike tsaye cikin matukar farinciki ya sauko daga kan matattakala karaga ya taresu . Nan take ya rungume Husam yananuna tamkar wanda yaga dan uwansa najini.. Cikin Girmamawa da karramawa ya kama hannun Husam yajashi Har zuwa kan karagarsa ta mulki suka zauna tare.. Ita kuwa mulki suka zauna tare . Ita kuwa zarisha sai ta mikawa zaunal Hannunwanta da nufin ta kamanashi ta jashi izuwa mazauninta sai yazuke hannun nasa ta kamo Lasmir.. Koda suka hada idanu sai zarish ta yiwa lasmir murmushin dole tta jata suka nufi wajen zaman nata suka zauna.. Page 4 Zidane kd.. Shi kuwa zaunal wani ba fade ya kai shi wani wurin dabam ya zauna.... Nan take aka kawo wasu Husa, abinci da abin sha na alfarma suka ci suka sha a lokacin da wadansu mawaka da yan rawa ke dauke musu kewa a tsakiyar fadar... Ana cikin wannan sha ani sai marzuk ya dubi Husam a cikin fara a yace har abada sark sarki ne ko da baya kan karaga ballantana sarkin dake daf da komawa kan karaga tasa . Sa adda Husam yaji wannan bati sai yayi dan guntun murmushi yace mecece Hujjarka har da zaka ce ina daf da komawa kan karagarta? Page 5. Zidane kd. Marzuk yayi murmushi yace ai zuwan wannan jarumin da kuke tare dashi ya tabbatar da hakan gareni da kuma zuwanku birnina.. Tsawoon Shekaru da kayi akan karagar Har ka sauka baka taba kawi min ziyara ba ni ma ban taba kawo maka ba alhalin muna makotaka da juna sai yanzu... To nima bincike nane ya nuna min cewar duk ranar da ka kawo kanka kasata a wannan lokacin zan cika babban burina da ya gagare ni tsawon shekaru cikin mamaki Husam ya dubi Barzuk yace menene Wannan burin naka? Buri na da naka kusan iri daya ne. Yar uwata wadda muke uwa daya uba daua kuma wacce ita kadai ta rage mini daga cikin zuri ata tana hannun boka zarmus bokan dake taimakon babban makiyinmu baskar.. Page 6. Zidane kd. Yau shekara goma sha daya kenan rabona da ita. Kuma duk yadda zanyi na yi domin na karbota na kasa... Bincike ya nunamin cewa dole kun hada karfi da karfe daku da yata Gimbiya Zarisha sannan zaku iya kawar da sarki baskar da boka zarmus sannan zan sake ganin yar uwata jalila kai kuma kaga matarka zaminat.... Sa adda sarki marzuk yazo nan a jawabinsa sai Husam yasake kamuwa da tsananin mamaki yace yanzu kana nufin kace zarisha jarumace?. Zarmus ya gyada kai cikin murmushi yace kwarai kuwa yata gagarumar jaruma ce kuma gawurtacciyarr matsafiya ba na zaton cewa akwai abinda za ku fita kai da yarka da bakon jarumi Zaunal sai dai akwai wani abu da Daya shigemini duhu akan zaunal. Page 7. Zidane kd. Husam ya gyara zama yace mene ne ya shige maka duhu akan jarumi zaunal? Zarmus yace bisa binciken danayi duk irin masifar da zaunal zai shiga da kuma tsananin walahar da zai sha babu wani mahaluki da zai sami nasarar hallaka shi walau mutum ko aljani kwaro ko wata dabba. Kaga kenan yana da wata baiwa ta musamman wacce mukakaso gano kota mecece nida zarisha.. Ka sani cewa nan da kwanaki biyu kacal za a kammala shirin wanna tafiyar izuwa Birnin Azzalumai ni ma dani za ayi wannan tafiya amma ina mai baka shawara da hakura dayin wannan tapiyarr ka barawa lasmir wannan sandar taka ta tsafi ta tafi kuma ka zauna anan ka jira mu muje mu dawo.. Cikin matukar mammaki akaro na biyu Husam ya sake duban sarki marzuk yace sbda me kabani wannan shawarar? Marzuk yayi shiru kamar ba zai bashi amsa ba yayi ajiyar numfashi sannan yace sbda idan kaje birnin azzalumai mutuwa za kayi... Sa adda Husam yaji wannan batu sai hankalinsa ya dugunzuma yayi shiru baice komai ba,.. Bayan an gama zaman fada sai aka kai su Husam masaukinsu.. Wani kayatacce gida mai dauke da komai na jin dadi. Kuyangin dake hidima a gidan sun kai su ashirin da biyar kuma dukkansu kyawawa ne yan mata. Nan take aka rabawa su Husa dakuna wato kowannen su aka bashi dakinsa daban.. Page 9. Zidane kd.. Bayan Jarumi Zaunal yashiga cikin dakinsa ya ajiye kayansa sai dawo falo ya zauna domin ya dan huta kafin lokavin barci yayi.. Zamansa keda wuya sai yaji an kawankwasa masa kofa.. Batare da yasan ko waye ba sai ya bada izinin shigowa... Sbda shi azatonsa Husam da Lasmir ne sukazo domin su tattauna akan gagarumar tafiyan dake gabansu... Kwatsam sai yaga ashe gaba dayan kuyagin gidan ne su ashirin da biyar suka shigo dukkaninsu sai suka jeru a gabansa.. Babbar a cikinsu ta dube shi tace ya shugabana gamu gareka ka zabi wadda kake bukatar data debe maka kewa... Kodajin wannnan batu sai mamaki ya kama jarumi zaunal kuma ransa ya baci ya dubeta a fusace ya ce bana bukatar dayanku ku fice mini daga dakii batare da wata gardama ba sai kunyangi suka fice gaba dayansu.... Page 10 DALILIN YASA NIMA NABI BAYANSU KENAN DAN KAR LAIFIN WANI YA SHAFE NI ......... SAI KUMA IN ALLAH YAKAIMU GOBE ... NAKU HAR KULLLUM ZIDANE KD.. BIRNIN AZZALUMAI 5. Littafe na biyar. . . PART B. Typing Suleiman zidane kd. Page 10 Kodajin wannnan batu sai mamaki ya kama jarumi zaunal kuma ransa ya baci ya dubeta a fusace ya ce bana bukatar dayanku ku fice mini daga dakii batare da wata gardama ba sai kunyangi suka fice gaba dayansu.... A dai dai wannan lokacin ne gimbiya Zarisha ta nufo dakin kwatsam sai ga Lasmir mata taho. Suna hada idanu sai lasmir ta murtuke fuska ita kuwa Zarisha sai ta kama yin murmushi. Kusan tare suka shiga cikin dakin suka iske jarumi zaunal a zaune yayi tagumi. Koda yaji motsin shigiwarsu ya dago kansa sai yayi arba da yanmatan biyu tsaye a gabansa. Cikin kaduwa da mamaki ya mike tsaye ya dube su yace lapiya? Me kuka zo yidakina yanzu? Lasmir tace inason nagana da kai ne ya kai dan uwana. Kodajin haka sai zarisha ta kyalkyale da dariya tace ta yaya zaunal ya zamo dan uwanki alhalin baki da wata nasaba ta jini dashi? Idan baki sani ba ki sani nafiki sanin komai a kansa kuma kai mana nasan komai akanki. Shi din nan da kike gani ba ya tsafi kuma tsafi baya tasiri a kansa kuma ya kasance ma abocin addinin musulunci. Koda jin haka sai idanun zaunal da na lasmir suka zazzari suka kamu da tsananin mamaki... Zarisha ta kyalkyale da dariya sannan tace ni da kuke duk min kamu da sonsa domin zukatanmun suna ta tunanin kuma suna tayi mana wasi wasi akansa. Soyayyar mu a gare shi ta banza ce domin dayarmu ba zamalleki shi ba.. Wadda zata mallakeshi zata bayyana a can birnin azzalumai kuma mace ce wacce duk tafi mu kyau ta fi mu matsayi ta fimu shekaru., tunda nidake duk baza mu mallakeshi ba ina rokonki da ki ara mini wannan rana ta yau da shi muyi soyayya ta dare daya... Kafin Zarisha ta gama rufe bakinta tuni jarumi zaunal ya daka mata tsawa yace da bakinki kinceni ma abocin addinin musulunci bane to mu a dokarmu ba ma kadaita da wata mace face muhararrama ko matar aure don haka ba na bukatar zaman wani lokacin ku alfarma guda daya ke da ita ku rufa mini asiri kada ku gayawa kowa cewa ni musulmi ne don fadin hakan zai iya janyo mattsala a cikin gagarumin aikin dake gabanmu.. Da jin haka sai jaruma zarisha tayi murmushi tace kada ka damu ba zan kara gayawa kowa ba, amma dai mahaifina ya san ko kai waye.. Page 13. Zidane kd Na yarda yanzu zan tafi na barka amma na tabbatar dacewa dole mu kasance tare ko da kuwa a mafarki ne.. Tana gama fadin hakan sai ta juya ta fice daga cikin dakin. Fitar ta ke da wuya sai zaunal ya dubi lasmir yace ku kuma me kike jira baki tafi ba?? Lasmir tace ina da tambaya guda daya a gare ka kafin kafin ka amince akan zaka taimake mu mu yaki Sarki baskar domin karbo Mahaifiyata daga Hannunsa Abbana yace ka fadi ladan da kake son mu biya ka? In dai ka ba ni amsar wannan tambayar ba zan sake kusantarka ba... Lokacin da jarumi zaunal ya ki wannan tambayar sai ya yi ajiyar zuciya sannan yace har yau har gobe na kasa yanke hukunci akan ladanDa zab nema a wajenku.. Page 14. Zidane kd.. Abin da zuciyata ta rayamini shi ne bazan iya gani abinda ya dace na nema ba face bayan burinki yacika. Sa adda lasmir ta ji haka sai hankalinta ya dugunzuma ta juya da nufun fita daga cikin dakin har tasa kafarta a wajen sai ta sake waigowa ta dubi zauna tace shi kayi tunanin ko wacecce zata mallake ka nan gaba? Shin ka amince da duk abubuwan da ta fada?. Zaunal ya numfasa yace a matsayina na musulmi bai kamata na yarda da duk wata magana ta matsafi ba.. Ina fatan baki da sauran wata tambaya a gare ni sai da safe.. Idan kin fita ki jamin kofa... Zaunal na gama fadin hakan sai ya mike tsaye ya shige can cikin dakin barci cikin sanyi jiki da matukar damuwa.. Page 15. Zidane kd. Lasmir ta juya da sauri ta fice daga cikin dakin kuma taja kofa da karfi ta rufe.. Kai da jin karar rufe kofar kasan cewa a fusace take... Kashe gari bayan su zaunal sun gama kalaci a babbar turakar sarki Marzuk sai ya gayyacesu izuwa wani babban filin dake tsakiyar gidan sarautar.. Shi dai wannnan fili ba a yin komai a cikinsa ba face gasar jarumtaka. Ga isarsu filin sai suka iske gaba dayan jama ar garin sun taru mazansu da matansu manya da yara sun yiuwa tsakiyar filin kawanya suna ta shewa da jinjina.. Koda ganin wannan al amarin sai mamaki ya kama Husam lasmir Da zaunal. Husam ya dubi sarki Marzuk cikin rashin fahimta yace me kuma za a yi anan har ka gayyace mu? Koda jin wannan tambayar sai sarki marzuk yayi murmushi yace ina son na gwada jarumtakarka da ta yarka a kaina da yata... Nida kai zamu fafata yanzunan yata zarisha zata fafata da yarka 'lasmir. Idan mune muka yi nasara a kanku to tafiyar da za ayi mune shugabanni. Idan kuma kuka yi nasara to kune shugabanin tafiyar caraf sai jarumi zaunal yace to idan kuma kuka yi ragas fa? Kuma yaya yanayin nasarar wannan gasar zata kasance? Sarki marzuk ya dubi Husam cikin murmushi sannan ya dubi husam cikin murmushi sannan ya dubi zaunal yace idan mukayi ragas kaine zaka zamo shugabanmu a cikin tafiyar... Yanayin nasarar wannan gasa shine ne duk wanda gadon bayansa ya taba kasa ya fadi gasar.. Gashi fadin hakan ke da wuya sai zarisha ta kurawa lasmir idanu tana yi mata murmushin mugunta.. Page 17. Zidane kd. Nan take sarki marzuk ya cire alkyabbar jikinsa sai gashi cikin gagarumar shigar yaki mai matukar kwarjini da ban tsoro.. Ita ma zarisha ta cire doguwar rigar dake jikinta sai gata a cikin shigar yaki da takubba guda biyu dauke akan cinyoyinra.. Sarki marzuk ya dubi husam yace maza ko koma masaukanku kuyi irin shigar yaki wacce kuka saba kuma ko debo makamanku ku dawo muna nan muna jiranku.. Koda jin wannan batu sai husam ya dubi yarsa lasmira suka yiwa junansu murmushi kawai sai suka juya da baya suka ruga da gudu izuwa can masaukansu. A wannan lokacin zarisha ta matso daf fa jarumi zaunal ta dube shi tace wai meke damunka ne gana baka cikin sukuni sosai? Zaunal yayi ajiyar numfashi yace ai babu yada za a yi na mai wwani sukuni sbda al amura gaba daya sai sauyawa suke. Da farko dai ni abin da yasa na baro kasa ta har yanzu ban sa ... Kafin ya karasa maganar sai zarisha ta tari numfashinsa tace shin kammanta ne da abin da na fada maka jiya daddare? Matar da zaka aura tana can a birnin azzalumai amma ba zaka ganta ba sai alokacin da muka fafata yaki. Koda jin wanna batu sai zaunal ya murtuke fuska yace nifa na gaya miki cewa duk abin da zaki fada daidai yakke da tsatsuniyar yara domin har abada bazan taba yarda da maganar tsafi ba.. Page 19. Zidane kd zarisha tayi murmushi tace amma dai ai kayi imani cewa akwai aljanu ko?. Duk ma abocin addininka yaya yarda cewa ubanjiku ne ya halarci mutum da aljan da sammai da kassai yarda cewa ubangijinku yana sanar da mutane ilmi iri iri a cikin har da ilmin taurari... Don haka kada kayi mamaki bisa du irin abin da zan fada maka.. Lallai zaka gaskata zancen idan lokacin yayi.. Tana gama fadin hakan sai ta tafi ta bar shi ta wuce izuwa cikin tsakiyar filin gasar.. A lokacin ne shi ma sarki marzuk ya bi ta a baya izuwa cikin filin.. Wohoho! Idan mutum ya ga lokacin da wadannan jarumi biyu ya da uba suka jera tare a cikin irin kirar da allah yayi musu ta kwarjini da jarumtaka da kyan siffa dole nesu burge shi.. Shigar su zarisha cikin filin gasar ke da wuya sai ga Husam da yarsa Lasmir sun shigo a cikin gagarumarr shigar yaki mai matukar kyau kwarjini da ban tsoro.. Nan fa kallo ya dawo kansu ai kuwa jama ar birnin ba su san sa adda suka fara yi musu jinjina da tafi ba.. Al amarin da ya karawa Husam da lasmir kwarin gwiyawa kenan suka nufin cikin filin gasar kai tsaye zuciyoyinsu dauke da sa ran samun nasara.... KUBIYO MU LITTAFE NA GAVA DON JIN YADDA ZATA KARKE.... SULEIMAN ZIDANE KD.. Mu HADU LITTAFE NA SHIDDA. WHATSAPP 08161272634::::: BIRNIN AZZALUMAI Littafi na shida 6 Na Abdulaziz Sani M Gini Complet Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.com.ng Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.com.ng Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com  BIRNIN AZZALUMAI 6 Littafe na Shida Part A Typing.. Suleiman zidane kd.. 08164272634 :......... Da Shigowarsu cikin tsakiyar filin inda sarki zarmu da zarisha ke tsaye sai suka tsaya suka fuskanci juna. A sannan alkalin gasar ya shigo ya tsaya a tsakiyarsu ya dadda tuna musu yanayin gasar da kuma dokokinsa.. Daga cikin dokar gasar shi ne in dai mutum ya fadi kasa da bayansa babu damar a sake kai masa wani hari ko a cutar dashi sannan kuma a cikin jaruman hudu duk irib yanayin daza su shiga wani bazai taimaki wani ba kuma duk wanda ya mutu a wannan gasa babu batun daukarr fansa sbda dama gasa ce mai hadari ta sai da rai. Alkalin yana gama yin wannan jawabin sai ya fice daga cikin filin ya koma cikin yan kallo yana zauna daf da jarumi zaunal. Faruwar hakan ke wuya aka buga gangar fara gasa. Nan take sai jaruman hudu suka ja baya kuma kowannen su ya murtuke fuskasa alamar cewa ba sani ba sabo kuma ba ragayya.. Kamar hadin baki sai dukkaninsu suka zare makamansu.. Husam da lasmir suna rike da takubbansu da garkuwoyinsu, sarki zarmus da gimbiya zarisha kuwa suna rike da takubba guda bibiyu. Bayan jaruman hudu sun ja baya ga juna sai suka fara kallon kalo kowannen su na nazarin abokin gwaminsa har izuwa tsawon yan dakiku daga can kuma sai suka rugo da gudu izuwa kan juna. Zarisha ta afkawa lasmir shi kuma sarki zarmus ya afakawa Husam aka ruguntsume da azabbben fada ya zamana cewa suna kai wa junansu sara da suka cikin tsananin zafin nama tunga da jarumtaka. Page 5. Zidane kd. Duk sa adda makamansu suka hadu sai dai kaji kara da tartsatsin wuta na tashi. Nan fa filin ya rude da shewar jama a . Sai da jaruman hudu suka shafe kusan dakika dubu daya da dari uku suna fafata azababben yaki batare da dayansu ya sami nasarar koda kwarzana a jikin daya ba. Babban abin da ya fi daurewa mutane kai shine duk salon da sarki zarmus suka zo shi sai a gasu zarisha ma sun iya hakama lasmir duk salon dasuka zo shi sai aga cewa sun hasam sun iya.. Koda jaruman hudu suka ga sun shafe wannan tsawon lokaci suna gurmurzu ba tare da sun sami wata nasara ba sai duk suka ja da baya. Page 6. Zidane kd. Kowannensu ya mayar da takobinsa cikin kube. Husam da lasmir suka yi jifa da garkuwowinsu izuwa can gefe daya suka gyara tsayuwarsu sina ganin haka sai sarki Zarmus da xarish suka dubi junansu suka yi murmushi alamar cewa suna murna da fidda raini da karfin damtse. Koda ganin abina dake shirin faruwa sai jarumi zaunal ya gyara zama cikin murna domin yana son yaga iyakar jarumtakar Husam kuma sai yaji a zuciyarsa yafi son su zarisha su sami nasara,,. Batare da bata wani lokaci ba sai jaruman hudu suka sake rugawa ga junansu suka kacame da

Chapter 3 of 4