da baza ta wuce 15 years ba
Tun bayan mahaifin shi ya zama governor wata izza da jiji da kai su ka saukar mishi
Duk abun da ya gani ya ce ya na so to sai ya same shi ko da ta karfi ce
Ga shi ba ya da mutunci ko kadan mahaifin nashi ma in ya bata mishi rai sai ya mishi kaca'kaca dan ba raga mishi ya ke ba
Tun haifuwar Nabila mahaifiyar su ta rasu , mahaifin na su ya sake aure har wajen sau uku
Amma duk wadda ya auro ba ta one month ta ke barin gidan sakamakon Dukan tsiyar da Hafiz ke yi musu
Mahaifin shi na sane amma ya ki yi mishi magana dan ya san ba karamin aikin Hafiz ne ba shi ma ya rufe shi da duka
Shi ya sa ya ja bakin shi ya yi shirin ya zuba mishi ido dan ya fi karfin shi
Duk wata badakala sa ya ke yi mahaifin shi na sane , sannu sannu har ya fara janyo Moctar cikin badakalar ta shi
Kullum su ne tafiya nightclub, ga shan giya da kayan maye
À takaice ba abun da ba su sha, sai dai ba su taba kusantar mace ba da sunnan Zina
Karewar zancen Nesrine da Inaya su ne mata na farko da su ka gani su ka ji su na son su
Yadda a ka yi Hafiz ya hadu da Nesrine
Wata rana ce driver din Ramatou bai zo daukar ta ba sai ta kira Moctar a kan ya zo ya dauke ta
A lokacin su na tare da Hafiz
Da su ka iso school din , su na tsaye bakin gate ita da Nesrine
Tun da Hafiz ya daura ido saman ta ya ji ya na son ta
Sai bayan sun koma gida ne ya ke tambayar RAMATOU wacece wanan yarinyar da su ke tare
Nan ta fada mishi wacece Nesrine sai dai ba ta fada mishi ba ta na da kanwa
Goben shi tun karfe 7 ya je bakin gate fin school din ya jiran ta
Amma wani ikon Allah ranar nan Nesrine ba ta zo school ba
Sai da ya gama tsayuwar shi ya gaji sannan ya koma gida ,
Goben shi ma haka ya dawo school din
Wannan karan ta zo amma ta na baya dan Inaya ta riga ta fitowa shi ya sa bai gane Inaya kanwar ta ba ce
Babu ko sallama ya kira ta cike da girman kai
Kallo guda ta yi mishi ta gane yayan Ramatou ne dalilin da ya sa ta fara sakin mishi fuska
Sannu sannu ta fara ganin halayan shi na gaskiya
Kullum sai ya zo college din su dan ya gan ta
Wata rana har waya mai tsada ya kama ta amma ta ki karba
Haka kuma ba karamin bata mishi rai ya yi ba har ya tsinka mata mari cikin fushi sannan ya bata wayar da karfi ya ce zai kire ta
Inda ya ajiye wayar nan ta bar ta ta yi tafiyar ta ko wa ya dauke ta oho !
Washe gari bayan ta zo school ya isko ta ya ke tambayar ta ina wayar da ya bata
Nan ta mishi karyar wai Mamar ta ta gan ta kuma ta amshe ta
Bai yi mata magana ba kawai ya bar school din , sai da ya yi wajen sati bai zo ba
Nan Ramatou ta zo ta hura mata kunne a kan Hafiz tsakani da Allah ya ke son ta ta daure ta ringa kula shi ko ya ji dadi
Abotar da ke tsakanin su ya sa ta yarda da zancen ta, dan ko ba komi yayan ta ne bai kamata ta wulakan tashi haka ba
Sannu sannu ta fara kula shi har ta fada soyayyar shi
Amma shi kuma ya na nan kamar dai kullum, bai sauya ba sam dan wani lokaci in ta bata mishi har marin ta ya ke wai a haka wai ya na son ta ( ni dai na ce humm)
Babu irin gift din da bai kama ta ba amma ko wane lokaci sai dai ta yar da shi tsakar hanya ko kuma ta bar shi nan inda ya bata shi
Sannu har soyayyar da ke mishi har ta fita zuciyar ta dan a ganin ta, Hafiz ba al'heri ba ne a rayuwar ta shi ya sa yanzu ta daina kula shi, shi kuma hakan ba karamin zafi ya ke mishi ba
TO KUN DAI JI WANENE HAFIZ DA KUMA ABUN DA KE TSAKANIN SHI DA NESRINE ✌
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : ANISH
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP
👇👇👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY
BOOK 1 ……………………………📚✍✍
[13/08/2024]
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 8 ❤🔥
▪Zayd
Zaune ya ke cikin motar su wajen mai zaman banza ya na rike da wayar shi ya na latsa wa ya na sanye da tracksuit sky blue colour ya na sanye da wadanan bakin glglass din nashi na gado
Yayin da Moussa shi kuma ke tukin, ya na sanye da Jeans baki da t-shirt Red colour
Su na a haka Moussa ya katse shirun na su da cewa " wai Amir ka fada ma babyn ka za ka yi tafiya ne ? " ya kai karshen ya na dan satar kallon shi ta wutsiyar ido
Shiru bai amsa mishi ba ko dago kai bai yi ba ya ci gaba da aikin shi
Dan murmushi geffen fuska Moussa ya yi sannan ya ce " Amir wai me ya sa ba ka kula yarinyar nan , ya kamata a ce yanzu ka fara yi mata magana tun da har za ta dawo tare da mu da zama "
Ba tare da ya dago kai ba ya ce " meye ruwan ka a ciki ? "
" babu kawai gani na yi bai dace abun da ka ke mata ba, ka ga fa kallon makaho da kurma ta ke maka ba ta san kai ainahin wanene ba, ba ta san kowa na ka ba, ko cikeken sunnan ka ba ta sani amma a haka ta ke son ka "
A hankali Zayd ya dago kai ya kali Moussa ya ce " me ka ke son cewa ? "
Yar karamar dariya Moussa ya yi kafin ya ce " lalle ma ka cika dan rainin sens, yanzu ka na son ka ce min duk soyayyar da ta ke maka ba ka ganin komai ? , lalle ma yau ka cika babban makaho " ya kai karshen ya na sake bushewa da dariya
" wait ! Maganar me ka ke yi haka, wannan baby har ya san minene soyayya ? na ga ai gaban ka ta ce dakwai wanda ta ke so , ni wlh maganar ta sai da ta ban mamaki , a sani na dai ban taba ganin ta da wani yaron ba , sai dai a cikin college din su " ya kai karshen ya na medo da kallon shi kan wayar hannun shi ya ci gaba da aikin shi
" humm wai kenan ba ka gane ba da sunnan ka ne ta so fada ba, dan ka na wajen ne ya sa ta yi shiru , kai a ganin ka duk abun nan da ta ke ma da sunnan makobtaka ne kawai, no Amir ! Wlh pure love ne ta ke yi maka, kallo guda za ka yi mata ka gane soyayyar ka a idanun ta, nassan wadanan bakin glass din ya hana ka gani, Amir kai ka ce min ka na son ka manta rayuwar ka ta baya , to wannan damar ka ce , ka karbi matar ka , and found your family "
Shiru Zayd ya yi bai ce da shi komai ba amma cikin ranshi ya na tunanin kalmomin Zayd tabass wanda ke maka kallon makaho da kurma , kuma a hakan mutumin ya so ka ya tabbata soyayyar gaskia ya ke maka
" no ! Gaskia she is to small for me , wannan ko dauko ta ba na tunanin za ta iya bare har a yi tunanin wata familyn, gaskia ban yarda da abun da Diya ke fada ba " ya fada cikin zuciyar shi
Cen kuma wata zuciyar ta ce mishi " in ta tabbata yanzu kai ma ka na son ta ? "
Da sauri ya girgiza kan shi ya ce " no ! Impossible i can't do that "
Kallon shi Moussa ya yi kafin ya ce " what you can not do ? "
Dago kai ya yi ya kali Moussa sannan ya ce " ba zan iya daukar ta a matsayin mata ta ba " sannan ya meda bayan ya jingina a bayan kujerar shi ya lumshe idanun shi
" Why ? na ga ai matar ka ce da aure a tsakanin ku "
" Diya ba za ka gane ba ne , ni fa ban san minene soyayya ba , ba na tunanin zan iya son yarinyar nan gaskia , she is to young , duk shekarun nata nawa su ke ? at least na yi biyun shekarun ta "
Moussa bai ce mishi komai ba ya yi parking din motar su a geffen hanya
ya na jin sun tsaya ya bude idanun shi a hankali ya kali Moussa ya ce " Why ka tseda motar ? "
bai ba shi amsar tambayar shi ba ya ce " Amir , na san dalilin da ya sa ka ce ba za ka iya daukar ta a matsayin matar ka ba , har yanzu kallon yarinya ka ke yi mata , ka na tunanin ba za ta iya ba ka hakin ka na aure ba , please ka Meda wannan zancen gefe , yarinyar nan ta na son ka tsakani da Allah , na sani kai ma ka na son ta cikin zuciyar ka , kawai wannan izzar ta ka ce ta gidan sarauta ke hana ka yarda da ka na son ta kai ma "
" I don't love her , ni dai na fada maka ba zan iya daukar ta a matsayin mata ba gaskia " ya kai karshen ya na lumshe idanun shi
" Why ? ba ta da kyau ne ? .. "
cikin nitsuwa Zayd ya katse shi da cewa " no , kai ma ka sani ta na da kyau , She is so cute musaman idan ta yi murmushi wannan dan dimple na ta ya fito "
wani kyawatencen murmushi Moussa ya saki cikin zuciyar shi ya ce " Sannu da rainin sens kawai , yanzu har ka San da ta na da wani dimple ? , mu je zuwa za ka aiki na "
a fili kuma ya ce " Kennan murmushin ta na burge ka "
" Yeah sosai ma , Kamar Fitar rana haka murmushin ta ya ke , ko ba ka so dole sai ka kalla "
( Kai fa da allamun Malam Zayd ya fara fita hayacin shi 🤣🤣🤣🤣 )
ya na gama fadar haka ya jiyo Moussa ya bushe da wata shegiyar dariya
a dubu dari Zayd ya bude idanun shi ya na kallon Moussa da ke ta dariyar shi har wasu hawaye su ka zubo mishi
dan karamin tsaki Zayd ya yi kafin ya ce " ka ga malam idan ba za ka tada motar nan ba mu tafi fada min na sauka "
dan tsagaita dariyar shi Moussa ya yi kafin ya ce " okay shikenan mu tafi , Mister Love " ya kai karshen ya na tada motar su ka bar wajen
shi dai Zayd bai ce mishi komai ba ya meda idanun shi ya lumshe , ko me ya ke tunani oho !
Ta kassan ido Moussa ke kallon shi , har sai da zayd ya lumshe idanun shi , Daga kafadun shi Moussa ya yi irin ban damu ba cikin ranshi ya ce " in ta yi tsami ma ji "
Haka su ka ci gaba da tafiyar su ba wanda ya ce ma wani ufan har su ka isa inda za su je
▪Inaya
Konce ta ke saman bed din su ta na kallon ceiling ta daura hannu daya saman ciki dayan kuma saman gashin ta, ko tunanin mi ta ke oho !
Ta na a haka malam ya shigo dakin ya na sallama
Ba tare da ta motsa ba ta amsa mishi sallamar shi kassa kassa
Bakin gadon ya karaso ya zauna sannan ya kai hannun shi ya daura saman nata da ke saman cikin ta ya ce " auta, wai me ya ke damun ki ne tun shekaran jiya na lura yanayin duk ya sauya ko waje na da ki ke zuwa kin daina ko laifi na yi miki ? "
A hankali ta janye hannun ta , sannan ta juya ta bashi baya sai ta ce " Abba me ya sa za ku min aure ba tare da na sani ba, nassan ku na ikon yin hakan amma Abba ni ba ni son wanda a ka aura min , gaskia Abba a raba auren nan "
" dalilin da ya sa wacen ranar na tambaye ki in kina son shi , amma ba ki ba ni amsa ba ki ka tashi ki ka tafiyar ki "
" ni Abba ba ku tambaye ni in ina son shi ba , "
" to shikenan yanzu bara na sake tambayar ki , ki na son Zayd ? "
Da sauri ta ce " ina son shi , duk da ban san meye so ba amma har cikin raina na ke jin shi , amma gashi yanzu kun raba mu har abada Abba ya zan yi na cire son shi a cikin raina " ta kai karshen kamar ta yi kuka
Dan murmushi yayi kafin ya ce " to ai ba sai kin cire son shi ba a ran ki "
" Abba ya zan je gidan wani ina son wani kuma, ni gaskia Abba ba ni son wanda a ka aura min , ko da ba za ku yarda na auri yaya Zayd dan Allah Abba kar ku aura min wanda ba ni so "
" na ga yanzu ki ka ce ki na son shi ya kuma za ki juya zancen "
Kuka ta saki ta fara harba kafafun ta kamar karamar yarinya ta ce " ni Abba ba shi ba na ce na ke so "
Yar karamar dariya malam ya yi dama da gangan ya ke jan mata rai
Sai da ya ida dariyar shi sannan ya ce " to shikenan wanene ki ka ce ki na so ? "
" yaya Zayd " ta fada cikin kukan nata
Hannun shi ya kai saman kafadar ta sannan ya ce " yo ai ni ma shi ni ke cewa, shi ne wanda na aura miki , amma tunda ba ki so zan kira shi in ce ba ki son auren " ya kai karshen ya na janye hannun shi da ga saman kafadar ta ya mike ya zai bar dakin
Har ya kai bakin kofar ya jiyo Muryar ta ta na fadin " da gaske Abba yaya Zayd ku ka aura min ? "
A hankali ya juyo ya na kallon ta
Ta na zaune tsakiyar gadon ta na kallon shi idanun cike da hawaye
Jinjina mata kai ya yi sannan ya sa kai ya fice dakin
Wani irin sanyi ne ta ji cikin zuciyar ta lokaci guda ba ta san lokacin da wani kyakyawan murmushi ya kubce mata ba har da wata yar karamar dariya
Ta dauko pillow ta boye fuskar ta, ta na dariya ta koma ta konta
▪After one week
▪Misalin karfe 5 na yamma
▪Inaya
Zaune ta cikin falon gidan ta buga uban tagumi kamar ta yi kuka ita kadai cikin gidan
Ta na a haka ta ji a na sallama
A hankali ta dago kan ta, ta amsa sallamar
Zayd ne da Moussa su ka shigo gidan ko wane ya na rike da ledodi
Ta na ganin su ta saki murmushi ta ce " sannu da dawowa "
Moussa ne ya amsa mata ya na murmushi ya na takowa ya ajiye ledodin hannun shi saman sofa sannan ya zauna saman sofar da ke fuskantar ta ta
Shi ma Zayd takowa ya yi ya ajiye ledodin hannun shi saman table sannan ya zauna geffen Moussa ya jingina a bayan sofar ya daga kai ya lumshe idanu shi ta cikin glass din shi
Murmushi ta yi kafin ta mike ta nufi dining table ta bude fridge ta dauko jug na ruwa ta ajiye saman tray da glass biyu
Sannan ta dauko tray ta komo falo , ta ajiye shi saman table ta zuba ruwan cikin glass ta mika wa Moussa
Karba ya yi ya na murmushi ya yi mata godiya
Har ta dauki guda glass za ta zubama Zayd Moussa ya yi saurin cewa " bari ba sai kin zuba mishi ba azumi ya ke "
Dago kai ta yi ta kaleshi sannan ta saki dan karamin murmushi sannan ta mike ta koma saman sofar da ta tasso ta na sunkuyar da kai
Ta na zama ko , Zayd ya mike tsaye ya nufi corridor ya shiga bedroom din shi
Da kallo su ka raka shi ita da Moussa har sai da ya shiga bedroom din shi sannan ta kali Moussa ta ce " yaya Moussa ina ganin yaya Zayd ba ya so na "
Dan murmushi yayi kafin ya ce " haba babyn malam ya isa ma ya ce ba ya son ki kawai aiki ne ya yi mana yawa kwanan nan shi ya sa ki ka ga ba ma yawwan zama gida "
Jinjina mishi kai tayi sannan ta sunkuyar da kai ta fara wassa da dan yatsun ta
Dan murmushi yayi kafin ya matso bakin sofar ya kai hannu ya dauki ledodin da su ka zo da su sannan ya mike ya tako gaban ta ya ajiye mata su sannan ya ce " Ga tsarabar ki nan, sannan ki shirya gobe za ki koma school "
Da sauri ta dago kai ta kaleshi ta ce " yaya Moussa school fa ? Yaya Zayd ya yarda ? "
Jinjina mata kai ya yi kafin ya ce " yes ya yarda mana shi da kan shi ya je ya sayo miki sabon uniform , da sauran abubuwan da za ki bukata "
Da sauri ta mike tsaye ta na tsale ta na dariya kamar karamar yarinya
Shi dai Moussa ya tsaya ya na kallon ta ya na murmushi " she is si innocente " ya fada cikin ranshi dai'dai lokacin da ya ke juya wa zai shiga corridor
Har ya yi nisa ya tsinci Muryar ta ta na fadin " nagode yaya Moussa "
Ba tare da ya juyo ba ya ce " ba ni ya kamata ki yi ma godiya ba "
Ya na gama fadar haka ya ci gaba da takawa ya nufi bedroom din Zayd
Bai mishi knocking ba kawai ya wuce bedroom din kai tsaye
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : MEERAH❤💫
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL
👇👇👇👇👇👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP
👇👇👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY
BOOK 1 ……………………………📚✍✍
[14/08/2024]
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 9 ❤🔥
▪Zayd
zaune ya kebakin gadon shi ya na rike da wayar shi , ya na sanye da jeans navy blue , da T-shirt white color , amma ya cire bakin glass din shi
ya na a haka Moussa ya shigo Dakin ya na sallama
cen kassan makoshi ya amsa mishi sallamar shi , ko shi kan shi Moussa bai ji amsar ba
Geffen shi Moussa ya tako ya zauna sannan ya ce " Amir ! "
Ba tare da ya dago kan shi ba ya ce mishi " uhmm ? "
" Amir na yi tunanin maganar da na yi maka za ka saurare ni , wai me ya sa duk abun da na fada maka in dai ba ka niya ba baza ka yi shi ba , yanzu sati guda da ka je gidan su yarinyar nan ka dauko ta amma ko kalma daya ba ka taba ce mata ba , ka ce min akwai binciken da ka ke son yi a kan ta, in ba ta zauna kusa da kai ba ta ya za ka yi binciken , Zayd wlh ba na jin dadin abun da ka ke mata , shin minene laifin ta a ciki, ka na ga karama ce sosai ko ba za ka iya soyayya da ita ba ka kula da ita a matsayin kanwar ka mana "
Shi dai Zayd ko dago kai bai yi bare ya ce mishi wani abu ya na ci gaba da latsa wayar shi
Sai da Moussa ya gaji da zubar shi sannan ya ce " Amir ni ina son in san dalilin da ya sa aka aura maka ita "
Wannan karan sai da ya dago kai slowly ya kale shi kafin ya ce " a kan hakan ni ke bincike "
Dan zaro idanu Moussa ya yi kafin ya ce " ban gane ba kawai malam zowa ya yi ya ce ka aure ta kai kuma ka yarda ? In da ba ka son ta na minene za ka yarda "
Ajiye wayar hannun shi ya yi saman bedside drawer sannan ya juyo da kyau ya kali Moussa sannan ya ce mishi " ba haka ba ne , shekara biyu baya , lokacin ka tafi Abuja dibo company , dai'dai na fito da ga cikin gida na hadu da malam ya na tafiya da sauri ko kallon gaban shi ba ya yi, a haka har ya kai min karo ya yi baya zai fadi , bayan na taro shi ya na yi min godiya kuka ya kubce mishi har da hawaye ya shiga yi min wasu magaganun allamun ya fita cikin hayacin shi , na yi matukar mamaki ya babban mutun na kuka haka kamar karamin yaro , na so na ji dalilin kukan na shi , sai na ja hannun shi mu ka shigo gidan nan na zaunar da shi sannan da hannu na tambaye shi minene ya ke kuka nan ya ke ce min " Zayd kashe min auta ta za su yi yanzu shekara biyu ina boye ta amma ina ji a jiki na wannan karan sai sun gano mu ban San ya zan yi ba , ita ce farin ciki na , ba zan iya jure rashin ta ba Zayd na shiga uku na " ni sam ban gane abun da ya ke nufi, sai na tsaya ina kallon shi ina son in karanci abun da ya ke nufi, sai da ya ida kukan shi sannan ya riko hannu na ya ce min " don Allah Zayd ina son in roke ka wata Alfarma " jinjina mishi kai na yi , ina