Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 9
mata Mike wa tsaye ya yi cikin bacin rai ya daga mata murya ya ce " ni za ki raina wa hankali ke har kin isa ki min karya " Ya na gama fadar haka ya kai hannu ya shake ta ya hada kan ta da bishiyar cikin tsawa ya ce " meye sunnan ta na ce miki " Cikin kuka ta ce mishi " Maryam sunnan ta Maryam " da kyair kalmar ta karshe ta fito dan ba karamar shaga ya yi mata ba Ganin ya na neman ya kashe ta ya sa Moctar kai hannun shi ya dafa kafadar shi ya ce " bro sake ta kar ta mutu " Da sauri ya janye hannun shi da ga wuyan ta , ya ja baya kadan kafin ya ce " nan gaba ki san irin amsar da za ki ba ni in na tambaye ki " ya na gama fadar haka ya juya ya bar wajen Bin bayan shi Moctar ya yi su ka bar wajen Su na barin wajen ta fadi kassa ta konta ta na sauke kuka mai cin rai Sai da ta share wajen good 30 minutes ta na kukan sannan ta mike a hankali ta na jan kafa ta nufi toilet din mata ta wanke face din ta sannan ta dawo ta dauki school bag din ta ta tafi class ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 3 ❤🔥 * After some hours Tafiya su ke saman titi a jere , Nesrine ta yi nisa cikin tunanin ta , ita kuma Inaya sai wassan nin ta ta ke kamar karamar yarinya Su na tsaka da tafiyar su wata mota fara kirar Mercedes ta tsaya a gaban su ta tare musu hanyar wuce Dum Nesrine ta ji gaban ta ya fadi dan ta san ko wanene Inaya kuma ta yi tsaye ta na kallon motar dan ita ba ta san ko su waye ba Su na tsaye a hakan su ka ga an bude kofofin gaban na motar Hafiz da Moctar su ka fito Gaban su ka zo su tsaye sannan Moctar ya ce " yan mata ku zo mu rage muku hanya mana " Dan murmushi Inaya ta yi sannan ta riko hannun Nesrine ta ce " mun gode amma mun iso gidan ai " ta kai karshen ta na rabawa ta geffen su za ta wuce Da sauri Moctar ya sha gaban su ya ce " haba yan mata taimako ne fa " " babu komai mun gode gidan mu fa cen karshen layin ne , ka ga kuma ba ni son Abban mu ya kan ki zai mana fada " Ba ta gama rufe bakin ta ba ta tsinci Muryar Hafiz ya na fadin " ke Nesi wuce cikin motar nan na kai ku gida " Wasu yawu Nesrine ta hadiye ta na tsoron ta shiga motar in malam ya gan ta zai yi mata fada, in kuma ta ki ta san halin Hafiz yanzu zai yi mata Dukan mutuwa kuma ba izinin ramawa, kawai sai ta tsaya ta na faman muzurai Ta yi nisa cikin tunanin ta sai tsintar Muryar Abdoul su ka yi ya na fadin " Nesrine me ku ke yi a nan ? " A razane ta juyo ta na kallon shi zuciya na duka uku uku Ya ko tsare da wadanan dara daren idanun shi " yaya Abdoul dama classmate din su Nesrine ne su ka ce wai su rage mana hanya shi ne na ce musu mun ma iso gida amma su ka ki yarda " Inaya ta fada babu ko tsoro " shikenan ba komai wuce ko tafi gida yanzu " Tun bai rufe bakin shi ba Nesrine ta kamo hannun Inaya ta raba ta geffen Moctar da sauri ta bar wajen Su na barin wajen Abdoul ya juyawar shi shi ma ya yi tafiyar shi su ka bar Hafiz da Moctar tsaye a wajen Bayan Abdoul ya bar wajen Moctar ya kali Hafiz da ke ta hura hanci ya ce " kai dan malam rage wannan fushin na ka, ga shi yanzu sun tafiyar su ba tare da mun ga gidan su ba " Dan tsaki Hafiz ya ja sannan ya juya ya fara takawa ya na fadin " ai mun hadu school " " kai malam kar ka manta ba college din ba mu ke , yawwan zuwan mu cen ya janyo mana matsala " Geffen driver Hafiz ya bude ya shiga Ya na ganin ya shiga motar shi ma ya bude geffen mai zaman banza ya shiga Bayan ya shiga Hafiz ya tada motar su ka bar wajen da mugun gudu Duk abun da ya faru a kan idon Zayd , dan ya na biye da su Inaya amma su ba su gan shi ba , ya na shirin ya je ya yi ma su Hafiz Dukan tsiya ya ga Abdoul ya shawo kwanar ya nufi su Inaya kawai sai ya yi tsayiwar shi sai da ya ga tafiyar su sannan ya juya ya kama hanyar komawa gidan shi Bangaran Inaya kuma , sai da su ka isa cikin gidan babu wanda ta ce da yar uwarta wani abu Sai da suka shiga cikin bedroom din su sannan Inaya ta kwace hannun ta da karfi ta dan ja baya ta na kallon Nesrine ta ce " wai me ya same ki Nesrine kin ga yadda saurayin cen ya yi miki tsawa kuma ki ka kassa ce mishi wani abu " Cire hijabin ta Nesrine ta yi ta ajiye saman sannan ta zauna geffen gadon ta dago kai ta kali Inaya ta ce " Inaya ke karama ce baza ki gane ba amma wlh ki raba hanya da samarin nan ko cikin school in ki ka gan su ki tsere ki buya dan wlh ba mutanan kirki ba ne " ta na gama fadar haka ta tashi ta fice da ga dakin Inaya dai ta na tsaye ta na kallon ta har ta ida maganar ta ta tashi ta bar dakin ba ta ce mata komai ba Nesrine kuma bayan ta fita kai tsaye toilet ta shiga Maimakon ta yi wanka sai ta jingina a jikin bangon toilet din ta aza kuka Cikin kukan nata ta ke fadin " ya Allah na roke ka raba ni da Hafiz , ya Allah ko ba ka raba ni da shi ba kar ka bari ya kusan ci yar uwata , ban San me na yi mishi a duniya ba ya ke neman ya cutar da ni , na shiga uku ni Nesrine , RAMATOU kin cuce ni kin hada ni da bala'i da na sani bazan taba yarda da abotar ki ba, Allah ya isa tsakani na da ke " Haka ta yi ta dimimuwan ta har ta gaji ta yi shiru sannan ta yi wanka ta fito ta koma bedroom din su Ta na shiga ta tarda Inaya har ta yi barci dan gajiya * Misalin karfe 5 na yamma * Inaya Zaune ta ke bakin kofar gidan su saman wasu duwatsu ta na faman wassa ita kadai kamar karamar yarinya Tun da ga nesa ya hango ta zaune ta cikin bakin glass din shi Ya na tare shi da Moussa, ya na sanye da wandon jeans baki da t-shirt dark blue , shi kuma Moussa jallabiya ce fara ya ke sanye da Lokacin da Moussa ya gan ta ya saki murmushi ya kali Zayd ya ce " Amir ga fa babyn ka cen ta na wassa " " ina ga yarinyar nan ta na da matsala a kwakwolwar ta gaskia " ya fada mishi cen kassa kassa ta yadda shi da Moussa kawai su ka ji abun da ya fada Jinjina mishi kai Moussa ya yi dan ya lura yanayin ta bai yi kama da masu cikakiyar lafya ba a shekarun ta Haka su ka ci gaba da tafiyar su har su ka karaso inda ta ke zaune su ka yi mata sallama A hankali ta dago kan ta, ta na amsa musu sallamar su kafin ta ce " ina wuni yaya Moussa " Dan murmushi Moussa ya yi kafin ya ce " lafya lau babyn malam , ko dai in ce babyn Zayd " Dan zaro idanu ta yi ta na kallon Moussa sannan ta kali Zayd da ya tsareta da ido Turo dan bakin nan nata ta yi gaba ta shagwabe fuska sannan ta ce " a'a ni babyn malam ce ni na ma tafiya ta wajen Abba " ta kai karshen ta na mikewa ta fara tafiya Da sauri Moussa ya ce " to tsaya mu raka ki mu ma cen za mu je " Da sauri Zayd ya kale shi dan ya lura Moussa na neman ya kwabo mishi ruwa Jinjina mishi kai kawai ta yi ta ci gaba da tafiyar ta Su kuma juya su ka bi bayan ta, ba yadda Zayd ya iya dole ya hakura ya bi bayan shi su ka tafi Tun da su ka kamo hanya ya ke kallon ta ta cikin glass Ita kuma sai wasu juye'juye ta ke ta na halba kafa ta na wassa yadda kassan me shekara biyar haka ta ke Shi kuma Zayd wannan abun da ta ke ya na yawwan tuno mishi da kanwar shi dan ita ma haka ta ke da rawan kai Kawai sai ya tsinci kan shi ya na jin wani bakon yanayi , cikin zuciyar shi ya ce " she is so cute and innocente why malam zai aura min ita da karancin shekarun ta haka , ya kamata na tambaye shi dalilin shi na yin hakan " Sai magana ya ke cikin zuciyar shi har su ka karaso sangayar Malam bai sani ba, sai da Moussa ya kai hannu ya taba shi ya na fadin " Amir ba ka ji ne malam na gaida ka ? " A dan razane ya juyo ya kali Moussa sannan ya meda kallon shi kan Malam da ke zaune saman tabbarma sanye da manyan kaya ga Inaya geffen shi ta rungume shi ta na murmushi Dan murmushi malam ya yi kafin ya ce " malam Zayd tunanin mi ka ke haka " Girgiza mishi kai kawai Zayd ya yi allamun ba komai sannan ya dawo da kallon shi kan Moussa ya mishi allamun su tafi Jinjina mishi kai ya yi sannan ya kali malam ya ce " malam za mu wuce sai mun dawo " Dan murmushi malam ya yi ya ce " shikenan Allah kiyaye hanya , Auta baza ki raka su ba " ya fada ya na medo da kallon shi kan Inaya da ke konce a jikin shi kamar baby Cikin shagwaba ta ce " Abba yanzu fa su ka rako ni , sannan kuma na sake rakiyar su , ni gaskia babu inda zan je " Malam na shirin magana ya ga Zayd ya kama hannun Moussa ya ja shi su ka bar wurin Ta na kallon su ta kassan ido har su ka bar wajen sannan ta mike da ga jikin malam ta ce " Abba , yaya Zayd sunnan shi ne hakan na gaskia ko " Jinjina mata kai malam ya yi ya na son ya ji abun da za ta cewa " to amma Abba me ya sa yaya Moussa ke kiran shi da Amir , Amir ai ya nufin yarima " ta fada ta na kallon malam Shi kuma malam juya kan shi ya yi ya kali su Zayd da su ka yi nisa cikin tafiyar su Ba tare da ya juyo ba ya ce " ni ma ban sani ba, halan sunnan da ya ke kiran shi ne da shi lokacin su na kanana kin San ba dole sai dan sarki ba a ke kira da Amir " Cikin ranshi kuma ya na tambayar kanshi shin wanene assalin Zayd din da su ka sani ( TOOOO ! MU MA DAI MU NA SON MIJI WAYE AINAHIN ZAYD DIN NAN 🙄 ) Haka ta zauna wajen malam ta na ta zuba mishi shagwaba shi kuma ya na biye mata sai da su ka ga magriba ta gaba to sannan su ka tashi su ka koma gida a tare , ta na rike da hannun shi ta na wassa da shi ( Ita dai wannan yarinyar da wuya ta zauna ba ta motsi 😑😑 ) Bayan sun koma gida , da kanta ta debo ma malam ruwa cikin buta ya yi Alwalla sannan ya tafi mosque Bayan ya fita ita ma debo ruwa ta yi Alwalla ta koma bedroom din su dan ta yi sallat Ta na shiga dakin ta tarda Nesrine ta na zaune saman dadduma ta daga hannayan ta sama ta na adu'a Dauko daddumar ta Inaya ta yi ta zo ta shinfida geffen Nesrine sannan ta tada sallar ta Ba su tashi da ga kan daddumar sai da su ka hada da sallar isha su ka yi a tare Bayan sun ida Nesrine ta mike ta nade daddumar ta ta mayar da ita wajen ta sannan ta fito da ga dakin Ta na fitowa ta ji sallamar Abdoul Dum ta ji gaban ta ya buga dan ta san da wuya ya kyale ta bai mata fada ba Kamar ko ta sani da sauri ta juya za ta koma dakin su ya kira sunan ta Wasu yawu ta hadiye a hankali ta juyo ta ce " na'am " Takowa ya yi ya zo gaban ta ya tsaya sannan ya ce " su waye samarin nan da na gan ku a tare " Sunkuyar da kai ta yi , Cikin in'ina ta ce " ni ma ban san su ba kawai sun tseda mu ne saman hanya wai mu je su rage mana hanya " Jinjina kan shi ya yi sannan ya ce " shikenan nan gaba kar ku sake tsaya wa ko sun muku magana ku kyale su " " to yaya Abdoul " ta fada ba tare da ta dago kai ba dan tsoron ta ke ji ya wanke ta da mari Shi kuma tsaya wa ya yi ya kare mata kallo da kyau ya ga yadda ta ke ta rawar jiki kamar ya ce zai dake ta Sai da ya dan jima a haka sannan ya juya ba tare da ya ce komai ba ya shiga bedroom din shi Ita kuma ta na jin ya fara takawa ta dago kai ta ga ya nufi dakin shi ta sauke ajiyar zuciya har da dafe saitin zuciyar ta ta na jan nunfashi a hankali Sai da ta nitsu da kyau sannan ta kama hanyar kitchen ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ (LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i BOOK 1 ……………………………📚✍✍ ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 4 ❤🔥 Da sallama a bakin ta ta shigo kitchen din, nan ta isko mama gaban murhu, har ta gaba girki Dan juyo wa mama ta yi ta kali Nesrine sannan ta ce " lafya idanun ki duk sun kumbura haka ? " Ta na shirin magana ta tsinci muryar Inaya ta na fadin " kuka ta yi shi ya sa su ka kunbura " A tare duk su ka jiyo su ka kale ta Ta na tsaye bakin kofar kitchen din ta na sanye da doguwar riga mara nauyi ta saka dan karamin hijab zuwa kirji Hararrar ta Nesrine ta yi kafin ta ce " tooo malama miye ruwan ki a ciki ? " Hannayan ta duka biyu Inaya ta sa ta rike kugun ta, ta ce " da ruwana , sai dai ki yi abun da za ki yi " ta kai karshen ta na murguna mata baki Da sauri Nesrine ta dauki wani plate ta juya za ta bugawa Inaya Da gudu Inaya ta juya ta bar kitchen din ta na kara Ita ma Nesrine bayan ta ta bi da gudu ta na fadin " yau sai na yi maganin ki mara kunya kawai " Inaya kuma ido a rufe ta yi da gudu za ta bar gidan Har ta kai bakin kofa ba ta sani ba, kawai sai ji ta yi ta bugi wani abu da karfi ta yi baya za ta fadi ta na sakin kara mai karfi, wanda ya sanya shi toshe kunnuwan shi da duka hannayan shi biyu Cak Nesrine ta tsaya ta na kallon su ta na zaro idanu Malam ne da Zayd su ka shigo gidan sai da su ka yi sallama amma Inaya ba ta ji su ba , har sai da ta bugi kirjin Zayd da karfi Shi kuma ya kassa taro ta dan ya na tsoron ya taro ta wani ya lura da hakan ya yi mishi wata magana da za ta bata mishi rai shi ya sa ya kyale ta ta fadi Inaya kuma ta na faduwa kan ta ya bugu dum ga kassa har sai kassar ta dan girgiza Da gudu Nesrine ta saki plate din hannun ta ta nufo ta da gudu ta na fadin " Inaya, Inaya , Inaya " kamar ta yi kuka Shi ma malam da ke tsaye geffen Zayd da gudu ya yi kan ta ya talabo ta ya na kiran sunan ta Ina ita ko jin su ba ta yi sai kuka ta ke kamar karamar yarinya Ganin yadda su ka bi su ka rude ya sa shi kauda kan shi gefe ya saki dan siririn tsaki A hankali ya fara takowa inda ta ke konce ta na kuka Dukowa ya yi gaban ta, ya sanya hannayan shi duka biyu ya dauke ta cak kamar baby ya mike tsaye sannan ya nufi tabbarma da ya gani a shinfide kussan dakin Abdoul Da sauri malam ya bi bayan shi , ita kuma Nesrine ta tsaya ta na kare mishi kallo cikin ran ta, ta na tunanin ya akayi ya san tabbarma ta na cen wajen , mutumin da ba shi gani Malam kuwa bai kawo komai a ran shi ba dan ya san akwaye makafi dayawa da su ke aiki kamar ma su idanu ba mamaki ya hadace inda su ke zama kullum shi ya sa ya nufi wajen kai tsaye ( HAKAN NA NUFIN MALAM YA SAN ZAYD BA KURMA BA NE AMMA BAI SAN SHI BA MAKAHO BA NE 🤔 ) Sai da ya karaso wajen tabbarma sannan ya kontar da ita a wajen ya koma gefe ya zauna , ita kuma har yanzu kuka ta ke kamar baby ba ta ma san an dauke ta ba Ya na kontar da ita malam ya karaso wajen ya zauna geffen ta ya talabo kan ta ya zaunar da ita ya rungume ta ya na fadin " ya isa haka auta daina na kukan nan haka kar ki janyo wa kan ki ciwo " A hankali ta fara rage sautin kukan ta ta na hadiyar zuciya Ta na a haka ta ji an tabo mata kafar ta Ta na konce a jikin malam din ta dago kan ta ta kale shi Ya na ganin ta dago kan ta ya kai hannayan shi biyu ya rike kunnuwan shi ya dan sunkuyar da kai allamun ya na bata hakuri Wata yar karamar dariya ta yi cikin kukan nata sai da dan dimple din ta na geffen dama ya banyana karan farko kenan da na gan shi kuma gashi ba karamin kyau ya na kara mata ba A hankali ya dago kan shi ya na kallon ta ta cikin glass din shi, abun har dariya ya so ya bashi yadda ta ke dariya ta na kuka lokaci guda " Shikenan auta ya wuce ko ? " malam ya fada ya na kai hannun shi ya goge mata hawayen ta Jinjina mishi kai ta kafin ta kai hannun ta bayan kanta ta ce " Abba wajen zafi ya ke min " ta kai karshen cikin shagwaba Dan murmushi malam ya yi kafin ya ce " babu komai auta na zai wuce tashi ki je daki, ki konta " Da to ta amsa mishi sannan ta fara kokarin mike wa da ga jikin shi Da sauri Nesrine da ke tsaye waje guda tun dazu ta na kallon su , ta karaso wajen ta kamo hannun Inaya ta taimaka mata ta mike tsaye su ka nufi cikin daki su Su na shiga cikin dakin Inaya ta Haye saman gadon ta yi rub da ciki ta na sauke nunfashi a hankali ta lumshe idanun ta Ita kuma Nesrine ta juya ta baro dakin ta tafi kitchen dan ta taimaka wa mama Ta na shiga malam ya kali Zayd ya ce " Zayd me ya sa ba ka taro ta ba, yanzu da ta ji ciwo fa, dama ta na da tabo a kan ta na dauka shi ne ya motsa yadda na ga ta na kukan nan " Kallon shi Zayd ya yi cikin sanyi murya ya ce " sorry uncle ban gan ta ba ne kai ma kai sani , amma wane tabo ne wannan ? " ya tambaya ya na son ya ji karin bayani Ya na shirin magana Abdoul ya fito da ga dakin shi ya na sanye da jallabiya brown mai dogayen hannu ya karaso geffen su ya zauna ya na yi musu sallama A tare su ka amsa sallamar ta shi amma ta kadai a ka ji , dan Zayd in ba kallon bakin shi ka yi ba baza ka gane ya amsa ba Sai da ya zauna sannan ya ce "malam, na ji wani ya yi kara, cikin gidan nan ne ? " Dan murmushi malam ya yi kafin ya ce " ba komai, auta ce ta dan fadi amma ba ta ji ciwo ba " Jinjina kan shi kawai Abdoul ya yi ba tare da ya ce komai Su na a haka Nesrine ta fito da ga kitchen ta na rike da plate ta shiga dakin su Ta na shiga mama ta fito da ga kitchen din ta na rike da tray madaidaici ta karaso wajen su malam ta yi musu sallama ta ajiye tray din gaban su , sannan ta koma kitchen ta dauko musu jug na ruwa da glass biyu ta ka ta ajiye musu sannan ta wuce dakin ta Ta na shiga dakin Abdoul ya bude musu tray din ya mika ma kowane spoon guda sannan ya ce musu bismillah Kamar yadda su ka saba haka wannan karan ma haka su ka ci Sai da su ka Kamala ba wanda ya ce ma wani ufan , sannan Abdul ya zuba mishi ruwa ya riko hannun shi ya daura cup din a sama godiya zayd ya yi mishi sannan ya kai cup din a baki Ya na tsaka da shan ruwan Inaya ta fito da ga dakin su ta na dafe kai da hannu guda ta na dan lumshe idanu kamar mai jin barci A tare duka su ka dago kai su na kallon ta ba wanda ya ce da ita komai Ta na tsaka da tafiyar ta ta ji wani mugun jiri ya debe ta ta yi fuuuuu baya ta tafi za ta fadi Da sauri Abdoul ya yi kokarin tashi dan ya taro ta amma sai dai mi ? Tun kafin ya mike ya

Chapter 3 of 9