Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 5
haifarwa ba, amma a lokacin da zai dauka kome ba kome ba, yana karatowa, amma wannan ku mishi amfani da shi. Tabbas akwai boyayyen al'amari a tare da shi da kuma muma alummar Nahara. Duk da akwai Lokuta maso tsawo dole ya kasance haka." "Kamar ya?" Mikewa nahira yayi ya nufi hanyar shi, Waziri ya bishi. "Kasan shi din an haife shi ne dan kafa tarihi! Kasan adadin mutanen da suke tsaye domin ganin bayan shi? Dan haka kowacce dakika ta rayuwarsu da shi suke kwana, mafi alkhairi ku dauke shi daga nahiyar nan domin zasu iya kashe shi a yanzu ma ai sun kashe shi kaɗan ya rage musu.. *Wannan littafin na kudi ne akan 500N* 500₦... Insha Allah' a tuntube wannan number 08130269641 Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah +22784506476 0142529598 Ramlat abdulrahman manga Union bank #Mai_Dambu *A Hausa historical ancient* 20/Nov/2023 #Mai_Dambu *......DASHEN ALLAH 🌳* Mai_Dambu... BABI NA TARA(9) *NAHMIFAK* _Collections_ ```Ina mata iyayen giji! NAHMIFAK collections tana muku albishir tare da tallata muku hajarta! Kayan mu sun kunshi Atamfa yar gaske! Laces Ubansu zuwan Lagos! Turaren zamani na wuta kana da Humra tare da Lafayyar yar Sudan, ba nan NAHMIFAK collections ya tsaya ba akwai Materials da kayan Gyara Aure na mata. Muna Garin Gombe za a iya tuntubar Number tarho din mu ta nan 08090744767 sai kun zo muna da sauki da rahusa! Kasuwa akai miki dole! Da abani labari Gara na bada``` Tabon ya yi fitar ban mamaki, domin duk cikin su na shi ne ya fito sak da sak. Dan haka Sarki Abbas yake da yakinin cewa jinin Hayatudeen Abdullahi Noye ne, tsawon kwanaki suna tafiya cikin Amincin Allah da bawayar shi har suka isa Masarautar Deehar. Kasancewar sun yi tafiyar akan lokaci sun isa cikin masarautar har zuwa fada ana fadanci, kafin su shiga fadar ne aka jiyo tsohuwar bishiyar cikin masarautar ta rangad'a gud'a, kafin kace me an fara busa algaita. Abin da ya girgiza mutanen fadar kenan, me haka yake nufi? Waye kuma kwankwaman tsohuwar bishiya ta amsa a matsayin Sarki? Koda yake ba mamaki Arshan ne. Dan haka kafin su shiga cikin fadar masu gajeran tunani sun yi tunanin ba mamaki ba zai tab'a yuwa ba. Sallama ne ya shigo da sauri ya zube yana mika gaisuwa, kafin ya ce musu. "Baki daga masarautar Rano ne har da shi kan shi Sarkin Rano" "A mishi iso" haka ya kuma fita can sai gasu tare da Abdullahi Noye, rike da hannun Sarkin Rano, sai kallon fadar yake yana mamaki dama akwai fadar da ta fi ta rano girma haka, a hankali ya juya idanun shi zuwa wata kujeran mulki an mata shimfidar alfarma. Kafin ya juya ga mutanen fadar yana kallon su. Mamaki ce dauke a fuskar su. "Kubrah!" Waziri ya kira sunan ta cikin mamaki, "Na'am Baba Waziri!" Ta furta a hankali. Nunawa sarki Abbas wurin zama suka yi, ya zauna yana kallon su a hankali. "Ku kaita cikin gidan mana," Waziri ya bada Umurnin haka, "Barka da hanya, shi ne baka turo sako ba." "Wani sako kuma? Ga abinda ya kawo ni. Abdullahi Hayatudeen Abdullahi Noye shi ya kawo ne, shekarun shi biyar kenan." "Ka saka mu a rud'ani!" Galadima ya fada a rude. "A'a ai ba abin rud'ani ba ne, shi din d'a ne ga Hayatudeen Abdullahi Noye." Sai da yaja numfashi kafin ya daura da cewa. "Alhamdulillahi, wannan shi ne cikin da aka yi tsammanin ya zube a'a bai zube ba, gashi nan." "Taya zamu yarda d'an shi ne bayan kowa yasan akwai yarima Arshan, wanda shima dan shi ne, wannan kuwa." Murmushi Sarki Abbas yayi sannan ya ce. "Galadima Yusuf kayi nazari da kyau, Abdullahi zo nan" ya yafito da hannu, a hankali ya kwabe mishi rigar jikin shi. "Akwai wani shaidar bayan wannan? Nasan ba iya shi hayatudeen Noye yake da ba, akwai alaka da gamayya kuma shima yana da shi" Shiru fadar ya yi, a hankali dattawan fadar suka fara nazarin toh me yasa ake boye Arshan? Kuma tabbas sauran Yaran hayatudeen Noye suna dauke da wannan tambarin. "Tabbas rayuwa ba yadda bata juyawa da D'an Adam,yanzu yaron nan sai da ya shafe shekaru biyu zuwa uku a jikin Uwar shi kenan? Hmm Allah ya raya. A gyara tsohon shashin su a kai shi." Mikewa Sarki Abbas yayi sannan ya ce musu. "Ni kam zan koma, domin abin da ya kawo ni kenan, na damka amanar yaron nan ga Waziri da Ya Musa. A karo na biyu" sannan yayi musu sallama zai tafi Abdullah ya rike hannun shi, idanun shi cike da kwalla. A hankali ya zame hannun shi ya dafa kafar shi yana faɗin. "Kar ka damu, zaka samu kulawa anan sosai" Gyada mishi kai ya yi hawaye na zuba mishi. Sannan ya tafi, shi kuma waziri ya kama hannun shi, suka shiga cikin gidan. Anan ya same Kubrah babu wanda yayi na'am da ita asalima kamar kan su a haɗe yake akan ta. Domin tunanin su, da goben su yana kan Arshan. "Ya haka baku tafi sashin ku ba?" Murmushi tayi, nan da nan ya umarci wasu bayi aka fara gyaran sashin su. Rike hannun Abdullah yayi ya shiga kowanni bangare da shi, kafin ya ya dire shi a sashin su, can yamma Ya Musa ya zo, yaga Abdullah. Cikin girmamawa ya dauke shi suka kara fita. Washi gari tun asuban farko ya bar gidan zuwa masallaci, koda aka idar da sallah an sha mamakin ganin shi ko ace waɗanda suka zo, wannan dabi'ar Hayatudeen Abdullahi Noye ne. Kaf masarautar shi yake fara isowa masallacin kafin ladan da liman su iso. Ana idar da sallah, ya jima zaune bai magana da kowa ba. Sai da rana ta fara d'agawa ya tashi ya fita, dattawan masarauta suka bishi da ido, tun yana haka ya fara bayyana wasu irin dabi'u, wannan idan ya kai shekaru ashirin toh wallahi baki daya zai bukaci mulkin ne. Shi kuwa daga nan hanyar gida ya nufa domin ya san Innar shi tana niman shi. Yana zuwa daidai tsohuwar bishiyar nan, yaga an shimfida mishi kilishi ga kayan karyawa har yana tiriri. "Karaso ranka ya dade! Wurin nan naka ne." Kallon mutumin ya yi, sannan ya isa wurin ya zauna, zuba mishi abinci mutumin yake cikin girmamawa. Har ya gama ya koma gefe, juyaws yayi yana kallon yadda mutanen wurin suke rayuwa, iya shi yake gani sai mutumin da yake tsaye a kan shi. "Kai Abdullah!" Galadima ya buga mishi tsawa, mikewa yayi jikin shi yana rawa. "Me kake yi a wurin?" "Kar ka kuma jin tsoron wani mahaluki sai Allah babu abin da zasu iya maka zauna kaci abincin ka" zama yayi ya cigaba da cin abincin shi. Lokacin da ya gama mutumin ya shafa kan shi yana faɗin. "Muna nan muna dakon ka" abin ya daure kan Galadima yadda yaga Abdullah yana murmushi, sannan ya wuce shi. Haka rayuwar ya cigaba da tafiya, bangaren Abdullah sai a hankali. Domin takai koda yaushe yana wurin tsohuwar bishiyar nan, a cikin irin wannan yanayin, wata rana suka dauke shi har tsawon kwanaki biyu. Hankalin Kubrah ya tashi koda ya dawo. Ta saka shi a gaba da fada. "Sadauki ka kyauta kenan? Ka tafi ka bi aljanu kasan abin da zaka janyo min ne? " Lumshe idanun shi yayi, tare da gyada mata kai. "Magana nace ka min ba shiru ba" ta fada a tsawace. "Kiyi hakuri, zai daina." Ya Musa ya fada, yana kallon shi. Wucewa dakin shi yayi, ya kwanta bai kuma fita ba. Washi gari Waziri ya dauke shi har wurin Sarkin yakin Deehar, akan a koya mishi yadda ake kare kai. Bayan ya kai shi, ya wuce fada. Ya samu kowa yana cike da shi. "Waziri mun ji ka ɗauki wancan Yaron ka kaiwa Sarkin Yaki Uzairu, meye nufin ka?" "Nufina ya zama jarumi kamar mahaifin shi, laifi ne idan nayi haka?" "Amma kasan akwai Arshan ko?" Garkuwa ya fada a fusace. "Toh shima ku fito da shi a basu horon tare" "Allah ya sauwaka ya yi horo da yaron da babu tabbacin jinin." Wani irin ƙara fadar yayi, tare da girgiza, kamar damar fadar zai fado ya rugurguzo kan su. "Ka iya da harshen ka." Waziri ya fada yana barin fadar, a hankali abin ya fara kokarin tab'a kimar su, domin a ganin su bai dace zakewar da Waziri da Ya Musa suke ba, dan haka wata safiyar Juma'a. Aka fito da Arshan. Shima fari ne kyakyawa, me zubin Fulanin asali kasancewar mahaifiyar shi bafulatana ce. Lokacin da yazo filin, kallon Abdullah yayi, ana take mishi baya har da lema sabida rana. Hannun Abdullah yana rike da wata karamar kari da baka, dan ya ce shi harbi yake son koya ba yaki da takobi ba. "Bilyaminu rufe mishi idanun shi. Ya gwada harbawa" Sarki Yaki Uzairu ta fadi haka, rufe mishi Idanu aka yi, ya juya ya sake Harbin idanun shi a rufe. Daidai kan allon haka ya sake harbin, babu abinda yake kara bawa Sarkin Yaki Uzairu tsoro sama da yadda yaron yake daukar kome kamar ana bude mishi ƙwaƙwalwar shi. "Barka da isowa Yarima Arshan, ga guri ka zauna" Cire Mayafin da aka rufe mishi, fuska yayi yana kallon Arshan da aka kira Yarima, shi kuwa kusan wurin da ranka shi dade. Jikin shi ne yayi sanyi ya sunkuyar da kan shi ƙasa. Ya ce. "Barka da isowa Yarima Arshan" "Wai kai ne Abdullahi?" Arshan ya tambaye shi yana mishi kallon kaskantacce. "Eh" ya fada kan shi a kasa. "Hmm! D'ago na ga kanka" Kasa d'ago kan shi yayi ai. Ko ba kome Arshan ya bashi shekaru uku, dan haka ya ki d'ago kan shi. Dariya suka saka shi da masu kula da shi. Haka suka gama tsulla iskancin babu wanda ya kula su, suna tafiya Ya Musa yazo daukar shi. Ya same mishi zaune. "Wani abu ya faru ne?" "A'a muje" ya fada suka nufi gidan, haka abubuwa marasa kyau da dadi suka fara faruwa, a gefen waziri so yake a tabbatar da Abdullah shi ma Yarima ne, Amma abin mamaki wallahi mutanen nan, suka ki suka kafe akan basu yarda shi din da ne ga Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye ba. Wannan abin ya kara dagula lissafin Waziri baki daya. Amma bai sare ba, dan baya son sarewa. .... A wurin koyar yaki, shi Yarima Arshan bai iya ko rike takobi ba, amma idan ya tafi wurin tsabar rashin mutunci. Haka zai ta takalar Abdullah da magana, ko kuma yayi ta sakawa ana mishi dariya. Duk yadda yaron yaso Daurewa sai ya kasa domin mulki a jikin shi take, basaraken asali baya jure cin zarafi. Dan haka ya dauki wata sanda wadda ake koya musu yaki da shi. Ya nufi wurin Yarima Arshan. Ya zabga mishi akan cinyar shi. "Wayyo Allah!" Ya fada yana yarfe hannu shi. Ya kuma tsulla mishi, ya fasa ihu yana kuka. Cikin fushi masu kula da shi, suka yo kan Abdullahi, ganin haka yasa shi ya sandar, ya ja zai gudu kamar wanda aka danne kafar shi ya tsaya cak, tare da rufe idanun shi. Hannun shi ya bude sandar ta koma cikin hannun shi. Ya ja kafar shi daya bata ya shafa layi yana me bude idanun shi da suka yi wani irin fari fat.... *Me dan kwakur yake nufi? 🤔🙄 Ikon Allah ba dai wani abu ya same shi ba zai yi fada da wadanda sun haife shi sau goma... Muje dai zuwa* #Mai_Dambu *A Hausa historical Ancient* For more information chat me:08130269651 *......DASHEN ALLAH 🌳* An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 5 of 5