Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 5
suka zube tare da kwasar gaisuwa. Kallon Juna suka yi sannan suka ce. "A bisa binciken da aka tura mu, toh zamu iya cewa Alhamdulillahi sannan gefe guda wasu Wuraren babu nasara, sai a wani ƙaramin gari ne da muke tsaya kafin mu isa masarautan kwantagora. Mun samu labarin Marigayi Sarki Hayatudeen ya tsaya a garin inda ya sayi wata baiwa suka wuce. Sannan muka shiga ga masarautar kwantagora inda muka samu wannan baiwa me suna Deli. Sai dai mun so dawowa da ita amma Sarkin kwantagora ya hana mu dawowa da ita inda ya ce mana. Ba zai bada ita ba, domin sai ta haihu ko kuma a turo wasu manyan da zasu tafi da ita gudun kar a halaka da abin ita da cikin ta" Shiru fadar ya dauka wato duk yadda aka so hana dauko wannan al'amarin sai da aka samu waɗanda suka binciko ta. Dayawan ransu yayi mugun B'aci dan haka suka boye domin kar su fitar ya zama matsala... *NAHMIFAK* _Collections_ ```Ina mata iyayen giji! NAHMIFAK collections tana muku albishir tare da tallata muku hajarta! Kayan mu sun kunshi Atamfa yar gaske! Laces Ubansu zuwan Lagos! Turaren zamani na wuta kana da Humra tare da Lafayyar yar Sudan, ba nan NAHMIFAK collections ya tsaya ba akwai Materials da kayan Gyara Aure na mata. Muna Garin Gombe za a iya tuntubar Number tarho din mu ta nan 08090744767 sai kun zo muna da sauki da rahusa! Kasuwa akai miki dole! Da abani labari Gara na bada``` *Ba a san maci tuwo ba sai miya ya kare* Taku har kullum #Mai_Dambu Saturday/November/2023 *Hausa Historical Ancient* *......DASHEN ALLAH 🌳* EXQUISITE WRITERS FORUM ```Ina mata iyayen giji! NAHMIFAK collections tana muku albishir tare da tallata muku hajarta! Kayan mu sun kunshi Atamfa yar gaske! Laces Ubansu zuwan Lagos! Turaren zamani na wuta kana da Humra tare da Lafayyar yar Sudan, ba nan NAHMIFAK collections ya tsaya ba akwai Materials da kayan Gyara Aure na mata. Muna Garin Gombe za a iya tuntubar Number tarho din mu ta nan 08090744767 sai kun zo muna da sauki da rahusa! Kasuwa akai miki dole! Da abani labari Gara na bada``` Mai_Dambu... BABI NA UKU (3) Ransu ya yi matukar b'aci amma sanin a kwai zagon kasa yasa baki daya babu wanda ya ce kala, sannan a ka shirya manyan dattawan Fadan Galadima da wasu mayaka kimanin dari biyu, suka nufi masarautar Kwantagora. Da yawan waɗanda suka nufi can kwantagora wasu zuciyar su biyu, domin sun tafi ne domin wata manufa nasu na kan su. Tafiya ce ta kwanaki da ba zasu wuce arba'in ba, ya kai su masarautar kwantagora. Cikin girmamawa a ka mashi jakadar Deehar kafin Mai Martaba ya musu iso akan bukatar su. Sun yi farin cikin jin haka. Sai da suka kwashe kwanaki kamar uku sannan a ka basu Zulai itace sad'akar sarki Hayatudeen. Suka nufi Deehar da ita. Lokacin da suka isa dare yayi dan haka suka yada zango a cikin harabar filin da yake cikin Masarautar tare da bai wa Zulai kariya na musamman. Cikin tsakiyar dare me ɗauke da al'amarin ban mamaki, wasu irin surutai marasa tushe da kan gado suka shiga tashi. Sosai aka fara samun iska me tafe da guguwa wanda sun san cewa aika ce daga wasun su, kuma duk wannan abin ana yin shi ne domin kar cikin Zulai ya kai labari, don haka aka shiga aiko da miyagun jifa. Irin wannan yana faruwa amma ba kasafai ba, sai idan an kusan Haihuwar Ɗa namiji a cikin masarautar don haka Galadima da Wanbai suka yi tsaye tare da kare Zulai wasu dakarun suna masu mamaye ilahirin masaukinta. Artabu ake har gari ya waye, sai da alfijir ya keto sannan waɗannan ababe suka sarara bayan sun fasa wata ƙara me ƙarfin gaske. Sannan suka tafi, ita kan Zulai tsoro yasa ta takurewa wuri guda. Har gari ya waye, sannan suka mata magana ta fito fuskar ta a kumbure domin bata rintsa idanunta ba daren jiya ba. Jagora suka mata har zuwa cikin fadar masarautar, aka gabatar da ita. "Ku kaita shashin gabar, a bata duk wani abin da take bukata" inji Waziri yana kallon ta. Kafin ya mai da hankalin shi kan sauran mutanen Fadar ya ce. "A saka idanu a kanta ita da abin cikin, domin bai zama dole su tsalleke yanayin gidan nan ba." Shigowar Sarkin gida da wasu abubuwan ya zube su a gaban jama'a, "Sarkin gida lafiya?" "Wannan sakon ya iske shi a turakar Marigayi Mai Martaba." Daukar takardan saman ya yi, ya mik'awa Maga takarda. Buɗe takardan ya yi cikin kulawa yaga tambarin masarautar Rano. Cike da mamaki yake kallon mutanen fadar, kenan mai Martaba kafin ya rasu yasan da za a nemi wannan sakon. _ASSALAMUN ALAIKUM_ *BAYAN DUBUN GAISUWA DA BAN GAJIYAR RANGADIN DA KAYI, ALHAMDULLAHI AJIYAR KA TAYI YAD'O DA YABAN YA ALLAH YASA KA ISO LAFIYA* SAKO DAGA SARKIN RANO Ajiyar zuciya kowa ya sauke suna kara jin wani irin tsana akan Marigayi Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye. "Ai sai a tafi Ranon ko a taho da ita, domin bata cikakken tsaro." Inji Chiroma. Kura musu idanun sarkin yaki ya yi, sannan ya ce musu. "Wannan matar itace Ya Musa yake tare da ita. Domin kuwa idan ba ita ba, toh akwai wani abu a ƙasa. Don haka ayi kokarin ganin a kawo ta, har da Ya Musan domin akwai wani abu." A hankali Zuciyoyin wasu ya kasu gida-gida domin kuwa basu zaci haka ba, dan haka aka shirya dakarun na musamman karkashin jagorancin Wazirin Deehar da Shamaki, suka nufi masarautan Rano. ** Tafiya kwanaki goma ya isar da su Rano, tare da samun tarb'a na musamman. Bayan sun huta, Waziri ya shigo da zancen rasuwar Mai Martaba sarki Hayatudeen Abdullahi Noye. Tabbas Sarki Abbas ya girgiza domin abokin shi ne tun Yarinta, dan haka ya yi kasa da kai sannan ya ce. "A kwai Yarinyar da ya gani anan tun zuwan shi kafin ya wuce rangadi, sunanta Kubra, Mahaifinta bayi ne da Sarkin Borno ya bamu su, lokacin auren mata ta Hadizah. Sune suka haifi Kubra suka mata takwara da mata ta. Yar ya gani ya amsa a matsayin sad'akar shi. Kuma ya yi wannan rangadin da ita." Jinjina kai Waziri ya yi sannan ya sauke ajiyar zuciya. Ya labarta mishi abin da yake faruwa. Shiru Sarki Abbas na Rano ya yi sannan ya ce. "Ya turo Ya Musa ko?" "Eh Ya Musa yana tare da su, sai dai nayi alƙawarin kare rayuwar ta da abin cikin " Jikin Waziri ne ya yi sanyi ya kalle Sarki Abbas. "Idan alkawari ne nayi maka rantsuwa da Allah zan bada rayuwata domin kare uwar da ɗan!" Sanin girman rantsuwa da Allah tare da girman Waziri ya mike tare da mishi iso cikin gidan, domin shi daya ya samu ganin Mai Martaba sarkin Rano. Shima din saboda a kwai kyakyawar alaka ce me karfi a tare da su. Lokacin da suka isa cikin gidan, ya saka a ka kira Fulani Hadizah, tana zuwa ta samu wuri ta zauna, sannan ta miks gaisuwa ga Wazirin Deehar. Kafin ya tattara nutsuwar ta ga Mijinta. Sai da ya yi shiru kafin ya ce mata. "Takwaran ki ce za a mai da ita Deehar" dake kirjinta tayi tana girgiza kai ta ce musu. "Deehar?" "Kwarai da gaske!" "Kubra tai kankanta da masarautar Deehar." Ta fada hawaye na zuba mata. Shi kan shi Sarki Abbas wallahi jikin shi ya mutu balle ita. "Kuyi hakuri, In sha Allah babu abin da zai faru da ita sai alkhairi" Zuwa yanzu waziri ya tsorata shi ma da son daukar Kubra. "Ba mu san me a ran ka ba, sannan ba zamu hanaka daukar ta ba. Sai dai a nimo Ya Musa." Haka kuwa aka tura Jakadiya, kiran shi. Yana shigowa ya zube akan gwiwar shi ya gaishe da Wazirin Deehar . "Ka kyauta ko! Ashe da wannan yanayin ka zab'i shiru ka sulale ka tafi, me yasa baka gaya min ba?" Waziri yake tuhumar Ya Musa. Idanun Ya Musa na zubda hawaye ya ce. "Ka gafarce ni, amma Amana daya ce ita ya bani akan Kwarkwarah Kubra. Taya zan rushe amanar da ya bani?" Ya fada yana share kwalla. Jikin waziri ya kara sanyi. Maganganun Magajiya ya dawo kan shi, ya kurawa Ya Musa idanu sannan ya ce mishi. "Amana daya ce! Kuma ya baka nima kuma na kara baka, sai dai dole a kaita su ganta sauran kuma ka yarda da Allah ka yarda da ni ba zan zalince ka ba. Itama kuma ba zan zalince ba" domin ya fahimci matukar ya saka zalamar son mulki jikokin shi ba zasu yi ba, Hakazalika idan ya juya ya ce sai yaga bayan abin da a haifa sai dai ya rasa ran shi. "Mai Martaba sarki Abbas, ina niman Alfarman saka baki su dawo Deehar babu abin da zai faru sai ikon Allah" Sun tsayar da maganar tafiya washi gari. Don haka Ya Musa ya musu iso har cikin gidan wurin iyayen Kubra, tabbas yaga mace inda ake kira mace dole Sarki Hayatudeen ya rud'e, duk da lullube take da babban mayafi, bai hana shi hango tsagwaran kyau da Allah ya zuba mata. Ya gaya musu rasuwar Mai Martaba sarki Hayatudeen, a firgice ta zuba mishi ido kafin ta sunkuyar da kai tana me fashewa da kuka, tabbas tayi rashi ita aka yiwa mutuwa, kuka take sosai me shiga jiki, shi kansa sai da ya fahimci irin kaunar da take yiwa Sarki Hayatudeen, ai dole taso shi kuma dole ta yi kukan mutuwar shi domin yasan kan mace, ya kuma san yadda zai bi da mace kome kankantarta ta fada kaunar shi mara iyaka. Haka ta kwana tana kuka, har kunya iyayen ta suke ji domin basu tab'a ganin haka daga gare ta ba, tana da kunya sosai domin ko cikin jikinta bata so su sani ba, sai dai rashin lafiya da walwla yasa dole suka d'ago ta, tare da kiran unguwar zoman masarautar ta duba ta. Washi gari Suka dauki hanyar Deehar, haka ba karamin al'amari ba ne a gare su, sannan an bata bayi goma mata masu kula da ita. Har suka isa masarautan, wanda suka mishi shigar almuru. Tun kafin su isa wurin Bishiyar kukan da Sarki Hayatudeen yake zama aka aji an fara bushe bushe da algaita da k'ak'aki, haka ya tabbatar da ilahirin masarautan sun fahimci wadancan mutanen boyen sun yi na'am da macen da aka kawo kenan. Dan haka suka wuce cikin Masarautan Deehar, babu b'ata lokaci aka nufi shashin Magajiya da ita, domin wannan tafiyar Waziri ce. Da kan shi ya mika ta da Yar shi. "Ga Kubra nan, nasan yadda zuciyar ki bata da tsatsa zaki kula da ita" wani kallo ta mishi sannan ta ce mishi. "Wallahi ba zan rike matar da Hayatudeen ya rab'e ta ba, domin kuwa ba zan iya cigaba da kallon idanun ta a matsayin matar da mijina ya kwanta da ita ba." "Ni..." "Baba ka tafi da ita kawai" haka ya fito da ita jikin shi a mace, ya nufi wurin Kilishi, wacce sai yanzu aka fahimci tana dauke da karamin ciki bayan rasuwar Sarki Hayatudeen. "Waziri ka tafi min da ita ba zan amshe ta ba, domin kuwa rab'ar mijina tayi, sannan abin da take dauke da shi, shi nima nake dauke da shi." Jinjina kai ya yi, sannan ya fice wurin Fulani Karama ya shiga da sama. "Kamar Muryar Waziri yaushe ka dawo daga Rano?" Wani matashin saurayi makaho ya tambaye shi yana rike da sandar shi. "Na ji kamshin Ya Musa" "Yarima Usmanu gani nan." Ya nufe shi yana kukan farin ciki. Juyawa yayi sannan ya ce mishi. "Ku uku ne?" Domin Allah ya mishi baiwar fahimtar mutane a wuri musamman suka haura biyu zuwa uku.... *NAHMIFAK* _Collections_ *Hausa Historical Ancient* #Mai_Dambu #wed/Nov/2022 *......DASHEN ALLAH 🌳* Mai_Dambu... *NAHMIFAK* _Collections_ ```Ina mata iyayen giji! NAHMIFAK collections tana muku albishir tare da tallata muku hajarta! Kayan mu sun kunshi Atamfa yar gaske! Laces Ubansu zuwan Lagos! Turaren zamani na wuta kana da Humra tare da Lafayyar yar Sudan, ba nan NAHMIFAK collections ya tsaya ba akwai Materials da kayan Gyara Aure na mata. Muna Garin Gombe za a iya tuntubar Number tarho din mu ta nan 08090744767 sai kun zo muna da sauki da rahusa! Kasuwa akai miki dole! Da abani labari Gara na bada``` BABI NA HUƊU (4) "Tabbas haka ne, mu uku ne tare da Sad'akar Mai Martaba " Waziri ya fadi haka, Shiru yayi yana kallon can gefe guda, sannan ya ce musu. "Me yasa kuka dawo da ita? Me yasa baku bar shi a can ya rayu lafiya lafiya ba? Kun manta inda muke ne? Bai zama dole ya kai labari ba. Dan haka Ya Musa hakki ne a kan na kare rayuwar shi." Kamar wadda aka watsa musu ruwa, suka yi shiru suna kallon shi. Fitowar Fulani Karama ta kalli Kubra da take tsaye. Sannan ta juya ga Waziri. "Baba Waziri lafiya?" "Ita ce sad'akar Marigayi shi ne nayi tunanin kawo ta kafin a gyara wancan wurin." Sake kallon Kubra tayi, yarinya ce karama ba babba ba, dan haka ta kalli Yarima Shehu. Kamar yasan tana kallon shi ya ce mata. "Ki daina kallona Ammah, ki kalli abin da yake gaban ki." Lumshe idanunta, ta yi sannan ta kwalawa baiwarta kira ta ce mata. "Shiga da ita d'akin da yake gefen turakata." "Toh uwar ɗakina" sannan tayiwa Kubra Jagora har dakin da yake shirye. "Allah ya saka da alkhairi, Kubra da abin cikinta, amana ce a gare mu don Allah." Mikewa tayi tana faɗin. "Abin kasuwa na mai ciniki ne, idan ta iya ta tsira. Idan ta fadi a rasa kowa ya huta." Jinjina kai Waziri ya yi sannan ya ce mata. "Na gode Fulani, fata na gari lamiri." Sannan suka fita, cak ta tsaya a bakin kofar shiga cikin bangaren ta. "Ammah lokaci ne yayi da zaki cika wasu mafarkan, domin masu iya magana sun ce ba ni in ba ka, shi ne tanka." Juyawa tayi ta zuba mishi idanu. "Mafarkina akan ku yake!" Ta fada a fusace. "Bikin Magaji bai hana na Magajiya, wannan fa so min tab'i ne." Ya fada yana me tafiya da sander shi har bangaren shi. Bin shi tayi tana kallon shi, tabbas akwai boyayyen al'amari a cikin kan d'an nata, sai dai kuma al'amarin yana bata tsoro. Ranar da Mai Martaba zai rasu da tafiyar shi da abin da ya faru sai da ya labarta mata. Tare da bata shawaran boye wasu abubuwan a ranta. Har ya kusan fita ya ce mata. "Kin zata haka kawai na ce miki ki amshi kiran da zai zo daga gare su Ammah? A ranar da Abba ya dawo naji ba na jin al'amarin d da yake fita a jikin shi idan ya kusanto ni. " Murmusa mata ya yi, sannan ya juya yana kallon inda take tsaye duk da baya gani kuwa. "Koda aka ce ya rasu naje dakin ni da sauran Yan uwana, amma ban ji haka daga gare su ba. Matar da suka gabatar a fada ban ji tana da nasaba da haka ba, murmusa mata yayi sannan ya ce mata. Mafarin ya iso dole ki tsaya a tsakiyar su, domin iftila'in da yake tafe ya wuce sanin me tunani. Ki taya Abba yaki." Juyawa yayi a hankali yana tafiya, yayin da yake lalube da sandar shi. Ta jima tsaye a wurin kafin ta wuce ta bawa Barirah umarnin ta kai mata abinci, har cikin dakin ta same ta. A takure kanta a sunkuye. "Gashi inji uwar gijiyata." Amsa tayi tana me cewa. "Na gode" sannan ta ajiye abincin tana kallon shi, juyawa Barirah tayi zata fita, Kubra ta ce mata. "Akwai mutanen da nazo da su, ba zan iya cin abincin suna can a waje ba." Shiru Barirah tayi sannan ta fita zuwa wurin Fulani karama ta gaya mata yadda suka yi. Kallon juna suka yi kafin ta ce mata. "Ki musu iso, zuwa dakin." Daga haka ta cigaba da gyara abin da take, abin ya bata mamaki domin dai nan iyakarta ce, kuma taya za ayi ta zo mata har da nuna ga yadda take so. ★‡★ Tsoma isga yayi me ɗauke da gashin saniya, ya watsa a jikin wuta. Kurawa wutar idanu yayi, kamar wadda aka wurgo shi ta shigo dakin. "Samu taya haka zai faru?" Watsa isgar ya yi cikin wuta, sannan ya kuma tsomawa cikin jinin da yake cikin kokon kan mutum ya watsa a wutar. "Kwantar da hankalin ka! Ai inda ba kasa nan ake gardaman kokuwa." Inji Samu, "Amma kasan mun yarda da kai? Kuma a tsawon shekarun nan mun alkawarin ba zaka tab'a barin ya hadu da wata mace." Mutumin ya fada yana kallon bokan, "Ƙaddara da rabo!" Ya furta yana kallon mutumin. "Idan har a kwai su toh babu abin da zamu iya, sai ma mu rasa yadda muke so, dan haka tunda an samu haka zamu yi kokarin da zai saka duniya ta girgiza." Tashi yayi sannan ya ce mishi. "Tabbas ina son mu ji sabon labarin nan da gobe da safe!" "Toh bari mu ga, amma dole sai an d'aga kafa domin ka'idar masarautar ku ce" Samu ya faɗa a hankali yana sauke numfashi. "Kwana uku na bada ayi duk uwar da za ayi, domin rashin mutunci biki ne, kowa ya yi maka ka rama masa." Gyada kai Samu ya yi, sannan ya ce masa. "Hmm rikicin duniya da me rai ake yin shi, don haka kwantar da hankalin ka zamu yi kome a hankali." Fita yayi abin shi, sannan ya bar boka Samu yana aikin tsubacce tsabuccen shi. ★‡★ Tunda suka isa masarautar, Magajiya ta samu labarin ai Waziri ya kai sad'akar Marigayi wurin Fulani karama, ranta ya tab'o. Shigowar Amintacciyar baiwar ta, Zuwaira ta zube a gaban ta, Zuwairah tasan sirrin gulma da munafunci. Gata ba ta cika magana ba, amma ta iya had'a husuma ta koma gefe tana dariya. Duk da Allah ya mata baiwar kyau da sura me kyau amma ya zama a banza, tsabar munafuncin ta. "Uwar dakina a kace min kina kirana." Shiru Magajiya tayi mata, kafin ta ce mata. "Kina da labarin sad'akar Marigayi a wurin Fulani karama ta ke?" Murmusa mata ta yi, sannan ta ce mata. "Hmm! Sandar dukar gurgu, yana kallo ake saro shi. Uwar dakina ai wannan ba sabon labari ne, domin dai Mahaifin ki ya dauki sad'akar Marigayi ya kaiwa wacce munafukar matar." "Tabdijam lallai saniyar da bata da Jela, Allah ke Kore mata kud'a." Magajiya ta fadi haka cikin jin haushi, a ce mahaifinka shi zai zama tsanin ruguza ka. Kamar Zuwairah ta san abin da Magajiya take tunani ta ce mata. "Ai wasu dangin al'ajabi ne, suna tare da kai suna maka yankar baya. Allah na tuba, ai tsuguno bata kare ba, an sai da kare an sayi mage. Yo wannan ai shi ne burmawa kai wuka." Sake cika tam Magajiya tayi tana kallon Zuwairah da take kara mata ingiza me kantu ruwa. Mikewa Magajiya tayi sannan ta sallame Zuwairah. Domin kara mata zafin kai take akan wanda yake cikin shi. Sai kai gwauro take tana kai mari, ta rasa meke mata dadi domin tana hango yadda mahaifin ta, ya ci amanar ta, a kan idanunta ya tafi ya dauko matar da suka haɗa miji da ita, sannan ya dauke ta, ya kai wa matar da suke asalin kishi kamar zata mutu. Domin ko ba a gaya maka ba, lokacin da sarki Hayatudeen Abdullahi Noye yake raye yafi nuna kaunar shi a kan Fulani karama, da Yaran ta. --- Sauran dakunan cikin gidan, sun ji labarin abin da ya faru. Sai abin ya zama kamar da ba'a da isgilanci, yadda aka fara sakewa bayin Magajiya magana marasa dad'i. Wannan ya kara fusata Magajiya, domin wannan ai cin mutuncin ta ne, dan haka ta saka aka kira mahaifin ta, shiru suka yi. "Baba me ka aikata haka? Kasan yadda ake zaman kishi a gidan nan, amma har zaka dauko wata sad'akar Marigayi, ka kaiwa Fulani karama ai sai a watsar da ita idan taso ta rayu ko ya mutu" "Ikon Allah, amma ke na fara kawowa Kubrah kika ce baki bukata ko? Toh ita da ba ni na haife ta baki ga ta amshe ta ba?" Kura mishi ido tayi, kwafa tayi sannan ta mike tana faɗin. "Umma, umma biyu, ta fi umma ɗaya. Kuma ina baka shawarar ka warware batun ajiye ta wurin Fulani karama." Murmusa mata ya yi, sannan ya ce mata. "Yau da gobe kayar Allah, komai gudun mutum ta kamo shi, dan haka babu gudu babu ja da baya a can zata zauna." "Baba har da kai, za a min zagon kasa?" Kwafa tai ta wuce dakin ta, kad'e babban rigar shi yayi ta wuce abin shi duk abin da tayi ita ta sani ba zai fasa kudirin shi ba. -- Kwana biyu a tsakanin, Kubrah ta koma sabon bangaren ta, inda aka zuba mata bayi da kunyangi, bayan waɗanda tazo da su, Ya Musa yana kan ta, ita da abin cikin duk wani abun da ake bukata yana tsaye. Kwanan ta uku da shigowa Masarautar. Da dare, tana barci sai wani irin take, mafarkin ga wasu kuraye sun taso ta, a guje sosai suke bin ta da gudu. Dakyar ta fada wani rami. ramin kuma ruwa ne a cikin shi, tana kokarin fitowa taji kamar an daki cikinta. Zafin dukar ya saka ta bude idanun ta a zahiri. Tana me share zufar da yake karyo mata, a tashi ta yi tana me nufar meke wayin ta, ta kama ruwa sannan ta fito, inuwar mutu ta gani, da sauri ta koma wuce gadon ta, ta kwanta. Dakyar barci ya yi gaba da ita. Cikin barcin ta fara jin ciwon ciki kamar zata mutu. Haka ta yi ta dungure. Har kusan asuba, asuba nayi ta samu barci me dadi ya dauke ta..har ta fara barcin, ta ji kamar tana fitsari a kwance. Dakyar ta mike sai dai ta kasa tafiya, kara ta kwala. ..... Fri/Nov/2022 #Mai_Dambu *A HAUSA HISTORICAL ANCIENT* *......DASHEN ALLAH 🌳* Mai_Dambu... ```NAHMIFAK* _Collections_ '''Ina mata iyayen giji! NAHMIFAK collections tana muku albishir tare da tallata muku hajarta! Kayan mu sun kunshi Atamfa yar gaske! Laces Ubansu zuwan Lagos! Turaren zamani na wuta kana da Humra tare da Lafayyar yar Sudan, ba nan NAHMIFAK collections ya tsaya ba akwai Materials da kayan Gyara Aure na mata. Muna Garin Gombe za a iya tuntubar Number tarho din mu ta nan 08090744767 sai kun zo muna da sauki da rahusa! Kasuwa akai miki dole! Da abani labari Gara na bada``` BABI NA SHIDA (6) Sunkuyar da kai ya yi, wannan wacce irin dama ce haka yarsu ta samu haka? Waye shi da zai ce baya buƙatar haka? Don haka ya yi kasa da kai ya ce musu. "Ai da kai da kaya duk mallakar wuya ce, duk abin da ya dace zaku iya yi wallahi ba ni da haufi" Gyara murya Sarki Hayatudeen ya yi sannan ya ce masa. "Ka nime izinin Yar da Mahaifayar." Yayi maganar da tausassawa. "In sha Allah, babu matsala a wurin mu" sannan ya tashi zai tafi , sarki Abbas ya ce mishi. "Dukiyar ta fa?" "A'a sai na nime izinin kamar yadda kuka ce" ya basu amsa, sannan ta tafi. Suna zaune da Inno, tana dokin kofa Inno tana cikin dakin tana kad'i, domin masakiya ce babba a cikin Masarautan Rano. Dakin ya shiga ya labartawa Inno abin da ya tawo da shi, da kuma dalilin kiran shi. "Malam ni ba alakar ce take ba ni tsoro ba, a'a kawai yadda masarautar Deehar zasu amshi yarinyar ce, duk da kasancewar masarautar Rano bata kai ta girma ba, amma ina jin tsoron kar wani abu ya shafi rayuwarta. Wallahi Allah daya kenan ban so ya kasance sad'akar sarki ba, domin zan so tayi aure ta samu yancin kamar kowacce mace. Amma Allah ya fimu sanin dalilin haka, Ubangiji ya sanya albarka da Alkhairi." Kawai bata da yadda ta iya ne, amma wallahi da ba zata tab'a yarda da irin wannan auren ba kuma shima Malam Audi ya gamsu da yadda ta nuna mishi illar haka. A can kuwa kasa zama Sarki Hayatudeen ya yi, ... "Wai kasan Allah duk abin da zaka yi sai dai kayi, tunda na baro barguna masarautar Deehar, ga wata bargon nasan zata lullube ni, har tsakar kaina domin makarin sanyi ne na hango." Girgiza kai Sarki Abbas na Rano yayi sannan ya ce mishi. "Wallahi ba zaka mai da ni, irin ka ba, kasan a cikin gidan ka akwai jikokin ka sa'aninta?" Komawa yayi

Chapter 2 of 5