da ƙamshi, da wayo. Na shagala... Na bar Amatu, wadda ta tsaya dani tsawon shekaru, wadda nake da tabbacin so ta gaskiya ce... saboda kissa.”
Hajiya ta runtse ido, tana kokarin shanye hawayenta.
Alhaji ya gyara zama cikin juyayi da takaici.
“Yanzu me kake so Nashwan ga abinda muke gayayama tun farko amman kaje kayi auren ka bada son mu ba wanan shine sakkayar iyayye ?”
Ya ɗago kai, yana kallon su da idanu cike da nadama.
“Bazan iya cigaba da zama da Azeeza ba. Na gwammace in ci mutunci na da gaskiya, in rabu da ita cikin kwanciyar hankali bana ƙi ta, amma bana iya daraja auren da aka gina bisa ƙarya.”
“Don haka... don Allah ku taimake ni. Ku raka ni Maiduguri zan nemi Amatu... idan har zata saurare ni wallahi... a duk duniya, babu wata mace da ta kai ta mutunci da amanar zuciya. Na gane, na girma... kuma yanzu na shirya.”
Hajiya ta share hawayenta da dankwali, ta ce da murya mai laushi:
“Nashwan... wauta ce tafi kowa da saurin komowa gida. Idan har kana da niyyar gyara, to nima ina tare da kai.”
Alhaji ya sauke numfashi mai nauyi, sannan ya ce:
“Sai ka nemi sadaki naka. Auren da ya rasa gaskiya, to ginshikinsa ya riga ya rushe. amma Nashwan... ka sani: Amatu ba ta sauƙi. Idan har ka je gareta, to ka tafi da zuciyar gaskiya, ba da launin da ka zo da shi ba farko.”
Ya gyada kai da hawaye — yana jin cewa rayuwarsa na da wata hanya ta sake farawa... amma sai ya dawo daga inda ya bar gaskiya.
MAIDUGURI
Garin ya lafa, rana na shirin fāɗuwa, iska tana busa sannu a hankali kamar tana fassara sabon shafi a rayuwar mutane.
Motar Nashwan da iyayensa ta tsaya kai tsaye dai-dai zauren gidan su Amatu. Gidansu ya yi kyau, shuke-shuke a gefen titi, ƙofar ba’a rufe ba—alamun karɓa zuciyar Nashwan tana tashi da sauri kamar agogon da ya kai minti na ƙarshe.
“Na dawo gida... first love never broken... Amatu zata gan ni, zata rungume ni, ta yafe min…” ya fito daga motar da sauri, kai tsaye cikin harabar gidan.
Yana shirin shiga, kwatsam...
Tana zaune a ƙasan zaure cikin wata shadda mai kyau, kanta a ƙasa, ta na wasa da zoben hannunta – kamar mai jiran magana mai daɗi. Fuskar ta faɗaɗe da kwanciyar hankali, har tana ɗan murmushi a gabanta kuma... wani saurayi ne.
Tsafta, fara’a, nutsuwa — Habibu. Hannunsa na daure da agogo mai ƙyalli, yana kallon Amatu da irin kallon da Nashwan ya taɓa yi mata shekaru uku da suka wuce... lokacin da bai san darajarta ba.
Zuciyar Nashwan ta tsaya. Jikinsa ya ɗauki zafi. Ido ya rufe da fari sai bugu! – zuciyarsa ta murɗa kamar an buɗe murhu.
“Wannan saurayin fa? Amatu tana wasa da zobe fa? Wannan fa murmushewar soyayya ce?!”
Da gudu ya karaso! ba wata magana, ba izini, ya chafko wuyar saurayin!
“Kai wanene?! waye kai da zaka zauna da ita?!”
Kowa ya yi turus.
Amatu ta miƙe da sauri, cikin firgici, da ramar da ba a saba gani ba:
“Nashwan??! wannan hauka ne! ka saki shi! me kake tunanin kake yi shine mijin da iyaye na suka zaɓa min ?!”
Habibu bai ce uffan ba – sai ya ɗan ƙwace hannunsa da natsuwa ya dafa wuyarsa, sannan ya ce da Nashwan da murmushi mai ƙayatarwa amma da kwarjini:
“Kishi ne da kake yi? Ko hauka ne da ya biyo kuskurenka?”
Nashwan ya tsaya—ido cike da hawayen da ba za su sauko ba fuskar Amatu ta tsananta, ta fuskance shi cikin murya mai ƙarfi da taushi a lokaci guda:
Nan ta zuba mai idanun cikin ido bugun numfashi su ya tsaya chakk na wasu mintuna “Na jira ka... shekaru. Amma kai ka je ka zaɓi wata ka ajiye ni kamar tsintacciya. Yanzu kuma ka dawo da idanu da rikici? Ka dawo da hannu, ba da so ba? Na yafe maka, Nashwan – amma ni fa yanzu na girma ne...”
“...Sabuwar soyayya da ba ta da gurguwar kafa irin ta farko.”
Hajiya da Alhaji sun iso daga baya, suka tsaya suna kallon abin da ke faruwa cikin alhini da kunya Alhaji ya furta da murya mai sanyi:
“Na ce maka, ba kowace ƙofa ake dawowa da sauƙi ba.”
Nashwan ya durƙusa — ba don wani ya hana shi ba, don zuciyarsa ta karye.
Zuciyar da ya bari a baranda, yanzu tana hannun wani mai tsaro da kulawa. Yana kallo ta faɗa cikin wani harabar da bai da izinin shigowa da wucewa.
Amatu ta gudu! Tana kuka kamar ruwan sama, ta shige gida hannunta na riƙe da kirjin ta. Zuciyarta tana bugawa da ƙarfi, soyayyar Nashwan ta sake dawowa – sabuwa, sabuwa fiye da yadda ta fara...
“Shin zai iya dawo da ni? ko kuwa wancan ta riga ta mallake sa?”
Kallon Nashwan da ya zo cikin kwarin guiwa da kukansa, da kishi da nadama... ya girgiza ta. Amma Habibu, wanda ya tsaya a kanta a lokacin da take cikin fanko da duhu – shi ne haskenta yanzu.
Sai ga Baban Amatu ya fito, ya tsaya yana kallon Hayaki da Nashwan da iyayensa. Kallon ɗan-da-ta da hanzari, yana fahimtar komai kafin a faɗa masa komai.
Habibu ya matso da ladabi, ya gaishe shi da salama da girmamawa.Baban Amatu ya buɗe ƙofa ya ce:
“Ku shigo maza ku shigo da ku da zuciyarku – wannan ba gidan sabani bane, gidan fahimta ne.”
Suka shigo daga nan aka basu ruwa, aka zauna. Nashwan yana durƙushe gaban su, kuka na fito daga idonsa kamar karamin yaro.
“Don Allah Baba... don Allah! na kuskure. na bari soyayya ta gaskiya don cutar zuciyata. Amma yanzu na gane – Amatu ce ‘yar aljannata don Allah a dawo min da ita!”
Baban Amatu ya ɗauki numfashi. Ya kalli Nashwan, ya kalli iyayensa, sannan ya juyar da idanunsa ga Habibu wanda ya zauna da tawali’u, amma fuskarsa cike da damuwa.
Sai ya ce “Nashwan, na ji kuma ka kawo ƙara tare da kuka. ka aiko da zuciyar ka da tausayi.”
> “Amma...”
ya kalli cikin gida, sai ya ce:
“Amatu ta fara mantuwa da kai tana shigowa daga duhu zuwa haske. Ta fara ƙaunar wani wanda ya tsaya da ita a lokacin da rayuwa ta mata nisa.”
Burinmu ba auren shi ba ne, burinmu farin cikin ta ne. Idan har har yanzu tana iya jure maka, to ka shawo kanta, ka dawo da ita. Amma ka sani – wannan karon fa, kai da kanka zaka neme ta, ka lalle ta, ka lallaba ta. Kuma ka girmama ta… idan kuwa ba haka ba, ka daina kawo kanka.”
“Amma... Idan har ka iya shawo kanta, da gaske ba da salo ba – na yarda. Ita ce zata zaɓa. Mu zamu kula, idan ta amince, zamu sasanta... a ɗaura auren ku.”
Shiru.
Nashwan ya saki wani kuka mai zurfi. Gaba ɗaya gidan ya shiru sai aka ji ƙarar ƙafa... Amatu ta fito daga ɗakin ta. Ido jajir, fuska cike da kwanciyar hankali.
Kallon Nashwan ta yi.
Ta kalli Habibu.
Sai ta ce:
“Na saurari kowa… Amma yanzu lokaci ne na sauraron zuciyata.”
NARNAH ƘANWAR SOJA ✍️✍️
https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC
💘 ZAƁIN ZUCIYA💔
THE HEART'S CHOICE
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA
PAGE 15 / 16
26 /7/2025
"When the heart chooses, even silence speaks..
🎂 BIRTHDAY DEDICATION – 26th July 🎂
“Rayuwar Amatu”
An sadaukar da wannan littafi ga marubuciya Sayeeda a ranar zagayowar ranar haihuwarta 26th July.
Littafin da ke ɗauke da rayuwa, ƙaddara, juriya da soyayya ta gaskiya — ya dace da zuciyar wacce ta rubuta shi:
Mai naci, mai hangen nesa, da zuciyar da ta ƙunshi ƙwazon mace ta musamman.
“Soyayya ta gaskiya kamar kyandir ce — tana iya rufta da rana, amma dumin ta yana nan har abada.”
Happy Birthday, Sayeeda!
Wannan littafi naki ne, kuma soyayyar kalamanki zata cigaba da rayuwa! ✨📚💝
GAISUWA
Ga ɗan uwa Najeeb Allah ya saka da dubbun alkaire ɗam gidan Mama Allah ya bar zumunci Nagode.( Ina chan ina bachi dare ƙarfe sha biyu na daren jita ashe yana ta wishing na birthday na Jazzakkalllahu kairan ).
GAISUWA
Zuwa ga mutanen Yobe Naji daɗin saƙon ku kuma Allah ya saka da alheri Rabbi ya bar zumunci Nagode
Kallon Nashwan ta yi.
Ta kalli Habibu.
Sai ta ce:
“Na saurari kowa… Amma yanzu lokaci ne na sauraron zuciyata.”
Miƙewa yayi daga inda yake durgushe ya zuba guiwar sa duka biyu a ƙasa ya dafa hannun sa akan yatsun ƙafan Amatu wanda yayi sillar sanya ta cikin shork ba kaɗan ba , idon sa ya ɗago sama nan sunaye four eye's da juna "
Don Allah Amatullah ke buɗe idon ke da kyau cikin nawa Wallahi inasonki , inasonki, inasonki,kicce zaɓin zuciya ta kice ganaganr jikin RUHI BIYU a guna kicce MADOBIN IDO NA Amattullah inasonki fiyyeda soyayyar Munir da Khadija ( MIJIN MAGE ) kisani na mallaka miki zuciya tace da amana na tabbatar bazaki rushe min amana ta ba don ki ɗin kin kasance HANYAR RUWA ne mai gudanar da dukkan tsaftattacen tamkar tsaftarr RAYUWAR UMMAH soyayyar ke gaskiya ne a dukkan nin hankali na da zuciya ta a koyaushe sonki ƙara zama yakiye tamkar FARASHIN SO yana hauhawa tamkar zuciyar maccen da takasance MAI CIKI CE , ke fittilar haske ce dake fittar da DUHU CIKIN HASKE kin gama mammaye zuciyarta tabbas bayan yafewa kaina wulakanta soyayyar ke da nayi baya ba ba'a sanina hakan ya faru ba ke yarda da zuciya ta da kallamai na , nine NASHWAN naki , kar koyar tunani akwai wata macce a duniyar nan da zatasa na manta da wanan kyakkyawar halitta da Allah ya bani tun fill azal ke Sarauniya tace sarautar ke ta zarci wata chan wai PRINCESS RAHILAT ina sonki sonda baxan iya haɗawa da AHLIN LAASHKAR BA shin kin san da cewa BAYAN WATA akwai wani haske da zai iya zarce KAƊANGAREN BAKIN TULU tabbas akwai zafi da raɗaɗin rashin mutuntukka dole zuciya tasha wahala a ƙaddarar RUHIN MARAICE Amman kisani cewa duk da cewa hawaye da tausayi kansa ace MASHIƘIYYA CE amman ta azabtar da zuciya ce bawai don zan barki ba lallai ke ta musamman ce kinye BIYAYYYA GA UWA da uba kin jira, kin jure wulakanta Amman kisani I LOVE U , FIRST LOVE NEVER DIE ,,,
EVEN IN SILENT EVEN IN DARK AND HURT I WILL STILL LOVE U , U ARE MY CHOICE PLEASE FORGET AND FOGIVE ME saboda darajar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ♥️
Shiru dukka sukaye tabbas soyayya gaskiya ce shi kansa Habibu sun kunyar da kansa yayi domin ganin asalin masoya suna sun junan su tamkar babo kowa a gun "duk son da zanwa Amatu nasan bazata so ne kamar Nashwan ba domin shine Zavin zuciya ta "kowa sai da ya tausaya mai ganin hawaye a idon cikakkakken namiji a durgushe,,
Mahaifin ta ne ya duƙar da kansa ƙasa yana jiran amsar Amatuu da tunanin kar ta zubar mai da mutunci sa idan har baya zaɓi Nashwan a karo na biyu ba tabbas basai me zaice musu ba ..
Hannu yasa ta share hawaye da yake zuba a idon ta ta ɗaura da cewa
“So yana da ƙarfi fiye da ɓacin rai. Ni na yafe maka Nashwan… kuma zuciyata ta kasa mantawa da kai. Zuciyata ce ta dawo ta gaya min cewa kaine ZAƁIN ZUCIYA ta don girman Allah ka riqi ne amana da gaskiya ta faɗa haka tana miƙa mai hannun ta biyu biyu cikin zama yasa hannun sa a hanun ta na miki Alƙawarin in Sha Allah bazan baki kunya ba ne naki ne har abada ....
Wannan kalma ta girgiza kowa a dakin.
Nashwan da Amatu sun sake sabawa da juna. Ya kawo lefen nadama da alkawura.
Ana gaban iyaye, Amatu ta saka masa zobe da murmushi cike da annuri kiran “Zuciyata ta dawo gida” ya mamaye gari.
Habibu ya yi murmushi mai cike da fahimta, ya ce:
“Idan wani zai sace zuciyar ki, to Allah ya zuba albarka. Ina fatan farin cikin ki har abada.” mahaifin Amatu, cikin tsantsar jin daɗi, ya ce da Habibu:
“Kaje kazo da iyayen ka na baka auren Safiya. Ita ce ta dace da mutuncin ka.”
A ƙarshe: Habibu ya auri Safiya, ƙanwar Amatu, cikin koshin lafiya da soyayya mai tsafta.
BANGON ƘARSHEN SHAFI
Farin Ciki da Tsarin Allah
“So na gaskiya baya mutuwa, sai dai a gwada shi da raɗaɗi. Idan ya jure to shi ne rayuwa.”
Zabin Zuciya
“Duk inda soyayya ta rayu, albarka na yawo.”
Yau ƙauyen Baggale ya cika da farin ciki, mutane daga nesa da kusa sun taru domin shaidar auren Amatu da Nashwan tare da auren Safiya da Habibu. Gida biyu, soyayya biyu, amma albarka guda ɗaya.
Kallon Amatu a dakin amarya sai ka rantse wata sarautar sama ce ta sauka. Fuskarta na sheƙi kamar safiyar Litinin mata suka zagaye ta suna ɗora mata kyakkyawar fure, idanunta cike da murmushin "na ƙarshe, na gaske."
Safiya kuma — mai sauƙin kai da nutsuwa — tayi kyau da dinkin Shadda milk white, tana murmushi da hankali kamar wacce aka shayar da madarar soyayya.
Hajiya maman Nashwan na kuka da dariya a lokaci guda, tana cewa:
“Na samu yarinya mai amana, mai kunya, mai haƙuri – kamar Amatu babu! Na gode Allah.”
A fagen biki, Nashwan ya durƙusa gaban Amatu yana mikar da zobensa:
“Na yi kuskure, amma soyayya ta gaskiya bata taba lalacewa. First love never dies – kuma ke ce nawa.” ta amsa da murmushin da ke cike da zuciya da kwanciyar rai:
“Zan zauna a zuciyar ka a matsayin wacce ka fara gani da idon soyayya.”
Habibu kuwa yana kallo Safiya kamar kyautar Allah da ya zo da ita daga sama. Ya ce da ita cikin sanyi:
“Kin maye gurbinta ba da haske ba… sai da annuri. Kuma zan girmama ki har abada.”
Amarya da angwaye biyu suka fito hannun juna motoci sun yanka hula, yara suna yawo da “kululun goro,” amarya tana raye-raye da zumudi.
TSOKACI NA
“Rayuwa na juyawa, ƙaddara na da kalar sa. Amma wanda aka rubuta a zuciyarka, ba zai bace ba.”
************
Bayan sun iso Kaduna, aka shigo da su gidan Amatu gidan da aka gina domin ita, gidan da soyayya zata zauna kamar alƙalami cikin ink.
Sashin nata kamar aljanna ce: tabarma mai launin shudi da zinariya, labulen satin milk white, furen roses a kowane kusurwa, da kyandiran romantic suna walƙiya da daddadan ƙamshi wani kiɗan light na soyayya yana kunne kamar ana busa saƙo ne daga zuciya zuwa zuciya.
Nashwan ya durƙusa a gaban Amatu, hannunsa ya dafe nata, idanunsa sun cika da hawaye masu zafi amma daɗi:
“Na ɗan rasa ki, na kusa rasa rayuwa amma Allah ya kawo ki mini har gida. Zuciyata ta daina bugawa a baya, yanzu ke ce kukan numfashina na kasa bayyana yadda nake jin ki – sai dai in ce: ki bar ni na mutu a cikin soyayyarki.” Amatu ta dafe kafadarsa, ta ce cikin sanyi: “ zuciyata ta yi wahala Nashwan. Ta sha hawaye da raɗaɗi. Amma duk da haka, zuciyata bata yarda da wani ba – sai kai.”
Suka rungume juna… kamar su guda ɗaya ne da aka raba da ƙarfin duniya.
Cikin dare aka shige sashin honeymoon, inda zuma ta haɗu da miya Nashwan ya ce:
“Na ƙaunace ki a duk yanayinki, Amatu. ki zama matar zuciyata, mai rabona da kwanciyar raina. Duk inda kika zauna, can ne gidana.” Ya sumbaci goshinta, ta rufe idanunta da murmushi. ta ce da shi cikin ɗari-ɗari:
“Ka rikeni da gaskiya, ka rungumeni da aminci. In har soyayya za ta rayu, sai da amana kuma kai na yarda da kai.”
sai kyandir ya kashe da kansa… wata ta rufe sararin sama… soyayya ta kulle kofa...
Ganin babo haske a ɗakin su da zan kawo muku rahoto nagaji da jira kawai na ajiye alƙalamin nawa a cikin labarin su na baza hijjabi na na kama hanyar Yola don naga tawa mahaifiyar Alhamdullah 💕
ALHAMDULLAH
ALHAMDULLAH
ALHAMDULLAH
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels