da ƙuncin da soyayyarsa ta jefa ni."
"Ko da ace na yi kuskure, ba zan cancanci wannan wulakanci ba."
"Wani lokaci nakan tambayi kaina, idan son shi laifi ne, to me yasa zuciyata ke dukan shi ba kowa ba?"
Tunda suka yi fadan nan, Amatu ta soma jin wani irin ƙorafi daga zuciyarta—na so da na zafi. Duk lokacin da ta ga Nashwan online, zuciyarta na harbawa, idonta na kallo cikin fatan cewa wataƙila zai turo saƙo ko ya kira, ya ce “Ina sonki, na tuba.”
Amma babu. Shiru.
Sai ta yanke shawarar cewa zata ja baya.
Soyayya ba wai azaba bace da za a cigaba da jurewa ba tare da kulawa ba. Ita ma tana da daraja.
A ranar Laraba, ta ga missed call nasa guda daya. Da niyyar komawa kira, sai ta tsaya. “Idan har ni kadai ke ƙoƙarin ceto wannan dangantaka... to ai ni ba itacen gicciyewa bace.”
Ta share kiran.
Ta tafi asibiti kamar kullum. Tayi murmushi da ma’aikata, ta yi aiki da gamsuwa. Amma duk da haka, a zuciyarta akwai rana mai yawan guguwa da ƙura—ƙuruciyar soyayya ke hura mata ƙonawa.
Layla ta lura.
Ta juyo ta ce mata da salo mai tausayawa:
“Amatu, kin fara zama kamar wacce ke cikin soyayya da namijin da ya manta da ita.”
Amatu ta yi murmushi, ya cika da hawaye.
“Ni dai Layla, soyayya ta kai ni ƙololuwa... amma rashin mutunci bazan jure ba. A zuciyata har yanzu ina sonsa—amma bazan bar kaina na ci gaba da wulakanci ba. Ni mace ce, mai daraja.”
Layla ta matso ta rungume ta.
“Kina da kyau, hankalinki kwarai da gaske. Idan soyayya zata ci ki—ki ci gaba da ja baya. Idan zai gane kuskurensa, zai dawo. Idan kuma ba haka ba... Allah zai baki wanda yafi shi daraja da kulawa.”
SHIN KUNA TUNANIN AMATULLULAH TAJA BAYA DAGA MASOYIN TA
WAI SOYAYYAR NISA HAKA YAKI DA AZABA
SHIN KUN TAƁA HAƊUWA DA MASOYI YANA WANI GARI KINA WANI GARI DISTANCE RELATIONSHIP YA ZAMA MATSALARKU
SHIN NASHWAN ME KE FARUWA DA ZUCIYAR SA AKAN AMATULLAH DUK DA CEWA YASO TA SOYAYYA MAI TSANANI
MUJEEE ZUWA BARE MUGA DA GASKE KO AMATU TAYI HANKALI ZATA JAH CLASS NATA INA TSORON KAR CLASS NIN DAI YA ZUBE
NARNAH ƘANWAR SOJA ✍️✍️✍️
Welcome to this journey... of love, of longing, of silence that speaks louder than words.
Let the novel begin... with a heartbeat. 💔💌
Love , Sad × Long-Distance × Hopeful * short story
Kwatsam, zuciya ta gama jurewa. Amatu ta kama wayarta da hannu mai rawar zuciya ta danna sunansa. Bayan ƙarar kira sau biyu, ya ɗaga.
“Hello…”
Muryarsa kamar ba daɗin ji. Ita kuwa ba ta tsaya gaisuwa ba, sai dai ƙorafi mai sa kwalla:
“Nashwan, me na maka ne har three weeks baka kira ni ba? Me nayi da zaka rika yin online amma ba zaka tambaye ni lafiyata ba? Ko zuciyata bata da daraja ne a gurinka?”
sai shiru ya biyo baya.
daga can Nashwan yace a sanyaye:
“Amatu... aikin nan da nake ciki ba sauki bane. Wallahi kullum ina yinta har dare. Amma gashi yanzu na tura miki dubu goma, don ki Hai napep zuwa asibiti
Sai transfer alert ya shigo. Gaskiya, ya turo.
Amatu ta lumshe ido, zuciyarta ba ta cikin kudin. Sai tace da wani yanayi mai cike da taushi da zafi:
“Ni ba kudi nake so ba Nashwan, ina so ka bani lokaci. Ko da minti goma ne kullum, ka tuna da ni. So na ba sabulun wanka bane da zaka manta idan ka fita.”
“Ni ina son ka Nashwan, fiye da karfina ma. Amma kamar ina soyayya da bango. Zuciyata na ƙonewa.” shi kuwa ya sake shiru. Sai yace:
“To... zan duba, zan gyara. Ki bani lokaci.”
Washegari
Da safe kamar kullum tana jiran kira ko sako, sai gashi ya kira. Da farko ta ɗauka farin ciki zai biyo, amma...
“Amatu, na baki minti biyar. Duk abinda kike da shi a ranki, ki fadi yanzu. Ina aiki ne.”
Zuciyarta tayi wani irin nauyi. Kamar ta furta:
“Ina son ka Nashwan… amma bazan iya soyayya da mutum da agogo ba.”
sai ta fara magana cikin kuka mai saukar hankali...
“Zuciyata Ba Takarda Bace”
Yana cewa “Amatu, na baki minti biyar. Duk abinda kike da shi a ranki, ki faɗi yanzu. Ina aiki ne.”
Amatu ta dafe kirjinta kamar zuciyarta na neman tsagewa. Amma ta ja numfashi, ta fara da nutsuwa:
“Nashwan, ka tuna lokacin da muke tare a makaranta? Kana bani lokaci fiye da abincin ka. Ka tuna da kalaman da kake faɗa min? Ina ƙaunar ka Nashwan, har yanzu. Amma yanzu kamar ni ce kadai nake tafiyar da soyayyar nan…”
“Kullum sai dai ni na kira, ni na yi rubutu. Ka shiga online, amma ko ‘Hi’ ba zaka turo ba. Wannan ba soyayya ba ce, Nashwan. Ni ma ina da zuciya. Bana son mu rabu… amma ina jin kamar ni kadai ce a cikin wannan dangantaka.” Shiru.
Can kuwa… ihun Nashwan ya buga a kunne kamar karar roka.
“To me kike so ne yanzu? Kina takura min ne fa, Amatu! Ko ina aiki ba zaki fahimta ba? Sai kace ni bawa ne naki?! Wai wannan ce soyayya? Ko fursuna kike son ni na zama??”
Wayar ta dauki tsawa kamar hayaki yana fita daga kunne.
Amatu ta kasa magana. Kamar rana ta ɓace daga duniyarta.
Daga nan sai “call ended”. Ya katse wayar.
ta sunkuyar da kanta, hawaye suka gangaro kamar ruwan damina.
“So na ba ya isar da ni gareka… amma kuma ka manta ni mutum ce.”
-
“Ni Ma Mutum Ce”
"Meye laifina?"
"Laifina kawai shine ina son shi?"
"Ni ma mutum ce, ba dutse ba. Macce ce mai rauni, da zuciya mai sauƙin kamuwa da so."
"Sai don na nuna mai so na, shi ne zai ce min minti biyar nake da su? Minti biyar! Kamar ina roƙon lokaci daga wani wanda ya mallaki numfashina yana jan min tsaki a waya ."
"Shin haka soyayya take? ko kuwa ni ce ban dace ba?"
"Yanzu sai na fuskanci cewa soyayya tana da laifi idan mace ce ta fara nuna gaskiya."
"Yana online, yana dariya da duniya. ni kuma ina nan ina fama da ƙuncin da soyayyarsa ta jefa ni."
"Ko da ace na yi kuskure, ba zan cancanci wannan wulakanci ba."
"Wani lokaci nakan tambayi kaina, idan son shi laifi ne, to me yasa zuciyata ke dukan shi ba kowa ba?"
Tunda suka yi fadan nan, Amatu ta soma jin wani irin ƙorafi daga zuciyarta—na so da na zafi. Duk lokacin da ta ga Nashwan online, zuciyarta na harbawa, idonta na kallo cikin fatan cewa wataƙila zai turo saƙo ko ya kira, ya ce “Ina sonki, na tuba.”
Amma babu. Shiru.
Sai ta yanke shawarar cewa zata ja baya.
Soyayya ba wai azaba bace da za a cigaba da jurewa ba tare da kulawa ba. Ita ma tana da daraja.
A ranar Laraba, ta ga missed call nasa guda daya. Da niyyar komawa kira, sai ta tsaya. “Idan har ni kadai ke ƙoƙarin ceto wannan dangantaka... to ai ni ba itacen gicciyewa bace.”
Ta share kiran.
Ta tafi asibiti kamar kullum. Tayi murmushi da ma’aikata, ta yi aiki da gamsuwa. Amma duk da haka, a zuciyarta akwai rana mai yawan guguwa da ƙura—ƙuruciyar soyayya ke hura mata ƙonawa.
Layla ta lura.
Ta juyo ta ce mata da salo mai tausayawa:
“Amatu, kin fara zama kamar wacce ke cikin soyayya da namijin da ya manta da ita.”
Amatu ta yi murmushi, ya cika da hawaye.
“Ni dai Layla, soyayya ta kai ni ƙololuwa... amma rashin mutunci bazan jure ba. A zuciyata har yanzu ina sonsa—amma bazan bar kaina na ci gaba da wulakanci ba. Ni mace ce, mai daraja.”
Layla ta matso ta rungume ta.
“Kina da kyau, hankalinki kwarai da gaske. Idan soyayya zata ci ki—ki ci gaba da ja baya. Idan zai gane kuskurensa, zai dawo. Idan kuma ba haka ba... Allah zai baki wanda yafi shi daraja da kulawa.”
SHIN KUNA TUNANIN AMATULLULAH TAJA BAYA DAGA MASOYIN TA
WAI SOYAYYAR NISA HAKA YAKI DA AZABA
SHIN KUN TAƁA HAƊUWA DA MASOYI YANA WANI GARI KINA WANI GARI DISTANCE RELATIONSHIP YA ZAMA MATSALARKU
SHIN NASHWAN ME KE FARUWA DA ZUCIYAR SA AKAN AMATULLAH DUK DA CEWA YASO TA SOYAYYA MAI TSANANI
MUJEEE ZUWA BARE MUGA DA GASKE KO AMATU TAYI HANKALI ZATA JAH CLASS NATA INA TSORON KAR CLASS NIN DAI YA ZUBE
NARNAH ƘANWAR SOJA ✍️✍️✍️https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC
https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC
💘 ZAƁIN ZUCIYA💔
THE HEART'S CHOICE
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA
🎉 Happy Birthday to Me
July Girl Special 🎂✨
Na sadaukar da wanan littafin wa karan kaina kasancewar sa a watan haihuwa ta July..
DIAMOND 💎 GLOW PEN'S TEAM
PAGE 11 / 12
24 /7/2025
"When the heart chooses, even silence speaks
Kamar da, rayuwa tana tafiya. Amatu ta koma aikinta da natsuwa, ta kara jin dadin zama da kanta. Duk da cewa ta ja baya da Nashwan, amma zuciyarta—ita bata fasa ji ba.
Sai dai kwatsam rana guda...
Ta buɗe WhatsApp, tana duba Status don kawar da gajiya. Sai wani hoto ya buɗo mata ido:
Nashwan da wata yarinya sun zauna a kusa da juna fuskar budurwar an rufe ta da emoji, amma jikin rubutun status ɗin:
“HAPPINESS IS LOADING...”
Gaba ɗaya jikin Amatu ya kakkarye.
Kamar fitar zuciyarta ke neman gaske numfashinta ya fara rikicewa.
wayar ta zame daga hannunta ta faɗi kasa da ƙarar da ta tada hankalin Mama a ɗakin ciki.
“Amatu! Lafiya ke? Subhanallah!”
Da sauri Mama ta karaso, ta tarar da ita kwance, shiru, ba motsi kamar wacce aka cire rai.
Mama ta zuba mata ruwa, tana kiran sunanta:
“Amatu! Diyar Mama! Ki tashi! ki daina tsorata ni!”
Amma ba amsa.
Sai zuciyar Mama ta fara bugawa da ƙarfi. Da sauri ta ɗauki wayarta ta kira Baba:
“Mallam ! Ka kira Mahir da Safiya su dawo yanzu! Amatu ta suma, na rasa me ke faruwa! muna buƙatar zuwa asibiti yanzu!”
A lokacin weekend ne, Mahir yana gida bai jima ba, sai aka ɗauke Amatu cikin mota, kai tsaye zuwa babban asibiti—Specialist Hospital Maiduguri
Zuciya da take jin so, tana jin daci.
Ta ja baya, amma zuciya ba kwalta bace da za a murɗa ba.
So ya sauya mata duniya, Nashwan ya bar mata ciwo maimakon kulawa.
Asibitin ya yi shiru da yamma. Amatu na kwance a gado, idanunta na kallon sama—ba komai a cikin su face yawu na hawaye.
Drip yana sauka da sannu... kwayar ruwa, kamar kwayar damuwa, tana ratsa jijiyoyin jikinta.
Mama na gefenta, tana karanta addu’a a hankali, tana share kwalla da saƙon zuciya mai nauyi.
“Ciwon zuciya da kake gani ba sai ta fashe ba...”
Amatu na cikin tunani, idanu sun cika da hawaye.
Da suka sallame ta, suka koma gida da dare, tana cikin shiru kamar macce bata da baki. Bayan wanka da sallah, ta zauna a kan katifarta ta buɗe wayarta.
Ta shafe fuskar wayar da yatsa kamar tana son share wani ɓacin ciki.
Ta goge number Nashwan ta share history.
ta share dukkan chats nasu.
Ta cire hoton sa da suka ɗauka tare.
Ta cire sunan sa daga zuciyarta… ko da hakan ya fi wuya.
Kukan da ta yi ba na banza bane, sai dai kukan soyayya da aka raina.
Ta dora hannu a kirji tana faɗin:
“Ni Amatu… na tafi da zuciyata. Na riga na yafe, amma bazan manta ba. Nashwan, kai ne zabin zuciyata, amma ka ruguza ta. So na gare ka ya zarce yanda zan iya fassara shi da baki. Har shekaru uku, ban taba kiran wani sunan da ka fi ba. Ka kasance abokina, masoyina, mafarkina… kuma yanzu, ka zame mini ciwo.”
Ta sauke numfashi, ta lumshe ido, tana cigaba da magana da karamin murya mai rauni:
“Duk abinda ka zagaye, Nashwan… wallahi ba zaka samu zuciyar da ta rike ka kamar tawa ba. Ba zaka sake samun wanda zai dinga jira ka cikin shiru da hakuri ba. Ni ce ragin da baka darajanta ba—Allah zai sakamin.”
“Ka raina amana. Wannan zalunci ne a soyayya amma ni zan tashi. Zuciyata ta mutu, amma zan haife sabuwa—ba don kai ba, don kaina ne.”
“Yau da Gobe”
Watanni shida...
Watanni shida tun ranar da ta share komai, ta watsar da zuciyar da ta gama fasa, ta dawo da kanta daga rikicin da so ya jefa ta.
Watanni shida da hawaye suka daina fita a ido, suka koma ɓoye a zuciya.
Sai dai so—so kam, yana nan. Kamar rubutun da ba zai goge ba, yana kwance a ɓangaren zuciyarta da ba kowa ke gani ba.
Amatu ta gama sadaukar da soyayyarta.
Sai dai abin mamaki, ko da sakon “Ina kwana” Nashwan bai sake turo ba.
Sai labari ya iso—labari mai nauyi.
Nashwan ya yi aure.
Ya auri wata. Wata daban. Wacce ba ita bace ta jira shi na shekaru uku.
Ta kalli labarin a shafin Instagram, fuskar su cike da farin ciki.
Amatu ta lumshe idanu.
ba kuka tayi ba... kawai ta yi shiru. Shiru mai nauyin lallaba zuciya.
Wanan rana kamar yadda aka saba, Baba ya ajiye ta daga aiki. Sunyi shiru suna kallon hanya har suka iso kofar gida.
Yana shirin tafiya kenan sai ya tsaya, ya kalleta da kulawa, yana da murmushi mai cike da tausayi amma da ƙuduri.
“Amatu, kin girma kin jure fiye da kima. Amma yanzu lokaci ne na sabuwar hanya. Duk mazan a duniya ba Nashwan ba ne. Kuma duniya ba zata tsaya ba. Ke mace ce mai daraja—kin cancanci samun miji nagari. Don haka... ki fito da wanda zuciyarki ke yarda da shi, kafin nan da wata uku. Ba dole sai yau ba, amma ki yarda da kanki, ki buɗe zuciyar ki ga dama. So bai ƙare ba—ya canza ne.”
Jan kunne ne, amma da tausayi.
Ta sauke kai, amma zuciyarta na tashi. Wata murya a cikin ta na cewa:
“Ina zan fara? shin akwai wani da zai ɗauki wannan zuciya da aka fasa, ya ƙawata ta?”
Sai dai lokaci—lokaci na iya warkar da kowace zuciya, har ta sake yin fari kamar sabuwa.
Wata rana... wata rana mai kyau, za ta kalli kanta a madubi ta ce:
“Na tsira. Kuma na dace.”
NARNAH ƘANWAR SOJA
https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC
💘 ZAƁIN ZUCIYA💔
THE HEART'S CHOICE
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA
🎉 Happy Birthday to Me
July Girl Special 🎂✨
Na sadaukar da wanan littafin wa karan kaina kasancewar sa a watan haihuwa ta July..
DIAMOND 💎 GLOW PEN'S TEAM
PAGE 13 / 14
25 /7/2025
"When the heart chooses, even silence speaks
Ta shiga ɗaki , zuciyarta na tsalle da rauni, zuciyarta na rawa da zafi ta zube kan gado kamar wacce aka cire wa rai kuka ya biyo baya kuka ba wai na ɓarna ba—na yanke ƙauna daga wanda ta so fiye da komai tana hawaye tana ce wa kanta:
“me nayi masa? so na ne laifi? menene nayi da bai ishe shi ba?” babu amsa kamar yadda kwanaki suka wuce babu dalilin cin amanar ta kamar yadda soyayya ta juya ba tare da gargaɗi ba.
Amma yau...
Amatu ta farka.
Ta fara jin wani sabon numfashi mai sanyi yana fito daga ɓangaren zuciyarta da ya daɗe da toshewa ta share hawayen ta, ta yi shiru.
sannan ta miƙe cikin kasala, ta ɗauro alwala, ta shimfiɗa dadduma, ta zauna gwiwa biyu ƙasa... da murya mai sanyi da firgici tace:
“Ya Allah, kai Ka fi sanin duk wani abu da zuciyata ke ɓoyewa. ka bani ƙarfin zuciya, Ka goge hawayena. Idan har akwai wanda yafi Nashwan alheri a rayuwata, ka kusanto min shi. Ka rabani da wanda bai cancanta da ni ba, ko ina ƙoƙarin ganin yana min ka bani soyayya da zata warkar da ni, ba wadda zata rusa ni ba...”
Sai ta lumshe ido...
Addu’a ta fara karɓar mata wuri, ta fara busar da ciwon da soyayya ta bar mata.
Zuciyarta ta ce “Ba zan rufe kaina daga soyayya ba zan jira wacce zata fito da ni daga wannan duhu. Amma ba zan sake jefa kaina ba, sai idan zuciyata ta amince, kuma addu’ata ta ce: ‘Amin.’”
*********NASHWAN**********
Gidan da aka ƙawata da kayan alatu, gado mai faɗi da labule masu sheƙi, amma Nashwan bai jin kwanciyar hankali.
A kwanaki talatin da auren sa da Azeeza, komai yana kamar mafarki mara tushe.
Tana da kyau — kwalliyarta na kama zuciyar ido, murya mai sanyi, motsinta na janyo hankali. Amma komai na waje ne, ba ta da ƙamshin hankali irin na Amatu.
zuciyarsa na cike da rudani duk lokacin da ya zauna, da zarar yayi shiru, sautin muryar Amatu ke dawo masa...
“Kai ne zabin zuciyata… amma ka ruguza ta.”
Ya shake kansa da tafin hannu kamar mai son korar sautin daga kai. Amma ba zai iya ba.
Azeeza, sabuwar amaryar sa, bata da sanin asalin namijin da ta aura. Ita dai ta fahimta wannan mutumin mai kuɗi ne, mai natsuwa, wanda ya zo da soyayya da buri. Ita kuma ta tafi da hoto—bata faɗa masa gaskiyar rayuwarta ba.
Har sai wata rana bayan wata guda, Nashwan ya dawo gida da wuri. Yana daga cikin dakin su, yana gyara laptop ɗinsa. Sai wayar Azeeza ta faɗi kasa ta buɗe ganin ba pincode ta shiga gallery kai tsaye hotuna suka bayyana.
Hotuna ne na Azeeza da wasu maza daban-daban — cikin wuri mai duhu, da tufafi na fallasa. Wasu hotunan suna dauke da bayani kamar:
"VIP Client 🖤 — Night to remember."
"Dubai night, ₦500k richer."
Nashwan ya zuba idanu hannunsa ya daina motsi zuciyarsa ta buga — kamar wacce ta ji bugun karshe ya kira sunanta da sauti mara daɗi:
“Azeeza…” tana fitowa da sauri, fuska cike da murmushi amma murmushin ya tsaya da taga fuskar Nashwan da gallery a budewa ya miƙa mata wayar “kamar ba ke ba ce a nan, ko? ko dai akwai wata 'yar uwarki da ta dace da ke sosai?”
Azeeza ta tsaya — shiru kamar dutse ba ta da amsa.
“Na tambaye ki saboda so na ke ki gaya min da baki ke gaya min, ke wacece?ni fa so nayi aure, ba na saya ba...” hawayen Azeeza ya fara sauka, amma Nashwan bai daga girma ba. “Kin yaudare ni Azeeza na nemi sabuwar rayuwa, amma na fada cikin hadari. Ke ‘yar bariki ce da kika san ni zan iya sauya rayuwarki — kin rufe gaskiya da kwalliya. amma komai ya kare yanzu.”
Zuciyarsa ta kulle ba sabo bane, ba laifi ne — kaddara ce ta bijiro da girmanta.
yana cikin shiru, hawaye bai sauko daga idonsa ba — sai tunani: "Amatu... da gaske na bar mace kamar ke, na zo na tara karyar duniya duk abinda macce ta mallaka kin mallake sa menene a cikin wayewa na ƴan matan yanzu da ya rufe min ido da barikanci na bar asalin tarbiyyar aure ?"
ya kama kansa da hannu biyu, ya dora a gwiwarsa, yana faɗin:
“Me nayi wa kaina? Amatu... yanzu na fahimta.”
"WAIWAYE"
Zuciya tana da nisa fiye da tunani. Idan ta ji ciwo, tana komawa baya — tana tono tarihin da aka binne da so da sakaci.
Nashwan na zaune a ɗakin falonsa, AC na busa sanyi, amma hawaye na zafi ke sauka daga idonsa. Ya makale cikin tunani — waiwaye sun fara mamaye zuciyarsa.
“Ta yaya hakan ya faru? ina na fara kuskure?”
ya lumshe ido... komai ya dawo daga farko.
Ranar Farko...
Wani taron kamfani ne na shekara-shekara, Corporate Gala a babban dakin taro na Oriental Hotel, Lagos. Nashwan ya halarta da wasu daga ofishinsu. Duk da ya zo da niyyar tafiya da wuri, wani ƙamshi ne ya ja hankalinsa.
Turaren Azeeza.
Mai ƙamshi kamar hadin jasmine da vanilla, mai sa zuciya rawar jiki ya waiwayo... sai idonsa ya sauka a kanta wata budurwa ce cikin rigar t shirt fara da wando baƙi sumarta a daure, kwalliyar ta ɗauke ido — ta haɗu!
Suna haɗa ido, ta saki murmushi. Murmushin da ya dora masa alaka kai tsaye da zuciyarsa. A lokacin, ya manta da Amatu, ya manta da soyayyar da ya jima yana tinkaho da ita.
Yayi kamar yana sane — amma zuciyarsa tayi yawo. Kissa da kissisina suka shiga daga wannan rana duk wani barikanci Azezza tayi mai anan taki ya fara tunanin yana duhu yanzu ya haɗu da macce da ta iya soyayya da faranta rai na masoyi
Ta fara “checking on you, handsome,” ta fara aiki da kalmomi masu lulluɓin so, ta zame mai saniya da murya mai lallashi.
kwana biyu... ya fara aika mata “sweet dreams.” kwana bakwai... ya fara kiranta da “my princess . my world. my future wife ”
har ya aike da zabin zuciyarsa gareta—ido rufe.
Yanzu...
Yanzu yana zaune shi kaɗai, Azeeza tana ɗakin gefe tana kuka da ban-haƙuri, amma shi hawaye ne ke zuba daga idonsa.
Yana tunani "Amatu ce ta tsaya tare da ni duk lokacin da na rasa kai na. Ita ce ta dinga hakuri, har lokacin da zuciyarta ta mutu tana riƙe da ni me ya sa ban gane darajarta ba har sai yanzu ta so Ni tsakanin ta da Allah kuma ittace ZAƁIN ZUCIYA ta ba kokkonta she is my first love soyayyar da muka gina da tsoron Allah da lamarin iyayyye da hanuna na rusa shi a sanadin Azezza shin me yafaru sani ba manta abada ƙauna ta ?"
Ya dafa kansa, yana jin nauyin gangancin da ya aikata. Fuskar Amatu na bayyana a gaban sa — tana dariya a lokacin da ya bata gift ɗin farko, tana kuka lokacin da ya ƙi amsarta, tana shiru lokacin da ya fara canjawa.
“Na cutar da ita na rasa ita.l na rasa kaina...”
ya faɗi ƙasa a guiwowinsa, yana ambato sunanta da murya mai rauni:
“Amatu...”
KOWACCE SOYAYYA AKWAI KALUBALE
A ASALIN LABARIN ZAƁIN ZUCIYA NASHWAN BAI TUBA BA HAR YANZU AMMAN YA ƘARA DAWOWA GUN AMATU YA BATA LABARIN RAYUWAR SA KUMA YAI MATA WASA DA HANKALI TA DOMIN YANA KIRAR TA YA TABBATAR MATA DA CEWA YANA SONTA HAR MA ZAI DAWO A BASHI AUREN TA DOMIN YA GANE KUSKURE SA .
A WANAN LOKACIN AMATULLAH TA MANTA DA CIWO NA BAYA DOMIN SOYAYYA BA ƘARYA BANE TA SAKI MAYAR DA HANKALI AKAN SA KWATSAM YA KIRA TA YACE IYAYEN SA SUNKAI SADAKIN WATA YARINYA DABAN BA ITA BA
ANAN TA TSUNDUMA IHU DA GUGUWA.
DOMIN TABBAS YA MUNAFURCHI TA YA KARYA MATA ZUCIYA YA DAWO HAR TA SANAR DA IYAYYEN TA SAI DAI YANZU GASHI YA DAWO DA CEWA ZAƁIN IYAYYE SA YA AURA DAGA NAN TA ZAGI SA A ZUCIYAR TA TABGAYYYAWA ALLAH KUMA TA GOGGE SA HAR ABADA YANZU NASHWAN YAYI AURE AMMAN AMATULLAH NA NAN TA KASA MANCEWA DA ABINDA NASHWAN YA MATA KUMA BATA SAMU WANDA ZUCIYAR TA TA AMINCE DASHI BA
DON HAKA MUNA MIKI ADDU'A ALLAH YA KAWO MIJI NAGARI ƳAR UWA KIMA ALLAH YA BAYYANA MIKI SARKIN KE ..
ZAN ƘARA SA LITTAFIN DA SALO NA
DON ANAN LABARIN TA YA ƘARE
INA FATAN KUN FAHIMTA
ALƘALAMIN NARNAH ƘANWAR SOJA ✍️ ✍️
https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC
💘 ZAƁIN ZUCIYA💔
THE HEART'S CHOICE
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA
PAGE 15 / 16
26 /7/2025
"When the heart chooses, even silence speaks..
🎂 BIRTHDAY DEDICATION – 26th July 🎂
“Rayuwar Amatu”
An sadaukar da wannan littafi ga marubuciya Sayeeda a ranar zagayowar ranar haihuwarta 26th July.
Littafin da ke ɗauke da rayuwa, ƙaddara, juriya da soyayya ta gaskiya — ya dace da zuciyar wacce ta rubuta shi:
Mai naci, mai hangen nesa, da zuciyar da ta ƙunshi ƙwazon mace ta musamman.
“Soyayya ta gaskiya kamar kyandir ce — tana iya rufta da rana, amma dumin ta yana nan har abada.”
Happy Birthday, Sayeeda!
Wannan littafi naki ne, kuma soyayyar kalamanki zata cigaba da rayuwa! ✨📚💝
GAISUWA
Ga ɗan uwa Najeeb Allah ya saka da dubbun alkaire ɗam gidan Mama Allah ya bar zumunci Nagode.( Ina chan ina bachi dare ƙarfe sha biyu na daren jita ashe yana ta wishing na birthday na Jazzakkalllahu kairan ).
GAISUWA
Zuwa ga mutanen Yobe Naji daɗin saƙon ku kuma Allah ya saka da alheri Rabbi ya bar zumunci Nagode
**************
Da safe da asuba ta kusa fita, Nashwan ya tashi daga bacci cikin jiri na nauyin damuwa bai iya runtsa da dare ba idanunsa sun kumbura — hawaye ne suka sha gajiya.
Ya yi wanka, ya sa kayan shiru masu kamun kai — ba kayan boss ba, kayan mutum mai tozarta zuciya ( lol )
Ya fito zuwa falon gidan iyayensa da sassafe, Hajiya maman sa na zaune da Alhaji suna shan shayi da suka gan shi, Hajiya ta ɗaga kai cikin mamaki.
“Kai Nashwan, lafiya da safe haka? me ya same ka?”
ya durƙusa gaban su — abu da bai taɓa yi ba.
“Don Allah... ku gafarce ni. Ku yafe min abin da nayi cikin duhun zuciya.” Alhaji da Hajiya suka zuba masa ido da damuwa, Alhaji yana girgiza kai “Nashwan, me kake nufi?”
Ya dafe kansa da hannuwa biyu, kamar wanda ke jin nauyin duniya a cikin kansa ya sauke numfashi, sannan ya fara bayani...
“Na aure mace ba tare da sanin cikakkiyar asalin ta ba. Azeeza ba wadda kuke zato ba ce ta yaudare ni da kyan fata,