Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 4
karewa daga sharrin hanya da mutane. “Allah ya tabbatar da alkhairi a yau, ya tsareki da alkawarin sa, Amatu,” Mama ta ce cikin muryar da ke cike da ƙauna da kulawa. Amatullah ta lumshe ido, ta amsa da "Amin Mama," sannan ta shige ƙofar gida cikin nutsuwa da sanyin safe mai daɗi, fuskarta a lullube da kwarjini na mace tagari. Ta tsaya bakin titi tana duba gefen hanya don samun abinda zai kaita hospital. Cikin sauri sai wata karamar napep mai kyalli ta tsaya gabanta, ɗan saurayin dake ciki ya leƙo da fara'a da sallama: “Assalamu Alaikum kyakkyawar halitta daga Ubangijin halitta amince ya tabbata a garinki.” Amatullah ta tsaya cak, zuciyarta na karanto sunan da bata ji ba tukuna, amma muryar da kunnenta ya tsinta ya janyo ta juya da hanzari. Ta sakar da dan guntun murmushi Habibu Saurayin da kullum baya gajiya da bin diddigin soyayyarta, kamar yaro da kuka yakan cusa kansa a cikin zuciyarta. Yana da shegen kawaici da zafin so, wanda ke jan hankali ko da a hankali take tafiya. “Lafiya dai Yaya Habibu?” ta ce cikin ladabi da kasaita, tana mai gyara jakar ta a kafada. “Lafiya kalau, nurse Amatu nace na kawo ki aiki yau, ko?” Ya ce yana ƙoƙarin bude kofar gefen napep ɗin cikin ladabi. Ta daga hannu cikin girmamawa amma da takama, “A’a Yaya Habibu, na gode wallahi. Ka daina wahalar da kanka, ni dai na saba zuwa da kaina.” Habibu ya dan sunkuyar da kai, ba tare da nuna damuwa ba, sai murmushi yayi da cewa: “Ai in har wahala ce ke kawo ganin fuskarki safe da safe, wallahi zan ɗauke ta a matsayin ni’ima ne daga sama.” Amatullah tayi dariya kadan, ta kauda kai cikin jin nauyi, sannan ta ce: “Nagode Yaya, Allah ya saka da alkhairi.” Sai ta juya cikin nutsuwa, ta nufi wata babbar motar haya da ta tsaya daga nesa. Habibu kuwa ya bita da kallo har sai da ya fice daga gani, yana kallon fuskarta kamar ana rubuta soyayya da alkalami a zuciyar sa. Tana cikin motar, fuskarta a window, tana kallon yadda iska ke jefa ganyen bishiyu cikin sanyi da natsuwa. A cikin zuciyarta, kalmomi ne ke yawo, kamar ana karanta su daga wani ɗan karamin littafi da ba kowa ke da damar budewa ba. "Ina ma ace Nashwan yana bani lokaci kamar yadda Yaya Habibu ke bani. Ina ma ace duk wata mace zata samu namiji daya damu da ita da zuciyarsa gaba ɗaya… to da kowacce mace daɗin rayuwa ne nata." Ta sauke ajiyar zuciya, sannan wayarta ta fara ringing. Ta zaro ta daga jakarta – Baba ne Sai ta dan lumshe ido kafin ta ɗaga ta kara a kunne. “Baba, barka da safe,” ta ce cikin natsuwa. “Kin fita ne kenan Amatu?” “Eh Baba, ina hanya yanzu.” “To Mama tace kana bachi , Zan dawo da wuri sai muyi magana.” “To ‘yata, Allah ya kiyaye hanya.” Ta katse wayar tana murmushi, zuciyarta na taune ƙaunar da iyayenta ke nuna mata – soyayyar da ke da tsafta da fatan alheri. Bayan ta isa asibiti, ta sauka a hankali, ta gyara veil dinta sannan ta nufi gaban babban ofishin su. Da zarar ta sa kafa a ciki, sautin murya da gaisuwa ya karade ofishin: “Happy birthday Amatu!” Kawayenta da abokan aikin ta suka taso suna rungumeta da murna da dariya. Ta ce da sanyi: “Oh my God! Kun tuna? Thank you so much everyone... Wallahi I didn’t expect it.” Daga nan sai su zauna tare da ƙawarta ta fi kusa da ita – Layla – wacce ko da yaushe tana tsaye mata kamar ‘yar uwa. Layla ta ce: “Wallahi yau sai mun saka miki wani abu, Amatu. Enough of this modest birthday every year!” Suka fara hira, cike da dariya da zolaya, kafin su nufi reception don karɓar jerin sunayen marasa lafiya da za su duba. “To Layla, yau ni da ke jan jini, ko?” Amatu ta ce tana gyara gloves ɗinta. “Eh mana, ko kina ta birthday, ai jinin mutane ba zai tsaya ba,” Layla ta amsa da dariya. Bayan an kammala duba marasa lafiya, Amatu ta miƙe da gajiya amma fuskarta na ɗauke da murmushi mai nutsuwa. Ta cire gloves ɗinta, ta wanke hannunta sannan ta ɗauki jakar ta a hankali, tana nufar ƙofar fita daga asibitin. Yayin da take tafiya, tana jin sauyin iska da hargitsin zuciya—saboda shi. Ta zaro wayarta domin kira. Sunanta biyu: “Nashwan”. Ta matsa kiran farko... ringing... babu ɗauka. Ta kara na biyu... "Missed call". Zuciyarta ta dan yi sanyi, kamar ruwa mai sanyi da aka jika makera. "Wai me yasa yake nesa da ni haka? na cancanci kulawa..." Bata gama tunani ba sai wayarta ta kara, Habibu ne—kamar kullum, girmansa a cikin zuciyarta bai wuce soyayya ba amma bai da gajiya da ƙoƙari. Sai kawai ta danna ɗaya cikin kiran goma da ya shigo a da. Muryarsa mai taushi ta karade kunnenta: “Assalamu Alaikum Amatu, ya aiki?” “Lafiya kalau yaya Habibu, sannu da kokari...” “Na dade ina kiran ki ne, ina so in gaida ki kafin ki koma gida.” “Ah, ai gani nan zan taho, Allah ya saka da alheri.” Ta kashe wayar tana jin tausayi. Habibu mutum ne mai hakuri da nuna kauna, sai dai zuciyarta bata nan gaba ɗaya a wurin sa. Tana son wani, amma wanda bata da tabbacin ya fi son ta. Da ƙarfe shida da rabi na yamma, lokacin rana na neman bacewa da iska mai sanyi tana hura gefen veil ɗinta, ta fito daga asibiti da takunta mai cike da natsuwa da ɗacin zuciya. Sai kawai ta hango Habibu a bakin titi, yana tsaye a gefen napep dinsa kamar yadda ya saba, idonsa cike da kulawa da kaunar da bai iya ɓoyewa. “Bismillah Amatu,” ya ce da ɗan murmushi. Ba tare da musu ba, ta shiga. Babu hayaniya a tsakanin su, sai sanyi da nutsuwa da ke bayyana daga kallon sa. Yana tuka napep ɗin da hankali kamar yana ɗauke da zoben zinariya a ciki. Ya kai ta har kofar gidansu, ya tsaya, ya ce: “Allah ya hutar da gajiyar ki, ki huta lafiya Amatu.” Ta kalli shi tana murmushi, da murmushin da ke tsakanin gaisuwa da alhini, sannan ta ce: “Na gode sosai, Allah ya saka da alheri, yaya Habibu.” Ta juya ta shige gida cikin nutsuwa, amma zuciyarta ba ta da kwanciya. Daya yana nuna ƙauna, ɗaya yana ɓacewa kamar hayaki cikin iska...... Amin uzuri don Allah na rashin posting da rashin time na buɗe group da reply a private message a chigaba da haƙuri in sha Allah komai zai dai dai ta na gode https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC 💘 ZAƁIN ZUCIYA💔 THE HEART'S CHOICE BY NARNAH ƘANWAR SOJA 🎉 Happy Birthday to Me July Girl Special 🎂✨ Na sadaukar da wanan littafin wa karan kaina kasancewar sa a watan haihuwa ta July.. Welcome to this journey... of love, of longing, of silence that speaks louder than words. Let the novel begin... with a heartbeat. 💔💌 Love , Sad × Long-Distance × Hopeful * short story DIAMOND 💎 GLOW PEN'S TEAM PAGE 5 & 6 best on true life story INTRODUCTION 16 /7/2025 "When the heart chooses, even silence speaks. Bayan sallar Ishaa, gidan ya lullube da natsuwa da sanyin dare. Safiya na gefen Mama suna gyara kwanon abincin da suka ci tuwon masara da miya kuɓewa mai ɗan yaji, wanda Amatu ke matuƙar so. Baba na zaune a jikin kujera yana duba littafin karatun sa, zuciyarsa cikin shiru, kamar yana nazarin wani abu. Sai kawai Amatu ta fito da ƙaramar jaka daga cikin daki, ta buɗe ta fito da zunzurutun kuɗi na Naira dubu hamsin, ta miƙa masa da girmamawa da murmushin ƙauna: “Baba, ga wannan. Dan Allah ka karɓa, nasan zaka yi amfani da shi da albarka.” Baba ya karɓa yana kallon kuɗin da ta miƙa, sai ya ɗan jinjina kai da murmushi. “Wannan duk name Amatu? Ina kika samo kuɗin nan haka kamar mai albarkar hatsi?” Amatu ta ɗan yi ƙasa da murya tana murmushi cikin jin kunya: “Nashwan ne Baba. Ya turo min a matsayin kyautar birthday. Kullum haka yake min, ba ya taɓa barin ranar ta wuce haka kawai.” Baba ya kalli Amatu sosai, kamar yana nazarin fuskarta da zuciyarta a lokaci guda, sai ya furta: “Ikon Allah. Shi Nashwan kam baya gajiya. Kuɗin da ya aiko miki da su, wallahi shine albashi na gaba ɗaya a wata. Na yaba da irin karamcin sa. Amma…” ya tsaya yana jinjina kai sannan ya ce da tsantsar tausayi da damuwa: “Sai dai me, ke Amatu... sai yaushe zai turo kansa? Ina jin tsoron kada wannan juyin zuciya ya zame miki juyin rayuwa. Idan har yana sonki da gaske, me zai hana ya taho ya gabatar da kansa? Ya zo ya gaishe mu, mu san iyayensa, su san mu? Ni nake fatan hakan... ba wai zuba ido muna jiran sakon waya da alert ba.” Amatu ta yi shiru, zuciyarta cike da ruɗani. Tana son Nashwan fiye da kowa, amma tambayar Baba tana da nauyi har yanzu, Nashwan bai taɓa fitowa fili da maganar aure ba ya cika da kyaututtuka da kulawa, amma shiru kan abinda take mafarki da fata... Baba ya ƙarasa da faɗar cikin murya mai sanyi: “Na fi son yazo ya ce min da bakinsa, ‘Baba na zo neman Amatullah, ku bani dama’ — haka kawai zuciyata zata huta da murmushi.” Amatu ta ɗan sunkuyar da kai, tana wasa da yatsun hannunta, zuciyarta na faɗin: “Ya Allah ka shiryar da Nashwan ya gane muhimmancin hakan...” Ta koma ɗaki, lokaci ya kusa da ƙarfe goma na dare. Tana cikin shirin kwanciya, rigar bacci jikinta, fuska a gajiye amma zuciya na yawan tunani. Wayarta ta yi tsit, sai kawai ta hango missed call ɗin Nashwan har sau biyu. Ta ɗan jiyo numfashinta cikin damuwa, tana mamakin dalilin kiransa a wannan lokaci. “Ina ma ba za’a gama da kiraye-kirayen dare ba...” Ta furta a hankali, sai kawai wayar ta ƙara ringing. Da kyar ta ɗaga, muryarta cike da gajiya da sha’awar bacci: “Hello…” agefe guda, muryar Nashwan ta karade kunne da sanyi da nutsuwa, kamar mai ɗauke da busar sarewa mai sanyi da tsantsar natsuwa. “My Amatu, kin tashi lafiya? Na gaji da rana, wallahi sai yanzu nake samun kansa.” Amatu ta lumshe ido, murya a sakakke: “Lafiya lau, na ga missed call naka. Nayi zaton ka manta dani ne…” ya ɗan murmura, muryarsa na ɗauke da raɗa: “Kamar ya manta dake? Ai ke ce zuciyata. Kawai ne nayi busy sosai yau, kin san aikin nan... amma a duk inda nake, wallahi ke na ke tunani.” Sukayi hirar da bata fi minti biyar ba, amma kamar zasu baje da soyayya. Sai Amatu ta nutsu ta faɗa masa: “Baba ya karɓi kuɗin da ka turo, kuma ya ji daɗi sosai. Yace duk da farin ciki da jin dadin karamcin ka, yana tambaya sai yaushe zaka gabatar da kanka.” Shiru ya biyo bayan kalmarta na ƴan dakiku. Sai daga baya Nashwan ya sauke ajiyar zuciya sannan ya furta da gaskiya: “Soyayya ta da ke ba wasa ba ce, Amatu. Wallahi da gaske nake. Amma akwai abubuwa da nake gyarawa yanzu, sai dai insha Allahu—nan da shekara mai zuwa, zan turo iyayena. Zan zo da kaina, mu gama magana cikin mutunci.” Zuciyar Amatu ta cika da farin ciki da fargaba a lokaci guda. Shekara guda? Haka za ta jira? Amma a lokaci guda, ta ji kwanciyar hankali da yadda ya furta kalmomin, ba da wasar magana ba, ba da ɗoki na banza ba. Da karamin murmushi ta ce: “Na yarda. Na karɓa. In Allah ya yarda, zan jira har sai lokacin nan.” Nashwan ya ce da ƙayatarwa: “Kuma har lokacin nan, soyayyata ba zata gushe ba. Na fi ƙaunar ki fiye da na kaina, Amatu.” ta saki ajiyar zuciya, murya a raɗa: “Ni ma ina son ka Nashwan... fiye da yanda zan iya faɗi.” Wayar ta kashe ne da salati da addu’a daga gare shi. Ta zuba wayar a gefe, ta lumshe ido da murmushi a fuska. Zuciyarta ta nitsar da wani irin sanyi — sanyi mai ɗauke da fata, ƙauna da alkawarin gobe... Washegari... Tun karfe bakwai da rabi Amatullah ta tashi, jikinta na da sauƙi, zuciyarta cike da kwanciyar hankali da farin ciki na soyayya. Tana gab da isa bakin titi sai Habibu ya zo kamar yadda ya saba da napep nasa. Ta shiga ba tare da wata damuwa ba, amma a zuciyarta tana jin sanyi... Nashwan dai ya saka haske a rayuwarta. Da suka isa asibiti, ta faɗa Layla rai a ɗumɗum. Bayan sun gama shiryawa a office, suna cikin sassanyar rana, suka zauna a gefen taga suna ɗan hutawa kafin fara aikin rana. Layla ta lura da murmushin Amatu, da wata annuri a fuskarta da ba kasafai ake gani ba. “A’ah ke dai yau kamar an baki labari mai daɗi. Me ke faruwa ne da wannan murmushin sirri?” Layla ta tambaya tana ƙara matsowa kusa da ita. Amatu ta lumshe ido tana ɗan kallon taga, sai ta juya da ɗan shafa sumar kanta tace: “Layla... Nashwan zai turo iyayensa — amma ba yanzu ba, sai shekara mai zuwa.” Layla ta zaro ido, ta rike hannunta cike da sha’awa da farin ciki: “Shekara mai zuwa?! Subhanallah, ke wallahi wannan albishir ne! me kika ce masa?” “Na ce zan jira shi duk da lokacin yana da nisa, amma kalmarsa ta daɗe da natsuwar sa sun saka na yarda. Soyayyarsa ta fi ni’imtar zuciyata.” Layla ta fashe da dariya tana girgiza kai: “Ke dai kina cikin naki duniya Amatu, Allah ya tabbatar da alkhairi. Wallahi Nashwan yana da kirki. Amma dan Allah... wato bazai yi tun da wuri ba kenan?” Amatu ta nisa “Yace yana gyara wasu abubuwa ne. Na fahimta kuma na yarda. Na fi son abu ya zo da tsari da cikar mutunci fiye da sauri ba tare da shiri ba.” Layla ta jinjina kai, tana murmushi: “Toh ai Allah ya sanya alkhairi. Amma sai ki shirya kyau-kyau da addu’a. Zaman jira yana buƙatar haƙuri da jajircewa.” “Na shirya,” Amatu ta amsa a hankali, “In har zan samu Nashwan a ƙarshen jirana — to na yarda da komai.” Suka ci gaba da hira cikin nutsuwa da kwanciyar rai. Soyayya ta gaske ke kera zuciyar Amatu, tana girgiza tunaninta da fatan gobe. Kuma da ƙawarta Layla a gefenta, sai ta ji kamar rayuwar ta na gyarowa cikin salo mai tsafta da albarka... SHIN WANAN JIRAR NA AMATULLAH ZAI HAIFAR DA ƊA MAI IDO SHIN NASHWAN ZAI CIKA ALƘAWARIN SA. LALLAI NASHWAN SHINE ZAƁIN ZUCIYA AMATULLAH MUCEE GABA DA KASANTUWA ANA MIN UZURI DA RASHIN ISASSHEN POSTING A KOYAUSHE FATAN ALHERI 🥳🎊 https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC 💘 ZAƁIN ZUCIYA💔 THE HEART'S CHOICE BY NARNAH ƘANWAR SOJA 🎉 Happy Birthday to Me July Girl Special 🎂✨ Na sadaukar da wanan littafin wa karan kaina kasancewar sa a watan haihuwa ta July.. Welcome to this journey... of love, of longing, of silence that speaks louder than words. Let the novel begin... with a heartbeat. 💔💌 Love , Sad × Long-Distance × Hopeful * short story DIAMOND 💎 GLOW PEN'S TEAM PAGE 7 & 8 best on true life story INTRODUCTION 19 /7/2025 "When the heart chooses, even silence speaks WAYE NASHWAN? Nashwan Ahmad saurayi ne mai kamala da nagarta. Kyakkyawan hali da sauƙin kai sun zame masa tufafi, zuciyarsa cike take da girmamawa da kula da wanda yake so. Tunanin sa mai zurfi ne, ba mai yawan magana bane amma idan ya furta kalma, zata dumi zuciyar mai sauraro. Asalin sa daga jihar Kaduna, amma rayuwar sa ta kai shi ko’ina. A lokacin da Amatu ke secondary school, shine ya zo National Youth Service (NYSC) a makarantar su. Zuciyoyinsu sun haɗu a wancan lokacin — soyayya mai tsafta, mai nasaba da kulawa da mutunci ta kulla tsakaninsu. Daga wancan rana har yau — shekaru uku kenan — soyayyar nan na raye cikin nutsuwa da girmamawa. Ba su cika haɗuwa da juna ba, amma kowacce tattaunawa tana da ma'ana. Yanzu Nashwan na da shekaru 30, yana aiki da wata Company mai zaman kanta dake Kaduna, kuma albashinsa na wata-wata na kai kimanin Naira dubu dari biyu (₦200,000). Duk da karancin ganawa da Amatu, Nashwan baya daina tura mata kyaututtuka, sakonnin ƙarfafa gwiwa da addu'o'in da ke tafiyar da rayuwar mace mai tsari. Sau huɗu kacal ya zo gun Amatu cikin shekaru uku, amma kowanne zuwan yana cike da ma’ana, girmamawa da soyayya. Yana kula da ita fiye da yadda yawancin maza ke kula da matan da suke tare da su kullum a zuciyar Amatu, Nashwan shine hasken da ke tafiyar da daren rayuwarta, kuma soyayyarsa shine mafita da kwanciyar ranta. BACK TO STORY BAYAN WANI LOKACI Karfe tara da mintuna goma sha biyu na dare. Amatu na kwance a kan gadonta, zuciyarta cike da fargaba da tambayoyi. Tana kallon last seen na Nashwan a WhatsApp – online yanzu yanzu ya sauka. "Shiru? tun safe ba text, ba kira, sai na ganka online kana faman hira da wasu amma ni kamar ba na cikin rayuwarka..." Tayi ajiyar zuciya, tana tura sako: "Nashwan, gaskiya bana jin daɗi. Duk da ina ƙoƙari na fahimce ka, har yanzu bana ganin ka fahimce ni. Soyayya ba kyauta ba ce kawai, tana bukatar kulawa da kalma mai daɗi a rana, kirar da zata sa ranka ya lafa. Me yasa kana yin kamar babu ni?" Bayan mintuna shida, sai gashi ya kira. Da ƙyar ta ɗauka. Murya ta cike da shakku da gajiya. "My Amatu... na san ba kya farin ciki, amma wallahi aikin ne... bana da lokaci fa, kinsan aikinmu..." "Ayyukan duniya ba su fi zuciyar da ke son ka ba!" Ta katse shi cikin murya mai sanyi da raɗa. "Duk da nisan da ke tsakanin mu, ina tsammanin zan fi ka ƙauna — ba don kyauta ba, ba don suna ba — sai don ina ganin ka a zuciyata fiye da yadda kake kallona." Shiru yayi, kamar yana narkar da kalmomin. Sannan yace: "Kin fi karfin komai a rayuwata Amatu. Amma ba koyaushe nake da lokacin da zan yi magana ba." ta numfasa, hawaye na gangarowa: "Ba na son auren da zai zama kamar daɗaɗɗen suna ne kawai. Ina son rayuwa da wanda zai damu da rashin saƙona, ba kawai ganin saƙona ba. Nashwan, ka dawo da kulawarka kafin zuciyata ta gaji da jiranka." Kamar wani yayi masa tsawa, Nashwan ya daɗe cikin shiru. Sannan ya furta: "Zan gyara. Kuma zan tabbatar da cewa kina da gaskiya. Tabbas, kina da gaskiya fiye da shiru na." Beep... ya katse kiran. Amma a zuciyarta, tana jin zafi mai sanyi — na soyayya da yawan jira. "Ina son Nashwan. Ina son sa fiye da yadda nake son ganin kaina cikin madubi. Amma duk zuciyar da ake soyayya da ita tana bukatar kulawa. Ina jira in ga ko zai cika alkawuran da yazo da su bayan wannan ƙorafi. Zuciyata na ƙauna, amma tana gajiya..." Sati biyu kenan. Ƙwarya-ƙwarya. Tun ranar da Amatu ta furta “Zuciyata na gajiya da jira”, Nashwan bai sake kiran ta ba, balle ya aiko da wani saƙo. Ba text, ba missed call — kamar soyayyar da suka ginaye akan lokaci da kulawa ta dusashe cikin iska mai sanyi da gajiya. Amatu na zaune a ɗaki, zuciyarta a haɗe da wayarta. Sau dubu a rana tana duba ko Nashwan ya aiko da text ta kira sa ba adadi ta mai text shiru ta mai magana a online ya buɗe shiru ba amsar shiru shiru mai nauyi kamar dutse. WhatsApp: Last seen: Online 10 minutes ago. “Yana lafiya? Ko yana tare da wani ne yanzu? Ko kuwa hakan kawai dabi’arsa ce – idan mun yi faɗa sai ya shude kamar ba mu taɓa soyayya ba?” Zuciyarta na bugawa da ƙara. Kowanne tick na saƙon da ta sake karanta a baya kamar ƙarar dukan zuciya ne ke sake tuna mata da yadda ake ji idan ka fi ƙaunar wanda bai damu ba. Tana kwance da fuska a mayafi, kwalla na ta faman gangarowa. Sai ta furta a hankali cikin numfashi mai nauyi: “Ina missing dinka, Nashwan... ko da baka missing dina ba.” Tayi ƙoƙarin cire shi daga tunaninta, ta mayar da hankali kan aikin ta, sai dai duk inda taje, kamar murya da kamshin Nashwan na biye da ita ne. Tana ganin sa a online, tana hango username ɗinsa, tana jin zuciyarta na amsa sautin sunansa — amma daga shi, shiru… shiru mai cike da tambayoyi. "Shin da gaske so ya tsaya ne? Ko yana kokarin hukunta ni ne da shiru? Ko kuwa... ya gaji da ni? Amma me nayi da har sai haka?” SOYAYYA GAMUN JINI NANARH KANWAR SOJA ✍️✍️✍️✍️ https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC 💘 ZAƁIN ZUCIYA💔 THE HEART'S CHOICE BY NARNAH ƘANWAR SOJA 🎉 Happy Birthday to Me July Girl Special 🎂✨ Na sadaukar da wanan littafin wa karan kaina kasancewar sa a watan haihuwa ta July.. Welcome to this journey... of love, of longing, of silence that speaks louder than words. Let the novel begin... with a heartbeat. 💔💌 Love , Sad × Long-Distance × Hopeful * short story DIAMOND 💎 GLOW PEN'S TEAM PAGE 9 / 10 best on true life story 21 /7/2025 "When the heart chooses, even silence speaks Kwatsam, zuciya ta gama jurewa. Amatu ta kama wayarta da hannu mai rawar zuciya ta danna sunansa. Bayan ƙarar kira sau biyu, ya ɗaga. “Hello…” Muryarsa kamar ba daɗin ji. Ita kuwa ba ta tsaya gaisuwa ba, sai dai ƙorafi mai sa kwalla: “Nashwan, me na maka ne har three weeks baka kira ni ba? Me nayi da zaka rika yin online amma ba zaka tambaye ni lafiyata ba? Ko zuciyata bata da daraja ne a gurinka?” sai shiru ya biyo baya. daga can Nashwan yace a sanyaye: “Amatu... aikin nan da nake ciki ba sauki bane. Wallahi kullum ina yinta har dare. Amma gashi yanzu na tura miki dubu goma, don ki Hai napep zuwa asibiti Sai transfer alert ya shigo. Gaskiya, ya turo. Amatu ta lumshe ido, zuciyarta ba ta cikin kudin. Sai tace da wani yanayi mai cike da taushi da zafi: “Ni ba kudi nake so ba Nashwan, ina so ka bani lokaci. Ko da minti goma ne kullum, ka tuna da ni. So na ba sabulun wanka bane da zaka manta idan ka fita.” “Ni ina son ka Nashwan, fiye da karfina ma. Amma kamar ina soyayya da bango. Zuciyata na ƙonewa.” shi kuwa ya sake shiru. Sai yace: “To... zan duba, zan gyara. Ki bani lokaci.” Washegari Da safe kamar kullum tana jiran kira ko sako, sai gashi ya kira. Da farko ta ɗauka farin ciki zai biyo, amma... “Amatu, na baki minti biyar. Duk abinda kike da shi a ranki, ki fadi yanzu. Ina aiki ne.” Zuciyarta tayi wani irin nauyi. Kamar ta furta: “Ina son ka Nashwan… amma bazan iya soyayya da mutum da agogo ba.” sai ta fara magana cikin kuka mai saukar hankali... “Zuciyata Ba Takarda Bace” Yana cewa “Amatu, na baki minti biyar. Duk abinda kike da shi a ranki, ki faɗi yanzu. Ina aiki ne.” Amatu ta dafe kirjinta kamar zuciyarta na neman tsagewa. Amma ta ja numfashi, ta fara da nutsuwa: “Nashwan, ka tuna lokacin da muke tare a makaranta? Kana bani lokaci fiye da abincin ka. Ka tuna da kalaman da kake faɗa min? Ina ƙaunar ka Nashwan, har yanzu. Amma yanzu kamar ni ce kadai nake tafiyar da soyayyar nan…” “Kullum sai dai ni na kira, ni na yi rubutu. Ka shiga online, amma ko ‘Hi’ ba zaka turo ba. Wannan ba soyayya ba ce, Nashwan. Ni ma ina da zuciya. Bana son mu rabu… amma ina jin kamar ni kadai ce a cikin wannan dangantaka.” Shiru. Can kuwa… ihun Nashwan ya buga a kunne kamar karar roka. “To me kike so ne yanzu? Kina takura min ne fa, Amatu! Ko ina aiki ba zaki fahimta ba? Sai kace ni bawa ne naki?! Wai wannan ce soyayya? Ko fursuna kike son ni na zama??” Wayar ta dauki tsawa kamar hayaki yana fita daga kunne. Amatu ta kasa magana. Kamar rana ta ɓace daga duniyarta. Daga nan sai “call ended”. Ya katse wayar. ta sunkuyar da kanta, hawaye suka gangaro kamar ruwan damina. “So na ba ya isar da ni gareka… amma kuma ka manta ni mutum ce.” - “Ni Ma Mutum Ce” "Meye laifina?" "Laifina kawai shine ina son shi?" "Ni ma mutum ce, ba dutse ba. Macce ce mai rauni, da zuciya mai sauƙin kamuwa da so." "Sai don na nuna mai so na, shi ne zai ce min minti biyar nake da su? Minti biyar! Kamar ina roƙon lokaci daga wani wanda ya mallaki numfashina yana jan min tsaki a waya ." "Shin haka soyayya take? ko kuwa ni ce ban dace ba?" "Yanzu sai na fuskanci cewa soyayya tana da laifi idan mace ce ta fara nuna gaskiya." "Yana online, yana dariya da duniya. ni kuma ina nan ina fama

Chapter 2 of 4