Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 7
da baya tare da furta “Ciki” da sauri Mom tayi k’an Yusrah ganin Haka yasa Yusrah Kara shigewa jikin Yusuf tana karkarwa shima rumgumeta yayi Dad ne ya fashe da kuka tare da fad'in “Baby uban waye ya Miki cikin Nan” Yana Magana tare da riƙe Mom dake Shirin karawa inda take Shuru Yusrah tayi Tana kallon Yusuf i'ta dai harga Allah taga cikinta na tasowa Bata yi zaton ciki bane sai yanzun, Shima i'ta yake Kallo cikin daka tsawa Dad yace “bada KE nake Magana ba dan Ubanki” hawaye ne ya gangarowa Yusuf a hankali ya d'ago zaiyi Magana Yusrah ta shiga girgiza Masa kai Kawar da k’ansa yayi daga kallonta sannan yace . “Ciki na ne” waige waige suka farayi dan ganin wake magana Amma Basu ga kowa ba i’ya sune kawai cikin karaji Mimi tace “me kace Yusuf?!” kallon Mimi yayi tare da sake furta “Ciki Na ne” wani Mari Mimi ta d’auke shi dashi Grandma ne tace “aii ya kwana Gidan sauki saiya Aure ta suje can su Karata maganin masu fita gasashen waje Kenna maganin masu Fita Office Kullun safiya Kenan” i'hu maijidda ta saka tare da fad’in “Aure fa kika ce Granny¿" Gyaɗa Mata k’ai tayi alamar Eh da Sauri Maijidda tace “Babu Aure tsakanin Yusrah da Yusuf” Zuba mata i’do sukai Gabad'ayan su Mom tace “kamar ya jidda?” cikin kuka Maijidda tace “Saboda Yusrah yar Mimi ce k’anwar Yusuf Ciki d’aya....” kafin Maijidda ta karasa maganarta Yusrah ta kwalla Kara tare da zubewa kasa sumammiya...... *FARHAT* 7/16/20, 3:29 PM - FARHAT UMMY BILAL🤰🏼: *_✺✺ BAN FARGA BA ✺✺_* ᴸᴼᵛᴱ ᴬᴺᴰ ᴿᴼᴹᴬᴺᶜᴵᴺᴳ ✺✺✺✺ ✺✺ *(F. J. W. A)* ✺✺✺✺ 17.... *Korafin yayi yawa my Guys, saurin mai kuke kubi littafin sannu a hankali dan yanzun aka fara🙃 Duk kuyi hakuri Gabad'aya Group d'in na cire kowa har ni k'aina Kunce a saku group an sakaku amma nakwa magana kun mayar da group sai kace gidan zaman makoki😃: COMMENT bai dame ni ba, cost bashine a gabana ba muje a haka zaku sami shi a sauran groups da nake* *Yauma ba Editing🙅🏻‍♀️* Da sauri Yusuf yayi k’anta Yana Kiran sunanta Amma i'na Ko numfashi batayi koman ta ya tsaya cak, hankalinsa yayi bala'in tashi Gurin Mimi ya nufa tare da riketa Yana jijjigata “mimi pls ki temaka min karta mutu wlhy Inna tsananin kaunarta sosai wayyyo Yusrah ki tashi Karki min Haka dan Allah” ya karasa maganar Hawaye na wanke masa Fuska Mimi dake tsaye Gabad'aya jin abin take tamk'ar a mafarki Kallon Jidda tayi murya ciki ciki ta fara magana. “Jidda mai kike fad’a Haka? Anya k’anki Bata samu matsala ba!” kafin Maijidda tayi magana sukaji Magana a bayan su “Gaskiya Maijidda ta fad’a Mimi Yusrah 'yarkice ta cikin ki” cewar Mai aikin gidinsu a matukar firgice Mom ta juyo tana binta da wani i'rin Mugum kallo cikin i’hu tace “Kamar ya Nida ’yata zakuce ba nawa ba? yau Naga karfin Hali Yusrah d’ince ba 'yata ba?!” Dad da tund’azun ya kasa Magana gabad’aya jikinsa yayi wani i'rin mugum sanyi Baffa kuwa dafe k’ansa yayi tare da zaman ’yan borin a kasa Granny ma i’do ta kwalalo waje tare da fashewa da kuka domin i’ta har ga Allah lamarinsu ya sata cikin duhu Kallon Maijidda Baffa yayi tare da fad’in “Jidda are u serious?” gyaɗa Masa k’ai tayi hawaye na wanke mata fuska Bata taba zaton Wanan ranar zata zo musu a Haka ba barin ma Mom tayi bala’in Bata tausayi Amma tafi jin tausayin Yusrah Minaty ne ta fad’o d’akin kamar wacce aka jehota kasancewar taji komai domin tun d'azun take tsaye babu Wanda ya lura da i’ta Kan Yusrah tayi ta d’agota tare da rumgumeta tana wani i'rin Kuka mai'cin Rai. Kukan da duk wani mai i'mani saiya zubda hawaye kowa a Gurin kuka yake Amma Banda Yusuf dake bin kowa da i’do mikewa yayi ya nufi Gurin Momy Yana nunata tare da furta “Momy da gaske ne Yusrah ba 'yarki bace Anya kuwa ba mafarki nake ba wannna wacce i’rin Mummunar Al'amari ce !! Ya Allah kasa mafarki nake Ya rabbi kasa inna tashi daga wanan barci Ubangiji karka sa na sake i’rinsa” runtsa i'do yayi Yana yamutsa gashin kansa sake bud’e idanunsa yayi fess cikin na Momy dake zaune tana Kallon Maijidda a hankali jidda ta dafa kafad’arsa tana fad'in “Wannan ba mafarki bane zahiri ne Yusrah k’anwarka ce uwa d’aya uba d’aya” Granny tace “menene shaidar ki na fad’in Haka?” mai'aikinsu tace “Dr ki fito ki musu bayani yanda zasu fahimta Dan Allah” Dr dake tsaye jikin kofa Gabad'aya jikinta yayi sanyi Bata bata zaton Abinda ta aika zai Zama musu matsala ba sai yau. Momy na ganin Dr Saddika ta mike da sauri tare da nufarta cikin in in na tace “yauwa ki fad'a musu a hannunki na haihu ki fad’amusu ke da k’anki Kika kar’bi haihuwata ki fad’a musu Yusrah ’yatace ta cikina ki fad’amusu nace Saddika ...!!” ta karasa maganar tare da cin kwalar rigar Dr hawaye ne ya wanke Dr Saddika fuska “Tabbas nice na kar’bi haihuwar ki Hajiya Maryam Naso ace Kuma abinda Kika Haifa ya rayuwa Amma Kash sai dai ba Haka Allah yaso ba naso ace Yusrah 'yar kice....” katse ta momy tayi cikin hargagi tace “ban Gane ba kamar ya kema kin bi sahunsu ne kai nifa kun hargitsamin kwakwaluwa” Ajiyar zuciya Minaty ta sauke kafin tace “Momy Amatsayin ki na uwa ya kamata ki fita ki bar 'yarki i'ta kad’ai a ’bangaren ku kullun in Zaki tafi aiki Yusrah kuka take maganarta d’aya yanzun momy tafiya zakiyi ki barni ni kad’ai ? Ke kuma sai kiyi tsaki Dad a matsayin ka na uba ya dace ta tashi ka tsallake kasarka ka tafi wata uwa duniya niman kud’i 'yace kwaya d'aya tal Ubangiji ya baku Amma saboda son aiki da ku yan Boko kullun sai dai a barta i'ta d'aya bayan kun barta kunsa maike faruwa bakwa Nan?” share Hawayen fusk'anta tayi sannan taci gaba “tirrr tirrr da iyaye masu i'rin Halinku gaskiya Iyaye musammam ma Mata ya akama a Gyara Ku FARGA tun huri ku lura da tarbiyar 'ya'yan ku Mata Momy ki duba rayuwata wani tasku ne bangani ba a Gurin matar uba kuma yar uwa ga Mahaifiyata gashi duk i'tace silar lalacewa ta gashi ta Bata min rayuwa rayuwar da in ba tare da mace ba bazan ta'ba jin dad’in yinsa ba Kullun inna kuka kuk'an bak’in ciki na rashin samun kulawa daga Gurin mahaifina da 'yanuwan shi gashi yanzun rayuwar dana ke ciki ba ta kwarai bace” karasa maganar tayi tana sakin wani i’rin kuka kowa na Gurin sai da ya tausaya Mata “Gaskiya ne Maganarki Amina *ban farga ba* gashi yau har 'yata ta cikina wai yau ciki ne a jikinta wayyo Allahna...” kuka ta saka sosai Baffa yace “Saddika Yusrah 'yar WACECE” sunkuyar da k’ai tayi kasa sanan tace “Yarka ce Alaji tausayi da tunanin halin da Hajiya mariya zata shiga Nan gaba ne yasa na Aikata abinda yanzun na dawo nake lamada da nasan haka zai kasance wlhy da tun Farko na barwa Hajiya mariya gawar 'yarta” shako waiyar riganta Momy tayi tare da fad'in “what... Da ...dagaske kike Saddika nawa 'yar ta mutu mai yasa Kika min Haka pls Mai yasa..” tarin da Yusrah tayi ne yasa suka nufeta dukk’ansu riƙe take da Hannun kawarta Minaty kallon kowa tayi kafin ta sauk’e idanunta k’an Momy wani kuka ne ya kufce mata matsowa Yusuf yayi da niyar kamata Amma sai ta dakatar dashi ta hanyar d’aga Masa Hannun “Karka matso Kusa dani” tsayawa yayi cak yana kallonta kamar zaiyi kuka mikewa tayi a hankali tana dafe Cikin jikinta har Gurin Mimi tazo ta rumgumeta “Shiyasa nake jinki daban a Raina Ashe kece mahaifiyata gaskiya an cuceni an cuce ki mahaifiyata Amma Babu komai Haka Allah ya tsara A yanzun bana bukatar komai bana son komai mutuwata kawar nake bukata domin an riga an ruguzamin rayuwa” rumgumeta sosai Mimi tayi cikin kuka i'tama ta fara magana “a a Yusrah Karki ce haka pls..” katseta Yusrah tayi da sauri sannan ta nuna cikin jikinta “ban ta'ba jin tsanar wani a duniya kamar cikin dake jikina ba Wai ace Yayana shi yamin mai zan Haifa d’a ko kani ? 'ya ko k’anwa? Nafi K'aunar mutuwata da inga wannna ranar ...” FARHAT 7/16/20, 3:29 PM - FARHAT UMMY BILAL🤰🏼: *_✺ BAN FARGA BA✺_* ✺✺✺ ®🌁(F.J.W.A) 18…. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GPGDyJ7D1piATNEJianNac *Sadaukarwa ga duk Masoyan Littafin Nan* Durkusawa tayi tare da kifa k’anta a kasa da rarrafe ya karaso inda take Magana yake son Mata Ama ya rasa ta Inna zai Fara domin bakinsa ya Masa nauyi d’agowa tayi jin saukar numfashi mutum gab da ita kad’an ya rage Bata fad’a kanshi ba, kasancewar tsaka ninsu baifi tsayin yatsa ba wani mugum Kallo ta auna Masa da sauri ya kama hannunta tare da furta “Am very Sorry” katse shi tayi da sauri “sake min Hannun !” murya a hasale ta karasa maganar ba musu ya sake ta mikewa tayi tare da nufar part d’inta da gudu Minaty ta biyo bayanta “Yusrah ki tsaya dan Allah inna zakije...” juyowa tayi tana Kallonta idanu cik’e da kwalla ta matso Kusa da ita tare da kama hannunta “Kawata inna sanki sosai bani da wata Aminiya kuma abokiyar shawara bayan ke zan.... zan rufe k’aina a d’aki har Zuwa lokacin da Allah zai kar’bi raina domin rayuwata Bata da wata Amfani ke ko a cikin Littafin ban ta'ba cin karo da labari irin na rayuwataba, ban ta'ba jin labari maisarkakiya irin labarina ba wlhy na tsani k’aina na tsani komai bana bukatar komai kamar mutuwa Ama kawata i'na so kimin *Alkawari kwaya d’aya tal* inna san rok’onkin da ki bar rayuwar da kike domin abinda kik’e babu Kyau bazaki Gane rashin k’yansa ba sai Nan gaba ama in na so kafin lokacin ki tuba ki daina hudd’a da Mata kawata i'na so kimin Alkawari...” kuka ne yaci karfinta ta kasa karasa maganar da take yi da sauri suka rumgumi juna suna kuka maitsuma zuciyar mai'sauraro kuka suke sosai kuk’an da duk wani mai'imani saiya tausaya musu a hankali ta k’ai bakinta dai dai kunnin Minaty sanan tace “kimin Alkawari zaki Auri YUSUF kinji kawata Karki ce min a'a domin a'a Yana nufin Baki d’auke ni yanda na d'auke ki ba” da sauri Minaty ta raba jikinta da nata hannunta ta kama gam cikin gunjin kuka tace. “a a Karki min Haka Yusrah bazan iya ba...” kwace hannunta Yusrah tayi da sauri ta nufi kofar d’akinta Magana take batare da ta juyo ba “Naji nagode yanzun nasan matsayi na a Gurin ki Allah ya had’a fuskokin mu da Alkhairi” da gudu Minaty ta nufeta ama i'na ta riga da ta rufe kofar buga kofar take da karfi tare da fad’in. “ Yusrah ki bud’e pls na amince ki fito dan Allah” buga kofar take da iyakacin karfinta ama ko sauraronta Yusrah batayi sabida tariga ta shige cikin d’akin da sauri Mimi tazo ta riƙe Minaty cikin rawar mury tace. “Amina mai Kika Mata ? Mai tace Miki pls ki fad’a min” Minaty tace. “mimi taki bud’ewa bare ta saurari amsar da Zan bata pls kema kisa Baki Amatsayin ki na mahaifiyarta ko zata Amince ” girgiza k’ai kawai Mimi tayi mikewa tayi ta Kama Hannun Baffa tana jansa tare da sak’in kuka Baffa da har yanzun bai hayyacinsa domin Ganin Abin yake kamar a mafarki gani yake kamar Barci ne haka ta ringa Jan hannunshi har d’akinta kamata yayi ya zaunar da i'ta domin taki zama fad’awa kawai tayi jikinsa tana kuka abin Gwanin ban tausayi rumgumeta yayi sosai Yana bubbuga bayanta alamar rarrashi sai da tayi kuka sosai Sannan ta d’ago tana Kallon sa a hankali ta Kira sunan sa. “Auwal da gaske ne Yusrah 'yarmu ce ?” Gyaɗa Mata Kai kawai yayi “Taya hakan ya kasance to menene Ainihin labarin mai'yafaru to a baya ya kamata Saddika ta fitar damu a Duhu” kokarin sauka take a jikinsa domin jikinta har bari yake da sauri ya riƙe ta cikin kwantar da murya yace. “ ki nutsu tukun yanzun mai'zakiyi ?”. Kuka ta saka harda buga kafa abin dariya yaso bashi cikin zuciyarsa yace. “Allah Sarki uwa Kenan gaskiya an cuceki Amma Babu komai a kwai Allah” sharemata hawayen fuskanta yayi sosai ya rarrasheta Saida ta nutsu sanan yace. “ki Bari mubi komai a sannu kinji” Lumshe ido tayi badan ranta yaso ba tace. “to” domin i'ta so take tasan ta yanda akeyi aka d’auki 'yarta aka ba Momy zamewa tayi tare da sauka a jikinsa jin ana kokarin shigowa YUSUF ne ya shigo gabad’aya yayi wani i'ri kallo d’aya zaka Masa ka fisk’anci Yana cikin tashin hankali durkusawa yayi ya bud’e Baki da niyar Magana Kenan Mimi ta katse shi. “fita min a d’aki karka kuskura ka furta komai a Nan wlhy mudin ka kuskura ka raka kusanto inda nake saina tsine mak...” kukan daya saka ne ya katse sauran maganarta. “Dan Allah Karki ce haka pls wayyo naji bazan Kara Zuwa inda kike ba Ama..” katseshi tayi cikin zafin Rai domin ko ganinsa Bata kaunar yi. “ama uwarka wlhy in ka Kara wani Magana sai ranka yayi mummunan baci shashasha kawai tashi ka Bani guri” Kallon Baffa yayi ko zaiyi Magana Ama sai yaga ya kawar da k’ansa yayi jikin a sabule ya mike tafiya yake kamar zai fad’i hannunsa ya daura a k’ansa ji yake kamar k’an zai bar gangan jikinsa, Yana fitowa ya ci karo da Granny zaune ta rafka uban tagumi matsowa yayi zai Mata Magana cikin tsawa tace “tashi Dan uwarka wlhy in ka min Magana da wanan bakin naka saina ruguza maka shi fitar mana daga d’aki ka tafi can Gurin shashashar uwarka” ta fad’i haka tare da nuna Masa part d’in momy. Mikewa yayi kamar zaiyi kuka haka ya nufi part d’,insu direct d’akin Yusrah ya nufa murd’a kofar yayi ya jishi gam bubbuga kofar ya fara yi da karfi Yana Kiran ta . “ Yusrah da Girman Allah ya bud’e kofar Nan ki zo zan kar’bi cikina dan Allah kizo pls gashi kowa yaki kulani kizo kinji Baby nah com and stay with me” _(Yusuf manya watao tazo zaka kar'bi cikin ? da bakayi tunanin zata d’auki ciki ba ka ringa hak'arta kamar rijiya family plan na gargajiya inhar bakya so ko baka so Kama matar ka ciki muddin kayi sex da i'ta karka yi realizing a jikinta haka nada kyau Shan magani barkatai Yana da illa sosai dan Haka a kiyaye ko kuma kuna gama sex da Sai kisha panta Mara sanyi or ki jika masoro da zaran kun gama sex sai kisha Ko Kuma kije kiyi fitsari duk wanan hanyace na Hana d’aukar ciki .)_ Haka ya ringa surutai Yana Buga kofarta har ya gaji ya zauna a kasa jingina yayi da kofar a Haka har barci ya d’auke shi Minaty ta kasa zaune ta kasa tsaye duk Bata cikin hayyacinta tana shiga Gida d’akinta ta nufa Nan taga sabuwar wayarta gata Fara kyakyawa gwanin sha'awa harara ta balla Mata Lokacin da ta tuna maganar Yusrah sai da taji hawaye da sauri Yarinyar ta taso tare da fad’in “Honey are u okay ?” Wani mugum kallo ta auna Mata cikin daka tsawa tace . “Uwar zuma d’in maza tattara kayanki Ki bar Nan kafin na illata ki ” da sauri Yarinyar tace . “Jessu Anya lafiyar ki kuwa madam ya Zaki kore ni bari na Kira Big Hajiya tazo ” (matar Baban Minaty) kafin ta fita taji an wani fusgota da karfi tana juyowa Minaty ta watsa Mata mari “ke ba Big Hajiya ba uwar ta Zaki Kira ita ta kawo ki” girgiza mata kai yarinyar tayi Cikin zafin Rai ta tunkud’ata waje tare da watsa Mata jakar kayanta, Kullun Sai Minaty taje Bata aiki sai buga kofar Yusrah ama Bata kulasu gashi yau kimanin wata biyu Kenna tana kulle a d’aki anyi anyi kofar ya bud’u yaki bud’uwa Gabad’aya Yusuf ya rame in ka gansa sai ka tausaya masa Kowa na gidan Babu mai cin Abinci barin ma Mimi domin tafi kowa shiga damuwa momy kuwa ba'a Magana dan nata yafi na kowa dan tana cikin tsananin tashin hankali yau da huri Minaty tazo Gidan haka ta Tarar Gabad'ayansu Suna bakin kofar Yusrah kaman kullun Suna had’a ido da Yusuf ta watsa Masa wani irin mugum Kallo kawad da kansa yayi mutumin da suka shugo tare ne ta nuna Masa kofar Tare da bashi umurni ya balle aikuwa cikin mintuna kalilan ya balle kofar ture Junansu suka Fara kowa naso ya fara shiga yaga Halin da take ciki da sauri Yusuf ya bangaje kowa tare da shigewa dakin da wani mahaukacin Gudu Yana karasawa cikin daki ya tsaya cak hango Yusrah yayi a can karshen Gado jikinta sanye da hijjab Gabad'aya Bata motsi kwance take tana kallon sama ga d’an cikin jikinta da yamata d’as yayi d’an tsini duk ta rame d’akin yayi kaca kaca sai wari da karnin amai d’akin yake momy CE ta karasa da gudu tare da rumgumarta tana jijjigata Mimi ma Gurin ta nufa tana jijjigata tare da Kiran sunanta Amma shuru Bata motsi Minaty ne ta hango yanda cikin Yusrah ke juyawa da sauri tace “Gaskiya ya kamata muje asibiti” Gyara muryan Granny suka ji daga bayan su tare take da Dr Saddika “basai anje asibiti ba ga Likita sai ta dubata” cewar Gran karawa kan gadon Yusuf yayi da k'arfi ya finciketa daga hannunsu fita yayi da ita tare da sakata a mota momy nata kwala Masa Kira Amma yayi banza dasu a guje yaja motar suma mota suka shiga tare da bin bayan sa, Wani irin mugum gudu taye kamar zai tashi sama..... *Zaku jini shuru 2 days saboda zanyi tafiya bana jin dad’i Inna bukatar Addu'ar ku nagode sosai* Ga Group nan na Bud'e sabida ku masoyana FARHAT 7/16/20, 3:30 PM - FARHAT UMMY BILAL🤰🏼: *_✺ BAN FARGA BA✺_* ✺✺✺ ®🌁(F.J.W.A) 19…. *Nagode sosai da Addu'oinku na i'sa lafiya💗* Cikin fargaba da tashin hankali suke bin motarsa Gabad'aya Hankalinsu ya gama tashi ganin i'rin Gudun da yake zubawa a Kan titi a wani tsadaden Asibiti ya tsaya da motarsa bai ma shiga da motar ciki ba domin a ganinsa Bata lokaci ne fitowa yayi ya d'auketa da gudu yayi cikin asibiti yana kwalawa nurse Kira da sauri suka fito ganinsa da Mara lafiya ne yasa d'aya daga cikin su komawa ba'afi minti 1ba, sai gata da gadon tura Mara lafiya Zuwa tayi da niyar Karban Yusrah wani banzar kallon daya watsa Mata ne yasata jan baya da sauri cikin ƙaƙƙausar murya yace “inna Doctor Dr...?” Dr Saddika da fitowar ta Kenan ya sata fad'in “Subahanalillah mai'yasa meta ko Haihuwan NE?” A hankali take bud'e idonta tun tana ganin dishi dishi har ta bud’e su fesss Ak'an fusk’ansa, dafe mararta tayi a hankali ta motsa labbanta alamar son yin magana ganin Haka yasa ya kai kunninsa dai²n bakinta “Zan mutu cikina sai juyi yake yi” ta karasa maganar Hawaye na wanke Mata fuska a hankali ya nufi d’akin da Dr ta nuna Masa dai-dai lokacin da su Mimi suka karaso gurin d’aurata yayi akan gadon kallonsu Dr tayi kafin tace. “kud’an bamu guri...” bai Bari ta karasa ba yace “babu inda zamu...” kallon tasana Minaty ta watsa Masa Taski yayi yana watsa Mata kallon banza, girgiza kai Mimi tayi domin Duk abinda sukeyiwa junansu tana ankare dasu a hankali ta kama hannun Baffa da granny suka bar d’akin Dad ma Hannun Yusuf ya kama suka fita d’aki ya saura daga momy sai Minaty a hankali suka karasa bak’in gadon Zuwa wannna lokacin Yusrah ta galabaita duk ta fara fita daga hayyacinta Momy tace “Saddika haihuwace wai ko menene?” lumshe ido Saddika tayi tare da jingina da bango a hankali tace “Haihuwa ce Amma bazata i'ya haihuwa da k’anta ba, Addu'ar ku muke bukata Momy” ta karasa maganar tana share Hawayen fusk’anta, Jiki a sanyaye momy ta nufi gadon da take a Hankali take Magana bayan ta Kama hannunta “Baby ki yafe min kinji Pls nasan ban tsaya na kula dake yanda ya kamata ba, maganar Granny gaskiya ce, da take cewa Ban farga ba..¡ gaskiya maganar Haka ne dana farga da ban barki a gida cikin part d’inmu ke d’ayaba, ashe maganar ki abin lura ce duk lokacin da zani aiki kina cikin damuwa da tashin Hankali ashe....Ashe... Kinsan abinda kike fisk’anta” kuka ne ya kwace Mata “Momyna Baki min komai ba, inna kaunarki sosai banji tsanarki ko kad’an a Raina ba.. nasan Haka Allah ya kaddaramun nasan kuma ni ba mai tsawon rai bace momy inna ji a jikina bazan kuma rayuwa a cikin ku ba, Inna jin wani i'rin a jikina inna ji kamar zuciyata zata fashe an Bata min budurcina bani da wani Amfani i’dan na rayu wa zai Aure ni wa zai Soni ?” lumshe ido tayi hawaye na gangarowa a k’an fusk'anta, “bani da wani Amfani momy domin duniya ta i'sheni Bata Raina bani da wata kima yanzun inna rayu zan dawwama cikin k’unci da bak’inci anyi min mugunta abin bak’inciki Yayana uwa d’aya uba d’aya Duk Ak'an rashin samun kulawar iyaye Haba yaza nayi...! yanuzun fa ciki gareni har wata d’add’aya wata Bakwai tsaban tashin hankali cikin bai k’ai haihuwa ba za'a fid’eni ya Allah kayi gaggawar d’aukar raina Rabbi karka barni na Kara a cik’akk’un mintis a duniya Allah yasa d’a ko ’yar da zan Haifa ya rayu ko ta rayu ya Zama lzina ga Iyaye masu i'rin Halin ku momy Amina inna sanki kamar 'yar uwata domin sanki a jinina yake pls ku fita ku barni kawai..” Kuka suke sosai Gabad'aya zuciyar likitocin ya karye sunji tsananin tausayin su haka suka bar d’akin kowa na sahrar kwalla “Allah Sarki Nima sai da na share kwalla domin na tuna da wani Abu ...lol” cikin gaggawa aka had’a kayan Aiki Zaman dirshan Yusuf yayi Yana kuka wiwi domin tayi mugum bashi tausayi lokacin da ya ganta za'a shiga da i'ta dak'in tyata granny ma kuka sosai take i'ta so take taji makasudin labarin .... So take tasan Taya Haka ya kasance ? Suna zaune shuru kusan awa d’aya ba Labari can Dr ta fito daga d'akin da sauri suka nufeta cikin rawar murya Minaty tace “Dr ya take ?” kallon su sosai Dr tayi ganin yanda suka Zama wani i'rin kamar sune masu nakudar ajiyar zuciya ta sauke kafin tace “An cire Mata 'ya mace... Yanzun za'a Gyara su kafin ku shiga kuganta” cikin minituna kalilan aka gama komai Nan aka kaita d’akin hutu gbdyn su suka shiga d’akin kwance suka isk'eta tana zubda hawaye Koda suka Gama shugowa idanunta ta watsa Masa Nan shima ya tsaya kallonta a hankali yazo tare da kama lallausar hannunta, wani kuk’an bak’in cikine taji ya kwace Mata daga ta fara wani i'rin mugum shaguwa wani mugum tari tayi Nan take sai ga jini a matukar firgice yayi k’anta da niyar kamata wani mugum tsawa Mimi ta watsa masa babu shiri ya ja birki... Kukan yariyar ne ya ankarar dasu sai yanzun suka ma tuna da jaririyar Dr ne ta d'auke ta tare da mikawa Yusrah girgiza Mata Kai Yusrah tayi tare da kawad da idanunta gefe ganin yarinyar sak Yusuf hannunta na dafe da Kirjinta wani i'rin juya kai take tare da fashewa da wani mugum kuka Saddika tace “kar’bi yarki ki Bata Nono Tasha Karki ce Zaki horata domin Bata san komai ba” Da kyar Yusrah ta i'ya

Chapter 5 of 7