Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 10
Rabi maƙociyarsu data yafo zani ta faɗa basu ankara ba sai jin faɗuwar Muneebba sukai ta zube ba numfashi a tare da ita, idanunta sun wani ƙaƙƙafe, "Innnalilahi wa'inna ilaihirraji'un Muneebba ki tashi dan Allah, mukaita asibiti" Hafsah ta faɗa tana kuka, Mamma ma kukan take ita da Khabir wanda ya ɗauki Muneebba da gudu ya nufi ƙofar fita da ita, karo suka ci da Dad Wanda yake yunƙurin shigowa hankali a tashe shima ya amshi Muneebba yana nufar motar da ita Sbd tashin hankali da ƙyar Mamma tasa Hijab ita da Hafsat suna shiga Motar tareda Khabir Dad kuma na wata motar wani gudu suke shararawa har suka isa Private hospital Wanda aka karɓeta da gaggawa ganin halin da take ciki kuka Mamma keyi riris Hafsat na bata baki, taƙi tai shiru, dukansu zaune suke sunyi jugum_jugum, Abbie dake daga gefe can yana kallonsu hawaye na bin kuncinsa, dashi da Habib wanda babu halin zuwa wajensu su duka, kallonta yake zuciyarsa na masa zafin yadda take zubar da hawaye, " wannan ma na gani Aysher ban san iya kukan rashina da kikai ba, dole nazo wajenki koda kuwa a yau ɗin nan zan fitar da numfashin ƙarshe ba zan juri ganin hawayenki ba Aysher na kasa jurewa" ya faɗa da ƙoƙarin tunkaro inda take, Habib ne ya jawosa yana girgiza masa kai hawaye na zuba yace "Abbie na roƙeka kada kaje zamu iya rasaka kasan kuwa iya jinin da kake zubarwa wajen yunƙurin zuwa garesu? Abbie kada ka ƙara cilla mu a wata matsalar ka barmu da iya wacce muke ciki ba dammu ba sai dan Mamma da kuma Ummi da suke buƙatar ka samo musu mafita" ya faɗa tareda riƙe ƙafar Abbie yana kuka shima, hawaye Abbie ya share yana dawowa ya ɗago Habib yana kallo yace "naji Habib ba zanje ba amma zanyi nesa da ƙasar nan ko dan ku da iyayenku, zan bar ƙasar gaba ɗaya na nisanci kaina daga Iyalina tunda hakan shine mafitata" ya faɗa yana barin wajen da sauri, da kallo Habib ya bisa yana share hawaye shima yabi bayansa dukkan wata zirga_zirga Dad ne ya dinga yinsa wannan ne ya tabbatarwa Mamma lallai zasu iya kular mata da ƴarta, hakan yasa hankalinta ɗan kwanciya suna jiran tsammani don Doctor ya Kira Khabir da Dad, ganin sun fito fuskarsu da ƴar walwala yasa Hafsat sauke ajiyar zuciya, kallon Mamma Dad yai da tausaya a fakaice yana share hawaye yace "Alhamdulillahi tunda an samu nasar daidaita Numfashinta, dama shine yake barazanar ɗaukewa yanzun anyi nasarar daidaita sa, bacci take yanzu sai tsawon 3 hours ta farka, sai dai na sake baku haƙuri akan abinda ya faru tunda lallai wannan auren sai dai muce nufin Allah ne wanda ba muyi zato da tsammani ba haka zalika shine mijin da Ubangiji ya rubuta zata aura tun dirowarta a doron duniya, ita ƙaddara zanen zabo ce, kuyi haƙuri da kalar rayuwar da kuka tsinci kanku insha Allah komai mai wucewa ne Bayan wuya sai daɗi" ya faɗa da Murmushi hawaye Mamma ta sake sharewa tana faɗin "bawan Allah ni bani da abinda zan gode maka dan ka fitar da ƴata kunya dani kaina da ka rufa mana asiri lallai na yadda da cewa komai a rubuce yake bawa bai isa ya sauya zanen ƙaddararsa ba, haka Allah ya tsarawa Muneebba bama da tsimi da dubara, Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi yasa kuma Abokin rayuwa ne" Mamma ta faɗa cikin dauriya Murmushi Dad yai yana ƙara jinjinawa Mamma akan tawakalli da yarda da ƙaddara, take away yai musu da yi musu sallama akan gobe zashi dawo, ɗakin da take kwance suka shiga,kwance take fuskar nan tayi fari fat hancinga sanye da oxygen hawaye Hafsat ta share tana duƙawa a wajen ta kama hannunta tana riƙewa gam, Alwalla Mamma tai tana salla la'asar da Magriba wanda tashin hankali bai barta tayi ba sai da daddare Khabir shima ya tafi zuciyarsa cunkushe da damuwa Misalin ƙarfe 3:30Am a hankali take ware manyan idanunta harta waresu duka akan farin silin ɗin Idanunta na zubar da hawaye wanda ta tabbatar da lallai ba Nazeer bane Mijin nata wani ne daban aka ɗaura mata igiyar aurensa a kanta, "Ya halayyarsa take, wane kalar mutum ne, wanene shi, wace sabuwar rayuwar ƙaddara zata gudanar, shin mai kyau ko akasin hakan?????" Waɗannan tambayoyi sune ta ɗinda maimaitawa kanta tana hawaye Gidan Mom sosai ya kacame da hayaniyar Mom tun la'asar take abu guda wanda ganin auren Bobbi na yawo a media ga kuma fuskar Dad wanda ke murmushi wannan ya tabbatar mata da lallai auren Bobbi ɗinne su kansu su Zameer abin ya ɗaure musu kai,uwa uba Maheer wacce take kuka taƙi magana sai dai bin kowa da ido, wannan ne ya ƙara tada hankalin Mom ta dinga kiran Dad da Bobbi ba ji ba gani....... Wayyo akwai fa cakwakiya, ina uban gayyar yake ma🥺ku dai yi haƙuri yau ba'a taɓo ɓangaren Fattu ba da kuma Bobbi [5/21, 8:12 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA* Book 1 *By Riamcool* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* *P.21&22* ___________Tayi kiran iya kira babu wanda ya ɗaga a cikinsu daga baya ma Bobbi kashe wayoyinsa yai dan lokaci shi kanshi yana buƙatar keɓewa Dad kuwa lokacin yana Asibiti wajen Muneebba sai daga baya yaga kiran kai tsaye gidan ya nufa da sallama ɗauke a bakinsa ya shiga fuskarsa a haɗe tamau babu alamun wasa ko rahama kallon ƙasa da sama Mom tai masa cikin ɓacin rai ta miƙe "mi kayi haka? wannan wane kalar tozarci da cin mutuncin kaja mana kasan kuwa abinda ka aikata?" ta ƙarashe zancen da huci "Yes nasan abinda na aikata dan na isa ne shi yasa na aikata aure na yiwa yarona kuma ita ce wacce na zaɓa masa abokiyar rayuwa ta har abada babu wanda ya isa ya hanasa zama da ita" ya faɗa yana haura up stairs binshi tai da azama tana faɗin "wallahi ba zai zauna da wata shegiyar ƴa ba in ba Maheer ba Maheer ce zaɓina kuma ita zai aura wannan kuwa ranar da tazo gidan a ranar zata barshi dan sai ya mata saki ukku cir, wanna wane kalar rayuwa ne ka saka ƴar mutane a damuwa gashi tunda Maheer taji auren nan ko Abinci bata ci ba ƙarshe ma kulle kanta tayi a ɗaki to wallahi tallahi indai ni na haifi Bobbi sai na saka ya saki ƴar matsiyatan can kuma zanyi bincike" kallonta yai yana kauda kansa gefe guda Sbd ɓacin rai "idan bake kika haifesa ba fa?" yai mata tambayar yana kafeta da ido, itama kallonsa tai tana sakar masa wani Miskilin Murmushi daga bisani kuma ta jijjiga masa kai tana barin wajen da sauri, da kallo ya bita har shiɗa, haurawa sama yai yana shigewa bedroom ɗinsa zama bisa bed yai yana dafe kansa dake masa ciwo Mom kuwa tana shiɗa dasu ABEED ta fara cin karo suma sunyi jugum_jugum kallonsu kawai tai ta wuce, duk lkcn data gansu ranta yana sosuwa sbd ta tsani Mahaifiyarsu ganinsu kansa tuna mata yake da Mahaifiyarsu, ita ce mafarin tarwatsa mata farinciki ita ce sarauniyar Ahmad ita ce magadiyar wannan gida Sbd haifafar ƴaƴa Mazan da tayi taya zata ma bari su kansu ƴaƴan nata suyi farinciki wasan na nan zuwa kansu *Asad BObbi* A hankali yake saukowa daga Step ɗin haɗaɗɗen benen wanda ƙarafen benen kanshi na zallar azurfa ne cikin gadararriyar tafiyarsa ta ƙarfafan maza yake saukowa harya ƙarasa saukowa a haɗaɗɗen Falon wanda yaji Furnitures Set Ukku haɗaɗɗu, dukkansu zubinsu na kalar gidan sarakai ne ga wani lallausan Cafet dake malaye a tsakiyar Falon zama yai ɗaya daga cikin kujerun yana ɗaukar wayarsa ya kunna, Missed call ɗin Mom ya gani yafi hamsin ɗaga giransa guda yai yana taune lips ɗinsa na ƙasa Data ya kunna yana ƙara shiga Instagram wanda anan ne Vedio yafi yawo kallon vedio yake yana ƙara maidosa baya ya tabbatar da lallai shi ɗinne aka ɗaurawa aure ba wani ba "Mace" ya furta yana ƙara tauna lips ɗinsa, babu halittar da yafi tsana a duniya sama da mace, mace ita ce maƙasudin cin galaba a kansu mace ita ce maƙasudin shigarsa ƙuncin rayuwa wacce bai san ranar fitarsa ba, Mace ɗaya ce yake so a faɗin duniya ita ce Mahaifiyarsa, shi abinda ya ɗauki Mace ita ce makira maƙaryaciya maci amana, kuma shi ɗinne ake son yayi rayuwa da mace har biyu "ta ina zan iya? ina bazan iya ba na tsani mata kuma bazan zauna dasu ba dole ko wace ta kama gabanta" ya faɗa a hankali tare da lumshe idonsa tuno da DEEN ɗinsa mace ce ta haɗa makircin kashe masa Deen shiko ta Ina zai iya mancewa da mace, ganin tunani zai masa yawa ya sashi tashi yana shiga wani Coridor wanda zai sadasa da wani haɗaɗɗen Bedroom wanda bai cika wani karikitai da yawa ba makeken Bed ne guda ɗaya kawai sai Wardrope da mirror bethroom ya faɗa yayo wanka ya fito iya boxes ya kwanta dashi yana jan blancked ko 5 Minute bai yi ba bacci ya ɗauke sa *MUNEEBBA* tunda ta farka take faman zubar da hawaye tana motsi da bakinta Mamma dake Lazimi jin motsi ya sata juyowa tana lalube harta lalabo Hafsat dake kwance "Hafsat duba man Muneebba ce ta farka" ta faɗa tana ƙara lalabo gadon da Muneebba ke kwance, kallon inda Muneebba ke kwance Hafsat tayi tana murmushi da hawaye tace "eh Mamma ita ce" da gudu Hafsat ta fita tana kirawo wani Doctor Oxygen ɗin ya cire mata, hannuta Mamma ta kamo tana jin shesheƙar kukanta "Muneebba" Mamma ta Kira sunanta cikin dakiya "na'am Mamma" "MUNEEBBA ke ɗin musulma ce kinsan ƙaddara kinsan jarabta, ina son ki ɗauki dangana da haƙuri ki ɗorawa rayuwarki Muneebba duniya ba dukkan abinda kake so kake samu ba, zata iya yuwa abinda kake so ba Alkhairinka bane wanda baka so shine Alkairi, dukkan musulmi ana son ya zamto mai haƙuri kinsan kuwa shi kanshi haƙuri yana da ladarsa, sannan ki zamto mai yadda da ƙaddara da dangana, indai ni Mahaifiyarki ce Muneebba kuma ni na haifeki ina so ki cire Nazeer a ranki kisan cewa da igiyar aure a kanki Tunanin wani ɗa Namiji bai kamaceki ba dukda nima kaina na ɗanɗana gubar da kika lasa Muneebba sai dai har abada bana so kiyi rayuwar dani nayi, ina so kiyi rayuwar farinciki Muneebba, Muneebba dan Allah ki cire damuwar nan a ranki" tunda take maganar Muneebba ke kuka "Mamma kece kika haifeni Mamma nai maki Alƙwarin zan cire Nazeer a raina dukda shi so baya taɓa ciruwa sai dai ya ragu amma ni zanyi ƙoƙarin ciresa zan koyi son wanda igiyarsa take a kaina,sai dai ban san wace rayuwar zan gudanar ba a sabon littatafin kundin rayuwata, wane shafin sabuwar ƙaddarar zan buɗe? wannan ne ban sani ba Mamma, kuma ko ke nasan kina wannan tunanin" ta faɗa da sakin murmushin takaici mai ciwo "Muneebba kada kice haka ki yiwa kanki kyakkyawan yaƙinin jin daɗi a gidan Mijinki insha Allah wahalarku ce ta yanke saƙa" Hafsat ta faɗa tana shafa kan Muneebba, kallonta Muneebba tai tana faɗin "Hafsah akwai kingin rina a kaba" ta faɗa tana lumshe ido, yanzu ne take jin tabbas akwai wata gagarumar ƙaddararriyar rayuwa da zata gudanar, tabbas jikinta ya faɗa mata zata buɗe shafin kundin ƙaddararta ne sai dai ita yanzu komai ya sameta zata godewa Mahaliccinta dan haka yake son ganinta shiru dukkansu sukai har ɗan bacci ya ɗauke su, har sunso makara sallar Asuba,babu laifi jikin Muneebba da sauƙi, koda suka gama sallah sunyi Azhar da karatun Alqur'ani, a haka har gari yai haske rana ta fito zaune suke suna ɗan fira jefi_jefi wanda Muneebba ta ɗan saki jikinta, sallamar Mamma Ladiyo da maƙotan su Muneebba ya saka su maida hankalinsu a kansu, da azama Mamma Ladiyo ta ƙaraso tana kama hannun Muneebba "sannu ƴar nan kinji Allah yasa hakan ne mafi Alkhairi kinji kuna ganin Jarabta" ta faɗa da share hawaye dukkansu sunyiwa Mamma ya mai jiki sannan Rabi maƙociyarsu wacce gulma ta kawota tace "Ohh rayuwa kenan shi kanshi Nazeer ɗinfa tunda aka ɗaura auren ya faɗi wanda yanzu haka yana asibiti bai farfaɗo ba,ance saima an fitar dashi ƙasar waje yau zasu tafi don ko motsi bashi yi" ta faɗa da sigar gulma wacce ke cinta wani kalar dum gaban Muneebba yai ba zata iya jurewa ba ita ƙara ace ciwon ya hau kanta da gudu ta tashi ta nufi Toilet tana kullewa sakin shawa tai tana sulalewa ta fashe da wani matsanancin kuka mai cin rai sai da ta daɗe sannan ta wanke fuskarta ta fito wanda kallo guda zakai mata kasan cewa kuka tasha sai dai ganin babban Mutum kamili hakimce a gadon yana sakar mata murmushi ya sata sadda kanta ƙasa tana gaisar dashi a ladabce, Amsa mata yai yana sakin Murmushi gefe kuma ga Iftihar wacce take mata kallon raini da wulaƙanci tana tauna chewing gum yafitota da hannu yai yana mata nuni data zauna, ƙasa ta nemi waje tana zama kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta, haƙuri ya fara bata da kuma tabbatar mata zata gudanar da rayuwar farinciki daga bisani ya haɗa mata da nasiha mai sanyaya jiki wanda jikinta ya ƙara sanyi laƙwas,sosai ya kwantar mata da hankali wanda hankalinta ya ɗan kwanta ganin yadda Dad bai ɗauki girman kai ya ɗorawa kansa ba dukda matsayi da kuɗaɗen dake garesa wanda ita sai a Jarida ta sanshi batai tsammanin haka yake da son mutane ba, sai dai tana fatan ace kamar yadda yake haka kingin Ahalin nasa suke ya ɗan daɗe sannan yai masu sallama suka tafi wanda Iftihar kamar ta fasa ihu haka take ji, suna fita Mamma Ladiyo ta bisu da kallo tana jijjiga kai idanunta sun sauya kala ya zuwa ja, ganin komai zai iya faruwa ya sata ficewa daga ɗakin ta dinga tafiya harta nufi ƴar wata hanya cikin asibitin inda ba kowa tsayawa tai tana huci "me na aikata kenan? Wallahi da nasan haka abin zai kasance da ban hana auren ba wace mafita garan yanzu nasan dama guda gareni kuma nayi amfani da ita babu batun sake dawo man da ita yan ya zanyi? Muneebba ta tsallake tarkona, wallahi bazan taɓa bari A'ishatu kiyi rayuwar jin daɗi ba keda ƴarki" ta faɗa tana huci tare da zama tana tunanin mafita, ta daɗe kafin yanayinta ya dawo, da murmushi ta shiga ɗakin tana faɗin "wai ɗan zazzagaya marassa lafiyar nai kinsan ana son dubiyar marar láfiya, kai jama'a wasu mutanen na cikin hali wallahi A'ishatu ba kiga wata mata dana gani ba sai da na zubar mata da ƙwalla" ta faɗa tana matso ƙwallon ƙarya Murmushi Mamma tai tana faɗin "Allah sarki ai kin kyauta Mamma Ladiyo" koda Doctor yazo yaga jikinta yadda yai sauki sosai ya basu sallama, tattarawa sukai suka koma gida, nan mutane suka dinga shigowa dubiya akasarinsu gulma ce ke kawosu Wata ashariya Mom ta danna jin zancen Iftihar "ƴar talaka kika ce? Dad ɗinku ya rasa wacce zai aurawa sai ƴar talaka kuma ƴar matsiyata wallahi ba zata saɓuba" "saɓuwa kau taka tas da soso da sabili Naja'atu wallahi aure anyishi an gama babu wanda ya isa ya warwaresa muddin ina numfashi da rayuwata wurin zama kuwa tuni na tanadar mata ki shirya tarbarta a goben nan" Dad ya faɗa da ɓacin rai kallon baka isa ba Mom tai masa tana tashi fuuu ta bar wajen, Aunty Meera ce tabi bayanta kallonta Aunty Meera tai tace "Mom calm down mana kinsan dai kina da iko akan Bobbi ranar da aka kawota ma zaki iya sakasa ya saketa to name tada hankali" kallon ashe ba kida hankali Mom ta wurgawa Aunty Meera tana faɗin "Ameera wane iko garan akan Bobbi? banida wani iko akansa tunda har yaga kirana bai maido ba kuma yake ƙaurace man ki faɗa man wane iko nake dashi akan Bobbi" ta faɗa tana tauna leɓenta na ƙasa "koma dai miye Mom ki kwantar da hankalinki kisa yarinyar can kamar ta bar gidan nan" banza Mom tai da ita dan ita kaɗai tasan abinda ke damunta, shigowar Maheer da akwati a hannunta ya sata kallonta tana faɗin "Maheer ina zaki? "gida Mom" ta bata amsa a taƙaice tana murmushi "Maheer duk lallashinki da nai baki haƙura ba?" "Lah ko kaɗan Mom haka Allah ya tsara man can dama ba ni kaɗai bace Matar Yah Bobbi" girgiza kai kawai Mom tai tana tashi ta rakota har garden wajen Parking space shiga Maheer tai tana jan Motar wanda zuciyarta kamar ta rabe gida biyu haka take ji *YOLA* ************** *FATTU* duƙe take tana rizgar kuka kamar ranta zai fita "Baffalo ka yiwa girman Allah kada ka aura man Ja'e wallahi ban sanshi kisa fa yake a gabanmu fa ya kahe Haruna, nima ya ce zai kasheni" sandar dake hannun Baffalo ya rafka mata yana hankaɗata yace "Fattu ki shiga hankalinki baƙin cikin Shanayen da mai gari zai bani kike? da zaki ce ba kya auren Ja'e to aradun Allah ko mutuwa kika sai na aurawa Ja'e gawarki.......... [5/21, 8:12 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA* Book 1 *By Riamcool* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* *P.23&24* __________"Wallahi Fattu ba zakiyi man buƙulun arziƙi ba, arziƙi na biyoni kina masa dundu, ki sani aurenki da Ja'e kamar anyi an gama ne ko mutuwa zaki bazan fasa aurar dake ba" kallonsa take da rinannu idanunta tana girgiza kai bakinta na karkarwa alamun magana take so amma ta kasa koda furta A saboda baƙinci, da gudu ta tashi ta nufi bukkarta kuka tasha sannan ta miƙe tana fita, ta bayan gari tabi don bata son wani yabi sawunta ballantana har aga JODDi kai tsaye dajin ta nufa, dutsen da take hawa tai busa nan ta hau tana shesheƙar kuka har tayi mai isarta saukowa tayi tana bin dajin tana zagayawa tana tsigo da ƴaƴan itatuwa Kai tsaye inda tasan zata sameshi ta nufo zaune yake ya haɗa kansa da gwiwa wanda wannan ya zame masa Al'ada, murmushi tayi tana tunkaro inda yake da dariya, ɗago da fuskarsa yai yana kallonta wanda itama shi ɗin take kallo Zama tai tana ɗibar ƴaƴan itatuwan data tsigo tana bashi, sannan ta ɗauki madarar shanu tana basa, sai da ya ƙoshi sannan ya miƙe yana haɗe rai yana shiga bukkar da kallo ta bisa tana murmushi ta bi sa a baya,kwance yake rigar jikinsa a cire daga shi sai dogon wandon jikinsa ko ina ka kalla yana glowing dukkan wata sura ta jikinsa ta fito duk mace mai lafiya ta kallesa tabbatas sai taji wani abu a kansa lumshe manyan idanunta tayi tana jin wani abu na daban na ziyartarta tun daga ƙafafuwanta har ya zuwa brain ɗinta kallonta yai yana nuna ta da yatsa alamun magana yake so yayi amma ya kasa,dafe kansa yai yana ƙara sama da hannunsa, Fattu ganin halin da JODDi yake ciki ya saka hankalinta ya ɗan tashi ta nufosa,hannunsa ta kama tana saukewa sannan ta ɗago da fuskarsa tana ƙare masa kallo tare da lumshe masa ido,kallonta ya keyi kamar mai son tuno da wani abu ya haɗe rai yana fincike hannunsa tare da tu reta yana miƙewa ya fito daga bukkar,ƴar ƙara ta saki tana miƙewa tare da turo baki ta miƙe itama tana fita sai dai turus tayi tana ɗora hannu a ka da zaro ido waje ganin waɗanda suka kewaye JODDi da kuma makamai a hannunsu *MUNEEBBA* rungume take a jikin Mamma tana faman rizgar kuka fuskarta lulluɓe da mayafin Lifaya wacce ta amshi jikinta fari mai ratsin zanen Flower gold jinta take duniyar tai mata ƙunci ji take da mutuwa zata zo mata tabbas babu abinda zai hana tai taimaraba da ita,ranar data daɗe tana mafarki da son kasancewa a ɗakin mijinta yau ita ce tazo mata a yadda batai zato da tsammani ba, wanda taci burin tarewa a gidansa ba shine wanda Ubangiji ya rubuta a Alƙalamin ƙaddararta ba Kuka ta sake fashewa dashi tare da sake shigewa jikin Mamma,shafa kanta Mamma tai itama hawayen na son zubo mata amma tai ƙoƙarin hanasu tana ƙara rarrashin Muneebba tare da mata nasiha mai kwantar da hankali wacce ta ratsa jikin Muneebba ta kuma shirya zaman aure tsam a ɗakin mijinta tare da amsar ƙaddararta Ƙwallon da akai a tsakar gida shi ne ya janyo hankalin su Muneebba da kuma Mutanen tsakar gidan kallon jiga_jigan matan suke yadda ko waccensu ke taunar Chewingum fuskarsu sanye da Glass ko wace fuska ba fara'a ko annuri wata uwar Ashariya Aunty Meera ta ƙunduma tana faɗin "ban zaci baƙin talaucin ya kai har haka ba,ko a mafarki ban zaci zan shigo area irin wannan ballantana haɗa zuriya da irinku"ta faɗa wani tuƙuƙin baƙin ciki na cinta wani wawan tsaki Seemah ta buga tana faɗin "Amma Dad yaci mutuncinmu da kuma arziƙimmu ko a ƙaddararren mafarki ban taɓa tsammanin zan haɗa hanya da wannan cin mutuncin ba,ke dalla fito muje" ta faɗa tana faɗawa ɗakin da Mamma da Muneebba suke harda yunƙurin take ƙafar Mamma cikin takaici da tuƙuƙin baƙinciki Muneebba ta ɗago tana dubanta baccin rashin kunya ba halayyarta bace da babu abinda zai hanata ciwa matar nan Mutunci ,kauda kanta tai tana taune leɓe tare da saukar wasu siraran hawaye waɗanda ta rasa gane na miye Miƙewa Mamma tai tana dafa kafaɗar Hafsat wacce itama baƙinciki ya hanata magana, kama Mamma tai suna fitowa tsakar gidan wanda lokacin su Aunty Meera har sun wuce suna jiran fitowar su Muneebba Mamma Ladiyo ce ta shiga ciki tana kamo Muneebba tana ƙara gyara mata mayafin lifayar tare da sakin wani Munafukin murmushi wanda ba kowa ne zai gane ba,hannunta ta kamo tana fitowa da ita tsakar gida, ɗakin Mamma Muneebba ta shiga wacce ta tsirawa waje guda ido Alamun tayi nisa a tunani da fata Muneebba tai wanda ya saka ta dawowa duniyar tunanin data lula, murmushin dole ta ƙaƙalo tana mata wanda ya kashe jikin Muneebba, dubanta Mamma tai ta ƙara mata nasiha wanda ta dinga kuka,har sai da aka fito da ita, koda zata fita taga Yaya Khabir ta rumgumesa tana sake fashewa da wani irin kuka, kallonta Khabir yai yana rarrashinta wanda shima dauriya kawai yake kamar kada ta bar gidan haka take ji har suka fito daga gidansu da ƴan rakiyarta sai Hafsat, kasancewar lungun nasu ba wajen ajiye motoci ya saka su ƴar tafiya har suka fita bakin Titi wanda security ne tako ina, ga manya manyan Motoci na Alfarma ƴan ubansu baƙaƙe wuluk, guda biyar, cikin ta tsakiyar Muneebba ta shiga kingin kuma ƴan rakiya ta gaban kuma su Aunty Meera da Seemah ne a ciki, A hankali Motocin ke tsula gudu cikinsu sai ƙamshi da kuma wani ni'imtaccen sanyi mai ratsa gaɓukka, a hankali ta runtse idonta ƙirjinta na mata wani nauyi wanda kamar an saka nannauyan dutse an danne mata shi haka take ji,ji take a yanzu ne shafin littafin kundin ƙaddararta ya buɗe, ta gaza fitar da Nazeer a cikin ranta,wanda tuno halin da yake cikin shine ke sakata kokowa da ɗaukewar Numfashinta,rufe idonta tai wasu hawaye masu ɗumj na sauka a kuncinta Wata haɗadɗiyar Anguwa ta jiga_jigan manyan masu kuɗi suka nufa tun daga get ɗin farkon shiga Unguwar kansa abun kallo ne, ƙerarrun gidaje ne haɗadɗi kai kace a ƙasar London aka ƙera su, ko a London sai ka amsa sunanka zaka iya kera gidaje irin wannan,ba zaka taɓa cewa a Nigeria akwai Anguwa irin wannan ba,zamanta sai shahararren mai kuɗi da jiga_jigan ƴan siyasa masu amsa sunansu da kuma manyan shahararrun ƴan kasuwa gidan da yafi tsari da haduwa nan suka nufa inda driver ya Danna Remote nan take Makeken Get ɗin farko ya wangale,ga samudawan sojojin dake ta muzurai suna tsaye sun kame a wajen Wani kalar dum gaban Mamma Ladiyo yai lokacin da taci karo da kalar gidan yadda get ɗin farkon kansa kamar ka shiga a wata duniya ta daban sbd haɗuwarsa da tsaruwarsa get na biyu suka tunkara inda zuciya ta kawowa Mamma Ladiyo iya wuya, gani kanshi get na biyu yanda yake wani sheƙi da walwali kamar da zallar Zinare aka kerasa,ga wasu kalar samudawan Security da suka kame a wajen, ɗaya

Chapter 5 of 10