gadon Shitu na raƙumma dukta cinye, har Shatu ta fara girma bata canza zani ba, don Ai'shatu tafi kowa cin wuyar Ladiyo, ganin a ɗan kwai sauran dukiyar Shitu yasa Ladiyo ƙwaceta suna bin ƙasa_ƙasa suna kasuwancin siyar da dabino,
A hankali take tafiya cikin Sahara ranga_ranga kamar zata faɗi, saboda zafi da ranar da ake ƙwalawa,ga ƙishin da take ji wanda shine ya ida tagayyarar da ita, so take ta tsaya ta huta amma babu halin hakan saboda wata matsananciyar rana da ake ƙwalawa,ga yashin sahara kanshi ya ɗauki zafi, bare ta zauna ta huta,ga fitinannanen ƙishin daya addabeta wanda shine ya ida galabaitar da ita da yunwar dake ƙwaƙwular hanjin cikinta, a haka harta iso inda mahaifanta suka yada zango,sun kafa runfa a wajen
A galabaice ta iso wajen tana kamfatan ruwa domin ta kai a bakinta, kofin dake hannunta taji an kwaɓe ruwan ya zube a ƙasa, kallon ruwan take yadda ƙasan wajen ya shanye,kuma tayi imani waɗannan ruwan da suka zube ba lallai ta sake iban waƴansu tasha ba,
hawaye taji ya cika mata ido ɗago da fuskarta tayi tana duban iyayenta waɗanda suka kauda kansu a gefe guda suka nuna kamar ma basu ga abinda Yaya Ladiyo ta aikata ba, durƙusawa wajen tayi tana share hawayen da suka samu damar gangarowa a kuncinta, a hankali ta samu waje ta sulale tana mai ƙara jin yadda maƙoshinta ya ƙara ƙafewa yana buƙatar ruwan da zai shiga a ciki
gashin kanta taji Mamma Ladiyo ta kamo tana jansa da ƙarfi,wanda ya sakata ƙwalla uwar ƙarar azaba, mari taji ta kira mata tas, wanda yasa fatar wajen tai jajir shatin hannuwa ya fito ruɗu_ruɗu
cikin ɓacin rai Mama Ladiyo ta dubeta tana faɗin "Shatuwa tun yaushe kika fita saido hatsi a cikin gari? tunfa jiya kamar yanzun tunda kika fita baki dawo ba sai yanzun, ki faɗa man wajen uban wa kika je ya ƙwaƙuleki, jibi yadda Nonuwanki suka sakaka duk an latse su" ta faɗa tana sake faska mata wani marin wanda yasa bakinta fashewa
mahaifanta kuwa sun sadda kansu ƙasa, duk wani mari da Ladiyo tayi mata sosai yake sake sake tsarga musu zuciyoyi, basu da wani halin yin magana don mugun shakkun Mamma Ladiyo da suke ji,
ita kam A'ishatu wani marayan kuka ta saki tana mai dafa ƙafar Mamma Ladiyo tace "Mamma Ladiyo dan Allah kamar yadda Allah ya temakeki nima ki taimakeni ki bani ruwa da Abinci idan ba haka ba mutuwa zanyi,kuma na rantse miki da Allah ni babu Namijin daya taɓa taɓa man koda ɗan yatsa" ta faɗa da ƙara fashewa da wani irin marayan kuka wanda da kajishi kasan mai yinsa yana fitar da ɗaci da kuma raɗaɗin zuciya ne
Ƙafa Mamma Ladiyo tasa tana shure A'ishatu sannan ta ɗaga hannunta mai kama da diga ta ɗaka mata duka a baya wanda yasa cikinta wani irin juyawa bayanta ya riƙe daga duƙen da take ta dinga sheƙa Amai wanda har ta hanci saida ya dinga biyowa dukda ba komai a cikin sai wa ƴansu korayen ruwa da take amayowa kai kace zata zubda ƴan cikinta
wani shurin Mamma Ladiyo ta ƙara kai mata wanda yasa numfashinta tsayawa cak idanunta sun wani ƙaƙƙafe, da gudu Mahaifanta suka yo kanta suna kuka wanda kallo guda Mamma Ladiyo tai masu suka janye idonsu daga gareta hawaye na bin kuncin Maman A'ishatu Mariya
jawota tayi yadda ta sume ta sakata cikin yashin saharan wanda cikin iyayenta ba wanda ya iya magana ko wane abin na ci masa rai
A hankali zafin rana ya fara dukanta wanda kamar ya gasata buɗe lumsassun Idanunta tayi ta ganta cikin rana yashe jikinta na mata tsami ta miƙe tana duƙawa a inda take, don tasan babu damar shiga tantin da suka kafa, don Mamma Ladiyo ba zata barta ta shiga ciki ba koda kuwa Mutuwa zatai hakan yasa ta zama cikin ranar wani masifaffen zazzaɓi na rufeta har dare yayi tana makyarkyatar sanyi wanda yasata yin baccin dole sai safe ta farka
A hankali ta buɗe idonta ta miƙe jiki ba ƙwari abinda ta gani ne da kuma Ihun Mamma Ladiyo da take ji ya sakata ware ido tana ƙara duban jinin data gani malale da gudu ta miƙe ta shigaTantin sai dai tana shiga turus tayi tana ƙara ware idonta ganin Iyayenta kwance anyi musu yankan Rago ga Mamma Ladiyo zaune tana sharce hawayen ƙarya wata kalar ƙara A'ishatu ta saki tana sumewa, ganin haka Mamma Ladiyo zuwa ta ɗauko ruwa ta malaya mata don karta zargi wani abun, don kuwa Mamma Ladiyo ce tabi dare taiwa su Malam Shitu yanakan Rago, koda Shatu ta tashi haka ta dinga jan ajiyar zuciya tana saukewa dan ko kukan ya kasa fita sai dai bin ko ina da kallo da take yi, ganin haka Mamma Ladiyo ta rarrasheta tace mata ɓarayi ne suka zo suka yanka su saboda kuɗaɗen dake garesu da suka ƙi badawa, ita kuwa ta bada nata harda na fansar A'ishatu shi yasa basu kashesa ba
ko kallonta Ai'shatu ba tayi ba hakan yasa Mamma Ladiyo fita cikin gari ta samo waɗanda zasu sallaci Shitu da Mafiya, A'ishatu naji na gani aka binne iyayenta
haka rayuwa taci gaba da tafiya ba wani sauyi, illa sauyin Azaba daya ƙara nunkuwa wa Shatu,
haka rayuwa ta tafiyarwa Shatu wanda Mamma Ladiyo tun sadda ta kashe su Shitu ta tattara suka koma Kaduna da zama, can take sana'ar siyar da Abinci tana ɗorawa Shatu talla sannan da dare ta ɗora mata tallar goro, wanda ƴan iska sukai wa Shatu caaaa ko wane da baƙin ƙudirinsa a kanta, wanda sai dai A'ishatu tai kuka ta share hawaye tana ƙara kaiwa Allah kukanta
ganin yadda ɓata gari ke kawowa Shatu farmaki yasa Mamma Ladiyo jin daɗi hakan yasa ta ƙara kaimi wajen ɗora mata tallar dare kuma idan bata saido shi ba haka zatai mata shegen duka kuma ranar sai tayi mata tsarki na kwaɓaɓɓen barkono
Wannan kenan
A dage da comments
*By Riamcool Star of the Squad*
[5/21, 8:08 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA*
*Book 1*
*By RIAMCOOL STAR Of the Squad*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
Bismillahirrahmanirrahim
*P.9&10*
_________✍️Haka taita gallazawa Shatu azaba kala da kala, da daddare idan ta fita talla goro haka zata daɗe bata saido ba wanda kowa zai siya saiya nemeta da iskanci ita kuma taƙi,hakan yasa take cinɓun goro kuma idan ta koma ba zata canza zani ba daga azabar Mama Ladiyo
Tunda ta taho take sharan hawaye don tasan muddin ta koma da goron da bata saido ba sai Mama Ladiyo ta ninka mata azaba fiye data kullum dama da zata fito saida tai mata jan Warning saboda rashin saido goron dare ko abinci tabar bata, sai dai tabi dare ta kankari ƙanzon tukunya tasha ruwa ta kwanta
tayi nisa cikin tunani ga dare daya fara ritsawa taji an rufe mata fuska an ɗauke ta ihu take son yi amma babu halin haka saboda rufe mata fuska da akayi, wani kango suka kaita suna ajiyeta wuf tayi ta mike tana cire abinda suka rufe mata fuska dashi kwaɗa mata Mari ɗaya yayi wanda ya sata kwala ihu da ƙarfi, fusata ɗayan yayi ya ƙara faska mata wani marin yace "don ubanki yi mana shiru uban wani yasa iyayen naki su doro miki tallan dare? to wallahi ba zamu iya maida kwaɗayimmu ba dole sai mun tasta ki" ya faɗa yana zuge mazagin wandonsa
Ihu ta ƙara fasawa cikin gunjin kuka mai cin rai tace "dan Allah bawan Allah ka dubi girman Allah ku ƙyaleni wallahi ni marainiya ce kada ku yaga man mutuncina da darajata" ta faɗa tana sake fashewa da wani irin masifaffen kuka
tunda ya doso wajen yake jin kukan mace cikin kango na tashi sharewa yayi zai wuce sai kuma yaji ba zai iya ba hakan yasa shi kutsa kai cikin kangon, turus yayi yana kallonsu da ɗai_ɗai ganin ɗaya daga cikinsu yana kokarin yaga mata kayan jikinta tana roƙonsa wata zuciya ce ta ciyosa ganin yadda Mutumen ke ƙoƙarin keta mata haddi, nufar wajen yayi yana kaiwa wancan bahaggon naushi wanda yasa shi ƙwalla ƙara har haƙoransa biyu na zubowa, ganin haka wancan ɗayan da gudu ya taketa ya fice, cikin ɓacin rai Mahamud ya shaƙo wuyan rigar wancan yana naushi sai da ya haɗa masa jini da majina sannan da ƙyar ya ƙwaci kansa ya gudu, ita kau Shatu ta rakuɓe waje guda tana gunsheƙar kuka, a hankali ya tako gareta cikin takonsa mai cike da izza ya nufota yana faɗin "miƙe" babu musu ta miƙe suna fitowa daga kangon, tana fitowa taga yadda tiren goron duk ya watse wani kukan ta sake saki tana faɗin "na shiga ukku nasan na koma wallahi sai ta kusa kasheni ƙara karna koma na kwana anan" ta faɗa da wani sabon tashin hankali wanda ya bayyana ɓaro_baro a. fuskarta, da mamaki yake kallonta ya tambayeta akan me take magana, nan ta kwashe komai ta faɗa masa da kalar azabar da zata fuskanta idan ta koma
girgiza kansa yayi yana cije lips ɗinsa na ƙasa yana mamakin mugun halin wasu mutane cikin tausayinta ya tambayeta goron na nawa ne, ta faɗa masa na 1k ne, hannu yasa Aljihu ya zaro 3k yana miƙa mata
zaro ido tayi tace masa ba zata karɓa ba, wanda da ƙyar ya samu ta amshi 1k da kanshi ya talata gida wanda har Mamma Ladiyo ta kulle gidan tana baccinta hankali kwance, cikin bacci ta taso ta buɗe mata tana shiga ta maida gida ta rufe tana jawo hannu A'ishatu tare da ɗakko wani makeken faskare ta miƙo mata hannu tace "bani kuɗin goron kada ma kice man wani abu ya bata a ciki dan tsab zan iya bazar dake anan ki mutu ubankowa ya huta" jikin Shatu na kyarma ta fito da Naira dubun ta bata wanda ya sata washare haƙora tana amshewa ta miƙe, babu tuhumar inda ta tsaya har dare yayi, tashi tayi ta tafi ta kwanta, ita kam A'ishatu sai da Mama Ladiyo tai bacci sannan tabi dare tana kankare ƙanzon tukunya taci tasha ruwa ta kwanta
tunda sadda A'ishatu suka haɗu da Muhammad yake jin bala'in tausayinta hakan yasa da yaga ta fito tallan goro zai mata juye ya bata kuɗin ta koma gida wanda yaiwa Mama Ladiyo mugun daɗi don a tunaninta iskanci Shatu keyi tana siyar da goron, yau da gobe shaƙuwa ce mai karfin gaske ta shiga tsakanin Muhammad da Shatu wanda harya kaisu ga faɗawa soyayya mai ƙarfi wanda hankalin Shatu ya fara kwanciya, nan take ya ɓullo mata da son aurenta zaiyi ta biyu da ita don yana da Mata harda yaro guda, ba tare da wata nuna damuwa ba ta amince masa sai dai matsalarta guda a lokacin ita ce Mama Ladiyo, wanda tunda ta tunkareta da maganar aure Mama Ladiyo tai mata jan Warning akan ta rabu da Muhammad ba shine mijin daya dace da ita ba don ta riga tai mata Miji ɗan Aminiyarta Jimmai wani ɗan shaye_shaye ne, kuka sosai Shatu tayi tana roƙon Mama Ladiyo akan ta barta ta auri Muhammad amma fir taƙi saima horon kulleta a ɗaki da tayi ta ɗaureta da sarƙa wai damma kada ta gudu
shi kam Muhammad tun sadda Shatu ta faɗa masa abinda Mama Ladiyo tace hankalinsa yai mugun tashi, babu yadda baiyi ba har da kanshi yaje gun Mama Ladiyo don ta barshi ya auri Shatu amma fir taƙi saima ƙarin cin mutunci da tayi masa
*wanene Muhammad*
Muhammad ɗa ne ga Alhaji Alhassan mai gwalagwalai Mahaifinsa mashahurin mai arziƙi ne inda ya auri Mahaifiyar Muhammad Hajiya Zinatu wacce babu ruwanta suna zamansu lafiya da mijinta harta haifi Khadijah ita ce ƴarta ta farko sannan ta haifi Sagir sannan Abdulkarim sannan autanta Muhammad wanda shima yai karatunsa har yai digiri ɗinsa, sannan ya auri Mansura wacce ita ce ta liƙe masa harya aureta suna da ɗansu ɗaya, haɗuwarsa da Shatu ita ce ta fara sauya masa rayuwa ta maida shi mai son jama'a da son taimakon Al'umma ta maida shi mai wasa da dariya ga dukkan wanda ya gani cikin ƙunci, ya faɗa cikin tarkon sonta da ƙaunarta haka zalika da son kasancewa da ita yai kwaɗayin zama da ita,ya bata ilimin da bata samu ba, wanda kullum cike yake da mafarkin son kasancewa a tare da ita sai dai kash Mama Ladiyo ta riga tai mai katanga da dukkan wani cikar burinshi akan Shatu, ya shiga cikin damuwa sosai harya kai ga ko walwala ba yayi
ɓangaren Shatu ma haka yake kullum cikin kuka take wanda ta ida lalacewa tai baƙi ta ƙara rama, amma a haka Mama Ladiyo babu tausai ta saka Sati guda da bikin Shafu da Idi ɗan Jimmai, hankalin Shatu ba ƙaramin sake tashi yayi ba, tana ji tana gani aka ɗaura mata aure da Idirisa wanda taci kuka ta tabbatar data riga ta rasa gatanta iyayenta, haka aka kaita gidan Idi wanda shima ya ƙara zame mata baƙin kurkuku wanda kullum cikin cin dukan Idirisa take ga cin zalinta da yake dan ko kwanciyar aure sai dai ace fyaɗe yake mata wanda ta ƙara lalacewa sosai ga shaye'_shaye da yake wanda har giya yake sha idan ya shawo haka zai zo ya malaya mata Amai a yace kuma dole sai ta shanye sa,idan taƙi yai mata ɗan banzan duka da taji wahala haka ta gudu ta koma gidan Mama Ladiyo ta faɗa mata komai, amma sai Mama Ladiyo tace mata tayi haƙuri ta komawa nan ai shine zaman auren haka Mama Ladiyo da kanta ta tisa Shatu ta maida ita gidan Idirisa, Abinci kanshi Idirisa bai damu daya bata ba, ganin yunwa zata kasheta yasa ta dinga bin makwabta tana amso wankau tana masu ,wasu tai masu wanke_wanke shine zata samu ɗan Abinci, randa kuma babu ta kwana da yunwa, ta samu ciki ya kai biyu amma fyaɗe Idirsa shike zubar da cikin..........
By Riamcool Star of the Squad
08109554986,only call
[5/21, 8:09 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA*
*Book 1*
*By Mariam sani Riamcool*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
Bismillahirrahmanirrahim
*P.11&12*
__________✍️Wahala ba kad'an take sha ba ta shirya guduwa sau ba adadi amma sanin bata da inda zata yasa ta haƙura a haka har suka cimma shekaru biyu da aure tana cikin uk'uba duk ta ƙara lalacewa idan ka ganta ba zaka taɓa cewa Yarinyar mace bace kuma wacce bata tab'a haihuwa ba,haka zalika dukda ni san da Muhammad yai mata zuciyarta bata taɓa mancewa dashi ba koda da second guda ne
kullum cikin kuka take da fatan mutuwa, wata ranar Alhamis tana zaune lokacin Idirisa yayo shaye_shayensa yazo yai mata mugun duka sannan ya had'a mata da saki ukku cir,ba ƙaramin farinciki tayi ba na rabuwa da k'addararren auren, sai dai tunawa da Mamma Ladiyo yasa murna tata komawa ciki dan tasan ta koma za'a dasa aya daga inda aka tsaya don muguntar Mamma Ladiyo ba zata canza zani ba, koda taje ta faɗa mata abinda ya faru, ga mamakinta sai taga tayi murmushi tana lallashinta abin sosai ya d'aure mata kai sai dai tasan wannan murmushin na Mamma Ladiyo ba Alkhairi bane gareta, hakan yasa taci gaba da neman tsari gareta, wani abinda ya ƙara d'aure mata kai bai wuci yadda take bata Abinci akai akai ba, don tun tana tsoron kar tasa mata guba abinci harta dayaye take ci, amma bata saki jiki ba, wani k'arin abinda ya d'aure mata kai harta yarda Mamma Ladiyo tuba tayi shine kukan da take fashewa ta nemi gafararta, wani mugun dad'i Shatu taji ganin cewar Marik'iyar tata ta dawo daga daga rakiyar shed'an wata kalar tarairaya take sha don harta kammala Idda amma Mamma Ladiyo bata d'ora mata talla don Mamma Ladiyo kud'i tayi sosai wanda ta rasa ta inda take samunsa ga fitar daren da takeyi kullum hakan yasa ta dasa mata ayar tambaya da bincikenta a b'oye amma bata gano komai ba
tunda A'ishatu ta gama idda take zuwa inda take tallan goro a da wai ko zata ga Muhammad amma shuru kakeji tayi kuka don tasan ta riga da ta rasashi
Zaune take fatar nan tata data yamushe a baya yanzu tayi luwai saboda cimar da take samu wajen Mamma Ladiyo hakan yasa ta ƙara fitowa shar da ita fatar nan tata ta buzaye kamar ka latsa jini ya fito, sanye take da wata Atamfa ja mai ratsin yellow riga da zani wacce Mamma Ladiyo ta d'inka mata, fitowar Mamma Ladiyo da shirinta na Alfarma yasa ta maida hankalinta wajen Murmushi Mamma Ladiyo tai mata tana shafa kumatunta tana kallonta da ƴan jajayen idanunta kamar na Mayu harshe ta fiddo sai dai tunawa da wani abin yasa tai control d'in kanta tace "am ki zauna zanje wani bikin d'an k'awata kila na dawo yau ko kuma gobe" ta faɗa tana ficewa da sauri don jin idan ta tsaya ba zata iya dakatar da kanta daga umarnin zuciyarta ba
da kallo kawai A'isha tabita zuciyarta na harbawa da sauri tana faɗin Allah yasa kar zarginta ya tabbata don ta tsorata da yadda idanunta sukai ja da tana kallonta hawaye ta share tana zama, sosai ta lula cikin tunani har yaro ya shigo yana sallama bata ji ba sai da yai mata ukku sannan firgigit ta dawo tana tambayarshi me za'a bashi
"Ance ana sallama da A'ishatu" da mamaki take kallon yaron don tunda take babu wanda ya tab'a cewa yana sallama da ita idan ba Muhammad ba kuma tasan shi ya riga da yai mata nisa
"Kaje kace ba nan gidan bane" ta faɗa tana shigewa d'aki ba da daɗewa ba saiga yaron ya dawo yace "wai ance nan ne ki fito ki ganshi"
Ƙaramin tsaki taja tana dauko mayafi ta yafa ta fita sai dai ganin dalleliyar motar dake wajen ya sata zaro ido don tasan anyi b'atan kai ba dai wajenta ba juyawa yayi da nufin komawa taji an rik'e mayafinta k'amshin da taji da bugawar zuciyarta ya tabbatar mata da ko waye a hanzarce ta juyo tana kallonshi yadda ya kafeta da ido yana sakar mata da wani lallausan murmushi ita kuwa k'a waro masa manyan idanunta take don tabbatar da shi d'inne hawayen da take riƙewa ne suka samu damar sauka a kuncinta a hankali yasa hannu yana dauke mata su, "haba Aysher ki daina kukan nan haka nan kinsan fa a halin yanzu ke babba ce da da rabo da kin ajiye babba kamata" ya faɗa da sigar zolaya
ba shiri tai dariya tana k'ara kallonsa tana matsa yatsun hannunta wanda yasha ƙunshin ja, "Ina ka shiga?" ita ce tambayar da taji ta fito a bakinta wani murmushi mai ciwo yayi yana share zancen da jawo mata wata fira, itama ganin bai bata amsa ba yasa ta share, a wannan karon ma ya ƙara mata maganar aure wanda zuciyarta taji ta tsinke don tana gudun Mamma Ladiyo ta ƙara yi mata auren dole wanda ba zata jura ba k'ara ta gudu tabar gidan da ta rasa Muhammad a karo na biyu
ha sukai sallama jikinta a mace yake tana cikin zullumi, kwanciya tayi tana sak'e_sak'e a ranta bacci ya fara d'aukanta taji ana lashe mata fuska wanda firgigit ta buɗe idonta tana kallon baƙar magen da ke tsaye tak'i matsawa ta kafeta da idanunta juyayi tana fito da jan harshenta tana tand'e bakinta, Addu'a take son yi amma ta kasa da ƙyar ta samu taja wata Addu'a wacce yasa magen ja da baya tana mata Murmushi sannan ta jijjiga kai ta haura katanga,wata kalar zufa ce ta dinga tsatsafo mata cikin tsoro ta samu tayo Arwalla tayi salloli tare da Azkhar har bacci ya ƙara kwasheta
da safe Mamma Ladiyo ta dawo ganin jikin A'ishatu na kyarma alamun zazzaɓi ya sata tunkararta tana tambayar ta abinda ya sameta cikin tashin hankali, magani ta bata tasha ta gasa mata jikin
haka ta kwana biyu sannan ta warware ga Muhimman bai dawo ba,zaune take tana matsa hannunta bakinta na motsi alamar son ta yiwa Mamma Ladiyo magana, lura da hakan yasa Mamma Ladiyo fad'in "faɗi maganarki mana ƴata naga har yanzun kamar baki ida sakin jiki dani ba"
murmushi kawai tai mata cikin shakku ta faɗa mata yadda sukai da Muhammad, a mamakinta murmushi tayi nan take ta amince ta kuma nunawa Shatu jin daɗinta
sai da akai sati Sannan Muhammad ya dawo wajen Shatu ba ɓata lkc ta faɗa masa amincewar Mamma Ladiyo wanda yai murna kamar ya taka rawa haka yake ji, ba ɓata lokaci ya turo magabatansa aka tsaida ranaku wanda iya Sati aka saka, sati na zagayowa aka ɗaura auren A'ishatu da Muhammad wanda faɗa maku irin farincikin da masoyan suka shiga ɓata baki ne, wani satin na zuwa ta tare a katafaren gidanta wanda Part biyu ne nata saina Mansura sosai suke zuba soyayya wacce a gaban kowa basa jin kunyar nunawa junansu ita
haka sosai dangin Muhammad suke nuna mata harma da Abokiyar zaman ta Mansura wacce ta riƙeta da Amana, da kanshi Muhammad ya samo mata mai koyamata karatun Addini dana zamani, a haka har suka kwashe tsawon shekaru biyu A'isatu na samun ciki yana ɓarewa, wanda anyi na Asibiti dana gida amma babu sauyi, don duk lokacin data samu ciki haka zatai mafarkin magen nan wacce ta taɓa gani tana zaƙulo ɗan cikinta tana cinsa, da tashi cikin jikinta ke zubewa
da ƙyar aka samu cikin ikon Allah ciki ya tsaya a jikinta harta haifi Kyakkyawan yaronta mai kamar ubansa wato Khabir wanda duk wata kulawa tashi tana hannun Mansura, haka Habib shima yake kula dashi tamkar wanda suka fito ciki guda
sai da yai 7 years sannan A'isha ta samu wani cikin inda ta haifi ƴarta mace sak ita ta biyo, ranar suna yarinya taci suna Muneebba, wanda Muhammad yayi bajinta yai hidima tamkar bai san ciwon kuɗi ba, don tun ranar da Muneebba tazo duniya yake jin sonta daban a cikin yaransa, bayan kwanaki kaɗan itama Mansura ta haifi ƴan biyunta Mata waɗanda suka ci suna Hanifah da Sharifah, haka rayuwa ta gangara har Muneebba ta cika 3 year
misalin ƙarfe biyun dare gudu yake sosai harya ƙaraso Part ɗin A'ishatu yana zuwa ya saɓi Muneebba yana tashin Mamma, (wato A'ishatu) a firgice ta miƙe zatai magana ya rufe mata baki ya tado Khabir, a galabaice ya buɗe get ɗin gidan yana Aman jini haka yaja hannunsu suka dinga gudu har suka isa wani wajen Motar da yai parking shiga sukai ya fizgesu Ita dai A'ishatu ta kasa magana illa binshi da ido da take dan ta kasa gane me ke faruwa, ga bakinta yai mata nauyi ta kasa furta kalma koda guda ce wanda take ji tamkar an datse mata baki ne, tun dare suke tafiya sai gab da Asuba suka shigo garin Kano wanda ya saukesu a wata tshohuwar unguwa ya bata maƙuddan kuɗaɗen, ganin da gaske tafiya zaiyi ba mafarki take ba ya sata riƙo rigarsa ta baya wasu hawaye na bin kuncinta, shima kallonsu yake yana hawaye "ba nida zaɓi ne Aysher illa hakan, shine zai baku damar tsira da rayuwarku tabbas rayukanku na cikin haɗari, ba don ina so zan nesanta kaina daga gareku ba, saduwar Alkhairi" yana gama faɗin hakan ya janye hannunta yana shiga Motar ya wuce
durƙushewa wajen tayi ta fashe da kuka, da ƙyar ta rarrashi kanta har, tayi shiru.
kasancewar unguwar da jama'a yasa ta nemi temakon Jama'a ganin hada yara yasa wani Alhaji Mamman temakonta ta zauna a gidansa har saida ya samo musu gida da kansa, wanda ɗan zamanta a gidan tasha tsangwamar Maman Nazeer wato Matar Mamman wanda ko ɗanta yazo wajen Muneebba da zummar yi masa wasa zata dinga masa faɗa wani sa'in harda duka amma bai daddara haka washe gari zai ƙara zowa gun Muneebba da Khabir
Bayan sun dawo gidan sosai abubuwan suka rincaɓewa A'ishah Abinci kanshi na neman gagararsu sai wanda yaga Allah zai taimakesu a hakan ta saka ƴaƴanta makaranta, wanda tun dawowarsu taji mutane na faɗin wai wani yazo ya faɗawa mai unguwa a tada ita don ƴar bariki ce ƴaƴanta ma duka a hanyar bariki ta samesu, nan danan unguwar ta ɗauka wanda taci kuka sosai ta kuma daɗe kunnuwanta dana ƴaƴanta, sosai rayuwa ta ƙara juyewa Mamma a ciki kuwa harda makantarta wacce ta wayi gari kawai ta ganta taje anyi maganin amma duk a banza, ganin bata da isasshen