da yaci ya nemi dawo masa, ba arziki ya fito dashi daga bakinshi, sai kuma tunanin inda zai saka shi ya dinga masa yawo, cikin hanzari ya mike kamar zai kifa yana ficewa ya tura kyauren gidan ya jefa shi ya dawo ya zauna, lemon daya ajiye ya dauka ya kwankwade saboda zuciyarshi da taketa hargitsawa
Gabaki daya ba haka ya hango yau din ba, sai yakejin inama jiyan yazo, ya tabbata abinda ta shirya masa jiya yafi na yau nesa ba kusa ba, kawai dai ita din da kuma kwalliyarta ne suka danne masa rabin disappointment din, sai gata ta dawo dakin da sallamarta tana dorawa da
"Afuwan Habibi, kasan Matar Officer na gidan, yau nan tayi buda baki, nasan yanzun mijinta zaizo daukarta, akwai ajiyarta a wajena"
Matar Officer kamar yanda Aziza take kiran Yayarta Jalila dashi, daga Jalilar sai ita, tazarar shekaru biyu ce a tsakaninsu, sai dai Jalilar tayi aure da wuri, dan yanzun haka ma yaranta uku. Kuma daga yanda Aziza take yawan maganarta, akwai shakuwa mai karfi a tsakaninsu
"Haba ni da kin gama cikamun cikina, ga aiki na baro a shago, anya ma zan iya asham yau?"
Sai tayi dariya ta karasa cikin dakin sosai tana zama a gefenshi
"Baka cinye ba, ga cheese balls dinma baka cinye ba, kuma saboda kai nayi"
Ta karasa cike da rashin jin dadi a muryarta
"Cikina ya cikane sosai, naci daya dan yayimun kyau a ido"
Sai ta dan saki fuska
"Aikam sai in juye maka ka tafi dashi"
Baiyi musu ba, wannan ai mai sauki ne saiya cillar dashi a hanya koya samu wani almajiri ya bashi. Koma wanne abu dai, hira suka dingayi cikin nishadi. Ana fara kiran sallah yace mata
"An kiramu"
Ta turo baki
"Bangaji da ganinka ba"
Murmushi yayi
"Ni akace na gaji da ganinki ne? Gashi da wahala in sake samun damar zuwa kafin sallah idan Allaah Ya kaimu"
Aikuwa tayi kwal-kwal da idanuwa har yana hango kyallin hawaye a cikinsu, duk yaji ya susuce
"Kar muyi haka dake Babe, ga waya fa, ga video call"
Hawayen ta bari suka zubo
"Wanne video call? Abinda daka shiga gida baka yarda muyi saboda matarka, bayan nima yanzun ina da hakki akanka tunda ai aurena zakayi..."
Da sauri yace
"Inji wa ya gaya miki saboda ita ne? Nifa na isa da gidana, abinda nake so shi zanyi"
Aziza taja hanci tana kara narke masa
"To me yasa idan na kiraka baka dagawa? Aiko ba zakayi magana ba saika daga in ganka"
Ya jinjina kai
"Zan dauka, shikenan? Dan Allaah ki share hawayen nan bana sonsu"
Duk da haka saida ya kara bata lokaci yana lallashinta da yi mata alkawura kala-kala duk da yaji an tayar da sallah. Ya ajiye mata dubu goma cifa, sababbin yan dubu-dubu. Yaji dadin yanda ta manta da hadashi da wannan cheese ball din. Daya fito ne ma sukayi kicibis da Jalila tana tsaye, bayanta goye da karamin Jawad, sai Jabir da Jafar da suke gefenta, ga wata katuwar leda data ajiye a gabanta, zuciyar Aziza ta tsinke, kar dai har yanzun Balarabe baizo ya daukesu ba
"Habibi ga Adda Jalila ku gaisa"
Cewar Aziza cikin karfin hali ganin idanuwan Baffa akansu ya fara sauka, ta kalli Jalilan tana fadin
"Matar Officer ga Habibina"
Duk da Baffa yasan ya girmeta haka ya dan rage tsaho yana gaishe da ita, ta amsa shi fuska a sake
"Kinga kila ma ciki zan koma, yanzun Officer ya kirani wai kaman ya taka abune tayarshi tayi faci"
Jalila ta fadi
"Babur din Baba ne yayi faci?"
Jabir ya fadi yana kallonta cikin maganarshi da bakowa bane yake ganewa, Aziza tayi saurin kallon Baffa da alama baiji abinda akace bama, dan hankalinshi naga masallaci da har anyi raka'ar farko, tunda da alwalarshi yacewa Aziza
"Bari kiga inyi sallah kafin in wuce, lafiya kalau mashin dina idan na barshi anan?"
Kai ta daga masa da sauri, dan unguwarsu tana da tsaro sosai duk kuwa da yawansu, akwai karancin sace-sace musamman irin wannan lokacin ma da jama'a suke hada-hada. Baffa na shigewa tana juyo karar mashin din Balarabe tun daga kan kwanar layinsu kamar babu salansa a jiki, suka hada ido ita da Jalila cike da takaicin da har yau basu daina shakarshi akan wannan mashin din nashi ba. Saikuwa gashi nan ya karyo kwanar, kana hango sabon uniform dinshi shar
"Officer take aure ashe, soja ne ko dan sanda?"
Baffa ya taba tambayarta da tace masa tana gidan Jalila din tana kiranta da Matar Officer, farko-farkon haduwarsu, babu shiri ta katse hirar da fadin
"Minti daya Habibi"
Ta kashe wayar, tunda ai ba zata sharo masa karya ba, idan aurenta zaiyi dole wannan likon zai cire, ta ina zata fara ce masa Balarabe dan karota ne?. Ko gaisawa bata tsaya sunyi ba, dan kafin ya karaso ta cewa Jalila
"Adda sai munyi waya"
Ta shige gida abinta. Baffa kuwa ana sallar nan kamar an kara zazzage masa hanji haka yakeji, gashi limamin nan kamar ya zabi yayi tilawa ne a sallar asham din, kafafuwan Baffa har sanyi sukeyi kafin ayi ruku'u. So kawai yakeyi a idar ya karasa gida ya dirarwa koma menene Jamila ta tanadar masa, Allaah Yasa tayi zobo, dan yau jinshi yakeyi kamar baisha abinda ya kai masa inda ya kamata ba.
#LubnaSufyan ✨
#WomenOfWords
#09035723778
Littafin nan na kudine akan #1k kacal, zaizo a manhajar Telegram 10/12/2024 In Shaa Allaah, bayan mun kammala shafukan dandano.
9035723778
Opay
Lubabatu Sufyan
Saika turo shaidar biya ta lambar da take sama. Nagode da addu'a'inku, nagode kuma da kwarin gwiwar da bakwa gajiya da bani
*
Duka littafin nan sadaukarwa ne ga Marubuciya Aisha Shafi'i, idan kunci karo da littafin nan, kun nishadantu, kun karu ta kowacce irin fuska, ku rokawa mijinta Isma'il Rahmar Allaah, ku roka mata sauki da juriyar rashin shi, ku rokawa yarinyarta rayuwa mai albarka. Nagode
MATAR HABIBI
4
(Free page)
Adai-daita na ajiyeta, ta dauki katon kwandon data hada komai a ciki, don da taga almajiri ma shi zata ba ya dauka ya tsallakar mata dashi saita bashi ko Naira dari ne sadaka. Kwandon yayi mata nauyi, haka ta kinkima saboda wani mai mota daya gansu a tsaye, mata su wajen biyar saiya daga musu kafa suka samu suka tsallaka, sai nishi takeyi, ta ajiye kwandon a kasa dan ta numfasa. Ta godewa Allaah da tabarwa Rufaida har Nana. Da yake ba kwiya gareta ba, su Asaad na dauke mata hankali ta samu ta silalo, ai da taji a jikinta da daukar wannan kwandon. Yanda Baffa yace ba zai dawo da wurin nan ba, sai kaga har goma ta wuce ma kafin ya shiga gida, tasan yana son shan ruwan shayi wani zubin, saita hada masa shi yasha kayan kamshi. Shisa kwandon ya kara nauyi.
Kamar ance ta juya, ta hangi Baffa yana daukar mashin dinshi, sai dai ba kayan daya fita dasu bane a jikin nashi, yadi ne yanzun, kuma daga inda take taga yayi kyau duk kuwa da bai saka hula ba. Babu yanda za'ayi ta ware baki ta kwala masa kira, bata kuma fito da wayarta ba. Hakan yasa ta dauki kwandon, nauyin shi na hanata sauri yanda ya kamata, sai dai kafin ma ta karasa Baffan ya haye mashin dinshi yayi gaba, tunda baya ya bata ya fice ta dayan bangaren shisa bai ganta ba
"To ko dai gida zai koma?"
Wata zuciyar ta raya mata, sai tayi tunanin ta karasa shagon taji. Haka kuwa akayi, Abbati ne ya fara ganinta tunda yana bakin kofar shagon a tsaye da kankana a hannunshi
"Maman Asaad"
Ya fadi yana dorawa da gaisheta a daburce
"Naganshi ya fita ma yanzun, kar dai gida ya koma, yace mun zaku dade yau a shago saboda akwai ayyuka"
Sai Baffa ya juya yana kallon Isma'il cikin neman dauki, dan shi karya bata cikin dabi'unshi, ko da kuwa ta kare kaice, kalamai ma gabaki daya basa yawaita a bakinshi.
"A'a um...yaje ya dawo ne"
Cewar Isma'il shima sarkin maganar yau da alama ya rasa ta cewa, kuma hakan nada nasaba da yanda Jamila takeyi musu kwarjini. Macece da nagartarta take shimfide akan fuskarta. Yanayinsu, da kuma yadin jikin Baffa ta hada waje daya a cikin kanta, kwakwalwarta ta dai-daita mata lissafin. Shisa ya kirata yau kenan? Shisa yayi mata kirki? Saboda zaije zance wajen AZ dinshi kenan, acan zaiyi buda baki kome? Ita tana can tana kitimillin hada masa, banda ruwa da dabino bata saka komai a cikinta ba tanata sauri ta fito, ashe tana da rabon ta cika cikin nata taf da bakin ciki.
"Na bar yara a makota, ga kayan buda baki nan, bari in wuce"
Saboda jikinsu a sanyaye yake su duka, kamar sune suka saka Baffa tafiya zance a ranar yau, sai suka kasa wani yunkuri har Jamila ta juya, ta tare napep, zuciyarta na wani irin tafasa. Numfashi kawai take maidawa har suka isa, dari biyar din data bashi ma ca tayi ya rike canjin ta wuce ta shiga gidan Rufaida, taji dadin samunta ta tayar da sallah dan kwata-kwata bata son wani dogon surutu, ta sabi Nana tana riketa a hannu ta cewa su Asaad
"Ku taso mu tafi"
Bata san ko muryarta bace ko yanayin fuskarta yasa duk suka shiga hankalinsu. Tana zuwa kofar gida kuwa ta samu Yayarta Yasmin da take tsaye tana danna waya
"Yanzun nake shirin juyawa dan nagaji da kwankwasa kofa..."
Murmushin karfin hali Jamila tayi
"Kai su Maman Danjuma babu hakuri"
Yasmin din tayi dariya. Tun haihuwar Yasmin ta biyu, ta kwallafa rai akan idan namiji ne za'a saka sunan mahaifinta Abubakar, har shafa cikin take tana fadin Assadiqu kamar yanda take da niyyar kiranshi, ta shiga watan haihuwarta, Kanin mijinta ya rasu, kawai tana haihuwa da yayi masa huduba, bata kawowa ranta ba Abubakar din ya saka ba, sai ranar suna taji ana
"Ashe yaro sunan margayi yaci, Allaah Sarki Ya'u"
Ta tabbata da ba'a zaune take ba sai jiri ya tikata da kasa, ita tun yana da rai ma ba shiri sukeyi ba, duk da ance babu kyau tado da halayen mamaci musamman wanda ba nagartattu ba, shi kam mutum ne mai tsugudidi, sannan ya saka mata ido ainun, duk wani husumi da zai taso tsakaninta da dangin mijin nata in aka bibiya shi ya kitsa zancen. Kamar mace haka yake da gutsiri tsoma. Da yake kuwa ranar Juma'a ne ta haihu, saita fara kiran yaron da Danjuma, wani suna da mijin nata da dangin shi suka tsana saboda sunce akan meye zata boye sunan yaro, shima mijin da yayi magana sai tace masa
"Ni da nayi dakon wata shida, nayi nishin nakuda ai ayi mun alfarmar kiran yaro da sunan daya kwantamun ko? Tunda ban hana kowa ya kirashi da sunan da aka rada masa ba"
Haka dole ya hakura ya kyaleta, tunda yasan hali, jan maganar kamar neman zunguro sama da kara ne tunda har batace masa ta tafasa ba akan sauyin sunan da aka samu. Tun daga lokacin ta tashi daga Adda Yamin a wajen kannenta ta koma Maman Danjuma, tun suna kiran sunan da zolaya har yanzun kusan kowa ma haka yake kiranta dashi. Gidan Jamila ta bude suka shiga, su Arif suka gaishe da ita
"Mu karasa ciki mana"
Kai Yasmin ta girgiza
"Keni ba zama zanyi ba, Yaya Babangida ne ya hadani da aiki, ga sakonki nan"
Cewar Yasmin tana mika mata ledar data shigo da ita, kafin ta fara kokarin sauke jakar kafadarta, sai ga wuta sun kawo, daman fitilar caji ce da take dorawa sama, ita ta haske tsakar gida, saita wuce daki da yara ta kunna musu tv ta dawo, Nana ce kawai ta makale taki sauka. Kudi ne Yasmin ta mika mata, tasa hannu ta karba
"Kudin dinkin kine yace a baki"
Haka kawai sai taji hawaye ya balle mata, wani irin rauni ya mamaye ta
"Jamila, ikon Allaah, meya faru kuma?"
Da sauri tasa hannu ta goge hawayen, kawai tana hasaso tarin kauna da hadin kan da suke dashi, yanda ta fahimci ba sai iyayenka nada kudi bane kake kasancewa dangata, ita kam 'yar gata ce, sun taso cikin tarin kulawa, yanzun gashi aure ya rabota da gidan nasu, ya kuma sakata yunwar wannan kulawar. Tunda in ba yunwarta da takeyi ba, wayar kasa da mintina biyu da sukayi da Baffa itace fa tasa ta son faranta masa
"Wai menene? Kinsan banason wannan shirmen banzar naki"
Yasmin tayi maganar cikin fada, amman zaka iya tsintar damuwa a kasan muryarta. Saboda tasan halin Jamila, abinda zaisaka hawayenta zuba ba karami bane ba, akwai kujerun roba guda hudu, wata cikin wata daga can gefe, Yasmin ta karasa ta dauko guda daya, duk da batayi niyyar zama ba
"Kiyi mun magana tunda dai ai baki da wanda suka fimu"
Numfashi Jamila taja tana saukewa
"Baffa ne"
Ta fadi, Yasmin ta kalleta tana jiran karin bayani
"Zance ya tafi"
Sai Yasmin din taja wani dogon tsaki
"Shine kike shararar hawaye sai kace wanda ya nakadawa duka, to in ba daukar kafa ba ke ina ruwanki da zancen shi?"
Wasu hawayen suka ciko idon Jamila
"Adda bafa dan ya tafi zancen bane ba, kayan buda baki na shirya masa na tafi na kai saboda yace mun zai dade bai dawo ba, na samu ya tafi wajenta"
Kureta da ido Yasmin tayi
"Da yace miki zai dade sai yace kiyi abinci ki kwashi kafa ki kai masa?"
Ta girgiza kai
"Shegiyar kankanba ce irin taki kenan"
Tayi shiru
"Ke yanzun waye yace miki anayi wa maza wannan kankanbar? Ai kina budurwa ne kafin ya sameki, shine zaki burgeshi da irin wannan iyayin, amman yanzun tunda ba sakaki yayi ba gara ki rufawa kanki asiri, in ba kina neman ciwon zuciya bane ba"
Fada sosai Yasmin tayi mata kafin ta dora da lallami, ta nuna mata duk taji, ta kuma lallasu, haka sukayi sallama, ta rakata tana dawowa. Ta duba ledar, lace ne mai kyan gaske sai atamfa kala biyu, sai kuma shadda da tasan ta Baffa ce. Da yake Yaya Babangidan yanzun kasuwa nayi dashi, kuma shi din mutum ne mai son hidimtawa dangi, babu ruwanshi da kana dashi, inya tashi zaiyi maka, su matan har mazajensu yake hadawa. Ta tattara duka ta shige dakinta dasu ta adana. Kamar yanda Yasmin ta fada mata ne, ita ta kai kanta, babu wanda ya aiketa. Amman ta kasa daina jin takaicin wai saboda yana so yaje zance ne yau yayi mata kirki.
Tana da hakuri, amman tasan idan bata rama wannan abin da Baffa yayi mata ba, zata jima dashi a rai. Ta samu tayi sallar isha'i da asham, ta dan zuba abinci kadan taci, tazo ta dauki su Asaad da sukayi bacci a falo ta kaisu dakinsu, tana tashin kowanne yayi fitsari, tukunna tayi musu addu'a, Nana da take goye a bayanta itama tayi bacci, taje ta kwantar da ita. Taji ana kwankwasa gida, wani abu ya taso mata, haka ta sauka taje ta bude masa, ta kuma danne zuciyarta tayi masa sannu da zuwa
"Kece da sannu ai Mamin yara, ya naji gidan tsit, ko har sunyi bacci"
Data kalle shi, yanda yadin yayi masa kyau bai hanata ganin bakin shi ba, sai takejin kamar dariyar da yakeyi mata dinma duk ta yaudara ce yau. Shikuma ganin irin kallon da takeyi masa yasa shi saurin cewa
"Kinganni da yadi ko? Hmm, kwata na fada, Allaah Ya taimaka Isma'il ya dinka mun wannan yadin, na samu na canza, kayan na can ma shago na manta dasu"
Baffa ya karasa maganar yana gyarawa mashin dinshi zama
"Da mashin din ka fada kwatar?"
Jamila ta tsinci kanta da tambayarshi duk kuwa da shiru taso yi
"A'a fa"
Ya fada da sauri
"Da naje azahar ne"
Sai wani guntun murmushin takaici mai sauti ya kwace mata hadi da mamakin yanzun ne Baffa ya koyi shararo karya haka, ko kuma tunda can ne itace dai bata maida hankali ba.
"Allaah Ya kara tsarewa"
Ta furta tana wucewa ta shige daki, bata kuma tsaya ko ina ba sai dakinta, ta haye gado, tana shirin kwanciya ne Baffa ya turo kofa, ta daga kai ta kalle shi
"Abinci na Mamin yara, bakiji yanda cikina yake daurewa ba"
Zuciyarta tayi wani tsallen murna a cikin kirjinta, ta danyi 'yar dariya
"Yau kuma zolayar taka ce ta motsa, wanne abincin kuma Babansu? Banda wanda nasan yau har makotanku a shago sai sun samu rabonsu"
Ya dan diririce yana juya maganarta, yana juya maganarta, sai yayi dariya shima duk da kuwa bai gane me take nufi ba
"Ni dai a dawomun da robobin dana zuba zobo dan Allaah"
Jamila ta fadi, zuciyar Baffa ta buga, kar dai abinci ta aika musu dashi shago?
"Bari dai insa wayata caji"
Yace mata yana ficewa daga dakin, zuwa yayi yasa wayar tashi a caji, ya kunnata, ya dan zauna a wajen yana jira ta gama kawowa, sai ga sakonni, na Aziza, sai kuma Isma'il, da hanzari ya fara bude na Isma'il din
"Inata kiran wayarka a kashe, yanzun Madam tabar shagon nan, ta kawo mana kayan buda baki, amman dai munce mata kaje ka dawo"
A fili ya furta
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Bayan ya karanta sakon, a yanda yasan Jamila, ya tabbata abinci ne niqi-niqi takai, kuma anan gida din wanda zata bari ba mai yawa bane ba, tunanin karyar da zaiyi mata ya samu ko da taliya ce ta dafa masa yakeyi, saboda da gaske yunwa yakeji. Haka ya bar wayar batare daya ko bude sakonnin Aziza ba, ya sake komawa dakin Jamila ya ganta tana duba drawer din gefen gado
"Me ake nema?"
Batare data dago ba tace masa
"Paracetamol zan hadiya, kaina ke ciwo"
Ya danyi jim
"Sannu, kuma da zuwa nayi ince a zubamun abinda aka rage, kinsan yan shagon nan, musamman Isma'il, shiya fita da plate yan shagon Rahusa suka ganshi, nan suka tattaro suka zo, dan abinda nacin ba mai yawa bane ba, anayi asham duk ya zazzage"
Sai lokacin ta kalle shi, amman ya kasa hada ido da ita
"Aikuwa babu wani abu sai abincin Sahur dinka, shisa na zuba muku shi da yawa daman, ko da baku kadai zakuci ba, kuma da yake banma zaci yanzun zaka dawo ba"
Yayi shiru, itama tayi shiru
"Bani shi inci kawai yanzun din, da sauran biredi? Ko shayine sai in sha anjima din"
Ta jinjina masa kai, tana mikewa, acan kitchen din ta zuba masa a filet, ta samu dan karamin kwano ta zuba masa miyar, tana dan saka masa kifin kadan, duk kuwa da yawan da yake dashi a cikin miyar, ta daukar masa pure water da kofi, a falo ta same shi zaune, ta ajiye masa komai a gabanshi
"Ko dan zobon bai rage ba Jamila?"
Tayi 'yar dariya
"Ai kam dai bai rage ba, mun shanye ni da yaranka"
Ya kalli shinkafar
"Bari inje in samu maganin nan in sha in kwanta ko zan samu bacci"
Da sauri Baffa yace
"Kisa alarm dan Allaah karmu sake makara"
Ta jinjina masa kai kawai tana wucewa batare data amsa ba, haka ya tashi da shinkafar tas, miyar tayi masa dadi, ya dinga cancana dan kifin da yake ciki kamar karya kare. Ya sha ruwan yaje ya kwanta, sai lokacin ya dauki wayar shi yana kiran Aziza. Hira sukayi sosai, harda video call din da yayi mata alkawari, duk da bai bari video call din yayi nisa ba, ko dan dare ne, gashi ba hijabi ta saka ba, duk da baya ganin komai banda wuyanta sai kuma gashin kanta da yake kwance luf har akan goshinta,hular data saka ta dan zame baya. Gashi duk ta narke sai shagwaba takeyi masa, yaji ya fara susucewa, kuma tunda watan azumi ne, yasan bashi da halin labewa bayan shaidan.
Haka yayi mata sallama yace zai kwanta, kuma kwanciyar yayi, amman cikinshi daya murda ne ya saka shi tashi babu shiri yayi bandaki, wasa-wasa kafin karfe biyun dare ya shiga bayi yafi sau takwas, danma Allaah Ya taimake shi cikinshi bai fara ciwo ba, da yazo ya kwanta dai sai yaji jikinshi yayi laushi matuka, kamar duk yinin ranar baici komai ba, yasan dole ya lallaba Jamila anjima ko indomie ce ta dafa masa ta soya masa kwai kamar guda biyar yayi sahur dashi, dakyar ya samu bacci yanata mafarkin abinci
Abinda Baffa bai sani ba shine Jamila bata kwanta da niyyar tashin shi ba...
#LubnaSufyan ✨
#WomenOfWords
#09035723778
Littafin nan na kudine akan #1k kacal, zaizo a manhajar Telegram 10/12/2024 In Shaa Allaah, bayan mun kammala shafukan dandano.
9035723778
Opay
Lubabatu Sufyan
Saika turo shaidar biya ta lambar da take sama. Nagode da addu'a'inku, nagode kuma da kwarin gwiwar da bakwa gajiya da bani
*
Duka littafin nan sadaukarwa ne ga Marubuciya Aisha Shafi'i, idan kunci karo da littafin nan, kun nishadantu, kun karu ta kowacce irin fuska, ku rokawa mijinta Isma'il Rahmar Allaah, ku roka mata sauki da juriyar rashin shi, ku rokawa yarinyarta rayuwa mai albarka. Nagode
MATAR HABIBI
5
(Last Free page)
Kudin da Baffa ya bata ta kirga bayan tafiyarshi, saita tabe baki, saboda ta raina dubu goma, kamar yanda ta raina kayan sallar da yayi mata, musamman lace din. Ko Mummy da ta ganshi saida tace
"Wannan lace din ai karami ne Aziza, ba zai wuce dubu sha biyar ba"
Aikuwa dansu tabbatar haka ta dauki hoton shi ta turawa kawarta da take siyar da kaya tana tambayarta, ita a wajenta ma dubu sha uku da dari biyar ne
"Inya baki wasu kudin a hankali saiki tarasu ki hada ki dauki babban shi"
Haka Mummy ta bata shawara. Jaka da takalmin dai sunyi mata kyau sosai. Taji sanyi da ba da Baffa kadai ta dogara ba, sauran samarinta sunyi mata hidima kamar yanda suka saba. Kawai matsalar zuciyarta ce, itace ta narke akan Baffa, saboda tana tunanin fata da kuma bakin Mummy ne yake binta, ita take yawan fadar
"Kefa ba matar kananan yara bace ba, In Shaa Allaahu ke din matar babban mutum ce"
Manyan mutanen ne suke binta kuwa, masu kudi, dattijai da suka kusan haifarta dama wanda suka haifi kamarta sau babu adadi. Tana son rayuwar hutu da jin dadi, amman fa auren tsoho bai taba burgeta ba komin kudinshi. Duk kuwa yanda take ganin jin dadi shimfide a fuskar Mummy din idan sun hidimta mata, wani zubin ko don Mummy ta huta sai taji kamar ta duba wanda suka fi dama-dama a cikin maneman nata, a lokacin ne kuma ta gane da yawansu ba auren bane ya kawosu. Alhaji Sadisu ne kawai yayi mata maganar aure da kanshi, shikuwa matanshi uku a yanda ya fada mata, uwargidanshi ta rasu, da ita yake so ya cike ta hudu.
Shikuwa ko bai fada ba ta tabbata ya ba saba'in baya. Ba tajin tarin dukiyar shi zasu lullube mata shekarun shi. Samarin kuma da suke tareta bata ma bata lokacinta akansu, tunda ta tabbata ba aurenta zasuyi ba. Baffa shine namiji na farko da yazo wajenta taji ya kwanta mata har cikin ranta, duk kuwa da taso ace yafi haka kudi, saboda Mummy da ta tabbata Baffan ba zaiyi mata ba, ya aka kare ma lokacin auren Jalila da Balarabe. Shisa Mummy ta tattara burinta da fatanta kacokan akanta.
Aziza itace 'ya ta hudu a wajen Marigayi Malam Ayuba da matarshi Rahanatu. Shi din Bafullatani ne dan asalin garin Adamawa. Neman kudi ya shigo da iyayensu garin Kano, da kuma rabon suma din arzikinsu yana nan Kanon. Rahanatu kuma 'yar Dawakin tofa ce ta asalin garin Kano. Haka iyayenta duka 'yan Kano ne. Ta taso cikin gidan yawa, mata hudu, su kuwa yaran gidan sun bawa talatin baya. Haihuwa ake a gidansu da ta zama gasa, duk da mahaifinsu ba mai karfi bane ba. Dan 'yana aiki ne a gidan sarki, da yana cikin masu gadi, da yake mutum ne shi mai shisshigi da tusa kai, haka ya dinga shiga da fice har saida aka maidashi bangaren kula da dawakai. Sannan wannan shisshigin nashi yasa yake samun alkhairi babu laifi tunda gwani ne kwarai wajen koda duk wani ahali na gidan Sarkin.
Kusan a cikin yaran gidan, Rahanatu itace tafi kowa haske da manyan idanuwa, hakan yasa mutane suke cewa tafi kowa kyau, da yake za'a iya cewa ta biyo halin mahaifinta, saita kara da iyayi da kuma son ace wata ce, da ta kafa rigima da naci saida aka sakata a makarantar bokon da har mazan gidan ba damuwa sukayi da ita ba. Ta kuwa rungumi fadin rai ta dorawa kanta, duk inda zata zauna saita san yanda tayi ta fadi cewa ita jinin sarauta ce. Yaran unguwa da aka taso tare kullum cikin gulmar wannan karya ta Rahane suke tunda mafadaciya ce ta gaske ba'a isa ayi a gabanta ba. Ko Rahanen ma ta hana a kirata dashi sai Rahanatu.
Tana aji uku a sakandire ta hadu da Ayuba, dan gaye dai-dai da zamanin shi. Yana da shagon saida kayan masarufi. Gashi Bafullatanin usul, fari sol dashi. Cikin kankanin lokaci akayi bikinsu, yana kuma yi mata hidima har ya zarta karfinshi wani lokacin saboda yanda take da son harkar karya.