Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 4
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels #LubnaSufyan ✨ #WomenOfWords #09035723778 Littafin nan na kudine akan #1k kacal, zaizo a manhajar Telegram 10/12/2024 In Shaa Allaah, bayan mun kammala shafukan dandano. Duka littafin nan sadaukarwa ne ga Marubuciya Aisha Shafi'i, idan kunci karo da littafin nan, kun nishadantu, kun karu ta kowacce irin fuska, ku rokawa mijinta Isma'il Rahmar Allaah, ku roka mata sauki da juriyar rashin shi, ku rokawa yarinyarta rayuwa mai albarka. Nagode MATAR HABIBI 1 (Free page) Daya tashi zaune, saurarawa yayi, wai ko kunnuwanshi ne suke son yaudararshi, da gaske sallame sallah ne yakeji "Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..." Ya furta yana janyo wayarshi, ya duba lokaci, karfe biyar da minti goma sha biyu, cikinshi yayi karar daya tabbata ta yunwa ce tunda daren jiya ba wani abincin kirki yaci ba, sai kuma cikin nashi ya sakeyin wani sauti, wannan karin na tashin hankali ne, ya kuwa diro daga kan gado cikin hanzari yana bude kofar dakin shi ya nufi hanyar da zata sadashi da dakin Jamila, ko tunanin ya zurfafa ba zai iya tuno ranar da Jamila ta makara ba, in ba don ita ba ai da ya tabbata makota sun sakashi a jerin mazan da ba'a gani a masallaci sallar asuba "Jamilaa..." Ya kira bayan ya tura kofar dakin nata, a kwance ya ganta kan darduma, jikinta sanye da hijabi ruwan toka, ta dunkule jikinta waje daya, alamar da tayi sallah bacci ya dauketa a wajen, karasawa yayi yana dan bubbugata hadi da sake kiran sunanta "Jamilaa" Motsawa tayi da sunan Allaah a bakinta, tayi hamma tana kokarin mikewa "Lafiyarki kuwa yau?" Karasa mikewa zaune tayi "Sallah nayi fa, ina lazumi ashe bacci ya kwasheni ban sani ba" Dan karamin tsaki Baffa yaja jin tana lafiya "To kuwa yau babu kanta, dan wallahi mun makara" Dauke da tashin hankalin da Jamila ta aro ta shimfida kan fuskarta tace "Subhanallahi, makara kuma?" Tana mika hannu ta dauko wayarta da take kan gado "Wallahi kuwa..." Bayan ta duba ta kalle shi tana fadin "Kayya, baccin daya daukeni ne, kasan kuma ba alarm nake sakawa ba tunda na rigada na saba tashi" Kai Baffa ya dan dafe ya sauke hannun shi "Allaah Ya kyauta, amman akwai damuwa, saboda ba wani abin kirki naci ba jiya, ga aikin da yake gabana a shago yau, ni anya ma na tabayin dorere a rayuwata?" Sai taji zuciyarta tayi mata wani iri, tausayin shi yana neman danneta, sai kwakwalwarta ta dawo mata da maganar shi "Nifa ba karamin taimako na kikeyi ba tunda kike tashina, badan ke ba ai in ta matar nan ne sai dai inyi dorere..." Gabaki daya dan tausayin sai taji ya murmushe "Ai shikenan haka Allaah Ya nufa, sai ka samu kaje kayi sallah, lokaci na tafiya, bari in shiga bayi..." Ta karasa maganar tana mikewa, tana jin yanda yake binta da kallo, sai bayan ta shiga bayin kuma tukunna taji karar budewa da rufewar kofar dakin nata, alamar ya fita. Ta danyi mintina biyu kafin ta fito, saita cire hijabinta ta koma kusa da Nana da take ta bacci, har yanzun kirjinta yayi mata nauyi. Tun da ta auri Baffa, bai taba gajiyawa wajen nuna sha'awarshi ta auren mace fiye da guda daya ba, shisa ma ta sakawa ranta salama, duk kuwa da yanda take da zafin kishi. Wani lokacin bayan tayi masa addu'ar karin yalwar arziki sai taji kamar ta koma tace Allaah karya bashi da yawa, iya wanda zai ishesu hidimarsu batare da sun takura ba, amman banda na karin aure. Wata rana sai taba kanta dariya, lokacin daya fara gini, haka ya daukota akan mashin dinshi yazo ya nuna mata, ta dinga kallon yanayin tsarin gidan cike da sha'awa, musamman da yake fada mata za'a dora bene, saboda yanason yayi part biyu "Aikuwa saman nake so" Ba zata manta ba yayi dariya yace mata "Idan kuma amarya zansa fa?" Taji dirar maganar har tsakiyar kanta, amman saita dake ta amsa shi da "Sai ta zauna a kasan, ni kuma ina sama, ai dai naci arzikin kasancewa uwargida da akasha gwagwarmaya da ita a bani zabin inda nake so ko?" Dariyar dai Baffa ya karayi batare da yace mata komai ba. Kuma lokacin daya kammala ginin kasan, aka fitar da kafar benen akayi dakin da komai, sai suka tashi suka dawo, watanni takwas kenan, yace mata a nutse yake so saman ma suna ciki ana ginawa, da duk karsashin dawowarsu sabon gida, harma da kujerun da ya sake mata duk ya rage saboda tana tunanin kowanne lokaci zai iya rakito aure, amman da taga ko bulo ba'a shigo dashi ba saita fara sakin jiki. Amman gab da azumi ta fara kula da canzawarshi, shi mutum ne da inya shigo gida to yakan ajiye wayarshi ne ya zauna ya biyewa yara suyita shiririta. Kuma itama din akan zauna da ita a taba hirar, amman lokaci daya inya dawo, to yana manne da waya yana dannawa, sai kayi masa magana nawa baiji ba, hankalinshi yana kan wayar, da bata damu ba, saida ya fara tashi yana barin dakin in tana nan aka kirashi, tasan yanayin aikin shi, yana mu'amala da mutane kala-kala, kuma ciki harda mata, sau nawa suke kiranshi a waya, wata rana ma ba amsawa kawai yakeyi a gabanta ba, a lasifika yake sakawa yayi maganarshi a nutse. Saita kara ganin wayar bawai da daddare bane kawai, har da asuba. Baffa da ana idar da sallah zai shigo gida danya koma bacci, amman sai gari ya fara haske ma wani zubin kafin ya shigo, ko inya shigo din ya wuce dakin shi ya turo harya murza mukulli. Shi yasa Jamila sanin cewa wata tayi mata kutse cikin rayuwar miji, da ta ganshi rike da wayar sai taji zuciyarta nayi mata zafi, babu abinda yake dawo mata sai lokacin da yake neman aurenta, kalamanshi, yanda yake riritata kamar kwai, saita hasaso irin wannan riritar wata take samu, wani abu daya jima da mutuwa a tsakaninta dashi, amman taji dadi saboda a lokacin azumi na karatowa, tasawa ranta zata tsaya ta kara kyautata duk ibadunta a cikin watan, sai tayi addu'a sosai. Kuma hakan ne ya faru, har a sujjadarta rokon Allaah takeyi daya saka mata salama idan har Baffa nada rabon zama da wata matar bayan ita. Sai gashi ta fara samun sauki "Allaah Kasa kar mijina ya juyamun baya, Allaah Kasa kar in taba wulakanta a idanuwanshi, Allaah Kasa kar mutuncina ya zube a idanuwanshi, Allaah Kasa kar matar da zai auro ta cutar dani koni in cutar da ita, Allaah Ka rabani da kishin da zai zame mun fitina koya hanani zaman lafiya" Haka take jerowa tana sake maimaitawa duk sallah, duk wani motsi ma da zatayi, tasan Baffa, ko tace ta dauka ta gama sanin shi, shekaru bakwai ko tace takwas in za'a hada da lokacin da yake nemanta, ko kadan bata taba hasaso zai kasance cikin irin mazan nan masu kushe matansu a wajen 'yan matan da suke nema ba, tana can gurfane kullum tana addu'ar karta wulakanta a idanuwanshi, batayi tunanin hadawa da addu'ar kar ta wulakanta ta sanadinshi ba sam, tunda akwai wani wulakanci daya wuce ace mijin daya kamata ya kare maka mutuncinka shine yake zubar maka dashi? Abin yayi mata zafi matuka, kuma inda ma ya tsaya iya abinda tayi din da zaifi mata, sai gashi kirikiri ya yanko karya a cikin wata mai girma irin Ramadan "Hmm..." Ta furta a fili ko yanzun dinma, farkon aurensu ta dauka shine zai dinga tashinsu sallah, da yake ta saba gidansu har kananun yara ma sai an tashe su da asuba, mazan haka Baba zai tattarasu su wuce masallaci, to da lokaci yayi take bude ido, ko da bata sallah kuwa saita farka, tun tanayin luf da ita tana jiranshi harta gane in dai ta biyewa Baffa to zata daina yin sallar asuba a cikin lokacinta, saita tashe shi shima. Amman wai yau dadin soyayya yasa shi rufe ido yana zabgawa budurwa karyar cewa wai indan itace da sai dai ya dingayin dorere, budurwar da sai bayan ta tashe shi, yana zaune ma yana sahur zataji vibration din wayar alamar ta kirashi, ko taji ringing din wayar idan ya manta bai sata a silent ba. Shisa ta daukarwa kanta alkawari har azumin ya kare ta daina tashin shi, zata barshi da budurwar tashi, duk da ba karamin danne zuciyarta tayi ba kafin ta iya kin tayar dashi din, tunda ita ba sahur takeyi ba, sai dai tasha ruwa, da daddare take cika cikinta. Shikuma Baffa in an kira sallah ya sha ruwa ya tafi masallaci, koya dawo sai dai ya dan sha kayan ruwa, baya iya sakin jiki yaci abinci sai ya dawo daga tarawih. To jiyama daya dawo ta hada masa komai, sai waya ta dauke masa hankali, lokaci zuwa lokaci zaiyi murmushi mai sauti, tun tana danne zuciyarta har tace masa "Abincinka yana hucewa fa, daka hakura ka gama ci saika danna wayar" Cikin halin ko in kula yace mata "Kwashe kawai, ba yunwa nakeji ba yau, naci anjima idan Allaah Ya kaimu" Haka ta kwashe komai tanajin kamar ta fisge wayar ta kwala da kasa, balle da aka fara jera masa kira ya kalleta yana fadin "Akwai gajiya sosai a tare dani, ga kaina na dan yimun ciwo, inaso in samu bacci sosai yau" Tasan a fakaice so yakeyi yace mata ba sai taje dakinshi ba, tunda yanaso ya sake yayi wayar shi da budurwa, da wannan takaicin ta kwanta, shine ma abinda ya kara mata karfin gwiwar komawa daki abinta bayan tayi brush tasha ruwa. Haka tayi nafilarta, tayi addu'o'inta, ta zauna zuciyarta nata bugawa, tana kuma kasa kunne ko zata juyo motsin Baffa, amman shiru, har aka kira sallah, saida tayi, tana zaune tana azkar din safe ta juyo takun tafiyarshi, tayi maza ta kwanta ta jirashi, tana kuma aiwatar da diramar data shirya zatayi. Tun tana tunane-tunane har bacci ya kwasheta, rigimar Nana ce ta tasheta wajen karfe takwas da rabi, saita mike gabaki daya, tayi mata wanka, ta shiryata, tukunna ta hada mata shayi ta zuba mata a kofinta ta bata, ta kama hannunta zuwa dakinsu Asaad, ta lekasu, bacci sukeyi daga shi har Arif din. Idan akwai abinda take kara godewa Allaah akai shine yanda in dai babu makaranta sukeyin baccin safe, tana yawanjin iyayen yara na korafin yanda suke tashi da sanyin safiya idan babu makaranta, amman ita dai Allaah Ya duba mata. Ta gyara musu labulen dakin, taja hannun Nana suka nufi kitchen, saida ta zaunar da ita akan kujera irin ta katakon nan a cikin kitchen din tukunna ta hada wanke-wanke. Ta gama tana goge wajen Baffa ya fito, ya shirya cikin kananun kaya, fuskarshi fayau, yayi kyau kamar ko da yaushe, zuwa yanzun kuma ta tabbata bawai a idanuwanta bane kawai Baffan yake da kyau, tunda gashi nan ya haska a idanuwan wata ma "Sannu da aiki" Yace mata, ta amsa shi da "Yawwa Babansu..." Kamar yanda ta lakaba masa, shikuma ya kirata da "Mamin yara" In yanajin nishadi, gaisuwar safen da basuyi ba dazun ita tayi masa ya amsa a sanyaye yana dorawa da "Zan fita, saboda nasan aiki nacan ya cushe mana" A jikin doguwar rigarta dinkin bubu ta kara goge hannuwanta da suke da danshi tana fitowa daga kitchen din "Allaah Ya tsare Ya bada sa'a" Ta fadi tana rakashi har wajen mashin dinshi, ita ta bude masa gate tunda ba maigadi ne dasu ba, saida ya fita ta mayar da gate din ta rufe, ta koma ciki. * Karfe shida da kwata tagama komai tunda ba wani abu mai wahala tayi ba, doya fa kwai ta soya, tayi zobo, tana da sauran dafaffen nama, tayi miyar ganye, dan wannan tun safe ma tayi ta, saita tuka tuwon shinkafa dai-dai cikinsu, kuma ita da wuri take fara aikinta koma meye zata dafa kuwa, bataso ana shan ruwa tana kitchen sai dai bacin rana, sai su Asaad da Nana da suke binta, Asaad nata yi mata surutunshi kan abinda batajin ta fahimta gabaki daya, wani tsohon labarine akan yanda littafinshi ya bace a Islamiyya Tana kwasar komai zuwa falo, Arif yana nan zaune akan kafet yana kallon MBC3, Baffa kuma yana kan doguwar kujera a kwance kamar gawa, ko mintina goma baiyi da shigowa ba, sannu da zuwan da tayi masa ma da kai ya amsa, daga shi har mashin din kamar zasu tuntsire, idanuwan nan sun shige ciki, yayi zuru-zuru, ko dasu Nana suka dinga masa oyoyo ma dan rikesu yayi kadan batare da yace komai ba "Kuzo nan Babanku yau ya gaji, karku dame shi" Sai suka kyale shi din kuwa "Ka tashi an kusa kiran sallah" Tace tana kokarin danne dariyar da take neman kwace mata "Barni a kwancen nan, ki dai cikamun jug da koma menene kikayi mana na sha dan Allaah, ki matsomun dashi kusa, ki kuma zubamun abinci, yau inaga a gida zanyi Magriba" Saida dariya ta kwace mata, tun asali daman Baffa bashi da jumurin yunwa, dan azumi daga Ramadan, sitta shawwal sai kuma na arfa yakeyi, bayansu baya karayin wani azumi "Karka bada maza mana" Cewar Jamila tana karayin dariya "Ke ba zaki gane ba..." Dakinta ta shige bayan tasa su Asaad da Nana sun zauna kusa da Arif, ta dauro alwala tukunna ta fito, bata biyewa Baffa ba, ta samu kofi madaidaici, ta zuba masa zobo, sannan ta hada masa doyar ma a plate. Ya kuwa tashi zaune yana karbar kofin "Wai har yanzun ba'a kira ba?" Kafin ta amsa sukaji kiran sallar kuwa, nan da nan ya kwankwade zobon hannun shi, jikinshi har rawa yake lokacin daya sauke kofin ya dirarwa doyar "Baba kaci a hankali, babu kyau cin abinci da sauri ko Mami?" Asaad ya fadi "Bari ka fara azumi tukunna Asaad" Dariyar dai suka sake bawa Jamila, ta tashi ta tafi dan ta gabatar da sallar magriba yanda zatayi buda bakin cikin natsuwa. Sanda ta dawo a kwance ta samu Baffa "Kwanciya ka sakeyi?" A hankali yace mata "Cikina ke juyamun" Wani abu na rashin jin dadi ya tsarga mata, cike da tausayawa take ta jera masa sannu, doyar ma data dorawa buri saita kasa ci da yawa, ta dai zubawa yaran, zobo daman kowa na da robar shi da take zuba musu saboda a kofi za'a iya zubarwa a sakata aiki. Itafa ba haka taso ba, kawai dai taso ya dan sha wahala ne kadan, azumin ya gasa shi, bawai yayi ciwo ba. Sai gashi sallar Magriba a gida yayita, ya samu ya lallaba Isha'i saboda Tarawih. Daya dawo yasa ta zuba masa tuwo, saita tashi dansu Asaad da wuri suke kwanciya, kuma saita tsaya tana biya musu addu'ar bacci suna maimaitawa duk da sun haddace, ta karayi musu wata tukunna, ta goya Nana, dan itace take hirar dare wani lokacin Sanda ta koma falon Baffa ta samu rike da wayarshi, da alama ranshi a bace yake, tana zama yana mikewa ya nufi dakinshi, tana juyo yanda ya turo kofar garam kamar itace ta bata masa rai "Allaah Ya kyauta..." Jamila ta fadi, ta sauko Nana, ta janyo kulolin gabanta, a cikin kwanon da yaci tuwon ta zuba itama, tana ci tana bawa Nana itama, suka gama ta sake goya Nana dan tanaso ta kimtsa wajen kafin su kwanta. Kuma hasashenta ya zama gaskiya, ran Baffa a bace yake. Gabaki daya yau tunda ya fita shago komai ya rincabe masa, ya samu yaran shagon nashi sunata aiki, danma sun rufe karbar dinkin sallah tun saura sati biyu azumi, kuma shi yayiwa kanshi alkawari tuntuni, duk runtsi ba zai dinga kwana a shago yana dinki ba. Suna cikin aikin aka dauke wuta, tun jiya Gen dinsu yaketa wata qara, yau ma sai yaki tashi, daya kira Sani dan yazo ya duba musu sai yace masa sunje wata gaisuwa baya ma cikin garin Kano, sai yammaci, zaizo ya duba bayan shan ruwa, dan haka dole yayi abinda bayaso, aiki da keken dinki wanda bana wuta ba. Zuwa la'asar duk ya zazzage dan abinda yayi saura a cikinshi, ga ciwon cinyoyi da yakeji duk sun rike, kwata-kwata baima samu natsuwar danna waya ba, yama manta a silent ya sakata har sai bayan ya dawo daha Tarawih din nan, sai abin ya fado masa, ya riga yasan dole zai sha mita wajen Aziza. Yana duba wayar kuwa ya samu ta kirashi babu adadi, ga sakonni ta text da WhatsApp ta bar masa har yana rasa ta inda zai fara karantasu, sai kawai ya fara da tura mata da gajeran sako "Ayimun hakuri Babe, yau abubuwane suka rincabemun a shago, wayar kuma tana silent. Nayi missing dinki da yawa" Saida ya tura ya fara bin nata sakonnin, sai kuma zuciyarshi ta buga daya tuna yau yayi mata alkawarin zuwa yayi buda baki a wajenta, tun kwanaki biyar da suka wuce sukayi wannan tsarin, ya tabbata ta shirya masa shagali, lokaci daya yaji ranshi ya baci, musamman ma da ta dawo masa da sakon daya tura da "Ka kusa? Inata jiranka tun dazun. Gashi har tara saura" Yana shirin kiranta ne Jamila ta shigo, shisa ya tashi ya shiga dakinshi yana addu'ar Allaah Yasa karta biyo bayanshi, yasan halinta da naci wani zubin "Dan Allaah kiyi mun hakuri Aziza, dan Allaah..." Yake fadi cikin magiya da kwantar da kai saboda yanda Aziza ta birkice masa, kamar ma kuka takeyi "Ni ba sai kaci anan ba, kazo ka dauka kawai dan bansan yanda zanyi da abubuwan nan dana shirya maka ba" Muryarshi ya karayin kasa da ita "Na fada miki da zazzabi na dawo, yanzun haka ina cikin bargo a kwance, dan Allaah kiyi hakuri, ki sakamun komai a firij, na miki alkawari gobe In Shaa Allaah zanzo da wuri ma" Wani shiru ya ratsa a tsakaninsu kafin tace "Hmmm..." Gabaki daya a gajiye yake jinshi, bayajin ma yana da cikakke karfin fita da mashin din daya riga ya shigo dashi, balle harya falla unguwarsu Aziza "Ke kinsan babu yanda za'ayi haka kawai da gangan inyi missing din abubuwan da nasan kin shiryamun, kinsan yaushe rabon da inji wani abu mai dadi a bakina?" Cike da shagwabarta da take kara narkar dashi tace masa "Habibi saboda zuwanka fa nace yau 'yan gidama suci albarkacinka nayi tortilla da sauce din kwai" Duk da in za'a tsire shi baisan meye tortilla din ba, amman yanda ta fade shi tanayi kamar zata taune harshenta yasa Baffa hasaso wani abu da yaji naman kaza a cikin kanshi, ga kuma kwai data kira "Duk ki ajiyemun dan Allaah..." Bai sauke wayar ba saida ya tabbata Aziza ta hakura, musamman daya fara dauko mata hirar daya kula tafi faranta mata rai akan komai, hirar yanda in ta shigo gidanshi zata wanke masa takaicin rashin iya girkin Jamila, za kuma ta zame masa fitilar daya jima yana nema, a takaice dai, Baffa yace mata "Kina saka inaji kamar sai yanzun zanyi aure Aziza, kamar banma san iya abubuwan da na rasa ba sai yanzun da kika shigo rayuwata..." * Maza nawa ne irin Baffa? Mata nawa ne irin Jamila? 'Yan mata nawa ne irin Aziza? Kun shiryawa wannan tafiyar kuwa? #LubnaSufyan ✨ #WomenOfWords #09035723778 Littafin nan na kudine akan #1k kacal, zaizo a manhajar Telegram 10/12/2024 In Shaa Allaah, bayan mun kammala shafukan dandano. 9035723778 Opay Lubabatu Sufyan Saika turo shaidar biya ta lambar da take sama. Nagode da addu'a'inku, nagode kuma da kwarin gwiwar da bakwa gajiya da bani * Duka littafin nan sadaukarwa ne ga Marubuciya Aisha Shafi'i, idan kunci karo da littafin nan, kun nishadantu, kun karu ta kowacce irin fuska, ku rokawa mijinta Isma'il Rahmar Allaah, ku roka mata sauki da juriyar rashin shi, ku rokawa yarinyarta rayuwa mai albarka. Nagode MATAR HABIBI 2 (Free page) Yau kam fuskarshi ta nuna rashin jin dadinshi sosai "Nifa naji wani Malami na wa'azi in dai har sallar dare zatasa ka makara gara ka hakura da ita" A nutse take kallonshi "Babansu ai ana maganar sallar asuba ne, yau kuma bamu makara ba yanzun ma ake shirin tayarwa" A hasale ya amsa ta da "Amman ai mun makara sahur ko? Kinsan irin wahalar da na sha jiya kuwa Jamila? Gaskiya kisa alarm a wayarki yau" Kai ta jinjina masa "Kaje karka makara sallah" Kamar ba zai tafi ba sai kuma ya wuce, ta tabe baki, jiya bayan ta kwantar da Nana tayi mata addu'a sosai, da batayi niyyar zuwa dakinshi bama, sai kuma ta sake kayan jikinta zuwa doguwar rigar bacci da ta wuce har kwaurinta, ta kara goga humra, ta nemi hula ta saka a kanta sannan ta tafi, a kwance ta sameshi yana danna waya, da yake wutar dakin a kunne take saita kashe, tabi hasken wayarshi har zuwa kan gadon, kafin ma ta gyara kwanciyarta yace "Nifa a gajiye nake ba wani abu zan iya yi miki ba" Maganar tayi mata bambarakwai, a lokaci daya kuma wani abu yazo yayi mata tsaye a makoshi, tasan shi din ba wani mabukaci bane ta wannan fannin, saboda kaso tamanin cikin dari na lokutta itace take binshi, kuma tasan tana iya kokarinta wajen yin gyara, shi ba ma'abocin bada kudi bane ba, sai ayi watanni kyautar kudi bata gifta a tsakaninsu ba, ko roka tayi kuwa bako da yaushe yake bata ba, saima kaji yana mitar "Kin cika kashe kudi Jamila, meye zaki siya da baki dashi a gida?" Amman kyautar da 'yan uwanta suke mata lokaci zuwa lokaci tunda sun san ba sana'a takeyi ba, a ciki take dauka tana siyan magungunan mata, maganin sanyi kam wannan baya yanke mata sam ko dan yanda ake kara jaddada amfanin yawan shanshi ga mace ko da bata da aure balle kuma mai aure. Da kanta a WhatsApp ta fice daga cikin groups da dama na matan aure saboda yanda in an samu wata mai maganin matan, suka siya aka gwada za'azo ayita sharhi, kaji wasu suna bada labarin yanda miji ya manne musu, wata ma zatace "Nifa da niyyar kwana biyu yazo, amman kinganshi nan yana maganar ya kamata ace wannan komawar dani ya koma" To ita kuwa duk wani doki da rawar kai a wannan harkar Baffa yayi mata itane a cikin watanni ukunsu na farkon aure kafin ta fara laulayin cikin Arif da yazo mata

Chapter 1 of 4