baya da zabin daya wuce ya biyo bayanta shiga dakin cire hularsa yayi ya jawo stool ya zauna, ya kura mata idanu kamar maison gano wani abu a tattare da ita.
Ganin kallon dayake mata ne yayi yawa tace yaya Naseer wai kallon meyene hakan?
Ya nisa sannan yace "Amarsu ta Ango, kinsan wani abu? ranar bikin ki akwai bidiri, ranar bikinki akwai lik'i, kinsan cewa ban tab'a yin rawa ba koh, toh wlh ranar bikin ki saina cashe zan gyagije, sannan na girgiza, saidai kawai in aka kaiki gidan mijinki zanta kuka ne kawai, ya k'are maganar yana kyalkyala mata dariya cike da zolaya.
Shagwabe fuska tayi tamkar zatayi kuka tafara magana "Yanzu yaya Naseer meye na kawo wann maganar dan ALLAH, kai kanka kafi kowa sanin bana sonta, kai kasan banason wnn maganar kasan banason rabuwa da kai, ni bazanyi aure ba yanzu.
Cike da zolaya yace "Toh naji Al-masifatu yi hakuri" Tashi tayi tana kokarin fita daga dakin hawaye ciki da idanunta yace nace kiyi hakuri mana gani bata da alamar tsayawa yasa yayi saurin rik'o hannunta sauri sakin hannun yayi sakamakon wani Yarrr.... Dayaji tun daga gangar jikinsa har zuwa kwakwalwarsa ji yayi tamkar wayar wutar lantarki ya tab'a.
A bangaren Salma itama taji irin wannan abun da Naseer yaji, wnn yana faruwane a duk lokacin da hannayensu suka hadu tun suna yara kuwa wannan dalilin ne yasa sam Naseer baya yarda ya taba hannun salma.
Su umma suna zaune Alh Abbas yana bata labarin tafiyar dayayi, sai kawai sukaga wucewarta fuuu......
Umma tace "wannan yarinyar kuwa lpa....?" Bata gama rufe bakinta ba suka tsinkayo muryar Naseer yana cewa "umma yarinyar nan dai magana dayace kullum dai itace maganar aure, daga na fad'a mata maganar aure sai ta fara kuka wai ita batason ta bar gidann."
Umma ta kalleshi cikin natsuwa tace "Batason barin gidann ko dai batason rabuwa dakai.
Toh umma rabuwa dani ai yazama dole tunda duk matsayin mace a cikin gidansu dole wataran ta tafi gidan wani, kinga kenn idan ta tafi gidan wani babu wani abu daya rage tsakanin nida ita face ziyara.
Alh Abbas da tun dazu baice komaiba kawai kallon ikon ALLAH yake yace toh amman kai meyasa tunda kasan batason irin wnn wasan meyasa kk matashi?
Naseer yace "Abba kanwata ce fa, kuma bata da wani wanda ya fini a duniyar nan, nine abokin shawarta, nine abokin hirar ta, kuma ni gani nayi babu wata magana da zamuyi mai mahimmanci a yanzu kamar maganar auren ta, toh amman daga na fara maganar sai ta fara kuka," yayi ajiyar zuciya yace "Bari naje na bata Hakuri".
Har ya fara tafi Hajiya zainab tace "Naseer ya juyo ba tare daya amsaba tace "kasan dai su Aiman an kusa tashinsu daga magaranta kuma kai sukeso kaje ka daukosu basason direba yaje ya daukosu".
Yace "Ai insha ALLAHU Umma bazan dade ba kawai dai dan lallabata zanyi".
Shiga dakin yayi da sallam yace "Assalama Alaiki ya yar uwata" Kwance ya tarad da ita tayi rufda ciki sai sharbar kukanta take, jin anshigo dakin ne yasata rage sautin kukan datakeyi ta d'ago kai don gani wanene ya shigo dakin ganinsa tayi a tsaye ya kame hannayensa guda biyu ya d'orasu a kirjinsa, filo ta dauko ta jefosa dashi tana cewa "Ni ka fita ka bani waje Malam".
Hmmm toh ai idan kin isa katifar zaki dauka ki jefeni da ita bawani abu waishi filo ba.
Salma tace "Ai wlh dan bazan iya bane shiyasa da zan iya wlh da saina dauko na jefo maka ita.
Kujera ya samu ya zauna ya fara magana cike da kulawa da sanyaya zuciya yace "Bana tunanin akwai wasu yan uwa dasuka Shak'u kamr yanda nida Salma muka shak'u, lallai mun shak'u matukar shak'uwa, saidai inaso kisani cewa an dade ana zaman tare tsakanin yan uwa sanan an dade ana rabuwa tsakanin yan uwa, haka abun yake a rubuce sbd da haka nida ke dole sai munyi hakuri.
Salma tace "Yaya Naseer na fada maka cewa nifa baxanyi auren nan ba period!"
Wani kasaitaccen murmushi yayi yace "Sbd tuwon Mama?" Tace "Wlh kaga bana son haka ka daina mun wnn zance inba haka ba ni zan fece na barmaka dakin"
Yace haka zalika duk inda kikaje nima sai nabiki, tashi tayi a fusace ta bar dakin, shi abun natama dariya yake bashi, murmushi ya sake yi a karo na biyu ya mike yace "Problem Girl kenan" ya fice daga dakin.
__________________________________________________________________
Ta kasance yau safiyar Monday ce wadda Hausawa ke mata kirari da tushin aiki ko nasara na tsoronki, Naseer ne sanyi cikin wani lallausan yadi sky in colour ba karamin kyau dinki yayi masa ba, fitowa yayi daga dakinsa yana kokarin daura agogonsa mai dan karen tsada, a falo suka had'u da momy ta kallesa tace "Ah masha ALLAH" takare maganar tana murmushi.
Juyowa yayi ya dubi umman yace "Good morning mum"
Tace "Morning son how are u?"
Yace "fine mom"
Daga haka ya karasa izuwa dining table dan daman kowa ya hallara shi kadai ake jira, yana zama kuwa umman ma ta dawo ta zauna suka fara cin abinci kamar yanda suka saba.
Tom anan cikin cin abincin ne Abba ya dago ya dubi Naseer da kyau cikin zolaya yace Naseer wai sai yaushe xakayi aure ne a shekarunka fa ya kamata ace kayi aure for almost 37 years fa ai ya kamata inji ana ce mani grandy koh? ya k'are maganar yana kallon Hajiya Zainab wadda tunda Alh ya fara maganr ta daina cin abincinta ta tsaya tanajin su.
Umma tace "wlh kam Gaskiyarka Alh indai baso yake ya xama baba na shago ba" suka kyalkyale da dariya harda Khadija da Aiman wanda khadija bazata wuce shekara 13 ba sannan Aiman shima yana da shekara 10. Duk da basu fahimci inda umman ta dosaba amman datace Baba na shago shine abun ya basu dariya.
Naseer dagowa yayi a hankali yace Abba zanyi in harna samu wadda ta kwanta mini a raina zan sanar maka insha Allahu.
Abba yace "Ameen Summa Ameen"
Tashi yayi tsam yana mai duba agogon dake hannunsa yace "toh dady nidai na tafi mom sai na dawo yan biyu mom byyy". Yana kokarin fita ne daga falon ya tsinkayo muryar Salma tana cewa ni anmanta dani koh toh mun b'ata"
Juyowa yayi yace "No ba haka bane kinga na makara so we will talk letter" ya k'arashe maganar yana ficewa ba tareda ya jira mai zata ce ba.
Alh Abbas kwance kan bed dinshi amman sam bacci ya gagareshi sai juyi yake, dan bubbaga bayan Hajiya zainab yayi yace "Hajiya tashi muyi wata magana"
Tashi tayi ta zauna tana mai murza idanunta alamun baccin nata ya soma dadi, tace "Ina jinka Alh"
Yace "Hajiya inaga ALLAH ya nufa haduwar wannan yara wata kila shiyasa ubangiji ya nufesu da had'uwa a gida guda.
Alh Ga dukkan alamu abun ya nuna haka. Toh Alh mai zai hana a samu a kirasu a fad'a masu, tunda akwai aure a tsakaninsu ni inaga zasuyi farin ciki indan sukaji wannan maganar kuma gashi misali sun ruga sun shak'u da juna kai hasalima koh mu da muka haifeta bamu shak'u kamar yanda suka shaku da junansu ba.
Ya nisa yace "haka ne amman Hajiya ke kinsan da cewa halayyarsu ba daya bace tamkar wuta da ruwa haka suke duk da sun shak'u da juna, zasu iya samun matsala a zaman takewarsu ta aure sbd banbancin hali, ke kanki kinsani cewa bakya bukatar na sanar dake irin halayyar su tunda kinfini sanin halinsu.
Girgiza kai kawai tayi tace "Gaskiya toh inaga abunda za'ayi kawai a hakura a kyalesu kar ayi wannan maganar, kowa ya samu nashi, ita tasamu mijinta ta aura shima ya samu matarsa ya Aura, inaga hakan zai fi?"
Um...Um..had'asun shine mafi A'ala ki barni ina ganin zan fito da wata dabara mugani ko zata bulle.
Dubanshi tayi cike da dokin jin wannan wace iri yar dabarace tace "Alh wnn wace iriyar dabara ce?"
Yace "kedai kawai xaki gani kisa ido kiyi kurum"
___________________________________________________________________
Kwance yake akan lallausan gadonsa yana sharara baccinsa mai matukar dad'i khadija ce ta shigo dakin ta fara kiran sa.
Yaya Naseer! Yaya Naseer tana dan dukansa ganin baya da alamar tashi yasata ta kwala k'ara a daidai saitin kunnensa aiko ba shiri ya mike biyota yayi da gudu cike da matuk'ar baccin rai aiko itama tace kafa mai naci ban bakiba ta fece ta baro dakin nasa tayo falon su cikin matukar sa'a kuwa tayi kacibus da Umma ta shigo falon aiko bayanta tabi ta lafe tana cewa "Umma dan ALLAH 'boyeni wlh yau ya kamani na bani"
Umma da ta shigo rike da ruwan zafi a hannunta tace "yi hankali karki kona kanki wlh tana maganr ne takai dubanta ga kofar shigowa falon ido biyu sukayi da shi sai muzurai yake yana cika yana batsewa sbd da tsabar takaici tace "mai ya hadaka da ita ne?"
Furzar da iska yayi yace "Umma wlh yarinyar nan ta raina ni, wai ina kwance taxo tanata mani ihu a kunne kamar kaina zai fashe haka ake tashin mutum in yana bacci?"
Umma tace "To ai Alh ne yace yanason ganinka yanzu ma haka Salma tana can tana jiranka koh"
Tsuka yaza ya fice daga dakin, yana shiga dakin nasa birthroom ya shiga yayi brush ya sanya jallabiya da 3quatr ya fito domin amsa kiran dady.
Direct dakin dadyn ya nufa, da sallamarsa a bakinsa ya shiga suka amsa sallamar tasa da mamakinsa kowa ya hallara shi kadai ake jira.
Har kasa ya duka yace "Ina kwana Abba"
'lapiya lau my boy da fatan ka tashi lpa?'
Yace "Alhmdll ala kulli halin"
Dady yace "To masha ALLAH have a set ya nuna masa wata kujera dake kusa da Salma, jawota yayi ya zauna, yana mai sauraron abunda ya tarasu a gurin.
Sake kallonsa Abba yayi yace "Kun gaisa da momynka ne yace eh tun dazu muka gaida"
Yace "ohk"
Naseer, Salma Abba ya kira sunanensu wanda sukaji wata faduwar gaba ta ziyarce su a lokaci guda Abba yaci gaba da cewa mun kirakune dan mu karanta maku wani labari da zai matukar baku mamaki kuma jin wannan labari na tabbata sai kunyi matukar kad'uwa, naso mu ci gaba da rufe wnn sirri bamu bud'e shiba har abada toh amman sai mukaga yanda kuke gudanar da al'amuranku sai mukaga ya kamata mu bude wnn sirrin ba don komaiba sai domin samun farin cikin ku dakuma namu gaba daya.
Naseer bayan ALLAH ya azurtamu da samunka da shekara biyu, mahaifiyarka taso ALLAH ya bata wata haihuwar amman ALLAH bai bata ba, haka muka zauna munata tunanin yadda za'ayi har tsawon shekara hudu kai fiye ma. Sai mahaifiyarka ta kawo shawarar ko zamu tafi gidan marayu? Don mu samo jaririn da zata raina bayan kai, sai na amince da wannan shawarar data kawo nace amman mu fara zuwa asibiti kafin muje gidan marayun, sbd asibitima ana samun jariran da suka rasa iyayensu da ixinin gwamnati sai aba wadnda zasu raineshi, ALLAH da ikonsa muna zuwa kuwa muka tararda an kawo wasu accident din mata da miji duk Allah yayi masu cikawa harda jaririya a tsakanin su amman wani abun mamaki wannan jaririyar kwata-kwata bata samu koda kwarzane ba, a wannan lokaci akayita k'ok'arin neman yan uwan wannan bayin ALLAH amman aka rasa........
*Abubakar Saleh Al~Quyraemey*
_(young writer)_
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels