Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 7
hanunshi, yana kuma fiddo wayarshi daga aljihu. D'aukansu hotuna yayi tayi wani su biyu, ya musu d'add'aya snn sukayi tare dashi. Saida suka gama snn ya d'auko ledar da ya ajiye ya mik'awa nusaiba yace "Ku k'ara ku rabawa bak'i." Karb'a Nusaiba tayi tana cewa "Me kuma muka samu? Na lura sai wani ji da aunty salmannan kukeyi dukanku, wlh kukayi wasa nima sai na zuciya nayi karatun." tana fad'a tana bud'e ledar. Dariya dukansu sukayi snn Salma tace"ki zuciyan mana muma haka muka fiso." Snn ta juya ga ya al-amin."Yayanmu wancan bai isa ba har sai ka dad'o wani?" "Wnn dabanne sai na dawo ana jirana." Yace tare da barin wurin , suna kallonshi ya shige cikin mota. Kallon juna sukayi kafin nusaiba tace "Wnn kuma motar waye?" "Allah masani." Salma ta bata amsa. Fitar da abinda yake ciki nusaiba tayi , hand bags ne masu kyau da k'wari diff.colours. "Woow , duba aunty Salma ,hand bags d'innan sunyi kyau." Cewar nusaiba. Karb'a tayi tana dubawa. *Congratulations Ummu Salma.* *May Almighty Allah bless ur knowledge.* *Curtesy.....A.M.G.* K'ara girman idonta tayi tana kallo snn nunawa nusaiba. "Duba kigani." "Waye shi?" Nusaiba ta tambaya. "Ina zan sani." Salma ta bata amsa. Rik'e ledan sukayi a tare suka shiga gida, nan suka tarar an k'are wa'azi , malama Tasalla tana addu'ar rufewa. Fati suka tarar har ta fara rabon take away. Robobi ,mafici, cups ,da aka manna musu stickers, suka shiga rabawa, tare da bags d'in. Haka taro ya watse cikin farin ciki, sai fatan alkhairi ake mata. Da dare suna had'e dukansu a tsakar gida ,duka yaran gidan suna had'e har da Malam, kamar yadda ya saba zama cikin iyalanshi idan d'alibanshi basu zo ba ,hira suke cikin raha, duk suna cikin nishad'i. Al-amin ne ya shigo da sallama, dukansu suka maida hankalinsu kanshi suna amsa sallamar. Kusa da Mal. Yazo ya zauna ya gaisheshi snn ya gaida ummi da kanwarta, kannenshi suka mishi sannu da zuwa. "Hamza zo ka tayani d'aukan wasu kaya a d'akina. Cewar Ya al-amin, bayan ya mike yana zura takalmanshi. Ba tare da b'ata lokaci ba sai gasu sun dawo d'auke da kaya. Kayanya shiga fiffitarwa nan kusa da Mal. Saida ya gama fitarwa yace "Salma ga sak'onki." "Wnn fa daga ina ?" Mal. Ya tambaya yana kallon kayan. "Oganmu a gurin aikine ya bani na kawo mata." Wani zabura salma tayi har ta tsorata pendonsu dake zaune kusa da ita. Kamar wacce aka hankad'a ta isa gaban al-amin ta zauna tamkar wacce zatasa shi ya maida maganar da ya gama fitarwa yanzu. Hanunshi ta kamo ta rike ,bakinta na motsi ta kasa magana sai kallon shi takeyi. "Yayanmu." Tace still idanunta cikin nashi, ta rasa me zata ce mishi, ta rasa ta ina zata fara, Girgiza mishi kai ta farayi alamar maganar ki fitowa. Kawar da idonshi yayi tare da zame hanunshi daga cikin nata, kallon da take mishin ne yaji shi wani iri ,kallon yayi kama kwarai da na tuhuma, snn kwayar idanunta kamar suna nuna tamkar akwai wata laifi da ya aikata mata. *Mom Afrah🌹* [17/12 06:25] Hajara: *πŸ’”πŸ’”IN SO CUTANEπŸ’”πŸ’”* *Fasaha Online Writers.* *F.O.W.* *By Anty Rukie (Mmn Abduljala)* 27. πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’” *Wnn shafi nakine Hajiya Aisha (Hausa novels books, na gode da kulawa Allah ya bar zaumunci.* *** *** *** Kallonsu kowa yakeyi cike dason jin k'arin bayan. Lura da hakanne yasa ya al-amin ya fara nuna musu kayan da d'add'aya. Sphygmomanometer, na auna B.P. weigheing scale,na gwada nauyi. thermomether, na gwada temprture, first aid box da duk wani abin buqata, sai kuma qaton text book na research. Bin kayan da kallo salma takeyi zuciyarta na bugawa, a yau kam bata yarda da cewa kyautatawace haka kawai ba kamar yadda yayanta yake fad'a mata, a yau zuciyarta ta fara raya mata wani abin daban. Tana gama wnn tunanin taji hrt d'inta ya buga da k'arfi har sai da ta kamo yatsun hanunshi guda biyu ta matse da k'arfi. "Ya haka Salma?" Ya fad'a qasa qasa tamkar baya so a jishi. "Ya al-amin." "Ya dai?" Kamar nusaiba tasan abin da ke zcyr salma ta matso tace "Yayanmu hand bags na d'azu kuma daga ina?" Saida ya d'auke kanshi daga kallonsu, sbd kaucewa kallon kurillar da salma ke mishi, yace "Duka shi ya bayar." Kallo su salma tayi taga duk hankulansu na kan kayan snn tace , "Me yasa kake karb'an mishi kayanshi?" Ba tare da ya kalleta yace "Sbd ba kyau maida hanun kyauta." "Ka tabbata tsakani da Allah yake wnn abin?" "To da tsakaninshi da dake ne? dan mutum yayi kyauta sai a tuhumeshi? Na d'azu taya murna ne ,yanzu kuma gudunmawa ne dan ki taimakawa al'umma, ko ba daga yanzu karatunnaki zai fara amfani ba? Kuma ko bai saya miki ba ina da niyyar saya miki idan aka biyani kud'in aiki na?" Duk maganar da sukeyi a hankali sukeyi. Sai a snn ta d'an samu relief amma hankalinta bai gama kwanciya ba. Su kuwa sai yaba kayan suke suna sa mishi albarka , Su Hamza har da cewa tazo ta gwada B.Pn su , Fati da nusaiba kuma sukace ta gwada weight d'insu. Ita dai binsu takeyi da kallo tana kissima abubuwa da dama a ranta. Kallonta ta maida kan Mal. taga shi hankalinshi yana kan labarin da kanwar mamansu take bashi. Su nusaiba ne dai suke ta jujjuya kayan kowa na fad'an albarkacin bakinshi, daga qarshe fati ta tattara ta shigar d'akin Ummi. Har aka watse hiran Salma dai jikinta a sanyaye yake. Sai washegari su Ummi suka matsa mata da ta mishi godiya, ba dan ranta ya soba ta nufi d'akin al-amin. Maganar ma kamar shaketa akeyi tacewa wa al-amin ya qira oganshi ta mishi godiya. "Zan dai baki nambarshi ki qira shi." Yace mata . Cikin nuna gajiyawa da zancen tace bani da kud'i a wayata, in kaima baka dashi, sai in baka saqo kace mishi na gode." Mika mata wayar yayi yana cewa "Gashi kirashi." B'ata fuska tayi tace "in ce mishi wacece?" "Ummu salma "yace a taqaice. "Nikam karb'a ka fad'a mishi saika bani in mishi godiyar."ta karishe kamar zata sa kuka, bakinnan a cune. Karb'a yayi, yayi dialing nambar , saida ya d'auka suka gaisa snn yace mishi Ummu salma ce keson magana dashi." Miqa mata wayar yayi ta qara a kunne. "Assalamu alaikum." Tace a sanyaye. "Wa alaikumussalam." "jin tayi shiru ya sashi cewa Ummu ya kike ya mutanen gida." "Lfy, ina yini?" "Lfy lau Ummu ya hidima?" "Alhamdulillah." Tace snn tayi saurin cewa "Ya al-amin ya kawo min saqo ,na gode Allah ya qara bud'i." "Amin, Amin, nima na gode." Kit ta kashe wayar ta mika ma al-amin tayi gaba. *** **** **** Zaune take gaban dressing mirror tana shafa mai tamkar dole aka sata, gaba d'aya a gajiye take, ga wani irin kasala da takeji. Juyawa tayi ta kalli nusaiba dake kwance kan katifa tana karanta wani Hausa novel, sai sambad'a murmushi takeyi. "Ke malama, ni ki tashi ki zo ki shafa min mai a baya, duk kin bi kin gajiyar da mutum wai yawon rabon kati, idan kikayi wasa sauran ke zakiyi, ba gyaran jiki kikeyi ba ko fatar za'a canza gobe sai kin fita dan ni na gaji, tsabar rainin wayo ma instead ki nemi qawayenki suje miki sai kiyi ta had'amu da aiki, Fatinma gobe baza taje ba." Ajiye littafin tayi ta matso kusa da ita kafin tace "Yi haquri auntynmu, kwana nawa ne zaku gama, kuma mafa lada zaku samu, Allah ya bada ladan taku auntyna." "Ni kar ki wani isheni da zaqin baki, shafa min a baya wlh duk a gajiye nake, yau ko d'an kwalliyar jumm'ar ma mutum bai samu yayi ba ,har yamma tayi." Karb'an man tayi tana shafa mata tare da cewa "A dai qara haquri dai, kwanan nan zamu fara rabon naki in da rai." Pendonsu ne ta shigo ,tana ganinsu tace yauwa 'yan matana, shafa mata man da kyau, ko ta ina yaji kada saurayi ya tambayeta wani irin mai take shafawa." Dariya duka sukayi snn nusaiba tace "To dan me zai tambayeta" "saurara kiji ,idan kika ji saurayi ya tambayeki wani irin mai kike shafawa tofa baki iya shafa man bane, ina irin 'yan mata masu rataya kananan gyalen nan, sai kiji ana tambayar su wani irin mai suke shafawa, suko su ta fari da ido suna tsammanin abin kirki sukayi Ko sun burge basu san shi yasan abinda ya gani ba, bama kamar ta bayan nan sai kiga jiki fes baya kuma fari fat tamkar baiga ruwan wanka ba. Kwashewa sukayi da dariya tare da tafawa, "kai Mamanmu akwaiki da qalqaletion, su samarin ne suka fad'i hakan?" Dariya itama tayi,"To ku zauna dai ana fad'a muku gaskiya kuna maida abin wasa." Sallamar al-amin ne ya katse musu hirar da sukeyi. Ya leqa daidai lokacin da salma take fitar da kayan da zata saka. "Ummulu, idan kin gama ki same ni a d'aki ." "Toh." Tace tana ci gaba da shirinta.tsaff, ta saka 'yan kunne da sarqar gwal d'in da ahmad ya bata washe garin walimar graduation d'inta, ta fesa turarenta mai sanyin qamshi snn ta kama hanyar d'akin al-amin." Tana isa ta tsaya turuss tana kallon kofar d'akin. Takalma biyu ta gani a kofar kuma tana da tabbacin d'ayan ba nashi bane, hakan ya tabbatar mata ba shi d'aya bane cikin d'akin. Jin alamun motsi kuma ba'ayi magana ba yasa al-amin cewa "Waye a nan." Da sauri tayi baya ta shiga ciki ta d'auko hijabinta babba mai hanu ta saka. Dawowa ta tsaya bakin kofar ,haka kawai taji gabanta na fad'uwa , itafa yanxu al'amarin ya al-amin yana kulle mata kai, kar dai maganar ogannan nashi zaiyi mata. Tuna haka da tayi ,gashi kuma bata yarda shi kad'aine cikin d'akin ba yasa ta juyawa zata koma. "Ummu salma." Taji shi ya qirata. "Na'am." Tace, tana matsowa a hankali tamkar wata mai laifi. Sallama tayi a sanyaye, ilai kuwa muryoyi biyu suka amsa mata. [17/12 06:25] Hajara: *πŸ’”πŸ’”IN SO CUTANEπŸ’”πŸ’”* *Fasaha Online Writers.* *F.O.W.* *By Anty Rukie (Mmn Abduljalal)* 28. πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’” *Dedicated to my swt & lovely sister Halima Auwal.* Cakk ta tsaya bata shiga ba kuma bata koma koma ba. "Shigo mana Ummulu." Ta tsinkayo muryar al-amin. Kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ta shiga bakin ta d'auke da sallama. Kallon yayannata takeyi tana jira taji abinda zai ce mata. Shi kuwa ko kallonta baiyi ba. Tana daga tsayen tace "Gani yayanmu." Harara ya galla mata snn yace "Na ganki ai." Samun guri tayi ta zauna tayi qasa da kanta, dan ko da wasa bata nuna tasan da mutum a d'akin ba bayan al-amin. Fita al-amin yazo yi ta tashi ta bishi da saurinta. Juyowan dazaiyi har suna cin karo tayi sairin ja da baya. Qasa 2 yace "Baki ga mutum bane ko baki iya gaisuwa bane yau kuma." Itama a hankali tace "Mutum a ina?" Hararar ya kuma galla mata ,ya juya zai fita. Mutumin dake zaune kan resting chair tun d'azu yana kallon dramar da yaya da kanwar sukeyi ,ya ce " Ina zuwa kuma ameen?" "Sosa keya ya al-amin yayi yana 'yar murmushi yace. "Zanje nanne in dawo yanzu." Da ido ya mata alamar ta koma ta zauna. Komawan tayi ta zauna ta bakin kofar a darare tamkar tana jira a ce kett ta ruga. Duk haushin yayanta ya gama cikata, ko bai fad'a ba zuciyarta na fad'a mata wnn shine ogannashi. Shiru ne ya biyo baya kafin daga baya taji ya ce "Ummu." Cikin taushin murya. Duk da fad'uwar gaban da taji hakan baisa ta d'ago ba balle ta amsa. Bai damu ba yaci gaba da jera kiran sunanta ba ko gajiyawa. Mamaki ne ya isheta jin nacin k'iran yayi yawa yasata d'agowa, a ranta tana cewa wnn akwai nacin tsiya. Caraf suka had'a ido , ya sakar mata murmushi da yasa tajin wata irin tsinkewar zuciya . "Subhanallah." Tace qasa qasa. "Haba sister Ummu , haka likitocin suke treating patients nasu, ba gaisuwa, ina magana ba amsawa, an kuma d'aure fiska , taya zan saki jiki in fad'i cutar dake damuna har a bani magani ko shawara?" Jin haka yasa ta d'ago ta kuma kallonshi. Giranshi d'aya ya d'aga mata tare da cewa "Yess, ko ameen bai gaya miki patient ya kawo ba?" Girgiza mishi kai tayi ba tare da tayi magana ba. "Ashe laifinshi ne ,tunda bai sanar dake ba. Yanzu kin shirya in fad'i damuwata?" "Me ya hana shi zuwa asibiti ?."tace a ranta. Katse mata tunani yayi ta hanyar cewa "Are u ready, sister Ummu?" Shirun ta kuma yi. Sai da ya kuma maimaita tambayar snn ta gyad'a mishi kai. "Ok, listen attentively and look at me also." Taji yace. Tabd'i lallai ma, harda look at me, tunda bayani zaiyi ai kunne keji ba ido ba. Tace a zcyrta. "Ummu ,Kalleni dan Allah." Ya kuma cewa. "Fad'i ina jinka." "Um um nisai kin kalleni." Ya fad'a a shagwab'e. Ikon Allah, ko dai d'an auta ne." tace a zcyrta. Kallonnashi tayi , ya lumshe ido ya bud'esu tare da cewa "Yauwa ko kefa." Kasa ta kuma yi da kanta. "Kina jina?" "umm." Tace a taqaice. Tun bayan kwanaki takwas da suka shige nakejin kaina yake min wani DUUUUUM haka. kunnuwana kuma suke min SHUUUUUU. Zuciyata take bugawa KIKIB KIKIB KIKIB. Kina jina? Ya tambaya yana kallonta. "Umm." Ta ce, snn yaci gaba da cewa. "Snn idanuna suke min wani dishi dishi, ban cika ganin mutane sosai ba. Allah yasa kin fahimci bayanin da nayi miki." "Yanzu baka gani sosai kenan?" "Yanzu kam ina gani sosai ma kuwa, saidai nasan zuwa gobe abin zai dawo." Sakin baki da hanci tayi tana kallonshi, ba tare da ta sani ba. Shima kallonnata yakeyi babu kuma alamun wasa a fiskarshi. Wnn wani irin kwatancen ciwo ne? "Ya dai ummu ko baki gane bayanin bane in sake." Sai a snn ta fahimci kallonda take mishi tayi saurin kawar da kanta. "Da ka je asibiti wajen manyan likitoci inaga zasu fahimci bayanin." "ke fa?" Ya tambaya har da karya wuya. "Ban gane irin ciwon ba." Langab'ar dakai ya kuma yi ,"Yanzu ko d'an Bpn ma baza'a gwada min ba, kika san ko ya hau." Tunani ta shigayi, kodai yazo ya gwadatane yaga ko ta iya aikin, idan ba haka ba wnn wani irin ciwo ne? "Kinji." Ya kuma cewa. "Wnn mutumi akwai d'an banzan naci tace a ranta." Tashi tayi ,ya bita da kallo har ta fita , ya sauqe ajiyar zuciya snn ya d'auki wayarshi ya fara danne danne. Bada jimawa ba ta dawo d'auke da B.P apparatus a hanunta. Kusa dashi taje ta ajiye. "Gashi ka gwada." Tace dashi. Idanunshi ya waro. "Ni kuma ina zan iya Ummu, abinda ba aikina ba, fisabilillahi haka akeyi? Zo ki gwada kinga yamma tayi idan na dad'e za'a min fad'a a gida." Matsowa tayi kusa da shi snn tace "Bismillah." "Kafa zan miko ko hanu?" Ya mata tambayar. Dariyace ta sub'uce mata ba shiri ,taji kamar tace mishi kai zai mik'o, dan ta fahimci akwai rainin hankali a al'amarinshi, kamar wanda bai tab'a zuwa asibiti ba." Ta tuna hakan a ranta. "Hanun rigar zaka ja." "Zuwa ina ?" Ya sake tambayar yana kallon cikin idonta. Bata san sanda ta b'alla mishi harara sbd tsabar raina mata hankali da yayi. "ashe kema kin iya ?" Taji shi ya fad'a . "Me fa?" "Irin wnn kallon da kikayi min yanzu, sai naga ya qara miki kyau." D'aure fiskarta ta dad'a yi snn tace "Ka janye hanun rigar magriba ta kusa." Hanun farar shaddarsa ya janye yana murmushi aranshi ko cewa yake "Lallai zaisha fama da yarinyar nan, irin wnn shan murr haka. Abin gwajin ta d'auka ta matso kusa dashi sosai snn ta durkusa. *Mom Hanan*πŸ₯€ [17/12 06:25] Hajara: *πŸ’”πŸ’”IN SO CUTANEπŸ’”πŸ’”* *Fasaha Online Writers.* *F.O.W.* *By Anty Rukie (Mmn Abduljalal)* 29. πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’” Bin hanunta da kallo yakeyi yanda take taka tsan tsan kar hanunta ya tab'a jikinshi. Har ta iso gun damtsen shi. Kurawa murd'add'en damtsen shi ido tayi . Wnn kakk'arfa ne, dole yayi aikin gini. ta fad'a aranta. "Ya dai Ummu?" D'aurawa tayi taci gaba da abinda takeyi cikin k'warewa, har ta gama ta cire snn ta d'ago ta kalleshi. "Normal, ba wata matsala." "Kin tabbata?" "Hararanshi tayi qasa qasa ba tare da ta amsa ba, ta tashi daga kusa dashi ta koma inda take da. "To a bani result d'in a rubuce." "Bani da biro da paper." Ta fad'a fiska a had'e dan ya gama kular da ita. "Yanzu ko sauran na makarantan babu." Kamar baza ta amsa ba can dai tace "Sun k'are tun randa na rubuta last paper." Tana fad'in haka ta mik'e. "Dakata malama, ina zaki bamu gama ba?" Kamar zata yi kuka taja ta tsaya ba tare da ta kalli inda yake ba, shiko sai kallonta yakeyi yana dariyar yadda ta had'e rai. Bata ankara ba ta jishi yana magana dab da ita , "Na baki assignment kije kiyi tunani ko research kan ciwon da na kwatanta miki ,nd don't forget nace miki 8 days back ciwon ya fara min, but yau naji sauqi, kiyi tunani ko Allah zaisa in samu maganin ciwon daga gareki dan bana son zuwa gurin wani likita tunda nasan maganin bazai samu daga wajensu ba." Yana gama fad'in haka ya fice yana cewa "Na barki lfy, Allah yasa research d'inki ya mana amfani, kar kuma ki manta kwanakin , takwas nace. Ya dad'a jaddada mata snn ya ci gaba da tafiya. Tsaye tayi tana kallon yadda yake taku cikin k'asaita tamkar wanda ya fito daga tsatson sarauta. Saida ya fice daga gidan snn ta sauqe ajiyar zuciya tana mai hura iska ta hancinta tamkar mai fyato abu har sau uku wai ita batason qamshin tiraren shi da ya cika mata hanci, snn ta d'auki B.P.Machine d'inta tayi cikin gida. Ko da ta koma cikin gida harkokinta taci gaba da yi duk da dai tunanin kalar ciwon mutumin yana mata yawo a kai, tambayar kanta take, shin ciwon na gaske ne koko raina mata hankali yayi. Sai bayan sallar isha'i al-amin ya shigo, duk sun baje kan babbar tabarma suna cin abinci. Shima nashi abincin ya d'auko ya zauna kusa da Salma da tunda ya shigo bata kalleshi ba, so yake ya fahimci wani yanayi take ciki. Sai da ta tabbatar ya gama snn tayi qasa da murya tace "Shine ko?" "Wa kenan?" Ya tambaya tamkar bai gane abinda take nufi ba. "Oganka." "Eh shine ,me ya faru?" Shiru ta d'anyi ,daga bisani tace "Wai da gaske bashi da lafiya?" Kallonta yayi da mamaki sai kuma ya maze yace "Ba shi ya fad'i hakan ba?" "Eh, shi ya fad'a, amma ni kalar ciwon ya ban mamaki." "Waye yake rashin lafiya?" Cewar pendonsu. Gum al-amin yayi dan shi dai yasan lfyar oganshi qlau, baisan yaushe ya fara rashin lfyr ba. "Ogan yayanmu." Ta bada amsa. "Assha,Allah ya bashi lfy." cewar Ummi. "Amin." suka amsa baki d'ayansu. Fati tace "Ko shi kika duba d'azu aunty Salma." "Eh, shine." Har tayi shiru sai kuma tayi murmushi mai sauti tare da cewa "Ni ciwon nashi ne ma yaban dariya wlh." "Ciwo kuma ya baki dariya salma, ba kyau irin haka, kar kiyi haka amatsayinki likitta bai kamata ba. "Pendo ,bari man kiji irin ciwon, wai fa kanshi ke mishi Duuuuum, kunnuwanshi kuma suke mishi Shuuuuuu, snn idanunshi kuma wai dishi dishi suke gani , tun kwanaki takwas da suka shige, Ko me ya hana shi zuwa asibiti duk cikin kwananakin? snn abin mamaki yace d'azu idanunshi suna gani sosai saidai yasan zuwa gobe ciwon zai ci gaba. Kuji fa dan Allah. Snn wai zuciyarshi ke bugawa kik." Bata qarasa ba tayi saurin had'iye maganar sakamakon bugawar da tata zuciyar tayi, snn qwaqwalwarta ta fara fassara maganganunshi d'aya bayan d'aya. Dariya al-amin yakeyi qasa qasa a ranshi yake cewa "Lallai oganshi ya iya game, ko ya wasan zata qare?" Dariyar nusaiba ne ya dawo da ita daga tunanin ta fad'a. "Lallai wnn mutumi ya iya rashin lfy, kuma kwanaki takwas, kenan tun ranar da kika k'are makaranta." Nusaiba ta fad'a cikin dariya, Fati ma dariyar takeyi amma ba kamar nusaiba ba. Kan Salma ya kuma d'aurewa da ta tuna jaddada matan da yayi ,wai tayi lissafi ,kwanaki takwas , to lissafin me yakeso tayi. Nusaiba ce ta sake katse mata tunaninta da cewa. "Aunty wato rashin ganinki a hanyar makaranta ne yake tab'a ganinshi kenan." Yanzu kam har su Ummi dariyar salma sukeyi, ita kuwa ta saki baki kamar wawiya tana kallon al-amin. Indai haka ne nufinshi tabbas ya gama raina mata wayo, har da sata gwada B.P nshi. No wonder yace baya bukatar zuwa wajen likita,. "Allah yasa research d'inki ya mana amfani, kar kuma ki manta kwanakin takwas nace." ta kuma tuna kalamanshi. Gyad'a kanta ta shiga yi , ko ba komai nusaiba ta taimaketa, kuma ba wani research da zatayi. To ma ba sai ya sake ganinta bane zai raina mata hankali. K'wafa tayi ta tashi ta barsu a gurin suna ta mata dariya, dan a gurinsu komai a bayyane yake. [17/12 06:25] Hajara: *πŸ’”πŸ’”IN SO CUTANEπŸ’”πŸ’”* *Fasaha Online Writers.* *F.O.W.* *By Anty Rukie (Mmn Abduljalal* 30. πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’” *Wnn shafi kyauta ce gareku Fasaha Grp nvls members 1,2,3,4. muna godiya da dimbin qaunarku garemu.* Shiganta ba da jimawa ba nusaiba tabi bayanta ta zauna kusa da ita. Kafin tayi magana Salma ta riga ta da cewa. Nusai bakiga mutuminnan ba ,very gentle with innocent face, sam bai dace da abinda yayi d'innan ba, ya ban mamaki wlh. Gimtse dariyarta tayi tace "Me yayi miki ne aunty, har kike cewa ya baki mamaki." "karya mana da raina min wayo da yayi, wlh fiskarshi batayi kama da hakan ba sam." "To idan kuma ba karyan bane kike karyata shi fa ,ki bari ki tabbatar tukun ki yanke hukunci. " Tsaki mai qarfi taja snn tace "Ya zaki ce ba qarya yayi ba, mutum daka ganshi kaga lafiyayye ya wani tsaya yi min kwatancen shirme, ni sai yanzu abin yake bani haushi ma. ko da yake har da laifin yayanmu ma wlh, na jima da .. Bata qarasa ba kiran ahmad ya shigo wayarta ,hakan yasa ta dakatar da maganar da takeyi ta d'au wayar tana sauk'e ajiyar zuciya . Shima ajiyar zcyr ya sauqe , kwana biyun da basu had'u bane duk suke ji tamkar kwanaki da yawa suka d'auka basu ga juna ba, nan ma kullum suna waya fiye da sau biyu. Sam sun kasa sabawa da hakan . Hiran su sukayi cikin shauqi da ishqi wanda ya mantar da Salma b'acin rai da take ciki. _Two days later_ Kasancewar ko wani wkend suke wanki kayakinsu , hakan ya kasance yauma har da ya al-amin , suna yi suna hira cikin nishad'i da qaunar juna , su Hamza suke jawo musu ruwa a rijiya suna wankin. Har azahar suka gama kowa yaje ya bada farali snn suka baje dan bawa ciki hakkinshi. Saida suka gama nusaiba da Salma sukayi wanka , nusaiba sai dariyar tsokana takewa Fati dan ita zata yi musu girkin dare kasancewar time table suke dashi ,kowacce da ranar girkinta, shara, wanke wanke. Sai bayan sallar la'asar suka fara tattara kayansu da suka bushe suka fara ninkewa. Da na Ummi suka fara snn suka jibge nasu a d'akinsu suka shiga ninkewa. Na al-amin suka tattara suka kai d'akinshi suna ninkewa, suka ji sallamarshi. Murmushi yayi ganinsu duka biyu a d'akinshi kafin yace nusaiba tazo ya aiketa. Suna fita sukayi d'an kuskus d'insu bata daiji abinda suke cewa ba, sai dariyar nusaiba taji irin na shaqiyanci ma. A ranta take tunanin me nusaiba ta samu take wnn d'an iskan dariya. Can taji shiru, ta dai ci gaba da abinda takeyi, har wani raba kayan biyu tayi tana cewa "Ba dariya zakiyi ba,sai kin karasa ninke kayan nan." Tana cikin ninke kaya tana suruntanta taji abu ya tab'ata a baya,da saurinta ta juya bataga kowa ba sai hijabinta da ta gani a yashe a bayanta. D'auka tayi ta kalla ta ajiye a kan katifar ya al-amin taci gaba da abinda takeyi tana cewa "Nasan babu mai wnn aiki sai nusaiba." Sallama taji a bakin kofar, wadda yasa zcyarta tsinkewa tare da mummunar fad'uwar gaba. A gigice ta d'auki hijabinta ta saka. Sake kwad'a sallamar akayi wanda ya tilasta mata zama yaraf akan kayan da ta ninke, tana maida numfashi tare da dafe kirjinta dake bugawa da qarfi kuma sauri sauri, sbd gane mamallakin muryar. Saida yayi sallama na uku snn ta amsa. Shigowa yayi ya tsaya bakin k'ofar tare da hard'e hannayenshi a kirji, ya tsura mata ido. Kamar yadda bata kalleshi hakama batayi mishi magana ba. Takowa yayi ya iso kusa da ita snn ya tsuguna , sun d'au lokaci a hakan bata kalleshi ba kuma batayi magana ba, kanta a qasa ,fiskarta kuma a daure kamar wacce taga ajalinta. "Da fatar na sameki lafiya Gimbiya." Nanma shiru ba amsa. Wata zuciyarce take fad'a mata ta gaisheshi , ko ba komai ogan yayanta ne, kuma shi babba ne akanta. "Ina yini ." Tace dashi, ba tare da ta d'ago ba. "Lafiya ba sosae ba, dan bani da tabbas." D'an dagowa tayi ta kalleshi jin yadda ya bata amsa tamkar mai rad'a. Wnn karo english wears ne a jikinshi, bazata iya tantance kamanninshi ba tunda ba tsayawa kallonshi takeyi ba. Gyad'a mata kai yayi tare da lumshe ido, hakan yasata saurin kawar da kanta. *08161594233* [17/12 06:25] Hajara: *πŸ’”πŸ’”IN SO CUTANEπŸ’”πŸ’”* *Fasaha Online Writers.* *F.O.W.* *By Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)* 32. πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’” Ko kallonta batayi ba ta d'au buta ta nemi waje ta fara alwala. Hakan ya bawa nusaiba damar ci gaba da abinda takeyi. Saida sukayi sallar magriba sukayi addu'oinsu suka shafa snn salma tace "Nusaiba , wato munafurci kuka kulla ke da yayanmu ko, muna aiki, kika kama hanya kika fita kika barni." "To ni kuma aunty me na sani, yayanmu ne fa ya qirani ya aikeni kuma kinji lokacin da ya kiran." "Ba wani nan ina jinku kuna kuskus kice aikanki yayi." "aikan yake fad'amin kenan lokacin." "Wani irin aika ne ?" Ta fad'a tare da tsare ta da ido. "Haa ah, tace tana 'yar dariya "Sirri ne fa ,yace kada in fadawa kowa." "Nice kowan kenan, in ba munafurci meye na

Chapter 6 of 7