amma maganar gaskiya hakan bai dace ba, dan Allah idan tana kusa ka daina k'irana. Ko ni akaiwa haka bazan ji dad'i ba, kuma irin haka sai ka sa ta rika jin haushina wlh, kuma kaga maganar yawan zuwan nanma da gaske nake ,ka bada ratar atleast kwanaki biyu ko uku kafin kazo, dan itama tasan ka mutuntata."
Saida ya barta ta gama zuba zancenta yace "Idan naqi fa?"
Shiru ta mishi.
Ya kuma cewa "Auntyn asiya nace idan naqifa , me taya kishiya kishi."
Dariya ta d'an yi tace ,"nima sai naqi fitowa kalas."
"Allah, ko, to kalle ni mana ki rika bani amsa, kina magana kina sunkuyar da kai, kalli cikin idona ki fad'a idan da gaske kikeyi ."
Jin tayi shiru ya kuma cewa " ki gwada qin fitowa ki gani idan ban shiga har cikin gidan ba irin ba rannan kema kin san zan iya.
Nifa mamaki ma kike ban yanzu , kwanakin baya har da ciwo kikayi kan kishi amma yanzu ke kike taya kishiyar taki kishi akan kanki.hmm abin har da tsoro mafa ya fara bani , ko dai auren ne yasa kika rage sona salma?"
Kawar da kanta tayi gefe tanaji kamar tayi kuka ,dan ita tasan abinda take ji game da maganar auren nan nashi.
Daurewa tayi tace.
"Kaji tsoron Allah dai ka sauqe haqqin da ya rataya a wuyanka ,kuma kar ka cusa min ra'ayi nikam."
"To naji malama salma , wa'azin ya isa haka."
Ya fad'a yana tunani
a ranshi da yayanshi yasan wacece Salma da bai hanashi aurenta ba.
**** **** ****
Zaune suke cikin falon Ahmad, suna kallon wani indian film d'in da aka sa a bollywood.
Ahmad dai kallo yakeyi amma sam hankalinshi baya ga t.vn.
Tunanin yadda al'amarinshi da Salma zai kasance kawai yakeyi.
Har ga Allah abin ya fara bashi tsoro yanzu, babu abinda yafi d'aga mishi hankali kamar idan ya tuna salma ta kusa gama karatunta amma har yanzu babu alamar yayunshi zasu amince mishi ya aureta, tsoronshi duk ranar da zata ce mishi ya turo magabatanshi.
Ita kuwa asiya kallonnata rabi da rabi ne, tana kallon film, rabin hankalinta kuwa ya karkata ga son gano abinda yakesa Ahmad nisa cikin tunani.
Yawancin lokuta takan ganshi cikin damuwa da tunani mai zurfi, duk da yana kokarin sake mata suyi hira cikin nishad'i, yana bata kulawa daidai gwargwado ,amma ko ba'a fad'a ba tasan yana cikin damuwa.
Kwantar da kanta tayi a kafad'arshi, wanda ya tilasta mishi sauqe ajiyar zuciya , dan ya manta yana tare da mutum cikin falon.
Maida kallonshi yayi kanta snn yace "Ya dai Sal- asiya."
Bata amsa mishi saima kokarin d'aga kanta da takeyi .
Kwantar da kannata dad'ayi yana mai tuhumar zuciyarshi da bakinshi wajen gaza b'oye halin da yake ciki.
A kullum mutuncin yarinyar qaruwa yake a idanunshi sbd hakuri da kuma kawaicinta.
Yasha kiranta da sunan Salma ,duk da dai ba amsawa takeyi ba, amma bata nuna mishi damuwarta ko a fiska ,har ya zamo idan ya kirata da Salma shi da kanshi abin yake bashi kunya.
Asiya bata da matsala, ga haquri ga tsafta ,kullum fes fes zaka ganta daga gidanta har ita kanta.hakan ya bata matsayi mai girma a zuciyar Ahmad, saidai yasan babu abinda zai girgiza kujerar sarautar sarauniyar da ke mulkar zuciyarshi. wato Salma.
K'ok'ari yakeyi kar damuwar da yake ciki ya shafi zamansu , amma ya rasa me yasa zuciyarshi da bakinshi suke nuna gazawarsu.
Kallonta ya kuma yi yaga ta lumshe ido tayi lamo tamkar maijin barci.
"Barci ko?"
Girgiza mishi kai tayi alamar a'a.
A sanyaye tace ina tunanin yaushe zanje inga Adda na ne.
Tausayi ta bashi yanda tayi maganar a sanyaye ,yasan ba wnn kad'ai ke damunta ,amma ya zasuyi dukansu cikin damuwar suke, ya san yama fita damuwa dan a tunaninshi nata mai sauqi.
Yau aurensu watanni hud'u kenan da kwana shida.
Ita kanta tasan zuwa wnn lokaci an samu canji daga ahmad sosae ba kad'an ba.
Tasan haqurinta ya mata rana ya kumayi amfani, shawarwari da naseehar Addanta sun mata amfani sai dai damuwar da take gani a fiskar ahmad wasu lokuta yana d'aga mata hankali., har yakansa taso tasan taqamammen matsalarshi duk da dai jikinta yana bata damuwar bazata wuci a kan yarinyar da yace mata yana so bane.
[17/12 06:25] Hajara: *ππIN SO CUTANEππ*
*Fasaha Online Writers*
*F.O.W*
*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*
21.
ππππππ
Kwanto da ita yayi jikinshi gaba d'aya snn yace mata "Yaushe kike so kije ki ganta?"
Da sauri tace "ko yanzu ma."
Hancinta yaja yana murmushi yace "'Yar adda ,yanzu kam dare yayi ai, saidai gobe ko jibi ko gata ko..."
"Kaiiii...π³ta katse shi tana zaro , wnn dogon lissafi? goben dai dan Allah."
Ta fad'a a shagwab'e.
Ajiyar zuciya ya sauqe "Sai goben to in Allah ya kaimu."
"Allah ya kaimu"
tace zuciyarta fal farin ciki.
"Amma fa tare zamuje mu dawo dan ba jimawa zakiyi a can ba."
"Ayya dai."
Ta fad'a da fiskar tausayi.
"To ba ganin su kawai zakiyi ba?"
"Har da Abba fa ,kasan shi ba lallai ne na same shi a gida ba, sai yamma yake dawowa."
"Sai nayi tunani akai idan naga zan iya."
"Zaka iya ma, naga kai d'inma sai yamma kake shigowa."
"To kuma wa zai min girki?"
Shiru tayi ta rasa ma me zata ce mishi.
"Hmmm, baki ji bane?"
"Naji, basai ka siyo mana ba abu na rana d'aya kawai fa."
"ni kuma naki nakeson ci ya kenan?"
Da sauri tace "to zan dafa maka in na dawo."
"Huta abinki ,da wasa nake miki, Allah ya kaimu goben."
"Ameen ."Tace tana jin dad'in gobe zata je gidansu, dan tunda tayi aure bata je ba sai k'annenta ne suke zuwa mata.
Sai kuma gidansu ahmad da taje sau biyu.
** ** **
Tafe suke ita da k'awarta faleela , paper rik'e a hanunta sai jakarta da ta rataya.
Dukansu biyu sanye suke da uniform na sch. Of nursing.
A nitse suke tafiya suna tattaunawa , hakan yasa Salma bata tari napep da wuri ba, har saida suka zo ta inda faleela zata ratse ta yi hanyar gidansu suka d'an tsaya dan su k'arasa tattaunawarsu.
Sallama suka wa juna kowa ta kama hanyarta .
"Sssssss."
Taji ake signal ,kusa da ita.
Ko alama bata nuna taji ba balle ta juya .
"ke 'yan mata."
Juyowa tayi da murmushi d'auke a fiskarta jin muryar yayanta Al-amin.
"Dama kai kake min wnn k'iran 'yan itskan."
Dariya sukayi dukansu sbd yanda ta ambaci iskan ,ta fitar da harafin s d'inne bayan ta danne harshenta da hak'oranta ta fito dashi tsakanin tsiririn wushiryarta.
Kamar yadda qaninsu khalil yakeyi.
Halittarshi ce haka amma ko da yaushe ya ambaci harafin sai sunyi mishi dariya.
"Me kakeyi anan yayanmu?"
"Aiki mana baki gani ne?"
Ya fad'i yana nuna blocks d'in dake tare a kusa dasu ,labourers sai jida sukeyi suna kaiwa wani wajen da wasu ke gini.
Sai a snn ta lura da blocks d'in.
"Yanzu ya yayanmu haka kake d'aukan blocks d'innan masu nauyi."
"Wa ya gaya miki suna da nauyi."
"Da nauyi mana da gani ma ba sai an fad'a ba."
Ta fad'a tare da sunkuyawa tana kokarin d'aga block guda.
"Wasshh."
Tace tana yarfe hannayenta bayan ta ajiye block d'in da ba wani d'agawan kirki tayi ba sai raki .
"Madam karambani ,kin d'auka aikin da ragwayene irinki."
Ya fad'a tare da dungure goshin ta.
'yar dariya tayi tace "Gaskiya fa kuna kokari yayanmu."
"Neman halas kenan ummulu yana da wuya ."
"Aikam ,Allah dai ya biyawa duk mai neman halaliyarsa bukatunshi,Allah ya sanya albarka a sana'ar."
"Amin ummulun ummi ,muje in raka ki ,kinga sunyi nisa a aikinsu sun barni."
Ya qarashe maganar yana nuna ta gefen da yake ginawa ya bari.
"Au ginin kakeyi kenan?"
"Eh, wad'ancan suke kai mana blocks muna ginawa, gidansu oganmu ne muke renovating."
"Allah ya taimaka ."
Tace ,daga nan suka ci gaba da tafiya, har bakin hanya.
_Two days later_
"Ummulu, an bani saqo na manta ba isar ba."
"Mik'o."
Tace tana mik'a mishi tafin hanunta.
Kallonta ya tsaya yi snn suka tuntsure da dariya dukansu biyu.
"Daga an bani saqo sai mik'o, yaushe kika zama haka?"
Dariya ta kuma yi tace
"Nayi tsammanin kud'i aka baka ka bawa baiwar Allah Salma."
Har da wani marairaicewa.
"To ba shi bane sai ki had'iye kwad'ayinki."
"Menene yayanmu."
"Oganmu ne yace in gaisheki."
π³"Oganku?"
*Slm, fans pls a rika haquri damu , masu magana ta pc da masu yi a grps, duk wanda yayi magana ban amsa ba that means ban gani bane, wasu kuma waiting yake nunawa, and masu magana a grps kuma, ba ko wani chat nake iya bi na karanta ba dan grps d'in sunyi min yawa ,idan nace ko wanne sai nabi na karanta to fa bazan samu time na typing ba, idan har kayi magana a grp ba response ka min magana personally in har na gani zan amsa, so bear with me , ina qaunarku kamar yadda kuke qaunata ,na gode.πππ*
[17/12 06:25] Hajara: *ππIN SO CUTANEππ*
*Fasaha Online Writers.*
*F.O.W*
*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*
23.
ππππππ
"Zauna kiji salma."
Zaman tayi tana fiskantarshi.
"akwai abinda baki sani ba, ogan nan da kike gani?"
Da sauri tace nakeji dai ban tab'a ganinshi ba ai.
"Sorry, da kike ji to.
Duk mutum mai son karatu burge shi yake yi, yanason mutumin da yasan kanshi.
Tun ranar da ya ganki da uniform, kuma nace ke kanwatace , yaji kin burgeshi"
Katse shi tayi da cewa ,ni d'in ce na burge shi ,ko uniform ko kuma karatun?"
"Duka."yace a taqaice.
"Kuma idan kika sake katse ni ,zaki bar nan da rarrafe."
"Afuwan ya akhy."
Ta fad'a tana rike kunnuwa.
"Yauwa kina ji, ce min yayi ,babu yadda baiyi da qannenshi mata ba su karanci science courses, amma sam sunki ,wai da wuya , tsoro sukeji, baza su iya ba, shi kuma yayi burin a cikin k'annenshi a samu doctor ko nurse , ya musu alk'awarin ko nawa zai iya kashe musu ,amma duk sunki, abin takaicin dukansu yaran gidan su babu wanda ya karanci science."
"To shi me ya hana shi karanta ,tun da yana so?"
Harara ya galla, mata tayi saurin rik'e bakinta , "sorry yayan ummulu, mantuwa nayi."
"Baki ji me nace miki bane? K'annenshi mata yace yakeso su karanci course d'in sbd kishin addini da kuma taimakawa mata 'yan uwansu , ko kema ba hakanne ya saki karatunba?"
Gyad'a kai tayi tare da cewa "hakane."
"To shi yasa da yaga kanwar d'an gidanshi tanayi yaji dad'in abin kuma yaga zai iya bada tashi gudumawar ,kuma ba ke kad'ai yake bawa irin wnn kulawar ba, matasan unguwarsu masu kokarin karatu ma yana taimaka musu,snn ko ni nan da kika gani lokacin da nake makaranta ba k'aramin taimakona yayi ba, yanzu haka shawara yake bani da inje in had'a masters , ina fata kin fahimta?"
"Na kusa dai."
"Tashi ki bar na, tunda yau kuma kwakwalwar ta cushe."
Ya fad'a yana mikewa .
Cikin dariyar kular da shi da tayi tace "Tsaya ina da tambaya."
"Shi wani mataki ya taka a karatun, da shi da matarsa duka."
"mts bana son tambayar ganganci, mutum mai karfafawa wani gwiwa yayi karatu, shi kuma me zai jira yana da hanyar karatun."
"To kuma shine ya tsaya aikin gini ,ko yana wani aikinne?"
"Wai ance miki dole mutum idan yayi karatu mai zurfi sai yayi aikin goverment ne? ina ce iliminshi a kwakwalkwarshi take, kuma da abinda ya karanta zaiyi aiki,.
Shi wnn da kike ji babban contractor ne, yana kuma da companyn kayan aikin gini masu inganci, yana da gidan block na musamman ,gari gari ake bashi contract, har k'asashen waje yake zuwa, duk tafiyar da kika ga nakeyi tare dashi ne , dan ina d'aya daga cikin amintattun yaranshi.
Kuma kin san me ?"
"sai ka fad'a."
"Office yake dashi musamman ,government ta san da zama shi ,snn ya da motoci na d'aukan kayan aiki da blocks ba sai ma an nema a wani waje ba."
Tab'e baki tayi tace.
"Allah ya taimaka to, ka kuma ce mishi na gode."
Dan ita gani take b'ata lokacinshi kawai yakeyi wajen son fahimtar da ita ko waye mai gidanshi.
*** *** ***
Ma sha Allah, gidan ahmad yanzu sai sambarka, komai ya daidaita ,zama suke cikin aminci.
Duk da har yanzu babu abinda ya ragu na soyayyar salma cikin zcyr ahmad, haka kuma bayan kwana biyu yake zuwa gun salmar,
Snn daga gunta ma babu wani canji.
Snn babban karin farin cikinshi kuma a iya zamanshi da Salma bai tab'a ganin ta ko yaji labarin an ganta da wani ba.
hakan bai hana shi bawa asiya kulawa ta musamman ba.
A kullum kokari yakeyi yaga ya danne damuwar shi da kuma soyayyar da yakewa salma a gaban asiya, dan a yanzu tana da matsayi na musamman a zuciyar ahmad.
Babban abin da ya k'ara mata matsayi da k'ima a idonshi shine cikinshi da take d'auke dashi na watanni uku.
Rabo kenan.
*** *** ***
Sati biyu da dawowar salis aka sa lokacin bikinsu.
Shirye shirye suka shigayi , tare da salma da pendonsu kanwar mamansu,sai fati, suka shiga kasuwa sukayi wa nusaiba sayayyan kayan kitchen masu kyau, dadai k'arfinsu.
Tun ana saura wata guda biki pendonsu da take kaduna ta iso ,nan ta fara gyara amarya yadda ya kamata.
Cikin kwanakin kuma Salma ta k'are karatunta bayan taci wuya ,har rama tayi.
Farin cikin ta ya gaza b'oyuwa, ba ma ita kad'ai hatta malam da ummi da sauran 'yan uwanta sunyi farin cikin kamalla karatun nan nata ,sai da fatan samun sakamako mai kyau.
Alk'awari ta d'aukarwa kanta ,duk lokacin da Allah ya sa ta k'are makarantar lafiya zata shirya walima , dan nuna tsan tsan farin cikinta da godiya ga Allah da ya bata ikon yin karatun.
Hakan ko a kayi ta fara shirye shiryen walimah ,tare taimakon ,malam, ummi, da al-amin.
Nusaiba taso ta haqura su had'a walimar da na bikinta ,tace sam, bazaiyiyu ba, walimarta daban na bikin nusaiba daban.
*Gaisuwata gareku.*
*Rakiya yakubu.*
&
*Habiba Muhammad.*
[17/12 06:25] Hajara: *ππIN SO CUTANEππ*
'
*Fasaha Online Writers.*
*F.O.W*
*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*
24.
ππππππ
*Ina kike uwa ma bada mama, wnn shafin naki ne, uwa hana kukan talauci, uwarmu abar alfaharinmu, HAJIYA FA'IZA ALIYU BASHIR (Aunty)*
*Allah ya bada tsawon rai mai amfani.*
*Ina alfahari dake mamana.*
Yau suka tashi da shirye shiryen walima , gida ya cika da dangin Malam da na ummi, duk sunzo taya Salma murnar k'are karatunta.
Yadda aka tsara da yamma za'ayi walimar .
Wanka ta fito tana gyara fiskarta bayan ta gama shafa mai.
Fati ko tana fitar mata da sabon kayan da al-amin ya d'inka mata na fitar walima.
Nusaiba ce ta shigo tana mika mata wayarta da take ringing .
"Wayene?"
Ta tambaya tana kallonta.
Mik'a mata wayar tayi tana mita k'asa k'asa "Kullum mutum ya bata waya sai tambaya wayene, tamkar bata san sarkin nacin ne yake kiranta ba."
Bata kulata ba ta karb'a ta kara a kunnenta ita kuma ta juya ta tafi.
"Assalamu alaikum, Ahmad an wuni lfy?"
"Wa alaikumussalam, amma bazan amsa gaisuwar ba."
"Me ya faru."
"Tambayata ma kike me ya faru? Salma yanzu kina ganin kin kyauta kenan?"
"Me nayi ahmad?"
"Ina ko zaki san abinda kikayi tunda yanzu bani da wani matsayi a gunki, fii sabiilillahi a ce zakiyi walima na qare makarantar ki baki sanar min ba , me kike nufi?"
Jimm tayi ta ma rasa abinda zata ce dashi.
"Dole ki rasa ta cewa tunda kinsan baki da gaskiya."
"To ahmad me zan ce maka, naga walimar na mata ne , ko zaka turo amarya ta taya ni murna ne?"
'Yar karamar tsaki yaja ,a kufule kuma yace ,"Idan na mata ne kuma bani da matsayin da za'a sanar dani kenan, da ba don na k'ira nusaiba ta d'auka ba har ayi a gama ban sani ba dan ban kai matsayin ba ko?"
"Allah ya baka haquri ni ba haka nake nufi ba."
"To yayane in ba haka ba?"
Kamar zatayi kuka tace "Ni dai kayi haquri."
Katse wayar yayi yana maijin haushi abinda tayi mishi.
Wato taki sanar dashi ne dan kada ya ce zai d'auki nauyin wani abu.
Mttss yaja tsaki, yasan hakan halinta ne ,tunda suke da ita bata tab'a rokanshi abu ba , snn koshi ya bata ma sai yayi da gaske take karb'a ,wani lokacin sai ya bawa kannenta sukai mata.
Duk da hakan yana qara mata daraja a wajenshi amma yaji haushin abinda tayi mishi ba kad'an ba kuwa .
Saida ta gama shiri tayi d'as da ita kamar wata sabuwar amarya .
Ta cewa fati ta kirawo mata nusaiba.
Suna cikin magana nusaibar ta shigo , itama wankan ta yiyo .
Harara salma ta galla mata, ita ko ta d'auke kanta tamkar bata ganta ba.
"Nusaiba me yasa kika fad'awa ahmad maganar walimar nan?"
Kallonta takeyi baki sake, daga bisani tace "Wai kina nufin dama baki sanar dashi ba ?No wonder yake tambayar ya yaji hayaniya , ashe bai san da maganar ba , amma dai baki kyauta ba wlh."
Har ta d'auki mai zata shafa ta sake juyowa takalli salma "Ina fata ya nuna miki b'acin ranshi kuma kema ya b'ata miki naki ran, wlh nima kin ban haushi aunty, meye abin b'oyewa a gurin abin farin cikin? Wlh in nice shi zai fara sani."
"ke ya isheni haka masifaffiya, yarinya kamar an d'auko hayarki kimin lecture?"
"Allah ya baki haquri aunty, kinyi kyau fa kamar yau za'a kaiki gidan lucky."
Ta fad'a tana washe baki da son basar da zancen dan taga aunty nata har ra fara hawa.
Kafin ta yi magana suka jiyo sallamar friends na salma , suna shigowa suka had'a baki wajen fad'in "Wooww ,sister salma ,kinga yadda kika fito?"
Murmushi tayi tana mika musu hanu d'aya bayan d'aya suna shaking, snn suka zazzauna aka fara chapter.
"Allah ya nuna mana bikinki sister, wnn had'uwa haka ?"
Faleela ta fad'a , dukkansu cikin farin ciki suke ,kowa ta cab'a ado na gani na fad'a.
Wata cikinsu tace wlh nima nanda kwana biyu zakuzo nawa walimar, ina komawa zan fara shiri."
Kwashewa dauka sukayi da dariya "Ke da kika ce sai party, yaushe kika canza shawara?"
Cewar d'aya daga cikinsu.
"na fasa ,nima walimar zanyi ."
Fati ce ta shigo tana ce musu su fito an gama had'uwa su ake jira ,har malaman da zasuyi wa'azi sun iso.
Fitowa sukayi sai zuba k'amshi sukeyi.
Kanwar mamarsu ta kaduna ita tazo ta rike hanun salma tana cewa "Ma shaa Allah 'yata kinyi kyau."
Shadda ta saka zani da riga da d'ankwali purple colour yasha aiki , d'aurin steps tayi a kanta wanda ya dad'a fito da kyaun fiskarta sai gyalenta fari da ta yafa , takalminta silver colour sai purse da agogon hanunta , sarka da 'yan kunne ,abun hanu zobuna duka silver colour.
Simple make up tayi wa fiskarta ,daga powder, kajal sai janbaki colourn kayanta.
Canopies biyu aka kafa cikin gidan kasancewar akwai babban fili a gidan.
Sai da ta fara zuwa ta kwashi gaisuwa gun manyan malaman da aka gayyata domin gabatar da lecture.
*Hajiya Faiza Aliyu Bashir.*(Aunty)
*Hajiya Aishatu (Malama Tasalla.)*
*Malama Mamuji*
Sune manyan malaman da aka gayyata domin gabatar da wa'azi a wnn rana ta farin ciki ga k'awata Salma.
[17/12 06:25] Hajara: *ππIN SO CUTANEππ*
*Fasaha Online Writers.*
*F.O.W*
*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal)*
25.
ππππππ
*Wannan shafi kyauta ce gareku Qungiyar Khairul Umma, at large ban rage ko d'aya ba.*
*Allah ya biyaku.*
Wad'annan manyan mata masu daraja malamai ne daga qungiyar mata musulmai na Jalingo ,dake jahar Taraba .
*KHAIRUL UMMATI*
Qungiyace ta musamman wacce take bada muhimmiyar gudumawa ga musulunci da musulmai.
Aiki suke tukuru wajen ganin sun d'aukaka kalmar Allah, ba dare ba rana.
Suna sadauqar da lokacinsu, qarfinsu, da dukiyoyinsu wajen d'aukaka kalmar Allah.
Lunguna, saquna, qauyuka ,suke shiga dan yin da'awa.
Suna musuluntar da wad'anda ba musulmai cikin hikima, baseera, da ilmin da Allah ya hore musu.
Suna kuma d'aukan nauyin wanda ya musulunta 'yan uwa da dangi suka k'ishi sanadiyyar shiga addinin musulunci.
Karatu ,ci ,sha, sutura ,muhalli, wnn duk basa gazawa wajen d'aukewa masu buqata.
Ruwa da iska, zafi da sanyi , zafin rana, akwai da babu duk ba sa hana su tsayawa tsayin daka wajen ganin sun yiwa addini hidima.
Allah ka sakawa wad'annan bayi naka da alkhairi , ka biya musu buqatunsu na duniya da lahira, ka qara musu lfy, ka basu ikon cika qudurin su na alkhairi.
Ka kare su da kariyarka ,kama karesu daga sharrin dare da rana, mutum da aljan.
Ka kare su daga sharrin dukkan abin qi.
Ka kara d'aukakasu.
Ka basu ikon ida nufinsu na alkhairi.
*Ameen*
Malama Tasalla ita ta bud'e taro da addu'a tare da karatun alqur'ani mai girma.
Daga nan Hajiya Fa'iza ta fara gabatar da lecture akan muhimmancin ilimin 'ya mace.
Muhimmancin karatun likitanci ga 'ya mace a wnn zamani da muke ciki, wanda ma'aikatan asibitoci suke d'aukan ran musulmi ba a bakin komai ba , ake wulakanta musulmai, a tozarta su ,ana musu kallon banza da raini, ana ganinsu basu san komai ba, more especially mata masu ciki in anzo wajen haihuwa.
Tayi magana akan likitoci musulmai da suke biyewa colleagues nasu wad'anda ba musulmai ba wajen kin taimakawa da tausayawa ga 'yan uwansu musulmai.
Sai kaga an kawo mace mai nakuda ,tana fama, ace idan ba kud'i baza'a karb'e taba.
Ko da kud'in ma baza ta samu isasshen kulawa ba tunda musulmace kuma ba a ga maiko a tattare da ita ba.
Su kuma 'yan uwan namu musulman sai su nuna halin ko in kula ga lamari.
Shin tsoro ne ko kuma qangarewar zuciyace.
Wata ma kina gani musulmace 'yar uwarki, sai arne ko arniya ta tsaya kanta tana bata kalmar "JESUS."
Instead ke ki bata kalmar shahada.
Allah ya tsare.
Wani abin takaicin zaka ga mace tana fama ,wai dan ta d'auki lokaci bata haihu ba dan kar ta b'ata musu lokaci sai a nemi mijinta ko 'yan uwanta ace su sa hanu za'ayi mata tiyata bazata iya haihuwa da kanta ba, ke kuma 'yar uwa musulma kina gani kin yi shiru baza ki taimaka da baiwar da Allah ya baki ba.
Nasan ba duka aka taru aka zama d'aya ba ,amma masu taimakon basu da yawa.
*Sister Jamila Usman Nyaja (Mmn Al-Mustafa)* kina kokartawa, kina bawa mata kulawa ta musamman naji daga bakin mutane da dama .
Allah ya saka miki da mafificin alkhairi.
Nurses kuji tsoron Allah, ku tausayawa 'yan uwanku musulmai ,ku taimaka musu da iliminku, Lokacinku da kuma aljihunku inda hali.
Akwai lada mai tarin yawa cikin wnn aiki naku,.
Nan dai Hajiya Fa'iza ta rika kwad'aita musu lada da kuma falalar dake cikin wnn aikin.
Har Salma da sauran colleagues d'inta suna jin zasu iya bada kowace irin gudumawa ta fannin wnn karatu da sukayi.
Gaba d'aya sun kwad'aitu da falalar da ke cikin wnn aiki.
Karshe ta bawa iyaye shawara da k'arfafawa yaransu gwiwa dan su rika karanta science courses sbd mu samu wadatuwar likitoci musulmai.
Daga nan Malama Mamuji ta karb'i wa'azin inda ita kuma tayi fad'akarwar akan mata ma'aikatan gwamnati da suji tsoron Allah , su rik'e mutuncinsu da mutuncin aurensu.
Su kame kansu aduk inda suka tsinci kansu.
Su guji cin amanar Allah, da ta mazajensu.
Snn ta zayyano d'imbin azabar da tab'ewa da ke jiran duk mace mara tsoron Allah, mai cin amana , mai munafurci da annamimanci.
Wayyo Allah , kuzo kuga yanda guri yayi tsit, tsoron Allah ya Shiga zuqatan mahalarta wannan taro .
Kuzo kuga idanuna yadda nake zaro su ,ina bin aminai na da kallo, Maryam Mazad, Amina Sale Muri, Lubabatu kyauta, Salamatu Ibrahim Bawa, Ummul kulthum Aliyu Bashir, Nafisa D'ahiru,Hajara Aliyu, Sister Jamila, Sadiya sale, Jamila Mu'azu, Maryam Adamu lanko,Sadiya Ibrahim, ga kuma swt sister Halima Auwal, Ga Nafeesat (Mrs Bashir Bello.) Kai ,muna da yawa fa.
Sai zura gula gulan idanunsu sukeyi, anji maganar lahira.
Malama mamuji badai iya sa tsoro ba, idan tana wa'azi sai kaji kanka na juyawa, kwakwalwarka na amsa quwwa, tsigar jikinka na tashi, ka rika jin wani zuuuuuu irin kana gangarawa lahirannan.Lol.
Allah kasa mufi qarfin zuqatanmu.
Ana cikin wa'azi sai ganin almajirai akayi suna shigowa da kwalayen juices da snacks.
Mikewa salma tayi tana rarraba ido , can ta hango Nusaiba ,zaune tayi zugum jiki a sanyaye, alamar wa'azi ya shigeta.
Cikin sanyin jiki ta ...
Na gaji wlhβΉ
[17/12 06:25] Hajara: *ππIN SO CUTANEππ*
*Fasaha Online Writers*
*F.O.W*
*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal)*
26.
ππππππ
*Wnn shafi kyautace gareki Hauwa .S. Zaria, nagode da qauna Allah ya bar zumunci.*πΉ
Cikin sanyin jiki ta fara ratsa mutanen har ta isa wajen nusaiba ta kamo hanunta.
Saida suka fito sarari snn suka tsaya.
Lokacin nusaiba ta lura da kayan da ake shigowa dasu, ta tambayi salma daga ina.
Itama tace bata sani ba, dalilin da ya sata nemo ta kenan.
Kafin su qare maganarsu almajiran har sun gama sun fita.
Sbd haka nusaiba taja hanun Salma tana cewa "Zo muje mu duba."
Suna fita suka ga wucewar motar ahmad, sai almajirai a gefe da suke rabon kud'i.
"Ahmad ne wlh."
Salma tace tana nuna motar.
Kafin nusaiba tayi magana sai ga wata bak'ar mota mai tinted glass tazo ta parker kusa dasu, sai sheqi takeyi.
Babu ta yadda zasuga na ciki, sai na cikin ne yake kallon su.
Kamo hanun nusaiba salma tayi tana cewa ,"Mu koma to, tsayuwar me mukeyi.
Har sun kusa kofa suka ji ya al-amin na k'iransu .
A tare suka juyo ,suka saki murmushi a tare.
"Yayanmu nayi missing d'inka yau wlh."cewar nusaiba.
"Ke kikayi missing d'inshi ko ni, tunda garin Allah ya waye ban sashi a ido ba ,inajin ma tun asuba ya bar gidan."
Salma tace.
"'yan matan ummi kunga yadda kuka yi kyau kuwa, ku tsaya na muku hoto."
Al-amin ya fad'a lokacin da ya iso dab dasu ,ya ajiye k'atuwar ledar dake