Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 7
mata. Tuni kuma jikinta ya amshi sakon . "Ya Ilahi." Ta furta tana jin yadda zuciyarta ke bugawa . Da sassarfa ta shige cikin gidansu tamkar ana hankad'a ta. Bata yi gigin tsayawa wani tunani ba gudun kada 'yar sa ido ta gano ta . Da saurinta ta shige d'aki, ta jefa jakarta kan gado snn ta jinginu da jikin bango ta runtse idanunta ,jikinta har rawa rawa takeji yakeyi. Murmushi ne ya sub'uce mata da ta tuna killer smile d'in da ya sakar mata d'azu. Dafe kirjinta tayi tace a hankali "Ahmad zaka kashe Ummusalma." Still idonta a rufe ,ta kuma sakin wani murmushin. "Akwai good news kenan auntynmu." Ta tsinkayo 'yar sa idonta tana fad'a. Saurin bud'e idonta tayi ta watsa su kan Nusaiba ,take kuma ta daidaita nutsuwarta ,ba tare da tayi magana ba ta zare hijabin jikinta snn ta zauna bakin gadonsu tana maida numfashi a hankali. Binta da kallo Nusaiba keyi can ta tab'e baki tace "Yau kuma da abinda aka dawo kenan." Ganin bata kula ta ba yasa tayi sum sim ta fice daga d'akin. Washegari kasancewar weekend ne babu inda Salma taje tana gida suna wankin kayansu dana Ummi dana khalil, dan duk weekend suke had'a kayan su wanke. Sosae ta sake suna ta zuba hira cikin raha da kannenta dan ta kore duk wata tunanin Ahmad daga zuciyarta, saboda taga Nusaiba gab take da ganota . Kwance take kan sallaya bayan sallar magrib ,cazbaha rike a hanunta amma kuma ba abinda takeyi dashi sai fiskar Ahmada dake mata gizo , idan ta tuna murmushnsa sai itama ta murmusa. Ganin abin yaki barinta yasa ta d'an daki kanta tare da cewa "Wai meye haka ne." Nusaiba da Faty da suke ninke kayan da suka wanke duk suka juyo suka kalleta. "Me muka yi miki aunty." Cewar Nusaiba. Harara ta zabga mata "Ke kuma waya kasa da ke." "Au da Faty kike , me tayi to." Faty tayi saurin cewa "Ni kuma?" Karamar tsaki tayi ta juya musu baya taci gaba da kwanciyarta, tunani ta shigayi ,lallai asirin zuciyarta ya kusa ta tonuwa . "Me yasa Ahmad ya shiga zuciyarta haka . Me takeji wnn game dashi." Ni ko nace Na love ohhh my sisi. Tsaki ta kuma ja wanda ya tilastawa su Faty kallonta snn suka kalli juna. Aunty Salma dake hana su yawar tsaki yau ita ke da kanta take ta zabgawa. Lallai akwai matsala. *Mmn Abdul &Noorain.* [17/12 06:24] Hajara: *πŸ’”πŸ’”IN SO CUTANEπŸ’”πŸ’”* *Fasaha Online Writers.* *F.O.W.* *By Anty Rukie "Mmn Abduljalal.)* 5. πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’” Haka ta karaci kwanciyarta da tunaninta har taji an tada sallar Isha'i snn ta tashi ta bada farali. Karatunma yanzu idan anayin shi rabi karatu rabi tunani. Wani lokacin tana cikin karatu sai ta lumshe ido ta kama murmushi ita kad'ai. Ah lallai abun azeemun. Ranar sunday da dare bayan sallar isha'i tana kwance ta tashi taci abinci taki firr, ko da Ummi ta matsa mata sai cewa tayi batajin dad'in jikinta , ciwon kai zazzab'i ,ciwon ciki . Hhhhhh kodai ciwon zuciya Madam Salma. Ita kanta ta rasa takamammen wanda zata ce yake damunta. Ummi ta matsa mata dakyar ta tab'a kad'an ta cire hanu ta koma ta kwanta. Yanzu abinda take ji yafi karfin tunaninta . Zuciyarta nauyi yake mata, ji take kamar ta fitar ta huta. Ummi tace ta tashi su tafi asibiti nan kuma tace abin baikai haka ba. Taje ko chemist ne su Nusaiba su rakata a bata magani nanma ta dad'a narkewa bata son zuwa. Dama kuma sun san halinta sarai bata son magani bare uwa uba allura. Dama haka likitocin suke ?πŸ€” Ga tsoron allura su kuma sun iya tsirawa mutane.😊 Ko k'arya nayi Mmn al-Mustafa?😜 Sallamar yaro ne ya dakatar da Ummi daga fad'an da takewa Salma na kin magani. Dukansu suka amsa sallamar yaron suna maida hakulansu gareshi. "Ana sallama da Salma inji wani a waje." Rass Salma taji gabanta ya fad'i. A ranta tace Allah yasa Ahmadunta ne. "Kace batanan ." Ta tsinkayo Nusaiba tana fad'a, dan tasan amsar da zai samu kenan daga Salma. Abin mamaki sai sukaji tace a hankali. "Bari inje in duba inga ko wayene." Zuruf ta ta mike taje tana zura hijabinta. "Kai." Nusaiba ta kwala wa yaron kira dan har ya fara tafiya. "Kace tana zuwa." Galala Ummi tayi tana binta da kallon mamaki. Suma kannenta matan da mazan duk haka abun yake a wajensu. Salma da lafiyarta ma yaushe ta fita ta saurari wani bare kuma ba lafiya. Sumi sumi tazo ta wuce su tayi hanyar kofar gida. Tsayawa tayi tana leka ta kafar gate d'in "Hmmmmmm" ta sauke doguwar ajiyar zuciya. Wanda take fata da muradin gani shi ta hango tsaye ya zubawa kofar fitowa ido. Dafe kirjinta tayi ta lumshe ido tana murmushi . Wani sanyin dad'i taji yana ratsa ko wani sassa na jikinta. Minti biyu ta d'auka tsaye a wajen ,tunanin yadda zata fita takeyi tunda bata saba ba. A hankali take takowa cikin nauyi da kunya . Shiko gogan ido ya zuba mata kamar ya jawota ta iso da wuri. Ma k'asa yace "Faruk fito gatanan zuwa." Tana isa Faruk yana fitowa daga cikin mota. A kunyace ta gaishesu ba tare da ta d'ago ta kallesuba. "Malama Salma sai kika ga bak'i ba zato ko?" Cewar Faruk. "Hmm " kawai ta iya cewa. "Laifi kika mana muka biyo ki fa." "Laifi kuma ?" Tace a hankali tana mai d'ago kanta. Caraf suka yi 4 eyes da gogan ,ai a d'ari ta sauk'e kanta. "Laifi babba ma kuwa malama Salma." Cewar Faruk. "Kin sace min zuciyar aboki , kin hana mishi sukuni ,ya gaza samun nutsuwar zuciya. Da fatar za'a taimaka a agaza a maida mishi zuciyarshi ta koma daidai." Dad'a sunkuyar da kanta tayi tanajin ni'imtacciyar iska na shiga jikinta. "Salman, fili dominka sai ka kokarta ka amso zuciyarka. Faruk ya sake cewa . Kan su ankara har Faruk ya bar wajen. "Kaji min d'an iska ,zai tafi ya barni da ita." Ahmad yace a zuciyarshi yana mai bin Faruk da kallo. Haba Ahmad kamar ba namiji ba?πŸ€” Salman kuma? Ta maimaita sunan da taji Faruk ya kirashi dashi a ranta. Ita dai da Ahmad tasanshi to ya akayi yau kuma aka kirashi da Salman. "Uhm uhm" Ahmad ya d'anyi gyaran murya yana gyara tsayuwarshi tare da daidaita nutsuwarshi. Yau ga dama ta samu ba sanya. Kallonta yai still kanta a k'asa ,so take ta d'ago ta kuma kallonshi amma nauyinshi da takeji ya hana ta yin hakan. Kokarin bud'e baki takeyi tace mishi su shiga daga ciki dan bata saba tsayuwa haka ba ,amma bakinta ya gaza bud'uwa. Gaba d'aya kunya ya gama mamayeta. *Mmn Abdul &Noorain.* *Wnn shafin naku ne.* Reederh Malaysia Mmn sadeeq Zaa princess Foulani cerdia. [17/12 06:24] Hajara: *πŸ’”πŸ’”IN SO CUTANEπŸ’”πŸ’”* *Fasaha Online Writers.* *F.O.W* *By Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)* 6. πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’” A tsanake yafara gabatar da kanshi snn yaci gaba da bayanin abinda ke tafe dashi. Nishad'i suke ji dukansu hakan yasa basu gaji da tsayuwar dasukayi a wajen ba. Fitowar kannenta ne ya ankarar da ita abinda ta aikata ,sai yanzu ma ta tuna cewar bata da lafiya. Abin al'ajabi kuma ko alamar ciwon bata ji ayanzu. Sallamar shi tayi da cewar zata shiga gida dare yayi. Shikam ta biya shi a hakanma tunda ta tsaya ta saurare shi, ga dukkan alamu kuma ya samu karb'uwa duk da ba sakewa tayi da shi sosae ba amma ya fahimci kunya ce ta mata yawa. Al-amin ne ya zo shigewa yaga abinda ya bashi mamaki ,wato Salma tsaye da wani da gani kuma zance sukeyi . Baiyi k'asa a gwiwa ba ya nufi inda suke. Sallama yayiwa Ahmad tare da mika mishi hanu suka gaisa.Mamaki yake da kuma jinjinawa sa'a irin na wnn bawan Allah. Bayan ya wuce Ahmad ya tambayeta "Wannan shine yayannamu?" Kai ta gyad'a mishi alamar eh. Snn ta kuma cewa zata shiga dare nayi. Sallama sukayi har ta fara tafiya ya dakatar da ita. "Gimbiya a taimaka min da phone no. Ko zan samu bacci mai dad'i." Ya fad'a yana zaro wayar shi daga aljihu. Dawowa tayi ta amshi wayar ta saka no. Snn ta juya ta nufi gida. Har ta shiga yana tsaye a gun yana kallonta. Sai bayan ta shiga ne tukun ya nemi layin Faruk yace mishi yazo su tafi. Rufe kofar gate d'in tayi ta juya zata shige ciki taji an riko hijabinta. A tsorace ta kalleshi. "Yayanmu ka bani tsoro wlh." Ta fad'a a shagwab'e. "Sorry Ummulun Ummi, wani baban sa'a ne wannan ,har aka fita mishi da darennan." "Kai yayanmu ai ka bari mu shiga ciki ko?" Ta fad'a tana yin gaba. Binta yayi a baya yana cewa "Abinne ya ban mamaki, lallai wannan gaye mai sa'a ne." Suna shiga ciki ta ga Ummi zaune tare da khalil tana k'ara mishi karatun Qur'ani. Binta Ummi tayi da kallo ,ita kuma duk kunya ya gama cikata da tuna a yadda ta fita daga gidan daga cewa barin je inga waye. "Ummulu ya jikin ?" Ummi ta tambayeta. "Jiki kuma ?" Ta mayar wa ummi tambayar. "Dama bata da lafiya ne Ummi." Cewar Al-amin. Kwance take anan tana kukan ciwon kai, ciki, da zazzab'i aka aika kiranta, kaga yanzu har tambayata take wai jiki kuma?" Cikin zolaya Nusaiba tace "Ita tama manta bata da lafiya fa Ummi." Al-amin ya cab'e zancen da cewa "Maganin ciwon ne dai yazo." Yauwa al-amin ka canka dadaiπŸ‘Œ Itakam tuni ta shige d'aki dan kunyar Ummi taji da gaske. Shi kuwa al-amin sai ya k'ara da cewa "Meye sunan sirikin namu." "Lucky." Nusaiba ta bada amsa har da d'aga murya yadda Salma zata jiyo ta. "Kuma fa hakane." Al-amin ya fad'a yana dariya." Cikin farin ciki da annashuwa Ahmad ya koma gida ,yau jinshi yake kamar ya sauke wani kaya mai nauyi, jinshi yake sakayau. Ji yake tamkar babu kamarshi babu kuma wanda ya kaishi sa'a. Saida ta gama juyinta kan gadonsu cikin farin ciki snn ta d'au litattafanta ta fara dubawa. Har su Nusaiba suka shigo karatunta take yi hankali kwance cikin nishad'i ,ta kwana biyu bata karatu mai dad'i irin na yau ba. Karar wayarta ce ta katse ta , dubawa tayi taga new no. Jikinta ya bata cewar Ahmad ne ,sbd haka fiskarta d'auke da murmushi ta d'aga wayar. "Na kira nace miki na isa gida lafiya ne, na kuma miki mu saida safe." Murmusawa tayi snn tace "Na gode ,mu kwana lafiya." Ci gaba tayi da karatunta tayi bayan ta ajiye wayar, su Nusaiba duk sun kwanta. Can tayi nisa da karatunta ta sake jin wayar na ringing. Dubawa tayi taga shi d'inne. "Bakiyi barci ba?" Tambayar da ya jefo mata kenan bayan ya amsa sallamar da ta mishi. "Yanxu zanyi." "Me ya hana kiyi tun d'azu." "karatu nakeyi ." "Karatu kuma da darennan ,taimakeni dan Allah kiyi baccin yanzu." "To ai kaima bakayi yi baccin ba." "Jikina ne ya bani bakiyi ba shi yasa na kasa yi." "Hmm, Mu kwan lafiya ." Tace tare da kashe wayar kamar ita ta kira. *Mmn Abdul &Noorain.* [17/12 06:24] Hajara: *πŸ’”πŸ’”IN SO CUTANEπŸ’”πŸ’”* *Fasaha Online Writers.* *F.O.W* *By Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)* 7. πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’” Kamar yadda yace hakan kuwa tayi dan rufe littafan tayi ta adana su a ma'ajiyarsu. Alwala taje ta d'auro ta yi addu'oin da ta saba yi kafin ta kwanta. Soyayya mai karfi ya shiga tsakaninsu har ya zamanto basa iya yin kwana d'aya basu sa juna a idanunsu ba. Sau d'aya ya tab'ayin tafiya ta harkar kasuwancinsa . Hhh wnn lokacin sun ji a jikinsu dukansu biyu. Kwana biyar kacal yayi amma ji suke kamar sun shekara basu had'u ba, duk da cewa basu d'aukan lokaci mai tsawo sai sunyi waya. Daga nan kuma yace bazai kuma tafiya irin haka ba ,koma me ya taso zai tura yaranshi . waya kuma ako da yaushe cikin yinshi suke kamar ba ita ke jin haushin Nusaiba idan ta ishe ta da amsa waya ba. Snn kuma duk dare sai yayi ta kiranta yace ta kwanta ta huta baya so ta wahalar mishi da kanta ,baya kuma barinta sai ya tabbata ta kwantan. Karatu kam yanzu tab'a shi dai ake sama sama ba kamar yadda ta keyi da ba. Ita kanta ta rasa abinda yasa take biye mishi yake hana ta isasshen karatu duk son da takewa karatun kuwa. Da gaske zuciyarta ke mishi biyayya akan duk abinda yakeso ko da bata so hakan ba. Zaune suke k'asar bishiyar mangoro dake cikin gidansu suna shan iska. Ummi, Fati, sai kuma Salma , Ummi da Fati tsintar shinkafa sukeyi ,itako Salma jan lalle take zana wa yatsunta. Nusaiba dake cikin d'aki tana gyara ne ta fito rike da wayar Salma ta zo ta kara mata a kunnenta . Da hanu ta tambayeta wayene. Kamar tana jira tace "Waye kuma banda Lucky." Sallama tayi ya amsa ,suka gaisa tana satar kallon Ummi , Ummi ko kallonta batayiba ,idonta na kan trayn shinkafarta. Bayan sun gaisa tace mishi yayi hakuri aiki take yi zuwa anjima zata kirashi. Cire wayar Nusaiba tayi daga kunnen Salma ta nemi waje ta zauna. "Yauwa aunty Salma ya kamata ki d'an takawa yayannan namu birki hakanan. Kiran yana yawa ,atleast da dare kam ya bar ki kiyi karatu ,amma bini bini kira ,gaskiya zai wargaza mana tsari , yanzu fa sam bakya karatu kamar da." Ta karashe maganar tana satar kallon Ummi. "Adda magana ." Cewar Fati ,tana hararar Nusaiba. Itama Salma Hararar ta zabga mata snn tace "To maganad'isu ,yaushe kikaga banyi karatu ba, naga lokacin da nake karatun duk kunyi nisa a bacci." "A da kenan, yanzu kam ina zaki barmu muyi bacci mai nisa yanzu yanzu karar waya a ishe mu kuma da kashe murya." "Taraba state broadcasting service (T.S.B.S.)" Cewar Fati. Nusaiba ta amsa da "A a kin manta T.T.V. ne Taraba television." "Kin shiga uku da gulma Nusaiba ,dan tsabar gulma har wani ina hana ku bacci ,Sa idonki dai ya hanaki kada ki min sharri." Gyara zama tayi ta fara magana seriously "Aunty ki ture batun wasa, wlh ba gulma ko sa ido ,abinda na lura dashi nake fad'a nifa gani nake kamar Lucky bai damu da karatunki ba ,idan ya damu k'arfafa miki gwiwa ya kamata yayi ,amma kullum shike hana ki karatun ,anya wnn idan a gidanshi kike zai barki kiyi karatunma?" "Kai Adda Nusai kamar wacce aka aiko?" Cewar Faty. Zare mata ido tayi "Ke ban hana ki kirana da Nusai d'innan ba, ki kirani da full name d'ina 'yar rainin hankali, kuma daga fad'ar gaskiya sai ace an aiko ni, nifa so nake auntynmu ta fito da result mai kyau amma wnn d'an wailawan yana so ya kawo mana cikas." Ummi har yanzu bata kallesu ba balle tayi magana amma tana sauraron duk abinda suke cewa. Itako Salma kogin tunani ta fad'a ,maganar Nusaiba fa gaskiya ce ,tunda take tare dashi bai tab'a kawo mata maganar karatunta ba ,bai tab'a tambayarta burinta idan ta gama karatu ba ,kuma ko ya kirata tace mishi tana karatu bai tab'a ce mata Allah ya bada sa'a ko ya taimaka ba, shi dai kullum maganarshi ta amince ya turo manyanshi, kuma bayaso a d'au lokaci ba'ayi bikinsu ba. To me hakan yake nufi. Fati ce ta matso kusa da Nusaiba tace a hankali "Munji mama Nusai, zamu gyara, uwarsu matar ubansu." D'aga hanu tayi zata d'aka mata duka ta goce ta sake binta sai ta arce tayi cikin d'akinsu tana dariya. Kan gado ta fad'a tana dariya tana d'agawa Nusaiba hanayenta tare da cewa "Na tuba bazan kara ba Mama Nusai." Dariyar har kamar shaketa yakeyi . Lallai yau fati ana jin raha. Itama kanta Nusaiba dariya abin ya bata sai ta fad'a kusa da fati itama tana darawa. Tsagaita dariyar Fati tayi snn tace. "Fisabilillahi me yasa kikawa auntynmu haka, kinga bata ji dad'in abin ba wlh, nasan gaskiya kika fad'a amma dakin yi mata magana tsakaninku Ummi bata wajen." "Hmm baza ki gane bane Fati aunty tana yiwa mutuminnan matsananciyar soyayyar da ba lallai bane da saurareni ta fahimci abinda nake nufi. Da gan gan na mata haka ,ko ba komai nasan Ummi zata mata magana kuma in shaa Allah zata saurareta ta gyara." "Allah ya sa to." Fati tace. A can waje kuma su fati na barin wajen Ummi ta d'ago ta kalli Salma. "Ummusalma." Kusan a firgice ta d'ago "Na'am Ummi." *Mmn Abdul & Noorain* [17/12 06:24] Hajara: *πŸ’”πŸ’”IN SO CUTANEπŸ’”πŸ’”* *Fasaha Online Writers.* *F.O.W* *By Aunty Rukie (Mmn Abduljalal.)* 8. πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’” *Gaisuwa da fatan alkhairi masoya a duk inda kuke, ina kaunarku fiye da yadda kuke qaunata* *Gaisuwar ban girma gareki ummu D'alhat, Allah ya bar zumunci.* *Maryam A.I Gital* Kina raina ,Allah ya qara miki lafiya da basira. *Ciwo lokaci guda yake shiga ,amma sauqi sai a hankali, Alhamdulillah, na samu sauqi 'yan uwa saidai fatar Allah yasa ciwon ya tafi gaba d'aya.* *Naji jiki wollah.* "Nasan Nusaiba bazata yi miki k'arya ido da ido ba, kai ko a bayan idanki ma banyi tsammanin haka ba , abinda nusaiba ta fad'a yana kan hanya ,muddin kika biyewa Ahmad ya hanaki karatu baki kyautawa mal.ba. Mal. Ya yarda zakiyi kuma zaki iya shi yasa ya tsaya tsayin daka na ganin kin yi karatunnan domin cikar burinki. Duk da cewa tun farko aure yaso ya miki kika nuna ke karatun kikeso kuma ya biye miki. Kina tunanin zai ji dad'i idan lokaci guda kika watsar da wahalar dayayi na ganin kin cika burin ki." Kanta a duke tace "kiyi hakuri Ummi bazan k'ara ba." "Baza mu takura ki ba Salma idan auren kike so yanxu ki sanar damu dan baza mu tauyeki ba kinga sai in sanar da Mal. a fad'awa Ahmad d'in ya fito." Girgiza kanta ta shigayi "A'a Ummi wallahi sai na k'are karatun." "Ni dai na gaya miki kika ci gaba da biye mishi kina wasa da karatun matakin da zamu d'auka kenan." "In shaa Allah daga yauma an dena Ummi kiyi hakuri." Fati ce ta iso ta karb'i shinkafan da suka gyara tana kallon auntyn tasu da gefen ido ,dan son gane wani yanayi take ciki. Saida ta wanke lallenta snn ta bar wurin , tana isa kofar d'akinsu ta samu nusaiba zaune daga gefe tana kankare k'umbunanta . Kurr nusaiba ta kureta da ido ,itako tayi kamar bata ganta saima d'an murmushi da tayi ta wuce ta . Saida tazo ta bayanta snn ta talle keyar ta tare da cewa "wani irin kallo ne haka kamar baki da gaskiya. Ajiyar zuciya ta sauke dan duk a zatonta auntyn tayi fushi da itane. "Sorry my aunty ,ciwon sub'ul da baka ne ya kamani d'azu a gaban ummi." "Allah ya shirye ki uwar 'yan magana , Mama nusai." Ta karashe maganar tana murmushi dan tasan ta tsokano ta. Cuno baki nusaiba tayi "Allah zanci kaniyar Fati." "Nawa dai zaki ci tunda ni na fad'a." "Wane ni swt aunty ita dai da ta fara kirana da sunan." Haka suka ci gaba da rahansu tamkar babu abinda ya faru. Kamar yadda ta alkawarta haka ko akayi bayan yazo sun sha firarsu zai tafi yake ce mata sai tajishi anjima idan ya kirata. "Yauwa Ahmad dama akwai wata maganar da nakeso muyi da kai." Dawowa yayi ya zauna "Ina jin ki sweety na." Sai da ta d'an murmusa kafin ta fara magana. "Dan Allah Ahmad kiran daren nan nakeso ka d'an rage dan yana shiga lokacin karatuna ,bana samu nayi karatu kamar da wlh." Tunda ta fara magana ya kafe ta da ido har ta gama . "Karatu dai, karatu dai." Yace a ranshi. "kayi shiru Ahmad." "Salman dai." Yace mata fiskarshi d'auke da murmushi ,dan ya lura duk lokacin da aka ce mishi Salman sai tayi ta mishi kallon mamaki. "Wai ni me yasa ake ce maka Salman ." "To meye sunan idan ba Salman ba." "Ahmad nasanka dashi nidai." "A da kenan, tunda Ahmad ya had'u da Salma ya zama Salman, ina fata kin fahimta." "Lallaima Ahmad, to ni bansan wani Salman ba Ahmad na sani." "Daga yau na soke Ahmad d'in Salman zaki kirani." 'yar dariya tayi "Cabb, ni Ahmad na sani kuma shi zan kira ban san wani salman ba ehe." Ta karashe maganar harda d'an murgud'a bakinta. Ciza lower lip dinshi yayi yana binta da kallo tallabe da hab'a fiskarshi d'auke da murmushi. "Baka ce komai ba Ahmad." Tuni fara'ar fiskarshi ta d'auke ,shi da yayi tsammanin ya shashantar da maganar ashe bata manta ba. "To me kike so ince tunda rowar muryarki kike so kimin." Marairaicewa tayi tare da cewa "Ba haka bane Ahmad ,hiran yana tsawo yana affecting karatuna, har an gane a gida bana karatu kamar da, kuma kaga ina cikin shekaran karshe ne na gamawa, ya kamata in maida hankali sosai ko dan na samu sakamako mai kyau domin cikar burina." Tsura mata ido yayi na d'an lokaci yana nazarin kalamanta ,daga baya yace "Menene burin naki ." "Na zama nurse of course ,naga ina taimakawa 'yan uwana da sauran al'umma idan rashin lafiya ta samesu." "Akwai matsala ." Yace a ranshi, dan yasan da wuya iyayenshi su amince da hakan. "Salma me zai hana ki amince ayi aurenmu idan yaso ki kammala karatun a gidana." Shiru tayi nad'an lokaci tana tuno maganar Nusaiba. "Wnn idan kina gidanshi zai barki kiyi karatun ma?" Tunowa da hakan da tayi yasa ta fara girgiza kai. "Gaskiya Ahmad ,A'a, ka bari dai na kare karatun idan yaso ayi komai kafin na fara aiki." Shiru yayi yana tunanin yaya danginshi zasu d'auki wnn al'amari su da sukewa karatun boko fassara ta daban musamman ga mace. Zai jarraba sa'arsa ya gani idan har ya aureta koma me za'ayi ayi ,idan su zasu janye ra'ayinsu falillahil hamdu , idan kuma itan ce zata hakura da cikar burinta ,duk dai wnn sai ta shigo gidanshi . *Mmn Abdul&Noorain* [17/12 06:24] Hajara: *πŸ’”πŸ’”IN SO CUTANEπŸ’”πŸ’”* *Fasaha Online Writers.* *F.O.W* *By Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)* 9. πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’” *In dedication to my swt sisto Haleema Auwal (Mmn Aysha.)* Jin shirunshi yayi yawa ne ,ya sata shiga damuwa, dan yanzu ta dad'a tabbatar da maganar nusaiba ,Ahmad baya son karatunta ,idan ta sake ta shiga gidanshi kuma tayi ban kwana da cikar burinta. Hakan yasa ta mike a sanyaye ta mishi sallama tun bai amsa ba dan yayi nisa a tunani ,tayi gaba abinta. Shiganta d'akinsu ta zauna ta jinginu da bango , a ranta take cewa "Lallai nusaiba ta hango mini abinda na gagara hangowa kaina, yanzu idan yace bazanyi aikin ba hakura da aikin zanyi koko dashi zan hakura. Tana tuna yadda za ta hakura dashi taji gabanta ya bada damm, juya kanta ta shigayi ,"bazan iya ba ,duka biyu ina so." Ta fad'a a bayyane. Shi kuwa Ahmad kanshi ne yad'au caji, tunani yake yi lallai idan yayi sake Salma zata guje shi akan karatunta dan ya lura ba karamin kwallafa ranta tayi akai ba ,ina mafita. Mafita d'ayace ,itace yayi wa tufkar hanci tun abu baiyyi nisa ba ,saboda haka sai ya yanke shawarar yayi abinda zuciyarshi ta raya mishi . Zuwa yayi ya samu yayanshi ya bashi labarin ya samu yarinyar da yakeso ya aura snn yana so aje anema mishi auranta, amma bai fad'a mishi akan tana karatu. Yayanshi yayi farin ciki kwarai ,dama burin shi kenan yaga d'an autansu ya ajiye iyali. Saboda haka sai ya nemi sauran 'yan uwanshi ya sanar dasu snn suka sa ranar da zasu je dan su nema mishi aurenta. Kamar yadda suka tsara ko haka sukayi , sunje nemawa Ahmad aure gidansu Salma ba tare da saninta ba ,duk da a wurinsu suna tunanin saida suka fahimci juna kafin Ahmad ya tunkare su da maganar. Shi kuma Ahmad a tunaninshi so da yardar dake tsakaninshi da Salma bazai bari ta watsa mishi k'asa a ido ba koda za'a tambayeta ra'ayinta game da aurenshi. Sun samu tarba ta mutunci da karamci daga wajen Mal. Inda bayan gaishe gaishe suka gabatar da bukatar su ta nenawa k'aninsu auren Salma. Snn idan zai yiyu suna bukatar a gama komai cikin k'ankanin lokaci. Duk da Mal.yaji mamakin abin amma bai nuna musu ko a fiska ba, ya dai ce musu zai ji ta bakin yarinya dan basu sanar dashi wani abu makamancin haka ba daga cikin gidan. Snn bai b'oye musu ba ya sanar dasu salma tana karatu da kuma irin karatun da takeyi. Nan suka shiga kallo kallo kowa da abinda yake sak'awa a ransa. Sallama da godiya suka mishi suka kama hanyar komawa gida . Ahmad da yakasa zaune ya kasa tsaye yana jira yaji irin amsar da zai samu daga garesu . Ganin shigowarsu yasashi binsu yana musu sannu da dawowa. Daga yanayin fiskokinsu ya gano akwai matsala. Babu walwala a fiskar ko d'aya daga cikin su ukun. Ganin yadda ya tasa su gaba yake binsu da kallo cikin rashin sukuni yasa babban yayansu wanda yake tare dashi ya fara magana cikin zafin rai. "Ahmadu me ya had'a ka da 'yar boko? Wato bidi'a kakeso ka kawo mana cikin zuri'a ko? Ina kai ina auren likita ,kullum tana yawon zuwa asibiti bata da lokacin ka, duk 'yan matan garinnan ka rasa wacce zaka aura sai wacce ta tsofe tana yawon karatun boko. Ka bani mamaki Ahmadu ,kai da kake namiji ma bakayi karatun boko mai zurfi ba sai mace? To ba'a zuri'armu ba saidai idan zaka canza dangi, baza mu lamunci wnn aikin kafurcinba." Ya karashe maganar yana huci. Suko sauran 'yan uwan sai gyad'a kai sukeyi irin d'an uwansu is absolutely right d'innan. D'ayan yayannashi ya cab'e zancen da cewa "Kasan duk dangin mu ba'a tab'a irin haka ba kuma akanka baza'a fara ba, gwara ma ka canza shawara ." D'ayan ko da tausayin Ahmad duk yabi ya cika shi ganin yadda lokaci guda kamanninshi suka canza ,jijiyoyin kanshi suka tashi burd'um2 ,cikin sassauta murya yace. " Nidai shawarar da zan baka ,kayi hakuri ka daure ka cire yarinyar a ranka dan kasan aurenta ba mai yiyuwa bane, ka nemi wata ka aura." Babban yayan ya amshe da "Kada ma yayi hakuri in ya ga dama ,aurene dai bazai aureta ba, saidai

Chapter 2 of 7