irin duba Maah takeyi masa cikin wani irin takaici ganin yadda gaba ɗaya Esherh ta ruɗe ta kuma fita hayyacinta daga ganinsa, shi kuwa Fawaz kallo guda ya yi masa ya fahimci a buge yake wato tsaban rashin ta idon nasa har ya kai ya dinga buguwa yana shiga wuri na jama'a irin asibiti dan saboda yaji daɗin zubar wa da Familyn suna.
Ita kuwa Eaman shiru ta yi tana dubansa duk da tasan shi ne Lateeb sai dai haɗu war da suka taɓa bai fi sau biyu zuwa uku ba amma bata san abin nasa ya kai har haka ba.
“Lateeb a buge kake kayi gaggawar barin Ɗakin nan tun kafin ranka ya ɓaci kana firgita min Ƴa!”
Maah ta faɗa cikin danne ɓacin ranta.
Shi kuwa Fawaz sai da ta yi maganar sannan ya lura da halin da Esherh'n ta shiga ransa ya ɓaci dama yaji raɗe-raɗin Lateeb ɗin shi ne silar kasancewarta a halin da take ciki.
“Yah Lateeb Esherh bata buƙatar ganin ka kamar yadda Maah ta faɗa kawai ka tafi karka ƙara tayar mata da ciwo!”
Fawaz ya faɗa yana ƙoƙarin tare Lateeb ɗin da ya wani tunkari Esherh gadan-gadan kamar mai shirin kai ma ta runguma.
“Kam bala'i wato kai Fawaz kana ganin har idonka ya yi kaurin da zaka faɗa min magana to ka sani ita ma da ta faɗa san ranta ba kyale ta nayi ba kawai dai na kauda kai ne a matsayinta na uwar matata.”
Lateeb ya faɗa yana ture Fawaz dake ƙoƙarin riƙe shi sai dai Fawaz ɗin da yake shima namiji ko gezau bai yi ba.
Ita kam Esherh ma har ta fara fita daga hayyacinta domin har ga Allah tsoro ma Lateeb ɗin yake bata.
Suna tsaka da haka lokaci guda suka ji wani sassanya kuma daddaɗan ƙamshi ya mamaye Room ɗin kafin mamallakinsa ya bayyana shigowa Room ɗin ya yi da sallama ciki-ciki sanye yake da shiga na cikakken likita ya ɗaura farar kar ɗin lab coat saman kayan jikinsa ga wani medical kuma kana gani kasan expensive ne Glasses White rufe da idanunsa hannayensa zube cikin aljihu ga wasu nurses biyu suna take masa baya da alama yana tsaka da duba Patients ɗin sa sai ya yo nan ɗin.
Gaba ɗaya mutanen Room tsayawa suka yi cak kowa da irin kallon da yake yi masa ita dai Maah tana kallonsa ne a matsayin wannan Babban Likita wanda badan taimakonsa ba da yanzu Esherh wani labarin daban a ke gefe guda kuma sunan family da kuma kamanni da yake yi da tsohon mijinta wato Mahaifin Esherh.
Ita kuwa Esherh wani irin zaro ido ta yi cike da mamaki tana dubansa ganinsa sanye da kayan Likitoci mutumin da bata da wani maƙiyi a halin yanzu da ya wuce shi wai ma shin me hakan yake nufi ne ya akai ta ganshi da kayan Likitoci ne ya akai a ka haihu a ragaya?
Eaman kuwa duk da tasan shi ɗin Dr ne bayan kasancewarsa ɗan kasuwa amma ta razana ga ganinsa a zahiri ga wani madaran kyau da yake da.
Fawaz da Lateeb kuwa a matsayinsa na ɗan kasuwa suka san shi amma ba'a Dr ba shi ya sa ganinsa yanzu ya matuƙar basu mamaki.
“Hey, Hello, Salam, Please zaku iya fita ina da buƙatar duba Patient ɗina!”
Ya faɗa can ƙasa da muryarsa mai tafe da wani irin amo da kwarjini na ban mamaki.
Da tsananin ƙarfi Esherh ta cije labbanta na ƙasa jin kalamansa tambayar kanta takeyi wai shin wacece Patient ɗin tasa?.
“Sorry Bara mu fita.”
Cewar Maah da Eaman a tare shi kuwa Fawaz har ya kusa ƙofa Lateeb kam bashi da niyyar fita Dr Sameer yana sane da shi sai dai bai bi ta kansa ba dan sauri yake ya ƙari sa wurin Esherh da ta kafe shi da ido tanayi masa wani duba.
A ka kuwa ci sa'a suka haɗa ido ya sakar ma ta wani malalacin murmushi da ita a nata ɓangaren ta fassara hakan da wata manufa daban shi kuwa ya yi ne kawai da ganin irin kallon shock da take yi masa da yake ba wai kasafai yake shigowa dubata ba kuma mafi yawan lokuta idan ya zo tana bacci sannan duk bayanin da yake yi ma su ma a office ɗin sa ne.
“Madam gyara za'a yi allura”
Ya faɗa tare da juyawa ya amsa allurar hannun nurse ɗaya bayan ta zuba ruwan allurar airbubles ya fitar tare da mayar da dubansa kanta sai lokacin ya lura da idanunta dake kafe a kan sa kamar za su faɗo shi har ga Allah ma dariya taso bashi.
“I don't get it fa?”
Ta sama kanta da faɗa.
“what?”
Ya tambaya kamar bai san abin da take nufi ba.
“ba'a taɓa cewa za'ayi allura ba duk zamana a asibitin nan all of a sudden kuma sai yanzu wai ma ina likitan da yake dubani ne.”
Ta faɗa iya gaskiyarta domin bata gama yarda da cewa shi ne likitan da yake dubata ba.
“Hey ya ne Bahbah ban e gane ba ne kana nufin kaine zakayiwa Matar tawa allura to Alkur'an ba zata saɓu ba tun wuri ma kwara a nemo likita mace.”
Lateeb da yaƙi fita ya faɗa yana wani tunkarar wurin kamar zai kai wa Sameer ɗin bugu.
Shi kuwa Sameer jin kalaman Lateeb sai bai bi ta kansa ba sai kallon Esherh da ya yi ita kuma ganin kallon da yake ma ta kamar wani na zargi ta yi saurin girgiza kanta wai tana nufin Lateeb ba mijinta ba ne.
“Kai wai ya ne ina maka magana ka wani shareni zan....”
Lateeb ya sake faɗa yana wani damƙe hannu zai kai ma Sameer bugu sai kuwa Sameer ɗin ya kauce Lateeb ya bugi iska sai dai bai dandara ba ya sake ƙoƙarin kai masa duka lokacin Sameer ya ɗuka zai yi mata allurar sai ya tuna bana kafaɗa ba ne na baya ne hakan ya sa ya miƙe shi kuma Lateeb ya riga ya kai masa duka ai kuwa Lateeb ya goce tare yin kyakkyawan bugu da bango Ya kuma bugi hancinsa tsaban taurin kai bai dandara ba ya sake juyowa a fusace tare da damƙe hannu zai kai ma Sameer wani naushin ai kuwa a bazata Sameer ya juya tare da damƙe hannun nasa ji kake ƙass! Ya karya ƙashin sannan ya yarfar da shi gefe a yashe yana ihu.
Esherh kuwa wani irin daɗi ya kamata ganin abin da a ka yi ma Lateeb tsaban farin ciki ya sa bata ma san lokacin da ta juya ya yi ma ta allurar ba sai zafin shigar allurar ne ya dawo da ita hayyacinta shi kuwa yana gamawa ya nufa ƙofa.
“Am bakaji ba?”
Kamar ba zai juyo ba dan ya yi tunanin ƙorafi zatayi a kan karya hannun Lateeb da ya yi.
“Thank You?”
“For what?”
Ya tambaya yana kallon fuskarta.
Sai da ta kalla Lateeb dake yashe yana ihu, ta saki kyakkyawan murmushi sannan ta furta.
“Da ka ƙarya masa hannu da kayi.”
Daidai lokacin kuma Fawaz da Maah har da Eaman da ihun Lateeb ya sa suka yo Ɗakin a tare dan ganin abin da ke faruwa suka shigo a kiɗime hakan ya bawa Sameer damar ficewa ba tare da ya amsa wa Esherh ba sai wani killer smile da ya saki.
Turƙashi! Ƙaƙaƙara ƙaƙa ga akuya ga kura!!!
Wai me kuke tunanin zai faru ne ta ko wanne ɓangare fa abin ba sauƙi.🔥
1. Shin waye ma ainihin wannan Sameer ɗin ne 😏 meye dalilin rabuwar iyayensa?
2. Ga kuma Maah da nata rikicin wai shin wanene mahaifin Esherh ne?
3. Me ya sa kuma sunan Familyn su yazo ɗaya da na Sameer? Hakan na nufin suna da alaƙa ke nan
4. Jira jira jira ma wai me ya sa Fawaz yake shakkun har wani kamanni Esherh take yi da Dr Sameer, wai shin mene a ƙasa?
5. Karfa ku manta Sameer da Esherh manyan abokan gaba ne ko nace maƙiya ta fannin kasuwanci, wai shin wa kuke ganin zai yi nasara a cikinsu? Ita ma fa Esherh ba kanwar lasa ba ce😎
6. Ga kuma fitinanne Lateeb, shin zai haƙura da abin da Sameer ya yi masa ko kuwa zai nema ɗaukar fansa?
7. Lateeb fa ikirari yake da Esherh Matarsa ce wai shin kuna ganin hakan zai taɓa faruwa kuwa?
8. Ga fa Omer da Fawaz a gefe sun kasa sun tsare 😅 haka ma zalika Basma matar Omer ta kasa ta tsare.
9. Hmmm akwai rikita rikita fahh!!!
Mu dai haɗe a paid page's kawai ga waɗan da suka cire kyashi suka biya!!!!
This is the last free page's.
Saboda haka in kuna son ci gaba karatu sai ku biya kuɗin ku Naira (500) domin ci gaba da karatu.
Ku Tura Ta Wannan Details Ɗin!👇
8081129487. Sabi'u Khadija, MoniePoint Mfb.
Sai ku tura shaidar biya ta nan.
Chat via WhatsApp.
07067953066.
Ko kuma
0810 449 3215
Sai munjiku.
NainarhKD ❤️ Ammiey Laylerh.ꨄ
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels