Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 7
gudun kar Fawaz ɗin ya kasa riƙe fushinsa yaje ya illa ta Omer ɗin a Ɗakinta lamari ya kwaɓe shi ya sa ta furta wannan tausasan kalamai da hope ɗin Fawaz ɗin ya tafi dan shi Omer bata ɗauke shi a matsayin wani ajawali babba ba dan tasan ta yadda zata tafiyar da shi cikin ruwan sanyi. “Taya kike tunanin zan iya tafiya na barki tare da wannan psycho ɗin da bai san inda keyi masa ciwo ba.” “Fuck! Fuck! Ni kake kira da Psycho saboda ka mugun duban yanayina? Lallai ma Fawaz kake ko wa na rantse da Allah ka dena ganin kai ɗin Soja ne domin duk Ranar da ka sake kirana da Psycho to fa abin ba zai tafi mana daidai ba domin zan nuna maka cewar ni ɗin cikakken mahaukacin ne na gasken gaske ma!” Fawaz zai sake magana amma Esherh ta yi masa alama da ido a kan ya yi haƙuri, kwafa ya ɗan ja sannan ya ciro wayarsa da ta fara ruri ganin MOO-tee (Mom shi ne Mutti in German ke nan) ke kiransa. “Ohya zo kisha maganin kafin na wuce.” Ba musu Esherh ta ƙari sa ta karɓa maganin duk da ba son sha take ba amma haka ta sha. Sannan Fawaz ya fita ba tare da ya sake duban inda Omer yake ba. Ita kam Esherh komawa ta yi ta zauna ba tare da ta ce masa komai ba. “Me kike nufi dani ne Esherh?” Tajiyo muryarsa yana faɗin hakan sai dai wannan karon ba cikin tsawa ba. “Kin san fa ina son ki me ya sa kike son azabtar da zuciyata ne haka ta hanyar kula mutanen da basu dace ba?” Ya ƙara faɗa. Wannan karon dubansa ta yi Allah ya gani magana ma batason yi a wannan taƙin dan ya gama ɓata ma ta rai dama ta tashi sai a hankali ya zo da shirmensa da yake kira so ya daɗa jagula ma ta rai. “Yah Omer please ka tafi zamuyi maganar zuwa wani lokacin!” Ta faɗa bayan ta miƙe tare da ƙari sawa wurinsa ta karɓa wayarta da ya riƙe. “amma...!” “Please ka tafi kawai.” Ta katse shi daga ƙoƙarin sake magana da yake niyya. Sannan ta koma ta zauna tare da lumshe ido hakan ya sa Omer fita dole badan yaso ba. Ajiyar zuciya ta sauke sai da ta ƙara aƙalla mintuna goma a haka sannan ta miƙe fitowa ta yi daga Ɗakin kai tsaye ta wuce na Maah ɗin ta, da sallama ta shiga Maah da fitowarta daga Bathroom ke nan tana zaune gaban mirror ta amsa ma ta sallamar tana juyowa murmushi mai kyau suka sakarwa juna sannan Esherh ta ƙari sa tana faɗin. “Ai nayi tunanin ma tuni kin shirya ko dai kin fasa tafiya zuwa Lagos ɗin ne?” Esherh ta ƙare maganar lokacin da ta ƙari sa sannan ta ɗauki Dryer ta fara drying hair na Maah ɗin cikin kwarewa. “Zuwa sha biyu ne tafiyar yanzu kuma goma da wani abu ne shi ya sa na tsaya na shirya da wuri.” Maah ta bata amsa cikin kulawa. “Na kuwa ji daɗin hakan domin koba komai nayi fira da Maah ɗina.” Murmushi kawai Maah ta yi jin abin da Esherh ɗin ta ce. “Hmm wato Maah ashe ma kina jina da su Yah Omer shi ne ko kizo ki kwaceni ko?” Esherh ta faɗa tana ɗan kwaɓe fuska. “Ai bari nayi ki dinga solving matsalarki sa kanki.” Maah ta bata amsa. “Hmm wallahi Yah Omer mugun ciwon kai ne gaba ɗaya na rasa gane kanshi!” Esherh ta faɗa tana ɗan dafe kai. “Ki nutsu dai kiyima kanki zaɓen da ya dace domin ba zan hanaki kula su ba duka ƴan uwanki ne amma ki nutsu ki kuma san abin da ya dace ke ba Yarinya bace Esherh shekarunki ashirin da biyu baki da buƙatar sai na shiga miki komai a rayuwa domin kin kai Matakin da zaki ji da komai naki!” Maah ta faɗa cikin siga ta bada shawara, domin Allah ya gani ba wani son Omer da ɗiyar nata take ba kwara ma Fawaz bashi da wata matsala sai dai Mahafiyarsa wato MOO-tee ita ce matsalar domin sam basa ga maciji da Maah kuma ba komai ne sila ba sai baƙin ciki da hassada da take yi ma Maah ɗin sai dai sam bata kulata kuma bata ɗauki tsana kamar yadda ita MOO-tee ɗin ta ɗauka ta ɗaura ma Esherh, ita Maah bata ɗaura a kan ƴaƴan ita MOO-tee ɗin ba kuma sosai suke shiri da Fawaz domin ko kaɗan bai ɗauko halin mahaifiyar nasa ba. Shiru Esherh ta yi dan ta rasa ma mai zata ce Allah ya gani kaf cikinsu ba wanda zata ce tanayi ma wata aba wai SO abin da ta sani shi ne tana girmama su Matsayinsu na ƴan uwanta especially ma Fawaz sosai take bashi girma. Kawar da zancen ta yi da faɗin. “Ba ma wannan ba kin san fa yau ni da kaina zan rakaki har airport.” “Da gaske?” “Sosai ma kuwa Maah Tah!” Esherh ta faɗa tana dariya cike da nishaɗi domin Maah ita ce Mutum na farko da Esherh take zagewa suyi fira da nishaɗi sosai daga ita kuma sai mutane biyun nan da suka biyo baya wato Kakanta Sai kuma babbar ƙawarta Eman da a halin yanzu bata ƙasar. *❉্᭄͜͡𝘚O 𝘿𝔸𝑵☆ R̲A̳Yᑌᗯᗩ ♥️* _☆♥︎L⋆o⋆v⋆e⋆ ᖴOᖇ 𐐛օv𝖊♥︎☆_ 𝗕Ⲩ 𝔸mmⅈ𝖊ყ ℓαуℓєян & ɴᴀɪɴᴀʀ kd♡ ༆Ⴆҽʂƚ σɳ ƈɾҽαƚιʋҽ ʂƚσɾყ!!!༻ Page 3 ♡♡♡♡♡♡♡♡♡ A natse cike da ƙaunarta me zurfi Maah ta ɗan shafa saman kanta fuskanta ƙawace da kyakkyawan murmushi ta furta. "Haka nake son ganin farin cikin Shalelena fiye da komi dake cikin duniyar, kuma zanji daɗi ace yau best friend nawa ce da kanta zatayi driving nawa zuwa airport" ɗan kwantar da kanta jikin Ma'amah'nta tayi tana wani langoɓe mata tare da furta. "I love U Best Mammata! Ina sonki sosái tare da pa'apahh maaa" tayi maganar cikin sanyin murya me ɗauke da zallar rauni. A hankali Maah ta janye hannun ta dake cikin gashin 𝙀𝙎𝙃𝙀𝙍𝙃 ɗin yanayi na face nata na sanjawa daga wannan farar'n dake cike da fuskan. "Me yasa sau da tari kike son sama ranki abinda bazai taɓa iyuwa bane ESHERH?, Idan har kinason farin ciki na da gaske to kuwa tabbas dole ne ki cire maganar mahaifi a cikin rayuwarki!!!" Daidai da gama maganar nata ta miƙe tsaye tare da rataya handbag nata tana nufar doorhandle na room ɗin, Tun da Ma'amah'n ta soma mata maganan kanta yake duƙe hawayen da ita kanta bata san da zuwan suba na zubo mata. A fakaice ta sharce hawayen tana saurin miƙewa tare da ɗaukan car key data gani kan rug tana rufa mata baya da sauri da sauri, dan tasan Maah ɗin nata kaifi ɗaya ce bata jurar Raini ga kowa bare Maimaita zance ɗaya. A Mahaukacin parking house car na gidan ta tarar da Maah ɗin na shirin shiga wata motan daban. "Ma'amah!" Ta kiranyi sunan cike da rauni sosai a muryanta, chakk kuwa Maah ta dagata daga shirin shiga motar tayi tana juyowa ta kalleta. Kafin ta kawar da kanta daga kallonta domin zuciyarnta sammm bata iya juran kallon Shalelen ta cikin yanayi na damuwa. Cikin takunta me sanyi da nutsuwa ta ƙaraso har gaban motar a sanyeye ta kama tafin hannun Maamah ɗin tana jimƙewa da nata hannun. "Pls so sorry Ma'amah bazan...." Saurin taryar numfashin ta Ma'amah'n tayi ta hanyar sake riƙo tafin hannuwan Esherh'n tana furta. "Please kada ki sake cewa komai nasan kina jin tsananin zafin hakan a cikin zuciyarki amma everything will be fine _ESHERH_ will be fine kinji. I promise you zan maida kukanki zuwa farin cikinki, zan maida ɗacin dake bisne cikin zuciyarki zuwa madawwamin farin ciki" ta ƙarasa maganan tana rungume ƴar nata. Wani sanyi ne Esherh taji yana ratsa cikin zuciyarta A hankali cikin laushin da muryanta ya sake ɗauke ta furta "Ngd Best Friend" Ɗan bubbuga bayanta Ahankali Maamah ta shiga yi tana ta son sarrafa kanta daga wasu shuɗaɗɗun lamura baya can masu nisa da suka jima da shuɗewa. "Best friend I wasn't alone anymore babu godiya tsakanin mu duk matsalolinki nawa ne and I will do my best to see na kauda damuwanki, har gaban abada ba wanda zan bari yayi hurting naki akan Mahaifi saidai in bana numfashi, just take care of yourself. Dan nasan shi ne tsoron dake danƙare gareki Shalele" Wani kwanciyan hankalin maganan Maah ɗin Esherh taji yana kamata, domin ta riga da ta sani koma tace tafi kowa sanin halin Mommah ɗin ta kafff da kowa, dan haka taji wani kwarin zuciya da gwiwan ci gaba da Rayuwa na kamata,Hannun Maah dake cikin nata ta sake ƙanƙamewa gamgam tanajin wani kaunar mahaifiyarta na sake kamata ta furta. "Nagode Sweet Maah! Ina ƙaunarki and really miss Mee kafin ki dawo" daga haka taja hannun Maman suna nufar wata futinanniyar narkyakkiyar Rolls Rayce Spectre Blac car. Itane ta buɗe mata back side kafin ta nufi driver side ta shiga tana sanya ma motan lock tare da yin reverse tana janta ba da speed da yawa can ba. Slowly taci gaba da jan motar hakan har suka ƙaraso babban airport na Abuja. Tun kafin su ƙara sa airport ɗin ta hangi wani mugun tsaron da aka bama airport ɗin. Wani kalan bugawa taji zuciyan ta yayi hadi da karyewa duk a lokaci guda, domin ita ba mutum bace me son ganin ko taron cincirindon mutane bare kuma jami'ai. Amma ta danni kanta tana ƙarfafama kanta gwiwan hakan. Ita Maah ɗin duk kusan tare suka fito kowa ya buɗe na kansa da kansa. Motan ta rufe suna fara tafiya sedai tarin uban jami'an data kalla suna sake bema Kamar wani mutum garkuwa ne yaɗan so bata Mamaki ma ita kammm. Duk da cewan hakan bawai abin mamaki bane tunda gidansu ma haka yake da wannan bala'in tsaron. Kuma ma ganan uncle Fawaz nan shi ma kusan sakk haka ake bashi kalan wannan tsaron amma kuma se take jin wannan ɗin wani irin daban ba tare da ita kanta tasan dalilin na zurfafa kanta har haka ba. ★Ata cennn ɓangaren jami'an nan kuwa shi kansa airport ɗin kewaye yake da tsaro na musamman. Wani Kyakkyawan Matashin saurayi ne ya sanwo kansa daga fitowa daga cikin jirgin da kusan shi ne last ma daga cikin passinger's da jirgin ya sauƙe dan wani ɗan nannauyar bacci ne ya sure shi jirgin na dap da sauƙa. Shi ne ma dalilin daya sanya seda ya ɗan ƙara sa watstsakewa ma kana ya fito a jirgin. Ahankali cikin takun izza dajin kai ya fara tako matakalar benen. Cikin wani irin nutsuwa haka harya dangana diga digansa wa ƙan dandanin airport ɗin. Su kuma waɗan nan samudawan jami'an na aikin su na take mai baya da bashi kariya. cikin sauri manyan security'n dake zagaye da airport ɗin suka shiga bashi kariya wa kallon da jama'ar airport ɗin ke binsa dashi. Don kuwa kallo ɗaya zaka masa ka kasa ɗauke idonka a kanshi. Kyakykyawan Matashi ne ajin farko sedai ba fari bane can can amma kai tsaye ma iya kiransa da farin duba da yanayi na murjewan fatar jikinsa dake wani kalan shining na zallar hutu da jin dadin rayuwa. Ahankali yake taka Fararen sawayensa da tamkar wanda bai taɓa taka ƙasa da su ba haka suke, don tsananin taushi da kuma yadda suke sumil luwai....Yana Sanye cikin wasu haɗadɗun American suit blue black,kansa sanye cikin p-carp blue black sai facemask dake saman kyakkyawarn fuskarshin da ya mai wani irin kyau bana wasa ba, jikin sa kuwa sai tashin fitinannen ƙamshi yake hannun sa na ɗaure da diamond watch kyawawan kafafun sa na sanye cikin Hermes Birkenstock sandal wadda a kalla kuɗin sa ya kai $97000, kasan cewar takalmin launin baki ne sai ya yiwa farar kafar sa bala'in kyau na ban mamaki Hannunsa ɗaya kuma na riƙe da ipad nashi dayan kuma na riƙe da wata munafukar mini bag ta chanel se jacket ɗin Dior black dake ɗore akan suit ɗin dake sanye jikinsa ta. Ƙamshinsa ne ya tsananta yana sake gaurayewa da iskan wajen ya baje kowa na shaƙarsa hadi da sanyin wurin. Wanda iyaka ƙamshin sa dashi kawai ya rikita yan matan wajen. daga yanayin yadda yake takunsa kaɗai ze isar maka cewan Ehhh lallai shi ɗin Matashi ne dake ji da tashen samar taka wacce kuɗi da kuma jin daɗin Rayuwa suka taru suka ma taron dangi tsabar gata. Wani irin yuuuuuu duka jama'ar wajen suka bishi da ido masu manyan aji na wurin da kallo ɗaya suke yimay su rena kansu suma ɗin dai sun gaza janye kallonsu washi wannan matashin saurayin. Babu Esherh dake tafe tana ɗan sauri na kamo Mamma ɗin ta ne taji tamkar an ja mata mayafin da tayi Rolling dashi. Chakk ta tsaya tana gaza yin gaba ganin dai da gasken vail nata ne ya saƙali lug bag ɗin dake riƙe a hannunsa. Samm samm shi kam ma besan da hakan ba seda ya kusa jin tsaiwar mutum dab dashi domin woyarsa yake yi hankali kwance, fuskar nan ƙawace da smile duk da kuwa cewan ido da fuskan duk a ɓoye suke. lumshe mata idanu yayi kana ya buɗe su calmly akanta. Da kallon miya faru kuma? Ya bita dashi hakan ya sanya ranta shegen ɓaci da rainin Hankali guy ɗin nan. "Vail.... Ta furta muryan tan cen kasa tana masa nuni da inda yake saƙale da lug bag nashi.kallon inda ta nuna nashin yayi se kuma ya ɗan fuskanceta tare da lumshe idanunsa kana ya buɗe su ahankali ya sauƙe akan vail nata har zuwa zara zaran fararen yatsun hannunta da yabi da kallo. "Sorry!!!" Ya furta yana zare mata vail ɗin yaci gaba da tafiya abinshi escort din na biye dashi. Wani kalan langoɓe kansa yayi tamkar yana a gaban me wayar ne ya furta. "OUMMUY SAMEER yunwa ko break fast ban yi baaa! Kuma yanzun muke sauƙa ganan ma se yanzun zan nufa Hotel In dana yi booking" daga ta can ɓangaren me ƙiran kuwa banji abinda akace ba amma dai naga shi ya ɗan yamusta kyakykyawar doguwar farar fuskan shi wanda hutu da kuma jin daɗin duniyar suka gama ratsawa. "O'ohhh oummy Sameer kar muyi haka,na ce miki bana zuwa gidan su already ma na rigada na kama Hotel nikam" daga haka ya yanke ƙiran yana ci gaba da tafi cikin wani irin zati da cikakken ƙarfi irin na mazajen gaske yake takun nasa. Sedai kai a idonka baka isa kace wai sauri ko tafiyar ƙarfafa yake ba domin kuwa a natse normal yake takun nasa me cike da ƙasaita da kuma zarra..... Gaba ɗaya hankalin duka jama'ar dake cikin airport ɗin ne hankalinsu ya dawo kan wannan matashin..... _SAMEER OTHMAN KAMPALAH, Kenan Cikin Dr kuma shahararren ɗan kasuwar nan da duniya ke Masifa masifan ji dashi. Domin wani irin wasu irin makuɗan Mahaukatan Dollars in nera ɗin da yake da. Se dai a zahirance kowa da iyaka ɗan kasuwar kawai ya sanshi dan be yadda duniya ta gama sanin shi ne wannan shahararren Dr ɗin ba. Dan ko ayki zeyi to kuwa zaka kalle shi ne da facemark ko kuma Nosemark a tare dashi da kuma shade ɗin da yake toshe idansa dashi. Duk inda ya gilma tafiya yake da hankulan zafafan ƴan mata kuma ƴaƴan manyan dake cikin airport ɗin. Sabo da sammm sammm ya manta da wani batun cire pcap nashi dayay lokacin da sukaci karo da yarinyar tare ma da shade ɗin da koda yaushe yake toshe da idanuwan san. Shi kuwa hankali kwance yake ci gaba da taka dogayen ƙafafun shi cikin wurin escort ɗin da suka zo ɗaukan shi na zagaye dashi. Lumshe kyawawan fararen idanunshi yayi a karo na ba daɗi domin kuwa mayen ƙamshinta kawai ƙofofin hancinsa ke jiwo masa, tamkar wani yaro ɗan 3years ya wani zama pink lips nashi na ƙasa yana ɗan taunewa bada yawa ba kaɗan. Kafin kuma ya dafe saman ƙirjinsa wanda kawai yaji yana masa bugun da baima san dalilin yinsa ba. Tamkar wacce aka umarce shi ko akace kalla cen haka ya sake hangota lafe jikin matar da yake tunanin Mom nata ne, Sake ware idanunsa yayi a cikin zuciyarsa kuma yana ayyana (fita mana!!!) Kafe ta da lumsassun idanonsa yayi yana cigaba da kallon ta ganin yacce gandamemiya kamar ta na zuba shogoɓa gaban dubban mutane. A ranshi ya furta. {Oummuy Sameer zo ga Wanda ta fi Sameer naki iya rigima} a fili kuwa ɗauke kansa daga kallonta yayi dan wani baƙon yanayi daya fara jin kansa dangane da iyaka kallon tan da kawai yayi. Fuskanta da skin nata fresh na asalin ƴar hutu da aka haifeta ta ta taso a cikinsa yake sake kalla. Kalla yake tamkar yasan wannan face ɗin ko dai ya taɓa ganin me kama da ita. Ita kuwa ƙamshinsa ne ya tsananta a gareta yana bugar mata da zuciya da ciwon ƙirji. Ƙamshinsa me sanyi da daɗi ne dan haka ta kasa janye kanta daga kallonsa.. Tsoki a ransa yaja a bayyane kuma yana zube hannuwansa cikin suit ɗin dake jikinsa. Esherh kuwa goge ƙwallar da suka idaniyarta tayi na kawai missing Maah da zata yi na iyakar yau kaɗai yau ɗin ma kuma bawai kwana ne zata yi ba tunda ta ce mata zata gana da wani babban Dr ne da suka daɗe fata da kuma burin samun sa a cikin duniyar su dan kawai ita kadai ɗin ta Esherh'n... Dai dai da inda yaja ya tsaya daidai da sadda wasu irin tsadaddun motoci kusan uku na sanyo kansu cikin airport ɗin. Mahaukatan manyan jifa jifai ne guda duka uku kowaccensu baƙaƙe ne wulik dasu. Se wata ƙwalli dayan wata kafurar Black blue ɗin Mercedez Benz aka buɗe masa. Suka ɗauki hanyar wannan haɗaɗɗen Hotel ɗin nan da yayi booking tun a daren jiya. Dake babu wata tazara tsakanin support ɗin da kuma Hotel ɗin se abu nisa cikin cikin abinda bai wuce 35 minute ba suka isa ƙayataccen hotel ɗin... A gaban wani Mahaukacin KidCity Hotel Abuja suka yi Parking car's nasu. A gaban wani irin Mahaukacin Vemble Apartment Suites Suka yada zango ƙarƙashin wata welpeper screen tithy. _Welcome to Vemble Apartment Suites_ Shi ne sunan dake walainiya ta saman welpeper screen tithy ɗin dake haskaka ginin duka Hotel's ɗin In difference color's. Shi aka fara buɗe ma car ɗin kana sannu a hankali harya gama fitowa baki ɗayansa yana tsaiwa kan diga digansa jikinsa na ingarman namiji na sake bayyanuwa. Cikin takun jan hankali da mazan taka yake takunsa. Domin kuwa taku yake yi irin na cikakkun jarumai ko baka gan shi ba kaji sahun takun sa kasan cikkaken namiji ne mai jini a jika kuma. A room me lamba 105 Sameer ya ɗauka su kuma duk suka rarrabu daban daba. Yana isa cikin masauƙin nasa kai tsaye bedroom ya wuce yana zare rigar jikinsa da fresh skin ɗinsa fari tas ya bayyana yana daukan idon wani irin hutu dayake bayyane a ko'inan sa. Bayan ya gama bincike komi ya kuma yadda da ingancin komi ɗin kuwa. Sabon fari tass ɗin towel ya buɗe wanda ka'idan hotel ɗin ne haka. A ƙugunsa ya ɗora toewel ɗin yana faɗa wa toilet ya sakarma kansa ruwa yana rufe idanuwansa ahankali gudun kada ruwan su shigagmay. Yana fitowa kai tsaye ƙananun kaya marasa nauyi ya sanya yana kwanciyar sa kafin lokacin sallar zuhr yayi. ★ Alhamdulillh kam zamu ce domin kuwa maah ta sauƙa lafiya se dai kuma ya riska rashin sa'a domin kuwa tana sauƙa wanda suka yi da shi ze haɗata da Dr Sameer othman take gaya mata ay yama bar Lagos ɗin. Wannan magana itace ta kusan tashin hankalin Maah domin kuwa Esherh na dap da kaiwa matakin karshe a jinyar nata.wanda basa fata ko kaɗan ace yau wannan mummunar ranan ta riskesu ba tare da sun ga wannan ƙwararren likinta ba. Tana jin haka ko zama bata yi ba ta sake biyo jirgin daren ranar ta komawanta Abuja. *BY NAINERH KD ✍️ and AMMEY LAYLERH ✍️☑️* *❉্᭄͜͡𝘚O 𝘿𝔸𝑵☆ R̲A̳Yᑌᗯᗩ ♥️* _☆♥︎L⋆o⋆v⋆e⋆ ᖴOᖇ 𐐛օv𝖊♥︎☆_ 𝗕Ⲩ 𝔸mmⅈ𝖊ყ ℓαуℓєян & ɴᴀɪɴᴀʀ kd♡ Page 4 Sai washegarin ranar Esherh take sanin Maah a gida ta kwana domin koda Maah ɗin ta dawo dare ya yi kuma tuni Esherh ta yi bacci shi ya sa bata tashe ta ba sai da Safiya ta yi misalin takwas lokacin Esherh ta fito cikin shirinta tsaf na fita aiki ta sakko ƙasa. Versace woman suit ne jikinta launin pink da ta yi matuƙar dacewa da ita riga da wando ta riƙe coat ɗin a hannu ƙafafunta cikin wasu arnun ankle strap heels, sai ƙamshin perfume na Le Labo Kawai take fitarwa gashinta da ya sha gyara in upsweep style kuwa naɗe cikin veil na Louis Vuitton da ta yi rolling kanta da shi a hankali take taku ɗaiɗai daga kan stairs ɗin har ta ƙari sa sakkowa zaraf idanunta ya shiga na Maah dake zaune a Dining area da alama breakfast ta kammala jerawa shi ne ta zauna zaman jiran sakkowar Esherh'n. “Laa Maah Tah wai kece da gaske?” Esherh ta faɗa cike da zumuɗi tana ƙari sawa har da ɗan gudu-gudunta Dining Room ta a je mini bag nata Pink color a kan Kujerar Dining ɗin tare da ɗafalewa Maah ɗin ta rungumota tana dariya. Dariya Maah ta yi tana shafa kanta ta ce. “Wato dai ke har a kullum bakya girma ko? Yanzu Fisabilillah so kike ki karyani?” Turo Lips ɗin ta dake ɗauke da Fenty Beauty Lip gloss ta yi jin abin da Maah ɗin ta ce cike da shagwaɓa irin yadda ta saba ma ta ta ce. “Waassh MaahMaah kinji ki da wani batu fa yanzu ni ɗin har wani ƙiba gareni da zan karya ki?” Maah tana murmushi ta ce. “Sosai kuwa dan na lura kwana biyun tashen cin abinci da yawa kike fama da shi.” Dariyar da ya bayyana haƙoranta farare tar da su Esherh ta saki jin kalaman Maah tasan da biyu ta yi dan ta tsaya taci abinci. Sai lokacin suka gaisa cike da ƙauna irin na uwa da ‘ya kuma cike da raha sannan Maah ta ƙara da faɗin. “Zauna muyi breakfast ɗin kafin ki tafi dan nasan ba ƙaramin abu ba ne a wurinki ki iya fita Company ba tare da kinci komai ba” Maah ta faɗa tana ɗan kafe ta da ido har da wani ɗaure fuska wai dan ma kar Esherh ɗin ta ga fuska har ta ce a ƙoshe take. Ba musu kuwa Esherh ta zauna suka ci abincin suna yi suna fira bata ci da yawa ba ta tashi ta yi ma Maah sallama sannan ta baro Ɓangaren nasu bayan Maah ta haɗa ta da wani abincin a flask da shima musamman ta yi ma ta kamar yadda ta saba na Lunch sai da Esherh ta biya ta gaishe da kakan nata wato Mahaifin Maah ɗin ta cikin raha kamar yadda suka saba sannan ta yi masa sallama ta bar ɓangaren nasa daga nan ta ƙari sa wurin Security na musamman da Granny da kansa ya ware domin bata tsaro zuwa aiki kasancewar Ranar Monday ne tushen aiki wata farar JAGUAR XJL sabuwa fil ɗaya daga cikin security ɗin ya buɗe ma ta ta shiga sannan ya rufe kana motocin guda uku a jere suka ƙari sa harabar Babban Gate na Estate ɗin tare da fita daga ciki a nutse har suka hau titi kasancewar ta ba mai son gudu da mota ba shi ya sa motocin suke a jere kuma a hankali suke tafiyar. *Ethereal Kreations Joint EKJ* Shahararre ne

Chapter 2 of 7