ko auren ne gwanda ta auri fawaz ɗin tun da duk yafi su cikakken hankali da nutsuwar da zai dinga nesanta lefen Esherh ɗin ga mahaifiyar nashi. Kuma da can baya kafin lalacewar komai da ita Mummyn fawaz ɗin da ita Mammah'n Esherh'n ƙawayene sosái....
Kuma har kwanan gobe sukan gaisa harma da ziyartar juna kasan cewar ita Maman Fawaz ɗin ita da daddy Majeed suna Lagos ne da zama. Wanda shi ne ɗa na biyu a JEDDY's FAMILY. Wata kakkaurar Ajiyan zuciya ta sauƙe daidai lateeb ɗin na ɗagowa ya kalla jaddah'n da idanunsa da har wasu ruwa ruwan bala'i da masifa suka tara ta cikinsu. "Kika ce ba zaki bari na mallaki ƙaunata ba jaddah? Kin kuwa san babban zunubin da kika bari bakinki ya furta? To ni kuma na miki alƙawarin indai ina numfashi a cikin WANNAN DUNIYAR sena mallaki ESHERH KALTHOOM JEDDY's ko da na dare ɗaya ne koda ace na Rana ɗaya I promise you Wannan ɗin alƙawari nane jaddah ina son ki Rubuta hakan ki ajje komin........
Sauƙar marin da yaji saman lafiyayyar fuskar shi ne ya sa shi tsayawa chakkk tare da haɗiye kalamansa na ƙarshen da yay niyar faɗin....
"Idan baka da hankali toni inada hanyoyin dawo da kai kan daidai ɗin ka lateeb, wllh kafff zuriyata ba'ay tantirin da ze zo har gabana kan ido na yana faɗamin muggwan kalamai irin haka ba!ko ita uwar taka ina rabuwa da ita ne kawai domin duk abinda kama wani kai ma In Sha ALLAH se an maka. Kuma daga yau ina son ka ɓace ɓatt gaba ɗaya daga cikin rayuwar Esherh, tamkar haɗuwar hadarin kaka da kuma bajewarsa do You understand?" Jaddah'n ta faɗi tana kama hannun Esherh suka shige cikin lafiyayyen bedroom nata suna barinsa tsaye riƙe da face zuciyarsa na wani irin ƙumbura, yau da ace bason Esherh yake ba wllh da se yay gade fyaiɗe a gaban idon jaddah'n kuma ya aure tan da take ikirarin ba zata bari hakan ya faru ba in yaso ai wannan shi ne ƙarshen fita a rayuwar,In yaso in ma bugawa zuciyarta zaiyi to ya jima beyi ba sedai ta buga ta faɗi ta mutu....
A mugun ƙufule yakai ma iska naushi haɗi da wani kalar furzar da iska yana lumshe idanunsa yana sanya hannunsa cikin aljihun wandon sa ya zaro cigarettes da leiter ya na kunna wuta. Wata irin muguwar suƙa yama cigarrate's ɗin tare da wani lumshe ido yana fita a Room cikin wani mugun fusata.....
*ESHERH KALTHOOM*
Suna shigewa bedroom ɗin ta zame tana turƙushewa a wurin idanunta na wani kalan kaɗawa yayi ja sosai na tsananin kewar koma waye mahaifinta da take ciki. Idanunta ya kaɗa yay jajir tana son tayi kuka amma ta gaza domin ji tayi zuciyarta ta mata wani irin nauyin da ko kukan ba zata iya ɗauka. Wanda idan har batayi wannan kukan ba ciwonta da dama yake gaff da tashi na iya tashi take a wurin.... Ganin yadda jikinta a lokaci guda ya fara rawane ya sanya hankalin jaddah'n tashi tana nufarta...
Zaune takai tana kamo kafadarta zuwa kan ƙafafunta tare da kife hannuwanta biyu saman face na Esherh'n, kafin cikin muryan da yafi kama dana tashin hankali ta shiga faɗin....
"Yi kuka! Kiyi kuka ESHERH yi kuka dan ALLAH!!!. Karki bari hakan ya taɓa BRAIN naki inason kema ki ɗauka duk wani damuwanki ki ajje gefe ki ɗauka komai kamar ba komai ba ki ɗauka hakan kamar haɗuwar hadarin kakane ya haɗa,kuma ya baje ya ɓace ɓatt kamar komai ba'aiba. Karki bari abinda yake faru da Rayuwar ki yayi tasiri a ranki dahar zai yi pinning ɗinki down. FIGHT SHALELEN JADDAH'N TA fight the feeling and move on maza plsss ESH KALTHOOM JEDDY's....
Chakkk kuma ta dakata dan ganin yadda Esherh'n tayi wani kalan yunƙuri kamar zata tashi se kuma ta koma yarabbb bata ko numfashi...
Idanunta taja tana lumshewa Sakamakon wani kalan bugun da zuciyarta ya mata, wani abu me kama da ƙa shi na cake makwallaton ta. Itan ma numfashinta taji Yana neman tafiya amma taƙi bama hakan dama se ma cikin wani kalan tashin hankali ta furta.
*"ESHERH!!!......*
Ihun ƙiran sunan daya karaɗe ko ina da ke gidan kasancewar lokacin dare ya soma wajajen sha ɗaya ne da rabi... Dan haka sucurites ɗin dake zagaye da gidan sune suka fara isowa ɓangaren JADDAH'N. Se dai basa da iko ko izinin shigar mata bedroom dan haka sukay cirko² tsaitsaye suna ma parlour'n ƙawanya da bashi garkuwan idan ma wani abu ne me cutuwa yake a ciki ta yanda yana fitowa zasu fasa kansa...
Daddy majeed shi ne ya fara isa bedroom ɗin, kafin Abban Omer Wanda kusan tare ma suka shigo da Mammah suma suna jan turgwasuwa a inda jaddah'n ke zaune dirsham tayi zaman ƴan ɓori ga Esherh kwance a jikinta babu rai ya tafi..
Wani irin rawa ƙafafun Maah suka fara kafin tamkar kiftar ido ta koma ta fita a guje tana komawa passes nata. Only 1 minute se kata ta dawo hannunta riƙe da car key. Daidai lokacin da daddy ke mata ɗaukan jarirai kawai sukayi waje suna faɗawa cikin car ɗin da Maah tayi Parking nata dap da ƙofar parlour'n....
Da wani irin mugun speed Omer daya amshi key na car ɗin daga hannun Mammah yaja motar yana ficewa daga baki ɗaya passes ɗin jaddah'n....
Kai tsaye wasu motocin su jaddah suna faɗa suma suna rufama motar data ɗauka Esherh baya. A harabar building ɗin clinic ɗin Manyan Mercedes Benz black biyun da suka rufama motar baya ko kyakkyawan parking basuyi ba sukai saurin fitowa Babu Wanda hankalinsa ba'a tashe ba sabo da tsananin tashin hankalin dake cikin zukatansu na ganin yadda Omer ɗin ya shiga da Esherh clinic ɗin, yayinda wasu ɓoyayyun zukatan suke jin Allah yasa nesace tazo kusa Ashshe ta gaida umma bi ma'ana ta mutu ma kenan....
Mutuwar data kasance riga ce ga kowa ko kayi fata ko karka fata dole dole dolen dole dole ne kasan zaka mutu kai ma dan ba gadin duniyar za'a bar maka ba, tun dai ita mutuwar nan ɗaya ce in akayita ba'a taɓa dawowa har gaban abada abadan, don me kuma zaka ma wanin ka fatan ya mutu ɗin...
Arikice nurse's tare da doctors kusan biyar sukayo kan Esherh ɗin kawai dake kula da ita suka ƙaraso suna amsarta. Cikin gaggawa su kayi ciki da ita domin ceto numfashin ta,Wani irin yarfar da hannuwansa Omer yayi yana jingina da jikin motan tare da kulle idonsa kansa na wani irin sara masa. Tabbas yana jin cewar Esherh ita ce duniyarsa itan babu ta shima yana jin babu shi. Cikin wani irin tashin hankali likitoci da nurses ɗin asibitin suka rufa kan Esherh'n dake cikin private aminity emergency, Can kuwa waje Wani irin kuka Mammah ta fasa na tsananin tashin hankalin da Esherh'nta ke ciki Esherh'n da take jin itace Rayuwarta kuma sabo da ita ne take Rayuwa.
Jaddah kuwa wani irin rawa Jikinta yake ganin yadda jikinta ke rawane ya sanya manyan zaratan yaranta maza kewayeta daddy majeed na riƙo hannunta cikin nashi ya matse da ƙarfin daya sanya jaddah'n ɗagowa.
Idanunta da suka jaaaa ta zubama yaran nata kafin cikin wani kalan mugun tausayin Maah ɗin data kanta ita kaɗai ta turƙushe babu kowa wurinta. Dan haka ta sanya left hand nata tana janye hannun daddyn cikin nata tare da nufar Maah ɗin. Hannunta ta kama tana ɗamkewa a nata wanda kai tsaye koba a faɗa wa mahh ɗin ba tasan wannan ɗin ɗumin hannun mahaifiyar ta ne. Hakan ya sanyata faɗawa jikinta tana me sake fashewa da wani irin cunkushashshen kukan da tun farko yaƙi zuwar mata me ciwo da ƙona zuciya se yanzun...
"Jaddah ki ce mata kada ta tafi ta barni ita ma, karta rabu dani kamar yanda mahaifin ta ya rabu dani. Ku ce mata zanci gaba da kulawa da ita da bata kariyar da duk ta rasa tmtsayin rayuwarta.jaddah idan bata tashi ba nima bazan tashi ba mutuwa zanyi mu duka mu huta da wannan 𝘿𝙐𝙉𝙄𝙔𝘼𝙍! 𝙈𝙚 𝙘𝙞𝙠𝙚 𝙙𝑎 𝙩𝑎𝙧𝙞𝙣 ƙ𝑎𝙡𝙪𝙗𝑎𝙡𝙚....... Kuka take sosái jikin mahaifiyar nata kukan da yake fitowa tun daga hasalin zuciya da Ruhinta,kukan da duk wanda zaiji to kuwa Tabbas dole ze tausayawa me yin sane. Wani irin kuka ne me karya zuciya da ƙonewa...
Isowar Doctor NAINERH ne tana ƙarasowa harabar inda duk suke tsaye babu wanda ya iya ko zama a cikinsu ne ya sanya jikin kowa sake yin sanyi. kallon Mammah'n dake jikin jaddah tayi sai kuma ta ɗan saki ijiyan zuciya tare da faɗin.
"Sorry ma'am you have to wait here and please calm your self IN SHA ALLAH she'll be fine we'll do our all best just pray for her! And dan ALLAH ma'am ki dena mata kuka adda'an ki ita ne abu na farko da Esherh zata fara bukata First!"
Tana faɗin hakan ta juya ta shige tana ɗauke guntuwar kwallar data tarummata tare da wasu nurses biyu da suka zo shigewa da gudu suma zuwa emagency room ɗin da Esherh'n ke ciki. Baya Maah dake jikin jaddah tayi cikin tsananin tashin hankalin daya sake riskarta tare da fashewa da wani sabon kukan ganin yadda likitoci ke gudu suna shiga ɗakin da Esherh'nta take. Daddy dake gefen su ne yayi saurin taro su su duka biyun kafin cikin ƙarfin hali ya buɗe bakinsa daƙyar shima yasamu iya furta ma Mammah'n cewa.
"Please Mommah ESH ki dena kuka only just pray for her kinji and kiyi ta mata du'a kuka baya taɓa maganin damuwa okay?"
Wani sabon kukan ta sake saki tare da rintse ido tana me furta.
"Yaya majeed na gaji! Wllh na gaji da Wannan rayuwar, na gaji da ganin Rayuwar Sweetie Kullum cikin mugun haɗari. Zuciya na! Ina jin zuciyata tamkar zata buga ne ko kuma ta faso ƙirjina ta fito ta dena aikinta kowa ma ya huta yaya.......
Saurin rufe mata baki majeed ɗin yayi da sauri yana kallonta da idanuwansa da suka kaɗa sukai jajir tsabar tashin hankalin da suke ciki ga wani mugun bugu da wani irin sanyin da yaji yana ratsa masa har cikin jikinsa. Shi kaɗai a cikin zuciyarsa yake furta ALLAH yasa wannan karon Mummyn lateeb bata da hannu cikin tashin jinyar Esherh'n.
Juyawa Maah tayi ahankali ta kalla gefenta daidai isowar wata nurse ɗin daban a arikice ko gani sosai batayi tsabar tashin hankali tana isowa ta tsaya cak tare dabin kowa na wurin da jajayen idonta.
Kallo ɗaya dr Nainerh tayiwa Maah ta ɗauke kanta wani hawayen da batasan sanda suka tarun mata ba na cika jajayen idanuwanta itama, domin itama a yanzun tazama tamkar family na JEDDY's ne duk wani harkan lafiyansu na rataye ne a wuyanta. Irin kallon da Maah taga Nainerh ta mata da yanda ƙwalla ta cika idinta ne yasa nan take taji gwiwowinta sun gaza ɗaukarta ta zame daga jikin jaddah ta na zubewa kan gwiwowinta tare da rufe fuskarta da tafukan hannayenta wasu balaƴay'un hawaye na tsinke mata masu zafi da ciwo... Ɗauke kanta jadda tayi daga kallon Maah ɗin tayi ganin halinda da take ciki zuciyarta na ƙara sa yin nauyi sosae itama. Har hawayen da take ta ƙoƙarin dannewa na neman gangaro mata daidai loƙacin da ta ɗago kanta tana ɗora idanuwanta kan Mah.
Kafin Ahankali idanuwanta suci gaba da sauƙa kan duka mutanen da suke tsaye cirko cirko har Idonta yakai karshen kan LATEEB dake tsaye hannuwansa goye da bayansa sai kaiwa da komawa yake ya haɗa wata uwar zuba ta tashin hankali....
"I'm so sorry ma'am! Munyi duk wani ƙoƙarin mu na ganin koda numfashin ta ne ya dawo se dai hakan is to late ALLAH be nufa ba, yanzu haka numfashin ta na a matakine na 0:015 wanda muka ƙara sa bugar da shi domin gudun shima kada ya gudu!.....
Se kuma ta dakata domin wannan kalmar ta nemar wannan kwararren likitan masanin cutar numfashin shi ne kusan karo na biyar kenan da suke ta fafutukar neman ko ganin sun sama koda sunan shi ne.... A mugun hankali Maganar ta na rarrabe wa ta sake furta....
"A...aaaa....wan..nan... Ka...karon... dole ne.. muna da buƙatar sa!!! Mu na da buƙatar taimakon sa.....domin babu wanda ze iya ceto rayuwarta In ba....shi...ba!"
Rinannun idanunta Maah ta ɗago tana sauƙewa akan Nainerh dr tare da fara magana cikin muryanta da itama yake numshin ke gab da barinta ta ce.....
"Ko a wacce duniya yake, ko nawa zan kashe! Ko da kuwa ace katafanin dukiyana zata ƙare kafff ban damu ba indai za'a samo likitan!! To kuwa ban damu ba kai ciki harda rasa tawa rayuwar Lallai nan da 24 ina bukatar ganin wannan likitan gabana ko da kuwa se kai ga ɗurkusa masa ne zanyi in dai har a wannan karon ze ceto min Rayuwa da Numfashin bugun zuciyata ban damu ba maza a baza nemansa ko da kuwa yana a birnin sin ne lallai akwai buƙatar ya bayyana a wannan karon kamm............
Cikin son bama Maah ɗin hope ta buɗe bakinta tare da cewa.
"Sunan sa *SAMEER OTHMAN KAMPALA's, samm ba mazaunin Nigeria bane aikinsa kawai yawon zaga duniya ne, kuma shi ne wannan shahararren MONSTER ɗin ɗan kasuwar da ambatar sunan sa kawai kan haukata zuciyoyin maƙiyansa THE Billionaire Sameer othman kamfala's, se dai bana da tabbacin yanzun haka yana ko yana a wacce duniyar neee....
Kanta Maah ta riƙe sunan na mata kama da wani wasu data taɓa ji kota taɓa gani, sunan da bata ƙara jin koda kalan sa bane se a Ranar da Eemaan Sufyan ta ambaceshi.... Wannan tunanin datay ya sanya brain nata fara loosing itama take dan haka tayi baya luuuuuu....................
*BY NAINERH KD and AMMEY LAYLERH ✍️☑️💪*
Via phone Only WhatsApp
08104493215
07067953066
❉্᭄͜͡𝘚O 𝘿𝔸𝑵☆ R̲A̳Yᑌᗯᗩ ♥️
_☆♥︎L⋆o⋆v⋆e⋆ ᖴOᖇ 𐐛օv𝖊♥︎☆_
𝗕Ⲩ 𝔸mmⅈ𝖊ყ ℓαуℓєян & ɴᴀɪɴᴀʀ kd♡
P9&10
24hrs later.
*_Nisa Premier Hospital_*
_Abuja, Nigeria._
*_Dr Sameer Othman Kampala's, Consultant Neurosurgeon_*
Zaune yake hamshaƙe cikin katafaren Office nasa dake asibitin ya mayar da hankalinsa kacokan ga files da yake dubawa na marar lafiyar da zai yima aiki nan da mintoci masu ƙaratowa, duba file ɗin yake yana nazartar komai daki daki dangane da rashin lafiyar nata har ya zo kan suna da marar lafiyar da za'ayi ma aikin.
“Esherh Kalthum Jeddy's!”
Ya faɗa a zahiri zallar mamaki yana cika sa sai kuma ya juya ɗayan shafi na file ɗin take hotonta ya bayyana. Shiru ya yi yana ɗan nazari sai kuma ya basar ya ci gaba da nazartar rashin lafiyar da take da matakin da take har zuwa lokacin da ya yi daidai na shiga aikin, misalin ƙarfe takwas da rabi na dare suka shiga aikin yayin da Dr Sameer Othman Kampala's ya kasance ya jagoranci aikin cikin nasara sun kammala aikin ba tare da wata damuwa ba hakan ne kuma ya kwantar da hankulansu Maah dake a tashe tun lokacin a ka shiga aikin.
Sameer kuwa yana kammala aikin yabi ta wata ƙofar daban ya fice daga operation room ɗin, da yake aikin shi ne kaɗai wanda ya rage masa a asibitin shi ya sa bai ƙara mintoci biyar ba zugan motocinsa suka fi ce daga asibitin.
______
3 Day's later!
Alhamdullilah za'a ce domin sosai jikin Esherh ya yi sauƙi tun bayan aikin da aka yi ma ta sai dai ba'a bawa su Maah damar ganinta ba har sai da ta cika kwana biyu da yi ma ta aikin sannan Dr Sameer ya tabbatar musu da ba za'a sallame ta ba har sai ta cika sati guda a asibitin sai kuma wasu sharudda da za'a cika bayan an sallame ta.
Da sallama ɗauke a bakinta Eaman ta tura ƙofar Room ɗin da Esherh ke ciki sannan ta shiga, Esherh da fitowarta daga Bathroom ke nan ta dubeta ta watsar da yake fushi take da ita, amsa sallamar ta yi sannan ta ƙari sa ta zauna ba tare da ta kuma cewa Eaman ɗin uffan ba.
Murmushi Eaman ta yi dan tasan laifinta hakan ya sa tun kafin ta ƙari sa ta yi saurin kama kunnenta cikin muryar lallashi ta furta.
“Ayya am so sorry bestie i know you're mad at me and it's all my fault, an yi miki aiki guda amma ban zo ba har sai da a ka yi kwana uku nima ba haka naso ba Granny ɗin mu ce Allah ya yi ma ta cikawa shi ya sa muka tafi can KD ɗin ta'aziya kuma kinsan dama saboda jikin nata muka dawo daga US.”
Ta ƙare maganar daidai lokacin da ta ƙari sa wurin Esherh ba tare da ta zauna ba kuma bata saki kunnen nata ba.
Ajiyar zuciya Esherh ta sauke jin bayanin da Eaman ɗin ta yi.
Da muryarta irin ta marar lafiyar da bai gama warkewa ba ta furta.
“Hmph ai kuma kin kashe min kalamaina bani da abin faɗa tun da dai mutuwa ta wuce komai, Allah Ubangiji ya yi ma Granny Rahama, ke kuma yanzu ina tsaraba ta kin san dai kwaɗayi irin namu masu farfaɗo wa daga ciwo.”
Esherh ta kai zancen tana murmushi.
Murmushin ita ma Eaman ta yi tare da furta. “Tabbas ni kuwa nasan kwaɗayi irin naku shi ya sa nazo miki da tsaraba na musamman!”
Ta ƙare maganar tana clapping hannunta fuskarta ɗauke da murmushi.
Buɗe ƙofar ɗakin a ka yi Esherh da ta yi faƙare tana jiran ganin an fara shigo da abin daɗi ga tsananin mamakinta sai gani ta yi Fawaz ya bayyana sanye cikin kakinsa na soji, sakin baki Esherh ta yi tana dubansu duka su biyun daga Fawaz ɗin da ya ƙari so ciki har Eaman da take ta faman sakin murmushi dan a ganinta ba ƙaramin abin a yaba ma ta ta yi ba da har ta iya sakawa Fawaz ya baro aikinsa mai muhimmanci da yake ya dawo Nigeria domin ya ga Esherh'n domin kuwa tun lokacin da ta faɗa masa halin da Esherh take ciki ta e-mail gaba ɗaya ya ruɗe yaji ma gaba ɗaya aikin ya ishe shi so yake kawai ya dawo yaga halin da Esherh'nsa take ciki shi ya sa suka tsara da Eaman yadda zasu yi ma ta surprise na ban mamaki.
“Suprise!”
Cewar Fawaz yana murmushi.
Yayin da ita kuma Eaman ta furta.
“Ta-da!!”
Esherh kuwa da ta yi shiru tsaban mamaki tama kasa furta komai ga bakinta da ta buɗe cikin ready na a ka wo ma ta kayan kwaɗayi da kwalama rasa abin faɗa ya sa ta kwashe da dariya ta kuma ci gaba yadda kasan ta shaƙi laughing gas, idanu Eaman da Fawaz suka haɗa cikin mamaki sai kawai suma suka biye ma ta suna sheƙa dariya.
Tsabar dariyar Esherh har da hawaye sai da ta yi ma'ishi sannan ta tsaya tana dubansu sai kuma ta ce.
“To mene ne kuma na dariyar.”
Sake haɗa ido Eaman da Fawaz suka yi ai kuwa suka ƙara kwashewa da dariya Esherh ta zuba tagumi hannu bibbiyu tare da zuba musu ido tana jira su gama suna cikin haka sai ga Maah ta turo ƙofar ta shigo da sallama sai ta yi turus tana kallon ikon Allah.
Esherh da ta amsa sallamar tare da juyawa tana dubanta ta ce.
“Maah ƙari so mana dama yanzu nake shirin kiranki daga kije ki dawo gaba ɗaya kin barni cikin kewa.”
Esherh ta faɗa a shagwaɓe.
Ita kuwa Maah sai cewa ta yi.
“su kuma waɗan nan ƙalansu?.”
“Hmph ina fa da alama sun ɗan taɓu ne.”
Esherh ta faɗa tana ɓoye dariya, sai lokacin suka saita kansu, Fawaz ya ɗan duƙa yana gaida Maah. Amsawa ta yi tare da ƙara wa da.
“Sannu da ƙoƙari Soja mazan fama yanzu saboda Allah shi ne ka baro can ƙasar ka baro duka aikin dake gabanka ka dawo?”
Murmushi ya yi yana ɗan sosa kai ya ce.
“To ya za'ayi Maah ai haka ya zama dole ne gaba ɗaya hankalina ne ba'a kwance ba, But I'm so glad that now she's okay!”
Ya faɗa yana satar kallon Esherh.
Zama Maah ta yi cikin alfahari da nuna ƙauna da Fawaz yake ga ƴar nata sai dai matsalar ɗaya ne shi ne mahaifiyar Fawaz ɗin Maah tana jin badan ita ba da ta daɗe da aurawa Fawaz Esherh domin ya cancanta duk da ita Esherh'n bata taɓa buɗe baki ta ce tana son shi ba.
Zama duk suka yi suna ɗan taɓa fira da yawanci Maah da Fawaz ne suke yi su dai su Esherh sai dai suyi ƙusƙus ita da Eaman wani lokacin su haɗa da dariya har da tafawa da suka ishe Maah ta dube su tana faɗin.
“Ai shikenan kuma kun haɗu babu kwanciyar hankali an tasa gulma ko wato har kinji sauƙi ai kuwa sallamarmu za'a zo ayi.”
Cike da shwagaɓa domin har ta manta da ba su biyu ba ne a wurin Esherh ta ce.
“Laaa Maah Allah ba gulmar kowa muke ba kawai fa Eaman tana bani labarin reunion da aka yi na ƴan class mate namu na secondary school da ban sama zuwa ba shi ne take faɗa min yadda wasu suka koma har tana nuna min hotunan da su kayi ina ce ma kin san wani da nake yawan baki labarinsa lokacin muna secondary school shi ne ƙaramin ajinmu gashi ba ƙiba kuma ba girma har hakan ya sa ƴan class ɗin namu suke kiransa da Smolley shi ne fa yanzu bakiga yadda ya koma ba wai har ma bleaching yake ya yi ƙiba ya zama wani Alhaji shi ne fa abin ya bani dariya.”
Esherh ta ƙare maganar tana ƙara fashewa da dariyar tare da nunawa Maah hoton dake screen ɗin wayar Eaman dake hannunta.
Tun da Esherh ta fara maganar Maah ta yi shiru tana saurarenta gefe guda kuma tana hamdala ga Allah Ubangiji da cikin lokaci ƙanƙani yarinyarta ta dawo da cikakken lafiyarta duk da har yanzu Esherh'n taƙi ta sanar da ita ainihin dalilin da ya saka ciwon nata ya tashi amma da sukayi magana da Joddah ta faɗa ma ta komai a kan Lateeb ne sila, a lokacin da suke tsaka da tashin hankali na halin Rayuwa ko mutuwa da Esherh take ciki kwatsam kira ya shigo ma Maah a kan sun sama Approval na ganin Dr Sameer da suka daɗe suna fatan hakan, a lokacin da Maah ta yi ido huɗu da shi bayan taji cikakken sunansa da a baya bata sani ba domin da Dr Sameer kawai ta sanshi, matuƙar tashin hankali da mamaki ta shiga na ganin zallar kamanni da yake da Mutumin da ba zata taɓa mantawa da shi ba Rayuwarta baya ga wannan ga sunan Family ɗaya da suka haɗa hakan ya tabbatar ma ta da dole suna da alaƙa da shi, sai dai kasancewar a halin yanzu samun lafiyar Esherh shi ne a gabanta shi ya sa ta bar komai a kan gaba baya zata bincika domin sanin ainihin gaskiya.
Tana shirin magana a ka turo ƙofar da hakan ya sa gaba ɗaya suka mayar da hankulansu domin ganin mai shigowa.
Dumm! Ƙirjin Esherh ya bada sautin bugu na razana da kuma tsoro na ganin fuskarsa da ta yi hakan ya sa ta ƙanƙame hannun Maah ƙam idanunta kafe a kan Lateeb da ya shigo Room ɗin babu ko sallama tsaban rashin mutunci irin nasa sai ma cewa da yake.
“Sweetie ya da haka ke kuwa dama kinji sauƙi amma wancan ƴar baƙin cikin tsohuwar taƙi ta sanar dani wato ana baƙin ciki saboda kar na sani ko bayan ke ɗin tawace amaryata zaki zama nan bada jimawa ba.”
Wani