Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 4
ɗaya gidan ya hargitse da hayaniya kowa na faɗar Albarkacin bakin shi. ************************* Sumayya ce da Zahra suka fito cikin shirin tafiya Masallaci, cikin shiga mai kyau da hijaban su har ƙasa sukayi ma Mahaifiyar su Sallama suka fita, har sun kai bakin kofa Zahra ta juyo tazo tace ma "Mama Kulu duk abun da nayi miki ki yafe mun kinji." "Zahra ni baki mun komai ba, meya kawo wannan maganar kuma,? Kin sa jikina yayi sanyi." "Mama Kulu kuji tsoron Allah ko bayan rai na ki riƙe Amanar da Allah ya baki." Tana ƙarasa maganar ta juya tana jin hawaye na zubo mata. ************************* Laila ce take ta shiri, yayin da Mahaifiyar ta take tsaye tana kallon ta. "Laila kin tabbata kwana biyu zakiyi,? kin san halin mahaifin ku in har ya dawo Abuja bai ganki gida ba." "Haba Mom karki damu kwana biyu zanyi insha Allah, kin san Anisa in banje mata wannan Sallah show ɗin ba akwai matsala." "To shikenan A dawo lafiya, Laila ki kiyaye kin san halin dai daddy ku, banda shashanci." ************************* An sauko idi su Zahra sun fito domin komawa gida, da sauri Sumayya tayi gaba ta bar Zahra taje tana Amsa waya, bayan ta gama Amsa wayar sai ga Zahra ta iso dai dai lokacin da wani mai adai-daita sahu ya iso, Sumayya tana ƙoƙarin shiga Zahra ta riƙota "Rabin rai na ni hankali na bai kwanta da mai keken nan ba ki bari mu samu wani." Kamo hannun ta Sumayya tayi ta shigo da ita tace ma ta "Rabin rai wai meke damunki ne yau na ganki haka, kiyi addu'a kawai insha Allah ba Abun da zai faru." Sunyi tafiya mai Nisa kawai sai gani sukayi mai keken ya canza hanya..✍️✍️ SARAUNIYAR KANAWA👸👸 SANADIN ABAYAR SALLAH👗👗👗 TARE DA ALKALAMIN ✍️ ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU (sarauniyar kanawa) ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ *Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.* BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM PAGE 7 KADUNA Sosai Zahra ke kuka tana tanbayar me Adai-dai ta sahun ina zai kaisu, Amma Sumayya ko a jikin ta sai ma waya da takeyi sai da ta kammala wayar ne ta juyo tana kallon Zahra. "Haba Zahraty wai meke damunki ne,? Gidan su Ƙawata Shamsy fa zamu je." "To ai sai ki faɗamun kin sa hankali na ya tashi, shima mai keken yana ji na kaman kurma." Shidai Mai Keke bai ce musu komai ba dai-dai sun iso wani katafaren gida da ya Amsa sunan sa, ya sauke su bakin gate ya juya Zahra ta waigo ta kalli Summayya tace mata "baki bashi kuɗin ba." "Eh na sani shi zai dawo ya ɗauke mu ai." "Amma ba daɗewa zamuyi ba ko kin san yau Baba Bukar da wuri yake dawo gida domin mu ci Abincin Sallah tare kamar yadda muka saba yi duk shekara." "Na sani Zahraty ni mu tafi kina ɓata mana lokaci."dai dai an buɗe musu gate ɗin gidan "kune Sumayya da Zahra,"? "Eh mune." "Ok ku shigo ko." Tunda suka shiga gidan suka saki baki suna kallon irin haɗuwar da gidan yayi, basu ƙara tabbatar da haɗuwar gidan ba sai da suka shiga ƙayataccen falon gidan. Nan da nan mai aikatan gidan suka cika musu gaban su da kayan ciye-ciye, gaba ɗaya jikin Zahra yayi sanyi yayin da Sumayya ko take ƙoƙarin buɗe kulolin Abincin. "Yauwa ranka ya daɗe an samu kalan kayan da kake so, kuma kayan fa mai kyau ce yadda kake buƙatar shi kamar yadda dodon Asiri ya buƙata, Amma kafin nan sai mun huta da kayan fa." Ya ƙarasa maganar yana kwashewa da dariya irin na marasa imanin nan kafin ya cigaba da magana " ai in faɗa maka Alhaji ni naji daɗin wannan yayin Abaya da akayi, kaga ta sanadin shi mun samu abun da muke buƙata cikin sauki wallahi, ai dama muke maganin kwaɗayayyun ƴan mata, to shikenan sai aiki ya kammala mu haɗu a gidan tsafi kawai." Ya ƙarasa maganar yana ajiye wayar a kan table. ************************* KANO Katafaren Hotel ne da sai wane da wane suke zuwa gurin, can na hango Laila riƙe da ƙaramar akwatin kayan ta tana waya. Can sai ga Alhaji Tanko ya fito da wani ƙaton cikin shi a gaba yana washe baki. "Baby Baby, kin ganki kuwa sai kika fi kyau ma a fili fa." Yana maganar yana lashe baki, ya rungomota suka shige ciki tun daga hanya suka fara aikata masha'ar su. Wa'iyazibillah Allah yayi mana tsari da masu hali irin na Alhaji Tanko. Sunyi nisa gurin aikata masha'ar su aka kira Alhaji Tanko inda wayar ta katsemusu jin daɗin su har ya ɗauko zai kashe sai yaga ai wani Abokin duniyancin shi ne da suka haɗu a Abuja wata biyu da suka wuce. "Hello mutumi na ya akayi ne ka shigo Kano ne." "Eh wallahi nayi sabon kamu ne shine nake so ka samamun Hotel mai kyau nan da minti Ashirin ganinan zuwa." "Ok Alhaji karka damu nima yanzu haka fa ina kan aiki ne, ka rage mun jin daɗi na da wata ƴar shila." Ya ƙarasa maganar yana kai ma Laila kiss a kumatu. "kai Aboki na baka wasa da wannan harkar fa, kana moran ƴammatan social media fa, shiyasa ni bana barin ƴata ma da waya balle tayi wannan shirmen." "Hhhhh ashe muna ɗaya Alhaji ai ni gida na ma ba mai riƙe waya har Mata ta." "hhhh kai naka Abun yayi yawa kuma, sai nazo dai kawai a cigaba da jin daɗi lafiya." ************************ KADUNA BAYAN AWA UKU Sumayya ce da Zahra kwance su ba barci sukeyi ba kuma su ba idon su biyu ba ko hannun su bazasu iya ɗagawa ba, kuka sosai Zahra takeyi tana dana sanin biyo ƴar uwar tata, gashi ta kawo su ga halaka za'a lalata musu rayuwa a banza. Dai dai lokacin da Zubair ya fito daga shi sai gajeren wando da Vest sai wasu samudawar mutane su hudu da suke bin su a baya. Sosai Zahra ta zaro ido ganin mutumin da duk lokacin da ta ganshi sai gaban ta ya faɗi, dama nan Sumayya ta kawo su gurin wannan Azzalumin mutumin, shikenan tasu ta ƙare. duk Zahra ke wannan maganar a ran ta. "Sumayya manyan gari, da farko dai ina mai farin cikin shaida miki kin ci kuɗin sai da wasu sassa na jikin ƴar uwar ki, domin tun ranar da na ganku na gane cewa ƴar uwar ki na ɗauke da wani boƴaƴƴiƴar ajiyar da muke buƙata a jikin ta, domin ni da kike gani haka cikakken matsafi ne duk da kin sa kaya a jikin ki ba abun da ban gani ke in taƙaita muku har kayan cikin ku ina gani, ke kuma tun da na ganki na kwaɗaitu da surar ki daga gani zakiyi ruwa, Amma kafin nan takar ƴar uwar ki zan fara ku cire mun kayan ta." Cikin sauri waɗan nan gardawan suka tuɓe Zahra.Da ba abun da takeyi sai kukan da ba sauti da duk addu'ar da yazo bakin ta. Sumayya na kallo Zubair ya keta Mutuncin Zahra da karfi, yayin da waɗannan ƙartin duka su biyar duk da Zubair na shida suka shige Zahra a lokaci guda har ta duburan ta tun tana iya numfashi har yazo ta zama tamkar gawa, sunfi Awa akan ta wanda Sumayya na kallo ba dama ƙarɓan ƴar uwar ta, bayan komai ya lafa ne suka yanke duk wani abun da suke buƙata a jikin ɗan adam a jikin Zahra yayin da take furta kalmar shahada da sunan ƴar uwar ta shine kalmarta na ƙarshe ta Rasu. A take Sumayya ta sume, Azaba shiganta da Zubair da waɗannan matasan sukayi lokaci guda ya farfaɗo da ita, haka suka dunga aiki a kan ta har sai da suka gaji dan kansu suka koma suna mai da numfashi ita ko Sumayya suman ta biyar Azaba ke farfaɗo da ita. Sai gab da magrib suka kyaleta Zubair ya ba waɗan nan gardawar Umarnin su kwashe su Zahra suje su zubar dasu kan layin unguwar su tunda yanzu dare yayi. ************************* KANO BAYAN AWA UKU "Alhaji ya kamata kazo ka ɗanɗana nawa baby in ɗanɗana naka." "haka kuma fa za'ayi, to mu haɗu ganinan fitowa kai ma ka fito, ko kuma mu haɗasu ɗaki ɗaya mana kaman zai fi mana ɗaɗi.? "A'a kawai kazo nawa ɗakin nima in zo naka kowa ya ɗanɗana." Haka ko akayi Alhaji Tanko ya fito ya nufi ɗakin Abokin shi, shi kuma abokin shi ya nufi ɗakin shi. "Baby Bab!!!." bai ƙarasa maganar ba ta maƙale mai a Baki yana nuna yarinyar da ya gani kwance kan gado haihuwar uwar ta da uban ta. Yayin da shima ta ɓarayin Abokin Alhaji abunda ya faru kenan. "wa nake gani kaman Laila.✍️✍️✍️✍️ SARAUNIYAR KANAWA👸👸👸 SANADIN ABAYAR SALLAH👗👗👗 TARE DA ALKALAMIN ✍️ ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU (sarauniyar kanawa) ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ *Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.* wannan page ɗin sadaukarwa ce ga sabon kungiyar tallafawa marayu da muke ƙoƙarin buɗewa wato (ƊARIƘUL JANNAH DONATION FOUNDATION) ƴan uwa muna buƙatar addu'oin ku, ga dukkan mai niyar taimakawa wannan kungiya kuma kofa a buɗe take sai ku tuntuɓi wannan number 08037420816 ka bada ƙalelan Allah ya baka kaseeran🙏🙏. BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM PAGE 8 KADUNA Sosai hankalin Mama kulu ta tashi ganin har la'asar ƴaƴan na ta basu dawo ba, gashi Baba Bukar shigowar shi biyar kenan yana tanbayar ta sun dawo kuwa, kasancewar duk Sallah in an sauko idi gaba ɗayansu zasu zauna su ci Abinci a Faranti ɗaya gashi har yanzu Su Zahra basu dawo ba. Hankalin su bai ƙara tashi ba sai da magriba ta doso ba yaran nasu ba labarin su, sosai fa hankali ya tashi yayin da gaba ɗaya unguwa labari ya bazu da ɓatan su Zahra Sosai Mama kulu ke kuka saboda ɓatar ƴaƴan nata kuma tasan tabbas laifin ta ne da suka haɗa baki da Sumayya ta Amince mata cewa su bi mutumin da basu san ma asalin shi ba saboda son Abun duniya irin nata gashi ta rasa ƴaƴan ta biyu da su kaɗai ta mallaka a duniya, tabbas in har Bukar yasan wannan zance ta tabbata bazai yafe mata ba ƙarshe ma ya sake ta yau ta shiga uku ita Hauwa. sosai Mama kulu take ta sunbatu ita kaɗai can taji motsin shigowa gidan da sauri ta tashi tayo waje ganin Baba Bukar tayi ya shigo jiki a sanyaye. "Bukar kar kace mun ba'a gansu ba har yanzu."? Cewar Mama kulu tana nufar mijin na ta. "Kulu har yanzu ba'a ga su Faɗima ba, yanzu haka ma daga gidan Radio muka fito nida Alhaji sunce muyi haƙuri zuwa safiya." Ƙara fashewa da kuka Mama kulu tayi tana zaman ƴan bori "Shikenan Bukar na rasa ƴaƴa na tabbas na cuci kai na." "Bangane mai kike faɗi ba Kulu kimun bayani ko kin san inda yaran nan suke ne,? ko sun ce miki zasu wani guri ne."? "A'a wallahi ban sani ba Bukar." Cewar Mama kulu tana zare ido. ************************* "Wallahi Muntasir baka isa ba ni zaka ciwa mutunci kace ka sakeni gaban mutanen gida, to wallahi ba inda zani ehee, ke kuma munafuka wato har da bashi ƴa ko."? "Ahayye dama ni bari kiji in faɗa miki Hafsat haushin ki nakeji a gidan nan saboda irin hidiman da mijin ki yake yin miki shiyasa naci Alwashin sai na kashe miki Aure da yake ke shashace kika biye mun, to bari kiji ni ba Abayar da Mijina ya siyamun Arowa nayi don in kara haukata ki, wawiya kawai." Aiko nan gida ya ƙara kaurewa da hayaniya wasu suna ganin rashin kyautawar Maman Amir wasu kuma suna ma Hafsa Allah ya ƙara, ana haka dambe ya kaure tsakanin Hafsa da Maman Amir aka ma Hafsa ɗan banzan duka dama ba ƙarfi gareta ba. "Umma Muntasir ya sakeni." Ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka tana faɗawa jikin Umman na ta. "Ɗagani Hafsat aini kin bani mamaki, ina tarbiyar da mukayi miki,? tun kafin kizo naji duk abunda kika aikata kuma kiji da kyau Uban ki ma yau shekara goma kenan rabon da yamun kayan Sallah balle ke kin samu ɗan Albarkan yaron nan yana miki shine har sai kin zaɓa, to kizo ki zauna a gidan Uban naki da Abincin da zamu ci ma gagarar mu yakeyi balle wani abu wai shi kayan sallah, ga Ƙanen ki nan biyu duka sun isa a kaisu ɗaki ba mijin Auren, don yanzu Ƴan mata ma neman mijin suke ido rufe Amma ke kin samu kin yi mai riƙon banza, shiyasa banga Laifin Hajiya laure ba da tace ta bashi ƴar ta ko nice haka zanyi don Muntasir ba mutumin yardawa bane Amma tunda haka kika zaɓa kizo muyi ta zaman gidan har Allah ya kawo miki wani mijin." Umma ta ƙarasa maganar tana shigewa ɗaki abun ta. ************************* KANO "Daddy dama ba Abuja ka tafi ba kace ma Momy kana Abuja."? "ke kin ci gidan ku uban me ya kawo ki nan karki cemun Laila gantali kika fara don Allah, Innalillahi wa'innah ilaihirraji'un." Yana gama faɗi ya yanke jiki ya faɗi. "Wayyo Allah Daddy don Allah ka tashi kar ka mutu a wannan mugun yanayin." Ɓarayin Alhaji ma Abun da ya faru kenan haka yaran suka kwashe su da taimakon wasu mutanen sukayi Asibiti dasu. Bayan sun kaisu ne kuma faɗa ya ɓarke tsakanin ƴan matan kowa na tsargin kowa da bin Mahaifin ta. "Allah dai yasa kin gani dai naki Bunsurun Uban shi ya biyoni har Kano bani na bishi ba ehe, kefa da yake daga ke har uban naki Bunsuraye ne ai kema biyo mahaifin nawa kikayi, kinga kuwa ni ƙaramar karuwa ce tunda ban zuwa wani garin iyakata a garin mu." "ke dakata haka ya isheki karki sake ki faɗamun magana kema da Mahaifin naki meye in ba bunsurayen ba anyi gado." "Kune kuka kawo marasa lafiya."? "Eh Doctor mune." "To ku biyoni ofishi na." "To Doctor." Suka haɗa baki gurin faɗa, sannan suka bishi kowa na hararar ƴar uwar ta. Bayan sun Zauna ne yake musu bayanin, "ku meye matsayin ku ga marasa lafiyar."? "Iyayen mune Doctor meya samesu.? "To cuta dai ba mutuwa bace kuma komai ya faru daga Allah ne kuyi haƙuri ina mai sanar muku iyayen ku sun kamu da faralyse cutar ɓarin jiki Amma abu ma yazo musu da sauƙi dukan su, nan da kwana uku zamu sallamesu Allah ya ƙara sauki." ************************* KADUNA Tafe suke akan Babur su gurin biyar sun dawo kallon kwallo, tun daga nesa suka hangi wulƙawar wata baƙar mota ta fita layin a guje, su kuma suna shiga kwanar layin suka ga kaman mutane ne kwance a gurin kasancewar Babur ɗin nasu ba fitila yasa suka tsaya suna kiciniyar fito da wayoyin su don su haska su tabvatar da me suke gani.✍️✍️✍️ KUYI HAƘURI MASOYANA NA JINA SHIRU KWANA BIYU ABUBUWANE SUKAMUN YAWA NASO IN GAMA LITTAFIN NAN GABA ƊAYA YAU AMMA BAZAI YUWU BA, KU SANI A ADDU'OIN KU ALLAH YA CIKAMUN BURINA NA ALHERI DA DUKKAN ƳAN UWA MUSULMI🙏🙏🙏 sarauniyar kanawa👸👸 SANADIN ABAYAR SALLAH👗👗👗 TARE DA ALKALAMIN ✍️ ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU (sarauniyar kanawa) ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ *Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.* WANNAN PAGE ƊIN GABAƊAYAN SHI SADAUKARWA NE A GAREKU MUTANEN MAJALISAR MARUBUTA SON SO NAKE MUKU IYA WUYA ANA TARE🥰🥰🥰🥰 BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM PAGE 9&10 Sosai suka firgita ganin ƴan mata biyu kwance cikin jini tamkar basa numfashi. "kai Kamal haska mana da babban wayar ka sai naga kamar ƴan biyun gidan Malam Bukar da ake nema." Cewar ɗaya daga cikin matasan, da sauri wanda aka kira da Kamal ya fito da wayar shi yana ƙoƙarin kunna fitilar wayar, yana kunnawa duka suka rufe idon su saboda mugun ganin da sukayi suka haɗa baki gurin faɗin. "Innalillahi wa'innah ilaihirraji'un! kai duniya ina zaki damu don Allah ku dubi irin cin zarafin da akayi ma ƴan matan nan." Ɗaya a cikin matasan ya faɗa yana zubar da hawaye. "To yanzu meye abinyi.?" "Kai Kamal kaje offishin ƴan sanda yanzu kayi report, kai kuma Abdullahi kaje gidan Mallam Bukar ka kirashi." Amsawa sukayi da "To" suka juya cikin hanzari. Kafin kace kwabo gaba ɗaya labari ya cika unguwa, nan da nan aka cika a gurin tamkar ba dare ba. Mallam Bukar ne shi da Mama Kulu suke ta sauri su isa inda sukaji labarin cewar ga ƴaƴan su can kwance cikin jini, Mama kulu saboda tsaban ruɗewa ko mayafi ma bata sa ba. Mallam Bukar ya fara isowa gurin yayi tozali da irin cin zarafin da aka ma ƴaƴan shi take a gurin ya yanke jiki ya faɗi zuciyar shi ta buga ko shurawa baiyi ba. Hannu Mama Kulu ta sa a kai ta nufi gurin Mallam Bukar tana ihu tana faɗin, "don Allah Baban biyu kar ka mutu ka barmu a cikin wannan halin nida ƴaƴa na,! Jama'a ku taimakeni wai meya samu yara na ne har ya kai ga mijina ya yanke jiki ya faɗi.? "Ku riƙeta kar ku bari ta ƙaraso nan, yanzu zamu kwashesu duka zamu tafi Asibiti kafin mu fara binciken wanda ya aikata haka garesu." Cewar wani ɗansanda. Yayin da sai rirrike Mama kulu ake tana fisgewa tamkar mahaukaciya, haka aka kwashe su Sumayya aka tafi dasu Asibitin Dutse, ita ma Mama kulu wani ya goya ta a machine suka bi bayan su, shima Mallam Bukar aka ɗauke shi a wata motar don zuwa Asibitin a tabbatar ya mutu ko da sauran numfashi. ************************* "Hello Momy kizo Kano akwai matsala fa." "Ke Laila lafiyan kuwa da zaki cemun in zo Kano bayan kin san Daddy ki baya gari, da izinin wa zanzo,? ki faɗamun meke faruwa.?" "Momy wallahi Daddy ne gashinan a Kano ba lafiya kuma ki buɗe Datar ki in kiraki Vedio call ki gani." Jiki na rawa Hajiya Azima ta kunna Data ta kira ƴar ta ta domin tabbatar da abunda ta faɗi zuciyar ta cike da mamaki me ya kai mijin ta kano shi da yace zaije Abuja. Sosai hankali Momy Laila ya tashi ganin Alhaji kwance a kusa da ƴar tasu hannun sa an ɗora mai ƙarin ruwa. "Ke Laila mai ya sameshi ki faɗamun.!" Hajiya Azima ta faɗa cikin tashin hankali. "Momy ki bari ki zo tukunna sai muyi magama." cikin ƙanƙanin lokaci Hajiya Azima tayi bucking na jirgi zuwa kano kuma taci sa'a akwai jirgin da zai tashi nan da minti Ashirin. ************************* Muntasir ne yaci manyan kayan shi ya fito sak angon shi Maryam tana biye dashi da jakar shi sai tashin ƙamshi sukeyi shida ita. "To miji na a dawo lafiya Allah ya baka abunda kaje nema na halas Allah ya hana ka zuwa ga haram, ya karemun kai a duk inda kake kaje lafiya ka dawo cikin Aminci." Cike da jin daɗin addu'ar ta ya washe baki kasancewar shi Mutum mai yawan fara'a yace mata, "Ameen ƴar Albarka tabbas yanzu nasan nayi Aure na dace da mace ta gari, Allah yayi miki Albarka Maryama sarauniyar Mata." "Ameen miji na" Ta ƙarasa maganar tana miƙa mai jakar shi ta juya ta shige ɗakin ta, shi kuma ya fita yana mai jin kamar duk duniya ba wanda ya kaishi dace da mace ta gari. ************************* WASHE GARI ASIBITI Sosai Mama Kulu take ihu tana faɗin "Wallahi miji na da ƴa ta basu mutu ba.!" Yayin da ake rirriƙe ta, bayan an fito da gawar Zahra da Mahaifin su ita kuma Sumayya tana can Rai a hannun Allah an sa mata abun jawo numfashi. Mallam Bukar da Zahra dai sun rigamu gidan gaskiya sai dai muce Allah yaji ƙansu ya gafarta musu. ************************* Bayan kwana uku da faruwar lamarin Sumayya ta farfaɗo sai dai ta kamu da ciwon yoyon fitsari, sai kuma lokaci guda ta zabura tana ihu tana kiran Zahra, banda Sunan Zahra bata cewa komai, yayin da gefe guda Mama Kulu ta zama tamkar mahaukaciya tana zaune sai dai kaji tana sunbatu Abu dai gunin ban tausayi. ************************* Momy Laila ne Zaune ta tasa mijin nata da ƴar ta tana kuka bayan ta ɗaukosu daga kano kuma Laila ta faɗa ma Momy nata duk abun da ya faru bata ɓoye mata komai ba. "Yanzu Alhaji wa gari ya waya,? har ku kun isa kuyi ma Allah wayau ku lalata ƴaƴan wasu kuce baza'a lalata naku ba, to gadai ishara nan kun ganin ma idan ku." Hajiiya ta ƙarasa maganar tana share hawayen da ya cika mata ido. "Momy ki yafemun wlh sharrin shaiɗan ne." "Laila kiyi shiru ni banga laifin ki ko ɗaya ba laifin mahaifin ki ne, shi Zina ai bashi ce dole in kayi sai ka biya, sai dai kimun alkawarin bazaki ƙara ba." "Momy wallahi na miki alkawari bazan ƙara bin maza ba." "Allah yasa ƴata, Allah kuma ya shiryar da masu hali irin na mahaifin ki, ban son kowa yaji maganar nan ya zama sirri tsakanin mu domin rufin Asirin mu kinji ɗiyar albarka." Niko nace ai aikin gama ya gama domin mai afkuwa ta afku. ************************* BAYAN WATA TAKWAS Sumayya ce zaune a reception na Asibiti da katon cikin ta a gaba ga kuma robar fitsari kusa da ita, yayin da wata Budurwa wanda bazata wuce sa'ar ta ba ita ma tana zaune kusa da ita wanda kallo ɗaya zaki ma fuskar ta zai isar miki da sakon dake cikin wata tsoka da ke ƙirjin ta wato zuciya, inda tsantsar baƙin ciki da damuwa suka samu gurbin zama a zagayayyen kyakkyawar fuskar ta, wanda hakan bai hanasu yin hira da Sumayya ba jefi jefi, ba kowa bace Matashiyar Budurwar face Laila wanda bayan wani ɗan lokaci ta fahimci cewa lallai akwai bakon yanayi da ya shiga rayuwar ta wanda yake isar mata da saƙon cewa tana ɗauke da juna biyu, tabbas ranar da hakan ta faru sun shiga tashin hankali matuƙa ita da iyayen ta yayin da Mahaifin ta yayi kuka yayi da na sanin da bai da Anfani, yaji irin yanda iyayen yaran da yake batawa sukaji. "Sannun ku bayin Allah shin Doctor ta fara ganin marasa lafiya ne kafin masu ciki."? Cewar wata Matashiyar budurwa wanda zai iya zama su Laila sun girmeta ita ma ɗauke da ɗan cikin ta a gaba da ya zauna yayi mata ɗas a jiki. "Eh kema ki zauna ki jira yama kusa gama ganin marasa lafiyan ai." Cewan Sumayya tana mai gyara roban fitsarin dake jikin ta. "Sannu baiwar Allah ga

Chapter 3 of 4