Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 4
wani watanni Kulu ta samu ciki a wannan lokacin ne kuma wani Hamshakin tsohon ɗan siyasa kuma ɗan kasuwa suka haɗu da Bukar ta sanadiyar aikin wani ginin kamfani da su Bukar sukeyi, shine ya nemi da ya ɗaukeshi aiki ya dunga tuƙashi a Mota yana biyan shi dubu Ashirin, nan da nan kuwa Bukar ya Amince, a haka har Mama kulu ta haifi su Zahra, sosai Malam Bukar yayi farin ciki da samun ƙaruwar da yayi na yara biyu. Lokaci na tafiya shekaru sun tafi har ta kai su Zahra sun kammala Secondry school a inda nan ne kuma halin kowacce a cikin su ya fito, ita Zahra ta kasance nutsattsiya gata ba ruwan ta da rayuwar karya, saɓanin ƴar uwar tata da ta kasance ita tun suna Makaranta bata hulɗa ƴaran talakawa, kasancewar Alhajin da mahaifin su ke ma aiki ya ɗauki nauyin karatun su shiyasa tun daga primary har secondry na kuɗi sukayi, hakan yasa Idon Sumayya ya buɗe tun suna secondry duk da ƴar uwar ta da mahaifin ta suna iya ƙoƙarin su, yayin da gefe guda kuma mahaifiyar tasu ke ruguza komai domin ita dai mace ce mai son Abun duniya da rashin godiyar Allah ga hange-hange duk da bata cika nuna hakan a fili ba sai ita da Sumayya don cewa takeyi ita ce tayo halin ta. shiyasa so tari takan nuna banbanci tsakanin su, tun abun bai damun Zahra har ya fara damun ta. Bayan sun samu gurbin karatu ne a jami'ar Jaha dake kaduna Sumayya ta haɗu da su Shamsiyya, Surayya, Laila hakan yasa idon ta ya ƙara buɗewa sosai duk da wani Abun tana shakkan ƴar uwar tata don in har Zahra tayi fushi to hankalin Sumayya in yayi dubu ya tashi kenan. CIGABAN LABARI.. Suna zuwa suka tarar har Malamin ya shiga Ajin, tsayawa sukayi a bakin kofar Ajin suna tunanin yanda zasuyi su shiga. "Kin san dai Malamin nan bazai taɓa bari mu shiga ba kawai kizo muje mu samu guri mu zauna ma shiga darasi na gaba. Cewar Sumayya tana jan hannun ƴar uwar ta ta, suka je gurin da aka tanada don zaman ɗalibai suka zauna, kwata-kwata Zahra bata ji daɗi ba sai dai ba yarda zatayi shiyasa ta biyema ƴar uwar ta ta. Ita ko Sumayya ɗauko ƴar Vivo ta tayi ta cigaba da chat da wani sabon Saurayi da tayi jiya a facebook sunan shi Ahmad Sardauna irin ƴan ayi soyayyar media a hure ma ƴammata kunne ba Auren su zasuyi ba, duk group ɗin su ɗaya da su Saifullah, Mansir. Ahmad sai tsara Sumayya yakeyi da ƙarya irin na samarin media mussaman ƴan facebook, ita ko sai shiga takeyi tana jin ta a sama ita tayi sabon saurayi. "Baby Sumy yane,? dama kina nan na rabu da ganin ki kwana biyu, jiya na gama tanbayar Hanny love ke." Sai da Sumayya ta wani juya idanu sannan tace mai, "Wallahi Bashow ina nan, kwana biyu meye labari ne.? "Kedai bari kawai fatan kin siya naki Abayar ko,? don kin san wannan Sallah fa wankar Abaya za'ayi, mu samari muna nan mun baza ido muga na kanti muga na gwanjo." Ya ƙarasa maganar yana yarfar da hannu irin yanda gayu keyi. "Ai in faɗa maka Bashow mu namu Abayar ta daɗe da isowa wanda Daddyn mu yayi mana order ko ƴar uwa.? "Eh haka ne haka ne." Zarah ta faɗi maganar a daburce Alamun maganar ƴar uwar tata tazo mata a bazata. Bayan sun tashi makaranta karfe huɗu na yamma, sun fito baki gate ɗin makaranta, dun daɗe suna jiran abun hawa basu samu ba ga yamma na ƙarayi. Har sun cire ran samun Abun hawan sun ɗan fara tafiya a ƙasa don su rage tafiya, wata dalleliyar mota ce ta tsaya a kusa dasu, duk da hankalin Zahra bashi a kan Motar Amma ita Sumayya gaba ɗaya hankalin ta na ga motar ne. A hankali na cikin Motar ya sauke glass ɗin Motar haɗi da musu sallama. Inda gaba ɗaya jikin Zahra rawa ya keyi saboda tun da take bata taɓa ganin lafiyayyan mota irin wannan ba, Sumayya kuwa Amsa sallamar tayi haɗi da tsayawa, yayin da Zahra ke ƙoƙarin jan ta su tafi. "Haba ƴammata ya kamata ku saurare ni tun ɗazu nake ta binku kuma da Alamu ya nuna makaranta ku ka fito, bai kamata manyan yara kamar ku suna tafiya a ƙasa ba, in ba damuwa ku shiga in sauke ku." "A'a Mun gode ka barshh kawai." Cewar Zahra da ta ƙara ruƙo hannun ƴar uwar ta ta da take neman fisge hannun ta daga nata. "Haba ƴammata mai kyau kamar ki bai kamata tana shan rana ba, don Allah ku shigo Allah ai nace, ba siyar daku zanyi ba fa." "Ƴar uwa rabin rai kiyi haƙuri mu shiga, kinga yamma tayi gashi bamu samu abun hawa ba muyi addu'a mu shiga ba abun da zai samemu da yardar Allah." "Shikenan ƴar uwa tun da kin dage mu hau mu hau Allah ya tsaremu." "Yauwa Rabin rai na haka nake so. ta ƙarasa faɗar hakan suna nufan gurin motar Mutumin. Suna isa Sumayya ta shige gaba yayin da Zahra ta shiga baya, nan da nan hira ta ɓarke tsakanin Summaya da Zubair, inda nan da nan Zubair ya fahimci wacece Sumayya, kuma yayi farin ciki da haka, don zai aiwatar da ƙudirin shi cikin Sauki.✍️✍️ YANZU WASAN YA FARA🤣🤣🤓🤓 KU KASANCE DA SARAUNIYAR KANAWA👸 SANADIN ABAYAR SALLAH👗👗👗 TARE DA ALKALAMIN ✍️ ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU (sarauniyar kanawa) ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ *Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.* WANNAN PAGE ƊIN NAKI NE MASOYIYA HUMAIRATY DA FATAN KINYI SALLAH LAFIYA🥰🥰🥰🥰SON SO XAHEEESHATY. Page 4 BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM KADUNA Sosai Zahra taji haushin inda ƴar uwar tata take ta Zuba kamar wata mare aji. Bayan sun isa gida ne Zahra ta fice ta shige gida abun ta, yayin da Sumayya ta cigaba da zama tamkar motar Uban ta. Bayan sun gama hiran da zasuyi ne ta fito daga motar tanajin kan ta cikin farin ciki, tabbas burin ta zai cika domin da alama wannan mutumin bai san darajar kuɗi ba, don ita tunda take ba ta taɓa riƙe kuɗi kaman wanda Zubair ya bata ba, haka ta shiga cikin gida da sallamar ta haɗi da kiran Maman su. "Mama kulu !Mama kulu ! kizo kiga wani abun farin ciki. Ta ƙarasa maganar tana nufan ɗakin Mamar tasu. Yayin da Mama kulu ta fito da sauri suka haɗu da ƴar tata tana shirin shiga ɗakin na ta. "Yauwa Mama zo kiji wani abun farin ciki yau munyi kuɗi, mun haɗu da wani hamshaƙin mai kuɗi, Amma sai dai ba ni yake so ba fa Ƴar uwa yake so Amma ita da kyar ta Amince saboda kin san halin ta, Kinga kuɗin da ya bani fa." Ta ƙarasa maganar tana nuna ma uwar tasu kuɗin da ya bata. Tuni Mama kulu ta ruɗe kasancewar ta dama masoyiya kuɗi. "Aiko ya zama dole ta Amince don ba zatayi mana baƙinciki ba ehe." Mama Kulu ta faɗa tana miƙewa da kuɗin hannun ta, ta nufi ɗakin su Zahra. Inda Zahra tana ciki tana jin duk wani tattaunawar da sukeyi, tana jinjina son kuɗi irin na ƴar uwar ta ta da mahaifiyar tasu, gaskiya basuyi dacen mahaifiya ba, ita kaɗai take wannan tunanin har bata san lokacin da Mahaifiyar tasu ta shigo ba, kawai taji maganar ta ne. "ke Zahra tashi ki zauna ina son magana dake." "To Mama kulu." Ta ƙarasa maganar tana zama ta fuskanci mahaifiyar tata. "yauwa ƴar albarka, kinga wanda ya kawo ku gida da kuka dawo makaranta.? "Eh Mama kulu." "yauwa to shine yace yana son ki, kuma da Aure yake son ki, shiyasa nake so ki bani haɗin kai mu samu mu tatseshi sosai tunda yace shi da gaske yazo ba da wasa ba bayan sallah zai turo iyayen shi, to kinga kafin lokacin ko miliyan ɗaya muka samu ai mun rage koh.? "Mama miliyan ɗaya fa kikace tabdijam, yaza'ayi ma daga ganin mutum baku san halayyar shi ba kuyi na'am dashi haka, to ni gaskiya ban son shi kuma bazan Aure shi ba eheee, kuma wallahi kwaɗayi mabuɗin wahala nidai ba ruwa na, kuma baba Bukar ɗin zai dawo sai na faɗa mishi." Ta ƙarasa maganar tana juya ma mahaifiyar tasu baya ta kwan ta. ************************* "Abokina lafiya wai na ganka a firgice.? "Uhmmm ka bari kawai Abdullahi, wallahi Maman Ilham ta sani a gaba sai na siya mata Abaya gashi yanzu watan mu uku ba albashi, ga ɗan shagon da nake juya kuɗin an tashe mu a kasuwan sai dai buga-buga kadai san halin da nake ciki, wallahi yanzu har tunanin shiga gida nakeyi." Muntasir ya ƙarasa maganar tashi kamar zai yi kuka, saboda tsaban damuwar da yake ciki. "Innalillahi wa'innah ilaihirraji'un, kenan ita ma Hafsat ta shiga sahun kururuwar shaiɗan ɗin ne na ABAYA CHALENGE ɗin, ina ganin ta mai hankali da natsuwa, yanzu dai ka tashi muje in sameta ƙila a samu maslaha." "To Abokina Allah yasa ta saurare mu domin tayi nisa bata jin kira fa." "Insha Allah ma zata saurare mu Aboki taso muje. ************************* KANO Alhaji ne zaune a Offishin shi suna hira da wani abokin shi da ya kawo mai ziyara. "Ina faɗa maka Alhaji wannan yarinyar da muke tare ƴar shila ce, ta haɗu iya haɗuwa fa komai yaji, gata ƙaramar yarinya don da alamu ya nuna nunanniya ce kuma ba wanda ya fara taɓawa ni zan bare ta fa." Alhaji ya ƙarasa maganar suna tafawa da abokin shi, "daɗi na da kai Alhaji baka da girma sai na jikin ka, wato ƴar shila, kaima fa kana da ƴan shilolin a gida baka tunanin wani ya latsa kamar inda kake latsawa.? "Kaga Alhaji tsalha dakata,! ƴaƴana bazasu taɓa aikata haka ba kasan irin tsaron da nake basu kuwa,? kuma da kake faɗin haka ai ba dole na musu ba duk yarinyar da zanyi mu'amula da ita da Amincewar ta ehe, kuma laifin iyayen su ne da suka barsu sakaka ba kwaɓo, taya suna da balagaggiyar yarinya su bar ta da wayar zamani ta kai sha biyu ko ɗaya na dare tana chat ba tare da sun tuhumeta ba, kuma basu tsare mata matsalolin ta na rayuwa ba kaga dole zata roƙi wani muku a shirye muke da karɓan buƙatun kowacce yarinya indai zata bamu haɗin kai ai shikenan, in kanaji ana Alhazawan Mediya da Late comer to mune nan." Alhaji ya ƙarasa maganar shi yana wani dariya irin na shakiyan yan duniyar nan. "Lallai ne Alhaji Mudi kayi nisa bakajin kira Allah ya shirye ka, nidai ina baka shawara ka canja hali ni na tafi sai anjima." "To Alhaji Tsalha naji nagode a gaida gida harka kuwa yanzu muka fara, sai dai in har ƴammata bazasu buɗe mana kafa ba sai mun kwasa ehe.!" ************************* Zaune take ta ɗora kafa ɗaya kan ɗaya, sallama sukeyi Amma bata ɗaga kai ta kallesu ba balle su sa ran zata Amsa musu. Har suka shigo cikin ɗakin suka samama kan su matsuguni suka zauna. "Hafsat ba kiga Abdullahi bane hala."? "Na ganshi mana sai akayi yaya to." Ta faɗi tana girgiza kafa tana taunar chewgum. "Dama zakuyi magana ne da shi." "Au zuwa kayi ka kwaso mun shi,? to an faɗa maka ji zanyi ai, ai nayi nisa bana jin kira fa saboda haka ku tashi ku ɗauki zummar rayuwar ku ku barmun ɗakina tun kafin in muku hauka wallahi, don ka san halina Muntasir, kuma kaji da kyau karka sake ka ƙara shigowa ɗakin nan in har ba da Abayar sallah ta ba. ************************* "In har kinyi Alƙawarin zaki cikamun Alƙawari ranar sallah, ni kuma na miki Alkawarin Abaya kala biyu-biyu keda ƴar uwar ki." "Karka damu na maka alkawari insha Allah zan cika maka alkawari ranar sallah don ƴar uwa ta tanajin magana ta sosai in har na nuna mata bacin rai na akan abu ko bata so sai tayi shi." "Yauwa sarauniyar kyawawa, gobe zan zo in ɗaukeki muje Algazzaru plaza ki zaɓo muku rigunar." "Da gaske !? kai nayi matuƙar farin ciki." Ta ƙarasa maganar tana katse wayar ta tashi ta fara rawa tana juyi, yayin da Zahra kawai ta tsaya tana kallon ta tana mamakin irin halin ƴar uwar tata.✍️✍️✍️ SARAUNIYAR KANAWA👸👸🥰🥰 SANADIN ABAYAR SALLAH👗👗👗 TARE DA ALKALAMIN ✍️ ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU (sarauniyar kanawa) ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ *Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.* BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM PAGE 5 KADUNA Yau ta kama ranar jumma'ar ƙarshe a watan Ramadan, inda Musulmin duniya suka fara kewar watan yayin da Malamai suke ta ƙoƙarin rufe tafsir ɗin su bayan An sauka masallacin jumma'at. Zahra ne da Sumayya suke ta shirin tafiya gurin rufe tafsir ɗin babban masallacin dake unguwar su sun sha hijaban su har ƙasa da niƙab, suka fito riƙe da hannun juna sai da suka leƙa ɗakin Mama kulu don suyi mata sallama sannan suka wuce suka tafi. Babban masallaci ne ya cika yayi maƙil da jama'a, ƙarfe 1:30pm na rana an idar da sallar jumma'a an fara hada-hadan rufe tafsir inda ake gabatar ma da malam tanbayoyi yana Amsawa. "Allah ya ƙara ma malam lafiya da nisan kwana, game da tanbayar da yazo kwanaki akan maganar Abaya da ƴan mata da samari har ma da wasu daga cikin matan Aure ake ta cecekuce a kanshi mukeso mallam ya jawo hankalin iyayen yara akai." "To Alhamdulillah kwanaki an kawo irin wannan makamanciyar tanbayar nace a mun uzuri saboda ƙarancin lokaci, to yanzu insha Allah zanyi fashin baƙi akan maganar, da farko dai sai in ce Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un tabbas Al'ummar musulmi na cikin wani hali, gaba ɗaya an gurbata tunanin matasan mu an juya musu hankalin su akan abunda bai dace ba, yanzu a halin da muke ciki na rashin tsaro da kwanciyar hankali har matasan mu sun sami damar da zasu shagaltu da maganar sutura,? Tabbas Abaya shiga ce ta musulunci wanda ya samu Asali daga larabawa, to Amma wani hanzari ba gudu ba, shi wannan Abayar da ake magana ya sha bam-bam da na musuluncin don riga ce mai fidda duk wani komaɗa da sura na ƴa mace saɓanin na musulunci wanda larabawa suke sawa yalwatacce ne shi kuma mai duhu ne yana rufe duk wani Al'aura dake jikin mace, saboda haka ni zan iya cewa bai kamata kina ƴar musulmai kisa shi ba tare da babban mayafi ko hijabi ba, game da raɗe-raɗin da naji cewa har wasu na iƙrarin bada ƙimar su da martabarsu saboda Abaya, shin ƴar uwa kin san darajar kan ki kuwa,? shin kin san cewa in har kika rasa martabar ki kin rasa kenan har abada, ba'a siyan shi da kuɗi Amma saboda kin zama ballagaza takan abun duniya kike neman saida martabarki wanda in kin rasa kin rasa kenan har abada, ƙalubale gareku iyayen yara ku kula da ƴaƴan ku Amanace Allah ya baku kuma zai tanbaye ku ranar gobe ƙiyama." Haka dai malam ya dunga kira da jan hankali har aka gama aka rufe tafsir kowa ka gani jikin shi yayi sanyi banda Sumayya da ita wa'azin ma ba saurare takeyi ba ta na can tana chat da su Shamsy tana basu labarin Zubair suna ƙara zugata suna ɗorata kan hanya. ASABAR 10/5/2021 KARFE 4:00pm Zahra ne ta fito sanye da maroon ɗin material tana ma Mama kulu sallamar sai ta dawo. "yauwa Zahra karki kai dare kin san halin mahaifin ku kar ya dawo bai sameki a gida ba ya dunga faɗan nan nashi da ya saba." "Insha Allah Mama kulu sai na dawo." Ta ƙarasa maganar tana ficewa. "Summy! Summy! shiga muje koh." "To Alhaji." Sun isa plaza haka Sumayya ta zaɓan musu rantsattsun Abaya kala bibbiyu banda takalma da turaruka da sauran kayan kyale-kyale, Sumayya gaba ɗaya ta ruɗe saboda ɓarin kuɗin da Zubair ya dunga mata, haka ya dawo da ita da kaya niƙi-niƙi suka zo suka baje a tsakar gida, yayin da Zahra take gefe tana duba takardun ta kasancewar bayan sallah suna da jarabawa. "wai ƴar uwa baki ga kayan mu bane muma zamu shigo yayi zamu kece raini."? "Allah ya kyauta muku, nidai kullum bazan fasa faɗa muku kuji tsoron Allah ba, nuna son Abun duniya yana kai mutum ga halaka nidai ba ruwa na indai don ni yake wannan hidiman wallahi ban son shi." Ta ƙarasa maganar tana shigewa ɗaki. Malam Bukar ne yayi sallama da sauri Summayya ta kwashe kayan ta shige ɗaki dasu. ************************* "Maman Amir in faɗa miki ai na taso Muntasir gaba, jiya fa har abokin shi ya ɗauko mun, ni jiki na ya fara sanyi anya bazan haƙura ba kawai.? "Taɓ!! ki haƙura ba kika ce Maman Ilham zako kiji kunya wallahi, don jiya naji Maman Yusra tana cewa mijin ta ya siyo mata nata Abayar, kinga kenan kin gama kuri sai sallah yazo kiji kunya nidai kinga tafiya ta." "A'a Maman Amir tsaya kiji, yanzu ya kikeso ayi.? "Ai hakana nan zaki ƙara buɗe mai wuta duk yanda zaiyi sai ya yi ya siyo miki." ************************* KANO "Alhaji magana fa nakeyi ka mun shiru." "Hajiya kinga Abaya ne ba zan basu ba dole ne sai sun shiga yayin.? "Haka ma zakace Amma kaje ka ba kadangarun bariki ai, wannan abu fa ba siya zakayi ba shago kake dashi ɗauka kawai zasuyi kace ba haka ba." "Naji bazan bayar ba." Ya ƙarasa maganar yana saɓa malum-malum ɗinshi ya fice. SARAUNIYAR KANAWA🥰🥰🥰🥰🥰👸👸👸 SANADIN ABAYAR SALLAH👗👗👗 TARE DA ALKALAMIN ✍️ ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU (sarauniyar kanawa) ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ *Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.* BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM PAGE 6 12/5/2021 RANAR LARABA MISALIN KARFE 8:00PM NA DARE "Assalamu Alaikum." "Wasalam Alaikum, waye? shigo mana." Maman Maryam ce ta shiga ɗakin Hafsat ta samu guri ta zauna sannan tace, "Hafsat nazo gurin ki ne." "To Maman Maryam lafiya kuwa.? "Lafiya lau akwai ƴar shawara da nake son dama in baki ne." "To ina jinki kuma ina sauraran ki." "Game da halin da kika sa mijin ki a ciki ne, shin kin san adadin tsinuwar mala'iku akan matar da take ɗaga ma mijin ta hankali kuwa, wallahi mazajen mu na matuƙar ƙoƙari, ki kasance mai godiya ga duk abun da mijin ki yayi miki, in har kina ɗaukar zugar mutanen duniya tabbas zakiyi da na sani, ƴan mata nawa ne yanzu suke gaban iyayen su san rasa mazajen Aure Amma ke kin samu kina ƙoƙarin ki kashe naki, to wallahi ki rufama kanki Asiri ki lallaɓa mijin ki ku zauna lafiya, balle mijin ki mutumin kirki ga iya riƙe gida, wallahi in har kikayi sakaci kuka rabu koh to kinyi babban Asara ni kuma wallahi a ranar zan bashi Auren ƴata Maryama." "Kinga dakata Maman Maryam! dama munafunci da gulma ya kawo ki, dama tun ba yau ba nake ganin take-taken ki keda ƴar ki to wallahi mijina yafi ƙarfin ki, kuma ki tashi ki barmun ɗaki na, ko yau Aure na ya mutu nasan sai maza ɗari sunyi rububi na." "Shikenan dama wanda yayi nisa baya jin kira ai." Maman Maryam ta ƙarasa maganar ta tana ficewa daga ɗakin. Duk abun da ke faruwa Muntasir na tsaye bakin kofa yana ji duk abun da suke tattaunawa, bayan wucewar ta ya shiga ɗakin da sallamar shi hannun shi riƙe da baƙar leda. Da sauri Hafsat ta taso ta iso gurin shi, "Sannu da zuwa Baban Ilham saƙon nawa ne ya iso.? "Zauna Hafsat Muyi magana." Samun guri tayi ta zauna kamar abun Arziki tace "ina jinka." "Ga wannan leshi ne da da kayan ilham don Allah kiyi haƙuri ki ƙarɓa insha Allah ko bayan haka ne in Allah ya bani kuɗi sai in siya miki Abaya...." "Dakata kaji ko malam." Ko bari ba tayi ya ƙarasa magamar ba ta dakatar dashi haɗi da ɗaukar ledar ta jefa mishi a fuska. "Wallahi bazan sa ba, kuma ka tabbatar da cewar ko sata zakayi sai ka siyo Abayar nan." Ta ƙarasa maganar tana shigewa cikin bedroom ɗin su. Jiki ba kwari Muntasir ya tattara kayan ya mayar a leda ya fita jiki a sanyaye. ************************* KANO "Baby zan tura miki ƙuɗi ki ƙara gyaramun kan ki da ƙyau in da zan jiki zam-zam fa baby." Alhaji ya ƙarasa maganar yana lashe baki haɗi da shafa ƙaton cikin shi da yake gaba. "my Alhaji kar ka damu nidai kawai inji kuɗi za kaga aiki." Cewar Laila da take kwance kan makeken gadon ta. ************************* KADUNA Karfe 8:00pm Mama kulu ce suke zaune ita da Sumayya suna lissafin kuɗin da suka samu daga haɗuwar su da Zubair zuwa yanzu, ɓarin kuɗin da yake musu ya wuce na hankali. Zahra ce ta shigo ɗakin Mama Kulu haɗe da sallamar ta. "Mama Kulu Abun da kukeyi bana jin daɗi kwata-kwata kuɗi ya rufe muku ido ni ban ma yarda da mutumin nan ba, sai cin mai kuɗi kukeyi kuji tsoron Allah Sumayya ki daina biye ma Mama zata kaiki ta baro, tabbas bamuyi dacen uwa ta gari ba kuma kin ci Amanar Baba Bukar, kuma kin ci Amanar Ubangiji kuma bazan fasa faɗa muku gaskiya ba." "Ke Zahra ni kike faɗa ma haka,? to kiyi abun da zakiyi mara rabo kawai Arziƙi na kiran ki tsiya na kaɗaki to baki isa kimun baƙin ciki ba ehee.!" ************************* WASHE GARI 13/5/2021 DAI DAI DA 1/SHAWAL/1442 Ranar da ta kama ranar sallah, ranar da Musalmai na duniya ke murnar kammala Azimin watan Ramadan, in da kowa ka gani yana hada hadan tafiya sallar idi ne. "wallahi sai ka siyo shi ko baka ba yin salla cikin kwanciyar hankali." Cewar Hafsat da ta cakume wuyar Muntasir a tsakar gida, tana mai tijara, Matan gida sai bata baki akeyi Amma kamar ana zugata. Ran Muntasir gaba ɗaya ya ɓaci in da yana buɗe baki kawai cewa yayi "Hafsat kije gidan ku na sake ki saki biyu." Yana gama faɗin haka ya fincike rigar shi ya fice. Maman Maryam ta bishi ta ruƙo rigar shi ta tsaidashi "Matan gidan nan ku shaida ni Halimatu na ba Muntasir ƴa ta Maryam kuma ko ba Akwati ya kawo sadaki a ɗaura yau in an sauka idi." Aiko gaba

Chapter 2 of 4