An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
SANADIN ABAYAR SALLAH👗👗👗
TARE DA ALKALAMIN
✍️
ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU
(sarauniyar kanawa)
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ
*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*
INA MA ƊAUKACIN AL'UMMAR MUSULMI BARKA DA SALLAH ALLAH YA AMSHI IBADUN MU🥰🥰🥰.
Page 1
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
KADUNA STATE UNIVERSITY.
RANAR LITININ.
KARFE ƊAYA DA RABI NA RANA.
✍️Makaranta ce da ta tara ɗalibai Maza da Mata, a kowanne rukuni kama daga kan Samari, ƴan mata, har ma da Matan Aure.
Tafe ta ke tamkar zata faɗi saboda gajiya, ga dukkan Alamu ta fito daga ɗakin karatu ne, kuma a yanayin ta tamkar wani abu take nema don sai kalle-kalle takeyi.
Gurin da aka tanadar don hutawar ɗalibai ta nufa da saurin ta Alamu ta hango wacce take nema a gurin.
"Haba ƴar uwa kin san tsawon lokacin da na ɗauka ina neman ki a makarantar nan kuwa.? Ta ƙarasa maganar ta tamkar zatayi kuka. Ita ko wacce ta kira da ƴar uwa bata ma san tana maganar ba, don hankalin ta yana can kan hiran da sukeyi da ƙawayen ta, wanda in ka kalle su zaka san cewa lallai manyan Yara ne tun daga yanayin shigan su har irin wayar dake hannun su saɓanin ita wacce aka kira da ƴar uwar wata ƙaramar Atamfa ce jikin ta da hijab iya gwiwan ta, sai dai gugan da kayan yasha shi ya ɓoye tsufan kayan jikin ta, sai wata ƙaramar tsohuwar Vivo irin ta da ɗin nan a hannun ta.
"Ina faɗa muku Shamsy wallahi in kikaga Abayar nan ko duniya ce, Amma wai kun san da na tambayi kuɗin ta nawa aka ce mun kuwa."?
"Sai kin faɗa Surry."
"Wai dubu Talatin da takwas Amma fa taci kuɗin ta fa, bari kuga hoton Abayar." Ta ƙarisa maganar tana cire key ɗin wayar ta ƙirar Iphone+ ta shiga dubo hotuna tana nuna musu.
"Wowww Surry kalli wanan ya haɗu, kai dole fa wannan sallah muyi wankar Abaya challenge ɗin nan fa."
"Ai ina faɗa muku wannan Sallar in baki wankar Abaya ba ke ba babban yarinya bace, kin san meye,? sai kin ma shiga media kinga inda Ƴan mata ke maganar Abayan nan, nifa ko ta wani hali sai na sa Abayar nan kawai."
Sumy ne ta numfasa tare da cewa "Ni ai sai dai inyi kallo ina Baban mu zai sami kuɗin siya mana Abaya nida ƴar uwa ta."
"kin ji Sumy da wata zance, in da kike da ƙyau ɗin nan sai kinga dama ne bazaki sa Abaya ba."
"Faɗa mata dai Surry, ita kullum ana ɗora ta hanya tana kaucewa in da kika san tafi kowa tsoron Allah a duniya, to bari kiji in faɗa miki ko mu da muke yaran masu kuɗi bamu zauna haka ba balle ke."
"Kinga Surry tashi muje ga ustaziyar ƴar uwar ta nan tazo kafin ta fara faɗa mana Allah yace Annabi yace, bayan kullum sai munje tafsir tunda aka fara Azimi."
"Ahayyyye gaskiyan ki fa kawata." Surry ta faɗa suna tafawa da Shamsy, suka ɗauki jakunkunan su suka kara gaba suna karkaɗa maƙullin motar su.
Zahra ne ta numfasa ta zauna kusa da ƴar uwar ta."Sumayya bazan taɓa dena faɗa miki gaskiya ba akan waɗan nan ƙawayen naki basu dace da ke ba, ki tsaya dai-dai inda Allah ya ajiyeki, kar su kai ki su baro ki kizo kina da na sani, don Allah ki rufamana Asiri nida iyayen mu ki fita harkar waɗanan ƙawayen."
"Wai ke Zahra ina ruwan ki da ni iyehh,! tun yaushe nake faɗa miki ba ruwan ki da ƙawaye na, bazaki gane bane Zahra meyasa Allah bai yi mu masu kuɗi ba laifin me mukayi mishi ya jarabcemu da talauci..."
"Kar kiyi Saɓo Sumayya ki gode ma Allah a haka da kike rainawa kinfi wasu, taso mu tafi gida kin san dai yau Umma tace mu dawo da wuri tana so taje unguwa."
Ta ƙarisa maganar tana mai janyo hanun ƴar uwar ta ta suka kama hanya zuwa bakin makaranta.
Suna fitowa suka samu mai Nafef. "Mallam Hayi zaka kaimu nawa ne.?
"Ku biyun ne.?
"Eh mu biyu ne."
"Ku bada ɗari uku."
"Kayi hakuri mu bada ɗari biyu mana ka taimaka."
"ba damuwa ku hau Allah ya kaimu lafiya."
"Amin ya Allah."
Bayan sunyi tafiya mai ɗan nisa mai Nafef ya kunna Radio, dai dai lokacin da ake tafsir Malamin yana Amsa tambayoyi, mai karanta tanbayar yana cewa "Sako daga Hauwa'u unguwar Rimi, take cewa Mallam wata Masifa ce yanzu ta fito ga ƴan mata akan maganar Abaya har ta kai yanzu duk in ka hau social media kama da Facebook, whatsaap, istagram, twitter duk maganar kenan wanda har ta kai wasu ƴan matan na ikrarin sai da mutuncin su akan shi Abayar, shine muke rokon Mallam akan yayi kira da jan hankali ga ƴan mata da iyayen yara akan wannan batu, nagode."
"Wannan batu sai muce Innalillahi wa'innah Ilaihirraji'un, tabbas wannan magana abun a duba ne Amma saboda karancin lokaci insha Allah zamu ajiye tanbayar ki har zuwa shiri na gaba domin in samu inyi jan hankali da bayani masu kyau akan lamarin."
"kai wannan rayuwa ina zaki damu, yanzu don Allah in banda muma ƴan Nigeria sai a hankali muna fama da matsalar rashin tsaro ga talauci ga sace-sacen mutane da akeyi masu garkuwa da mutane hakan duk bai ishemu ishara ba sai an bullo da wani shirme da shiririta, maimakon mu mai da hankali akan ya zamu sama ma ƙasar mu mafita Amma matasan mu sun tsaya suna wani shirmen banza shirmen wofi wai Abaya kai tir da Allah wadai ga matasan mu wallahi."
"Kaga Mallam mu bamu tambaye ka ba, in kai ba shi ke gabanka ba su shi ke gaban su ina ruwan ka kowa da abun da ya dameshi, ko sunce ma ne basu damu da halin da ƙasar take ciki bane.?
"To Ƴan mata yadai,? kamar wadda take jirace dani daga magana zaki fara faɗamun maganar banza da wofi,ko kema dai kina cikin ƴan Abaya chalenge ɗin ne ƴan wahala baki da gashin wance kice sai kinyi kitson wance abi duniya a sannu dai ehe.
Daidai ya ajiye su a kwanar layin su, yake faɗin ma Zahra haka.
Abun yayi matuƙar ɓata ma Zahra rai a fusace ta fita a keken taje gaban shi tayi mai kallon sama da ƙasa sannan tace mai "Ni Zahra nafi ƙarfin kwaikwayo sai dai a kwaikwaye ni kalle ni da kyau ni ba matsiyaciya bace irin ka kuma banyi kala da yaran talakawa ba balle ka faɗamun ba daɗi mtswwww."
Ta ƙarasa maganar tana jan tsaki ta shige kwanar layin su.
"oh ni Sadeeq yarinya kina fama da guntun talaucin ki kin ɗauki karya kin sama rayuwar ki, don ni a layin nan banga alamun gidan masu hali ba, banza ƴar karya kawai duniya zata bi da ke wallahi.
"don Allah malam kayi haƙuri ga kuɗin ka mun gode.
"karki damu, kinji ki bar kuɗin, don Allah ki dunga ma ƴar uwar ki Nasiha naga alamun kinfita hankali da nutsuwa dama haka Allah yake al'amarin shi."
Yaja keken shi yayi gaba ya bar Zahra a nan kamar zatayi kuka, jiki sanyaye ta juya ta bi bayan ƴar uwar tata.
*************************
Karfe Tara na safe Mata ne suke zaune a tsakar Gida kowa da abun da takeyi, kasancewar
Gida ne irin na haya da ya tara mata sun kai su bakwai. Maman Baby kin san wani Abu kuwa jiya da naje gurin Tafsir naji ana maganar wannan sallar Abaya za'ayi yayi, kin gansu ma na turo a waya ta."
"Don Allah Maman Amir mu gansu, kai masha Allah kuzo ku gani Maman Ilham, Maman Nernah, Maman khairi kuzo fa kuga abun da za'ayi yayi wannan shekarar,kice shigar larabawa za'ayi ni dama kin ganni ina son Abaya wallahi ko ba wai yayi ba tun da shigane irin ta larabawa kuma shigan mutumci yafi a sa ɗan iskan ɗinkin nan matsattsu da akeyi aje idi dashi. cewar Maman baby bayan ta zauna tana ƙoƙarin karɓan wayar Maman Amir.
Dukan su suka bar abun da sukeyi har da wanda ba'a kira ba ma duk sun zo gani.
"kai Masha Allah yanxu nawa ake sayarwa.?
"Ai in faɗa muku daga dubu Sha biyar zuwa sama, ke har na dubu Arba'in akwai.
"Arba'in ! fa kika ce Maman Amir, wai wannan sai ku matan manyan ma'aikata.
"Ban gane ba Maman Baby ko kema sai dai in baki so sawa ba in dai kika ce ma Baban baby kina so.
"Uhmmm ai kaman Baban Ilham ma ya siya ya gama ni bani son ma ƙaramar babban nake so.
"kaji manyan matan gidan mu, uwar gida kuma Amarya a gidan Baban Ilham.
Sai wani fari da ido takeyi tana kara faɗi, suko matan gidan na ƙara zugata.
Maman maryam da take gefe tana ta ɗinkin jakunkunan ita da budurwan ƴar ta Maryam. Ta girgiza kai tana jinjina wauta irin ta Hafsa, ana zugata ta tilasta ma mijin ta yin abun da bai da halin yi.
*************************
Misalin karfe takwas da rabi na dare, Matasa ne suke zaune a wani guri na hutawa lokacin an sha ruwa, don gaban su kayan ciye-ciye ne kala-kala.
"Ɗan gidan Alhaji wai ya beb ɗin nan naka ne da kuka haɗu a Facebook.?
"kai dai bari Ajebo ai in faɗa maka ina chilling a facebook ɗin nan, jiya ma nayi sabuwar Beb fa. ya faɗi yana wani kashe ido irin na ƴan iskan nan.
Gaba ɗayan su Samarin suka kwashe da dariya, "ka san meye ma ta mun alkawarin haɗuwa fa ranar Sallah Amma indai zan siya mata Abaya."
"kai haba dai mutumi na."
"Wallahi kuwa to an faɗa muku niɗin na wasa ne."
"To kai yanzu zaka siya mata Abayan ne.?
"Haba Ajebo kai da kasan waye ni, mai zai hana in siya mata saboda naga alamar zan mori kuɗi na fa hhhh. ya ƙarasa maganar yana dariya.
"kai fa ɗan Air ne wallahi Mutumi na wato ban gishiri in baki manda koh.?
"Ah to da ni Uban ta ne da zan cire kuɗi har dubu talatin da ɗoriya in siya mata Abaya ya tafi a banza kaima ka san bazai yuwu ba."
"Hhhhh sai ɗan Alhaji kana wuta muna binka da fetur.
"Wai Jeey ya maganar Beb ɗin nan naka ne kai ma zaka siya mata Abayar ne.?
"Tab ni ai na gama yayin ta na riga na fanshe kuɗin Iphone ɗina, sau biyu fa muna zubar da ciki, ita kuma wai shashan tana jiran wai dad ɗin ta ya dawo daga London ne ta gabatar da ni a gurin shi, niko nace tana ruwa.
"Kudai wallahi ku ji tsoron Allah kun mai da social media matattara in kun gama da wannan ku samo wannan koh.?
"Eh mana ai duk yarinyar da ta hau tashar kwaɗayi tace zata biye ma samarin social media tana tare da wahala fa, kuma damu zata haɗe eh eh eeeee ! ko ya kuka ce abokai.?
"sosai ma kuwa.✍️✍️
🥰🥰sarauniyar kanawa🥰🥰
SANADIN ABAYAR SALLAH👗👗👗
TARE DA ALKALAMIN
✍️
ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU
(sarauniyar kanawa)
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ
*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*
Page 2
BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
KANO
Misalin karfe sha ɗaya na safe wani hamshaƙin Mutum ne wanda kana ganin shi kasan kuɗi ya zauna mishi, ga wani uban tumbi da ya aje a gaba tamkar mai juna biyu, yana zaune kan kujera a office ɗin shi yana juyi gaban shi kuma computer ce yake daddannawa yana murmushi.
"Baby kin san meye ki faɗi duk abun da kike buƙata duniyar nan zan miki matuƙar kin mun alkawari zaki zo kano da Sallah."
Vedio call Alhaji yakeyi da wata yarinya da a haife zaiyi jika da ita, Amma ita ce Alhaji yake bi Saboda tsaban son zuciya irin na ɗan adam.
Daga ɗayan bangaren laila ce kwance kan makeken gadon ta riƙe da wayar ta ƙirar Infinix hot8 daga ita sai rigar barci, "Amma baby ka tabbatar zaka kama mana haɗaɗɗen safe guri saboda ban son a samu matsala fa, kasan wlh Daddy na ya cika tsanani ne shiyasa." Ta ƙarasa maganar tana wani kashe ido ɗaya haɗi da ɗaga mai gira.
"kai baby na wannan irin fari ai sai kisa Azimi na ya karye fa." ya ƙarisa maganar yana shafo Sanƙon da ke kanshi.
"kai dai bari kawai Baby wai don ma muna Ramadan ne, ai ranar da muka haɗu dole in baka tukuici yadda ya kamata."
Ta ƙarasa maganar cikin kashe murya da wani juyi sai da tasa Alhaji yayi wani miƙa.
"Baby, Baby ai in faɗa miki karki samu damuwa Abayar ki tana hanya nayo order kaya daga Dubai ana kawowa ke zaki fara zaɓa kafin ya isa shago."
"Wayyo daɗi kashe Laila, ai in faɗa maka Alhaji akan Abayar nan komai zan iya yi maka, don kawai na fita kunyar ƙawaye na, kasan na musu ƙaryan cewa Daddy na ya bada order daga Dubai fa, kuma kasan wallahi duk kuɗin Daddy da kake gani bazai iya siyamun Abayar nan ba fa.
"Baby karki damu ai kina dani ba Abaya ba ko abun da yafi Abaya ce zan siya miki."
A ranshi ko yana kissifa yanda zai mori kuɗin Abayar shi.
*************************
KADUNA
"Yauwa Muntasir dama ina son zamuyi magana da kai."
"To in banda abinki Hafsat kya bari in kammala buɗa baki ko sai muyi magana, Amma yanzu hankali na zai rabu biyu ne ai."
"shikenan Baban Ilham rabin raina ka kammala ina jiran ka.
Ta ƙarasa maganar cikin shagwaba da karyar da murya.
Tari ne ya sarƙe Muntasir saboda abun da matar shi tayi yayi bala'in bashi dariya, shi dai yasan rabon da Maman Ilham tayi mai wannan muryan tun tana Amarya, tabbas yau da abun da take buƙata a gurin shi.
Bayan ya kammala cin Abincin ne ya fuskance ta yace, "ina jin ki Hafsat."
"Dama ina son in nuna ma wani Abu ne." Ta faɗi maganar tana miƙa mai wayar Maman Amir da ta karbo don ta nuna mai hoton Abayar.
Karɓar wayar yayi don yaga mai take nuna mai a wayar.
"Yauwa Baban Ilham kalan wannan rigar nake so ka siyamun na Sallah, kasan su za'ayi yayi fa."
"To yanzu wannan rigar nawa Hafsat."?
Muntasir ya faɗa yana kallon matar ta shi.
"uhmm uhmmm dama ance dubu Arba'in ce kuɗin ta."
Hafsat ta faɗa cikin fargaban kar Muntasir yace bazai siya mata ba.
"Amma kina da hankali kuwa Hafsat,? ina naga kuɗin da zan siya miki wannan rigar, kin san dai ni Malamin Makaranta ce, Makarantar ma ƙaramar makaranta na primary, kwata-kwata nawa ne Albashi na a wata, kuma kina ganin halin da ma'aikata a jihar nan suke ciki, mussaman ma Malaman makaranta, ga rashin biyan Albashi akan lokaci sai mu shiga wani watan ma ya raba ba'a biyamu ba, ga biyan kuɗin haya ga kuɗin makarantar Ilham ga hidiman Abinci, duk a cikin Albashin, sannan kice in siya miki suturar dubu Arba'in Hafsat.
"Haba Hafsat ki dunga tausayamun mana Hafsat Sata kike so inyi ko mene."?
"To wallahi baka isa ba ! sai ka siyamun in kuma ba haka ba, ba kai ba zaman lafiya a gidan nan, aikin banza kawai in gama kuri a tsakar gida in ce zaka siyamun shine kake neman watsamun ƙasa a ido, to wallahi sai ka siyamun ko sata zakayi."
Ta ƙarasa maganar tana ficewa daga ɗakin ta nufi ɗakin Maman Amir ko sallama ba tayi ba ta kutsa kai.
"Lafiya Maman Ilham na ganki haka.?
"Ina fa lafiya Muntasir naso yamun rashin Mutunci yace bazai siyamun Abaya ba, yajamun jin kunya a gurin matan gida."
"Tab wallahi kina ruwa kuwa, ni kinga Baban Amir har ya bada sakon nawa a siyomun a kano, wallahi karki yarda Mazan nan in kayi musu lakwa-lakwa sai su raina ka, haka da Baban Amir ya fara mun da na buɗe mai wuta tuni muka dai-dai ta komai nake so yana siyamun.
"Au abun hakane to wallahi ni da shi ne sai ko ya siyo Abayar nan."
Ta ƙarasa maganar tana fita daga ɗakin zuwa ɗakin ta.
*************************
Kasancewar lokaci ne na zafi ga rashin samun wadataccen Wutan Nepa da ake fama dashi, yasa Su Zahra sukayi shimfiɗa a ɗan karamin tsakar gidan su suna shan iska, kafin dare yayi nisa su koma ɗaki don yin barci.
Ƙur'ani ne a hannun Zahra tana dubawa yayin da Sumayya kuma take daddana ƴar Vivo ɗin ta tana chat a whatsaap, a group ɗin su na fitattun ƴan mata masu aji, kusan rabin hirar dai akan Abaya ce da ranar Sallah yanda kowa zata sa Abayar ta tayi hoto ta tura a group a tantance wacce tafi cinye wankar sai a haɗa mata kyauta mai tsoka aje har gida a kai ma ta.
"Laila na typing." cewar Hanny.
"ke Laila babbar yarinya wai mai kike runutawa ne tun ɗazu.?
"ku dai bari kawai ai in baku labari Abaya ta ta iso, bari in turo muku hoton Abayar ku gani."
Ba daɗewa ta turo da hoton Abayar.
"kai Laila babban yarinya wannan Abayar ta haɗu har na hangoki ranar Sallah nan."
Gaba ɗayan su sukayi shewa group ya hargitse da hayaniya da surutu.
Yayin da Sumayya ta ga Abayar Laila babban yarinya sai da ta tashi zaune.
"ƴar uwa zo kiga wata Abaya dai kai wallahi ya haɗu sosai."
Dai dai lokacin da Malam Bukar yayi sallama ya shigo gidan.
Da sauri Sumayya ta ɓoye wayar ta saboda dama Baban nasu bai san tana da waya ba.✍️✍️✍️
🥰🥰🥰sarauniyar kanawa🥰🥰🥰
SANADIN ABAYAR SALLAH👗👗👗
TARE DA ALKALAMIN
✍️
ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU
(sarauniyar kanawa)
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ
*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*
PAGE 3
BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
KADUNA
Washe gari ya kama ranar Talata, Su Zahra ne suke ta sauri saboda suna da Aji karfe Takwas da rabi gashi Malamin in har ya shiga Aji baya bari a shiga.
Maman su ne ta fito daga ɗakin ta, tana kalon yaran nata, "Sumayya wai me kukeyi ne a ɗakin har yanzu baku gama shiryawa ba sai lokaci ya tafi."?
"Wallahi Mama Sumayya ce ta tsaya kwalliyar nan tata shine fa har yanzu bata kammala ba."
"kaji sharri ƴar uwa ke da kika shiga wanka kika kusa rabin Awa fa."
Ta faɗa tana harar ƴar uwar tata cikin sigar wasa.
"Nidai naji tashi muje."
Zahra ta faɗa tana jawo hannun ƴar uwar tata suka fito suna dariya, sunyi matuƙar kyau sosai, kasancewar su irin chocolate colour ɗin nan, sai dai Zahra nada dogon fuska ita kuma Sumayya tana da kumatu Amma idanuwan su da yanayin shafe ɗin bakin su iri ɗaya ne, sai dai Zahra tafi Sumayya manyan ido.
Sun sanya wani Material mai kyau irin mai haɗe da gyalen nan, suna sanye da flat ɗin takalmi mai kyau, duk da kasancewar su talakawa hakan bai sa iyayen nasu sun gaza ba gurin samar ma da yaran kayayyakin buƙata musamman Mahaifin su.
"Mama zamu tafi sai mun dawo."
"To ƴan Albarka kundai ci tuwon ko.?
"Eh mun ci Mama." cewar Sumayya.
"Wallahi Mama ƴar uwa bata wani ci da yawa ba.
"To ai dama na sani, ku ƙarbi kuɗin Motar ku sai kun dawo Allah ya bada sa'a."
"To Mama sai mun dawo.
WAYE MALAM BUKAR.?
Asalin shi ɗan garin Maiduguri ne, wani ƙauye da ake kira Sambisa saboda halin da ƙasar mu yake ciki na rashin tsaro yasa duk Ahalin shi suka tarwatse sanadiyar dawowan shi kaduna da zama kenan.
Bayan zuwan shi kaduna ne ya haɗu da Mahaifin Mama Kulu shi ɗin aikin leburanci yakeyi, bayan ɗan zaman da sukayi da Audu Lebura yana binshi suna zuwa duk wani aiki da ya samu, har Audu ya yarda da Bukar ya bashi Auren ƴar shi Hauwa wanda suke ce mata Kulu.
Bayan Auren su da