karasa maganar tana kara kai masa kiss ta fita tana sakin wani irin ƙayataccen murmushi.
"Yes, komai ya kusa tafiya daidai, burina zai cika Soon To Be Mrs Adeel Muhammad Rohaan (Gimbiya)"
Ta fada fuska fal farinciki.
Ci gaba da aikinsa ya yi hankalinsa kwance.
Adnan ne ya shigo dakin yana fadin, "An kammala komai fa kan Baban Zainab har ma an fidda shi India komai da ake bukata ina tunanin an samu."
"Okay." Kawai Yareema ya amsa da shi.
Adnan ya kara fadin, "Ina take ne? Ta zo nan kuwa? Amaryar tamu." Ya karasa maganar cikin sigar tsokana.
Da harara Yareema ya bisa da shi yana, "Mahaukaciya dai." Daga nan ya yi shiru ya ci gaba da abun da ke gabansa.
Dariya Adnan ya yi, ya fice yana, "Haka dai ka gani kana so bara ma inje mu gana in gaida Gimbiya Matar Yareema."
Bangaren Uwar Soro ya nufa yana shiga kuwa ya tarar da Gaaji zaune ta baje Uwar Soro ta aje mata wasu manyan teddies ban da sambatu ba abun da take masu.
Tana ganinsa ta mike tana rike haɓa, "ka kawo mun Baffana ne? Ya ji sauki dai ko? Ina yake? Ka kaini gunsa in gansa ka ji."
Adnan ya karasa gareta yana, "Baffanki na asibiti an fara yi masa aiki zaiji sauki In Sha Allah."
"To akaini gunsa mana,nikam akaini inga Baffana." Cewar Gaaji da idanunta suka cika da hawaye tana kokarin yin kuka.
Adnan ya durkusa gabanta yana rike mata hannu, "Aa fa kar ki mun kuka, kin manta ke babbar yarinya ce yanzu? Kuma Kin manta alkawarin ku da Yareema? Sai nan da Wata bakwai kafin Baffanki ya gama jin sauki shikenan zaki koma rugarku kije ki zauna da Baffanki."
Gaaji ta Taɓe baki, "Tom ni dai ka gaishe mun da Baffana in kaje Kuma in baka labari?"
Adnan ya ce, "Eh."
Daidai da fitowar Uwar Soro daga cikin daki kenan.
Gaaji ta kalleta ta ce, "Kawo kunnenka in fada ma Kar taji Sirrine."
Dariya Adnan ya yi ya kalli Uwar Soro ya ce, "Barka da fitowa Baba."
"Barkanmu Dai Adnan kana tare da mutuniyar ne?"
Adnan ya ce, "eh Wallahi na shigo bakya kusa."
Gaaji ta katse su da fadin, " Ni kajo kaji in fada ma , in ba haka na fasa."
Murmushi Adnan ya yi ya ce, "Oh Sorry gani Ranki Ya Dade Gimbiya."
"Ni ba Soro ce ba ehee saidai kaine Soro nidai sunana Gaaji kuma ba gimbiya ba." Ta fada tana murguda baki.
Dariya ya yi ya ce, "To afwan gani nan."
Tsalle tayi ta janyo kunnensa ta fara raɗa masa, "Aradun Allah Yareema Dan ishka ne,tsirara fa yake zama a dakinsa naje na gansa kuma ranar ma na gansa yana faɗa da wata ita ma tsirara, kai dai ba dan ishka bane ba ko?"
Dariya ce ke kokarin subucewa Adnan ya ce, "Ni ai ba ruwana."
Sake masa kunne tayi tana, "Yawww to ni kai ma ina sho kai zan aura in Yareema ya sake ni."
Uwar Soro ta ce, "Kai dai yau ka gamu da gamonka."
Dariya kawai Adnan ya yi.
Gaaji ta mika masa hannu , "mu ma kulla ƙawance daga yau kaine babban abokina."
Mika mata yayi suka kulla Gaaji tana washe baki.
Ya ce, "To Shikenan dai yanzu bara in tafi ko ,ki kula da kanki."
Gaaji ta ce, "Tom sai ka dawo,ka dawo fa muyi wasa ka ji."
Murmushi Adnan ya yi,yawa Uwar Soro sallama sannan ya fice yana murmushi.
Bangaren Adeel ya koma.
Yana zuwa ya tarar da shi yana cin abinci.
Zama ya yi kan 2siter ya ce, "Safina tazo gidannan ko?"
Adeel ya amsa masa da ,"Eheen."
Nan take fuskar Adnan ta canja cikin fushi ya ce, "Na rasa mene ne yake damunka Prince na rasa mene ne damuwarka da ma abun da zaka so ji ajikin waccer yarinyar yar bariki, Mace ta dunga kawo kanta gareka kuma kana amince mata, shin wai kana mantawa da matsayinka ne? Ka manta kai wane ne?"
Ko kallonsa Adeel bai ba ya ci gaba da cin abincinsa cikin kwanciyar hankali tamkar bai san da zaman Adnan ba bare batun da yake.
Adnan ya kara fusata ya ce , "Ni dai bazan fasa fada ma gaskiya ba, Duk abun da zaka yi kana tuna kai wane ne da kuma darajar mahaifinka da Masarautar nan in ba so kake ka zubdawa kowa mutunci ba, in ma macen kake da bukata ba ga waccer yarinyar ba ka aura kayi koma miye da ita Ba wasu yan iskan titi ba."
Cikin fushi Prince Adeel ya dago fuska ya ce, "Ya isa! Na ce maka hakan ya isa, ni ban aureta Don ina sonta ko kasancewa da ita ba, sannan Safina da sauran ma baka da sanin abun da ke gudana a tsakaninmu."
Ya yi shiru yana ajiyar zuciya kusan Second Uku kafin ya ce, "Ka bar shiga abun da bai shafe ka ba."
"Ok ok haka zaka ce? Ba za dai ka fasa ba kenan? Ko a addinance kasan....
Adnan ya yi shiru bai karasa ba can kuma ya ce, "koma miye kayi duk abun da kake so nawa ido ne da fatan Allah ganar da kai."
Ko kaɗan Adnan baya son abun da zai iya taɓa rayuwar Prince Adeel domin jin hakan yake aransa tamkar shine.
Hakan yasa duk fada basa taɓa iya fushi da juna.
Yana cikin cin abinci yaji wayarsa na kara alamar shigowar sako.
Dubawan da zaiyi ya saki tsaki domin Number ce wacce aka saba turo masa da saƙo a kullum da kalaman soyayya.
Kamar kullum yau ma haka aka rubuto masa, " Duk da cewa baka maida mun da amsa a duk sanda zan turo sako hakan ba zai taɓa sawa na karaya ko inji cewa ba zan iya samun cikar burina ba, Prince Adeel Muhammad Rohaan INA SONKA, INA KAUNARKA, kuma da kai zan rayu har karshen numfashina,kasa aranka cewa ni kadai ce taka,kuma na dace da kai,muddin ina numfashi cikin duniya baka da wata matar da ta zarce ni, Inko ni ban zam matarka ba to ka tabbatar da cewa ba zaka taba yin aure ba,kamar yadda nima ba zan taba yi ba muddin in ba tare da kai ba, na taso da sonka tun kafin insan mene ne so, haka kuma na girma da sonka cike da tsoro da fargaban rasaka domin nasan cewa zan ci gaba da rayuwa ne kawai muddin kaima kana numfashi a doron kasa, ni kadai ce taka,kuma ni kadai zan amsa sunan Gimbiya Matar Yareema, Ina Kaunarka."
A kasa sakon aka rubuta
Gimbiya S.
Ajiye wayar ya yi gefe yana cewa, "Adnan ina so mu dan fita kaina juyawa yake."
"Okay." Adnan ya fada yana tashi.
★★★
Jakadiya na ganin Khalesa ta koma bangaren su tabi bayanta.
Sai da ta basu labrin yadda suka yi da Yareema ita da Hajiya Rabi kafin Jakadiya ta numfasa ta ce, "Yo ke hajiya ai sakarki ta yanke saƙa domin ina tunanin hakarmu na dab da cin ruwa, yanzu wannan aikin nakine , kai tsaye ki nufi Bangaren Fulani ki sanar da ita wannan labari cikin siga mai jan hankali zaki dawo ki bani labari."
Hajiya Rabi ta bude baki tana fadin, "Kuma fa har na dau hasken dadina dake kanki na matukar kawo wuta, ba zan bari abun nan yyi sanyi ba, yanzu yanzu ina zuwa."
Hajiya Rabi ce zaune A parlourn Fulani Babba kanta na kasa take fadin, "Allah ya ja da ran Fulani Daman wata magana ce na zo da ita ban sani ba ko nayi laifi ko kuma zaki ga dacewar hakan."
Fulani ta ce, "Ah Bismillah mana ina sauraren ki In Sha Allah."
"Umm Daman nace batun Yareema da Khalesa ne, ban sani ba ko kina da masaniyar cewa sun daidaita juna, umm kuma daman kin ga a tsari ma sune manya ita ke bi masa in aka hadasu aure zumunci zaifi kara danko."
Cike da mamaki Fulani ta ce, "Khalesa da Yareema kuma? Amman ko in hakan zai kasance zanji dadi gaskiya ,kuma shine na tambayesa ko da wacce yake so ya ce mun Babu?"
Hajiya Rabi cikin in ina ta ce, "Ranki Ya Dade ai da ke kinsan Yareema da miskilanci ba zai taba furta hakan da bakinsa ba."
Fulani ta girgiza kai, "kuma hakane kam Tabbas akwai bukatar in sanar da Mai Martaba cikin gaggawa na Tabbatar da cewa sai yafi kowa jin dadin hakan ba jan lokaci za ayi duk abun da ya dace, wannan albishir ne mai kyau ai." Ta fada cikin bayyanar da Farinciki fal fuskarta.
Daga nan suka ci gaba da taba hirar yadda ya kamata abubuwa su kasance.
Jakadiya na jin motsin alamar fitowar Hajiya Rabi cikin Sauri ta nufi bangaren Fulani Kilishi.
Ta kwashe dukkanin abun da ta jiyo daga dakin Fulani Babba kan ana shirin bawa Yareema Khalesa.
Fulani Kilishi ta ce, "Ah lallai Hajiya Rabi na son shiga gonata, Tabbas tana so takai kanta da Ɗanta kogin mutuwa na Tabbatar da cewa bata san ni wace ce ba har yanzu ganin cewa ina raga masu amman yanzu kam anzo gabar da zanyi fito na fito da kowa ba tare da shakka ba."
Jakadiya ta ce, "abun takaicinma Yarinyar nan bata ji fa, bin maza take kamar karya a kalla an zubda mata ciki yafi sau uku."
Zaro ido Fulani Kilishi tayi ta ce, "kee? Ina masarautar ban sani ba? Garin yaya? Bani bayani domin hakan ma wani babban taimako zai mun."
Magana take ciki ciki kamar zata shake ta ce, "Sirri ne zan fada miki amman mu ...
Ta fara leke leke kafin ta karasa, "Mu shige can ciki."
Like, Comments And Share Fisabillah.
Guntun Comments,Guntu Typing🌝
08103080717
[8/7, 9:47 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: https://chat.whatsapp.com/C1kXo17nLmb7vCXlubtu5o
*AUREN WATA BAKWAI*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*
© *Xayyeesherthul-humaerath*
Page-11&12
Suna shiga Jakadiya ta ce, "Ai ban da bin Maza ba abun da yarinyar nan tasa agaba, watarana fa bata kwana cikin Masarautar nan, In tayo ciki ni da kaina ake sawa in akesawa in kawo maganin zubdawan, Amman fa kar ki bari kowa ya sani."
Fulani Kilishi ta ce, "Umm babu mamaki, karki damu, kije ke dai ta bangarenki kimun kokari duk yadda za ayi da duk wata hanya da zata kawo tsaiko ga auren kiyi sauran aikin kuma nawa ne nasan me zan yi."
Jakadiya ta ce, "To,to,to ki fadamun shirin naki mana kinga sai muyi komai a tare har mu kai ga cin nasara."
Wata irin Dariya Fulani Kilishi ta yi ta ce, "Ni in fada miki shirina? Ai kinyi kadan wa inda ke gabanki ma sunyi kadan, Allah kadai ya san shirina kuma daga shi babu kari, kiyi aikinki ke dai kawai."
Duk Yadda Jakadiya ta so da ta ji shirin Fulani Kilishi ta kasa samun galaba haka ta fice zuciya fal takaicin Fulani Kilishi domin bala'in wayo gareta zata iya shan cikin kowa ta ji abun da ke ransa amman ita baza a taɓa jin ko tarinta ba har sai ta so hakan.
https://chat.whatsapp.com/C1kXo17nLmb7vCXlubtu5o
*AUREN WATA BAKWAI*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*
© *Xayyeesherthul-humaerath*
Page-11&12
Suna shiga Jakadiya ta ce, "Ai ban da bin Maza ba abun da yarinyar nan tasa agaba, watarana fa bata kwana cikin Masarautar nan, In tayo ciki ni da kaina ake sawa in akesawa in kawo maganin zubdawan, Amman fa kar ki bari kowa ya sani."
Fulani Kilishi ta ce, "Umm babu mamaki, karki damu, kije ke dai ta bangarenki kimun kokari duk yadda za ayi da duk wata hanya da zata kawo tsaiko ga auren kiyi sauran aikin kuma nawa ne nasan me zan yi."
Jakadiya ta ce, "To,to,to ki fadamun shirin naki mana kinga sai muyi komai a tare har mu kai ga cin nasara."
Wata irin Dariya Fulani Kilishi ta yi ta ce, "Ni in fada miki shirina? Ai kinyi kadan wa inda ke gabanki ma sunyi kadan, Allah kadai ya san shirina kuma daga shi babu kari, kiyi aikinki ke dai kawai."
Duk Yadda Jakadiya ta so da ta ji shirin Fulani Kilishi ta kasa samun galaba haka ta fice zuciya fal takaicin Fulani Kilishi domin bala'in wayo gareta zata iya shan cikin kowa ta ji abun da ke ransa amman ita baza a taɓa jin ko tarinta ba har sai ta so hakan.
★★★
★★★
Sai can wajen karfe Tara na dare Adnan da Prince Adeel suka koma cikin masarauta.
Gaaji na tsaye jikin window taga shigarsu da sauri ta fita, Adnan ya fara shiga Adeel ne ke kokarin shigewa rike masa hannu ta yi cikin Shagwaba ta ce, "Aboki ba ka mun alƙawari zaka dawo muyi wasa ba?"
Dake dukkaninsu Bakaken Riguna ne a jikinsu,hakan yasa bata iya bambamcewa ko tunanin cewa Prince Adeel ne ba Adnan ba
Adeel ya juyo da sauri yana yi mata wani irin kallo nan take ta razana jikinta ya fara rawa.
Fisge hannunsa ya yi, cikin tsawa ya ce, "Tafi anan."
Adnan na ji ya tashi da sauri tana kokarin komawa da gudu kenan ya ce, "Gaaji? Me ya faru?"
Tsayawa tayi daga nesa bayan Adeel ya shige ta ma Adnan alama da hannu, "jo ka ji."
Yana zuwa ta ce, "ni fa na zata kaine shine na rike masa hannu shi kuma yamun tsawa kuma ya bani tsoro da wannan idon nasa."
"Bai ganeki bane inaga fa, yanzu madadin sa na ce miki kiyi hakuri to,kin hakura?"
Murguda baki ta yi ta ce, "ai ni shi nake so ya bani hakuri ba kai ba wayace ya mun tsawa tom." Ta karasa maganar tana taɓe fuska.
Murmushi Adnan ya yi ya ce, "Oh Gaaji to ba ni bane abokinki?"
Baki a cune ta ce, "Kaine mana, ai shi ba ruwana da shi."
"Yawwa To Kiyi hakuri kinji ." Adnan ya fada.
Alama da kai ta masa tana kara shagwabe fuska.
Ya ce, "Yawwa to yi mun murmushi mu ga."
"Umm umm ni sai kace zaka zo muje muyi wasa da Yarana sai inyi ma Murmushin."
Adnan ya ce, "Eh na yarda to yi murmushin."
Washe baki tayi wanda ya bayyanar da asalin kyawunta da dimple dinta da ya shiga ciki.
"Yawwa To Oya Give me five."
Adnan ya fada.
Tsira masa ido tayi bata san me ya ce ba.
Ya yi dariya , "Au to bani biyar mu tafa."
Mika masa tayi dukan su suna dariya.
Ya rike mata hannu suka koma ɓangaren Uwar Soro.
Ta ce, "ai na hango ku shiyasa ma na zauna ina jira ta dawo gwanda da ka biyota ka ga ta gama cin abinci wanka zata yi ta yi brush take gudun nan."
Adnan ya kalli Gaaji yana zaro ido, "Daman wanka kike gudu? To ni bana kawance da mara wanka da brush gaskiya,ba ruwana dake daga yau,mu kunce ma."
Ya karasa maganar yana mika mata hannu.
Tuni idanunta suka cicciko kamar zata yi kuka ta ce, "Aa zanyi, amman wannan abun Buroshe din fa kwashe mun jini yake zan mutu ne, kuma ni kar ka yi fushi dani kace baka kawa dani."
Adnan ya ce, "Dattin bakinkine yake fita ba jini ba, indai da gaske ni abokinki ne to kije kiyi ina jiranki."
A shagwaɓe ta ce, "Tom nidai saidai kai kamun muje tare." Ta fada tana rike masa hannu.
Adnan ya ce, "Aa za dai amiki ai namiji baya yiwa mace wanka,ba kyau in ganki haka fa kije amiki ina jiranki har ki fito."
Gaaji ta ce, "Tom kar ka tafi kaji ina zuwa yanzu zanje amun."
Da kanta ta shiga toilet din, Uwar Soro ta bita tana murmushi domin tasan da ba Adnan sai dai suta dambarwa da kyar ta yarda.
Aikuwa Uwar Soro na mata wanka tana surutai tana ba Adnan labari yana amsawa adole kar ya gudu.
Har ta fito aka shiryata sannan ta koma parlour gunsa.
Adnan ya ce, "Yawwa ko ke fa Good girl."
"Mene ne? Ni ba gudu nake ba fa." Ta fada.
Dariya Adnan ya yi ya ce, "Cewa Na yi Good girl ma'ana yarinyar kirki."
Ta washe baki "to kai ma Guduo gu tunda kai ma yaron kirki ne ba irin wancen Yareeman ba."
Adnan ya yi dariya kawai yana binta da kallo ita kadai ta ce wannan ta ce wancen magana daya biyu sai ta ce Baffanta wanda hakan ya kara tabbatar masa da cewa bata da kowa fiye da baffanta.
Ta ce, "Ka ga kullum Baffana sai ya mun tatsuniya nake barci tunda ya fara ciwo kuma ya daina mun shikenan." Tana fadan hakan yanayinta ya canja damuwa ta bayyana a fuskarta.
Tsantsar tausayinta Adnan ya ji har cikin ransa ya ce, "Yanzu zanna miki tatsuniya madadin Baffa kafin ya ji sauki kin yarda?"
Da sauri ta ce, "Eh da gaske kake?"
Ya ce,"Ehen."
Gyara zama ya yi,itama ta matsa daf da shi.
Ya fara yi mata tatsuniya ban da dariya ba abun da Gaaji take yi,a haka har barci ya kwasheta ta fada jikinsa.
Dakansa ya dauketa ya kaita daki ya kwantar da ita, saida ya shafa mata addu'a kafin ya fita.
Gidansu ya nufa kawai ganin dare ya yi bai koma bangaren Prince ba.
★★
A wannan tsalelen daren.
Motar safina ce a gefe tana ciki waya take tana fadin , "inata kiransa fa bai dauki Kiran ba nikam na gaji zan tafi."
A dayan bangaren aka ce, "Kar ki damu ba sai ya dauka ba,na Tabbatar yanzu dai ya ci abincin daren da aka kai masa,inma bai ci ba to ya sha drinks din ko ruwan so kina shiga komai zai tafi daidai Don Allah karkiyi mana wasa da wannan damar domin ita ce ta karshe a garemu."
Dariya Safina ta yi,ta ce, "an gama Tabbas yau akwai shagali kace mun ka gama naka aikin saura nawa." Ta karasa maganar tana katse wayar tare da cizon bakinta.
Kai tsaye ta shige ciki tana shiga kuwa ta tarar da Prince Adeel kwance ga dukkan alamu yana cikin wani yanayi hannunsa akan gabansa yana juyi .
Tsayawa tayi daga nesa tana wani irin Murmushin Mugunta.
Adeel na jin alamar ta ya dago cikin wata irin gigitacciyar murya ya ce, "Safina Am in need Please."
Yana fada ta kara kwantawa.
Karasawa gare sa tayi cikin jin dadi.
Ta dagosa tana....
Comments,Like,And Share Fisabillah🥺🙏
08103080717
Urs Xayyeesherthuo
[8/7, 7:29 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: https://chat.whatsapp.com/C1kXo17nLmb7vCXlubtu5o
*AUREN WATA BAKWAI*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*
© *Xayyeesherthul-humaerath*
Page-13&14
*AUREN WATA BAKWAI GROUP, Son So fisabillah,Masoyan Yareema da Uwani Gaaji😂💔dama masoyan Safina da Khalesa tare da Uwar Gayya Jakadiya😂😘😻🥀*
Tana bin jikinsa.
Ya ce, "Ki dan gyara mun kwanciyar, ina so inyi barci." Ya fada murya a ƙasa cikin yanayin galabaita.
Tallafa masa tayi ya kwanta, ruf da ciki, nan take wani irin barci ya yi awun gaba da shi,tamkar matacce.
Kamar wasa ta kwanta ita ma tana jira ya farka amman ina,babu alamun motsi bare tashi har dare ya fara tsalawa wajen karfe biyu da wani abu.
Jijigashi ta fara yi tana, "Prince Ka tashi mana, wannan wani irin barci ne kuma, Ka tashi Please."
Bai ma san tana yi ba hasali ma nauyinsa duk ya sake yana barcin da kyar take iya girgizasa.
Ganin bata da yadda zata yi ga dare ya yi bata so ta kwana asamu akasi wani ya ganta haka ta tashi ta fita zuciya fal takaici da bakin ciki.
Tana shiga Motarta ta ,ta nufi hanyar gida rai ɓace.
Shigar ta kenan Wayarta ta fara ringing dauka tayi a dayan bangaren aka ce, "ina fatan komai dai ya tafi daidai?"
Tsaki Safina ta yi ta ce, "wani daidai? Da farko naje kamar abun arziki naga alamun ya ci abun da zai sa sa aikata abun da muke so dole, amman kuma sai barci ya dauke sa nan take ta yadda bazan iya aikata komai da kaina bama, don nayi kokarin hakan amman yanayin kwanciyar da kuma yanayin yadda surar jikinsa take na gagara aikata komai, anya ba kuskure akayi aka sa masa maganin barci madadin namu ba?"
"Taya zaki ce maganin barci kuma? Abun da ni da hannuna na zuba kuma ni na siyo,ni na fara tunanin kema dai kawai da naki bakya son ayi abun nan kowa ma ya huta, kuma kin san cewa nawa mai sauki ne a karshe kece da reward din samun nasara indai hakan ya tabbata."
Cikin Fushi Safina ta ce, "Oh ka dawo da laifin gareni kenan? Duk kokarin da nake a banza? Alright Shikenan ka gwada wata mana in Zata iya har ma ta jure miskilancin wannan mutumin gwanda ma ni ai."
Ya ce, "Na ji yanzu meye kike ganin mafita tun an kara samun wani tsaikon?"
Safina ta ce, "Akwai bukatar a kara komawa ta inda aka hau domin tanan ne kadai za a sauka, yana da taurin kai sosai kuma babu shakka akwai wani abu tattare da shi da dole sai an kawar kafin akai ga cin nasara."
"Umm tabbas yanzu nima na fahimta kuma indai hakanne za ayi gagawan tabbatarwa duk wannan taurin kan da duk wani abu da ya ke ji da shi sai ya gagaresa ba matsala ki huta yanzu kam baza ki kara kai kanki ba har sai ya nemeki."
Yana karasa maganar ya katse wayar.
Safina kuwa gyara kwanciya ta yi abunta sai barci.
Karfe Hudun dare Prince Adeel ya farka ban da zufa babu abun da ke keto masa, ya tashi ya yi wanka sannan ya dauro alwala.
Salloli ya fara yi har sai da aka kira sallar asuba ya fita yaje masallaci ya yi.
★★★Gaaji na tashi daga barci ta ce lallai ita baza ta yi wanka ba sai Abokinta Adnan ya zo.
Uwar Soro ta rasa yadda zata yi a karshe dai sai da ta kira Adnan suka yi Waya da Ita ya ce in bata tsaya an mata kwalliya ba,bazai zo gunta ba kuma ya mata alkawarin zai fita da ita ya siyo mata kaya masu kyau abubuwan ci na dadi.
Da tsallenta ta ce, "Yanzu zan yi wankan kuma zan tsaya amun da kyau in fita ka yi sauri kazo fa."
Tunda tayi wanka ta tsaya ta window tana leken ta inda Adnan zai bullo har wajen karfe uku.
Da kyar Uwar Soro tasa ta tayi sallah da dabarar cewa in bata yi sallah bama Adnan ba zai zo ba.
Duk da cewa sallar ta ta ma fanko ce domin kifawa kawai take tana tashi, a hankali tana dan nuna mata wasu abubuwan tana gyarawa.
Sai wajen karfe Biyar Adnan ya shigo, bai ma je gun Yareema ba gunta ya wuce kai tsaye.
Tana ganinsa ta bata rai, "Ni nayi fushi,na daina Shonka kuma ma mun kunce." Ta karasa maganar tana mika masa hannu alamar su kunce.
Durkusawa gabanta Adnan ya yi ya kama kunnen ya ce, "Afwan Gaaji Beauty kin ga na kama kunne na ko sai na mari fuskata?"
A shagwaɓe ta ce, "E amman kar ka mara da zafi a hankali kuma sai kace zaka goyani yadda baffana ke mun,kuma zaka na zuwa guna da wuri."
Marin fuskarsa ya yi yana dariya ya ce, "To na mara kuma zan goyaki in mun fita, sai kuma me zan yi yanzu ? Kin ga bakiyi murmushi ba."
"Umm umm ni na daina ma murmushi ai kuma?" Gaaji ta fada.
Adnan ya ce, "in dai bakiyi murmushi ba,to ni kuka zanyi ma."
Da sauri tayi murmushi tana, "tom nayi kar ka yi kuka."
, "yawwa Good girl bara in nuna miki wani abu sai mu tafi ko."
Ta ce, "Guduo gu ."
Dariya Adnan ya yi ya ce, "ni fa ba gudou gu bane, Good Boy zakina cewa."
"Tom Gudu bu."
Dariya yayi kawai yana girgiza kai.
Wayarsa ya ciro ya danna video call A WhatsApp likitan da ke kula da baffanta ne ya daga suka gaisa sannan ya bukaci da anuna masa shi.
Nuna wayar ya yi inda Baffan Gaaji yake, yana barci hankalinsa kwance jikinsa har ya fara canjawa.
Tsabar mamaki Gaaji ta kasa magana kusan minti daya kawai ta washe baki tana kallon baffanta nan take Farinciki ya gama bayyana a fuskarta ta ce, "Baffa am Noi ɓanduma? Volwunam,. Anani koiɗum ko?a umman a vawami ko? (Ya jikinka? Ka yi mun magana mana, ka ji sauki ko? Zaka tashi ka goyani?)."
Ta ka baiyi magana ba kallon Adnan ta yi ta ce, "Ka ce ya mun magana ina sho nayi magana da shi."
Adnan ya ce, "ba ki ga barci yake ba? Tunda aka masa aiki bai farka ba sai ya huta sosai inya farka sai mu kara kira ko." Ya karasa maganar yana yiwa likitan Sallama ya katse wayar.
Gaaji cikin yanayin Farinciki ta ce, "Baffana zai ji sauki."
Adnan ya ce, "In Sha Allah yanzu ta shi muje."
Suka shiga Parlourn Uwar Soro suka mata sallama sannan suka fita tare.
A mota ya sata tana ta kalle-kalle da tabe ya koma yawa Yareema magana.
"In ba abun da kake,kadan raka ni wani waje mana?"
"Okay." Kawai Yareema ya amsa.
Ya canja kaya ya fito.
Yana zuwa ya shiga gaban motar, Adnan ya ja su suka dau hanya.
Daga kansa da zaiyi a madubi ya ga Gaaji nata washe baki.
, "Adnan! Kana cikin hankalinka kuwa, Wannan yarinyar fa?"
Adnan ya ce, "Za muje SHOPRITE ne ta sha iska taga abubuwa sannan kuma ina so in mata siyayyan kayan sawa."
"Me zai sa baza ka bada a siyo ba har sai mun fita tare?" Prince Adeel ya fada.
Kafin Adnan ya yi magana karaf Gaaji ta ce, "Ehdin sai anje dani din ina ruwanka