Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 5
ya yi rai ba aure, ke ban ma ga ta zama ba,amman ina fatan dai baki sanarwa da kowa hakan ba?" Girgiza kai kawai Jakadiya ta yi alamar eh. Hajiya Rabi bata kara bi ta kanta ba tuni kawai ta dauki mayafi ta fice. Tana fita Jakadiya ta tuntsire da wata irin dariya ta wani wasu surutan da ita kadai ta san fassaran su. ★★★kiran Uwar soro Fulani Babba tayi kan tana neman Yareema. Uwar Soro ta sanar da shi kai tsaye ya nufi cikin Masarautar. Yana zuwa zuwa daga kafar shi da zaiyi ya shiga ciki kafar ta kame kam. [8/7, 9:47 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *AUREN WATA BAKWAI* *NOBLE WRITERS ASSOCIATION* © *Xayyeesherthul-humaerath* Page-5&6 Duk kokarin da ya yi wajen ganin ya ja kafar kin motsawa tai sam sam. Jakadiya na fitowa daga kitchen ta hangosa tsaye kafa a kame, rike baki tayi a zahiri tana fadin, "Subhanallahi Yareema lafiya?" Ko kallon inta take bai ba bare ya bata amsa ya ci gaba da kokarin daga kafa amman ina tamkar ana kara danna kafar. Bangaren Uwar Soro tayi tana kurma ihu, "Na Shiga ukuna,Yareema ya kame,kafar Yareema ta kame ya kasa takawa." Uwar Soro na jin hakan ta fito cikin sauri tana fadin, "Subhanallahi ya aka yi hakan? Ina Yareeman." Jakadiya ta ce, "Gashi can a kofar shiga bangaren Fulani Babba." Aiko Yareema na tsaye ban da zufa ba abun da yake tun yana kokarin motsawa har ya hakura. Uwar Soro na zuwa tayi kokarin jan kafar tasa amman ina sam hakan ya gagara. Addu'a ta shiga tofa masa,cikin kankanin lokacin gabadaya matan cikin Masarautar sun cika gun. Fulani Kilishi ce ta fara karasowa garesa tana, "Subhanallahi Yareema meke faruwa haka?in kafar nan taki motsawa ta karshenta sai dai a yanketa." Tana fada suka hada ido da Magajiya tare da sakin wani ƙayataccen murmushi. Uwar Soro ta umarce su da duka kowa ya bar gurin abarta daga ita sai Yareema,ba yadda suka iya ba don sun so ba haka suka tafi, Fulani Babba kuwa daman bata fito ba. Hajiya Maimuna ta ce, "Uwar soro ko zan iya tsayawa ni in taimaka?" Girgiza mata kai tayi alamar aa haka ita ma ta bar wajen. Addua ta ci gaba da tofa masa Kasancewar hakan ba sabon abu bane gareta tun yana karami lokuta zuwa lokuta kafarsa ta kan rike sai ta sha faman yi masa addu'o'i kafin ta sake. Yau yafi na kullum domin kuwa da kyar kafar ta sake, tana sakewa tare suka shiga bangaren Fulani Babba. Bayan sun shiga saida aka ɗauki kusan Second biyar kafin Fulani Babba ta fara magana. "Yareema!." Ta yi shiru kafin ta ci gaba da fadin, "ka san dai a yanzu ban da damuwa da burin da ya zarce ace yau ka yi aure." Tana fada tsigar jikinsa ta fara tashi kansa na yi masa wani irin tsiro. "Ban san mene ne dalilinka na rashin son aure ba kasancewar ka haka a yanzu baka da abun da ya kamaceka fiye da aure, na san cewa kana da nauyi akanka na juya dukkanin abubuwan da ke tafiya a masarautar nan, zuwan mata kila tana tallafa maka ta wani bangaren ka samu sauki ban sani ba ko akwai wacce kake so,indai akwaita zan so ace kayi gaggawar bayyanar da ita domin ayi komai kan lokacin da ya dace." Shiru ya yi bai ce komai ba kansa na kasa. FULANI babba ta kalli Uwar soro ta ce, "ko ya sanar da ke wata wacce yake muradin Aure?" Uwar soro ta ce, "Aa Ranki Ya Dade." "Hmm to ina jinka Adeel yanzu kai ba yaro bane kasan abun da ya ce da kai fiye da kowa." Cewar Fulani Babba. Yareema ya ce, "Babu Ranki Ya Dade amun hakuri tukun zuwa gaba." Fulani ta girgiza kai tana, "Shikenan Allah yasa mu dace." Tare suka fice da Uwar soro sai ta tabbatar ya shiga bangarensa kafin ita ma ta koma nata. Tana shiga ta samu Gaaji na surfa uban kuka ita akaita gun Baffanta tana so ta ganshi kar a kashe mata shi. Dakyar Uwar Soro ta lallabata har ta samu ta yi barci. Cikin dare ta farka wai tana jin kashi. Uwar Soro ta kaita toilet ta ce ta hau tayi. "Wallahi na Rantse da Ubangiji na ba jan hau wannan abun a wawushe mun duwawuna ba,haka kawai in rasa mazaune ni kam ba zan hau ba, kawai mu fita anuna mun kasa inyi yadda muke yi a ruga." Duk Yadda Uwar Soro tayi da Gaaji tayi kashi a toilet dinnan ki tayi fur daga karshe sai leda ta dauko mata,ta bata,ta tsuguna tayi, ga shegen yawa da uban wari tsabar da nannagi abinci harda na hauka. Tana gamawa tasa hannu ta kulle abunta a ledar ta ajiye a gefe tana, "kuma Aradun Allah karki samun kashina cikin abunnan a ajiyemun da safe zan dauke abuna da kaina inje in binne." Sai da ta koma barci kafin Uwar Soro ta samu ta je ta yi floshin din kashin. Prince Adeel Muhammad Rohaan Tun da ya koma kansa ke sara masa gabadaya wani gitaccen ciwon kai yake ji, zuciyarsa kuma ban da muradin kasancewa da wata ba abun da take. Wayarsa ta fara ringing, yana dubawa ya ga number Safina, a jiyar zuciya ya yi aransa yana raya tamkar tasan yana da bukatar ta a yanzu. Kara Wayar ya yi a kunne ya yi shiru. A bangarenta ta ce"Prince inzo mu kwana? Na kasa barci Please." Da "alright." Kawai ya amsa mata yana ajiye wayar. Tuni ta tashi ta feshi jiki da turare ta sa wasu irin kananun kaya da zai iya gigita kowanni Ɗa namiju daga kallo ɗaya, Mussaman ma ita da take da diri bayyananne mai daukan hankali. Tana zuwa ta kira wayarsa tashi ya yi ya bude mata kofar bayan ta shigo sannan ta rufe ta bi bayansa. Zama ya yi a gefen gadon yana danna wayar dake hannunsa, tana shiga ta wular da Doguwar rigar da ta rufe jikinta da shi tana wata irin tafiya ta karasa garesa tana shafasa, harshenta tasa a wuyansa tana bi tana leshewa, da hannunta tana bin jikinsa a hankali, tuni ta gama sakar masa da jiki, murya a sanyaye ta ce, "Please Prince, yau kada ka ƙi, ka yarda muyi abun da ya dace,ina da bukata kuma kai ma na Tabbatar da cewa zaka ji dadin hakan kaji." Ba tare da yace kamai ba ya kara janyota yana sa harshen sa cikin bakinta yana kankameta, ganin hakan ta fara kokawar rabasa da kayan jikinsa, subulewa tayi daga jikinsa tana binsa da wani munafikin kallo mai kara kashe jiki ta ce, "Wait taya hakan zai yiwu da kaya jikinka bara in cire ma ko." Shi ko tsayawa kallonta ya yi kawai tamkar hoto ta rabasa da kayan jikinta tana kokarin janye masa gajeran wando da ke ciki kenan ya dakatar da ita da hannu alamar aa. Wani guntin tsaki tayi azahiri cikin zuciyarta tana fadin, "duk abun ka dai Wallahi yau sai na samu abun da nake so nayi galaba akanka." Murmushi ta masa ta dawo jikinsa tana shafa girjinsa. Shi kuwa sakewa ya kara yi,yana bin dukkan ilahirin jikinta yana kai mata wasu irin saƙonni, ban da kokarin ta hake masa ita kuwa ba abun da take, da ta kai hannunta zai rike. Ya gama duk wasannin da yake da bukata janye jiki ya yi yana numfasawa ya ce, "Safina Is Ok Please ya isa haka barci nake ji." Kukan karya ta fara yi tana yi masa magiya. "Prince Wallahi baka ji yadda nake ji ba, zan iya rasa rayuwata muddin baka biyamun bukata ta ba, ka tausayamun Please, ko na yaune kadai just once." Jiki a mace idanun sa na rufewa ya ce, "Ki bari Gobe." Yana fada ya kifa da kansa tuni barci ya yi awon gaba da shi. Dafa kai Safina tayi tana, "wai wannan wani irin Bala'i ne kullum sai anzo gabar da zan aiwatar da aikina sai kace barci ko kuma wani abu ya faru? Baka da aiki sai romance? This wil be last time da zan bata lokaci na ba zan dawo gidannan ba sai da maganin da dole zai sanyaka aiwatar da abun da ake da bukata ko na huta." Tashi ta yi tasa rigarta ta fice,tana fita cikin duhu wani Mutumi ya karaso gareta yana, "Ya na ganki haka? Ina so inji labari mai daɗi kar ki fada mun akasin hakan." Tsaki ta yi ta ce, "ni fa na gaji wallahi kullum sai ya kaini makura sai ya juya mun baya, Gobe ko jibi ina da bukatar anemo mun magani mai karfi da zai rikitashi duk yadda za ayi asa masa cikin abun da zai sha inaga wannan shine shawarar karshe da zata iya aiki in ba hakan ba akwai Matsala,har na gaji da binsa Wallahi." "Shikenan kada ki damu zamuyi magana a waya." Mutumin ya fada yana waige-waige ya tafi. WASHEGARI. Tun da akayi sallar asuba ma'aikata da dogarai ke kai kawo cikin masautar kowa na aikinsa. MASARAUTAR BENONI babbar masarautace wacce ta amsa sunan masarauta a kasar hausa, ta tsaru iya tsaruwa daga wajenta har ciki,inda kudi da kayan masarufi na magana Tabbas na wannan masarautar in suka fara nasu ba sauki, Aljannar duniya ga wanda ya taba shiga cikinta domin babu mai tunanin fita koda kuwa cikin mafarki ne. Mai Martaba Sarki Muhammad Rohaan ya gaji sarauta tun daga gun Kakansa, kakansa na rasuwa mahaifinsa ya hau karagar mulki shi ma bayan mahaifinsa ya rasu ya hau wanda yake a yanzu shi ke jagorantar BENONI. Matansa Biyu Fulani Babba (A'isha) da Fulani Kilishi (Hafsat) Yaro Ɗaya garesa Prince Adeel Muhammad Rohaan wanda yake tamkar gado ga ahalinsu Basu cika haihuwa sosai ba, Kakansa shi kadai ne, kamar yadda mahaifinsa yake shi kadai,haka kuma shi ma ya Kasance shi kadai sannan ya haifi Ɗa shi kadai. Mai Martaba sarki Muhammad Rohaan mutum ne mai karamci da sanin ya kamata cike da jin kan talakawa,sannan baya taba fadin magana biyu, Indai ya ce abu to babu shakka,ba canji a wannan batun, baya da yan uwa na kusa sai wa inda suka zam dangi garesa na nesa, yan uwan mahaifiyarsa ,yayunta da kanenta, dukkaninsu suna rayuwa cikin Fada da matan su da 'Ya'Yansu Waziri, Sarkin Fada, da Sarkin Yaƙi. Waziri shine Mijin Hajiya Maimuna Yaranta mata yan biyu Nasmah da Basmah. Sarki Yaƙi mijin Hajiya Rabi suna da yara uku mace Ɗaya Khalesa da kuma Ameen da Noor,da kuma sarki fada mijin Magajiya Da yarinyarsu Ɗaya Rumaisa. Prince Adeel Muhammad Rohaan shike tafiya da shigar da fitar dukka wani kudi da ke wakana a MASARAUTAR BENONI kasancewar ya kammala digirinsa a bangaren tattalin arziki. Khalesa da Nasmah suna masifar sun Prince Adeel sanadiyar yadda kowa ke bayyana soyayyarsa gareshi yasa basa shiru da juna ko kadan, wajen zama ma in daya na gun daya bata taba zuwa. Hajiya Maimuna da Magijiya suna matuƙar nuna soyayya tare da kauna ga Adeel cike da gujewa dukkan abun da zai iya cutar da shi saɓanin sauran matan da ke bayyanar da kishinsu da tsantsar tsana a zahiri. Aranar da Yareema yazo duniya aranar sai da aka nemeshi aka rasa a Masarautar daga karshe sai Uwar Soro ce ta tsinto shi cikin kwali a na kokarin fidda shi daga fadan. Hakan yasa tun Adeel na karami Mai Martaba ya zaɓi kebantar da shi tun yana da shekara Uku ya koma gun Uwar Soro har sai da ya fara girma ya kammala secondary zai shiga Jami'a kafin aka fara bayyanar da shi Wanda tunanin wasu ma da yawa a garin gabadaya ya mutu fitowarsa kuwa ya girgiza tunanin kowa da ke Masarautar da garin. Wannan kenan. Karfe Bakwai na safe Uwar Soro ta ga barci Gaaji fa bana karewa bane tadata tayi ta ce mata tayi sallah. Kallonta tayi ido duk kwantsa ta ce, "Sallah? Tab ni fa ban girma ba ai sai an girma ake sallah ki barni inyi barcina ni." Ta kara shigewa bargo. Sai da taji tace mata ga abinci aiko zumbur ta tashi ta na kokarin kubcewa. Uwar soro ta ce, "aa fa sai kinzo munje Kinyi wanka Kinyi brush kiyi alwala kiyi sallah kafin kici abincin nan?" "Boroshe? wannan abun na jiya da kwashe mun jini ko? Na rantse banyi haka kawai aje ata kwashe mun jini saidai in wannan abun zaki sammun abaki inshanye shi kam da gardi aradun Allah kums wanka nayi jiya ai banyi yau sai ranar sallah ehee." Uwar Soro ta ce, "to tashi muje kiyi dai koma miye sai kici abincin." Fashewa da kuka Gaaji tayi tana, "Ni yunwa nakeji hanjin cikina kuka suke,na shiga ukuna na mutu na lalashe ki bani abunshi inci kar in mutu." Ta ƙarasa maganar tana birgima akan gadon harda rike ciki kamar mai nakuda. Uwar soro ta ce , "Oh ni Jummai na gamu da gamona, ga shi zan baki kici amman kimun alƙawari in kinci zakiyi duk abun da nace kiyi kin yarda?" Ta girgiza kai. Mika mata tayi, tuni ta fisge ta fara ci kamar tsohuwar mayunwaciya. Sai da ta cinye tas Uwar Soro ta ce, "Yawwa yanzu bara in dauko miki zani ki cire kaya muje bandakin ko." Uwar Soro na shigewa dayan dakin ta kalli gefe da gefe taga ba kowa da gudu ta fice ta shige bangaren Prince Adeel. Tana shiga ya fito daga wanka kenan yana zaune yana shafa mai ya zame towel din jikinsa babu komai a jikinsa. Tana shiga tana ganinsa da ta kwallara wani ihu.... *DUK WACCE KE SO TA BIYA A MATA ADVERT A PAGES KOFA A BUDE TAKE YI MUN MAGANA KAI TSAYE TA NAN 08103080717* Urs Xayyeesherthuo [8/7, 9:47 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: https://chat.whatsapp.com/C1kXo17nLmb7vCXlubtu5o *AUREN WATA BAKWAI* *NOBLE WRITERS ASSOCIATION* © *Xayyeesherthul-humaerath* Page-7&8 Rufe idonta tayi tana kankame jikinta tamkar zata suma ta wata irin gigitacciyar ƙara. Prince Adeel ya kalleta ya kauda kai,yaja towel din sa ya daura, yana kokarin sa kaya,ci gaba da ihun tayi kamar wacce aka sawa saban batir, har cikin Dodon kunnensa yake jin saukan kararta. Cike da takaici ya karasa inda take yana daka mata tsawa. Maimakon ta nutsu tsawar da ya mata yasa ta ci gaba da kwallara ihu tana kokarin shidewa. Rufe mata baki ya yi da hannunsa yana mata alamar tai shiru. Ita kuwa ido ta kafa masa suna kallon juna,aransa yana sakawa , "Anya wannan yarinyar na da hankali kuwa? Watakila ma mahaukaciya ce ga dukkan alama." Ita ma a zuciyarta ta ce, "Cab lallai wannan ƙasurgumin Dan ishka ne,kawai ya zauna tsirara ba kaya, Aradun Allah watarana na kara ganinsa haka nan sai na yanke masa wannan jelar mai kama da beraye." Kusan Minti Daya suna haka kafin ya saketa yana sauri ya shige toilet zuciyarsa na tashi, wanke hannunsa ya yi ,yana jin kyamarta dama bai kai hannunsa bakinta ba don gabadaya yanzu a tsarge da kansa yake. Har zai fita , haka ya koma ya kara wani sabon wankan Amman duk da haka hankalinsa bai kwanta ba,hannunsa ji yake kamar har yanzu da yawunta a jiki. Ita kuwa yana saketa,ta falfala aguje ta koma bangaren Uwar Soro tana haki kamar wacce ta dibo kaya. Da sauri ta riketa tana, "Ya Salam, Gaaji ina kika je? Ba wanda dai ya ganki ko? Ki daina fita in kina fita kamaki za ayi a kulle." Gaaji ta ce, "Ni fa gun Yareema naje in ce masa ina Baffana ya jikinsa, shine fa kawai na gansa a tuɓe aradun Allah Yareema dan iska ne ashe, kin gansa kamar wani Dodo cab." Uwar Soro ta ce, "Kul kada in kara jin hakan a bakinki kinji." Cuno baki tayi tana, "To wayace ya zauna ba kaya,ai yan iska ne ke zama tsirara dai ga shi fa wani katon garde da shi abun tsoro ni Allah sa ma kar nayi mafarkinsa in kasa barci." Ta fada tana rufe idonta. Uwar Soro ta yi dariya kafin ta ce, "Na ji dai, daga yanzu in zaki je bangarensa kina fadamun kuma sai kin kwankwasa kofa ya baki izinin shiga kafin ki shiga." "Ni ban kuma zuwa masa ma inje inga abun da zai makantar dani in daina gani ana cemun makauniya, Shikenan in kasa ganin Baffana." Gaaji ta fada tana dafe haɓa. Rike mata hannu Uwar soro ta yi tana, "to na ji, yanzu kizo muje in miki wanka, kuma kin ga wannan kan naki ma dole a wankesa arage masa Dauda a gyara sai in miki kitso." Take Gaaji ta bata rai tana hada girar sama da ƙasa ta ce, "ni fa nace miki bana shon wankan nan bana sho nikam fatar jikina zata zama roba, kuma ta dafe." Uwar Soro ta ce, "Ba zata dafe ba fa zata yi kyau ne tafi yanzu haske kuma karfin ma zaki kara ne,ki zama yan mata Sosai." Uwar Soro ta ce, "aiko in baki yarda anyi wankan nan ba bake ba abincin Rana irin me dadin nan." Ko magana Gaaji ba tayi ba ta fara cire kaya tukun ta ce, "Mu je kin ji, Wallahi ba zan iya zama da yunwar ga ba,gwanda kawai ayi wankan nikam na hakura fatar ta ta kodewa karfin ma ya tafi amman dai abani abinshin in ci Don Allah." Da kanta ta shiga toilet din,Uwar Soro ta mata wanka, ta dan wanke mata gashi aka rage masa dauda dan ba za dai ace ya fita duka ba, dan kwana biyun nan har ta fara chanja kala haskenta da ya dafe dan dauda har ya fara dawowa kyanta na asalin bayyana. Dole wasu kayan Fulani Uwar Soro tasa aka nemowa Gaaji domin duk kayan da ta bata tasa cewa take ita bazata sa ba,ba shine kayan su ba. Yau ya kasance ranar Juma'a wacce ta kasance a kowacce Juma'a Yareema na zuwa su gana da Mai Martaba kafin su shiga Masallacin Fada suyi sallah tare. Hakan ne ya wakana kuwa yana fitowa daga wanka ya shirya ,Shamaki na tsaye yana jiran fitowarsa yana fitowa suka nufi Cikin Fada tare. Bayan Shamaki ya raka Yareema fada dukansu suka fice waje kamar yadda aka saba. "Barka Da Safiya Ranka ya dade." Cewar Prince Adeel. Mai Martaba ya ce, "Barka dai Yareema, ina fatan komai yana tafiya daidai ba tare da wata matsala?" Prince Adeel ya ce, "AlhmduLillah komai na tafiya daidai kuma abisa tsarin da ka umarta." Mai Martaba ya saki murmushi kafin ya ce, "Ma Sha Allah, wato kaidai ba zaka taba barin wannan shigar kasar wajen ba, ka riga ka gama sabawa da hakan ko ince kafi jin dadin hakan ko?" Shiru Yareema ya yi kansa a kasa yana sakin Murmushi. Mai Martaba ya ce, "Kodayake nima nayi na gaji na hakura watarana da kanka zaka daina sawa har ma ka manta da yadda ake sawan." Shi dai Yareema bai ce komai ba sai Murmushi. Shi kuwa Mai martaba kara jin so da kaunar ɗan nasa ɗaya tilo a duniya yake har cikin ransa, a zuciyarsa shi ma bai da muradin da ya zarce ace Yareema ya yi aure ya haifa masa jika ya gani tun yana raye,amman sam baya iya masa maganar hakan aransa ji yake cewa haka ba karamin takura bane,kuma babu abun da yafi so fiye da farincikin Yareema zai so ace da kansa ya ji sha'awar kasancewa mai iyali. Sun dan taba hira daidai gwargwado kafin suka nufi masallaci suka saurari Huduba sannan suka yi sallah. ★★Nasmah na Tabbatar da cewa an idar da sallah ta nufi kitchen kai tsaye ta ce wa Magajiya, "Ina abincin Yareema?" Magajiya ta ce, "ga shi can ina jira Uwar Soro ta turo a daukan masa ne." "Aa ni zan kai masa yau,ya ce in kai." Ta karasa maganar tana kada kokarin daukan abincin. Daga nesa taji tsawar Khalesa na fadin , "Dakata! Kada ki kuskura ki yi gigin daukan Abincin Yareema domin yau Ni nake da alhakin kai masa." Nasmah ta ce, "What? Ban gane kamar ya?" Bige hannun Nasmah, khaleesa tayi akan tiran abincin tana janyewa, "eheen abun da kunnenki suka jiyo shi nake nufi, Ai Babban Ɗa Sai babbar 'Ya kamar yadda nake Babbar 'Ya mace a Masarautar nan haka zan kasance mata ga Yareema atakaice dai Gimbiya duk da kin sani gwanda in kara jaddada miki don kuwa na lura da cewa kunen kashi gareki." Ta karasa Maganar tana kare mata kallo sama da kasa tana wani irin juyi. Magajiya ta ce, "Amman dai dukanin ku kun san cewa babu mai alhakin kaiwa Yareema abinci ba tare da izinin Uwar Soro ba ko?" Khalesa ta ce, "agunki kenan don ni ai a yanzu nafi Uwar Soro kusanci ga yareema zan gansa a lokacin da na so kuma nayi niya Don haka ni zan kai abincin Yareema ba wanda ya isa ya hanani kaiwa." Nasmah ta ce, "ai bai zam mallakin ki ba a yanzu Don haka kowacce na da hakkin amfani da damarta duk wacce tai nasara shikenan." Ta karasa magana tana kokarin fisgewa. Wani azababben mari Khalesa ta sake mata a afuska da sauri Magajiya ta karasa inda suke daidai da lokacin da Jakadiya ta shiga kitchen din. "Kai kai kai.. mai zan gani haka me ke faruwa ne?" Jakadiya ta fada. Nasmah na kuka ta ce, "na zo daukan abincin Yareema ne zan kai masa Khaleesa ta kwace wai ba zan kai ba kuma ta mareni." Khalesa ta ce, "Karya kike karamar munafuka." "Aa fa ba ayi haka ba kema dai Nasmah kin fiye tsaurin ido taya Khalesa zata kaiwa Yareema abinci kice ke zaki? Ai ido ba mudi ba amman yasan kima,ita da muke fata nan da kwanaki kadan muji ta zam gimbiya, aa aa Maza Khalesa je ki kai wa Yareema abinci." Kuka Nasmah ta kara fashewa da shi ta fice da gudu a kitchen. Khalesa tayi tsaki tana, "Kya yi kya gama Yareema dai kam nawane." Suka hada ido da Jakadiya suna sakewa juna Murmushi. Nasmah na zuwa ta fada jikin Hajiya Maimuna tana kuka tana fada mata abun da Khalesa da da Jakadiya suka yi mata. Hajiya Maimuna ta share mata hawaye tana murmushi, "Hakanne ya saki kuka? Mene ne na kuka akan haka? Lallai baki tanadi zuciyar da zaki tallafi soyayyarki ba, ki zam jaruma,mai maida komai ba komai ba koda kuwa komai dinne,ki sa aranki cewa indai Yareema mijinki duk rintsi duk wuya babu fashi sai ya kasance naki, rabon kwado ai baya taba hawa sama,ko ya hau ma dole ya fado, don haka ki kwantar da hankalinki." ★★ Fita tayi tana tafiya tana rangwada tamkar bazata taka kasa ba,tana zuwa Tayi Nocking shiga bangarensa, Shamaki ya fito ya sanar da ita yana barci ta bada abincin a ajiye masa. Khaleesa ta ce, "ka tashesa ka ce nice ina son ganin sane Don Allah." Shamaki ya ce, "Kin san dai in ba wani uzuri babba ba ba damar tada Yareema a lokacin da yake hutawa mussaman rana irin ta yau." "Ni dai Don Allah yau kadai amun wannan alfarmar." Komawa ciki shamaki ya yi,ya yi dace kuwa yana zuwa ya tarar da Yareema zaune yana danna laptop ga dukkan alamu yana duba wani abu mai mahimmanci ne. Shamaki ya ce, "Ranka Ya dade Khaleesa ce awaje ta kawo ma abinci." "To ka karba mana."Yareema ya fada hankalin sa na kan system din dake gabansa. Shamaki ya kara da, "Aa ta ce wai kai take son gani abata izini ta shigo." Da Okay kawai Yareema ya amsa, Shamaki ya fita ya cewa Khaleesa ta shiga. Tana shiga ta ajiye Abincin kan daining sanan ta karasa daf inda yake ta zauna tana, "Good Afternoon Darling Prince." "Afternoon." Ya amsa kawai. Shagwabe fuska ta yi tana, "I Call You but you didn't pick Why?, i just want to hear Your Sweet Vioce, nikam ko laifi Nama ne?" Tana ta surutun ta yana ji amman hankalin sa baya kanta kuma bai da niyar bata amsa. Ta ci gaba da magana. , "Wai yaushe zaka gabatar masu da cewa nice zaɓinka ne? Nikam na matsu ina so ayi adaura mana aure." Sai a lokacin ya juyo ya kalleta cike da mamaki ya ce, "Aure? Dawa?" "Da kai mana, ka san dai nice babbar 'Ya mace kamar yadda kake namiji So mu muka fi dacewa da juna ni yanzu ma da zaka barni dawowa nan part din zanyi ya yi mun kyau gaskiya in munyi aure zanji dadin zama anan Sosai." Ganin bai da niyar kara kulata ta fara mannewa a jikinsa tana magana cikin sanyayyar murya. Prince Adeel ya yi saurin....... Comments,Share&Like, Fisabillah.😻🙏 08103080717 Urs Xayyeesherthuo [8/7, 9:47 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: https://chat.whatsapp.com/C1kXo17nLmb7vCXlubtu5o *AUREN WATA BAKWAI* *NOBLE WRITERS ASSOCIATION* © *Xayyeesherthul-humaerath* Page-9&10 Ya yi saurin kauce mata yana zame jikinsa. Kara damƙosa tayi ta ce, "Please Just Once Prince." "Stop it, i said stop it Nasmah, bana so ki je Ki tafi Don Allah inna gama aiki zan nemeki da kaina." Murya a shagwabe ta ce , "Promise?" Girgiza mata kai ya yi kawai yana gyara zamansa. "Alright ga abincin ka nan byebye." Ta fada tana kokarin fita. Har taje bakin kofar ta dawo, rungumesa tayi tana kissing dinsa sannan ta raɗa masa a kunne, "For me, you're like a lethal deadly drug. Once taken, you're addictive,I Love You So Much Darling Prince." Ta

Chapter 2 of 5