An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
[8/7, 9:47 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *AUREN WATA BAKWAI*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*
*© Xayyeesherthul-humaerath*
*Dedicated To NimcyLuv*
_*Auren Wata Bakwai!* daga jin sunan kun san cewa za ayi cakwakiya Iya cakwakiya,ba zan dai baku satan amsa ba, kar ku bari a baku labari, wacce ta karanta ta huta.😻_
Page-1&2
*MASARAUTAR BENONI*
Ihu take da magiya hannunta rike da get din shiga masarautar tana jijjigawa ,"Useni aççe am mi nasta,Hokkam dama je Karshe useni,Don Allah ku barni in shiga Inga Yareema,ku bani dama ta karshe,Miyida misandiri denyo 'am,Ballite yonki am, Baffana zai mutu, ku taimakawa rayuwata."
kuka take na fita a hayyaci.
Tana fada cikin muryar fulatanci wacce daga ji zaka Tabbatar da cewa hausar bata isheta ba.
Daya daga cikin dogaran ya ce, "Karya kike, Mayya anaci,turo ki akayi ki cutar mana da yareema."
Yana fada suna janyeta daga jikin get din tana kara kankamewa.
Ta ce, "Aradun Allah,na Rantse ba abun da zan wa Yareema, taimakonsa nake nema, Don Allah ku barni."
Bulala suka shauɗa mata wacce ta kara hargitsa mata tunaninta wani irin tsalle tayi ta dire da gudu tana neman hanyar gudu.
Wata farar mota ce kirar MERCEDES-BENZ ML350 ta tawo a hankali.
Adnan dake gefen glass yana hangota cikin sauri ya ce wa Driver ya dakata.
Ya na tsayawa Adnan ya fita yana, "Kee! Kee."
Idonta a rufe ta daura hannu akai.
Jikinta na rawa.
Yarinyace da bata zarce shekara Goma sha hudu ba, sanye da kayan fulani, duk ya fita a hayyacinsa kamar yadda ita ma ta fice a hayyacinta,kallo ɗaya za ka yi mata ka tabbatar da cewa tana cikin wani mawuyacin yanayi,ko dankwali babu akanta, gashi duk a cucure ga yawo da santsi, Dogowa ce siririya mai dirin Fulani,ba a sata sahun farare can can ba kuma baza asata sahun bakake ba,duk da yanayi na tashin hankalin da take ciki hakan bai hana bayyanar da kyawunta ba.
Karasawa ya yi gabanta ganin kamar bata san yanayi ba ya cire hannunta da ta rufe fuska da shi.
Cike da mamaki ya ce, "You ,?
Cikin isa da kasaita gami da Izza ta jinin sarautar da ke yawo ajinin jikinsa duk wata ilhama da kamala ta bayyana a tare da shi, Prince Adeel Muhammad Rohaan ya fito a motar ya yin da aka bude masa.
Cikin second guda ga gukkan kwayar Idon da ya kallesa zai fahimci tsantsar jinin sarauta ne anan wanda Ubangiji ya tsara masa hallita mai cike da kwarjini da Izza, Fatar jikinsa bakine ba irin sosai dinnan ba,baƙi mai kyau da sheƙi,ga idanunsa da suka kasance Sexy Eyes da ke birkita yan mata, yana da fadin kirji da duk wani abu da 'Ya mace ke bukatar kasancewa ga Namiji ko ince fiye da haka ma.
Kananun kayane a jikinsa kamar yadda ra'ayinsa da tsarinsa yake baya taba sa kayan sarauta har sai in da wani dalili wanda ya zam dole.
Saukarsa kenan daga America wanda ba kowa ke sanin shigarsa da fitarsa ba domin tsaro.
Driver bai ajiyesa a ko ina ba sai daidai kofar part dinsa dake ta bayan masarautar kebantacce wanda ba kowa yasan da nan din ba.
Yana Parking ya fito ya Bude masa kofa cikin hanzari.
Tafiya yake tamkar ba zai taka kasa ba.
Shigewa Adeel ya yi kaitsaye ba tare da ko kalli inda Adnan yake ba,bare har ya yi tunanin yi masa magana ko jiransa.
Adnan ya gyara tsayuwar sa ya na kare mata kallo ya ce, "What is your Name?"
Zaro masa manyan idanunta da taci kuka ta koshi ta yi.
Ya ce, "Oh Sorry Ya Sunan ki?"
Cikin Muryar fulancinta da gurbatacciyar hausarta ta ce, "Zainab a rugar Jauro ana she mun Gaaji."
Adnan ya ce, "Alright biyo ni mu je." Ya karasa maganar yana mata nuni da hannu.
Bayansa ta bi tana kalle kalle har suka shiga cikin bangaren Adeel.
Kai tsaye bangaren Prince Adeel suka nufa cike da mamaki take kallon wajen tamkar wata duniyar a zuciyarta take rayawa, "Oh ba don na san ban mutu ba nace nan shine Aljannata yadda Baffa yake fadamun anya ma aljannar takai nan ko?"
ADEEL na zaune a parlour ya dan kishingida zama irin na sarauta.
ganin Adnan da Gaaji kawai sai ya tsaya yana kallon su ba tare da ya ce komai ba cike da mamaki.
Adnan ya kalli Gaaji laɓe a bakin kofa duk alamar tsoro ya gama tattara game da ita.
Ya ce, "ke ya kika tsaya abakin kofa bakya tunanin za a dake ki ne?"
Fashewa ta yi da kuka.
Ta ce, "Don Allah ni taimaka mun Baffana zai mutu."
Adnan ya juyo yana kallon Prince Adeel ya ce, "Exactly da Mamaki,meyake faruwa ne? ni dai san zuciyarka irin haka ba."
Prince ADEEL ya bi sa da ido kawai ba tare da ya ce komai aransa yana so ya yi magana,amman saboda isa da Izza irin ta jinin sarautar da ke yawo a jinin jikinsa ya kasa furta komai illa yanayinsa da ya canja na bayyanar da ɓacin rai.
Adnan kuwa sanin halin abokin nasa sarai yasa bai damu da shirun nasa ba ya ci gaba da magana.
"Atlest koda zaka daina taimakon al'umma, wannan ya zama taimako na karshe da zaka yi, sai ka ga Ubangiji ya kara buda maka hanyar samunka,idan ka taimaki wannan fulani girl din,ba ka san wani hali take ciki ba,da condition din da mahaifin nata ya shiga ba,tunda ka ga har ta nace zuwa wajen biyar, tana zuwa neman taimako baka saurarenta kana wulakanta ta,Don Allah ka taimaka ba don halinta ba, kuma ba don ta isa ba,sai Don Allah,da kuma darajarata na abokinka da nake rokonka."
A fusace Adeel ya juyo yana, "Kai Mahaukaci ne,ko mahaifiyata bata taba shigo mun parlour ba,amman kai ka dauko wata kazamiyar fulanin yarinya ta shigo mun parlour."
Yana gama fadan hakan ya yi shiru.
Adnan ya ce, "Ai awajen Ubangiji da kai da ita duk dayane babu bambanci, kawai dai anan kai mai kudi ita talaka,kai mai mulki ita baiwarka,so shine bambancin kuma ya zame maka dole ka taimaketa."
Rai bace Adeel ya furta abun da bai taba furtawa ga duk wanda ya nemi taimako gunsa, "BA ZAN TAIMAKA BA, may be ma uban nata mutuwa zaiyi,ka fitar mun da wannan kazamiyar yarinyar daga part."
Nan Shi ma Adnan rai ya baci cikin fushi ya ce, "ba zan fitar da ita ba,in kanaso ka tashi ka fitar da ita da kanka ta karfi in zaka iya ko kuma ni ka dakeni ka sa in fidda ta."
Girgiza kai Prince Adeel ya yi ya sunkuya yana wuce tare da kokarin danne fushinsa a zahiri.
Sai da suka haura sama sosai, ita kuwa Gaaji mamaki take tana kallonsa cikin ranta take sakawa daman akwai mutumin da zai iya yiwa dan uwansa mutum fatan mutuwa? Kenan zuwa zaiyi har rugar su ya kashesa? Ban da haka don kawai baffanta na kwance bai da lafiya sai yana yi masa fatan mutuwa? Wani abu take ji na yawo a cikin ranta na rashin son ganin Prince Adeel bata san miye tsana ba Amman ji take ta washe sa kamar yadda ta washi mutuwarta.
Shiru suka yi dukan su na yan mintuna
Sai da ya ja numfashi kafin ya ce zan iya taimakonta in ta yarda Amman da sharadi zan.....
Ya yi shiru nan zufa ta fara keto masa tamkar mai nakuda.
Ya yi shiru.
Adnan ya ce, "Kai muke sauraro fa kuma yi shiru."
Goge zufar da ke kokarin jika masa jiki ya yi ya ce, "Zan... Zan....zan Aureta na tsawon Wata Bakwai kawai in ta yarda, Ana daura auren zan biya ko million nawa ne a fidda mahaifinta waje a masa magani,sannan duk inda wata bakwai ya yi zanyi signing a takadda in saketa."
Cike da mamaki Adnan ya ce, "Aure? Kuma wannan? Prince,Why?"
Da hannu ya masa alamar dakatarwa kawai ba tare da ya ce komai ba.
Gaaji ta kallesa ta yi tsalle ta diri tana, "ni? Aure ka? Inma kai mai yankan kai ne ki yanka ni? Cab Allah Saa'anam mi yiɗa ma. Allah ma ya sutura ni bana shonka."
Murmushi Adeel ya yi yana mamaki wai wannan yarinyar ce ke cewa bata sonsa, shi da yan mata ke bi amman wannan kwailar kazamiyar ce ke cewa bata sonsa.
Tashi ya yi ya shige ciki yana, "In ta yi tunani to,in kuma so take Mahaifin nata ya mutu fine wannan ba damuwata ce ba,ban da hadi da shi."
Adnan zai mata magana kenan ko tsayawa batai ba ta fice a zuciyarta tana sakawa,me ma zata yi da wannan wanda yake yiwa Baffanta fatan mutuwa.
da take ji hanjin cikinta ban da kadawa ba abun da suke.
Waige-waige take ko zata samu abun taɓawa ban da ruwan wani kogi ba abun da ta samu.
Haka ta tsaya bakin kogin tasa hannunta ta dibo ta sha sannan ta ci gaba da tafiya.
Tsakanin Rugar Jauro da cikin gari sai anyi tafiya ta kusan minti arba'in ko fi ma wani zubin akanyi awa guda indai tafiyar kafa ne,domin mota bata shiga Rugar har sai ranar kasuwa kadai sau daya a sati.
Tun tana tafiya da kwarinta har sai da ta koma jan kafa a haka ta isa rugarsu.
Shigewa bukkar su tayi jiki a mace.
Numfashin da taji na tashi sauri sauri a cikin bukkar yasata saurin karasawa ciki.
Aiko baffanta ne ranga-ranga jiki ya kara tsanani tuni ta birkice ta ma rasa abun yi tamkar za a zare ransa.
Ta kasa yi masa komai ban hawaye da ke ambaliya daga idanunta.
Ficewa tayi da wani mugun gudu.
Tuni har ta manta gajiyar da ta kwaso a hanya.
Gudu take ba kakkautawa ta fadi ta kurje ,ta kara tashi bata fasa ba,har saida ta isa cikin gari tsabar sauri a minti talatin ta isa.
tana zuwa kuwa
Bangaren Prince Adeel ta nufa kai tsaye da mugun gudu kasancewar babu kowa agun.
Tana shiga ta na numfarfashi daga kan da zata yi ta ga abun da kara firgitata tuni jikinta ya dau kyarma.
Price Adeel ne kwance da wata matashiyar budurwa suna Wasanni, babu komai jikin budurwar shi kuwa daga shi sai gajeran wando.
Jikinta ne ya fara karkarwa ta kasa motsawa tsabar tsorata bata san lokacin da ta sake fitsari ba.
Sautin Numfashinta na kara fita da sauri-sauri
Dogowan da zaiyi suka hada ido da ita nan fa ta kara firgita ta ja kafa zata gudu.
Wata irin tsawa ya mata yana janyota, "Mene ne ke kuma?" Ita ma budurwar sai a lokacin ta juyo tana kallonta."
Cikin yanayin firgici ta ce, "Naaa,naaa,naaa ga fada kuna yi ne na zo na fada ma na amince ne,na yarda."
Like, Comments And Share Please😻🙏
08103080717
Xayyeesherthul-humaerath
[8/7, 9:47 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *AUREN WATA BAKWAI*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*
*© Xayyeesherthul-humaerath*
Page-3&4
Tashi ya yi daga Kan Safina Yana kokarin janyo rigarsa ya sa.
Ita kuwa wani irin takaicine ya turniketa da jin tsana cike da haushin wannan gazamiyar yarinyar da ta katse mata jin dadi, domin har cikin ranta ta gama kudurta cewa lallai yau sai tayi nasarar kasancewa da Prince Adeel amman sai dai kash wannan yarinyar ta hana hakarta kaiwa ga ruwa.
Cikin kasalalliyae muryarta ta ce, "Prince ina zaka kuma? Me wannan yarinyar take anan kasan fa bamu gama ba kuma?"
Ko kallon inda take baiyi ba take ya shige toilet, ganin hakan tasan sarai ba zata taba samun kansa ba yasa ta tashi ta maida kayanta jikinta tana bin Gaaji da wani irin mummunan kallo.
Ita kuwa kanta a kasa bata ma san tanayi ba domin har yanzu jikinta rawa yake,karo na farko da ta fara ganin mace da namiji cikin yanayi irin haka.
Yana fitowa ya sanya riga sannan ya dauki Wayarsa ya kira Shamaki ya sanar da shi ya je bangaren Uwar Soro.
Sanan ya kira Adnan ma a waya ya fada masa.
Tashi ya yi sai da yaje har kofa zai fita kafin ya juyo ya ga tana tsaye ya mata alama da hannu kan ta biyosa, sannan ta bi bayansa.
Ɓangaren Uwar Soro dake daf da bangarensa suka nufa wanda yake shima keɓantacce ne ban da Yarima ba mai zuwa in ba da wani babban dalili ba, kasancewarta wacce ta raine shi tun yana karami har kuma ya girma a yanzu babu mai sanin sirrinsa fiye da ita.
Yana shiga ciki Gaaji ta bi bayansa da mamaki Uwar Soro take binsu da kallo daga shi har gajin cikin sauri ta gyara zama tare da amsa masa sallamar da ya yi.
Yana zama sai ga Shamaki da Adnan sun shigo.
Bayan sun zo duka ban da kallonsu babu abun da Prince Adeel Ke yi.
Har cikin ransa yana jin nauyin furta masu abun da ke zuciyarsa ta wani fannin yana jin cewa hakan ba karamin kaskanci bane garesa,amman ya zaiyi? A tunanin sa hakan dai shine kawai mafitar da zai dakile duk wata kofa da ke kokarin bude masa.
Zufa ce ta ci gaba da keto masa tamkar ba yanzu ya fito daga wanka ba.
Adnan ya ce, "Prince, ka kiramu kuma ka yi shiru Go On Please."
A gajarce ya ce, "Daura mun Aure da wannan Yarinyar za ayi."
Cikin yanayi na Mamaki Uwar Soro ta ce, "Ran Yareema ya dade, Aure kuma wannan? Ina tunanin in ma itan kake so akwai bukatar a gyarata kuma a Yantata daga baiwa tukunna kafin a gabatar da ita ga MAI MARTABA da FULANI."
Dakin ya dauki shiru na kusan Second Arba'in kafin Prince Adeel ya kara da, "A haka za ayi, ba tare da sanin kowa cikinsu ba, kuma a yanzu nake so a gabatar da komai."
Dukkannin su suka koma kallon kallo.
A ƙarshe Adnan ne ya katse shirun da fadin, "Shikenan Shamaki ki kira liman yazo."
"An gama ranka ya dade."
Shamaki ya amsa da haka ya fita domin kiran liman kamar yadda aka umarta.
Ba jimawa sai gashi da liman, Adnan ne da kansa ya sanarwa da Liman dalilin kiransa domin ya san in Prince ne zai kara magana sa gaji da zaman jira.
Ba tare da bata lokaci ba Liman ya aiwatar da abun da aka umarce shi da yi, Adnan ya zam Waliyin Amarya, Shamaki ya zama Waliyin Ango Bisa sadaki Million Uku wanda Adnan ke hasashen ya wadatar a fidda mahaifin Gaaji kasar waje har a kammala masa komai na bukata.
An daura auren amman har yanzu mamaki ya gagara barin zuciyar Adnan domin ya gagara sanin dalilin da zai sa Prince ya ce zai auri yarinyar nan wanda ya tabbatar da cewa koda kyauta aka basa bazai taɓa karɓa ba, mutum da a kullum ma bijirewa batun aure yake,tare da nuna cewa bai da lokacin tsayawa kula wata mata da niyar aure,dole akwai Dalili,to Amman miye dalilin?.
Ana kammala daurin Adnan ya ce da Uwar soro , "Baba zamu tafi yanzu, ki ajiyeta agunki ana yi mata dukkanin abun da ya dace kawai."
Sun tashi zasu fita itama ta tashi tana kokarin binsu.
Rike mata hannu Uwar Soro ta yi da alamar su tafi Gaaji ta ce, "Aa Baffa, Baffana Yana shen."
Adnan ya juyo yana, "ki zauna anan kinji zamu je akai Baffanki gun mai magani ne yanzu In Sha Allah."
Haka ta bita ba don ta so ba zuciyarta fal tsoro kar suje su kashe mata baffa tunda daman Yareema ya fara yi masa fatan mutuwa, ita kuma su cinyeta.
A cikin Part din ta shigar da ita wani dake, dake babban wajene tamkar gida guda wanda ciki da wajensa ya tsaru cikin ƙawa tamkar wata duniya ta daban.
Ko da suka shiga dakin kara binsa da kallo kawai Gaaji keyi tana mamakin kasancewarta a gun shin da gaske nan kuwa duniya ? Cai wannan duniyar inaga dai wacce ake zuwa lokacin da mutum zai bar duniya ne.
Abun da take ta radawa aranta kenan.
Uwar Soro ce ta katse mata tunani tare da fadin, "Ranki ya dade mu shiga banɗaki na haɗa miki ruwa zan miki wanka."
Binta da wani mugun kallo tayi tana zare ido, wanka kuma? Ita ai ta jima da manta cewa ana wani abu wai shi wanka,ko da baffanta ke lafiya ma ita sai ranar sallah kadai suke wanka a rafi da sauran matan karkararsu, wannan shekarar kuwa da yazo bai da lafiya ko yi bata yi ba,bare kuma yanzu da ba sallah ba mai zai kaita yin wanka? Katse tunanin tayi da furtawa a zahiri, "Cab Wanka? Aradun Allah banyi haka kawai ba sallah she tazo ba zaki ce nai wanka? She kace fara?"
Uwar Soro ta ce "Ranki Ya Dade ai ba sai agwagi ne masu wanka ba, hakan tsaftane da tsaftace jiki,kuma kin ga Yareema Baya son kazanta ba za kuna shiri ba in bakya wanka zai ce ma baya sonki."
Gaaji ta cuno baki ta ce, "Ni bana shon shi daman ai tunda yake yiwa Baffana fatan mutuwa kuma sai dai shi ya mutu ya bar mun baffana raye."
Dakyar ta samu ta shawo kanta tare da Tabbatar mata cewa in bata yarda an mata wanka ba Yareema ba zai kai Baffanta a masa magani ba.
Suna shiga Toilet din ta fara ihu tana, " nan ai ba gun wanka ne ba ni ki barni kawai ai Dauɗa karin karfine karki ragemun karfina a dakeni in kasa ramawa."
Uwar Soro ta ce, "nan ne ban dakin wanka anan duk haka suke,kuma in kika yi wankan ma kara karfi zakiyi saboda muna da sabulu mai kyau."
Haka ta tuɓeta da kyar tana sa mata ruwan zafi a jiki ta kara sulle mata tana ihu, "Zaki karni ne Baba, na shiga ukuna ni Gaaji zata ƙona ni."
Haka sukata fama tana gudu tana binta har aka rage daudar dan ba ace ta fita duka ba,kanta kuwa kin yarda ma tayi a taɓasa sam bare a wanke.
Suna gamawa ta dauko sabon brush tasa mata toothpaste ta ce, "Yawwa ungo wanke bakinki."
Tana karba ta suɗe toothpaste din tas ta shanye ta fara tauna brush din.
Uwar Soro ta bude baki, "Subhanallahi wanke baki ake ba sha ba fa." Karba tayi ta kara zuba mata wani sannan ta wanke mata bakin da kanta.
Ai kuwa datti kamar ruwan kasa jini ma bakin ya fara yi, tuni Gaaji ta rikice ta fara kuka tana ganin jiki ta ce, "Dok Allah karki shanye mun jinina kadan ne dani ba yawa kuma bai da zaƙi ma Don Allah."
Sai da dariya ta kusan subucewa Uwar soro ta danne tana, "shikenan yanzu ga ruwa kuskure bakin,kar ki shafa,ki kuskurewa kawai."
Nan fa tana sa ruwa abaki ta shanye tana, "ita ba zata zubar da jininta a banza ba ta mutu."
★★★CIKIN GIDA
FULANI ce kishingiɗe a parlour hannunta dauke da tuffa tana ci a hankali, gabadaya yanayin fuskarta sam babu walwala kallo ɗaya zaka mata ka tabbatar da cewa tana da damuwa cikin ranta.
Jakadiyar ta dake gefe tana lure da hakan ta ce, "Ranki Ya Dade Fulani lafiya kuwa?"
Ta ce, "Jakadiya kira mun Hajiya Maimuna."
Tashi tayi ta je ta kirata cikin sauri.
Hajiya Maimuna wacce take Aminiyar Fulani kuma mata agun Kawun Mai martaba ce ta shigo bangaren Fulani kamar yadda ta samu kira daga gun Jakadiya.
Zama tayi tana fadin, "Ranki Ya Dade na amsa kira, amman ya na tarar da fuskarki ba walwala fatan dai muji Alkairi."
Jakadiya na fita ta laɓe abakin kofa tana sauraren abun da Fulani zata ce.
Numfasawa tayi tana gyara zama, "Maganar Yareema ne, kina ganin kullum mai martaba kara girma yake,kwanaki na kara ja, lokacin murabus dinsa na ta kara tawowa, tsufa ya kamasa, amman Yareema sam yaki mai da hankali kan batun aure kuma kin san ba makawa shi za a daura, ba ma wannan ba ni kaina ina bukatar ganin wata wacce za ace sirika ce gareni ta haifa mun jikoki, yanzu haka fa ya kusa cika Shekara talatin a duniya."
Murmushi Hajiya Maimuna tayi ta ce, "indai Don Wannan ne ki daina damuwa Uwar giyata,ina tunanin kawai za a shirya yi masa auren ba zata ne kawai ba tare da saninsa ba kuma ba tare sanin kowa cikin Masarautar nan ba, Mai martaba kawai zaki sanar a shirya bikin na Tabbatar da cewa Yareema ba zai taɓa bijirewa zaɓinku ba amman kafin hakan a gwada tuntubarsa na ƙarshe ko yana da wacce take zaɓinsa,in ya tabbatar da cewa babu kawai sai mu shiga shirye-shiryen abubuwan da ya dace kuma a zaɓo matar data dace."
Gyara zama fulani tayi tana sakin Murmushi ita ma ta ce, "Maddallah da ke Hajiya Maimuna babu shakka hakan za ayi domin kuwa shine mafita kawai, amman Babbar Matsalar ma ban san ko yana gari ba, zan binciki Uwar Soro muji."
Jakadiya na jin motsin Hajiya Maimuna ta wuce da gudu ta nufi dakin Fulani Kilishi.
Amarya ga Fulani Babba wacce take ita ma mata ce ga Mai Martaba ta biyu.
Tana ganinta ta daka mata tsawa, "Ke Lafiya zaki shigo mun daki haka? Kina da hankali kuwa?"
Ta ce, "Ranki Ya Dade labari na samo miki ina so Hajiya Maimuna ta wuce ne kada ta ganni."
Tsaki ta daka mata tana fadin, "Oya ni fadamun to ."
A hankali murya irin ta munafukai ta ce, "Za ayiwa Yareema auren bazata ance ba wanda zai sani sai Mai Martaba da Fulani Babba."
Wani irin Murmushin takaice ..... Ta yi, "Aure? Wannan zance ne, hakan ba zai taɓa yiwuwa ba ma kada ki damu ni na san matakin da zan dauka,bama wannan ba , shin wa za a aura masa?"
Jakadiya ta ce, "basu kai ga fada ba,sun dai ce za a duba."
Dariya ta fara wacce azahirine kadai take dariya a zuciyar ta kuwa ban da tsantsar mugunta babu abun da ke ciki.
"In an fada yarinyar ki zo ki sanar mun, ba wanda ya isa aiwatar da komai cikin Masarautar nan ba tare da sani ba, don ban haihu ba hakan baya nufin in zam saniyar ware ahir."
Jakadiya na fita ta kara nufan bangaren Hajiya Rabi wacce take kishiya agun Hajiya Maimuna ta sanar da ita.
Tsaki Hajiya Rabi tayi tana fadin, "Lallai kuwa za a sha mamaki cikin Masarautar nan, Mussaman in ya kasance ba ɗaya daga cikin 'Ya'yana za abaiwa Yarima ba saidai kowa ya rasa ko ya mutu ko