Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na gani a ɗakin sa yace min wata ce ta bashi na bikin yayarta ne"

Abba ya kalli Ammar yace "A ina take kuma 'yar waye? Meye haɗin ka da ita har da zata baka wannan kayan haka?"

"Abba wallahi bakomai a tsakanin mu, kawai na ɗauke ta ne ta bar kayan ta a Napep ɗina, shine na kaima ta, ta bani katin ɗaurin aure, yau da naje shine ta bani wannan kayan" ya ƙarasa maganar yana ɗan ɓata rai.

Abba yace "Ammar ka gayamin gaskiya, ba ina maka haka ne dan in ɓata maka rai ba ina gaya maka gaskiya ne, idan kuna son juna ne in shige gaba in tambayar maka, Ammar ya kamata ka ajiye iyali, ba seka tsofe a titi ba"

Da sauri Ammar ya kalli Abban sa yace "Abba yarinya ce fa ƙarama, Halima ta girmeta sosai, da shekaru na in auri 'yar mitsitsiyar yarinya ko fa secondary bata gama ba zaman Aure zanyi ko kuma raino?"

"Rufemin baki, meye a ciki zaman aure ba' a shekaru bane, kaiwa kanka faɗa dai wallahi"

Se yanzu maman Ammar tace "Malam dan Allah kayi haƙuri, shi Aure lokaci ne"
"kullum haka kike cewa shiyasa yake ƙin auren yake ƙara sangarcewa"

********************

Sosai Mufeeda take kewar yayarta Amina, gefe guda ga son Ammar dake ƙara mamaye zuciyar ta ba tare da sanin ta ba, da farko dai niyyar rainawa Ammar hankali tayi amma tunda ta tambayi uncle ɗin ta ya tabattar mata da alamomin da take ji game da Ammar alamomi ne na soyayya, duk wanda yace yana son Mufeeda daga lokacin zata dena ganin mutuncin sa ta tsane shi, Amma yanzu soyayya ta mata mugun kamu.

Dukda tana da lambar wayarsa amma tana fargabar kiran sa, dan da alama baya son raini, ɗan haɗuwar da suka yi bata taɓa ganin dariyar sa ba, tana tsoron karta kira ya yarfata, wanda babban abunda ta tsana a rayuwar ta be wuce a dizgata ba.

Tunani duk yabi ya addabe ta, ta ɗanfi jin daɗi idan taje makaranta amma da zarar ta dawo duk se walwalarta ta ɗauke, da Mamanta ta zata kewar Yayarta ne yake damun ta kafin daga bisani taga damuwar tata kaman ƙara yawa take.
****************

Kamar kullum Mufeeda taje makaranta amma abun mamaki yau babu sunan ta a 'yan surutu, babu' yan makara tsit kaman bata ajin, kusan kowa yasan ta a makarantar nan mussman saboda laƙanin ta na professor, ga rashin ji duk wani laifi da ita a ciki, wani lokacin ko laifi akayi aka rasa su waye se asaka sunan ta, wasu malaman kance professor marasa jin magana.

Aka tashi daga makaranta zasu tafi gida ita da fati da yake hanyar su ɗaya, Fati tace

"Mufeeda wai me yake damun ki ne? Ko baki da lafiya ne?"
Girgiza kai Mufeeda tayi tare da ajiyar zuciya tace
"Fati ni abunda ke damuna ba zaki iya maganta min ba"

"to gayamin inji meke damun naki?"

Taja Fati suka tsaya jikin wata bishiya sannan ta kalle ta

"Fatee ina missing ɗin Yaya Ammar sosai, tun ranar da yazo ɗaurin Auren Yaya ban kuma saka shi a idona ba, wallahi duk inda na zauna tunanin sa nake"

Wani dogon tsaki Fati ta ja tace "ke kam anyi wahalalliya, daga haɗuwa da mutum a titi shikenan se kuma ki dinga tunanin sa, to me kike nufi da hakan?"

Mufeeda tai murmushi tace "tabbas son Yaya Ammar nake kaman yanda alamomi suka nuna"

"Taɓɗijan amma kinci kai wallahi, tashi mu tafi ni rana ta nayi"

"Fati idan har baza ki tsaya ni neman mafita ba karki ƙara tambaya ta meke damuna, kuma ki yi tafiyar ki dan sena gama tunani zan tafi"

Tausayin Mufeeda ne ya kamata dan iya sanin ta da ita idan mutum yace yana son ta shikenan ta samu abokin gaba, Amma yau da kanta take furta ta faɗa soyayya in dai hakane to tabbas dagaske take.

Cikin kulawa fati tace "Mufeeda bazan iya barinki cikin damuwa ba, Amma ta yaya zaki cigaba da son mutumin da kuka haɗu a titi, ke kike sonshi ba shi ke sonki ba"

"waya gaya miki baya sona? Ke nifa harna faɗa a gidan mu shi nake so"

Ɗan zaro ido fati tayi tace "to shi yace yana sonki ne?"

"oho masa inma baya sona ni dai ina sonshi, tashi mu tafi gida kar Mama taimin faɗan nata akan na daɗe"

Suka tafi ba tare da Mufeeda fa kuma cewa komai ba.


Yanzu ma a kwance Mufeeda take tana jujjuya wayar ta, tana kallon Lambar Ammar da ta rubuta Yaya Ammar ɗina, ta rasa ta inda zata fara, ita dai bata taɓa soyayya ba, bata san ya take ba amma tana ganin wasu sunayi a lissafin ta yau sati uku rabon ta da Ammar, Amma kullum ta rufe ido shi take gani.

Zuciyar ta ta dinga bata shawarar ta kira lambarsa taji ko yana lafiya?

Danna lambar tasa tayi taita ringing be ɗauka ba, ta sake gwada kiran wannan karon ya ɗaga cikin muryar sa me kama da ta me Izza yace "Asslam Alaikum, a kira anjima zanyi salla ne"
Lumshe ido tayi jin muryar sa tasa ta sakin murmushi, ba tare da tace komai ba ya yanke wayar.

Miƙewa itama tayi ta gabatar da sallar isha'i ta nemi Abincin dare taci seda ta gama abunda take ta hau kan gadon ta ta kuma kiran Ammar, seda ta kusa yanke wa sannan ya ɗauka tare da yin sallama.
Se Ajiyar Zuciya take amma ta kasa cewa komai
"ina ji wake magana"

"Yaya Ammar nice" tana magana gaban sa ya faɗi, yaji ƙirjinsa na bugawa da ƙarfi, shi yama manta da yarinyar nan amma ya ƙara tsuke fuska yace
"Ke wa?"
"Ƙanwar ka ce Mufeeda"
"Ya a kayi?"
"Na kira in gaishe ka ne, ka manta dani"
"to Nagode ki gaida mutan gidan" ya katse kiran, Zuciya ce ta ɗibi Mufeeda saura ƙiris ta yi jifa da wayar ta amma ta fasa, ta ji haushin abunda Ammar yayi mata sosai tunanin mene mafita ta shiga yi ta nawa kanta tambayar

"dama haka soyayyar take? Wahala da ɓacin rai, ji yadda raina ya ɓaci a banza, da ina zamana lafiya nikaɗai Amma tunda na haɗu da kai na rasa nutsuwa ta, kai kuma kana can kana hutawar ka, kalli yadda ya amsa min waya, na kira shi dan inji sassauci amma ya watsan ƙasa a ido, aikam baka isa ba dani kake zancen bazan sha wannan wahalar nika ɗai baZan nuna maka WATA KISSAR... (SAI MATA) "
haka ta ci gaba da surutu kamar taɓaɓɓiya har Mama ta shigo ɗakin tace
"ke Mufeeda surutun uban me kike ne haka?"
"bakomai Mama"
Ƙarasowa Mama tayi gefen gadon Mufeeda ta zauna tace
"Mufeeda ki gayamin meke damunki ne? Tun bayan bikin Amina na lura kin zama wata iri, gayamin mene ne?"
Ai kaman Mama ta sosa mata inda yake mata ƙaiƙayi ba fargaba kanta tsaye tace
"Mama Yaya Ammar ne"
"Waye kuma hakan?" Mama ta tambaya
"Mama me A daidaita sahun da ya kawomin kaya na"
Ɗan ƙara nutsuwa Mama tayi tace "Me yayi miki?"
"Mama tun ran bikin Yaya ban kuma ganin sa ba fa"

A fusace Mama ta kalleta tace "idan kika bari na tashi sena samo Madoki nazo na casaki a gurin nan, jimin Shashar yarinya, yarinya ƙarama dake kike wani zancen kina son wani ƙwaya nawa kike? Ki maida hankali akan karatun ki ki bar zancen wannan yaron in ba haka ba ni da kene"

Cikin shagwaɓa tace

"Mhmm Wallahi Mama ina son Yaya Ammar ɗina ni ba wani karatu da zan iya idan wata ta rigani Auren sa fa? dan Allah Mama ina candy ni Aure zanyi na ci gaba idan nayi Auren"
Riƙe haɓa Mama tayi tace

"Mufeeda rashin kunyar taki har ya kai ki kalli tsabar idona kice min ke ba zakiyi karatu ba Aure zaki yi, to yanzu in gaya miki mace mai Ilimi tafi daraja a gidan Aure"

"Haba Mama kefa kika ce bamu da sama dake duk abunda ke damunmu mu gayamiki ko mu tattauna a tsakanin mu, baki yadda wani yaji sirrin mu ba, ke kikace babu kunya tsakanin mu dake, Amma na gaya miki abunda nake so se hantara ta kike yi, kuma da su Yaya ne ba haka zakiyi musu ba"

Mama tace "Hakane Amma, ke kin san meye Aure kuwa? Mufeeda har yanzu ba ki gama hankali ba, kinyi ƙanƙanta da Aure, tsaya ma idan an miki Auren me zaki je kiyi? Me yasa kike son yin Auren?"

Seda Mufeeda ta kusa ƙyalƙyalewa da dariya, a ranta tace
"Mama me kika ɗaukeni ne" Amma ta maze  tace
"to Mama Auren wani abune me wahala, ba Kawai in dinga dafa masa abinci bane, yi nayi bari na bari da akai ta gayawa Yaya Amina, nifa wallahi kawai son Ammar nake, kar wata ta rigani auren sa"

Miƙewa Mama tayi tace
"baki da hankali, shi kansa Auren baki san menene ba, babu uban da ze miki Aure yanzu, tun wuri ki ɗakko litattafan ki ki ci gaba da karatu keda Aure se naga hankali ya gama ratsaki, a yadda kike ɗin nan baza ki iya kula da miji ba"

Bayan Mama tabi da kallo harta fice daga ɗakin, murmushi Mufeeda tayi tace
"Mama kenan aikuwa zan baki mamaki, idan baki yadda ba zanje in yiwa Baba bayani nasan shi ze fahimce ni"
Wayar ta ta ɗauka ta shiga lambar Ammar ta tura masa saƙo

"Wulaƙanci be kamaci mutum me karamci da Amana kaman ka ba Yaya na, ka kula da wanda ya damu da kai, Allah yasa in ganka ko a cikin mafarki ne zanji daɗi Sosai.
Allah ya tashemu lafiya ya tsare ka daga dukkanin sharrin abun ƙi, a gaida Mamana.
Your sister Mufeeda"

Ammar na ɗakin Abokin sa Jabir da Aminu suna hira, shi Aminu yana da Aure shikuma Jabir ya kusa su Ammar kuwa ba labari, ƙararrawar saƙo ta buga alamar Saƙo ya shigo wayar Ammar, gaba ɗaya suka bishi da ido, wayar na gefen Aminu ya kalli screen ɗin wayar yace
"Ammar an turo maka saƙo kuma lamba ce"
Ammar ya karɓi wayar ya buɗe saƙon, juya saƙon ya dinga yi badan tasa sunan ta a ƙarshen saƙon ba cewa zeyi ƙaryane ba ita ta rubuta ba, wannan 'yar mitsitsiyar yarinyar ce ta zauna ta rubuta wannan saƙon?

shiru ya ɗanyi yana nazari kafin daga bisani ya aje wayar tare da jan gajeren tsaki.

Jabir yace "ya dai naji kana tsaki meye ya faru?"

Wani tsakin ya kuma yi sannan yace "wani shirme aka turomin"
"shirme kamar yaya? Waye ya turo maka?"

"Hmm wata fitinanniyar yarinya Allah ya haɗa ni da ita daga na ɗauke ta a babur ɗina duk ta addabeni"

Dariya Aminu yayi yace "Malam kaimana bayani kai tsaye, Ashe kawai mu fara tara kuɗin goro"

"Aminu meye haka? Yarinya ce fa ƙarama, kuma kasani bani da ra'ayin Auren ƙaramar yarinya"

Jabir yace
"kaifa abun haushin ka yafiye yawa, ƙaramar yarinyar wataran ba ita zata zama babbar ba?"

Aminu yace "ganemin hanya dai"

"Bazaku gane ba, bafa tafi shekaru goma sha biyar ba, in tayi wuta shekara sha shida, uwar me zanyi da Jaririya dan wannan bata isa zaman Aure ba se dai ayi rainon ta"

Wata irin dariyar ƙeta su Aminu suka yi Jabir yace
"Wallahi Ammar kai ba ƙaramin ɗan rainin hankali bane, to meye a ciki ka raine ta harta zama yadda kake so se kuyi zaman Auren"

"Allah ya kiyaye, wannan yarinyar me shegiyar tsiwa, tana magana kaman wata tsuntsuwa ga iyayi"

Aminu yace "Ahhh kaman tsuntsuwa yabonta fa kayi gaskiya ɗankwali ya ja hula"

Banza Ammar yayi masa ya haɗe rai a ransa yake tambayar kansa "dagaske yabonta nayi kenan?"

Jabir yace

"Abun mamakin ma Aminu shine ya akayi ta samu lambar sa?"

Aminu yace "ƙwarai kuwa, gayamana ta yaya tsuntsuwa ta samu lambar maza gumbar dutse"

Tsaki Ammar yayi ya miƙe ya ɗau wayar sa dan sun fara bashi haushi, dama gashi ba wuya yayi fushi.

Aminu yace "Ammar ina Zainab ne?" banza yai masa ya fice ya bar musu ɗakin.
****************


Mufeeda tayi sallama ɗakin baban ta yai mata izini ta shiga, ta shiga ta tarar da shi yana 'yan rubuce2,
"me girma professor barka da zuwa Auta na, ya akayi ne zoki zauna"
Ƙarasawa tayi kusa da Baban ta ta zauna, ta kalli Mahaifinta tace

"Baba na sirri nazo muyi da kai nasan zaka fahimce ni, ita Mama komai nayi laifine a gurin ta"

Murmushi yayi yace "Ai ta nayi ne saboda son da take miki"

"A'a ai kai baka yimin yadda take min, a hankali kake gyara min laifina banda Mama ta fiye faɗa, dama tunda bikin yaya Amina take jin haushi na, na gaya mata abunda ke damuna amma taƙi saurara ta"

Dattijon ya gyara zaman sa yace "Ina jinki Autana"

"Baba nifa na fasa zama wannan professor ɗin a yanzu"

"Meyasa?"
"Baba" sekuma tayi shiru
Baba yace "karki damu Baba ne fa, me zaki ɓoye masa, mun saba yin sirri mu tattauna karki ji komai gayamin"

"Yawwa baba na, dama.. Amm dama.. Gaskiya Baba ni idan nayi Candy.. Yaya Ammar nake so"

Shiru yayi yana nazarin ta sannan yai murmushi yace "Wannan me Napep ɗin?"
Da sauri tace "Yawwa shi Baba"
"Me yasa kike son shi, kuma kika zaɓi ki aure shi?"

"Baba yana da kirki ne sosai, kuma ni ban san yadda akayi na fara sonshi ba, kawai kullum in ta tunanin sa na tambayi uncle yace min wai sonshi nake"

Baba yakuma murmushi irin na manya sannan yace
"Autar Baba daɗi na dake faɗar gaskiya komai ɗacin ta, gayamin me yayi miki, ko me yake gaya miki haka daya sa kike sonshi haka, har kika janye ƙudurinki na zama professor?"

Nan ta kuma zayyane masa yadda ya kawota gida da zuwa bikin Amina da yayi.
"niba abunda yamin ko ya gayamin, yana da kirki ne, kuma ɗan gayu ne, ai ka ganshi ranar ko?"

Baba ya jinjina kai yace "hakane ɗaan gayu ne kam, yanzu idan kinyi candy aure zakiyi?"

"Baba zanyi candy kafin in cika shekaru goma sha bakwai ne, sefa na jira na shekara sha takwas zan shiga University, kuma gashi wasu suyita zagin matan da suke zuwa jami'a, ko kuma su dinga musu kallon marasa tarbiyya, Amma idan nai Aure sannan nayi karatun ai se anfi ganina da mutunci, kuma fa badan Ammar ina sonshi ba bazan ce zanyi Aure yanzu ba, kullum se naita tunanin sa nafi son in dinga ganin sa kullum"

Jinjina kai Baba ya dingayi sannan yace
" 'yar ƙarama me tunanin manya, maganar ki gaskiya ne Auta na, indai ze barki kiyi karatun ai babu damuwa, dama ita soyayya ai gamon jini ce, wani halinsa ne kawai zesa kaji kana sonsa, in dai yayi miki kuma nai bincike akan halayen sa na yadda da halayen sa babu damuwa kije ki gaya masa ina son ganin sa"

"to Baba nagode da fahimta ta da kayi sannan... "

Shigowar Mama ce tasa ta yin shiru, Mama ta Harare ta.
Mufeeda tace "Baba zan dawo mu ƙarasa zancen mu"

"to shikenan Auta na"
Ta miƙe ta fice.

Ta koma ɗakin ta tana ta farinciki, se kuma ta shiga zullumin me zata cewa Ammar wanda ze kai ga yazo yaga mahaifin ta har ya yadda da maganar auren su?.

"Taɓɗijan ga ƙoshi ga kwanan yunwa"

(Duk abun nan fa Oga Ammar bece yana son ta ba 🙄🙄🙄)



More Comments More typing. In ba comment zan aje littafin gaba ɗaya

Domin sharhi, gyara ko kuma shawara
A tuntube ni akan wannan lambar
What's App
Ayshercool
07063065680
✨✨✨✨
        *WATA KISSAR...... *
                  ✨✨✨✨✨

                      ( *Sai Mata* )

         

                        

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail Www.ayshertadam@gmail.com


                            Page 4


Juyi kawai Mufeeda take akan gado tana tunanin mafita, Amma ta kasa samawa kanta mafita, ji tayi kanta ya fara sarawa dan haka tai Adduoin ta na bacci ta rufe ido.


Maman Mufeeda ta kalli mahaifin Mufeeda tace

"Wai yanzu dagaske yarinyar nan zuwa tayi ta same ka akan maganar nan? Ban san lokacin da Mufeeda za tayi hankali ba, waya gaya mata zaman Aure aikin rago ne, guda nawa Mufeeda take da har zata tun kare ka da batun ita Aure take so"

Mahaifin Mufeeda yace
"Kwantar da hankalin ki maman yara, Abun ai duk bana zafi bane, ki sani tarbiyar da kika yiwa su Murja a zamanin su idan har kika ce irin ta zakiyi wa Mufeeda a wannan zamanin da muke ciki zata iya bijirewa"

"Hakane dan taurin kanta yayi yawa, halinta ya fita daban dana 'yan uwan ta kaman bani na haife ta ba, ace yarinya ba kunya sam"

Yai murmushi yace
"Karki manta a tarbiyar da muka yi wa yaran mu babu kunya tsakanin mu dasu, mun ɗora su akan kome ke damunsu game da rayuwar su mu zamana mune mutane na farko da zamu fara sani, karki manta kowace yarinya kafin in Aurar da ita babu wadda ban san date ɗin da take Al'ada ba, ni nake siya na basu abunda za suyi amfani da shi lokacin Al'ada, hatta ƙanan kaya inner wears ɗin su in sun lalace kai tsaye suke tunkura ta su gayamin haƙƙi nane inyi musu, kuma babu inda Addini yace hakan haramci ne, idan haka ne wace kunya kike tunani tsakanina da su? kin fi kowa sanin ban yadda da kunya tsakani na da 'ya' ya naba, basu da sama damu jansu a jiki da muka yi ne ya sa suke iya bayyana mana matsalolin su, me kike tunani idan har da kika gwale Mufeeda nima Gwale ta nayi? Tana kan ƙanan shekarun ta na Adolescent period komai ze iya faruwa musamman idan tana ta'ammali da gurɓatattun ƙawaye, inda na godewa Allah Mufeeda rawar kan ne kawai da surutu amma tana kula da kanta"
Ɗan lumshe ido Mama tayi tace

"Hakane Amma menene mafita? Tayi ƙanƙanta da Aure"

"Ke kike ganin tayi ƙanƙanta, a hirar da mukayi da ita na fuskanci cewar Ita ba wai Auren ya dame ta ba, tana ƙaunar yaron ne sosai, na bugi cikin ta inji ko wani ke zigata ko wani abun yaron yake mata take sonshi, kin santa bata rufemin komai, yadda na fuskanta Soyayya ce kawai, tana sonshi sosai kuma mafita ɗaya ce shine zan cewa yaron ya fito "

Da sauri Mama ta kalleshi tace
" haba shekarun ta nawa da za'a aurar da ita? Dr. kana kallon yadda nake fama da ita a cikin gidan nan ta yaya zata iya riƙe miji? Kuma karatun ta fa?"

"Sarat shekarunki goma sha huɗu nikuma ashirin da biyu muka yi aure, muna tare ki kayi karatun sakandire har zuwa diploma, ko kin manta? yadda kika iya riƙeni itama zata iya"

"Dr. Yanzu fa ka gama faɗin zamanin mu na da, da yanzu ba ɗaya ba, mazan yanzu ga rashin tabbas da rashin haƙuri ta yaya mufeeda na zata iya zama da miji yarinya ce ƙarama fa"

"Calm down my wife, muyi mata Addu'a, Soyayya ba ruwan ta da shekaru kin san a baya, ko zancen Aure bata so dan baya gabanta, da kanta tace tunda ni ban kai ga zama professor ba ita zata zama, tana son karatu matuƙa, Amma tunda tace yanzu ta fasa. kuma ta bani gamsassun hujjojin ta na son yin aure kafin karatu.
Kuma da yaro ƙaramine tace tana so nasan wannan shashanci ne, Amma naga yaron kaman yana da shekaru ba yaro ne ƙarami ba, muyi mata Addu Allah ya sanya musu Alkhairi "

Haka Baba ya ci gaba da rarrashin ta, yana kuma nuna mata illar rashin amincewa da bukatar 'yar autar tasu.

*****************

Ammar ya sai Sabuwar waya, ya maida simcard ɗin sa kai, yayi setting WhatsApp ɗin sa da sauran Abubuwansa sannan ya ajiye wayar ya kwanta.

Cikin Bacci Mufeeda ta farka da zazzafan zazzaɓi da ciwon kai, yamutsa fuska tayi ta juya da nufin ta ci gaba da bacci amma abu ya gagara, ta ture abun rufarta ta tafi banɗaki tayi wanka ta dawo ta kuma kwanciya tana tunanin zazzaɓin ze sauka.

Sosai zazzaɓin ke kuma hawan ta se rawar sanyi take yi, bata son taje ta ɗagawa iyayen ta hankali a daren nan.
"ko wayar Baba zan kirane?" ta faɗa a fili taita tunani ta rasa menene mafita.
Kasa komawa bacci tayi ta ɗakko wayarta ta ga ƙarfe sha biyu saura na dare.

Ta rasa lambar wa zata kira, data ɗin ta ta buɗe saƙonni suka dinga shigowa, ta shiga what's App ɗin ta tana duba contact, ba zato ba tsammani taga lambar Yaya Ammar ɗina tayi appearing a contact ɗin ta.
Da sauri ta miƙe zaune dukda zafin da jikin ta ya ɗauka, ta shiga kan hoton dp ɗinsa, tabbas shine hoton sa ne a tsaye a gaban Napep ɗinsa hannun sa ɗauke da makulli da handkerchief kalar kayan jikin sa, ya ɗanyi murmushi ba ƙaramin kyau yayi wa mufeeda ba, zooming ɗin hoton tayi tana ajiyar zuciya
"You are handsome my man" ta furta a fili tana kuma ƙare masa kallo, message ta tura masa

"Asslam Alaikum warahmatullah, Yaya Ammar dama kana what's App amma baka kulani ba?"

Ta ci gaba da kallon hoton sa, sannan tayi murmushi ta ajiye wayar ta kwanta, Amma bacci yaƙi zuwa tamkar jira zazzaɓin yake ta kwanta, kanta ya dinga sarawa ga cikin ta ya ƙulle yana ciwo, Nan ta dinga shrara kuka ita kaɗai a ɗaki, se juyi take ga Amai yana taso mata.

Wayar ta ta kuma ɗakkowa da nufin ta kira Mama a waya, amma tana cire key ɗin kan wayar ta hoton Dp ɗin Ammar ne bata fita ba.
Wani saƙon ta tura masa, Tana gama tura saƙon ta saki wayar ta faɗo ƙasa daga kan gadon daga nan bata ƙara sanin inda kanta yake ba.

*****************

Alarm ɗin Ammar ya buga ƙarfe uku na dare, ya miƙe ya shiga banɗaki yayi alwala ya zo ya tada salla, yai nafilolin sa ya ɗakko wayar sa ze karatun Al'qur'ani amma yaga data ɗin sa a buɗe messages suna ta shigowa.
Rufe data yayi ba tareda ya duba saƙonnin ba yai karatun sa be koma bacci se Da yayi sallar Asuba.

*************

Mufeeda kam se farkawa tayi ta ganta a gadon Asibiti an ɗaura mata ruwa, tana ganin haka ta fashe da kuka, Baba ya ƙaraso da sauri bakin gadon ta yana faɗin

"Sannu Auta na yi shiru kin gammu a kusa da ke, sannu ya jikin naki?"
Jinjina wa Baba kai tayi ba tare da tace komai ba, ta cigaba da kukan ta.

Mama tace
"Ke meye kuma na kukan kiyi mana shiru, idan mutum bashi da lafiya addu'a yake ba kuka ba, meye Amfanin kukan?"

Cikin kuka Mufeeda tace
"Na dauka na mutu ne fa"

Dariya Baba yayi yace  "A'a baki mutu ba, meyasa baki da lafiya baki gayawa kowa ba? seda Asuba Mamanki taje tashin ki ta ganki a ƙasa a sume a cikin amai, me yasa baki faɗa ba?"

Maimakon ta amsawa Baba tambayar sa sema fashewa da ta kuma yi da kuka tace "Baba ciki na da kaina ciwo suke min"

"Ya isa haka yi shiru, yanzu likita zezo ya duba ki"






Ammar ya bayan sallar asuba ya ɗan koma bacci.

Ƙarfe takwas na safe ya farka daga bacci ya ɗakko wayar sa yana duba saƙonni.
Message ɗin Mufeeda yaci karo da shi a what's App ɗin sa kafin ya buɗe message din ya buɗe hoton kan dp ɗin ta, itace akan dp ɗin da kayan dinner ɗin yayar ta, tana sanye material maroon, tayi kyau matuƙa.

Ɗan taɓe baki yayi ya buɗe voice message ɗin

"Yaya Ammar ɗina bani da lafiya, kaman zan mutu nake ji, narasa me ke mun daɗi kamin Addu'a dan Allah"


Shiru yayi yana kuma kunna message ɗin yana ƙoƙarin gane da gaske take yi ko kuwa dai wani abun take shiryawa, tsaki yayi ya ajiye wayarsa ya fita yai brush ya yi breakfast ya ɗau babur ɗin sa ya fice.





Seda

Please Login or Register in order to submit comment