Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iya zamana da kai na gane abubuwan da mahaifiya ta da 'yan uwana suke jiye min, Yaya Ammar ko dan Darajar Soyayyar da nake maka ya kamata kayi min Adalci ban cancanci jin wannan kalaman daga bakin ka ba, a zaman mu da kai a Alkhairaina guda nawa ka yaba? Amma yau akan kuskuren da baka da tabbas na Aikata ka hukunta ni da kalamai masu muni, kalaman da bazan manta ba har in koma ga Allah, Shikenan Nagode sosai, sannan bazan gajiya ba Allah ya baka haƙuri, idan ka sakko daga Fushin nayi maka bayanin abunda ya faru, Adawo lafiya Allah ya kiyaye hanya "

Tana gama maganar ta tafi ɗakin ta tana shehssheƙar kuka me tsuma zuciya, seda Mufeeda tai wannan maganganun sannan Ammar ya dawo hayyacin sa ya fara tunanin Anya kalaman da yayi Amfani da su sun dace? Take kuma yaji kamar be kyauta ba gaba ɗaya jikin sa yayi sanyi, tabbas ya kamata ya bincika kafin yayi mata hukunci, haka nan ya ɗau key ɗin babur ɗin sa ya fice.

Bayan fitar sa Mufeeda gaba ɗaya ji tayi ta tsani zaman gidan, gaba ɗaya ta rasa abunda yake mata daɗi ga zuciyar ta da take ta faman bugawa da ƙarfi, miƙewa tayi tasa hijjabin ta ta ɗau wayar ta ta fice, tafiya kawai take dan wani matsanancin ciwon kai ne ke damun ta ga Jiri da take ji dan haka kawai jefa ƙafar ta take, tana fita bakin titi ta tare me Napep ta gaya masa unguwar daze kaita ta faɗa ciki tana goge Hawaye.

Akan idon Sa'idu me kayan miya hakan ta faru, dan haka ya jinjina kai yace "Yau akwai zazzafar Jarida"

Me Napep ɗin daya ɗauki Mufeeda kuwa tsoro ya fara ji karta mace masa a Babur, dan wata irin shaƙuwa take tana sauke numfashi da ƙyar, seda ya kaita har ƙofar gidan Yaya Amina, Mufeeda ta fito daga A daidaita sahu abu ya faskara dan harta fara fita daga hayyacin ta da ƙyar take numfashi.

Ƙwanƙwasa gate ɗin Yaya Amina me Napep ɗin yayi, akayi sa'a Yaya Amina ce ta buɗe, suka gaisa dame Napep sannan yace mata

"dama waccan baiwar Allah na ɗakko tace nan zan kawo ta, kuma gashi munzo ta kasa fitowa kamar bata da lafiya"

Aikuwa Yaya Amina na leƙawa ta hango Mufeeda a cikin Napep ɗin ta riƙe ƙirji, da Sauri Yaya Amina ta koma cikin gida ta ɗakko mayafi suka fito tare da mijin ta, Mufeeda na ganin Yaya Amina ta sake fashewa da kuka, suka ɗakko ta daga A daidaita sahu zuwa cikin gidan, mijin Yaya Amina ya sallami me Napep.



A tayani Share ba dan halina ba 😍😍😜


NAGA NAFARA ƁATAWA 'YAN TEAM ƊIN MUFEEDA RAI, ANA CEWA HAƘURIN MUFEEDA YAYI YAWA, GA WATA TAMBAYA, DA MUFEEDA BATA KASANCE ME HAƘURI BA WANI IRIN ZAMA KUKE TUNANIN ZATA YI DA WANNAN MIJI NATA ME BAUƊAƊƊEN HALI? IDAN BA TAYI HAƘURI BA TAZAMA ME YAWAN ƘORAFI YANA HAƊA SHI FAƊA SA 'YAN UWAN SA A SANNU WATARAN SE IYAYEN MIJIN TA SUN FARA JIN HAUSHIN TA.
AYIMIN HAƘURI LABARIN NE YAZO A HAKA DAN HAKA KU BIYONI SANNU A HANKALI DAN JIN YADDA ZATA KAYA
KISSA BATA NUFIN KWALLIYA DA KWARKWASA BANE, AKWAI HAƘURI DA JURIYA.

Taku har Kullum Aisha Humaira, Daddy's girl ko ince Ayshercool, ina godiya sosai da ƙauna da kuma bibiyar littafin da kuke

Domin sharhi gyara ko shawara
07063065680...✨✨✨✨
*WATA KISSAR...... *
✨✨✨✨✨

( *Sai Mata* )

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail Www.ayshertadam@gmail.com

Please follow me on Wattpad, vote and Comment

https://www.wattpad.com/1096499534?utm_source=android&utm_medium=com.fmwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Ayshercool7724&wp_originator=NWkhlySuZ8Eug%2BopXFfcycv2JGS3axjaccC5%2FbUYT6YzeXAYV4ybw7FnTr8fHQDwo5ncF8TNfQfelSdeR5t0OZi0%2FKAiAcvwuLa561y0j%2BMpxBPI15z3EyzU4ZruY9KP

ELEGANT ONLINE WRITER'S

                      Page 23

A falo Su Yaya Amina suka kwantar da Mufeeda, mijin ta ya kunna fanka, Yaya Amina ta ɗakko ruwa tana shafawa Mufeeda a goshin ta, har yanzu Mufeeda sauke ajiyar zuciya take tana jan numfashi da ƙyar, kusan mintuna Ashirin wani wahalallen bacci yayi awon gaba da ita, zuba mata ido suka yi gaba ɗaya kafin Yaya Amina tace
"Hubby ina tunanin me yasa mu Mufeeda haka harta fito a wannan yanayin? Ko shi Ammar ɗin yana ina oho?"
"Nima nayi wannan tunanin, Amma dai karki sanarwa da kowa mu bari ta tashi muga yadda hali zeyi, idan ta kama mu tafi Asibiti ne semu tafi a duba ta dan na tsorata gaskiya"
Jinjina kai Yaya Amina tayi suka cigaba da dakon farkawar Mufeeda.

Ammar kuwa bayan fitarsa abunda ya faru tsakanin sa da Mufeeda ya tsaya masa a rai, Yanzu yake tuhumar kansa akan me yasa yayi amfani da wannan Kalmomin masu nauyi akan Matar tasa, Kalaman sunyi zafi da yawa, Yayin da gefe guda kuma wata zuciyar take gaya masa me yasa zata yi masa haka, akan me zata yi Soyayya da wani a waje alhalin da Auren sa a kanta? Ace har a iya tararsa a waje a gaya masa a ganta tana zance a layi, ga wayar da aka kirata yaji da kunnen sa ga messages ɗin da ake turo masa akan ta gaba ɗaya kansa ya kulle, Alkhairan ta ya shiga tunawa wanda ita dai kullum burin ta ta ƙara Jaddada masa tana sonsa, Idan har tana sonshi kamar haka ya za'ayi ta aikata wannan aiki haka? "

Mufeeda ta daɗe tana wannan baccin sannan ta tashi, koda ta tashi seta ji sassauci a zuciyar ta, Yaya Amina ta kai mata ruwan wanka tayi wanka ta kawo mata Abinci Amma tace ba zata ciba
Mijin Yaya Amina yace " Haba Autar Baba ya zaki ce ba zaki ci Abinci ba? Kinzo a mawuyacin Yanayi gaba ɗaya mun tsorata da halin da muka ganki a ciki, dan Allah kici Abinci kinji"
Girgiza kai tayi tana goge Hawaye tace "Na ƙoshi Yaya Auwal"
Auwal yace "Amina ko zaki tambaye ta idan wani abun take so a siyo mata"
Saurin girgiza kai Mufeeda tayi tace "Nifa na ƙoshi"
Yaya Amina tace  "wai ke meye hakane, ya za'ayi ta fama dake kici Abinci kamar wata Jaririya"
Auwal yace "A'a My love mu bita a hankali tana cikin damuwa ne, be kamata kiyi mata faɗa a wannan yanayin ba"
Da ƙyar suka takura Mufeeda ta sha tea da slides na dankali ta ture tace bata ci.
Seda Mijin Yaya Amina ya tabattar babu wata matsala Mufeeda ta samu nutsuwa Sannan ya koma ɗakin sa dan ya basu guri, dan inda Amana Mufeeda ta hannun daman sa ce baze manta Yadda ta tayashi campaign a gurin neman Auren Amina ba.

Bayan tafiyar sa Amina ta kalli Mufeeda tace "Auta bana son wannan halin naki na zurfin ciki da ɓoye ɓoye, kiyi min bayani me yake faruwa?"
Shiru Mufeeda tayi ta sunkuyar da kai wasu hawayen na bin idon ta amma taƙi magana.
Ba yadda Amina ba tayi ba akan Mufeeda tai mata bayani amma taƙi, Yaya Amina tace
" shikenan tunda ba zaki gayamin ba bari in kira Mama in mata bayani, wataƙila ita zaki iya gaya mata"
Da sauri Mufeeda ta riƙe hannun Yaya Amina tace
"Yi haƙuri dan Allah zan gaya miki, Amma kiyi min Alƙawarin ba zaki gayawa Su Mama ba ko Anty Fadeela, kinga ke kaɗai ce abokiyar Sirri na wadda zata tausaya min, idan kuma Mama taji zata ji babu daɗi"

"Shikenan naji babu wanda zan gayawa, gayamin meyafaru ? Kuma bance ki ragemin komai ba indai kin yadda ni yayar kice kuma abokiyar shawarar ki"

Nan Mufeeda ta zauna ta warwarewa Yaya Amina yadda suka yi da Ammar da yadda take fama da Wasu daga cikin 'yan uwan sa, ɗan shiru Yaya Amina tayi sannan tace
"Amma gaskiya Mijin ki bashi da kirki, se kace bashi da' yan uwa mata, ko dan keba ƙanwarsa bace ba uwa ɗaya uba ɗaya kuke ba shine ze dinga miki rashin mutunci? ko kuma yana ganin ya Aure ki a ɓagas seya dinga wulaƙanta ki, a da na goyi bayan ki Aure shi saboda naga yadda kike sonsa, Amma ya bani kunya wallahi zega tsiya tunda bashi da mutunci "

Ɗan tura baki Mufeeda tayi tace
" Ni gaskiya ki dena zagarmin mijina "
Buɗe baki Yaya Amina tayi dan mamaki sannan tace
" Dan kin samu baki hallaka ba, kin manta yadda kika zomin rai a hannun Allah shine kike wani in dena zagin sa, an zage shi ɗin bashi da mutunci, kema kuma sokuwa duk surutun naki da rashin kunya akan 'yan gari ya ƙare ki zauna yana neman ya kashe ki da ƙuruciyar ki"
Yaya Amina ta harzuƙa sosai, tana da haƙuri dan tafi duk su Mufeeda haƙuri, Ba ƙaramin abu ne yake ɓata mata rai ba.

"Yaya Amina nice fa a ƙarƙashin sa, Idan har nace zanyi masa rashin kirki ban kyauta ba, duk abunda mutum yayi maka na laifi akwai buƙatar kayi masa Adalci, Yaya Ammar yana kula dani fiye da tunanin ki, in bani da lafiya ze kaini Asibiti na kuɗi in shine yaje na gwamnati, ya yadda ya hana kansa ko yaci Abinci mara daɗi ni inci abunda nake so, Saboda shi na dena ɗora kayan ƙyale ƙyalen mata akan status ɗina, ko in ajiye su a waya ta, da ya gani, komai tsadar su indai ze iya seya nema ya siyamin indai ze iya, ko a hira na faɗi wani abu idan yana da kuɗi se ya saimin abun nan, ba abunda na nema na rasa a gidan sa se Soyayyar sa da kuma yawan fushi da rashin bincike idan akace masa nayi laifi"
Ta ƙarasa maganar tana kuka hadda sheshsheƙa, Yaya Amina ba ƙaramin tausayawa Mufeeda tayi ba, gaskiya Ammar halin sa seshi, tayi mamaki da suke zaune da Mufeeda ma, Saboda babban abunda yake haɗa Mama da Mufeeda ko a gida yawan Faɗan ta da rashin ɗaukar raini, Amma yanzu Allah ya haɗa ta da murɗaɗɗen Namiji wanda tilas yasa ta ajiye nata rawar kan.

Yaya Amina ta numfasa sannan tace "Shikenan ya isa haka, Amma Gaskiya Mufeeda kinyi wauta, seda na gayamiki, ki gaya masa abunda yake faruwa amma kika ƙi"
"Yaya Amina ba ƙi nayi ba a lokacin ma sama sama yake dani, maƙota na sun kawo masa ƙara ta"
Yaya Amina tace "Maƙota kuma? Me kuma ya haɗaki da maƙota zasu kai masa ƙarar ki?"
Nan ma ta zauna ta warwarewa Yaya Amina komai, Yaya Amina ta jinjina kai lallai ƙanwar ta tana ganin ƙalubale a cikin rayuwar Auren ta, Yaya Amina ta riƙe hannun Mufeeda tace
"ki kwantar da hankalin ki kiyi haƙuri Insha Allah komai ze wuce ze daidaita, amma sena koyawa wannan mijin naki hankali, waima uban waye ya gaya masa ya ganki kina zance da wani?"
"Wallahi ban saniba Yaya Amina, Amma akwai wani mutumi da yake bina a unguwar wai yana sona, hana da kuɗi sosai, Amma wallahi Yaya Amina rashin mutunci nayi masa nace ni matar Aure ce, ban san waye ya gaya masa hakan ba"
"to ke uban me ya hana ki gaya masa ga abunda mutumin yake miki?"
"Hmm Yaya Amina kenan, me ɗaki ai shi yasan inda yake masa yoyo, Nasan halin mijina tsaf kallo ɗaya yakewa abu yai masa hukunci ba tare da dogon bincike ba, koda na gaya masa se yaga laifina nima"
"Shikenan ya isa, ki dena kukan haka nan" A hankali Yaya Amina ta dinga janta da hira domin ta rage damuwar da take ciki.

*********************
Gaba ɗaya idan Ammar ya tuna abunda yayiwa Jaririyar matarsa da yadda take kuka se yaga be kyauta ba, ya tuna yadda ya baro ta a yanayi mara daɗi dan haka ya yanke shawarar komawa gida don yaga halin da take ciki.
Koda ya koma gida be san ta ina ya kamata ya fara ba, zuwa ɗakin ta zeyi ya duba ta kokuma yaya? Tuno irin maganganun da yaji ana yi mata a waya yayi nan da nan yaji ransa ya ƙara ɓaci ya nemi guri ya zauna a falo, shiru shiru be ji motsin ta ba, ya fara mamakin anya kuwa taji dawowar sa, ko yana fushi da ita idan ya dawo seta fito ko baze kulat ba za tayi masa sannu da zuwa, a hankali idon sa ya kai kan inda hular ta ta faɗi lokacin da ta biyo shi tana bashi haƙuri, se yanzu ya lura da yadda ya fita ya bar gidan haka ya dawo ya tarar da shi.
Da sauri ya miƙe ya fara leƙe leƙe amma komai yana nan yadda yake, ya nufi ɗakin ta da sauri ya buɗe ƙofar amma bata ciki ga ƙofar wardrobe ɗinta a buɗe, ya buɗe banɗaki nan ma bata ciki, a gaggauce ya dinga duba lungu da saƙo na gidan nan amma babu Mufeeda babu alamar ta.

Hannu yasa a Aljihun sa ya ɗakko wayarsa ya fara kiran layin ta, Mufeeda na kwance a ɗakin da Yaya Amina ta sauke ta wayar ta ta fara ringing, kallon inda wayar take tayi taga sunan My lovely Bae akan screen ɗin wayar.
Ƙurawa wayar ido tayi tana ci gaba da ringing, idan ta katse ya sake kira ya kira ya kai sau takwas, Amma Mufeeda taƙi ɗagawa kuma ta kasa kashewa, Yaya Amina ce ta jiyo ringing ɗin wayar ta shigo ɗakin tace
"Auta ba wayar kice ke ringing ba?"
"Waya tace Yaya Amina, Yaya Ammar ne yake kira na"
Yaya Amina tace "maza yi rejecting ɗin kiran nan ki kashe wayar"
Girgizawa Yaya Amina kai tayi tace "bazan iya rejecting ɗin kiran sa ba" Wata uwar Harara Yaya Amina tayi mata, ta fizage wayar tayi rejecting ta kashe wayar gaba ɗaya sannan ta cillawa Mufeeda wayar.

Hankalin Ammar ya tashi da yaji ya kira taƙi ɗagawa ƙarshema ta kashe wayar, nan da nan gumi ya fara tsatstsafo masa, yanzu ina Yarinyar nan ta shiga? Me zance wa Iyayen ta? Gaba ɗaya kansa ya kulle ya rasa abunyi, idan Yace zeje gida ya gayawa iyayen sa halin da ake ciki to tabbas ze fuskanci ɓacin rai musamman a gurin mahaifinsa, dama Yaya Jidda ba'a maganar ta dan babbar banza ce, ita kuwa Yayarsa Amina da suke cewa Ummi 'yar ba ruwana ce, har gara Maryam wadda yake bi tafi su fahimta, dan haka ya yanke shawarar yaje gidan Yaya Maryam yaji ya zasuyi dan gaba ɗaya ya rasa abunyi.
A sukwane ya rufe gidan ya ɗau babur ɗin sa ya tafi gidan Yaya Maryam, tayi mamakin ganin sa a wannan lokacin amma yanayin sa ya nuna mata Akwai matsala akwai abunda yake damun sa, Yaya Maryam ta kalleshi tace
"lafiya kuwa Ammar?, naganka kamar ba a nutse ba, meke faruwa ne?"
"Akwai matsala ne fa"
"Matsala kamar yaya? Allah yasa ba wani abun kayi wa Mufeeda ba"
Ammar ya ɗan sosa kai, cikin jin nauyi yace "A kanta ne"
"ina jinka"
Nan Ammar ya kwashe komai ya sanar mata, shiru tayi tana kallon Ammar seda ya gama tsaf ta jinjina kai tana ci gaba da kallon sa, can tace
"Amma Ammar ban taɓa tunanin rashin hankalin ka ya kai haka ba wallahi"
Haɗe rai yayi yace "ya za'ayi dan nazo na gaya miki matsala ta ki kirani da mara hankali"
Babban abunda yasa Ammar yake shiri da Maryam shine yadda take girmama shi, daman akwaishi da son girma, Be taɓa zaton zata kira shi da mara hankali ba.

A fusace tace "Na faɗa mara hankali, dama da naje gidan ka wancan satin yarinyar nan tana cikin damuwa nayi nayi ta gayamin idan akwai matsala amma tace babu ashe cutar ta kake"

"Ya zaki ce ina cutarta ni bance ta cutar dani ba da Aure na take kula maza a waje"

"Karka ƙara cewa tana kula wasu mazan a waje tunda baka gani ba, baka da tabbas ashe duk Nasihar da Baba suka dinga yi maka lokacin da aka baka Auren Yarinyar nan da wadda nayi maka duk baka ɗauka ba, iyayen ta sun baka ita a mutunce da girmamawa amma kayi haka, kai a marrar nan ka samu Yarinyar da harta san tayi laifi ta baka haƙuri, amma kake wulaƙan ta ta, niba abunda zan iyayi maka akai, kaje ka samu Su Baba kayi musu bayani aje gidan su a duba, in tana can in taga zata dawo shikenan, ko dayake ma ai babu Aure a tsakanin ku tunda har zargi ya shiga ciki "

Zaro ido Ammar yayi yace " Ubanwa yace miki zargin ta nake, ko duk duniya zasu taru akan Zata aikata zina zan ƙarya ta kowaye, Yanzun ma na yadda ne saboda da kunne na na ɗaga wayar naji, kuma ita mace ce me son kulawa da soyayya sosai "

Yaya Maryam tace "Eh Mace ce me son kulawa da Soyayya, kai kuma bazaka iya nuna mata soyayya da kulawa ba kana ganin yin hakan kaman ka faɗo ne ko? Shiyasa ka yadda za tayi Soyayya da wani a waje, ai in gaya maka kaɗan da aikin mace idan har zatayi abu ba zaka yaba ba tayi ta burge wasu  a waje, ai ita mace tana so a yaba mata kai kam nasan bazaka iya ba"

Ammar ya ɗan kalleta ya ɗauke kai,
"Nasan halinka ai Ammar, Yarinyar nan tana sonka bekamata kayi mata haka ba, da kaji wani ya kira ta bincike ya kamata kayi, Idan tana chatting ne a social media akwai sakarkarun maza marasa tarbiyya da suke bin lambar mutane su dinga kira, zata iya yuwuwa a cikin su ne, kuma me ya kaika ɗaga mata waya? Da har kaji wannan maganar"

Cikin damuwa Ammar yace "Amma fa har message ake turomin akan in saka ido akan ta tana aikata rashin gaskiya a bayan idona da ban yadda ba amma abun ya fara ɗauremin kai"

"Taɓɗijan to waye yake turomaka?"

"Nima ban sani ba, anyi hiding ɗin lamabar"

"to tabbas me turomaka saƙon yana da Alaƙa da wanda ya kira ta a waya in ba haka ba ya akayi yasan tana aikata rashin gaskiyar? Kuma me yasa ya ɓoye lamba, ai kamata yayi ku zauna ku tattauna, ko ka yi bincike a ɓoye ka gane gaskiya kafin ka yanke mata hukunci "

Shiru Ammar yayi ya dafe kai yana tuna lokacin da Mufeeda ta biyo shi tana riƙe rigar sa tana kuka, yadda bata son ɓacin ransa sam, gaba ɗaya tausayin ta da nadama ya kama shi, Jiki a sanyaye yace
"Yanzu meye abunyi? "
"Abunyi kaje ka samu Abba kuyi maganar"
"Haba Yaya Maryam, idan har zan gayawa Abba meye amfanin zuwa gurin ki, Abba bazemin da daɗi ba, inason sanin takamaimai tana ina, na kirata yafi a ƙirga bata ɗauka ba, ƙarshe ma ta kashe layin ta gaba ɗaya"

"Koma menene dai kai ka janyo shi, dan ka kaita bango ne shiyasa ta tafi ta bar maka gidan ka, da alama ka daɗe kana muzguna mata, yanzu abunyi shine kaje gida zuwa gobe in Allah ya kaimu se asan yadda za'ayi"

Zare ido yayi yace "har zuwa gobe? Ban san inda ta tafi ba kuma bansan a wani hali take ba?"

"to seka fita kaje ka neme ta ai, kasan da haka amma kai mata wulaƙanci"

Jiki a sanyaye Ammar ya tashi ya koma gida, gaba ɗaya ya shiga damuwa tare da tunanin ina ta tafi haka? Abunda zesa Mufeeda taƙi ɗaga wayarsa ba ƙaramin abu bane, lallai indai tana cikin ƙoshin lafiya ba ƙaramin fushi take da shi ba, ɗakin ta ya kuma komawa yana dubawa kota dawo amma still bata nan, Ammar ya kasa zaune ya kasa tsaye.
Ya shiga tunanin idan Mufeeda wani gurin tayi da wani ido ze kalli iyayen ta, Abun duniya ya ishe shi gidan yayi masa faɗi, daren ranar sam bacci ya ƙauracewa idon sa, yayi zurfi a tunanin ina ze gano 'yar mutane.

Ɓangaren Mufeeda ma tunanin sa take yi, tasan hankalin sa yana tashe besan inda ta tafi ba, A ranata tace "Allah yasa kar yaje gida nemana bana son su Mama su san abunda ke faruwa"
Ji take kaman ta kunna wayar ta ta kira shi saboda tasan ze shiga tashin hankali rashin ganin ta, amma da ta tuno kalmar mayaudariya munafuka da ya kira ta da su se wasu zafafan Hawaye su zubo mata, ƙoƙari ta dinga yi ta manta da shi amma abu ya faskara, dan wani tausayin sa ne ya mamaye zuciyar ta dan tasan tabbas Ammar baze iya bacci ba yau.

Wasa2 kwana uku babu Mufeeda babu labarin ta, hankalin Ammar ya gama tashi, ko Abinci baya iya ci, yaje gidan su Mufeeda ya fake da gaishe su yaje yi Amma ya tarar bata nan, kuma bega wata alama a fuskar Mama da yake nuna wani abu ba, Ammar ba bacci babu cin Abincin kirki saboda tunani da fargaba, Yayi niyyar ya nemi Aminu koda shawarar daze bashi se kuma ya fasa, sam Ammar ya rasa kwanciyar hankali.

Yaya Maryam ma nata ƙoƙarin trying lambar Mufeeda amma taƙi shiga.

Har yanzu Mufeeda tana fama da damuwa ga shi bata da lafiya har yanzu, Mijin Yaya Amina yace idan ya dawo zasu tafi Asibiti.

Yanzu ma Yaya Amina ta saka Mufeeda a gaba akan tayi breakfast, gaba ɗaya mufeeda bata jin daɗin Abincin ta riƙe cokali tayi shiru tana zancen zuci, Yaya Amina tace
"Kinga Auta karki wa kanki illa da wannan tunanin ki maida kai kici Abinci kafin Ya dawo mu tafi Asibiti"

Mufeeda ta ajiye cokalin ta kalli Yaya Amina tace "Yaya Amina wallahi tunanin Mijina nake, besan inda nake ba hankalinsa ze tashi sosai, kuma ma ko yaci Abinci yanzu? Nasan ba lallai yana cikin nutsuwar da zeci Abinci ba"

"Sannu Tattabara uwar ƙauna, ko ince sarkin Aure, ke ba kiga halin da kike ciki ba saboda shi, amma tausayin sa kike ji baki da zuciya"

"Ba rashin zuciya bane Yaya Amina, abun da Yaya Ammar yayi shi duk wani Namiji da yake son matarsa zeyi, tun ɗazu na kunna wayata kiran sa yake shigowa, Zuciya ta na rayamin in ɗaga nasan zuwa yanzu yana cikin nadama"

A fusace Amina tace  "Wallahi kika ɗaga wayarsa sena gayawa Mama abunda ke faruwa"

Wayar Mufeeda ta fara ringing, tana dubawa taga Anty Maryam ce, ta kalli yaya Amina tace
"Yaya, Anty Maryam ce Yayar Ammar"
Yaya Amina tace "bani wayar nan" ta karɓi wayar tare da yin sallama, suka gaisa da Anty Maryam.

Anty Maryam tace "dan Allah Mufeeda nake nema"

"Ba ita bace Yayar tace"

"Masha Allah, gurin ki ta taho kenan?"

"Eh muna tare, nan ta taho"

"Dan Allah ki temaka ki gayamin inda gidan ki yake zanzo muyi magana"

Yaya Amina tayi mata kwatancen gidan ta, befi awa ɗaya da rabi ba sega Anty Maryam, Yaya Amina tayi mata kyakywar tarba, Kallo ɗaya Anty Maryam tayi wa Mufeeda taga ta rame sosai kuma kana ganin ta kasan bata da lafiya, Anty Maryam tacce "Mufeeda ran da naje gidanki ba yadda banba ki gayamin in akwai matsala amma kika ƙi"

Yaya Amina tace "Ai ba zata gaya miki ba, yanzu ma dan taga ta kusa mutuwa ne yasa ta zo gidana, dan lokacin da tazo ko numfashi bata iyayi"

Nan Yaya Amina ta zauna ta gayawa Anty Maryam komai kamar Yadda Mufeeda ta gaya mata, kallon jinjina take wa Mufeeda tace
"Sannu Mufeeda Allah ya baki ladan biyayya da haƙuri, amma maganar gaskiya koni bazan iya wannan haƙurin da kikayi ba, Amma ku ƙyaleni dashi ze gane kuskuren sa, yanzu Alfarma ɗaya nake so kiyi min, ki bani ita in tafi da ita, zan kaita Asibitin ta zauna a gurina na wani ɗan lokaci, bana son wani daga iyayen mu yasan hamin da ake ciki, amma tabbas zan koya masa hankali "

Da farko Yaya Amina bata yadda ba, se daga baya ganin Yadda Anty Maryam wadda ta girmesu gaba ɗaya keta magiya yasa ta Amince, ita dai Mufeeda bata da ta cewa, Yaya Amina ta bawa Mufeeda wasu daga kayan sawarta da yake ba tazo da kaya ba sena jikin ta tabi Anty Maryam gidan ta.

Ammar kam seya raba dare a falo a zaune, idan yayi salla kuwa bashi da Addu'a se Allah ya bayyana masa Matarsa yasa tana lafiya, idan ya zauna a falon nan ya dinga tuna yadda take tattalin sa tana kula dashi, be taɓa tunanin ya shaƙu da Mufeeda haka ba se yanzu, ji yake duniyar tayi masa zafi rashin ganin giftawar ta a gidan.

Kwanan Mufeeda biyu a gidan Anty Maryam kulawa take bata kamar ƙanwarta

Please Login or Register in order to submit comment