Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Matsala Jidda ta kawowa Umma, dan haka yaga be dace ace shima ya faɗa mata matsala ba, dan haka ya gaida Umma yai tafiyar sa.

Zuciyar sa ce ta ci gaba da tafasa, ya rasa inda zesa ransa, baze ji daɗi ba idan har be amayar da abunda yake ransa ba, dan haka ya tafi gidan Anty Maryam.

Yai sa'a tana nan tana ta ɗinki, kallo ɗaya tayi masa taga damuwa ƙarara a fuskar sa,
"Allah yasa dai lafiya, na ganka kamar an koroka, Allah yasa ba wata matsalar ka kuma kunnowa ba tsakanin ka da Mufeeda"
Girgiza mata kai yayi yace  "Lafiya muke sedai mutane daga waje dake ta kunna mana matsala, yanzu daga gida nake, naje in gayawa Umma abunda ke faruwa na tarar da Anty Jidda a gida tana kuka, naga bekamata in ƙara mata damuwa ba kawai na taho nan"

Anty Maryam tace  "Mhmm ai Anty Jidda reshe ne ya juye da mujiya, mijin ta ne ze ƙara Aure tabi ta ɗaga hankalin ta"

Ammar yace  "shine taje ta saka Umma a gaba tana kuka kamar wata ƙaramar yarinya, seta ɗaga mata hankali"

"to nima dai haka nagani, itama me gayawa wasu ce, su Khalil ɗinta ds mata ne aida tuni ta aurar dasu, amma take wannan, mata nawa akayiwa suka jure, shekara Ashirin da uku dayi mata Aure amma be ƙara Auren ba se yanzu, amma tabi ta ɗaga hankalin ta da nasa"

Ammar yace "Yaya Maryam wallahi duk wanda ya hana ɗan wani zaman lafiya a gidan Auren sa shima baze zauna lafiya ba, Anty Jidda yaya tace, Amma maganar gaskiya ta cutar da mata ta"
nan ya warwarewa Maryam duk abunda yake faruwa, daga bisani yace
"wallahi Maryam ina matuƙar jin nauyin Mufeeda, ta dinga ɗaukar laifukan da bana ta ba, naita mata faɗa sedai tayi kuka ta bani haƙuri, bata taɓa gayamin abunda suke mata ba, naji kunya Maryam"

Yaya Maryam Tace "Abunda nake gaya maka kenan, saurin zuciyar nan taka da izza ba zasu haifar maka da ɗa me ido ba, dan ma yarinyar ta samu kyakkyawar tarbiyya ba dan haka ba Wallahi da bazata zauna da kai ba, ka dinga cewa kai ba sonta kake ba, me za ka yi da ita, raino zak....

Ammar ya katseta ta hanyar cewa "dan Allah ki dena tuno wannan abubuwan, wallahi ina matuƙar jin kunyar abunda nayi, Mufeeda 'yar Aljanna ce Insha Allah"

"Kaji da shi dai, seya zame maka izina Ammar, Addu'ar iyayece ta rabaka da Zainab ka Auri Mufeeda, dan wallahi wannan Zainab ɗin ba zata yi maka biyayyar da Mufeeda take maka ba"

"se bayan na Auri Mufeeda nima na gane haka, tana min Biyayya fiye da yadda bakya zato, laifi ko ita tayi koba ita tayi ba har ƙasa zata durƙusa akan gwiwowinta tana bani haƙuri, indai ana samun Aljanna a gidan miji Mufeeda ta samu Insha Allah"

Murmushi Yaya Maryam tayi tace  "gaskiya ƙwaila ta iya kissa, tunda har tasa 'yan maza suka zubar da makaman su na muzurai da haɗe rai, suka afka duniyar soyayya"

"Maryam kenan, kafin inyi Aure ne nake ganin' ya mace bata isa ta juyani ba, seda na Auri Mufeeda nagane duk izzar namiji da mulkin sa ya Auri mace tagari kamar Mufeeda dole ya duƙa, ai WATA KISSAR SE MATA"

Dariya Sosai Yaya Maryam ta dingayi wa Ammar sannan tace
"wani mataki ka ɗauka akan su Fa' izan?"

"matakin me zan ɗauka? Na barsu a hannun hukuma su da Allah, wallahi ban yafe haƙƙin ƙaramar yarinya da suka ɗauka ba, suka sa na dinga gaya mata miyagun maganganu, tana kuka ta biyoni tana bani haƙuri, wallahi Allah yasaka mata, nida Fa'iza har abada wallahi Shikuma Faruk shima ya je shi da Allah "

Ammar yayi maganar kamar zeyi kuka saboda baƙin ciki da takaici.

Anty Maryam Tace " ka dai bi komai a sannu kayi haƙuri, se kaje ka maida hankali ka ƙara riƙe matar ka hannu biyu da mutunci, abunda kake rainawa kake ganin kafi ƙarfin sa wani nan duniya shi yake so"

Ammar ya dinga yabon Mufeeda yana jinjinawa ƙoƙarin ta game da haƙurin ta, lallai ta cancanci yabo.
Anty Maryam ta ci gaba da yi masa Nasiha.

Wayarsa ce ta fara ringing ya ɗaga ya duba, Maman Fa'iza ce take kiran sa
Kamar kar ya ɗaga se kuma ya ɗaga

"Ammar ka tafi ba kace komai ba, kan case ɗin nan"

Ammar yace "mezan ce Mama na barsu da Allah kawai, shi ze sakamin kuma anfi cutar da Mufeeda ita ya kamata abawa haƙuri, a madadin ta kuma mun barwa Allah kawai"
ya kashe wayar sa yana kuma jin tsanar Fa'iza da Faruk.

Yayiwa Anty Maryam sallama ya tafi, yana tafe amma tunani daban daban sun cika masa kwanya yama rasa wanne ya kamata yayi.

A can police station kuwa, da ƙyar DPO ya bada belin su saboda Ammar yace ya barwa Allah komai.

***************

Ƙarsfe sha ɗaya na safe aka fito da Saima daga theater, anyi cikin nasara sedai Jaririn yazo babu rai, haka aka kaita ɗakin ta tana bacci, Jabir ya ƙura mata ido duk tayi wani iri gwanin ban tausayi.

Haka Ammar ya koma gida jiki a saɓule, yauma yana komawa Mufeeda ta karanto damuwa a kyakywar fuskar sa, ɗan ƙyaleshi tayi tai masa sannu da zuwa, se binta yake da kallo yana tuna lokacin da yake mata faɗa akan wasu laifukan amma ba zata taɓa kare kanta ba sedai ta bashi haƙuri.

Hakanan yaji kunyarta tana kama shi, ya tuna lokacin da take nuna ita a duniya babu wani namiji da take so seshi yaita Gwaleta, tayi abu danta burgeshi amma yai banza kamar be san me tayi ba, amma bazata karaya ba gobe ma se tayi wani abun da zesa yaji daɗi.

Gaba ɗaya tausayinta ya sake kama shi.

"Wai na canza kamanni ne? Naga ana ta kallo na"

"gani nayi kin ƙara kyau"

Murmushi tayi tace "Kyau se Yaya Ammar amma ni ina naga wani kyau"

Ammar yace  "eh nagode, ko baki faɗa ba nasan ai ni mummuna ne"

"Idan ka kuma cewa mijina mummuna sena ɗau mataki akan ka"

Kallon ta Ammar ya ci gaba da yi sannan yace  "Am sorry Mufeeda"

Kallon sa tayi cikin rashin fahimta tace  "Sorry for what?"

"Nasan kinyi haƙuri dani a zamanmu, nayi miki abubuwa da dama na rashin kyautawa, ina neman afuwar ki Mufeeda, ina jin kunyarki mussman idan na tuna abubuwan da suka faru a baya"

Juyowa tayi ta tattara dukkanin hankalin ta akan Ammar, ta riƙo hannayen sa a nata sannan tace
"Mijina Alkhairanka sunfi kura kuranka yawa da matsayi a idona, a zamana da kai nima haƙuri kake dani ai, idan harna manta alkhairin ka na kalli kuskurenka bazan taɓa yi maka Adalci ba, kasawa zuciyar ka ni babu abunda kayi min, Ni jina nake nafi kowace mace sa'ar miji, Allah ya barni da abun sona"

Tai maganar tare da sumbatar hannun sa.
Murmushi yayi yana kallon ta Mufeeda akwai hikima da iya kalaman kwantar da hankali
"Ina sonki Mufeeda"
"I love you more my heart, amma gayamin kace ranar daka fara ganina ka fara sona how comes?"
Murmushi yayi yace  "Ranar da na fara ganin ki, wannan iyayin naki da shagwaɓa har raina naji sun burgeni, a fili kuma abun ya ban haushi, ƙaramar yarinya kamar ke kina wannan abubuwan? Da na koma gida duk abunda zanyi sena tunoki, idan na kwanta bacci se in dinga mafarkin ki, lokacin da kike turomin saƙoni kullum nagani se naji daɗi, duk ranar da baki turo ba se inta fushi babu dalili "

Dariya suka dingayi tare, ta shafa gemun sa tace
" Gayamin meke damunka ne? "

Girgiza mata kai yayi yace
" Babu komai "

"ƙarya ba hakinka bace Mijina, duk yadda ka kai ga ƙoƙarin ɓoyemin damuwar ka ina ganewa, gayamin meke damunka? Ko har yanzu nayi ƙanƙanta in san damuwar Mijina"

Girgiza mata kai yayi ya ɗan lumshe ido yana tuna irin abunda Faruka ya aikata shida Fa'iza, a hankali yace "Family issues ne Mufeeda, karki damu"

"Shikenan, amma kabi komai a sannu kaji mijina"

Ya jinjina mata kai, sannan yace  "ki shirya Anjima da daddare insha Allah zamu je ki duba Saima, yau aka yi mata aiki, munyi waya da Jabir yace babyn yazo ba rai"

"Allah sarki, Allah ya bata lafiya, ai da sauƙi tunda ba ita ta mutu ba"

Murmushi yayi yana ƙara riƙe hannun ta a nasa yace
"Allah ya raba ki da cikin nan lafiya, Jaririya ta"
"Ameen Babyn Jaririya"
Suka yi murmushi gaba ɗaya.

******************************

Su Maman Nur kuwa aka karɓi Jaririn ta aka kai shi Asibiti, su kuma akaƙi sakin su, Hajara tace kotu take so akai su sunyi mata ƙazafi ga tada tarzoma a unguwa, da ƙyar aka shawo kanta ta yadda aka sake su, amma sunji a jikin su dan kamar 'yan gudun Hijira haka suka koma, wasu babu takalmi haka aka kamo su.
Abun kunya ace an kama matar Aure akan dambe da tada tarzoma ki bar gidan mijin ki ki tafi yawan gulma, abun takaicin ace harsa namiji baligi wanda ba muharraminsu ba suke zama a teburin sa suyi hira

(Mace kenan, wata ko me kifi ta tare zata siya ta dinga masa rangwaɗa kenan tana kashe murya tana yayana, dan yayi mata ragi wanda ba lallai tayi wa mijin ta ba, Mata aji tsoron Allah, a dinga kama kai)

Aure dayawa ya mutu a sanadin wannan tashin hankali da akayi a unguwar su Mufeeda, da ƙyar aka sake su yayin da aka miƙa Sa'idu ga 'yan sanda domin tattara bayanai a gurfanar da shi a kotu, sakamakon tara matan daba muharramansa ba yake hira da su, yana haɗa husuma.

******************

Se la' asar Saima ta farka daga nannauyan baccin da take yi, ƙanwar mamanta ce a gurin ta, ta temaka mata ta zaunar da ita, da yake an samu ci gaba a yanzu likita yace a bawa saima tea, saɓanin da da idan akayi theater se ace se mutum yayi tusa za'a bashi Abinci.

Ta gama shan tea ɗin tana kashingiɗe tana jin yadda wani irin zafi ke ratsa inda aka yanka ta, dan Allurar harta sake ta, cikin zuciyar ta kuma na ƙunar rashin Jaririnta, seda ta haihu take jin da ɗan yana da rai Jabir kome zeyi ba zata barmasa ɗanta ba kamar yadda ta faɗa a baya ba, se dai yaje wadda ze aura ta haifa masa.
A hankali ta lumshe ido hawaye na bin kuncin ta, zuciyar ta na mata raɗaɗi, muryar ta can ƙasa tace
"Jabir duk a sanadin ka har yankamin ciki aka yi, amma nice abar wulaƙantawar ka"
Sunkuyar da kai tayi tana ci gaba da share hawaye.

Ƙanwar maman ta tace "wai Saima bazaki dena wannan kukan ba, ki fawwalawa Allah mana, kima gode Allah da ya barki da ranki da lafiyar ki, Allah ya kaimu baɗi iyanzu ki kuma haifo mana wani"

"Ba Ameen ba Gwaggo, bazan koma gidan Jabir ba"

"Meyasa?"

"Gwaggo ni kaɗai nasan abunda nake fuskanta a gidan nan, bar masa gidan sa shine mafita baze ƙarasa hallaka ni ba"

Suna cikin maganar ne mariƙin Saima ya shigo da matansa duba ta, bayan sun gama yi mata ya jiki sun zauna ana ɗanyin hira, sega Jabir ya shigo hannun sa ɗauke da leda, kamar na Allah ya durƙusa ya gaida 'yan uwan Saima, ya ƙarasa gaban gadon ta yace
"Saima ya jikin naki?"
"Ban sani ba da sauƙi ko babu sauƙi be shafe ka ba malam ina fatan kazo min da takaddata ta saki?"

Mariƙin ta cikin fushi yace  "ke Saima meye haka? Mijinki nefa kike gaya masa wannan maganganun, ya sake ki akan me?"

"Kawu duk abunda ya sameni Daga Allah ne, Amma Jabir ne Sila, wallahi na koma gidan sa kasheni zeyi da baƙin ciki, dama ko bance ya sakeni ba yace ze sakeni dazarar na haihu, ya auro wadda zeyi Arziki ta sanadin ta"

Maimakon kawun Saima ya tsaya yaji ba'asi kawai ya balbale Saima da Faɗa ta inda ya shiga bata nan yake fita ba, ya zage ta tsaf harda gori a gaban Jabir, yace seta koma gidan ta dan baze iya ci gaba da riƙe ta ba wanda yayi a baya ma Allah ya Amfana.

Seda wata metron tazo ta kori duk na cikin ɗakin saboda hayaniyar da suke, aka bar gwaggon Saima kawai, bayan fitar su Saima ta samu ta zayyanewa Gwaggon ta halin da take ciki.

"Allah sarki marainiyar Allah ina gefe ai ban san halin da kike ciki ba, ban san irin zaman da kika yi a gidan kawun naki ba kenan"

"Dan Allah gwaggo kisa baki, wallahi ba zan iya zama da Jabir ba"

"Shikenan kwantar da hankalin ki, nima ban goyi bayan kikoma ba, bari inje in samu kawun naki muyi magana"

Kusan mintuna Ashirin da fitar Gwaggo bata dawo ba, turo ƙofar ɗakin aka yi Mufeeda ce da Ammar, sekuma Fiddausi da mijin ta Aminu.

Saima na ganin su tayi murmushi tace
"Sannunku da zuwa, maraba"

Fiddausi tace  "yana ganki ke kaɗai babu kowa?"

"sun reception suna magana, ga guri ku zauna, Mufeeda naso mu haɗu kafin in haihi Allah beyi ba"

Mufeeda ta ƙarasa gaban gadon Saima ta zauna tace  "Bakomai Anty Saima sannu ya jikin naki?"

Nan suka gaisa suna mata sannu, Mufeeda tace  "Amma jinin naki ya sauka ko?"

"Eh Alhamdilillah, Jijjiga nayi shine aka yimin aiki"

"Allah sarki Anty Saima sannu"

Tai maganar cikin tausayawa tana riƙe hannun Saima.
Ammar yace  "Nida ta tayarmin da hankali ranar da Aminu ya kirani yace wataƙil ma kin mutu, ta kasa zama ta kasa tsaiwa, to gashi dai Anty Saima tana raye.

Suka yi murmushi ana ta hira da Saima, taji daɗin zuwansu, sun ɗebe mata kewa, ta samu sassauta daga ɓacin ram da take ciki.

Mufeeda tace  "Anty Saima babyn ba rai ko? Allah ya kawo mafi Alkhairi"

"Babu rai yazo Mufeeda"
Tai maganar tana goge ƙwalla.

Mufeeda tace  "Anty Saima ya zakiyi kuka? Ki gode Allah da kina raye Allah ya baki wani"

"Mufeeda kenan dole inyi kuka, wata tara yaron ma ciki na na saka rai, Amma Allah yayi ikon sa"

Fiddausi tace  "kiyi haƙuri Saima, ki kwantar da hankalin ki, kin san baki da cikakkiyar.....

Ai ba ta ƙarasa maganar ba kawun Saima ya shigo yana banbami yace

"ba dai baki da mutunci ba kin dage sekin kashe Aurenki, to idan ya sake ki ki nemi gurin zama ba gida na ba, dan bazan ƙara riƙe ki ba wahalar da nayi dake a baya ta isa"

Gwaggon Saima tace  "ka dai ji kunya, dama can ba wata tsiyar kuke tsinana mata ba, tayi zama ne tamkar baiwa a gidan ka, a matsayin ta na 'yar ɗan uwan ka, nayi imani da Allah da' yar ka ce bazace ta koma ba, shima shegen yaron kwaɗayayye ashe 'yar gidan Alhaji Saminu Kwangila ce yake ƙuzun Aure, ai nasan yaran gidan maza yaje ya kwasa, nidai tunda ya sakarmin ' yata yaje ya ƙarasa, fuskarsa ta nuna dama haka yake so"

Mufeeda ta silalae ta bara ɗakin dan ba zata iya jure kallon wannan wulaƙancin ba, kowane tarkace sedai a ɗora shi akan mata.

Ammar ma bayan ta ya biyo ya kunna babur ɗinsa suka tafi, shi kansa ransa a ɓace yake, yana jinjina wulaƙanci da rashin mutunci irin na Jabir, sesa Mufeeda tayi kuka saboda tausayin Saima.

Haka suka tafi kamar kurame, a daidai danja 'yan sanda suka zo suka kewaye babur ɗin su Mufeeda, suka sa hannu suka kashe babur ɗin suka zare key, ɗaya ya kalle shi yace
"Ammar ko?"
Ammar yace  "Eh nine Yallaɓai amma me nayi?"

"dalla rufewa mutane baki, kalle ka kamar mutumin kirki ashe ma cuci ne, ana haɗa kai da kai anyiwa Fasinja fashi fito yai dubunka ta cika"

"Kai Yaya Ammar ɗin? Wallahi bashi bane ba, ba yaya Ammar ɗina bane, wallahi bashi bane baze aikata haka ba"

Shikam gaba ɗaya kan Ammar ya kulle, yama rasa meze ce, shi dai ba da wani suke exchanging ɗin babur ɗinba, balle ace shine shi a iya sanin sa ko fitinar nan ta ƙuruciya beyi ba balle yanzu da girman sa.

"zaka fito ko sena ɓaroka munafuki"

Ammar jiki a sanyaye ya fito daga babur ɗin, yasa hannu a aljihunsa ya ɗakko kuɗaɗen dake ciki ya kalli Mufeeda yace
"Mufeeda kinga dare yayi, karɓi kuɗin nan maza ki tafi gida, Insha Allah da safe zan dawo, tunda nidai nasan ban aikata laifin komai ba"

Mufeeda ta fashe da kuka ta riƙe rigar Ammar tace  "Wallahi sedai a haɗa dani, ni Ammar ɗina mutumin kirki ne Officer dan Allah, wallahi bashi ake nufi ba"

"Yi haƙuri 'yan mata maza ki tafi gida, yana division ɗin gangare zamu tuhume shi"

"Maza ki tafi gida dare yanayi, sannan karki sanar da kowa se zuwa gobe in Allah ya kaimu inga yadda hali zeyi"

Aka saka Ammar a motar ' yan sanda, suka tuƙa Napep ɗinsa suka tafi da shi.







Kai masha Allah, ban san haka kuke son book ɗin nan kuke following ɗinsa ba, kwana biyu da ban posting ba nasha kira a waya, ina godiya ta musamman Allah ya bar ƙauna, kar' amanta in an karanta ayimin share dan Allah ba dan halina ba
🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏

Wanda sukamin magana akan voting na gasar dana shiga, se an kammala gasar ne za'a bada link ɗin da fans zasu shiga suyi mana voting, nagode da kulawar ku


Domin gyara, sharhi, ko shawara, ƙofa ta a buɗe take
Ayshercool
07063065680..✨✨✨
*WATA KISSAR...... *
✨✨✨✨✨

( *Sai Mata* )

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail Www.ayshertadam@gmail.com

Please follow me on Wattpad, vote and Comment

ELEGANT ONLINE WRITER'S

NOT EDITED

                         Page 29



Gaba ɗaya jikin Mufeeda rawa yake, ji take tamakar a mafarki, wace irin masifa ce wannan? Daga wannan se Wancan
"Ya Allah ka fitarmin da mijina"
Haka ta tari Abun hawa ta tafi gida, unguwarsu baƙi ƙirin saboda duhu, har ƙofar gidanta me Napep ya kai ta.

Safa da  Marwa Mufeeda ta dinga yi a ɗaki ta rasa me ya kamata tayi, se sharce hawaye take tana tunanin ya Ammar ze iya kwana a ceil, waye yai masa wannan sharri haka?
Tayi tunanin ko ta kira Baba a waya ta gaya masa, seta tuna Ammar yace karta gayawa kowa.
babu Alamar Bacci a tattare da Mufeeda, tai alwala dinga salla tana kai kukan ta ga Allah, har dare ya raba kuka Mufeeda take sosai ga tsoro da take ji.

Tana zaune a tsakar ɗaki ta dunƙule a guri ɗaya tana kuka, ji tayi ana buga gate ɗin gidan, da sauri ta miƙe ta koma kan Gado tana rarraba ido, cigaba da bugun aka yi, wata zuciyar tace idan kuma Ammar nefa ya dawo, da sauri ta sakko daga kan gadon ta buɗe falon ta fito tsakar gida cikin sanɗa.

Buga ƙofar aka cigaba dayi, cikin sanɗa take tahowa ta tsakanin gate da garu Mufeeda ta leƙa yanayin inuwar wanda yake tsayen ba tayi kama data Ammar ba.

Da gudu ta koma ta rufe falon ta, ta koma ɗaki ta kulle ƙofa, ta hau gadon ta ta dinga Karanto Addu'oin da suka zo bakin ta.

Yadda Mufeeda taga rana haka taga dare, cikin tashin hankali ta wayi gari.

A gurguje tai wanka ta shirya, ta girka Abinci ta rufe gida ta fice.

Station ɗin da'aka kai Ammar ta tafi, tun ƙarfe takwas na Safe ta tafi, taita Jira a station ɗin, se ƙarfe Goma aka fito da Ammar daga shi se dogon wando da vest, da alama an dake shi ma, sedai cikin Jarumta yai mata murmushi yace

"meyasa kikayi Sammako haka?"

Kuka ta fashe da shi Sosai, ta kalli ɗan sandan tace  "Yallaɓai wai baku gama binciken ba? Dan Allah ku sake shi wallahi Yaya Ammar mutumin kirki ne"

Ɗan sandan yace "Ke kije gida kizo da wani Babba daga gidan ku, ko baban ku ko wani babba, 'yar mitsitsiya dake ba dake za muyi magana ba"

Mufeeda tace "haba Yallaɓai cewa kukayi zakuyi bincike ku sake shi, wallahi mijina mutumin kirki ne"

Zare ido ɗan sandan yayi yace  "Miji kuma? Ke yanzu wannan ne mijin ki, kai Ashe banda tuhumar da muke maka, akwai buƙatar Human right su bincike ka, wannan ai child Abuse ne Wannan Yarinyar ce matarka?"

Banza Ammar yayi masa ya kalli Mufeeda yace
"Ina fatan kinyi bacci jiya, dan nasan halinki"

"Wallahi yaya Ammar banyi bacci ba, aka dinga bugamin gida jiya a tsorace na kwana ga hankalina yana kanka" tai ƙarasa maganar tana kuka.

"ki kwantar da hankalin ki, ki kira Aminu a waya ki gaya masa ina nan"

"Yaya Ammar, Har yanzu basu gama binciken ba? nasan ba zaka aikata haka ba"

"Mufeeda ni kaina na kasa gane kan lamarin nan, har yanzu banga fasinjojin da ake zargin nayiwa fashin ba, sun tirsasani in amsa laifina naƙi, Amma ki kira Aminu"

"Yaya Ammar, ba zamu gayawa su Baba ba"

Girgiza mata kai yayi yace  "ba yanzu ba, kina gaya musu hankalin su ze tashi, ki bari mu ga yadda hali zeyi"

Haka Mufeeda ta koma harabar station ɗin ta kira Aminu ta sanar da shi halin da'ake ciki, Aminu ya kaɗu sosai da jin Abunda Mufeeda ta gaya masa

Yace "ki kwantar da hankalin ki Mufeeda, gani nan zuwa Insha Allah, Amma abun da mamaki gaskiya"

Befi mintuna Arba'in ba sega Aminu yazo station ɗin.

Ya shiga ya samu officer on duty, suka gaisa Aminu yace
"Yallaɓai nazo ne akan case ɗin ɗan uwana da aka kama"

Ɗan sandan yace  "Eh mun kama shine saboda muna zarginsa da haɗa kai da 'yan iska suka yi wa fasinjansa fashin waya da kuɗaɗen sa, munyi2 yaƙi ya amsa laifin sa"

Aminu yace "Amma Yallaɓai ai se mutum ya aikata laifi sannan ze amsa yayi, sannan wanda kuke zargin nan da iyalinsa da mutuncin sa beyi kama da wanda ze aikata wannan laifin ba kag.....

"Kai zaka koyamin yadda zanyi aikina ne? Su mutanen banza a fuska ake gane su?" ɗan sandan ya katse shi

Aminu yace  "A'a Allah yabaka haƙuri, yanzu meye abunyi? Ina so abani belin sa"

"zamu bada belinsa amma zaku biya yaron da akayiwa Fashi kayan sa, yaron ɗan makaranta ne yana school yanzu amma in anjima zezo, in bahaka ba mu miƙa ku kotu"

"Amma yallaɓai abunda ba'a tabbatar ba, har a yanke masa wannan hukunci haka"

"kaga idan baku shirya karɓar belinsa ba, zamu tura ku kotu a satin nan kuma kasan hukuncin fashi da makami za'a yanke masa"

Aminu yace  "Shikenan ina jinka meye abunda za'a biya yaron?"

"Naira dubu ɗari da goma ne abunda za'a biya"

Da sauri Mufeeda ta ɗago kai ta kalli ɗan sandan, idon ɗan sandan kawai ze nuna maka rashin imani, yanzu ace da ire iren wannan bara gurbin  'yan sandan a cikin Al' ummar mu ta ina za'a zauna lafiya.

Mufeeda tace "Yanzu kai ko tsoron Allah ba kaji ba, dubu ɗari fa saboda mugunta, wallahi se Allah ya saka mana, duk wanda yake da hannu a cikin yiwa mijina sharri se Allah ya wulaƙanta shi, idan da haɗin bakin ku Insha Allah sekun rasa aikin"

"Ke ni kike gayawa haka? A gaban hukuma fa kike"

"Hukumar banza da Wofi, Allah ya Tsinewa hukumar indai irin wannan ce, Azzalumai kawai"

"Ke idan baki wasa ba sena saki a ceil na koya miki hankali, mutuniyar Banza kawai"

Aminu na ƙoƙarin rarrashin ɗan sanda, amma Mufeeda ta hasala ƙarshe tace

"Kai ka isa kasani a ceil, wallahi ka sani a ceil seka rasa aikin ka har gaban Abada, indai Alfarma ce nima inada wanda zasu tsayamin a fitar da mijina, sannan a hukunta ku"

Da ƙyar Aminu yasa Mufeeda tayi shiru yasa ta tafi gida, dan indai tana nan ƙarshen ta Ammar baze fita a yau ba, seda aka kai ruwa rana Aminu yaita fama sannan aka bari Aminu yaga Ammar, Aminu ya gaya masa abunda suka ce, Ammar yace

"shikenan, Mufeeda ta ɗau wayata tayi maka transfer ɗin dubu tamanin da biyar, su kenan a Account ɗina, dama ina tara kuɗinne saboda in fara yiwa Mufeeda siyayyar haihuwa, ka ciro ka basu in bar

Please Login or Register in order to submit comment