Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗinsu, tare da basu shawarwari kuma ya jadaddawa Jalal cewar se yayi haƙuri da wasu halaye da ze ga tanayi wanda ba tayi masa a baya, yanayin ciki ne zesata yin hakan.

Sun kai kusan minti talatin a gurin doctor Salis, sannan ya rubuta mata magungunan da zatayi amfani dasu kafin ta fara zuwa awo.

Suka baro office ɗin doctor Salis sam bakin Jalal ya kasa rufuwa saboda farinciki, ɗakin da Mummy take kwance suka koma.
Jalila tace "ko zaka bawa Mummy Abinci da kanka na bata Abincin ta ƙi ci"

Jalal yace "kinga ki ƙyale ta nima idan na bata baci zata yi ba haushi na take ji, tun ɗazu nake fama taƙi ci munyi waya da Daddy jiya anyi sa'a yana Maiduguri yace yau zezo"

Jalila tace "A'a yakamata ka gwada mata ko yaya ta samu taci"

"Ke wai ina ruwan ki dani ne? Dole ne bazanci Abincin ba cikin ki ko nawa? Kinibabbiya kawai"

Tsawar Da Mummy tayi seda Jalila ta ɗan tsorata, Jalal yace "Wannan yana daga cikin abunda yasa bana zuwa gurin ki, yanzu me tayi miki dan kawai tace kici Abinci? Haba Mummy zuwa yanzu yakamata ace kindena irin wannan abubuwan da kike yi"

"ka rufamin baki tun banci mutuncin ka ba, naji duk abunda ka aikata, uwar matarka ta fini tunda har ka iya ɗaukar ta aka fita da ita tai jinyar shekara biyar, ka sa uban ka ya maida tsohuwar matarsa saboda tana ƙaunar matar ka, yanzu ba ko kunya kazo gaba na kake faɗar matar ka tana da ciki, ka je kayi duk abunda kaga dama Jalal, indai kaine na sallamawa mace kai, kaje ta maida kai cikin ta tsabar ƙauna"

Murmushi Jalal yayi yace "Mummy Allah yana son bayinsa masu godiya, idan yayi maka ni'ima ka gode masa seya ƙara maka, karki manta a baya ko kwatankwacin haka baki samu ba daga gare ni, kowa harkokin sa yake yi ba ruwa na dake, na rasa dalilin da yasa har yanzu baki ɗau darasin rayuwa ba, yanzu kome zan miki baki da taka maimai dalilin da yasa kike ƙina da Jalila, matar da kika so in Aura a baya Ilham kin gani da idonki abunda suka yi min, so sukayi su kassara rayuwa ta saboda ke, kin taɓa tunanin meyasa nake gudun ki nake kyautatawa wasu? Idan duniya da gaskiya ya kamata ki tuna Ummi ta riƙeni ta maida ni ɗa lokacin da kika ajiyeni kika tafi neman duniya, ko kin manta waye Jalal ɗin naki,? kin Manta halina ne a baya? Ba wanda zeso ya raɓeni saboda mugun halin Shaye2 da rashin girmama ɗan adam, Rayuwa ta fa ta rushene saboda ke Mummy, Abaya bama shiri da Jalila amma kin taɓa tunanin wani dalili ne yasa na ɗaukaki soyayyar mata ta da mahimmanci? Me yasa baki tsani Jawwad haka ba se Mata ta?"

Jalila tace
"ka tausasa harshe Zaujee Mummy ce"
Ɗagawa Jalila hannu yayi alamar tayi masa shiru ya ci gaba da magana

"A baya in ba mutum ya sanni ba ko yaji sunana ba se a ɗauka Arne ni saboda yanayin saka suturata ma sam beyi kama da na musulmi ba, Yanzu kalleni Mummy Allah ya shiryeni, da kinsan gudunmuwar da Jalila ta bawa rayuwa ta da koda wasa bazaki mummunar magana akan ta ba, a gabanki akace sanadin ta Asirin jikina ya karye, Mummy ko a lokacin da aka ɗaura mana Aure da Jalila ina shaye2 ban fasa ba, Amma ba wanda ta kaiwa ƙara ta, tayi aiki ba dare ba rana dan ganin na shiryu, ni wani irin butulu ne da ba zan nunawa duniya ina sonta ba, Mummy haifa ta fa kawai ki kayi, Tarbiyya ta da sauran Al'amurana mahaifina da duniya ce sukayimin, wallahi Mummy idan baki dena butulci ba abunda ya faru da Umman Ilham kema ze faru dake"

Da sauri ta ɗago tana kallon Jalal, Amma ba tayi magana ba.
Ta wani fannin Jalal gaskiya yake faɗa, Mummy wata irin mace ce ma kafiya da taurin kai, gata da riƙo wata irin zuciya ce da ita yanzu take ganin lallai Daddy yayi haƙuri a zaman sa da Mummy.

Daddy ne ya turo ƙofar ɗakin ya shigo da sallama.
Amsa masa sukayi tareda gaishe shi, yayin da Mummy ta juya baya ta rufe idon ta, gefen gadon daddy yaje ya zauna ya kai hannun goshin Mummy yace
"Sannu deejah me yake damunki haka?"
Shiru tai ko motsawa ba tayi ba balle tai masa magana.
Ƙara matsawa Daddy yayi ya riƙo hannayen ta yace "deejah fushi kike dani haka? Me yake damunki haka,? kin rame sosai"

Jalal yace "hawan jini ne yake damun ta ya hau over, ko Abinci taƙi ci, mu zamuje gida mu ɗan huta"

Daddy yace "shikenan ku gaida gida, Jalila zanzo a kwance jaka dani ba abani tsaraba ta ba"

Murmushi Jalila tayi tace "shikenan Daddy insha Allah da kaina zan kawo maka har gida"

"to shikenan Allah ya huta gajiya"

Su Jalila suka tafi gida, Daddy kuma ya zauna zaman rarrashi Amma kamar yana tunzura Mummy taƙi saurarsa, likita ya sallame ta tareda bata magunguna Daddy ya ɗauke ta suka koma gida.

Ilham fa Abubuwan babu sauƙi, ta rasa inda zata saka ranta, basu da komai komai ya ƙare musu, gashi ita kanta Ilham ɗin cikin dare tsorata ta akeyi, taita gane2 da jin sautuka marasa daɗi, ta fara gajiya da jinyar mahaifiyar ta, babu wani ci gaba kullum jiya i yau ga babu wani me kawo musu tallafi koda na hatsi ne Ilham kuma tasan bata isa ta tunkari gidan Mummy ba.

Kwanan Daddy biyu a kano amma Mummy bata saurarsa, gashi komai a hankali take yi, saboda idan ta fiye aiki se taji kaman numfashin ta ze ɗauke.

Yanzuma Daddy yana ta lallaɓata taci Abinci Su Jalila suka zo dubiya, Amma ba Jalila ba hatta inda Jalal yake bata kalla ba, Jalila tazo da manyan kwalayen turare ta bawa Daddy sannan ta bawa Mummy tace "tsarabar su ce"

Jifa Mummy tayi da jakar kayan tace
"ke nifa bana son jaraba, na meye dole sekin min shishigi? Shegiyar yarinya makira sekace mayya, a baya ma dana yadda dake ban ɗauka haka kike ba, jarababbiya in dai Jalal ne gashi nan kije ki cinye shi, daga yau in zezo inda nake karki ƙara biyo shi, shi na haifa bake ba bana son salon munafunci bazan taɓa ƙaunrki ba, bazaki taɓa wani abu ki burgeni ba, yadda Asirin da'aka yi masa ya karye haka wanda kika yi masa ze karye, in ba aikin Asiri ba ya za'ayi namiji kamar Jalal ya dinga rawar ƙafa akan yarinyar da ta dinga ci masa mutunci a gaban uwar sa, ba miyagun kalaman da bata yi amfania dasu gurin muzanta Jalal ba, Amma mara zuciya ya liƙe mata se kace ita kaɗaice mace, ni ban yadda son da Jalal yake mata na tsakani da Allah bane, tunda uwatta beyerabiya ce ta shiga ta fita an.........
"Enough Mummy" Jalal ya katse mahaifiyarsa daga maganar da take son ƙarasawa, ita kuwa Jalila ta shi tayi ta bar falon tana kuka, dan taji zafin maganganun Mummy ba kaɗan ba kai tsaye ta fice ta tafi gidan su.

Daddy ma ya fusata da abunda Mummy tayi dan haka yace "Khadija ke kam bansan me zaki gani a rayuwa da zesa ki dawo hayyacin ki ba, ina ni mijinki ne nima fa wata ce ta haife ni kika aura, kika rabani da 'yan uwana da kowa nawa, kin auri ɗan wata kin mulkeshi dan me ke baza' a auri naki a mulka ba,? ki gode Allah ke ta hanyar data dace a ke juya naki ɗan ya kike gani in da za'a miki abunda ke kikayi? Kina dama da kanki amma kina kishi da matar ɗanki wannan wane irin abun kunya ne? Hakan baze ja miki komai ba se zubewar mutunci "

Jalal yace
"tunda ba kya ƙaunar ganin Jalila nima ba kya ƙaunar ganina, sannan dan ta muzanta ni a gabanki a bayan idonki dubun ta sun muzanta ni, dukda kina mahaifiya ta idan na biye miki na cutar da Jalila se Allah ya saka mata, kin san baƙar wahalar da ta sha akaina kuwa? Dukda tana muzanta ni, Amma a bayan idonki baki san gwagwarmayar da tayi akaina ba, duk wanda yake ƙin Jalila ni yake ƙi, sannan tun bani da hankali mahaifiyarta tayi ɗawainiya dani ta kula dani, duk abunda ya faru a baya da Jalila tayi min ƙuruciya ce kuma ya wuce, Sannan ɗaya daga cikin manyan maƙiya ne da yayi kwangilar ɓata min rayuwa da shi da uban gidansa Oga KB Jalila ce tai sanadiyar zuwan su prison don ta nesanta su dani in dena shaye2, kullum muka haɗu ƙoƙarin ta da nasihar ta be wuce in dena wulaƙanta iyaye na ba musamman ke, kuma kinsani duk lokacin da ta gayan muguwar magana to tabbas ta kamani ina aikata abunda be dace bane, ni wani irin baƙin butulu ne da zan tozarta ta? So kike nima inyi dana sani inzo ina cizon yatsa kaman yadda kika yi, duk me son ya so Mata ta da dangin ta, sunmin abunda dangin uwa ta ba su yi min ba"
Jalal ya ƙarasa maganar kaman yayi kuka, ya nufi hanyar fita ya tsaya ya juyo yace
"Insha Allah Jalila bazata ƙara zuwar miki gida ba balle ki ɓata mata rai, har ga Allah a yanzu ma banji daɗin abunda kikayi mata ba" ya juya ya fice zuciyar sa a cunkushe

Jalila kam tana fita ta shige gidan su, Maama tana parlour tana shan tea Jalila ta shigo tana kuka, seda gaban Maama ya faɗi tace
"Jalila lafiya meyafaru haka kike kuka?"
Seda Jalila tayi kuka me isar ta sannan tace "Maama wai dan Allah da ba a yafiya a duniyar nan da zamu cigaba? Da Allah baya yafe laifukan mu da zamu kawo iyanzu muna morar ni'imomin sa?"
Maama ta girgiza kai tace "A'a Jalila, Kullum cikin laifi muke Allah yana yafe mana, ba dan yana yafe mana ba da tuni ya kawar damu ya halicci wanda zasu bauta masa ba tare da sun saɓa masa ba"

Jalila ta goge hawayen ta tace "Maama meyasa Mummy bazata yafe laifukana na baya a idon ta ba, ta tsaneni bata ƙaunata, kullum se tayi mitar a baya na muzanta ɗan ta a gaban ta, Maama Jalal da bakin sa ya yafe min abunda nayi masa, Amma kullum se Mummy taci mutunci na"

Maama tace "Jalila shiyasa a rayuwa dan mutum yana aikata kuskure be kamata ka dinga yi masa gatsali kana cin mutuncinsa ba, kin gama yi masa rashin ta ido ƙarshe ya zama mijinki wanda yake matuƙar ji dake, Amma mahaifiyarsa bata ƙaunarki, duk abunda kikayi wa ɗan ta na kirki ko akasin haka uwa bata mantawa, Nima ƙaunarki ga 'ya' yana ce tasa na dawo hankalina na gane kuskure na, dan haka ko nan gaba ki kiyaye muzanta ɗan mutum a gaban iyayen sa, sannan be kamata ta cigaba da ƙinki ba dan ƙoƙarin da kikayi akan rayuwarsa yafi laifukanki, ya kuma ci ace ta yafe miki"

Cikin kuka Jalila tace "bana tunanin zata yafe min ta tsaneni yadda ba kya zato na rasa ina zan saka rayuwa ta, kuma tun a wancan lokacin da ta tsawatar min ta nuna min bata son abunda nake wa Jalal da bazan kuma ba"

Maama tace "Hakane Amma kiyi haƙuri, ba'a taɓa kyale ɗan adam ba'a jarrabashi ba"

Yarone yayi sallama Maama ta amsa, yaron yace "wai Jalila ta fito su tafi gida inji mijin ta"

Maama tace "to kace tana zuwa"

Jalila na miƙewa ta zura da gudu ɗakin su.
Maama tabi bayan ta tana faɗin "wannan wane irin sakarci ne kuma? Ki taso kije ku tafi"

Cikin kuka Jalila tace "ni ba inda zani bazan bi shi ba, Mummy ta zaɓa masa matar da take so ya zauna da ita"

Maama tayi tayi amma Jalila ta ƙeƙashe tace "ba inda zata"

Jalal ya gaji da jira dan haka yazo yana ƙwanƙwasa ƙofar parlourn Maama tazo ta buɗe, Jalal ya durƙusa ya gaishe ta, wanda da se su kusa karo a hanya baze kula ta ba alhalin a gidan ta yake wuni tareda ɗan ta, tabbas idan Mummy ta dage gun raba Auren su Jalal zata tafka kuskure mafi muni.

Bayan sun gaisa Maama ta nuna masa ɗakin da Jalila ta shige tace "tana ciki tunda ta shigo bata kulani ba bansan me ya faru ba"
Jalal ya jinjina kai ya nufi ɗakin da Jalila take, ta ƙule akan gado tana ta sharar hawaye, Jalal yaje ya zauna a kusa da ita yace "Jalila ki taso mu tafi gida"
Shiru tayi ba tace komai ba.
Yasa hannu ya ɗago ta gaba ɗaya yace "kiyi haƙuri kizo muje gida se muyi magana"

"ni ba zan biki ba ka ƙyaleni, ka bari Mummy ta samo maka matar da take so ka aura"

Ɗan ƙura mata ido yayi kafin daga baya kaman wanda aka yi wa dole yace
"har kina tunanin akwai macen da zata iya zama dani bayan ke? Kin sanni fiye da yadda kowa yasan halina, Jalila just recently kika gama gayamin cewar duk tsanani bazaki rabu dani ba, yanzu har anzo tsananin da zaki karya Alƙawarin da kika yi? Duk ƙoƙarin da nake yi ba kya gani? Mene makomar rayuwar mu da ɗan da yake cikin ki idan muka rabu? Anya Jalila kina min son da nake miki?"

Ɗagowa tayi fuskarta sharkaf da hawaye tace
"Jalal idan har ina maka son gaskiya ne, to zanso in kasance da kai har cikin Aljannah, Jalal bazan so Allah yayi fushi da kai saboda saɓawa iyaye ba, Amma nima nasan tabbas zan shiga mawuyacin hali idan na rabu da kai"
Ta ƙara sa maganar tareda rungume Jalal ta fashe da kuka ta cigaba da cewa
"Jalal nayi wauta abubuwan da nayi maka a baya, Amma dan Allah Mummy tayi haƙuri karta rabani da kai, hukunci mafi tsauri da zata yi min shine rabani da kai, in aka rabamu zuciya ta ba zata iya ɗaukar hukuncin ba ina sonka Jalal, nayi dana sanin abubuwan da nayi maka a baya Amma dan Allah ku yafe min "

Tausayinta ya mamaye ilahirin jikin Jalal, gaba ɗaya jikin sa yayi sanyi ya ɗago ta suka fuskanci juna yasa hannu ya share mata hawayen fuskarta

"Babu me raba wannan soyayyar se ubangijin da ya haɗata, lokaci ne Mummy zata yi nadamar abunda ta aikata, Amma kuskure mafi muni a gare ni shine kice zaki rabu dani, Akwai hatsari a cikin aika ta hakan, ki dena kuka kar kisa Baby na cikin damuwa"

"kafi damuwa da Babyn ka dani ko?"

Jalal yace "ni na isa ina sonku gaba ɗaya, ku ɓangare ne me girma a tare da ni, Allah ya raba ku lafiya"

Jalila ta amsa da "Ameen"

Jalal yace "tashi mu tafi gidan mu"

Maƙale kafaɗa tayi tace

"sedai in zaka saimin goba me tsami"

Murmushi yayi yace "shikenan tashi mu tafi"
Ta ɗauki mayafinta suka fito, Suna fitowa Maama tace "zaku tafi ne? Jalila ina da fura zo ki karɓar muku"
Jalila tabi Maama Jalal kuma ya fita.

Maama tace "Jalila shi lamarin Aure haƙuri ake yi, karki ƙara cewa zaki rabu da mijinki akan abunda be kai ya kawo ba"

"Insha Allah Maama bazan ƙara ba"

Tabawa Jalila fura da Nono suka yi Sallama suka tafi.

Daddy kam faɗa ya cigaba da yiwa Mummy, Mummy ta nisa tace
"waini abunda ya bani mamaki shine ya'akayi yarinyar nan tasan Kabiru har tayi sanadiyar zuwan sa prison? Ko dai kuna rainamin hankali ne kawai kaida ɗanka?"

Daddy yace "se kije ki bincika, abunda ya dace kiyi kenan tun farko ba shirme da son zuciya ba"

Daddy beyi mata wani bayani ba ya tashi ya ƙyale ta.

Jalal ba ƙaramin tausayin Jalila yake ba, cikin na wahal da ita ɓangaren Abinci wataran da Asuba haka ze farka ya ganta a zaune tana cin biscuit ko goldenmorn wataran ko brush ba tayi ba, bata laulayi sedai zazzaɓin dare da yawan ciwon ciki.
Jalal ya fara shirin komawa Lagos dan hutunsa tuni ya ƙare, ya ƙara ma sosai, Jalila se rigima take baze tafi ya barta ba, ya rasa inda ze sa ransa se rarrashin ta yake amma fafur taƙi se koke koke take, ta koma masa kamar wata 'yar ƙaramar yarinya yace "ze tafi da ita Lagos tace ba zata ba makaranta zasu yi final exams"

Saura kwana ɗaya ya tafi, tana kwance a jikin Jalal tana ta zuba shagwaɓa, ya biye mata yana ta rarrashi, Wayar Jalila ce ta fara ringing Jalal ya miƙo mata wayar tasa hannu ta karɓa taga Ummi ce, zumbur ta miƙe zaune ta ɗaga wayar

"Ummi na ya kike?"

"lafiya ƙalau ya me jiki kuma?"

"lafiya ƙalau Ummi, jikin ta da sauƙi"

"Masha Allah dama zamu zone gobe insha Allah"

Tsalle Jalila tayi tana murna "Allah yakawo ku lafiya Ummi na"

Ta ajiye wayar tana tsalle daga wannan kujerar zuwa waccan tana rawa, Jalal kallon ta kawai yake yace "Ayi a hankali dai, kar ki illata min yarona dan Allah"
Zuwa tayi ta zauna kan cinyar sa tace

"Ummi ta fanshe ka mijin so, a tafi Lagos Allah ya kiyaye hanya se an dawo, gobe insha Allah zasu zo"

"Allah ya shirye ki, da su Ummi baza su zoba haka zan ci gaba da fama dake ko, kiyi ta bani wahala?"

Ɓoye fuskar ta tayi a ƙirjinsa tana dariya tace
"kaifa ranar kace Yaya Jawwad dole ya kula da Hanan tunda ɗansa ne, kaima yanzu tunda naka ne sekayi haƙuri damu"

Dariya Jalal yayi yace "ba kya mantuwa ko? Zaki ramawa Jawwad"

Dariya tayi tace "daɗin ta dai kai ka faɗa ba wani ba"

Washegari da wuri Jalal ya tafi Lagos, su Ummi kuma suka zo da Yamma, Jalila tayi murnar ganin su Ummi, Ummi da mahaifiyar ta da wasu 'yan uwan ta suka zo, Jalila ta rasa inda zata sa ranta dan murna, tai musu kyakywar tarba da Abincika kala2, Ummi taji daɗin inda Jalila ke zaune kuma ga dukkan alamu Jalila na cikin kwanciyar hankali a gidan Auren ta.
Ummi ta kalli Jalila tace

"Baby wannan ƙiba haka?, kice in fara tara kayan yara, Babyna girma yazo"

Jalila ta kalli cikin ta ta rufe fuska tace "ni bani da komai, sedai in kayan teddy wasa na zaki saiwa"

"hmm kinkusa ɗaukar teddy me rai ai, Allah ya raba ku lafiya"

"in ba da hanjina zamu rabu lafiya ba ni ba komai a cikina"

Ummi tace "Jalila baki da kunya, ko kunya ta ba kyaji ko ni zaki kalla kiyi wa wayo Allah ya shirye ki"

Rufe fuska Jalila tayi tana dariya.

'yan uwan Ummi basa jin hausa, se yarabanci turanci, da fulatanci kaɗan kaɗan.
Jalila ta sake ta sha hira da Ummi, ta gaya mata halin da ta ke ciki da Mummy, Ummi taita rarrashin ta tana bata haƙuri.
Ƙarfe goma na dare Abba ya turo da mota yace a ɗakko su Ummi, Jalila tayi tayi su Ummi su kwana a gidan ta suka ƙi suka tafi gidan Abba.

Washegari da safe Jalila ta kira Jalal a waya tace masa tana so tabi su Ummi gidan Abba ba ta jin daɗin zaman gida ita kaɗai, Jalal ya batta da safen ta shirya ta tafi gida itama.

Ummi ta shiga duba Mummy, Sam tarbar da Mummy taiwa Ummi bata ji daɗin ta ba amma ta danne ta ƙyaleta.

Kwanan su Ummi uku Jawwad yai waya "Hanan ta haihu ta haifi mace", Jalila kaman ita akace ta haihu ta dinga murna.

Maama tace "Allah ya raya, saura Nana itama Allah ya raba lafiya Jalila kuwa dama da saura"

Kwanan Hanan biyar da haihuwa Nana ma ta haihu, Itama mace ta haifa, sedai Nana seda aka mata aiki aka ciro yarinyar.

Ba'ayi suna ba seda aka jira Nana ta zo Nigeria, aka shirya gagarumin taron suna a garin Bauchi, sunan Jaririyar Hanan Zainab, ta Nana kuma Ummu Salma sunan Hajiya Salma.

Jalal yayi bajinta shi yayiwa Jarirai abun yanka, banda kyautuka da ya basu, se bayan suna Ummi ta koma garin su.

Jalila tasha labarin labor a gurin Hanan hakan yasa ta ƙara tsorata sosai, Jalal ya ɗakko Jalila suka dawo kano.

Komai ya ƙarewa Ilham, gidajen masu kuɗin unguwarsu take bi tana musu wanke2 da wanki ana biyan ta sannan ta samu na Abinci, gashi yanayin rashin lafiyar mahaifiyar ta da firgitar da take cikin dare yafara taɓa ƙwaƙwalwarta, wani lokacin da rana tsaka ma se taita zabura kaman zata zura da gudu, Abun ya haɗu ya yamutse mata, gaba ɗaya ta koma wata iri ta koma kamar wata tsohuwa gaba ɗaya a firgice take.

Jalila ciki ya fara tsufa, ta kammala makaranta zata yi service ɗinta a kano, Seda Jalal ya shirya mata walima a gida akaci aka sha ga cikin ta nan yayi girma gwanin sha'awa yayi mata kyau, 'yan uwa da abokan Arziki sun halarci taron sosai.

Har yanzu Mummy a ƙule take da Jalila, bata sonta sam bata ƙaunar yadda Jalala ke nan nan da Jalila, haka dangin Daddy ma suna matuƙar ƙaunar Jalila tanada kirki ga kyauta, ɓangaren Daddy ma yanzu ya dena ɗaukar abunda Mummy ke masa a baya, duk sati uku yana zuwa ya ganta amma halinta yake sawa yaji baya son zuwa inda take, Hajiya Salma kam tana ta ƙara ƙoƙari gurin ganin ta kyautata wa Daddy, Sosai hawan jini ya taso Mummy a gaba, yanzu ko gani bata yi sosai seda glass hawan jini ya taɓa mata zuciya da kuma ganin ta, ga dukiyar a jibge amma bakomai take iya ci ba, ba ko ina take iya zuwa ba saboda yanayin larurar da take ciki.



Jalal koya tafi Lagos baya iya daɗewa saboda hankalinsa yana kan Jalila, yana tausayin ta bakomai take iyayi ba cikin yayi girma, dan haka ya ɗauke ta ya tafi da ita Lagos yaci gaba da kula da ita.

Wani labari ne ya iske Mummy daga kamfanin Jalal abun ya matuƙar girgiza ta ya ɗaga mata hankali hakan yasa ta kira Jalal a waya tace lallai yazo tana son ganin sa, ya sanar mata yana Lagos tace "lallai ya bar abunda yake yi ya dawo"

"Mummy a ƙarƙashin wasu fa nake aiki, haka akeyi kawai in taho ba tare da izini ba, idan na samu matsala fa?"

"Jalal dole ka bar wannan banzan aikin ka dawo ka kula da dukiyar ka akwai matsala, bazan lamunci abunda ke shirin faruwa akan dukiyar ka ba"

Cikin rashin fahimta Jalal yace "meke shirin faruwa akan dukiyar tawa?"

"idan kazo ka ji"



Comment yayi ƙasa fa ko kun gaji ne, nima se in tafi hutu se kun ganni 😡😡😡😡




Share please

07063065680
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔸𝔻𝔼ℝ𝕊💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 6️⃣3️⃣117

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724



_MY FIRST NOVEL _

Ajiye wayar Jalal yayi tare da dafe kansa yayi shiru, Jalila tace "me yake damunka ne, Ina fatan dai lafiya ko?"

Cikin damuwa yace "Mummy ce ta kirani wai lallai in koma tana son ganina, Akwai abunda taji yana shirin faruwa akan dukiya ta"

"Subhanallah Allah yasa dai lafiya? Yaushe zamu koma kenan?"

"ba inda zani" Jalal ya bata amsa

"Saboda me? Kiran mahaifiyarka ne fa"

"Nasani Jalila nasan akan abunda take magana, indai zan biye wa Mummy bazan taɓa abun Arziki a rayuwa ta ba, shiyasa bana son raɓarta komai nata na son kanta ne"

Jalila cikin sigar rarrashi tace "Jalal me yasa kake me tausasawa ga wasu can bare amma baka iya tausasa wa mahaifiyarka, duk wanda yakamata ya more ka a bayan ta yake, kayi haƙuri da

Please Login or Register in order to submit comment