Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

harkar Maama, har gara Jawwad ma yana zuwa gaisheta, Nana kuwa seda Jalila tasata a gaba ta nuna mata be dace ba abunda take yiwa Maama, wannan abunda yafaru tsakanin ta da Abba ne da kuma' yan uwan ta, sannan ta samu Nana ma take shiga sabgar Maaman, Abba ya gayawa Maama ranar Lahadi zasuyi baki, za'a kawo kudin Auren Nana, abakin su Nana taji batun haduwa da 'yan uwan Abba a Bauchi, ba tayi mamaki sosai ba jin ance su Hanan' yan uwansu Abba ne ba, sakamakon matukar kamannin dake tsakanin Jalila da Hanan, sedai taji haushin rashin sanar da ita da Abba beba.

Tun ranar Juma'a suke shirye2 domin bakin daza'ayi, Jalila ce jagorar girke2 da shirin yadda za'a karbi baki.
Gefe guda Jawwad yana ta shirye2 Ranar litinin shima ze tafi gurin nasa Aikin, ba karamin kulawa Hanan take bashi ba, da soyayya da kuma shagwabarta, yanayin yadda take nuna yarinta a wasu bangaren ba karamin birge shi yake ba.

Kamar yadda aka saka ranar lahadi daddyn Hanan yazo Kano aka karbi kudin Auren Nana, itama lokaci dayane dana Jawwad dakuma Abdallah Yayan Hanan, ranar har mutan bauchi seda sukazo garin kano karbar kudin, da kuma kara taya juna murnar haduwar su a matsayin 'yan uwa. Jalila taji dadi da akazo hadda Hanan da Mummynta, Maama seda ta sha jinin jikinta ta raina kanta ganin manyan mutanen da sukazo gidan, Abun Arziki ya hadu dana Arziki, dangin Su Jawwad dana Su Jalal, Ranar anci ansha, kai ka dauka bikin Aure akeyi rana ce me matukar tarihi da wannan Ahali bazasu manta ba. Jalila sam bata samu kebewa da Hanan ba, saboda Hanan na manne da Jawwad, sam bata jin kunyar kowa take nuna masa soyayya.
Mummyn Hanan se mita take tace "Ni gaskiya naso a hada abun nan hada na Jalila, in aurar da 'ya' ya uku, amma in shirya da kyau, amma bakomai anata se nafi shiri ko Jalila?"
Ita dai Jalila sedai tayi murmushi ta sunkuyar da kai.
Duk yadda Maama take jin kanta take kuma jin haushin Auren Hanan da Jawwad boyewa tayi, Saboda sam bata da makusa, 'yar dangi ce, kuma' yar uwar dan tace, tana da kyau dai2 gwargwado kuma tana da Ilimi, yanayin kyau da gayun mahaifiyar Hanan ya isa ya nuna maka 'yar ta ma hakan take. Koda ta hasko Naja seta ga abun se A hankali, kuma tun abun nan da sukayi mata ta tabattar da Ko Auren akayi Naja zata iya wulakanta ta.
Da ire iren wannan tunanin yasa ta ajiye duk wani bacin rai aka shiga hada2. Tareda tsara yadda suke ganin bikin ze kasance, Ba laifi Mummyn Hanan ta saki jiki Maama, Sunyi hira sosai kaman sun saba, sannan suka tattauna akan yadda harkar bikin yaran nasu ze kasance. Se la'asar Suka tafi, mutanen Bauchi suka tafi, Su Hanan ma a ranar suka juya kaduna saboda Su Hanan suna jarrabawa, su kuwa danginsu Mahmud, suna kawowa Mahmud kudin Aure sukaci Abinci suka juya Borno.

Wasa2 sosai tunanin Jalila ya hana Jalal sukuni, da yafara aiki in ya tuna da ita gaba daya se yaji duniyar tayi masa zafi, yarasa inda zesa kansa, meyasa Mummy tayi masa haka? Idan yaji abun ya dameshi se ya tafi club yaje ya cika cikinsabda giya, dukda wasu lokutan yana bawa aikin da yaje yi mahimmanci, Sam Jalal bashi da sakewa da mutane, dan haka be saba da kowa ba, sedai yana girmama shugabanninsa na gurin aiki, girmamasun da yake besa sunga alamar ze bari su taka shi ba, inda yake burgesu yana maida hankali akan aikinsa sosai.
Duk lokacin da yaje Club mata da suke damun sa ne ga kuma shigar tsirara da suke yasa shi dakatar da kansa ga zuwa Club, idan yaji ba yadda zeyi se yayi shaye2 se yayi abunsa a dakinsa na hotel da yake ciki.
Amma duk da haka yarasa dalilin da yasa mata ke binsa, sedai in baze fito ba.

Hannah ce zaune akan kujera tana kwalliya, Sa'ada na kwance akan gado tana danna waya, dan dakatawa da kwalliyar Hannah tayi ta dan kurawa madubi ido, sekuma can ta daki kan mirror tace "Impossible baze yuwu ba wallahi"
Sa'adah ta waigo ta Kalle ta tace "lafiya kuwa?"
"Akwai matsala Sa'ada" Hannah ta bata amsa
"matsalar me fa?"
"Sa'ada ki kalleni ki kara, kimin kallon tsaf tun daga sama har kasa, ki kalli yadda nake gara kan maza, in taka wanda naso in wanke wanda naso, amma a hakan har rububina wasu suke, in sauke Ajina in cewa Jalal idan ya Aureni zan dena bariki, Amma ya watsa min kasa a ido"
Wani dogon tsaki Sa'ada tayi tareda fadin "Nina dauka ma wani mutumin kirkin ne, A she akan wannan mashayin ne, ni ba wannaan ya dameni ba a yanzu"
Hannah tace "Mutumin kirki ne mana, ki kalleshi kallon tsaf Sa'ada Namiji ne irin wanda duk wata mace zatayi burin Aure, shaye2 ne kawai matsalar sa, da farko da nakewa su Jeje aiki, nna zata zan samo kansa ta sauki ya yadda dani, Amma duk wata dabara da kisisina ta matan bariki nayi amma yaki amincewa dani"
"to kibi wani mana, ko shine kawai namiji?"
"bazaki gane ba Sa'ada, bakiga irin kirar da Allah yayi masa bane, kuma da kike ganinsa a haka, dukiya ce dashi kaman abun banza"
"Ya akayi kika sani, nasan dai babansa yana da kudi, amma shikam ko aikinyi ba shida shi" Sa'ada tayi maganar tana yatsina fuska
"Hmm to wallahi har ki mutu in ba wani ikon Allah ba, kaf danginku daku da abunda kuka mallaka, bazaku kaishi dukiya ba, yana da kudi da mahaifinsa yasa ake juya masa, Jeje yaso ganin bayan dukiyar nan shida mai gidansa amma abun be yuwu ba suka kare a prison"
Sa'ada ta tashi zaune tace "to ke yanzu meye abunyi, ni ban taba sani ba, kin san ya taba kusa tonamin Asiri ina zuwa club agaban babarmu"
Dariya Hannah tayi tace "Abune mawuyaci ya tona miki Asiri, bar ganinsa a haka, yasan abunda yakeyi, naje har gidansu na dana masa tarko, amma ga dukkan alamu ya tsallake shi, wannan karon zan masa tarkon da zan rike shi a wuya, be isa ya kuma subuce min ba"
"Yakamata kam, Amma ni nan tunanin yadda zan huce abunda abokinsa Jawwad yayiwa Naja nake, kiri2 yafasa Auren ta, yarinyar nan duk ta shiga damuwa"
"Allah sarki, to wai ya'akayi aka fasa Auren? Waye yaje yai mata gulma a gurin baban nasa?"
"ya za'ayi in sani, Amma da nafi kyautata zaton wannan munafukar kanwar tasa ce"
"Wace kanwar tasa ya'akayi tasan abunda Naja take? Ko dai itama tana ta bawa?"
"Ke bari, wata yarinyace yadda kika san boka haka take, ni dai ban san tana wani biye biye ba, Amma kina zaune in taso seta nemo waye ubanki koda ke baki sani ba, wai ita Jalila makirace ta bala'i, idan tace bata san abu seta ga bayansa, tasa Jawwad ya fasa auren Naja se kawarta"
Jin an ambaci Jalila yasa Hannah zare ido tace
"Kan bala'i ai nasan wannan yarinyar, tabdijan ni zan gaya miki makira ce, ke wallahi keda kike bariki tafi ki iya rashin mutunci, ke zata iya yuwu wa ita tasa aka hana, bari in gayamiki yarinyar nan tafiki bala'i, dan koni tasa min ido akan Jalal, ita take rusa min komai "
Cikin mamaki Sa'ada ta kalli Hannah tace" wai kin santa ne? "
" Nikuwa na santa, kuma nasan illar ta, munyi Arranging da Jeje mun gama komai, zamu sace Jalal ranar birthday din sa, idonta na kanmu, muka bugar da shi da giya ta shammace mu tasa aka dauke shi daga gurin, ke ina jin kishin cewa ita tasa aka kama Oga KB"
Zaro ido Sa'ada tayi cike da mamaki tace "Ke haba dai? Shikuwa oga KB yana me,duk iya kuri da gadarar rashin mutuncin nasa, yarinya ce fa karama"
Hannah tace "hmm ke dai bari, mace kenan, kaidin wata yafi wata, irinsu kuma sa'a ce dasu a rayuwa, kibi a sannu kawai"
"Tabdijan amma babu kama, dan bakiga cin mutuncin da muke mata ba mu da babarmu, kin san uwarta tsohuwar arniya ce, bakiga cin mutuncin da muke mata ba"
Hannah tace "Yawwa kuma ga cin mutuncin da tayi muku nan, kuma ta gama daku ba"
"Sosai makuwa ta gama damu"
"shiyasa wannan karon shirina ita da Jalal ne, dan bana ta wannan Ilham din dan wannan ba mace bace, wannan tafi hatsari, baze tsallake wannan tarkon ba a yanzu, na duba mashayar da yake zuwa ba adadi amma ance ya dena zuwa, duk da haka zan nemoshi"

Yauma duk da tarin farinciki da Jalila ta tsinci kanta a ciki yau, amma bacci ya kauracewa idanuwanta, jikinta na bata Jalal yakoma shan giya, da kyar ta samu bacci ya dauke ta, amma mafarkin Jalal a cikin wani yanayi na shaye2, yasata farkawa, gabanta na wata irin mummunar faduwa, wayarta ta dakko ta duba karfe biyu da rabi na dare, ga shi ita ba lambar Jalal ce da ita ba, tarasa mema zatayi gallery dinta ta shiga tana dubawa, tsofaffin ajiyayyun hotunan ta take dubawa, hotunan da sukayi da Jalal tun wani zuwa da Hanan sukayi, haka taita kallon hotunan, a haka har ta kawo kan hotunan birthday dinsa, cin karo tayi da wani hoto da'akayi harda Hannah a ciki, take gaban Jalila ya fadi, dan sam ta manta da Hannah, kuma barin Hanna ba tareda daukar wani mataji ba tamkar kashe maciji ne ba'a sare kansa ba a rayuwar Jalal.
A hankali ta ajiye wayar, ta sakko daga kan gadon ta shiga toilet tayi alwala tazo ta tada salla.

Ranar litinin Jawwad shima yayi nasa shirin tsaf domin tafiya Gurin nasa aikin dake birnin tarayya, Abba yayi masa Nasiha sosai tareda sa masa Albarka, haka ma bangaren Maama, tayi masa Addu'a da sa Albarka, dukda marin da Maama tayi masa akan Naja, hakan besa ya nuna mata har yanzu yana fushi ba, Bangaren Jalila kuwa har kuka tayi, saboda zatayi kewar Yayan nata sosai
Abba yace "Jalila kina kuka dan zeyi tafiya, kuda kwanan nan zeyi Aure gaba daya zasu bar gidan, su barki seke kadai"
Kara fashewa da Kuka Jalila tayi, Nana tace "Abba ka gani ko? Wannan yar taka ta fiye shagwaba wallahi"
Jawwad yace "haba babyn Abba, sekace ba jaruma ba, zan dawo ai kidena kuka"
Sukayi ta tsokanarta ita kuwa dagaske take kukanta.
Haka sukayi sallama da Jawwad shima yakama hanyar tafiyar sa.

Jalal yana waya da daddyn sa sosai, sannan suna waya ds Jawwad, suna shirye2 yadda biki ze kasance a tsakanin su.
Abban su Jawwad yana kasuwanci ne a tsakanin Kano da lagos, dan haka in yaje suka haduwa da Jalal.

Jalila Nason sanin halin da Jalal yake ciki, amma babu wata hanya da zata san hakan, dan haka taketa kokarin boye damuwarta.

Maama Allah ya temaketa Abba ya sakko daga fushin dayake da ita, sannan tunda abun nan ya faru Su Yaya mairo ko a waya basu kara neman Maama ba, abun ya dameta sosai dan haka ta shirya da kanta taje gidan su.
Tunda tayi sallama suka amsa suka shareta suka ki kulata, ita tayiwa kanta gurin zama, ta gaida Yaya mairo amma taki kulata, seda ta bata 'yan kayan data saba kaimusu, shine Yaya mairo ta dan saki rai suka gaisa, Naja ta gani a lullube tana bacci, Maama tace "Yaya, Naja ba lafiya ne?"
Kafin Yaya mairo ta amsa Naja ta fara magana cikin maye "Ni... Ni.. Ba... Wallahi baaaaani da.... Da lafiya, Shiyasa naiwa kaina caaajiii, baaaa danki yaki Aure na baaaaaa, wallahi....
Cikin tsawa Yaya mairo tace" yimin shiru dan ubanki, ciwon mara take, shine ta sha magani fiye da ka'ida"
Gaba daya jikin Maama yayi sanyi saboda babu tantama Naja maye takeyi. Shiru tayi takasa cewa komai, Naja ta cigaba da surutai, can kuma ta kwalla uwar kar, sega jini na gudu a tsakar dakin daga karkashin Naja.

Se bayan la'asar su Jalila suka gama lectures ta gaji matuka, haka kurum tun suna lectures takejin gabanta yana faduwa, da kyar ta tsaya aka gama lectures ta fito, danma manu direba ne yaje dakko ta daga school, abunda yabata mamaki be wuce ganin motar Hannah a gabansu ba, tana tsala gudun wuce sa'a, kuma da alama layinsu zata shiga, Jalila tasa Manu direba yayi parking a farkon layinsu, ta sauka ta shiga layin da kafarta, aikuwa tana zuwa taga Hannah tayi parking din motarta ta shiga gidansu Jalal, Jalila batayi shawarar komai ba ko tunani tabi bayan Hannah zuwa cikin gidan.






Masu kirana a waya please am sorry, ku dinga min magana ta what's App, ina kokarin duba messages, amma kira musamman idan ina aiki, bana samun daga bakuwar lamba am sorry.
Ina godiya da kulawa.




Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
πŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈ

What's app only 07063065680.
Watpad @Ayshercool7724
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(π•Žπ”Ό 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 π”Ήπ•Œπ•‹ π•Žπ”Ό'ℝ𝔼 π”Έπ•ƒπ•Žπ”Έπ•π•Š, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 π•†π•Œβ„ π”Ήπ”Όπ•Šπ•‹ 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ π•†π•Œβ„ β„π”Όπ”Έπ”»π”Όβ„π•ŠπŸ’ͺ)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 4️⃣5️⃣98

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724



_MY FIRST NOVEL _

A hankali Jalila ta cigaba da bin bayan Hannah, ba tareda ita Hannah ta sani ba, Hannah ta bude kofar babban palourn ta shiga, Jalila ta biyo bayanta amma ta tsaya a corridor yadda ba wanda ze ganta, Hannah ba karamin mamakin kyai da tsaruwar gidansu Jalal tayi ba, an kashe masa dukiya matuka, tun daga harabar gidan zaka gane mzauna gidan na cikin ni'imar ubangiji ta dukiya da yake bada ita ga wanda yaso a lokacin da yaga dama.
Koda ta shiga palourn ba kowa, seda ta tsaya ta karewa tangamemen palourn kallo, sannan ta jinjina kai tareda yin ajiyar zuciya, ta fara sallama, Mummy dake kitchen ta amsa tareda fitowa da jug a hannunta, suka gaisa da Hannah, Mummy na mata kallon rashin sani,
Mummy tace "bari in kira miki Ilham din, dan a zatonta kawarta ce" Hannah tace "A'a ba gurinta nazo ba, Mummy dan Allah Jalal fa?"
Mamakine yakama Mummy amma ta dake tace "Ai kusan watansa guda baya gari, yana lagos"
Hannah tace "Ai dole ya lallaba ya gudu lagos mana, Ina fatan mahaifinsa yana nan"
Mummy tace "lafiya kuwa?"
"Ina fa lafiya, ina son ganin mahaifinsa tunda shi baya nan"
"me mahaifinsa ze miki ne? Ki gayamin menene?" hakan yayi daidai da fitowar Ilham da alama fita zatayi, kawai taga Hannah, take gabanta yayi mummunar faduwa, kirjinta yafara dukan goma2, ta wani hade rai, ta karaso palourn cikin kasaita kaman gidan father dinta, tazo ta tsaya tareda kama kugu tanawa Hannah kallon da wacce kika zo?.
Kallo daya Hannah tayi mata ta dauke kai, tareda yin murmushi a ranta ta kalli Mummy tace "Gara in gayawa mahaifin Sa abunda ake ciki, na gaya masa wancan karon be dau mataki ba, shi namjine ke ba lallai ki iya daukar abunda zan fada ba"
"ki Fadamin bakomai ni mahaifiyarsa ce ai"
Hannah ta gyara zama, sannan ta kalli Mummy tace "wancan karon da nazo nayiwa mahaifinsa magana, nace yayi yadda zeyi a hadu mu rufawa juna asiri amma ba'ace min komai ba, nikuma asirina yana daf da tonuwa, Ina dauke da cikin Jalal na watanni uku a yanzu"
Da sauri Jalila tasa hannu ta toshe bakinta tana zare ido, gaba daya taji kafafuwanta suna rawa.
Hannah ta cigaba da cewa "muna haduwa da Jalal a hotels, kokuma idan yake night clubs, yasaba yimin ciki yace in zubar, wannan karon likita yace rayuwata na shirin fadawa hatsari muddin na zubar da cikin nan, ga iyayena na kokarin ganewa, soyayyar Jalal ce tasa na bashi kaina, wallahi koya aureni ko nayi kararsa ya kula dani da dansa"
Hannah ta karasa maganar cikin kukan kisisina, kasa magana Ilham tayi saboda mamaki.
Hatta Mummy kasa motsawa tayi daga inda take, se ido da take bin Hanna dashi
Hakan yayi dai2 da fitowar Daddy sakamakon jin hayaniya sama2
"lafiya me yake faruwa haka?"
Kafin su bashi amsa, ya sauke idonsa akan Hannah, be manta ta ba, ya kalleta yace "yarinya lafiya kuwa?
Cikeda karfin hali Hannah ta korawa daddy bayani kamar yadda tayi wa Mummy
"Karya kikeyi, Wallahi Jalal baya neman mata, mata basa gaban shi, yana shaye2 amma be yadda da neman mata ba, Jalal ba mazinaci bane ba" Ilham tayi maganar ilahirin jikinta yana rawa
"Masha Allah, dukkan yabo ya tabatta ga Allah, kin fadi magana kuma kin karyata kanki Ilham, tunda kinsan Jalal ba mazinaci bane, ta yaya kika san ina bashi kaina?"
Jalila ce ke maganar cike da kwarin gwiwa, gaba daya suka juyo inda Jalila take, kanta tsaye ta tako har gaban Ilham ta Kalle ta ido cikin ido tace
"Nagode Allah, kinyiwa Jalal kyakyawar sheda, yadda baya neman mata nima ba'a haifi namijin da Jalila zata bashi kanta a titi ba, Wallahi Ilham kinji kunya, tun wuri ki canza hali, tun kafin ki kaini bango in miki abunda se kin kasa shiga mutane"
Ta juya ta kalli Hannah tace

"Ni na manta da ke a doron kasa, in ban manta ba haduwar mu ta karshe yafi shekara, katsam jiya kika fadomin a rai, da irin abubuwan da kike aikatawa, haka nan naji kasa sakewa, zuciya ta tanata bani wani abu zw faru, katsam akan hanyata naga motarki na kokarin shigowa layinmu, shiyasa na biyoki dan duk inda kikaje babu Alkhairi Hannah "
Gaba daya kan Hannah ya kwance bata taba tunanin zata hadu da Jalila a wannan lokacin da take shirin hurawa Jalal wutar da babu me iya kashe masa ba.

Jalila ta kalli daddy tace
"Wallahi daddy karya take yiwa Jalal, ba wani abu dayake tsakanin ta dashi, sema ita da take kokarin cutar da shi"

With full confidence Hannah tace

"Karya kike inyiwa Jalal karya, ina dauke da cikinsa ne, kuma wallahi wannan karon bazan zubar ba, kamar yadda yasaba sani ina zubarwa"

Cikin tashin hankali daddy yace "Jalal din nawa ne yai miki ciki? Kiji tsoron Allah, bana tunanin hakan ze faru, wancan karon akan wannan maganar yayi fushi har ya nemi ya bar kasar nan, narasa waye me gaskiya a tsakaninku"

Jalila tace "Daddy ka kyale ta taje ta kai duk inda zata kai, Kai ka haifi Jalal kasan abunda ze iya da wanda baze iya ba, kasan baya shakkar kowa, idan ya aikata baze ji tsoron gaya maka ba, Daddy karya takeyi wallahi, I dan ba haka ba, taje ta shigar da karar"

Sosai Jalila take kokarin kare Jalal, abunda yabawa daddy mamaki, dan agabansa ya sha ganin irin artabun da sukeyi da Jalal, amma wani tabbaci take da shi akan Jalal haka, kuma y'a kayi tasan Hannah?
Ilham kam harar Jalila kawai takeyi ji take tamkar taje ta maketa a gurin, sekace Jalal din ubanta ne, ita so take tayi amfani da wannan damar, a tirsasawa Jalal yin Aure, amma Jalila nata karewa.
Mummy tace "Waike meye haka? Ban hanaki shiga duk wani shirgi daya shafi dana ba, banda munafunci da son jin kwakwaf hada biyo ta kizo kiji me ze faru, kina.......
"Rufe min baki khadija, Kinsan meyasa take kokarin kareshi, meye da dannaki da kike wani kumfar bakin adena shiga harkarsa"?
Daddy ya kalli Jalila yace "Jalila a ina kika san wannan yarinyar?"
Jalila ta kalli Hannah tace "daddy nasanta a gurin birthday din Jalal ne, Kuma sannan"
Sekuma tayi shiru, "Sannan kuma me?"
Daddy ya tambayeta, Jalila tace "bakomai daddy, amma makaryaciya ce"
Hannah ta fashe da kuka tace "Shikenan tunda ba 'yar kuce niba kun zabi zubewar mutuncina, wallahi mutuncina baze zube ni kadai ba, ku saurari sammaci, wallahi karar Jalal zanyi"
"Karki fasa sekin dawo, Amma idan har karya kike abunda ya faru da iyayen gidanki ze faru dake, idan har kin iya makirci za' a nuna miki ranar dukiya, ki fice kibar gidan nan da kafafuwanki kafin insa akama min ke"
Hannah ta tsorata da gadar zaren da Jalila tayiwa su Jeje suka rufta, dan haka ba kunya ta juya zata fice, daddy yace "Amma ta tafi ba'a gano bakin zaren ba"
Jalila tace "daddy ka rabu da ita, ko ta kai kara, kota bari ya dawo ayi maganar amma babu dalilin da zesa ta dinga maka karya tana bata maka rai akan danka"
Ta juya ta kalli Mummy tace "Mummy Allah ya huci zuciyarki, ban biyo Hannah dan shiga cikin lamarin iyalinki ba, sedan sanin hatsarin Hannah ga rayuwar Jalal, Amma Insha Allah kome ze faru bazan kuma shiga lamarin ba, in dai ya shafi gidan nan"
Ta juya zata fice, daddy yace "Jalila ita wannan yarinyar wacece? Sannan meye hatsarin ta ga Jalal? Menen alakarsu?"
Jalila tace "Daddy ba a bakina yakamata kaji ba, amma dai nasan babu wata alaka ta kusa dake tsakaninsu, na tafi se an jima" ta juya ta fice zuciyarta cike da bacin rai.

Maama ta dubi Yaya mairo tace "Yaya wannan jinin kuwa na lafiya ne?"

"Al'adace haka yake zuwar mata"

"haba Yaya, kalli guda gudan dayake zuba kice min Al'adace, yakama tunda nazo da mota mu kaita Asibiti"

"ba wani Asibiti da zamu kaita" yaya mairo ta bata amsa tana kokarin temakawa Naja ta mike zaune, amma tana tabata taga bata motsi, numfashinta da kyar yake fita, ga jini se cigaba da fita yake daga jikin Naja, ba shiri Yaya mairo ta mike, Maama ta temaka mata suka gyara Naja, suka sata a mota se Asibiti,
Sunkai awa biyu suna jira, Yaya mairo takira Naja a waya, tazo suka hadu a Asibiti, likita ya fito ya tambayesu alakarsu da Naja, sukayi masa bayani, yace su bishi office dinsa, haka suka bishi sukaje suka zazzauna suka zubawa likita ido, ya danyi gyaran murya sannan ya kallesu yace
"To kun san duk abunda yasamu bawa mu kaddarine daga Allah, kuma Allah yana jarrabar bayinsa ta ko ina, kuma dukkan musulmi se yayu Imani da kaddara sannan Imaninsa ze cika, Hakikanin gaskiya mara lafiyar ku tana dauke da ciki karami, kuma tayi Amfani da miyagun kwayoyi wanda hakan yayi sanadiyar zubewar cikin jikinta da kuma lalacewar mahaifarta"
"Innalillahi wa inna ilaihi raji un" shine abunda suka dinga nanatawa, gaba daya Maama taji jikinta yafara rawa, Yaya mairo ta dora hannu aka tafara ihu, likita yace "Haba baiwar Allah kamar ba yanzu nagama yi miki nasiha ba, ba wannan bama, yarinyar nan ta zubar da jini da yawa, Akwai bukatar a sama ta jini, kuma a bincike da mukayi tana da cutar Hepatitis B, (ciwon Hanta), dan haka ku gaggauta nemo Jini, a duba a 'yan uwa wanda jininsu yayi dai2 se a samata"

Haka suka fiti office din nan suna salallami, jiki a sanyaye Yaya mairo tace "bari a kira yayanta a waya, Zainab kira Jawwad suzo

Please Login or Register in order to submit comment