Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce take magana, da suka shigo ita da Maama, tace

"duk Nasihar da'akayi miki baki jiba kenan? Meyasa bazaki dauki kaddara ba, ko ba'ayi haka ba dama Allah ya rubuta shine mijinki"
Kuka Jalila takuna fashewa da shi maama tace

"Jalila kidena kukan nan haka, batun mahaifiyarsa bata sonki ze wuce, musamman idan ta gane mahinmancin ki ga danta, Jalila tunda kika iya jure rayuwar gidana duk taren kalubalen da kika fuskanta daga gareni da 'yan uwana, bana tunanin akwai wani kalubale daze tsoratar dake, Anmiki ba dai2 ba tabbas, Amma kiyi hakuri ki rungumi kaddara ki riki mijinki, ki masa biyayya, idan kikayi hakuri kikayi biyayya se Allah yayi miki Rahama saboda hakan"

Mummy tace

"wannan gaskiyane, kuma shi Ahmad da kike magana, ai Daddy ne yace ya bashi da farko, yanzu kuma ya bashi hakuri, Jalila na tabattar nan gaba sekin fi kowa jin dadin zama da shi"

Jalila sam bataji nasiharsu na shigarta ba, ita kawai an gama da ita basu san waye Jalal bane shiyasa suke fadar hakan.
Maama tace
"Nana ki shirya kayanku, gobe in Allah ya kaimu hadda ita zaku tafi maiduguri"
Jalila na jin haka ta kuma rusheewa da kuka.
Yusuf ne ya shigo dakin shima a fusace yana fada

"haba Mummy, meyasa daddy zeyi haka dan Allah? Yaza'ayi a Aurawa yarinya wanda bata so, kuma bayan yasan ďan shaye2 ne, a family din nan ba wanda aka taba yiwa Auren dole meyasa za'a fara akanta?ga shi sam wannan yaron bashi da mutuci, ga gadara da girman kai"

Mummy tace

"Sannu jagoran marasa kunya, meyasa bakayiwa daddyn ba seni? Kafi su sanin abunda yakamata ne?"
Hanan Kallon yaya Yusuf kawai take yadda yake zakewa yana masifa

Jawwad nai yai sallama a dakin shima fuskarsa dauke da damuwa, ya hango Jalila ta takure a gefe idon nan kaman gaita saboda ja, ga fuskarta duk ta kumbura. Bebi takansu Maama ba gaje gabanta ya tsuguna yace
"Baby why? Meyasa kike kuka haka? Gashi baki da lafiya? "

"ba dole yarinya tayi kuka ba, an mata Auren dole, an Aura mata ďan shaye2 wanda bata so"

Jawwad yace

"Yusuf meye haka? Ana kokarin hankalin ta ya kwanta kana son ka kunna wata wutar, koma dai meye an riga an daura Auren nan, ayi musu Addu'a da fatan Alkhairi mana" Jawwad ya kalli Jalila yace

"We are sorry Baby, kaddara ta riga fata, dana san ba kya son Jalal bazan bari ayi Auren nan ba, saboda nasan Jalal baze ban kunya ba shiyasa na amince"

"Yaya Jawwad ni bana sonshi"

"Jalila kulawar da kike bashi da babu so bazaki yi ba, na miki Alkawarin Jalal baze bada kunya ba, kuma shi Alkhairi ne a rayuwarki, dan Allah Jalila ki kula da rayuwar Jalal kamar yadda kike yi abaya, Nabaki amanar ďan uwana please Jalila" ya karasa maganar kamar zeyi kuka.
Girgiza kai Jalila ta shiga yi
"Yaya Jawwad....
"Shhhh kiyi shiru, ki karbi Amana ta kidena wannan kukan"

Hanan tace

"Jalila son da Haidar yake miki baze bari a baki abunda ze cutar dake ba kiyi hakuri da kaddara Queen"
Jalila shiru ta musu ba tace komai ba, ita ka dai tasan me takeji a ranta.
Jawwad ya mike yace
"Mummy seda safenku" sukayi sallama.
Yusuf dai ya cigaba da banbami da mita.
Su Maama suka cigaba da rarrashin ta tareda Nasiha.
Hanan kuma ta shiga hadawa Jalila kayanta dukda tarin gajiyar biki dake tare da ita.

Jawwad yakoma masaukin Jalal, ya tarar Jalal yana shirin kwanciya, Jawwad yace
"Ango ka sha kamshi"
Jawwad ya lura kaman Jalal baya walwala
"Jalal Lafiya kuwa? Naga kaman baka walwala, ko baka son Auren"?

"Jawwad ba wai bana son Auren bane, idan inason Auren itafa?"

Jawwad ya dafa kafadarsa yace

"brother karka damu, nasan zataji babu dadi da farko, saboda an mata bazata ba tareda masaniyarta ba an daura mata Aure, Amma nasan tana sonka, kuma a hankali zaku daidaita cikin kankanin lokaci"

Jalal yace

"Hmm haka dai kake gani"

"Hakane ze kasance, ni dai gata nan Amana Jalal, kayi hakuri da ita"
Jalal bece komai ba ya danyi murmushi, daga nan suka shiga wata hirar.

Hatta Inna ba'a barta a baya ba gurin rarrashin Jalila da yi mata nasiha, dan ita Inna har cikin ranta Jalal yayi mata, dan seda ta zage Yusuf tsaf saboda masifar da yakeyi akan anyiwa Jalila auren dole.

Jalila dai yau tayi kwanan bakinciki, dan sam bacci ko na minti goma batayi ba, Ga Jalal ya kwace mata waya balle ta kira Ahmad, gaba daya tausayin Ahmad takeji, yasaka rai akan Aurenta, yana da matukar kirki ya nuna mata soyayya, shiko wannan Jalal din da magana se ya ga dama ta ina ze nuna mata wata soyayya. Har akayi kiran sallar Asubah batayi bacci ba se sakawa da kwancewa, bayan tayi salla ta koma ta kwanta tana jin yadda kanta ke sarawa, ga kirjinta da yayi mata nauyi, se karanto Addu'oi take daban2 ko zuciyarta tayi sanyi.
Wajejen karfe bakwai da rabi, Mummy tazo ta kira Jalila suka tafi cikin gida, dakin da'aka sauki hajiya Salma ta kaita, mutane sun ragu sosai duk an watse, se tsirarin mutane da zasu raka Hanan Abuja, sekuma ma'aikata da suke ta kokarin gyara gidan.
Bayan sun shiga Jalila kanta a sunkuye ta gaida Hajiya Salma da Antin Jalal, Suka Amsa mata Antyn Jalal tace
"Sannu Amaryar mu, Kin tashi lafiya?"
Take Jalila ta kuma jin wasu hawayen suna zubowa daga idon ta, Mummy tace
"Ikon Allah, har yanzu baki gaji da kukan nan ba?"
hajiya Salma tace
"haba Jalila, banyi zaton haka daga gareki ba, mun san an miki laifi amma kiyi hakuri, Jalila zakiyi Alfahari da mijinki, yana sonki fiye da yadda kike tunani, gaba daya hope dinmu yana gurin Allah kuma yana gurinki, dan Allah ki kwantar da hankalinki ku zauna lafiya, ki gode Allah, Jalal baya kule kulen mata, ke kadai ce macen dana san yana saurara, kiyi hakuri Jalila "

Cikin kuka Jalila tace

"Mummynsa fa bata sona, tace in rabu da shi, kuma ba irin maganganun da ban gayawa Ilham akan sa ba, na kirashi da sunaye marasa dadi, kuma kawai ace shi na aura"

Hajiya Salma tace

"to shine me? Mahaifiyarsa bata sonki ni ba'a gaya miki abunda tayi min ba, ita da Saudat, gidan mijina abun kaunata seda ta rabani da gidan hankalin ta ya kwanta, ko kin fison a ya auri Ilham din ne? Jalila kece zakisa zaman gidan Aurenki yayi dadi in kin so, ki manta da abunda ya riga ya wuce kinji yarinya ta, Allah ya Albarkaci rayuwar Aurenku, kije ki shirya anjima kadan zamu tafi"

"wai a maidugurin zanta zama? Makaranta fa?"

Antyn Jalal tace "A'a ba'acan zaki zauna ba, Se a inda yakeso zaku zauna, amma akwai dalilin zuwanki can ďin"
Jalila dai ba tace komai ba suka cigaba da rarrashin ta. Haka Maama tazo ta ja hannunta domin fara shirin tafiya.


Daddy ya samu Hajiya Salma a masaukinta, shar da ita bakace ita haifi Mahmud ba, sekace kaninta, har yanzu tana tare da Gayunta,
Daddy yace "To Salma kinga abun Allah ko ba zato ba tsammani danki ya samu matar Aure, kodayake na dade ina burin Jalal ya Auri yarinyar nan"
Hajiya Salma tace
"Hakane, yarinyar tana da nutsuwa da kirki, dangin yarinyar nan sun gama yimana komai, Amma daddy wai ya'akayi abun nan ya kasance"
"hmm ai shekaranjiya dana zo, yazo ya ganni muna tare da iyayen Jalila, shine suke tambayarsa ya aikinsa? yace bayason zaman lagos, nake ce musu yanayin sabanin Addini da al'adun mutanen garin ne yasa baya son zaman garin, bayan ya tafi ne, kawai Captain Abdurrasheed yace ; inyana da wadda yake so ai masa Aure ya tafi da matar can lagos, se nake ce musu bana tunanin yana da budurwa, saboda yace yasan babu me bashi 'yarsa yana wannan halin, se captain Rasheed yace; indai yana son Jalila ya bashi ita, shine aka kira Jawwad da yaron daza' a bawa ita da, aka tambayi Jawwad yana ganin in aka Aurawa Jalal ita ze zauna da ita? Jawwad yace "ai Jalal yana sonta, dan haka suka kira shi wancan yaron suka bashi hakuri, shikansa Jalal be saniba se jiya a gurin daurin Auren"

Hajiya Salma tayi ajiyar zuciya tace

"Allah me yadda yaso, kaga Al'amarin ubangiji, ba zato babu tsammani my Son yasamu mace ta gari"

"Hakane amma yaushe zaku bashi ita? Naji kince da ita zaku tafi maiduguri"

Tai murmushi tace

"Daddy kenan, yadda aka daura aure a bagas ba tareda ya sha wata wahala ba, bazan bashi yarinyar nan a bagas ba, bazamu bashi ita ba se mun tabattar da irin Son da yake mata, dagaske yana sonta kokuwa? Zata zauna damu tasanmu, sannan muyi mata shiri irin namu na 'yan barno"
Daddy yai murmushi yace "haba Salma, a takaice dai ta wani bangaren kuna son ku wahalar min da yarone kawai"
Tayi murmushi tace

"Zamu temake shi dai, yawwa sannan Jalila tana kukan matarka Khadija bata sonta har tana zarginta da Jalal, wannan karon bazan lamunci duk wani nau'i na rashin mutunci daga gareta ba, idan baka dau mataki akan wannan lamarin ba, Zeyi wuya mu bawa Jalal matarsa anan kusa, saboda nafi kowa sanin khadija nasan abunda zata iyayi, a wannan karon bazan bari ta cutar da 'yar mutane ba kamar yadda ni tayimin ba"
Ta mike tsaye tace

"daddy bari inje in karasa shiryawa, da wuri zamu tafi"

Ta wuce cikin dakin, Daddy yabi bayanta da kallo, har yanzu Salma tana nan da gayunta da iya kwalliya, nan ya dinga tuna abubuwa da dama da suka wuce a baya.

Wanda zasu yiwa Hanan rakiya tuni sun shirya dan yiwa Hanan rakiya can gidan Jawwad dake babban birnin tarayya, Hanan tasha kuka, da kyar aka banbare Hanan daga jikin Mummyn ta, daddy yayi mata nasiha Sosai, suka hau motoci sukayi gaba.

Da kyar Maama ta takura Jalila ta ci Abinci aka bata magani, Karfe dayan rana Aka gama kintsa Jalila da Nana, suka fito domin tafiya, Jalila ko ganin gabanta batayi saboda kuka.
Tunda su Jalila suka fito Jalal ya sauke idonsa akanta ta rame sosai ga idanuwanta sunyi Jawur, gaba daya tausayinta ya kama shi, ko ya takeji a ranta oho? Sosai yake jin tausayinta a ransa.

Yadda Jalila da Nana suke kukane yasa jikin Maama yayi sanyi, shikenan Nana zata bar kasar se lokaci2 zata dinga ganinta, duk kiyayyar da tayiwa Jalila a baya, bata taba zaton zataji babu dadi haka ba, Zatayi missing din yarinya me kara da kawaici, ga Jawwad shima ze tafi, zasu bar mata gidan se ita kadai, yadda Jalila ta rirrike Maama tana kuka kamar mahaifiyarta yasa Maama ta kamu da matsananciyar kunyar muzgunawaa Jalila data dinga yi, ba tayi aune ba taji itama Hawaye na bin idonta ta kuma rungume Jalila a hankali tace "ki yafemin Jalila" . Jalila ta kankame Mama tana cigaba da kuka

Abba yace

"haba in kina kuka zaki karya musu gwiwa ne, kiyi hakuri, ki gode Allah da ya nuna miki Aurensu kuka rabu lafiya"

Antyn Jalal tace

"Ai dole tayi kuka, kowace uwa haka takeji a lokacin da take bankwana da 'ya' yanta, yaranta uku zasu tafi su batta lokaci daya, maman Hanan ma tana can ta nayi"
Daddy yace

"ya za'ayi se hakuri"
Haka aka sa su Jalila a mota, ana musu fatan Alkhairi.

Mota daya Jalila, Nana da hajiya Salma suka hau, kanin Mahmud ne ze jasu, sekuma tawagar Angwaye da sauran 'yan uwansu dazasu biyo bayansu, Hajiya Salma tace Jalal ya biyosu a tasa motar, Jalila naji na gani suka ďaga suka nufi borno.


Tunda aka kira Ahmad aka bashi hakuri akam Aurensa yarasa ina zesa ransa yana matukar kaunar Jalila, sannan duk yadda zeyi yaga Jalila be samu damar yin hakan ba har suka tafi.
Yusuf kam ko sallama beyi musu ba saboda bacin ran abunda akayiwa Aminin nasa, haka kurum an hana mutumin kirki an bawa wannaan sakaran.


Daddy ma ya shirya kayansa tsaf, yayi musu Sallama ya koma kano, yayinda Abdallah ma da tawagar abokansa suka tafi yi masa rakiya kaduna kasancewar a can ze zauna.

Tuni Labari yafara karade unguwar su Nana cewar an ďaura Auren Jalal da Jalila, da yake Akwai wanda sukayiwa Maama kara sukaje mata biki 'yan anguwarsu, Labari ya zaga unguwa inda wasu suke ganin an kwari Jalila da aka Aura mata wannan mara tarbiyar dan shaye2, bayan ita kamila ce, me kirki da faran faran ga kowa, Amma duk abun nan ba wanda yaje ya Tari Mummy ya gaya mata.

Bayan la' asar Daddy ya je gida, da ya koma gida be gaya mata ba, seda yaci Abinci yayi wanka yai salla.
Suna zaune da Mummy tana ce masa "ya hanya? Ya kabaro su?
" lafiya kalau Alhamdilillah, Jawwad da iyayensa suna godiya "
Ya mike ya debo goro da alawowi dayawa ya zube a gabanta.
Ta kalleshi tace
"wannan kuma na menene? "
" Na Auren ďanki ne"
"ďana kuma? Wanne ďan nawa, daza'a abani wannan kayan haka?"
"Aike yaran naki ukune, ga Jawwad, ga Mahmud, ABDUL JALAL"
"Jawwad din dai, Mahmud ba ďana bane, sannan ba wanda ya isa yayiwa Jalal Aure ba da izinina ba, idan ma anyi ko 'yar uban waye se an fasa shi, kodayake wace mace ce zata yadda ta Auri wannan ďan naka?"
Daddy yace "to shikenan tunda baki yarda ba"
Ya dau remote ya kunna tv abunsa. Ta shi tayi tabar masa palourn ta koma dakinta, tunani ta fara yi, tasan daddy da zolaya wani lokacin, Amma kamar in serious tone yayi maganar, tana cikin tunanin ne wayarta ta fara ringing, seda ta kusa tsinkewa hankalin Mummy ya kai kan wayar taje ta ďaga
"Salamu Alaikum"
Mummy tace "wa'alaikum salam, hajiya Rahama barka da yamma"
"yawwa Mummy ya gida ya taro?"
"taro kuma?"
"Au tambayata ma kikeyi? Baban su yacemin ;yaje ďaurin Auren ďan gidan Alhaji Usman a bauchi, ashe bayan na Mahmud har dana Jalal amma baki gaya mana ba, na miki magana ta what's App bakiyi responding ba"
Ai Mummy bata jira me zata karasa cewa ba ta kashe wayar ta kunna data aikuwa messages suka dinga shigowa ana mata Allah ya sanya Alkhairi, wasu na mata mitar bata gayyacesu ba, jifa tayi da wayar kan gado ta nufi part din daddy
"dama dagaske kayiwa Jalal Aure ba da izinina ba? Akan me? Saboda me?"

"haba Deejah, kefa kikace Jalal ya isa Aure, to menen laifi a ciki dan namasa Auren? Kuma ma yana son matar da'aka Aura masan"

"Sekuma nace kayi masa Aure ban saniba, wane irin wulakanci ne wannan? Wallahi baku isa ba daga kai har munafukan da kuka hada kai aka masa Auren"

Sintiri tafara yi a dakin, wani irin gumi yana tsatstsafo mata ita Daddy ze yiwa haka?
A fusace Tace

"Tukuna ma 'yar gidan ubanwa aka Aurawa masa ba tareda masaniyata ba? Kowace' ya ce wannan ta tarowa kanta abunda bazata iya ba, dan sena ga bayan Auren nan Wallahi, sena murkusheshi, bazan taba bari Jalal ya zauna da matar da bani na zaba masa ba, dan babu yarinyar da zan yadda ta juya min ďa, nasan baya son Ilham shiyasa na dage ya Aureta, Amma yanzu Ace an min bazata an rusamin shirina baze yuwu ba wallahi "

" Shikenan deeja abunda kike gudu akan ďanki fa se ya faru, Sannan koma wacece zatazo har nan ta gaisheki seki ganta.







Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️

What's app only 07063065680.
Follow me onWatpad @Ayshercool7724
..🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔸𝔻𝔼ℝ𝕊💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 5️⃣0️⃣ 103

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724



_MY FIRST NOVEL _




Da Sauri Mummy ta sha gaban Daddy tace

"Wallahi Habib seka gayamin dan me zaka yiwa Jalal Aure ba tareda nasani ba? Sannan kuma 'yar ubanwa aka Aura masa? Wato kaje kun haďa kai da wannan munafukan' yan uwan naka aka Aurawa ďana yarinya ban sani ba, to wallahi baze yuwu ba, ďa dai nawane nina haifi abuna, dan haka ba'a isa a yanke masa hukunci game da rayuwarsa ba tareda sani na ba"

"sekuma kiyi, naga yadda zaki raba Auren ai, indai Jalal ne gaki nan gashi, dai dai yake dake, Akan kira bashi da yarinyar nan zaki kuma lalata alakarki da shine kawai, dan nagaya miki yana sonta"

"karyane Wallahi, Jalal bashi da wata yarinya da yake so, Yarinyar dana zaba masa ita ze Aura"

Dama daddy yasan ze fuskanci wannan kalubalen daga matar tasa, dan haka ya ture ta daga gabansa yabar mata palourn.

Se magariba Su Jalila suka isa garin maiduguri, koda sukaje sun gaji sosai, musamman su Jalila, su da suka sha hidimar biki, basu huta ba akayo wannaan uwar tafiyar.

Gaba daya Jalila ji take jikinta kaman ba nata ba saboda gajiya, har suka je maiduguri kanta a kasa yake, se dai ta jimgina da jikin Nana, ko mota tayi bacci, in aka jima ta shige cikin mayafinta tayi kuka, har sukaje Jalila bata kula kowa ba seda taji an tsaya ance sufito.
Gidan da akayi parking din motar ne yayi awon gaba da tunanin ta, sekace ba a duniya ba, kallo daya zakayiwa gidan kasan mamallaka gidan sunyi hannun riga da talauci, ko da suka fito daga motar Se guďa akeyi, Jalal idonsa gaba daya yana kan Jalila da take a takure, Suka nufi cikin gidan, tun daga harabar gidan wani irin sassanyan kamshi ke tashi, har zuwa cikin gidan, cikin gidan da'a akwai mutane a gidan da sukazo domin karbar Amaren.
Cikin gidan ma kamshin da yake na musamman ne, fiye da na harabar gidan.
Aka basu ďaki, suka gabatar da sallolin da suke kansu, Sannan aka kawo musu Abinci, Jalila da Nana ne kawai a dakin dan haka Nana tace

"Jalila ki daure kici Abincin mana"
Girgiza kai Jalila tayi tace

"Na koshi, ke dai kici kawai, ni kaina kemin ciwo"

"to ko inyi musu magana a nemo miki magani?"

"A'a base kinyi hakan ba, A yanzu dai babu wani magani daze warkar min da wannan ciwon kan"
Suna cikin wannan mujadalar ne Anty ta shigo da tray din fruit a hannunta tace
"Jalila kuci Abincin mana, ga dangin baban Jalal can suna son ganinku kafin su tafi"
Nana tace
"Anty Jalila taki cin Abincin, wai kanta ke ciwo"
"Subhanallah har yanzu kan ke miki ciwo? To daure kici Abincin se a kira likita ya dubaki"
Da kyar Jalila ta cakali Abincin nan ta barshi.
Suka fito parlour inda dangin Daddy keson ganin Amare, se hausa suke suna hadawa da yarensu, sunga fuskar Nana yayinda Jalila ta dukunkune a mayafi taki bari su ganta, dare ya farayi sukayi musu nasiha da Addu'oi, tareda jadadda godiyarsu ga Jalila sannan suka watse a hankali.

Dakin da'aka bawa Su Jalila yana da kyau da matukar girma, suka koma suka canza kaya, Hajiya Salma da kanta ta kawowa Jalila magani ta sha, tana shan maganin ta nemi guri ta kwanta tayi lamoo akan gado, tana missing din wayarta, tun randa Jalal ya kwace be kuma bata ba, tana son tayi amfani da wayarta amma ya rike a gurinsa sekace shi ya saimata.



Nana na kwanciya Mahmud ya kirata a waya, Suka dinga hira suna soyewa, kaman ba gobe zasu tafi ba, suna ta soyayya gwanin sha'awa, Jalila ta tuna kowacce ta samu zabinta, ta auri wanda take so suna cikin farinciki amma banda ita, an haďa ta da wanda be damu da kansa ba ma balle wani, take taji wasu hawayen na zubo mata, ta tabatta Auren Jalal wani sabon shafi ne na kaddarar Rayuwarta.


Hanan kam gidanta yana da girma amma ba can ba, Amma ya tsaru anyi masa gini na zamani, dauke da wadataccen gini, an kashewa gidan kudi sosai, Sannan daddy ya zuba mata kaya yadda yakamata. Wanda sukayi wa Hanan rakiya suna zuwa a ranar suka juyo gida, suka barota tanata rikici, Seda kowa ya watse bayan sallar magariba sannan Jawwad ya shigo gidan, ya sameta tayi zaman dirshan a kasa ta jingina da gado, ta takure kanta sosai, tayi kuka harta gaji, dan girgiza kai yayi ya karaso gabanta ya tsuguna se kamshin turare yake, A hankali yace

"Haba Hanan, kukan ya isa haka, i know you miss home, Amma ba gani ba, sekace wadda akayiwa auren dole, ko kin dena sona ne?"
Girgiza masa kai tayi alamar A'a

"Yawwa my love 😍, kukan ya isa haka, yau ranar daza muyi farinciki ne, kar kanki yayi ciwo, ko nima kina so ki sani kukan ne?" ya fada yana goge mata hawayen fuskarta.

A hankali tace "A'a ni karkayi kuma nadena kukan" tai maganar cikin shagwaba

Murmushi yayi mata yace "Yawwa ai nasan baza kiso ki ganni ina kuka ba, shiyasa nima bana son ganin kukanki"
Haka ya cigaba da rarrashin ta har ta dan saki jiki tana hira, Jawwad da kansa yaje kitchen ya dakko plate da cups, ya bude musu kazar da ya shigo da ita, ya cika mata kofi da youghut me sanyi, yace "Bismillah"
Ta kalli kazar ta kalleshi tace "Ni na koshi"
"me kika ci da kika koshi?"
"bakomai" ta bashi amsa, ya lura gaba daya a firgice take, har hakan yaso ya bashi dariya amma ya maze ya ďan bata fuska yace

"in baki ci ba, zan kwana da yunwa ne, kuma ni inajin yunwa sosai, tunda aka fara biki bana samun cin Abinci fa, se Ulcer ta kamani ko?"
Yai maganar a ďan shagwabe, dariya ya bata tace

"in Ulcer ta kamaka ba rabin zamce ai, Dama haka ka iya shagwaba, wallahi tayi maka kyau"

tai maganar tana dariya, cikin hikima yanayi ya namata hira ya dinga bata kazar tana ci, seda suka kammala, Jawwad ya jagorance su sukayi Sallar nafila, domin nuna godiyarsu ga Allah da kuma fatan zaman lafiya me dorewa a cikin Rayuwar Aurensu.
Se Hamma take tana lumshe ido, da alamun gajiya da kuma bacci a tareda ita, Jawwad ya kalleta yace
"Wannan hammar da kike karki hadiyeni mana"
Tayi dariya ta Mike, tana cewa "gara in hadiyaka in huta ai"
fita Jawwad yayi domin rufe kofofin gidan, da kuma tabattar da komai lafiya.
Hanan ta canza kaya, ta nemi guri ta kwanta, wani nannauyan bacci yayi awon gaba da ita.
Cikin baccin nata ne tana kokarin yin juyi ta jita a jikin mutum, a hankali ta bude ido tace "Haidar"
"My love" ya amsa mata
"bakayi bacci ba?"
"Banyi ba"
"meyasa?"
"ina tunani ne"
"Nasan me kake tunani, be wuce su Jalila ba, ni na gaya maka komai ze wuce, zasu koma normal, Jalila tana son Jalal, kawai dai kasan ta da taurin kai"
A jiyar zuciya yayi, ya kuma kwantar

Please Login or Register in order to submit comment